Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baje a gurin.


Haka dai rayuwar mu, taci gaba tafiya cikin kulawa, da tattali da ƙaunar juna muna kiyaye duk wani abun da zai bamu matsala a zaman mu dashi, cikin ikon Allah watan mu biyar a ƙasar, wata ranar labara na tashi da ciwon ciki mai tsanani, a ruɗe ya ɗauke ni, ya kaini asibiti gwajin farko, aka sami kyakykyawan result, Allah ya bamu ƙaruwar cikin wata, ukku, da sati biyu, murna a gurin mu ba a faɗa, su Mom ya kira ya sanar dasu, ai kuwa koda muka dawo gida a nan muka same su harda Muhseen Mom Dad Shuraim,


dan Salma ta daɗe da komawa Nigeria, sai tambaya ta sukeyi miye zan ci, ko miye nake so, kuma sun ce, kada ya yarda ya cika matsa mani da takura mani, duk abunda nake so, yayi mani ko a kira su a sanar dasu Shuraim kuma ya ce, ba zai koma ba, a nan zai zauna ai kuwa korar sa, Salman ya yi, wai kada ya takura mani ya riƙa saka ni yawan magana, nikam dariya suke bani, kuma da yaga Shuraim yayi fushi sai ya fasa barin a tafi dashi, dole aka bar sa, daman sun san ba zai bari a tafi dashi ba, dan mun sha zuwa ɗauko ana hana mu.



Haka dai akaci gaba da tarairayya, ta, har Allah yasa cikin ya kai watan haihuwar sa, har kwakin haihuwar da aka bamu ya wuce, zama daket tashi da ket, Shuraim wata rana har kuka yakeyi, idan yaga ina son tashi tsaye na kasa, Salman kuma jin yakeyi kamar cikin ya dawo a jikin sa, wata rana shi da kansa yake ɗauka ta ya tayar dani tsaye mu fara tafiya saboda motsa jiki.


Yau kam tun da na tashi nake jin ba dai dai ba, ciwo_ciwo sama_sama, tun ina jin kamar da wasa har na kasa hakuri, nace, "Shuraim kira wo mani Daddyn ka, wash...! "



Ai da gudu suka iso baiyi wata_wata ba, yazo ya ɗauke ni, Shuraim ya buɗe muna motar muka shiga, sai asibiti ai da sauri muka ƙarasa, yana yin parking, ya fito ya ɗauko ni, abu da ƙasar waje kawai sai ga ma'aikatan asibitin sun zo da gadon ɗaukar masu ciki, suka bar su a nan baya aka shiga dani, aka hana su shiga sai go and come sukeyi tare da addu'a Shuraim kuka kawai yakeyi.


Cikin ikon Allah ko a awa ba'ayi ba Allah ya sauke ni lafiya, aka sami yan biyu namiji da mace ai kuwa zo kuga irin yanda su Salman suke tsalle da hamdala, ɗakin da aka kaini futu suka shiga, idon su, a kaina, sai da suka tabbar da lafiya ta lau sannan suka ɗauki yaran sai dariya sukeyi, sai alokacin ya kira Mom yake sanar da ita, ya kira Dad da Muhseen da Salma sai ya kira Yaya Auwal dasu Jafar, kai Salman kusan sai nace, zaucewa yaso yi sai da na anshe wayar dan photo yake ɗaukar yaran iri daban_daban yana posting ɗin sa.



Mom na zuwa ita dasu Dad kowa guri na ya fara zuwa sai da sukaji lafiya ta, sannan suka ɗauki yaran wanda Muhseen da Shuraim suka kan kane gurin sun hana kowa ɗauka, Mom ce ta anshe yaran ta kore su, awar mu shidda aka bamu sallama bayan a duba lafiya ta da lafiyar yaran, muka dawo gida ai kuwa sai shirye_shiryen zuwa gida Nigeria akeyi wanda Mai martaba ya bada umarni, sake shirya wa mukayi, dan Muhseen ya tafi da Shuraim airport mune kawai ake jira, haka muka fito cikin farin ciki muka nufi airport ɗin, bamu wani jima ba jirgin mu ya ɗaga sai Nigeria.


Da misalin ƙarfe biyu na dare muka iso, ai kuwa motocin Mai martaba ne suka ɗauke mu sai fada, muna isa bakin kofar faɗar kamar rana haka muka sami gurin cike da mutane, fulani ce da kanta ta janyo hannu na, muka shiga cikin gidan wani ɗakin ta nufa dani, muna shiga tace, "ki kwanta kiyi bacci ki futa har zuwa da safe kinji jika ta? ".


Murmushi na sakar mata tare da gyaɗa mata kai na, ta juya ta fita ni kuma baccin gajiya ne ya ɗauke ni akan wannan gadon na alfarma, ban falka ba, sai gurin ƙarfe takwas na safiya, ina falkawa sai a idon fulani ai kuwa da kanta ta kaini bayi, tayo mani wankan da ba zan taɓa manta irin saba, a rayuwa ta, muna fitowa ta shirya ni da kanta, aka kawo yaran duk an gyara su, sai uban ƙamshi suke zuba wa, harda Shuraim a biye dasu, shayar dasu nayi, aka fara jero mani abun kari nama rasa wane zan ci wane zan bari, Mom ce ta shigo cikin ɗakin da kanta ta soma ciyar dani har sai da na ƙoshi.


Anan ne Fulani da Mom suke sanar dani cewar, Mai martaba ya ce, zamu zauna ne a fara yin walima sannan mu tafi gurin su Umma na, dan za'a haɗa ne da bikin naɗin sabon sarki.


Na ce, "babu damuwa duk yan da kuka tsara mu masu biyayya ne".


Ai kuwa sun ji ɗaɗin wannan maganar tawa, har sai da suka nuna farin cikin su.



Tun daga wannan ranar fulani da Mom sune suke kulawa dani har zuwa yau da mukayi kwana shidda kuma yau ne walimar, walima ce, wadda ta tara manyan malamai sarakai masu mulki da masu muƙamai talakawa da masu kuɗi, samari da yam mata, yara da manya, tsoho da tsohuwa, su Salma da su Humaira dasu Amrah tun daga lokacin da suka zo jiya basu futa ba, sai kai komo suke yi, anyi walimar lafiya an watse lafiya.


Sai shirye_shiryen zuwa gida kawai mukeyi, muna gamawa, aka ɗauke mu cikin motoci na alfarma muka nufi garin Yola domin ƙarasa wannan gagarumin bikin, cike da ɗoki nake son na buɗe ido na, naga irin farin cikin da Umma na zata nuna mani da na cika mata burin ta, su Hindu da Salma sai tsokana ta, sukeyi, ina share su.


Saboda tafiyar Asubanci ce mukayi kuma bamu tsaya ko ina ba, zuwa ƙarfe goma muka iso, ƙofar gidan mu, muna sauka da sauri nabar yaran hannun su Amrah nayi cikin gidan da gudu ina kiran Umma..! Inno...! Yaya....! Gani nazo na ganku".


Dariya suka sakar mani cike da farin ciki, Mama ta rungume ni, ta ce, tunda ni badani ba, a cikin mutanen da kike kira ni na fara tarbon ki.


Da sauri na rufe ido alamar naji kunya nace, "Afuwan Mama duk cikin mararin ganin kune".


Inno ce, tace, "munyi farin ciki da ganin ki, amman ki daina gudu ba kyau".


Dariya nayi na faɗa jikin Inno, haka su Amrah suka same mu, Yaya ma rungume ni tayi, yan gidan kuwa, gurin ɗaukar yaran suka nufa idan wannan ya ɗauka sai wannan ya ɗauka, nikam hayewa sama nayi, na nufi cikin ɗakin Umma, ai kuwa tare da mutane na sameta, suna jin sallama ta, duk suka taryeni tare da yi mani barka, duk suka fita, aka barni nida Umma sai Mama Luba, jikin Umma na faɗa ina dariya ta fara shafa mani kaina, tana murmushi, Baban da ya shigo cikin ɗakin ya ce, "wa nake gani kamar Narjeesah na? ".


Ai da sauri nayi kansa na faɗa jikin sa ina dariya sosai mukayi farin ciki a cikin ɗakin Mama Luba ce, ta ce, "Narjeesah Ashe ansami ƙaruwa Allah ya raya, am sai kuma gashi kin sameni a cikin gidan ku, dan Allah ki yafe ni laifin da nayi maku na cin mutumci ta korar wula'kanci sai gashi kuna barin garin komai nawa ya lalace hayar ma dana ke biya na kasa biya, ke daga ƙarshe ma na rasa komai nawa sai bara nadawo ina yi a rin wannan rayuwar ne, Allah ya kawo mani Umman ku, ita ce ta zo dani har ta bani kuɗin ɗaukar wani gidan hayar, tare da kuɗin siyen kayan ɗaki da sutura, haƙiƙa gaskiyar magana na yarda hassada ga mai rabo taki ce, ku yafe ni ".


Murmushi nayi, na ce, "nikam na yafe maki bana iya riƙe kowa a zuciya ta, Allah ya yafemuna baki ɗaya ".

Kowa ya ce, "Amin".

Cikin falon muka dawo Baban mu kuma ya fita, muka soma fira da su Amrah har nake tambayar ta sauye_sauyen da nagani, ta ce, "duk aikin Yaya Salman ne, dan dashi da Shuraim duk ƙarshen wata, suna zuwa su kwana biyu, shine ya baiwa Umma dasu Inno jarin miliyan biyu_biyu, su Yayan mu kuwa, aiki ya nema masu, mukam dubu ɗari biyar_biyar ya baiwa mata mu dogora da kan mu, yara dubu hamsin_hamsin,



Sai kuma provision ɗin da buɗawa Baban mu, sannan ya baiwa duk su Yaya mota, harda Baban mu ai kin ga gidan cike da motoci, sannan wan can gidan na gumel ya gyara masu shi, harda su get, su Yaya suna ajiye motocin da ya basu ke harda moƙota duk sun sheda, dasu kawu, wai duk kina nufin cewar baki da labari? "


Kallon ta nayi cike da mamaki nace, "ke ni wallahi duk ƙarshen wata suna yin tafiyar kwana ukku ko huɗu amman ban taɓa sanin nan suke zuwa ba, saboda ya ce, dani wani aikin ne suke zuwa yi, wata ƙasar ".


Amrah tace, "shi yasa nake ƙara godewa Allah da ya sanya kika zamo alkhari haka Shuraim zuwan sa, a rayuwar mu alkhari ne, wannan maganar haka kowa yake faɗar ta, harda wanda suka jahilci abun a can baya ".


Haka dai mukayi ta fira, su Mommyn Humaira duk suna gidan harda moƙota, gidan ya cika sosai biki akeyi sosai ƙaton sa aka yanka da rago huɗu, wai harda na bikin Shuraim za'a haɗa, mukam dariya mukeyi, matan su yayan mu duk suna nan harda Mrs Yaseer a cikin yan bikin, kayan barka kuwa kamar wani company, kai komai cikin nasara akayi sa, yara sun ci sunan Mai martaba muna kiran su, da Sultan da Sultana, kwana biyu mukayi ana bikin saboda naɗin sarautar Daddy wanda Salman yayi masa wayo ya amsa.


Taro ya watse lafiya inda muna zaune dasu Humaira wata ce, ta shigo tace, tana son ganin mu shine, su Mariya suka kawo ta gurin mu, kallon ta, mukeyi a take duk muka tashi tsaye nida Hindu da Humaira, Hindu ta nuna ta, ta ce, Haleema ke ce, daman kina nan!? "


Ta ce, "ina nan ku zauna daman nasan zan sameku a tare".


Zama mukayi muna kallon ta, duk tayi baƙi ta fita hayyacin ta, Haleema yar gayu ta dawo wata bakar tsohowa dan daga gani tasha baƙar wahala a rayuwar ta.


Ta ce, "nabi ruɗin zuciya ta, na Auri wanda zuciya ta, take mararin sa na bar tsohon zaɓina, zaɓin iyaye na, nayi Aure batare da yardar suba, bada sanin suba, ga yaudar Jafar da nayi, duk haƙƙin sune ya hanani sukuni, munyi zaman soyayya nida zaɓi na, sai gashi watan mu biyu, mun fara samun matsala inda yake bani maganin hana ɗaukar ciki tun ina sha cikin farin ciki har na ƙosa dashi na daina sha, kwatsom ciki ya shige ni, nayi ciwo mukaje asibiti kwajin farki aka tabbar muna da ina ɗauke da cikin wata, biyu, tun daga cikin asibiti ya ɗaure fuska yace, a zubar dashi a take nasha jinin jikina, na fara cewa ba za'a zubar dashi ba,



Tun a asibitin ya soma duka na, har muka dawo gida da belt yake duka na, yana taka cikin ai kuwa yayi sa'ar zubar dashi tun daga wannan lokacin ya dawo kulawa dani, saboda son da nakeyi masa, bana jin haushin sa, kwatsam na sake samun wani cikin, shima ya ce, a zubar a wannan lokacin kam na hana, har dukan da yayi mani cikin bai zube ba, sai ya riƙa zuba mani magani a cikin abinci da abun sha ba tare da sani na ba,



Aikuwa gurin zubewar cikin na kusa rasa raina, asibiti sun so ƙin yi mani aiki, da ket suka anshe ni, tun daga wannan lokacin muka dawo kamar wasu maƙiya a take ya tsiro mani da asalin halin sa, na rashin kulawa da kawo yan matan sa, a cikin gidan, idan nayi magana sai duka, kai da abun ya dameni, sai na fara tunanin, cewar ko dan anyi wannan Auren ne bada albarkar iyaye ba ne, shin ya kawo wannan rashin jituwar, ke wata rana ina ina aikin tunanin makomar rayuwa ta shine ya shigo tare da worgo mani takardar saki, inda na shiga kaduwa, tare da tarin nadamar wannan Auren da nayi, yan zun haka yau zan koma a gaban iyayena,



Bayan na zauna a gidan wata ƙawata, na cika iddah, shine yan zun nace, bari na zo na sameku tunda na sami labarin anyi bikin haihuwar da Nargeesah tayi, shekaran jiya, shine nasan zan sameku a tare, dan Allah Humaira kiyi hakuri ki dawo mani da Jafar nasan da sanin cewar kin Aure sane saboda ni na guje sa badan kuna shiri da juna ba, wallahi nayi maki alkawarin zan kula dashi, kuma zan anshi yaron da kika haifa zan riƙesa tamkar yaron da zan haifa da ciki na!".



Ta fashe da kuka nukam kallon ta kawai mukeyi, zuwa can na ce, "to nidai ban san miye zan ce dake ba, amman ina iya faɗar Allah ya kyauta kuma Allah yasa yanda muka hana iyayen mu kuka muma, ya'yan mu kada su saka mu kuka, dan son zuciya ɓatan ta".


Hindu ta ce, "a nufin ki muji tsoron gujewa aikata son zuciyar mu, ko kuma kin kawo muna kukan ki ne? Dan na kasa fahimtar komai ".


Humaira ta ce, "Haleema ke nan to yan zun kam na fahimce ki, wato tunda ga Humairar mahaukata, ai dole ne naci gaba da baki farin ciki na, kina saka ni kuka, kuma dolene yi maki duk abunda kike so, to bari kiji wani abun, Haleema ni da kike gani a yan zun na wuce da sanin ki, wato nasa daukar da ɗana Haniff na baki, uwa uba soyayyar mijina, duk dan ke kiyi farin ciki, to lallai ne sai yan zun na tabbar da kina hauka ne Haleema, ina son Jafar ko nace dake abu Haniff, bana jin zan iya barin wata mace ma ta raɓesa da sunan soyayya ballema ace Aure, ni Ummu Haniff nayi maki nisan da ba zaki iya hango koda wutsiya ta bane, Yaya Jafar nawa ne dan ni akayo sa, ai kin riga da kin koya mani son Jafar dan haka, ba zan ce, ba zanyi zumunci dake ba, amman kada ki yarda zuciyar ki ta ƙara raya maki cewar ni Humaira zan sake sadaukar maki da farin ciki na, eh lallai ne na Auri Yaya Jafar bana son shi shima baya sona, amman kuma abun al'ajab anan kuwa shine a yanzun nida Yaya Jafar mun afka a tafkin soyayya mai zurfin gaske, wanda ko masoyan da sukayi Auren soyayya ba zasu kaimu shauƙin junan mu ba, dan haka ki iya halshen ki Haleema "


Haleema sakin baki tayi tana kallon mu, su Yaya Jafar da suka shigo tun ɗazun ne ya ce, "Haleema kike koma waye, oho!? ban damu ba, Humaira ita ce rayuwa ta ai sai yan zun ma da kika dawo na sake gane hakan, Ummu Haniff ita ɗaya ce, a zuciya ta, dan haka ki ja jikin ki, Humaira taso muje gida dan yau ina jin idan na tsaya a gidan nan za'ayi abun kunya".


Haniff dake rarrafe ne ya rarrafa yayi gurin Yaya Jafar ya ɗaga shi sama yana yi masa wasa, tashi Humaira tayi suka tafi bayan tayi sallama da kowa haka Hindu tare suka fita itada yaya Aliyu, haka Haleema taja ƙafar ta, tana kuka tabar gidan.


Bayan kwana biyu Inno ke tambaya ta, wai kuwa Salman yana gari kuwa? Dariya nayi nace, "baya nan ai Dad ne ya saka shi ya kammala masa wani aikin a london to da fushi ya tafi shi yasa, suka daina jin sa, ni ce, ma nake kiran sa, ina saka shi ƙara jin haushin tafiyar".


Dariya aka saka Inno ta ce, "ai kuwa zan rama masa, bari dai zaki gani"


Ban damu ba dariya ma Kawai nake yi, haka har mukayi kwana arba'in da biyu, gyara kam nasha shi, kitso da lalle akayi mani na yawon arba'in, sai gashi Inno da Yaya suka ce, zan je na yiwa Mai martaba barka da wannan matsayin da Allah ya bashi, suka haɗa mani kayan da zamu dasu, suka rakani har mota, ina shiga da Shuraim ya zauna aka ɗora masa Sultana a ƙafar sa, ni kuma Sultan ne a jiki na, muka ɗauki hanya, sai airport inda Yayan mu, ya kaini, muka shiga jirgin, muka ɗaga, sai garin Abuja.


Muna sauka sai alokacin ne na tuno ashefa Abuja muka zo to miye yasaka Yaya Auwal yayi muna bucking na jirgin Abuja? Run gume ni akayi ta bayana, ai da sauri nake ƙoƙarin kubcewa, ina jiyowa sai akan Salman ido na ya sauka ya rungume Hannuwan sa, yana kashe mani ido ɗaya yana ɗaga gira ɗaya, ya ce, "ya dai madam, kin yi mamaki ne? Ai daman nace zan rama gashi dai su Inno sun tayani ramuwa"


Haushi naji na ce, "haba dear ban fayi yawon arba'in ba fa, ni wallahi ba a kyauta mani ba".


Dariyar shakinyan ci yakeyi ya anshi Sultan yaja hannun na, Shuraim a cikin motar muka same sa nima ya saka ni, ya shiga aka rufe motar muka ɗauki hanyar gidan sa, sai fushi na keyi shida Shuraim sai dariya sukeyi wai ashe haka na iya smile, bai sani ba, Shuraim duba ka gani, yau tafi kullum kyau ko? "


Da sauri Shuraim ya ce, "Daddy fuskar Mommy idan tayi fushi tafi kyau, gashi har da baki take turowa kamar na Baby Sultana tana son nono".


Doke masa baki naso yi Salman ya tare masa, ya ce, "kai hubby harda dukan nan irin na naji daɗin yanda ake yabo na? ".


Ai kuwa kukan shugaba na fashe dashi dan duk sun cika ni, sai suka dawo lallashi na har nayi shiru, wani haɗaɗɗen gida Salman ya kai mu, tsayawa faɗar kyauwan sa, ɓata lokaci ne, dan yafi wan can tsohon gidan ba, komai bane akan wannan.



Kai Alhamdulillah soyayya muke kwasa da kulawa nida yara na, sai sam barka, arzikin Salman ƙaruwa yakeyi sai dai muce Alhamdulillah.


Bikin su Yaya Auwal aka haɗa dasu Amrah da Mariya amman banda Nusaiba inda Amrah ta Auri Muhseen ashe sun daɗe suna soyayya ni ce, ban sani ba, sai da abun yazo, a gaskiya munsha shagalin biki.



Nida Salman zama mukeyi, na amana da ƙaunar juna, tarbiya muke baiwa yaran mu ukku babu abunda muka nema muka rasa.

*Alhamdulillah*



*Nima dai anan nake cewa Allah ya yafe muna kura kuren da naikata a cikin wannan littafin da laifuka na baki ɗaya, Allah ka jiƙan iyayena, Allah ya yafe masu ya kai haske kabarin su tare da yan uwa musulmi baki ɗaya amin*



*Sai Allah ya sake haɗa mu a cikin littafi na gaba Ummu Ihsan ce keyi maku fatan alkhari*


*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment