Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba a bi ta kan muba kawai suka fita aka kira dillalai akayiwa gidan kuɗi akaje aka duba gonar Baban mu, suka je gurin malamai akayi rabon, muda muke zaune a gidan su goggo da Mama da sauran su Anty Asma dasu duk suna kasa sun tsare sunƙi fito cikin ɗakin, har su kawun suka shigo gidan.

Kiran Umma na akayi da ƙanne na a take kawu ya fara magana wadda ban san ranar da zan iya man tawa da ita ba, yace, "to an raba maku gado daman nasan shi su Narjeesah suke jira ita da Umman ta, dan hakane suka tsiri ɓatawa gidan nan suna, to Allah ya fiku, ga abunda kuka samu dubu ɗari biyu da saba'in ku dukan ku, yan zun sai kuzo ku bar gidan nan ku kwashe kayan ku, yau_yau ɗin nan nake buƙatar kubar gidan nan! "


Inno tace, "wannan wane irin rabon gado ne haka da rana tsaka, kuma kuce ga abunda suka samu bayan baku sanar da abunda kowa ya samu ba? Wallahi wannan ba adalci a cikin sa, indai ba zalunci kuka tsaro ba".

Cike da masifa akayo kan Inno wadda su Yaya jafar suka dakatar tare da faɗa, "sufa bazasu ɗauka ba kuma gaskiya Inno ta faɗa"

Rigima ce aka sanya kowa ya faɗi albarkacin bakin sa, Yaya tace, "kowa a sanar dashi abunda ya samu dan gaskiya nima ban yarda ba".

nan dai aka ce, Mama mai "ya"ya maza su shidda mata ukku sune sukaci rabin gidan duk girman sa, Inno da take da "ya"ya maza biyar mata hudu, taci kusan rabin gidan kaɗan aka rage ɗaki ɗaya da zaure, sai aka baiwa yaron Yaya ɗaya wannan ɗakin da Zauren, sai aka koma gona, inda muda sauran su Yaya aka rabawa gonar.

Umman muce ta shigo cikin ɗakin ba tare da tayi magana ba, kawai ta bashi hannun ta, a take duk suka zuba mata ido shi uban gayyar kuɗin ne ya watsa mata, wanda duk muka zaro ido waje muna kallon wannan wulakancin.


Umma tace, "nagode sosai fa" Sannan ta dubi tace "Inno mun gama shirya wa ga su Amrah can suna fitar da kayan mu ina ga ma sun kusa kwashe wa dan basu ɗaya bane harda yaran, unguwa zamu tafi duk wanda muka yiwa laifi to yayi hakuri".

Babu wanda yayi magana daga cikin su, Umma ta dubeni tace, "Ke! kuma ki tashi ki baiwa masu gida gidan su ki fito ga mota can tana jiran mu".

Kafeni da ido Umma tayi wanda a tarihin rayuwa ta shine na farko haka zalika a tarihin rayuwa ta wannan shine maganar da Umma ta taɓa yi mani a cikin mutane jikina sai rawa yakeyi, ashe bani ɗaya ba, duk wanda yake gurin yasan Umma yau anyi mugun cika ta, dan ita sam bakajin bakin ta koda kuwa kashe ni za ayi a gidan mu kuma bata taɓa yi mani magana ba, koda a cikin ɗakin mune ballema acikin mutane.

Tsaye tayi, har sai da ƙanwata Amrah tazo a gaban Inno ta tace, "Inno bani ɗan albarka na nan gurin abun sona farin cikin rayuwar mu wannan yaron da kike gani ya shige a cikin zuciya ta, yaron nan daga gani mujaheed ne dan zaiyi taimakon addinin Allah da taimakon mutane, shi daga ganin sa ba zaiyi aiki da jahilci ba kuma, bazaiyi aiki irin na jallai ba".


Dariya Inno da Yaya sukayi dan kowa yasan Amrah ta sakar wasu kawu Bala magane, Inno tace, "amman kuwa kin zaba masa sunan da ya dace dashi dan Allah ki riƙa kawo mani shi ina son shi wallahi har cikin raina, Allah sarki Allah ya rasa rayuwar musullunci" amin aka faɗa.

Yaya tace, "kice dai a riƙa kawo muna shi duk da muma cikin satin nan zamu bar gidan nan amman ni kun san gidan da nake dashi wanda na bada haya a can zan koma, dan Allah ku riƙa kawo muna shi Allah ya rayasa Allah yayiwa rayuwar sa albarka Allah yasa ya zamo farin ciki a garemu baki ɗaya amin ".


Amrah ta ansa ta goya shi,Nusaiba na shigowa ta raɓa kowa tazo ta kwashe kayana da suke ɗakin Inno ta rufe jakar ta riƙa hannu na tabi ta gaban Umma dani muka fita, Inno ta share hawayen idon ta, tazo ta anshi kuɗin wanda kowa ya kasa ɗauka ya bata, ita ta ɗauka ta baiwa Umma, Umma ta ce, "to mu yafi juna Allah yasada mu da alkawarin sa"


Fita Umma tayi ta duba ɗakin taga babu komai tayi murmushi ta juya zata fita Inno da yaran ta, da Yaya da yaron ta suka rako Umma har gurin mota, Inno ta dam ƙawa Umma kuɗin wanda ta ɗaure da leda, Umma ta amsa, ta shiga cikin motar, mu kuwa a lokacin muna ciki, ga mutane ƙofar gidan kamar rana duk kuwa da cewar magriba ce, sai da motar ta tashi muka ɓacewa ganin su .


Umma ce ta kalli Amrah tace, "Amrah kin sheda masa inda zai kai mu ko? "

Amrah ta goge hawayen da takeyi tace, Umma na sanar dashi amman Umma kina ganin su kawu Habu zasu yarda mu zauna a gurin su kuwa? Kin fa san halin sa da zafin zuciya ga rashin fahimta Umma ni wallahi tsoro nake ji".


Umma dai kallon su kawai tayi ba tare da tace dasu uffan ba.

Sai ƙarfe tara na dare muka ƙarasa unguwar su kawu Habu sai gaban mu ke faɗuwa, dan kowa a tsorace yake, sauka mukayi aka fara sauke muna kayan mu harda mai motar, Umma ta bashi kuɗin sa, muka shiga cikin gidan a tsakiyar gidan muka sami kowa da kowa, Kawu yace, "ina fatan dai ba cikin nan ne aka haife ba, kuma kuka dawo mani dashi gidan nan ku raine shi a gidana ba".


Shiru Umma tayi kafin ta ce, "kayi hakuri kawu, ka barmu mu kwana anan da safe zamuje mu nemo gidan haya sai mu koma a can kaga dare ne yan zun ".


Matar shi tace, "haka kawai zaku kwaso ƙafar ku harda kayan ku da shege ku zo muna gida cikin dare ai dai kwana ɗaya kika roƙa kuma shi zakuyi ehe! ".


Umma dai batayi magana ba, ɗakin aka bamu ɗaya har kayan mu, nidai ban samu na rimtsa ba dan nasan nice duk silar faruwar hakan, Umma ce naga ta tashi tayo alwala ta fara nafila, da addu'a yaron ne ya motsa wanda yake kwance a jikin Amrah da sauri ta tashi ta kawo mani shi tace, "dan Allah bashi yasha kin ga yaron akwai hakuri".

Ansar shi nayi na fara gir_giza shi amman kukan yakeyi fitila Umma ta hasko mani, tun da naga hakan nasan mi take nufi, gyara shi nayi na soma bashi, kawai muka jiyo masifar kawu Habu da matar sa, suna faɗar "wannan wace irin jaraba ce haba ya zaku sakawa mutane hawan jini ku hanasu kwana? Nifa wallahi idan naga kun cika damuwar mu muda moƙwota sai dai muce kubar gidan nan ".


Shikuwa bawan Allah harma ya koma bacci, suka gaji da masifar su sukayi koma ɗakin su.

Tun da aka fito sallar Asubahi, muka gaisa da mutanen gidan muka fita ko karya wa bamuyi ba, muka fara neman gidan haya, har ƙarfe tara na safe bamu samu ba kuma bamu ci abinci ba, gashi ina jego, ganin hakan ne yasa Umma ta sai muna ƙosai da koko muka zauna Zauren wani gidan muka ƙarya muka tashi muka shiga yawon neman gidan haya, ga baki ɗaya sai da muka bar unguwar sosai zuwa sha biyu na rana Allah yasa muka dace kuma gidan babu kowa cikin sa ɗaki biyu ne da kichin da bayi, shekara ɗaya dubu, talatin haka muka biya anan aka barni nida yaron suka tafi gurin kwaso kayan.

Zaune nake na buga uban tagumi ina kallon yaron wanda nake jin yan zun ina kaunar sa, to amman ya ya rayuwar mu zata kasan ce ne nida yaro na, zuwa gaba, har yaushe ne zan saka Umma na da yan uwana farin ciki?.


Jin ana shigo da kaya yasaka ni dawowa hayyaci na, kawai na tashi na baiwa Nusaiba yaron ta ansa ta goya sa, ni kuma na taya saka kayan Umma ɗaki ɗaya muka saka mata gadon ƙarfen ta da da wadurof din ta da mu kuwa a ɗaya ɗakin muka saka gado ƙarami da katifa ɗaya, waje kuma aka saka durom naruwa da tukunyar ƙasa.


Kichin Umma ta shiga ta gyara komai da komai, kayan miya ta fito dasu zata fara jajjage da sauri Amrah ta ansa ta ce, "haba Umma kibar shi muyi mana ai ke ya kama ta ace kin futa kawai".


Umma ta ce, "naga kun gaji da yawa kibar shi kije ku futa, taliya ce kawai zan dafa muna".


Dariya Nusaiba tayi tace, "Umma Allah ya raba mu da fu kina aiki muna zaune muna kallon ki da ran mu da lafiyar mu".


Dole Umma tayi dariya wadda rabon da muga dariyar ta tun kafin cikin jiki na ya bayyana sai yau dan haka kowa sakin baki da hanci ya yi yana kallon Umma, itama sai ta daina dariya ta zo ta wuce ni ta shiga cikin ɗakin ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa ta zauna, tashi nayi na shiga cikin kichin ɗin da kaina na fara gyara itace zan fura wutar Nusaiba tazo ta ansa tana faɗar kai Anty su waye suka taɓa barin mai jego na aiki, ai mai jego sarauniya ce ko ya ki ka ce, Anty ƙarama? ".


Dariya Amrah tayi tace, "wato dai ba zaki sauya mani suna ba ko? "


Haka dai suke ta bidirin su abun su, suna gama dafa taliyar suka ɗora mani ruwan wanka, suka zuba wa Umma nata mu kuwa suka zobo muna guri ɗaya abincin muka ci sai da muka ƙoshi Amrah da Nusaiba suka fita suka nemo ganyen bedi suka kawo mani suka kwashe mani ruwan wanka naje nayo kamar yanda su Inno suka fara yi mani, cikin zuciya ta nace Allah sarki ashe dai su Inno gata ne suke yi mani da suke yi mani wankan nan yan zun gashi nice nake yi da kaina.


Koda na fito Amrah ce na sama tana yiwa yaron wanka Nusaiba na ce mata, kiyi masa a hankali mana kada kije kisa sabulu ya shigar masa, ni wallahi inda nice nafi ki iyawa dan nataɓa yiwa Anty Basira wankan saifullah so da yawa".


ai kuwa nikam dariya na zauna ina yi masu bayan sun gama yi masa wankan aka zo gashin chibi, Umma najin ihun yaron da sauri tasa hannu ta anshe sa ta fara faɗa, "kashe ɗan mutane zakuyi ne waye yace maku da zafi sosai akeyi, dallah ku tashi ku bani guri nayi masa ni bana son hauka! ".


Ba niba hatta Amrah da Nusaiba sakin baki sukayi suna kallon Umma ni kuwa harda murza ido na keyi, fita iskan mu Umma tayi, kamar ba san mun tsare ta da ido ba, gashin tayi masa har sai da yayi bacci Amrah tace, "Anty kayan da zamu sakawa yaron nan fa? Dan naga kamar kala biyu gare shi "yan gobe suna".


Shiru nayi ban ce da ita komai ba, Umma ce ta tashi ta buɗe akwatin ta, ta ɗauko kayan jarirai har kala biyar kuma masu kyau da zanen goyo na saƙa da kayan sanyi saiti.



Cikin farin ciki Amrah ta kwaso kayan tana tsalle, ita kuwa Nusaiba sai rawar jiki takeyi zata saka mashi kayan da sauri Amrah tace, "nifa zan shirya masa bara na ɗauko masa pampas din sa wanda na ajiye masa".


Itama cikin kayan ta ta ɗauko pampas da wando na jarirai masu yawa da swafa da fula harda takalmi, itama Nusaiba tace ni dai bari ku gani, cikin kayan ta taje ta kwashe su, ta fara ɗauko mayukan shafawa da powder dasu turare ta kawo ta ajiye a gurin Amrah tace, "nima ga nawa kayan Baby boy a gyara muna abun mu mukam muna son shi".


Ni kam cike nake da mamaki ba kamar Umma da zan iya cewa wannan shine karo na farkon da ta taɓa yin abun da faran ta mani rai sabo duk wani abun da yake da dan gata da farin ciki na Umma bata taɓa yin saba, ni ada nama ɗauka Inno ce ta haifeni sai da Inno tayi da gaske san nan na yarda da cewar Umma ce ta haife ni dan ko ɗin kin sallah bata yi mani amman Amrah da Nusaiba da Mariya 'yar ɗakin Inno dan kala biyar_biyar sai tayi masu harda takalmi kala ukku, ni kuwa Inno tayi mani ɗaya sai kuma idan Allah yasa mutanen arziki sun yi mani dan haka duk kowa ya fini yawan kayan ado, wata rana kuma idan antashi yin ankon biki idan ta kai ayiwa su Amrah ɗinkin biki, nike zuwa na anshe turmin zane ɗaya, idan taji sai ta kaiwa Inno ƙarata Inno kuwa tace, tayi mani magana da kanta mana, to anan ne nake samu nasara akan ta.



Umma ce ta gyara masa tayi masa shiri mai kyau wanda abun ya yi ta bani mamaki, Umma kuwa basu yaron ta yi suka ɗauka suka fita, nima ina gama gyara wa, na fita cikin "yan uwa na ina kallon su na ce "Amrah Nusaiba " kun kam mala jarabawar ne ko kuwa?.


Amrah tace, Anty nifa na ajiye 'kara tun bokon nan kamar yanda kika ajiye jss 2 kallon ta nayi cikin jin haushin maganar ta nace amman kuwa bakiyi mani adalci ba, ai ni kinga tawa ƙaddarar ke nan, dan haka dan Allah kuyi karatun nan kada ku manta burina bai wuce nayi karatu mai zurfin gaske ba boko da Arabi amman ku dubi yanda na kasan ce, to dan Allah kuyi hakuri kuyi karatun nan kunji!?.


Shiru duk sukayi cikin tausayin halin da na tsinci kaina, sukayi mani alkawarin yin karatu.


Haka dai mukaci gaba da rayuwar mu, a can makaranta su Amrah suka jiyo maganar Auren da za'ayi nasu Yaya Auwal dasu Surajo dasu Shamsiyya da Zuwaira dasu Balkisu wanda duk suna gaba na wasu shekaru biyar suka bani wasu shekaru ukku, bikin wanda aka ce a sanar dani kada na yarda naje gidan naɓata masu biki, 'yan gidan mu suka faɗawa mutanen gari kuma da Mariya da kanta tazo har gidan mu ita da wasu ƙannen mu, suka sanar damu wannan maganar.


Ita dai Umma ta yarda taje gidan ita dasu Amrah inda suka dawo gidan kamar wanda aka koro.


Hawaye na gani a idon su Amrah cikin tashin hankali na buɗe baki zan tambaye su, kawai naga Umma itama kukan takeyi, da sauri naje ina tambayar Umma hawaye na zubar mani amman Umma bata ce dani komai ba, tabbas nasan babban abune ko miye, daket Umma ta buɗe baki tace........




*Comment And share*



*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

💐💐 *NARJEESAH* 💐💐


_*RUBUTAWA *_ 🖊
*NANA KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN CE_*

*YA ALLAH KAJIKAN IYAYE NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU DAGA CIKIN DAUSAYIN ALJANNA SU DA DUK KANNIN MUSULMI BAKI ƊAYA AMIN YA ALLAH*

*_BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM_*

*5&6*

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Umma ta ce, "kada ku yarda naji wata magana ta fito daga cikin bakin ku har sai idan naso hakan, wannan umarni na ne! " kawai ta shige cikin ɗakin ta, ta saki labule.

Tunda mukaji umarnin Umma sai duk jikin mu yayi sanyi babu wanda ya sake cewa komai tashi nayi nima kashige cikin ɗakin mu na kwata, ina nazari, tabbas duk abunda ya saka Umma kuka baƙara min abu bane, amman kuma Umma ta hana nasan ko miye wannan abun, kai koma miye babu shakka duk abunda ya faru nice sanadiyar komai ya Allah kadube mu.



Duk yinin ranar bamu da wata walwala kowa a cikin damuwa yake har aka kwana biyu, yau muna zaune muna fira ni dasu Amrah Nusaiba na goye da yaron yana bacci, sallamar su Inno ce ta katse mu, cikin farin ciki muka tarbe su Inno da Yaya da Mariya, Umma ce ta fito cikin ɗakin ta, tazo ta, tarye su da farin ciki, tabarma aka shimfiɗa masu suka zauna na kawo masu ruwa Amrah taje maƙota ta siyo masu zuɓo ta kawo masu, bayan sun sha aka gai da tambayar ya akaji da hidimar biki suka ce Alhamdulillah angama lafiya taro ya tashi sai dai abunda ya faru ne wanda basu ji daɗin saba.


Umma tace, "ai komai ya wuce".

Da sauri nace, Inno dan Allah miye ya faru a ranar dan Umma ta hana kowa ya sanar dani, sun barni cikin duhu da tunanin miye yake faruwa, bana bacci ina cikin damuwa, duk da nasan da cewar ba kowa bane ya janyo wannan matsalar ba sai ni.


Inno ta ce, "ai koni ma ba zan iya sanar dake komai ba, da kuma wanda sukayi abun kasan cewar nafi kowa sanin halin ki Narjeesah idan kika san ko su waye da abunda akayi ba zaki ɗauka ba, kasan cewar ki mafaɗa ciya, daman cikin da kike dashi ne yasaka ki yin sanyi amman yanzun nasan zaki iya fafatawa da kowa".


Yaya ta ce, "tabbas hakane Narjeesah zaki san wani abun amman banda wani abun, ranar a unguwar mu anyi faɗa sosai har makarantar islamiyar ku inda akace malan Abbakar shine ya yi maki ciki kasan cewar sa yana sonki tun kina ƙaramar ki, kuma Baban ku ya sani amman yace, sai in kinyi hankali kin ce kina son sa, to ganin irin yanda idan baki zo makaranta ba yake zuwa ya sakaki a gaba kije makarantar shine aka ce shine ya yi maki cikin yaron nan, shi kuma ya ƙaryara rigima har aka koresa a makarantar duk da kuwa kasan cewar mahaifin sa shike da makarantar".


Hawaye naji suna zubo mani nace wallahi Inno bashi ne yayi wannan cikin ba kuma wallahi ko kalmar kebewa a wani gurin, ko a makarantar bai taɓa furta mani ba.


Inno tace, "ana cikin wannan rigimar ne, wani mai mota yazo daga ganin sa anga dan shaye_shaye to shine ya ɗauki hankalin kowa inda ya ce, shine wanda ya yi maki cikin yaron nan kuma yazo ya anshi abun sa ne, saboda duk lokacin da ku ka tafi makarantar boko shike zuwa yana ɗaukar ki yana zuwa gidan sa dake har sai da kika ɗauki cikin sa, kuna tare shine ma yace ki zauna ki raini cikin zai Aure ki, to yan zun ya fasa Auren ki yaron kawai yake so ko kiba shi yaron da arziƙi ko kuma yazo da "yan sara suka sai dai su kashe ki da duk wanda yake tare dake su ɗauki yaron! ".


Da sauri na tashi tsaye na fara ja da baya ina zubar da hawaye nace wallahi Inno da Yaya, wannan ba shine uban yaron nan ba, wallahi ba zan bada shi ba! .


Inno da Yaya suma suka tashi tsaye suka haɗa baki gurin fad'ar, "to waye uban yaron nan tunda kin ce wannan bashi bane!? Kuma kina nufin kin san inda uban yaron yake ke nan! ".


Nace wallahi wannan ƙarya yake yi maku bani da wata alaƙa dashi, mutum nan ɓarawon yara ne kada ku yarda dashi.


To wane ne uban yaron nan tunda kin san shi kuma a ina yake kuma ya ya sunan sa? "Inno ce" ta jero mani wannan tambayoyin da suka riki tar dani a take na dabur buce na rasa ma wace irin amsa ce zani bata, gashi duk ankafe ni da ido.


Sai da na haɗiye yawu masu ɗaci ga uwar zufar da take , zubo mani ta kowane saƙo na jiki na nace, a gaskiya duk bani da amsar da zan baku daga cikin wannan tambayoyin amman gaskiyar zance "wannan mutanen ban taɓa sanin sa ba! "


Inno tace, to ya zama wajibi tsakanin yau ko gobe ki sanar damu Baban yaron nan, ko kuma kubar garin nan, sati ɗaya mutumen ya bada zai dawo kuma dawowar sa ba abu bane mai sauƙi dan da alama zai iya aikata duk abunda ya faɗa saboda a tare yazo da maso shaye_shaye harda takubban su"


Daɓas na zauna a ƙasa na fashe da kuka kamar raina zai fita, suma su Amrah kukan ne sukeyi sosai, Umma dai bata ce uffan ba, har su Inno suka dawo a kusa dani suna lallashin mu, kallon Inno nayi nace, "Inno dan Allah ku anshi adireshin sa da number sa ku ajiye mani ita har na tsayin wani lokacin".


Insha Allah suka faɗa, Inno ce ta kawar da wannan kukan ta ce, yo ni wannan iyayen na daban kuke kuna nufin ba zaku bani maigidan ba na ɗauke sa, ba har sai na roƙa ko? ".


Dariya mukayi, nidai shiru nayi Nusaiba ta sauke shi ta bata shi tace, "gashi nan Inno bama rowar ɗan baiwa".


Dariya sukayi Yaya tace, "ni kuwa wane suna ne kuka sakawa angon namu dan naji har yanzun baku faɗa ba, kodai sunan bai da daɗi ne ace yaro wata biyar bamu san sunan shi ba? "


Dariya mukayi, "Nusaiba tace suna kam mai daɗin gaske sunan hafizai".

Inno tace, "um kaji iyayen "ya"ya da kauɗin tsiya, wane suna ne wannan? ".

Amrah tace, "Shuraim ke nan Inno yaro hafizi ga daɗin murya".

suka haɗa baki gurin fad'ar, "kai masha Allah, Allah ya raya muna Shuraim yaro mai suffar larabawa da sunan larabawa abu ya yi kyau".


Mariya ce ta anshe sa, tana kallon sa, tace, "kai Inno wallahi wannan bai kama da wannan ƙaton mutumen mai ƙaton hanci kuma gashi baƙin sa ya yi yawa kawai dai ɓarawon yara ne, a gaskiya a gudu da yaron nan daga garin nan ma baki ɗaya, saboda naji ana raɗe_raɗin cewar cikin dare za'a nuna masu gidan nan ni wallahi yaron nan tausayin sa, nakeji! "



Kallon_kallo muka shiga yi nida su Amrah cikin damuwa Amrah tace, "Insha Allah babu maiyi sai Allah, burin wasu ba zai cika ba"


Sai marece su Inno suka tafi, Umma ce taja Nusaiba suka fita, Amrah ta sameni a cikin ɗaki kwance ina tunani ta dafani, na ɗaga ido na kalleta na tashi zaune tace, "Anty nifa a tsorace nake da maganar da naji su Mariya na faɗa nifa ina ganin zan baiwa Umma shawara, ne yau mu nemi gidan da zamu je mu ɓuya a can".


Kallon ta nayi, nace "Amrah "duk nice na janyo maku shiga cikin wannan hatsarin nifa ina ganin zan ɗauke yaron nan nabar garin nan gudun kada azo kashe ni a haɗa daku duka na bani, nayi sanadiyar mutuwar mahaifiyar mu daku kan ku, kuma aje a maida yaron nan wani irin mugun mutum".


Rufe mani baki Amrah tayi ta ce, "Anty dan Allah hankalin ki ya dawo jikin ki, ai duk inda kika saka ƙafar ki muna sai mun saka dan haka zamu gudu tare mu tsira tare".


Koda Umma ta dawo, ita da Amrah har mun gama abincin dare mu gyara ko ina, sannu da zuwa mukayi masu.

Da dare bayan munci abinci muka rufe gidan tare dayin Addu'oi sosai muka ɗauro alwalar kwanciya muka rufe ɗakin mu nida Amrah, Umma da Nusaiba suka kwanta ɗakin Inno suka rufe, addu'a sosai mukayi, kafin mu kwanta na shafe Shuraim da addu'a wanda shi tuni yayi bacci.


Can cikin dare muka fara jiyo, motsin ana shirin cire muna ƙofa ta shigowa cikin gidan, ai kuwa duk muka tashi zaune a tsorace addu'a muka somayi, ai kuwa dukan ƙofar akeyi da ƙarfin gaske kuma da makamai ake dukan ƙofar da sau muka diro ƙasa, nasa hannu, na ɗauke Shuraim na goye shi nasa wani zane na taresa dashi, sai muka lallaba, a hankali muka buɗe ƙofar ɗakin mu muka fito anan ita Umma suka fito sai jikin mu ke rawa, addu'a duk wadda tazo bakin mu ita muke yi.


Gashi har ƙofar ta fara alamar da kuwa, ta maƙotan mune aka saƙo tsani, da sauri muka ja da baya dan mun riga da mun san tamu tazo ƙarshe, hannun Amrah naja da niyar mu koma

Please Login or Register in order to submit comment