Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke damunta.

Da sallama yashigo, karɓa masa tayi batare da ta ɗago ta kalleshi ba, wanja ƙafarta yazo ya zauna sannan ya gaisheta haɗi da jingina kansa a ƙafarta.

Yajima ahaka amma bai ji tayi masa abinda take masa ba, wato tasanya hannuta akansa tana ya mutsar masa suman kanshi, haka take masa tun yana yaro shiyasa yake son tayi mishi haka.

Dubanta ya yi har ya buɗa baki yayi magana sai yaji muryar Dady na faɗin,

Ɗan Hajiya saukar yaushe?".

" Duk da yanzu ka girma shiyasa naga ko tafiya zakayi babu dole kasanar damu".

Murmushi yayi haɗi da basu haƙuri yace tafiyarce ta zo a bazata, sai Dady yace to muma yau zamuyi maka baza ta, dan tabbas ƙarshin watannan zamu ɗaura maka aure da wadda duk wadda muka ga dama, amma idan kaga mu bamu isa da kai ba kaje kagayawa Hajiyar da ke goya maka baya.

Har ya buɗe baki yayi magana sai Dady yace bana son jin komai daga gareka nariga na gama magana sai ka farashirin karɓar amarya kai da abokanka da ƴan matan ka.

Dady na gama faɗar haka suka barmishi parlour kanshi sai juya masa yake.

Yau saura kwana biyar a ɗaura aure Kabir da amaryarshi Nana, kuma a yau ne Kabir yake so ya gayawa Mumy zaiyi aure, danshi koda gari ya waye ba inda yaje, duk abinda take son shi yake yimata, sai kwasar soyayyya suke ta mutunci, ita ko Mumy sai kafa-kafa take kar tayi abinda zai ɓata mishi rai, ranar gida ya wuni har dare, bayan sunci abinci sunyi wanka, dan yau ko wanka tare sukayi , har man shafawa shi ya shafa mata haɗi da sanya mata kayan bacci waɗanda ranshi ke so, kallonta yayi ciki da nuna mata tsantsar so yace,

" Baby wallahi sonki ko da yaushe ƙara ruruwa yake a zuciya na, dan Allah ki taimaka min kici gaba da zama dani kada ki barni, duk da a halin yanzu ni mai laifine a gareki".

Bata ce dashi koma ba ta haɗa bakinshi da nata waje ɗaya suna kissing ɗin juna, sai da sukayi son ransu sannan tace,

" Baby duk yadda kake sona ni nasan nafika sau dubu wallahi soyayayarka zata illatani dan Allah kar ka barni, burina a koda yaushe naganin tare da kai".


" Muna tare masoyiya ta, ba wanda ya isa ya rabamu ko anƙi ko ansu dole abarmu, amma ina so ki fahince ni, wallahi nima badan son raina haka zata faru ba, kiyi haƙuri kinji, saboda Mumy ce ta haɗa ni da ɗiyar abokiyar ta, wai ita yarinyar ce ta ganni wai ba wanda take so sai ni, duk wanda yafito tace sai ni, shine su Baba suka ce tunda yarinya tace ni take so nayi haƙuri ayi aure, tun kafin na buɗa baki sai Mamarta tace komai ta ɗauke min har sadaki itace zatayi komai, burinta kawai na aure yarinyar, shine Baba yace to tunda haka ne ranar alhamis za'a ɗaura aure".......wata ƙarace Mumy ta sanya wadda gidan gabaki ɗaya sai da ya amsa.....





*SUMMY M NA'IGGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*





*SHAFI NA 18*

Tashi sukayi kai suka fita, ɗaki ta rufe kana suka kama hanya zuwa dubin Baban Ahamad, mai napep suka tsayar Ahamad ya gaya mishi sunan unguwar da zai kai su, tana jin sunan unguwar tace itama idan sun gama dubiyar Babanshi itama su zo aduba Babanta, yace da ita ai ba damuwa Allah ya basu lafiya.

Dai-dai ƙofar gidan mahaifinta yace mai napep ya tsaya, kallonshi tayi sosai amma ta kasa buɗa baki tayi magana.

Bayan sun sallami mai napep suka kama hanyar shiga gidan, gabanta ne yayi mummunar faɗuwa lokaci ɗaya wani jiri ya fara ɗi barta.

Faɗuwa ta tafi tayi Ahmad da sauri ya rungumota haɗi dayi mata sannu, kallonshi ta farayi amma ta kasa magana har suka shiga ɗakin da yake kwance sai wari yake saboda yayi kashi kuma anrasa mai kula dashi.

A wannan lokaci Ahmad ne ya rufe hancinsa, ita ko saboda shiga ruɗani ko warin ɗakin bata jiba, a hankali ta buɗa baki tace,

" Ahmad shine ma haifinka?".

Bai ce da ita komai ba ya riƙo hannuta yafito waje kana yace,

" Kiyi haƙuri Baby nazo dake wannan wajan ko?".. ...tsawa ta daka masa tace,

" Tambayarka nayi kabani amsa?".

" Eh shine Hauwa, nasan bai dace yazama ubana ba ko, kiyi haƙuri nima bana jinshi a matsayen uba".

Hannu Hauwa ta ɗaura saman kai kana tace,

" Shikenan tawa ta ƙare!.

Ta faɗi haka hawaye na zuba a idonta.

Da sauri ta bar wajan cikin tafiyar gudu-gudu sauri-sauri.

Ahamd na ganin haka shima ya fara sauri yana kiran sunanta amma ko wagowa batayi ba bare yasa ran zata karɓa.

Yana ciki sauri dumin ya kamota sai ga mai napep ta tsayar shiga tayi haɗi da faɗa masa inda zai kaita tace yayi sauri.

Dai-dai ƙofar gidansu aka sauke ta, kuɗi ta bashi batare da ta karɓi canji ba tashiga gida hankali tashe.

Tun a soron gida ta fara jin hayaniya natashi haɗi da jin sautin kukan Babarta, cikin azama ta faɗa gidan kamar walkiya, abinda idonta yaganine yasa tayi tsayuwar daba tashirya ba.

Kayan ɗakin Babarta ne aki fitar wa waje ga Alhaji Abu na tsaye yana faɗin wallahi in har bazaki zauna wancan ɗaki ba wallahi sai dai ki bar gidannan da tabbas ba wanda ya isa ya hanani aure......tun bai kai ƙarshin zanci ba Hauwa tayi dirar mikiya kansa tace,

" Aure ? da wace abu zakayi aure? wace kaddararrace zata aureka?".

" Uwaeki ce kaddarra ita da ta aure tsohon ɗan tashi irin ubanki".

Ido da hanci Hauwa ta saki tana kallon Alhaji Abu, a hankali ta furta mike shirin faruwa dani ne!.

Bayan su Mumy sun sauka gida ɗaki ɗaya aka warewa Hansa'u akace shine ɗakin ta, kuma idan bai mata ba za'a sauya mata ɗaki, godiya tayi harda kukanta saboda wannan kularce bata samu ba a wajan Babarta.

Kwanan shi biyar garin abuja sannan ya dawo gida, kai tsaye part ɗinshi yashiga, wanka yayi sannan ya nemi waje ya kwanta dan ko iyayenshi basu san ya dawo ba bare abokanshi, sam ya manta da wata yarinya gaba kiɗaya ya manta da ita bare yace yaje gidan hutawarshi.

Baccinshi yayi mai isarshi sannan ya tashi yayi wanka kana yayi sallah sannan ya fito dan ya gsishe da Mumyn shi.


Abdulrazak kenan yaro kyakyawa ga kuɗi ga aji.

Koda gari ya waye ya je karɓar mashin akace ba'a kawo ba sai sati mai zuwa, dan haka yazo ya shaidawa Mumy halin da ake ciki da ta tambayeshi ba kasuwa yaje saya ba, sai yace akwai wanda yayarda dashi kuma shi mutmin yasan mashin mai kyau shiyasa ya bashi yaje legos ya sayo masa.

Sai Mumy tace ai tunda ga kuɗi isasu da kasaye abunka anan yafi tsayawa jiran aje logos, yanzu da hanya ba kyau.....har ta buɗa baki tayi magana ya daka mata tsawa yace,

" Badan kin bani kuɗi bane zaki tsareni da faɗa, idan kuɗin ki kike so sai a mayar miki ai ba dole, kuma ba roƙonki nayi ba ke kikayi ra'ayi ki bani, sannan zaki zo ki tsareni da maganar banza".

Jiki a sanyaye Mumy tazo ta faɗa jikinshi tana faɗin,

" Dan Allah Baby kayi haƙuri wallahi ni ba haka nake nufi ba dan Allah Baby".

Ta faɗi haka kamar tayi kuka.

Tsaki ya jamata haɗi da tunkuɗeta daga jikinshi ya tashi ya shirya yafice gida.

To tundaga lokacin ya sauya ma Mumy, idan ya fita gida baya dawowa sai ƙarfe ɗaya na dare idan kuma gari ya waye tun ƙarfe bakwai na safe yafice kuma sai ƙarfe ɗayan dare, Mumy tayi kuka har ta zuba masa ido, shiko duk ba komai ke riƙeshi ba sai hidimar bikinshi......


Commen and share.


*SUMMY M NAIGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*MARUBUCIYA*
*UMMU JA'AFAR✍️*




*SHAFI NA 20*


Haɗe yayi a jikinshi haɗi da buga bayanta, sosai ya kijin yadda take sauke zuciyar, haƙuri ya fara bata kana yace,

" Kinsan Allah duk son da nake miki da kinyi min haukar nan da mata keyi wallahi zaki sha mamaki dan wallah zan baki horo wanda bakiyi tunani ba, shawara nake baki gara ki natso ayi komai cikin kwanciyar hankali".

Yana faɗar haka ya sauke ta daga jikinshi cikin nuna ɓacin rai

Tana ganin haka ta tashi jikina na karkarwa tace,

" Baby karka damu wallahi na ɗau alƙawri bazanyi tashin hankali ba, amma kasan dai dole nayi kishi akanka ko?".

" Naji".
Haka yace da ita a taƙaice.

Fuska haɗe ya tashi ya shirya ya bar gidan ko beark bai tsaya yayi ba, ba yadda batayi ba yace a'a akwai inda zai je.

Badan taso ba haka yashirya ya bar gida.

Tunani ta fara tayaya za ta karɓo mijinta dan itakam tabbas bata son ya barta, sosai take sonshi , dan haka dole tayi haƙuri ta nuna kamar ba komai ba ne.

Tundaga ranar bai sake zama gidaba kullum yana can shida abokanshi da ƴan uwanshi ana shiri-shirin aure, ana gobe ɗauren aure shine bai shigo gida ba sai ƙarfe biyu saura na dare.

Har wannnan lokacin zaune take sai tunani take haɗi da tunanin Hansa'u shikenan tunda ta koma gidan kakarta ta barta ko, to ko ita bazata nemeta ba, taje can wajan dangin ubanta ta zauna, tana cikin haka yashigo tashi tayi ta tarɓoshi, abinci ta kawo masa amma yace ya ƙoshi, wanka yayi ya kwanta batare da ya kalleta ba, taso susha soyayya ta bankwana, dan tasan ita dashi sai bayan kwana biyu amma yace shi yagaji ko ruwan jiki bashi da yanzu dan haka ta saurara masa .

Tashi yayi daga kwanciyar ya kai dubanshi gareta yace,

" Saboda kina baƙin ciki zanyi aure shine baki je komai na biki ba bare kije kiyiwa iyayena Allah ya sanya alhairi ko?".

"A'a daman nace bari sai gobe sai naje da safe inyaso sai dare zan dawo".

Tsaki yaje ya koma ya kwanta ya barta zaune tana ta gumi, ahaka bacci yayi auwon gaba da ita.

***********

Hanyar da suka bi ya bi da kallo yana tunanin maganar da iyayenshi suka faɗar masa, to miyayi zafi haka da zasu yanke masa wannan huƙunci, ko wani abu aka zo akace yayi?.

Ahankali take taka ƙafarta cikin shigar da tayi riga da sikt na atamfa, sosai tayi kyau, kwanan biyu da tayi gidan har haskinta ya fito ta kuma wata ƴar lokota sosai tayi kyau ba kaɗan ba, mutsin da yaji ne yasa shi ɗaga ido a tunaninshi Mumy ce ta dawo, idonshi ne ya faɗa kan fuskar ta, lokaci ɗaya ya mike tsaye sai yanzu ya fara tunan yarinyar da yarufe gidanshi, bata kula dashi ba har ta ɗau abinda zata ɗauka ta koma ɗaki, ido ya kifa mata har ya daina ganinta sannan ya fita cikin tashin hankali.

Kai tsaye mota yashiga ya fige ta bai tsaya ko ina ba sai gidanshi, Baba mai gida tunda ya buɗe masa get yake ta gaisheshi amma ko kallonshi baiyi ba bare yasa ran zai karɓa masa, bedroom ɗinsa yashiga wayam yagani bai ganta ba, gabanshi ne yayi masifar faɗuwa, lokaci ɗaya ya ƙara tuna yarinyar da yagani gidan iyayenshi.

Cikin zafin nama yafita zuwa wajan mai gadi, ko gaisuwa bai tsaya sunyi ba ya tambayeshi waya shigo gidannan da baya nan? kai tsaye mai gida yace ba wanda yashigo, wuyan Baba mai gida ya cinkomu ya matse haɗi da zari ido yace,

" Wallahi ko ka gaya min ko yanzu nayi maka yankan rago wajannan".

Irin yadda yaga idonshi sun sauya sun koma kalar ja lokaci ɗaya yasa Baba mai gida cikin rawar ɗari yace,

" Alhaji ne yazo shida Hajiya suka.....kasa ƙarasawa yayi......tsawa ya daga masa yace,

" Suka yi me!".

Hanyar bedroom ɗinsa ya nuna masa da hannu yace,

" Suka shiga".

Hannu ya ɗaga zai wanke tsohon mutane da mari, kuma miya tuna sai ya fasa.

Tunkuɗe shi yayi sai da ya faɗi ƙasa kana yashiga mota ranshi a matuƙar ɓace, to waya gayawa Dady da Mumy ya kawo wata gidan? tabbas in ba abokansa ba to wannan tsohon mai gadi, dan yasan suna shiri da Dady kuma asali ma Dady ya kawoshi gidan dan yayi masa gadi.

Kai tsaye gidan iyayen nashi ya koma.
==========
Hawaye ne suka fara zubar masa kana ya dube Ahamd baki na rawa yace,

" Amma ba abinda ya haɗaku da Yayar taka ko?".

Ya faɗi haka a ɗan tsorace.

Ahamd bai samu damar buɗa bakinsa ba ya fito ɗakin da Baban nasu yaki ciki da tashin hankali, kai tsaye gidan Babarshi ya isa, koda yaje tana ɗaki ita da mijinta.

Ko sallama baiyi ba ya faɗa ɗakin, da sauri ta tashi tasaka hijab ɗinta haɗi da rufe mijin nata da zanin gado kana tace,

" Ahmad wai yaushe ka lalace! ashe zaka iya shigowa ɗakin nan batare da neman izini ba, kasan halin da zaka tarar damu? ai ko ba komai yana da kyau kayi sallama"......hannu ya ɗaga mata yace,

" Ni bashi nazo ji ba, yau ina so ki sanar dani waye mahaifina, kuma ya muke da wancan dakike cewa shine mahaifina".

Hannu ta ɗaura akai tace,

Yau minake shirin ji ko gani, Ahmad yau ni zaka zo kacewa haka!?".

Ta kai ƙarshin zanci tana kuka.....



*Comment and share*


*SUMMY M NA'IGE✍️*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment