Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wannan sabuwar rayuwar ta ce, "to Narjeesah muna godiya sosai zamu tashi wannan gidan mu barwa sauran yaran mu da sukayi Aure, ke kuma da mun koma zaki bi mijin ki, ku ɗauki ɗanku ku tafi dashi Allah yayi maki albarka ya huci zuciyar ki, ya ƙara maku haƙuri ya baku zuri'a ta gari mai albarka, mun gode sosai Narjeesah yar Albarka keda sauran yan uwan ki da abokan ku duk Allah ya albarkace ku da iyalin ku baki ɗaya ".


Duk muka amsa da, "Amin " Baban mu kuwa farin ciki kawai yakeyi, su kawu da goggo kuwa, hawaye suke sharewa.


Haka akaci gaba da fira, kullum cikin farin ciki muke shirye_shiryen tafiya akeyi mutane sai zuwa taya murna sukeyi Shuraim kuwa tun da safe idan yaci abinci akayi masa wanka bana sake saka shi a idona sai dare idan yayi bacci.


Yau tun da safe Humaira take sanar damu su Salman suna a hanya, tun a lokacin nake jin wani irin, ganin idan fa yazo zan bar su Umma dasu Amrah da gani sai Shuraim, kawai naji kuka ya zo mani.


Sun fahimci abunda nakeyi wa kuka dan haka suka shiga bani baki.


Ƙarfe goma na safiya suka iso nasan kuwa a garin mu suka kwana, tare da motocin ɗaukar kaya suka zo, ai kuwa aka shiga fitar da kayan mota ake saka su, gidan gaba ki ɗaya muka fito motoci muka shiga, aka rufe gidan muka ɗauki hanya........



*Comment and share*



*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


💐💐 *NARJEESAH* 💐💐


*Rubutawa*
*NANA KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*

*ELEGANT ONLINE WRITERS*

_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_

🔚

5⃣6⃣⏭️6️⃣0️⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Alhamdulillah mun iso lafiya cikin amin in Allah, tun lokacin da muka ɗauki hanyar unguwar mu, su Mariya aka fara buɗe ido, suna kallon yanayin unguwar, bamu tsaya ko ina ba, sai bakin kofar gidan mu, su Yaya Aliyu basu ma shiga cikin gidan ba, sukayi tafiyar su, mu kuwa fitowa mukayi, muka dum fari bakin get ɗin mu, na fara ƙoƙarin buɗe get ɗin, duk da ido suke bin mu cike da mamakin ganin irin wannan haɗaɗɗen gidan.


Kasa hakuri Yaya tayi tace, "anya kuwa Narjeesah gidan ne kuwa? "


Murmushi na sakar mata, ban bata amsa ba, har na buɗe gidan Shuraim da gudu ya riga kowa shiga, su Yaya Auwal suka ɗauki kayan suka mara masa baya, Umma kuwa ita ta yiwa su Inno jagora suka shiga cikin gidan kwasar kaya muka tsaya yi, na baiwa Auta makullin ƙofar falon, ai kuwa da sauri ta shiga ciki dan ta buɗe masu ƙofar, muka ɗauki kayan muka mara masu baya, a bakin kofar falon na ajiye masu na dawo na rufe get ɗin, na juya na shiga cikin falon.


Koda na shiga duk sun baje a tsakiyar falon wasu a kujeru wasu a ƙasa, nida Amrah Nusaiba da Humaira da Hindu muka haye sama, ɗakin Umma muka shiga muka kwashe mata kayan ta, muka dawo dasu cikin ɗakina, muka shirya mata komai nawa kayan kuwa a akwati suka zuba su, da kayan Shuraim.


Bayan mun ƙarasa ne, muka fito muka shirya wa Inno nata, ɗakin inda muka kwashe kayan Umma, a ɗakin kusa da Inno muka shirya wa Yaya nata, haka Mama ma mukayi mata, muka sauko Amrah ce ta sanar dasu, suje ta nunawa kowa nasa ɗakin, haka kuwa akayi Mariya a ɗakin su Amrah aka kai nata kayan, su Zuwaira Shamsiyya nasu ɗakin daban.


Su Yaya Auwal kuwa a ɗakin ƙasa suka zaɓa sai farin ciki suke yi Baban mu ma ɗakin sa yana sama yana daga gefen nasu Inno.


Kai Alhamdulillah gidan kam sai sam barka kowa ka gani a cikin farin ciki yake, kamar wanda akayi wa albishir da kujerar makka.


Bayan komai ya dai_dai tane, su Humaira suka tafi, gidan iyayen su, mu kuwa duk yam matan a kicin muka haɗu domin shirya abinci, saboda basu san takan komai ba hakan ya saka muka dage gurin koyar dasu, bayan mun kam mala ne, Zuwaira Basira da Shamsiyya suka ni a gaba suna ƙara neman yafiya a gare ni, nikam na ce dasu, "na riga da na yafewa kowa dan Allah abar tuna baya".


Godiya sukayi mani, haka muka yini cikin farin ciki muka tashi cikin farin ciki, su Mommyn su Humaira da Hindu da Haleema, duk sun zo tare da yaran su, sosai suka nuna farin cikin su da jin daɗin su, akan dawowar familyn mu guri ɗaya.


Bayan kwana biyu, muna zaune anata fira, nace, Yaya Auwal gafa motoci nan guda biyu a harabar gidan nan muje ka zaɓi wadda kake so, ɗayar kuma su Yaya sai ku san yanda zakuyi da ita, dan nikam na mallaka maku ita halak malak amman Yaya Auwal shi ɗaya yake da wadda ya zaɓa"


Cike da farin ciki muka doshi harabar gidan ai kuwa Anty Asma da Anty Basira suka zaɓar masa, shi kuwa kukan farin ciki yakeyi musam man lokacin da na bashi makullin motar su kuma na basu makullin ɗayar.


Yau ne a tarihin rayuwa ta naji Mama ta kama hannu na, ta rungume ni, tana zubar da hawaye tana faɗar, "haƙiƙa ɗan hakin da ka raina shine yake tsone maka ido, haƙiƙa ko wane ɗan adam Allah ya rubuta masa arzikin sa, a haƙiƙa zafin nema baya kawo samu, tabbas hassada gamai rabo taki ce, na yarda da wannan Narjeesah tun daga lokacin da Allah ya nuna mani, cewar bani da dubara kuma babu wanda yake tserewa ƙaddarar sa, kuma yan zun na ƙara yadda da cewar, mutum yana tare da arzikin sa, Narjeesah gashi Allah ya nuna mani da ido na, cewar ke ɗin dai da nake fatan naga kin dauwa ma a cikin baƙin ciki, sai gashi Allah ya nuna mani, ke baiwar sace, shine mai tsara komai akan bayin sa, gashi dai a ƙarƙashin ki yau muka dawo, ina riƙon Allah da ya yafe mani,




kuma kema ki yafe ni, kada kiga laifin yan uwan ki na rashin sonki nace na ɓata ki a gurin su, ada ina dariyar kinyo cikin shege duk da na fahimci kin ɓiye wa kowa gaskiya ne, kuma ni kaina na fahimci cewar cikin jikin ki, ba shege bane, tun lokacin da na fara shegan ta cikin na fahimci hakan amman a lokacin bana sonki da farin ciki shiyasa nayi ta, zagin ki ina saka kowa ya kyace, ki, Narjeesah tabbas duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba, to shi tashi tukunyar ko zafi ba zatayi ba, kuma tabbas na yarda da cewar mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege dan bai sani ba ko ya haifa, sai gashi ina zagin ki ashe nima a cikin ɗaki na, akwai shegu har huɗu, dan Allah kiya feni wallahi haƙin kine yake bibiyar rayuwar mu...


Kuka mai cin rai Mama ta fashe dashi tana mai dur ƙusawa a ƙasa saman kafafuwan ta, da sauri na ɗago ta, nace, "Mama na daɗe da yafe maki Allah ya yafe muna baki ɗaya ".

Riƙa ta nayi muka dawo cikin gidan a gurin Umma taje neman yafiya kuma Umma tun kafin tayi maga ta ce, ta yafe, haka su Inno duk sun yafe kowa ya yafi kowa, sai zaman lafiya akeyi, da godiya a gurin na, sai da na fara jin haushin hakan har ina ɓuya, sai da suka nemo ni.


Satin mu biyu da dawowa aka sake gyara mani jiki tare da kitso da lalle, kullum cikin nasiha su Inno Mama da YAya sukeyi mani, mai shiga ciki, tattalin miji tsabar ƙirsa iri daban_daban wani lokacin har kunya suke bani, gyaran jiki kam ciki da waje, komai zam_zam sai sam barka.


Yau muna zaune Yaya ta bani zuma ina sha mukaji tsayuwar motoci, Shuraim kuwa da gudu ya sauka jikin Inno yayi waje yana kiran "Daddy Daddy "


Duk mun ɗauka shirmen sa ne, kawai naji muryar Salma tana faɗar, "Antyn mu Narjeesh nayi fushi gaskiya"

A da sauri na tashi na tar yota muka baje a falo suka shiga gaisawa da mutanen gidan, na ce, "Inno Gaggon Shuraim ce, kan war Daddyn Shuraim ce, fa".


A da sauri su Shamsiyya dasu Mariya suka zazzauna a kusa da ita sai gaisuwa akeyi, Amrah ta kawo mata abun taɓawa, fira kawai mukeyi, Daddyn Shuraim ne ya shigo ɗauke da Shuraim suna dariya Muhseen yana biye dasu, su Mom ne suka shigo harda Dad, da sauri muka tarbe su, suka zazzauna suka shiga gaisawa dasu Inno, Baban mu ne, ya fito cikin farin ciki, suka gaisa dasu Dad, Umma kam ana gama gai sawa ta bar gurin, sai su Inno ne a gurin, Mom tace, "to mufa yau mun zo tafiya ne da 'yata da jikan mu da fatan zaku yarda da ƙoƙon barar mu".


Dariya aka shiga yi, nikam jinin jiki na, nasha, Dad ya ci gaba da faɗar, "kuyi haƙuri da abunda ya faru gashi dai suna da Aure amman ba'ayi biki ba, duk da mukam a can london mun sha bikin mu babu ango babu Amarya, gashi kuma shima Shuraim ba ayi hidimar bikin haihuwar sa, ba, amman idan ranar cikin shekara biyar ya zo da haihuwar zamuyi masa bikin sa, dafatan zaku duba yanda abun ya kasan ce, ku daure ku bamu, wannan kyakykyawan irin naku mai albarka, dan ci gaba da samun yaɗo".


Dariyar manya su Baban mu sukayi, Baban ya ce, "to Alhamdulillah Narjeesah dai ta kuce daman iyayen ta, sun gama shiri, suna jira ne kawai daga gareku, kuma tun da Allah ya kawo ku, sai muce, Allah ya dai daita hankalin su, ya bada zuri'a mai albarka ".


Da amin aka amsa, Yaya tace, "to Salman Narjeesah abunda nake so daku shine, dan Allah ku zauna ku fuskan ci matsalar ku, kada ku yarda ko da Shuraim ne, ya gane cewar bakwa shiri a tsaka nin ku, ku zauna lafiya ku iyaye ne, kuma yan zun kun fara girma tunda Allah ya mallaka maku Shuraim, tarbiyar sa idan ta gyaru daga gare ku ne, idan kuma aka samu akasin hakan, Allah ma ya kyauta duk akan ku haƙƙin yake, dan Allah ku zauna lafiya Allah ya zaunar daku lafiya ya baku zuri'a mai albarka ".


"Amin" aka amsa sosai akayi muna nasiha mai shiga jiki, aka ce, naje nayi sallama da Umma su Amrah su kwashi kayan mu, su fito dasu waje.

Haka naje gurin Umma ina kuka nake neman yafiyar ta, ta janyo hannu na, ta zaunar dani a jikin ta, atake naji wani irin farin ciki ya mamaye ni, ta ce, "bani da matsala da irin tarbiyar da kike dashi, kuma nasan bayanin da zanyi maki su Inno sunyi maki fatana kawai shi, kiyi hakuri ki rungumi mijin ki da ɗanki, kada aji kanku, ina son naji kyakykyawan albshir nan da wasu watan ni daga gareki idan kikayi mani wannan saka makon to ki sanya a ranki, har ƙarshe rayuwa ta, ina cikin farin cikin da kika saka ni a cikin sa, kije Allah ya albarkacin ki da zuri,ar ki baki ɗaya ".


Amin na ce, na ƙara run gume Umma yau nice Umma take baiwa umarni tare da sanar dani burin ta,? A take na saka a raina Insha Allah, Umma zata dauwa ma da farin ciki, indai daga gare ni ne.


Tashi mukayi ta rako ni har gurin su Inno, ai kuwa duk kowa ya tashi tsaye suna dariyar farin ciki, da yabon wannan ranar wanda Baban mu da kasan ya ɗaga hannun sa a sama yana mai nuna godiyar sa a gurin Allah da ya nuna masa wannan ranar, ai kuwa kowa cike da farin ciki yake, hannu na da hannun Salman ta haɗa tayi muna addu'a sannan ta ce, "ku tafi Allah ya kare gaban ku da bayan ku ta kare idon maƙiya a kanku ya albarkacin zuri,ar ku baki ɗaya ".


Haka kowa yake amsawa da Amin cikin tarin farin ciki.


Har a gurin motoci suka rako mu ina zubar da hawaye muna shiga cikin motar, Inno ta rufe aka tayar da motar muka ɗauki hanya, Shuraim sai farin ciki yakeyi idan ya dubeni ya dubi Daddyn sa, sai yayi dariya"


Tafiya mukayi sosai babu mai magana a cikin mu, sai airport abun mamaki jirgin tafiya london kawai muka shiga, muna sauka motoci ne irin na alfarma suka ɗauke mu, nikam cike da al'ajab nake ƙarewa ko ina kallo a wayan ce, bamu tsaya ko ina ba sai a wata haɗɗiyar unguwa, kai Alhamdulillah a gaskiya kam london tayi ba ƙarya, nikam tun ina sa ran akawo, har bacci ya ɗauke ni, kawai can a cikin barci na, naji kamar ina a jikin mutum ai da sauri na buɗe ido na.


Ai kuwa na zaro ido waje da sauri na ce, "dan Allah ka ajiye ni, baka ganin mutane a gurin kuma gashi a tare muke dasu Mom? "


Dariya ya sakar mani ya ƙara shigar dani jikin sa, ya ce, "oh ashe dai ba tare nake da kurma ba, ai na ɗauka ke kurma ce, malama, kuma su Mom kam sun nufi nasu gidan mu ma, yan zun mun kusa isa namu gidan Shuraim yana gurin su, kuma nan ƙasar ba wani abu bane dan miji ya ɗauki madam ɗin sa, babu ruwan wani da wani, dan haka ba zan sauke ki ba, ke wai ma anya kuwa kina cin abinci kuwa"!?.


Nasan ba zai sauke ni ba, dan haka na saƙalo hannu na a wuyan sa, na maƙala, na ce, "aa bana cin abinci kullum sai an rufe ni a ɗaki ake cin abinci "


Ya ce, "haba dai nikam na sani, amman malam maka am, na ɗauki babbar mace amman har Shuraim ya fita nauyi? "

Da sauri na ce, "ai da gaske? "


Ya ce, "anya ma kuwa zakiyi kukan amarci kuwa? Nifa naga idon ki a tsai tsaye sai rainin dake tsakanin mu, anya kuwa ba, tun yau zamu fara amarci ba? ".


Rufe ido na nayi, shi kuwa ya samu gurin tsokana ta, har muka iso bakin get ɗin gidan da zamu shiga sai bashi girma mutane keyi, manya da yara, sunayi masa barka da zuwa, yam mata da samari ma, barka sukeyi masa, tare dani, ina jin su nayi kamar bacci nake yi har muka wuce gurin mutane muka iso bakin nasa gidan, aka buɗe muna ƙaton get ɗin muka shiga cikin harabar gidan, sai a matakalar da zamu taka na ƙarshe ya ajiye ni ya buɗe gidan muka shiga ina daga bayan sa, ya kunna glub a take gidan ya haske ko ina, kwashe kyallayen da aka rufe kujerun mukayi, nikam kwanciya ta nayi, ina kallon sa ya gama kwashe komai shima ya zauna a kujerar da nake kwance, a kusa dani.


Shiru mukayi zuwa can mu ɗan futa na tashi na ce, "mu fara gyara gidan sai muyi wanka muyi sallah mu nemi abincin da zamuci ko? ".


Dariya ya yi yace, "nima hakan naga zai fi".


Ai kuwa a take muka hau gyaran gidan har ɗaku nan na ƙasa da sama, da kichin da bayi duk sai da muka tsab tace komai, san nan, na haɗa masa ruwan wanka ya shiga ni kuma na dawo falon na kunna kalli sai da ya fito ya saka kayan shan iska, nima na shiga nayo wankan na fito ke nan, naga ya a jiye mani kayan da zan saka na shan iska ina ɗaukar rigar da guntun wandon, na ajiye na ce, "kam lallai ma, taya zan iya saka wannan yan iskan kayan na fito falo, na zauna? Ni kam ba zan iya ba, haba kamar wata yar iska dai! ? ".



Hijab na saka, gashi towel ɗin ƙarami ne, baya rufe mani cinya ta, ai kuwa na soma faɗar "Daddyn Shuraim! Daddy Shuraim..! Kazo Allah ni ba zan yarda ba, haka kawai a ce, na rasa kayan da zan saka sai wannan kayan haba ɗan Allah, kuma kace naje na zauna kamar wata marar kunya? "


Ido rufe nake ta masifa, shi kuwa ya shiga cikin ɗakin ya harɗe hannayen sa, yana bina da ido, ganin ba zan dai na masifar bane, kuma ba zan buɗe idon bane, ya saka shi yin wani makirin murmushi, ya matso dab dani, ya fisgen hijab ɗin, ya riƙe a hannun sa, ya zuba mani ido kallona ya keyi tun daga sama har ƙasa, ko ƙyafta ido ba yayi.


Ni kuwa mutuwar tsaye nayi, cikin fir gici na, buɗe ido na zaro su waje, ganin abunda ban shirya ba, a kuwa da gudu na juya zan faɗa toilet na rufe kawai, taku biyu yayi ta tare ƙofar shiga bayin na faɗa jikin sa, ai ban san lokacin da na kwatsa masa wank uban ihu ba, sai da ya rufe mani baki da hannun sa.


Ya ce, "wallahi idan baki saka wannan kayan ba, yau sai dai ki zauna da wannan towel ɗin kuma ba zaki saka wannan hijab ɗin ba, ke nama fasa kada ki saka wasu kayan kiyi zaman ki a hakan kin fi ma burge ni, wallahi ".


Ai tun da naji yayi rantsuwa kuma dai naga ya ɗaure fuska kawai, na ce, "dan Allah Daddyn Shuraim kayi hakuri Allah zan saka kaga bama zanyi sallar ba, kaje kayi sallar kawai ni na yarda in dan wannan kayan ne Allah ".


Dariya ya yi, ya ce, wato dai aboki na ne ya zo, ashe dai nan da wata tara zaki sake haifo mani yan biyu, ko ƙuratul aini? ".


Jin nakeyi kamar na nutse saboda tsabar kunya amman Daddyn Shuraim ya sauya mani lokacin ƙan ƙani, kwata_kwata, ya ajiye kunya a gefe, sai zuba mani fitsara yakeyi.


Kuka na fara harda hawaye, ya ce, "ashe ko dai zan cire wannan towel ɗin yan zun sai naga yan da ake kukan shagwaɓa".


Ai haɗiye kukan nayi, na ce, "nifa kukan yunwa ne nakeyi ba wani kukan ba".


Dariya yayi yace, "haba dai ƙurratul aini, ai nasan halin basajar ki, yan zun jeki ki saka kayan bara na kawo maki pad da fant, na tausaya wa yar yarinyar nan, kai na gode wa Allah fa, na Auri yar shekara sha shidda gani da ɗa kusan shekara biyar kuma ita matar yan zun zata cika shekara ishirin kai nikam ɗan baiwa ne, yan zun take zama cikak kiyar mace, wayo Allah na....!, kai ƙurciya zallar ta ".


Rasa bakin magana nayi, daman tsokana ta ce, yakeyi kuma tsokanar ta samu shiga, dan hawaye naci gaba dayi".


Da dariya ya mai dani gefe, ya je ya ɗauko kayan ya bani ya fita yana dariyar keta gashi da hijab ɗin ya fita, hawayen na shiga sharewa, shigo wa ya sake yi ya bani leda ya fita yana, lasar baki yana shafa sajen sa, da harara na bisa har yaja ƙofar.


Haka na shiga na shirya, na saka kayan rigar mai haɗe, da gidan bra, kuma hannun bra ne da ita, iyaka cibiya, ta tsaya, sai wandon iya karsa, cinya, kasa fito wa nayi, nayi zama na a cikin bayin gajiya yayi da jira na, yazo ya buɗe bayin ya shigo yaja hannu na muka fito waje bai bari muka haɗa ido dashi ba, muka dawo cikin falon ya zauna akan kujerar ya zaunar dani akan ƙafafuwan sa, ya janyo abincin da yayi order aka kawo masa, ya buɗe ya soma bani, a baki, ganin bai ma damu yanda nake shigewa cikin jiki na ba saboda kunya, sai da ya tabbar da na ƙoshi ya bani ruwa, sannan ya soma ci, har ya ƙoshi.


Ya ce, "to ki tashi kije ki shirya sai ki dawo muyi fira kuma idan baki dawo ba, da kaina zan je kin dai san sauran ". ya kanne ido ɗaya.


Tashi nayi jiki babu lakka na nufi cikin ɗakin, naje nayi sha, fa mai na fesa turare da humra nayi, sai yar powder da jan baki, na tashi gashi ina jin kunyar sa, haka na fito na samesa yana kallon labarai, naje na zauna a kusa dashi yasa hannun sa, ya dawo dani sosai a jikin sa, mukaci gaba, da kallon a tare, har naji bacci, a jikin sa na kwata ya gyara mani kwanciya, a take nayi bacci.


Shi kuwa koda ya gama kallon ya kashe kayan kallon, ya ɗauke ni, ya kaini, ɗaki ya kwantad dani shima ya shiya ya kwanta yayi muna addu'a, nikam saboda tsabar gajiya bacci sosai nasha, sai a suba na falka, ina buɗe ido kawai na tsinci kaina, kwance a jikin mutum da sauri na yuƙura zan gudu ya janyo ni nadawo ya ce, "gudun na miye madam? Bayan duk kin bi kun shure ni da ƙafafuwan ki, kin zubo mani yayun bacci "


Nikam ban san lokacin da na ce, "wallahi ban yarda ba, ina da ja ni bani da nauyin bacci kuma bana saleɓa, kai sai dai idan kaine kake yi, ni rabu dani, naje na gyara jiki na, malam, haka kawai kazo kana yi mani cin kashin kaji? ".


Dariya ya yi, daman burin sa ke nan yaga ina masifa, kuma iyakar gaskiya ta na keyi, tashi nayi nace, "ka bani kayan da zan sauya ni kam, wallahi ko kuma ka nuna mani inda suke kaji? ".


Ya ce, "aa malama zo ki doke ni, ki ɗauki kayan kin ji...? Matar Salman? Uwar ya'yan Salman yar yarinyar Salman, mai ƙuruciya, shagwaɓaɓbiya t.... Maman Shuraim ƙurratul aini, nikam yau dai da kai na zan yo maki wankan nan fa bari na tashi dai na cire maki wannan kayan ".


Ai at 3√6o na faɗa jikin sa, na rufe ido na shige jikin sa, sai dariya yakeyi, ganin ya samu abunda ya keso naji, kunya, sannan ya ce, "ni tashi mani a jiki kada ki karya ni, kin ga kayan ki can a wan can seat ɗorowar, kuma sau ran kan yan suna a ɗaya dorowar, maza jeki ki fito kizo muyi baccin safe".


Kayan naje na ɗauka, na ce, "halan kayi sallar ne da zaka sake yin baccin? ".


Ya ce, "kina can kwance kiji fata mai laushi a baki sanin na tashi ko ban tashi ba, amman zan rama nikam dan ba zan yarda ba ".


Kyalesa nayi na shiga ciki bayin nayo wanka, da brush na shirya na fito, koda na fito yayi bacci, nadawo na kwanta a gefen sa, na kwanta sai bacci.


Sai sha biyu muka fito muka nemi abunda zamuci, bayan mun ci, muka fito muka nufi falo, ya ce, "muje ki sauya kayan nan mu fita ki gano gari".


Cike fa farin ciki muka dawo cikin ɗakin ya ɗauko mani sweater da dogon wando, da gyale nayi rolling ɗin gyalen, shima irin shigar mu ɗaya, har ta kalmi, muka fito, hannu na a cikin nasa hannun, muka fita yawon shaƙatawa, kai nikam sai dai na ce Alhamdulillah.


Birnin london kam mun zaga shi sosai nida Salman tattali da soyayya da kulawa duk ina samu, a gurin Salman, ga tsokana kamar miye? Wata rana har sai taga ina kuka yake dawowa yayi lallashi, babu abunda na nema ba rasa a gurin Salman, gidan su Mom munje ya kai sau nawa, a gurin su ma nida Shuraim gata suke nuna muna, har gurin dan gin Mom ya kaimu, a masarautar su Mom kuwa kwana biyu ne kawai muke tsallakewa.



Zaune muke nida Daddyn Shuraim ina sha masa ƙamshi shi kuma sai famar dariya yakeyi, ya ce, "ke kuwa wannan haɗe ran fa ba zai hana anjima na sake yi maki wani wa'azin ba, keda naga harda su kabbara kikeyi mani, saboda tsabar ɗaukar wa'azi, ai my love, kin iya bada hankali gurin ɗaukar wa'azin Mr Salman Daddyn su Shuraim da 'yan uwan sa ".



Filo na jefa masa ya ci, gaba da dariya, yana tsokana ta, na ce, "yau ma nawa ga wata ne? "

Ya ce, "oh zaki fara lissafin cikin wata nawa ne? Yau dai kwana ɗay... "

Da sauri na haye saman jikin sa, muka shiga ko kawa, dashi ina son rufe masa, baki, shi kuma yana son ƙasawa, sai da muka gaji muka

Please Login or Register in order to submit comment