Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo musu taimako, kuka sosai takeyi amma na zuciya ganin kiran nata shiga ba'a ɗagawa.

A ɓangaren Zarah kuwa tun ƙarfe 12:30nr kwamishina ya mata kiran gaggawa domin su gana, fiye da awa ɗaya yanata yi mata surutan da basu shafi gefen da take aiki ba amma a matsayinshi na shugabanta ta kasa tanka mishi duk da tanason komawa gida su gaisa da kakanninta da ƴan uwanta da sukazo.
Wayoyinta gabaɗaya suna cikin mota hakan yasa batasan irin kiran da Rahma ke mata ba.

Sai da suka tabbatar da babu wani sauran mai rai a cikinsu kafin su bar gidan.

Ganin Zarah bata ɗaga kiran ne yasa Rahma danna kiran wani abokin Yayansu Mustapha dake aikin soja, bugu biyu ya ɗaga kiran yana mamakin kiranshi da tayi domin ya daɗe yana mata magiyar soyayyarshi amma tana wulaƙantashi.

Yana ƙoƙarin magana ta riga shi.

"Ka taimakeni Mustapha zasu kashemin iyayena dan Allah kazo da sauri". Ta faɗa da disasshiyar muryarta saboda kukan da takeyi.

Jin abinda ta faɗa ne yasa shi miƙewa daga zaunen da yake.

"Rahma su waye zasu kashe miki iyayen kuma a ina suke.?"

"Suna cikin gidanmu yanzu haka sun ɗaure kowa da kowa nima basu ganni bane, dan Allah kazo da sau..... " kuka ne yaci ƙarfinta batare da ta ƙarasa maganarta ba.

"Subhanallahi! Ki zauna a inda kike gamu nan zuwa."..

Bata iya amsawa saboda toshe bakinta da tayi tana kuka.

Cikin mintuna goma sha biyar taji jiniyar sojoji wanda hakan ya tabbatar mata da Mustapha ya iso da jami'ansu na soji.

A farfajiyar gidan kuwa mai gadi ne da sauran ma'aikata biyar dake musu aiki kwance basu motsi, tun daga hakan Mustapha ya gane tabbas babu lafiya hakan yasa suka tunkari ƙofar babban falon cikin shiri da ƙwarewar aiki.

Jini suka fara arba dashi bayan buɗe ƙofar har zuwa cikin falon, da basu kasance sojoji ba toh tabbas sai wasu daga cikinsu sun firgice da ganin gawarwakin mutanen dake kwance domin kuwa kisa aka musu tamkar a kwata.
Lungu da saƙo na gidan gabaɗaya sun duba amma babu kowa hakan ya tabbatar musu cewa masu laifin sun samu nasarar tserewa.
Duk da haka sai suka raba kawunan su a ɓangarorin gidan ciki da waje.

Ƙarfin hali kawai Mustapha yake yana maida hawayen dake son zubo mishi, lambar Zarah ya shiga kira saidai ba'a ɗagawa. Ganin haka ya canja akalar kiran ga wani maƙocin shi D.P.O yayi mai bayani tunda case ɗin ba wanda sojoji zasu shiga bane, taƙaitaccen bayani kawai ya iya yimishi ya kashe wayar.

Cikin mintunan da basu wuce talatin ba ƴan Sanda da sojoji suka kewaye gidan ta kowanni fanni.

Hayaniyar mutane da taji sosai ne yasata jarumtar buɗe ƙofar banɗakin, saida ta fara leƙowa taga taron masu kaki ne sannan ta fito gabaɗaya.
Abinda ta gani ne yasata sakin ihu tare da faɗowa ƙasa sumammiya.

Sai a lokacin mutanen dake falon suka ankara da ita, shikuwa Mustapha sai a lokacin ya tuna da ita tun bayan da yayi arba da mummunar ɓarnar da akayi musu.

"Ya kamata a sanar da wani a cikin danginsu domin bazamu iya yin wani abu da gawarwakin batare da izinin su ba." cewar D. P. O. dake kusada Inda Rahma ke kwance.

Waya Mustapha ya ciro tare da danna lambar Alhaji Sulaiman sannan ya miƙama D.P.O wayar domin baisan ta ina zai fara faɗin wannan baƙin labarin ba.
Fita yayi bayan ya karɓi wayar bai jima sosai ba ya dawo sannan ya miƙawa Mustapha wayar.

Ƙarfe huɗu daidai motocin Alhaji Sulaiman da tawagar shi suka iso, motar farko mutane biyar ne a ciki. Direba dake jan motar sai Alhaji Sulaiman dake gefenshi a baya koma Baaba Faɗimatu, Ammi da Momi.
Sauran motoci biyun koma abokan kasuwancinshi ne a ciki daya sanar musu da rasuwar suka biyoshi domin yin jana'iza.

Ganin Ƴan sanda da sojoji yasa kansu ɗaurewa domin dai Alhaji Sulaiman ɗin bai sanar dasu abinda ke faruwa ba umarni kawai yabada su shirya suzo garin Bauchi.

Momi ce tayi ƙarfin halin magana lokacin da direba yayi parking.

Tace" Daddyn su meke faruwa ne haka, meya kawo jami'an tsaro haka a gidan. Kodai Zarah ta karɓi masu tsaron da aka bata ne.?"

"Tambayoyin sunyi min yawa ku sauka mu shiga ciki, tada Baaba daga baccin nan haka tunda mun iso." Ya faɗa gamida ficewa a cikin motar

Ammi kuwa ta kasa tankawa domin zuciya da gangar jikinta sun tabbatar mata babu lafiya.

"Meke faruwa ne naga ƴan'uwansu Zara'u sun cika gidan.?" Faɗin Baaba Faɗimatu da farkawarta kenan daga baccin data fara tun a hanya.

"Mu shiga daga ciki dai Baaba sai muji abinda ke faruwa domin dai waƴannan jami'an tsaro akwai abinda ya kawosu ko kuma suke tsaro." Momi tafaɗa tana mai buɗe ma Baba ƙofar.

Cikin rashin kuzari Ammi ta fito tabi bayansu suka nufi hanyar shiga cikin gidan.

Sam Alhaji Sulaiman baiyi tunanin irin ɓarnar dazai tarar ba kenan domin D.P.O ɗin ce mishi kawai yayi ƴan fashi sun shiga gidan ɗan'uwan shi sunyi fashi haɗe da kisa.
Kuka yake bil hakki ganin irin kisan wulaƙanci da akayi musu duk da kasancewar ƴan Sanda sun gyarasu daga asalin yadda suka samesu bayan likita ya tabbatar babu wani mai sauran numfashi a cikin su. Saidai tambarin *Alpha*🌴 da aka zana da jini na nan a tsakiyar falon.

Da sauri ya miƙe da nufin tsayar dasu daga shigowa falon kasancewar su mata yasan dole basu da juriyar da zasu iya ganin wannan aika aikar, hatta shi dayake namiji yanajin tamkar ya ciro zuciyarshi ya aje a ƙasa saboda tarin baƙin cikin daya shige shi a lokaci ɗaya.

Saidai kash!!! Kafin yakai ga ƙarasawa ƙofar fita daga falon Momi da Baba Faɗimatu sun sako kai bakinsu ɗauke da sallama, duk da haka saida ya ƙarasa inda suke cikin sassarfa ya kare fuskokinsu daga ganin cikin falon.

"Baaba da kun ɗan tsaya a waje ana gudanar da bincikene anan."

"Sulaimanu wani irin bincikene akeyi haka daya saka zubar da hawaye, ka matsa ka bamu guri mu ƙarasa muga abinda ake ɓoye mana. Shin ina ahalin gidan ne.?" Faɗin Baaba kenan tana mai kaucewa daga hanyar daya tare.
Bayanta Su Ammi su bi domin ƙarasawa falon.

Abinda ya guda shiya faru domin a tare gabaɗaya su ukun suka zube a ƙasa sumammu, shima dai hawayen ne yake zubo mishi.

Wani daga cikin mutanen falon ne yayi dabarar watsa musu ruwa saidai Momi ce kawai ta farfaɗo itama ba'a cikin hayyacinta ba.

"Dan Allah ku tayar dani daga wannan mummunan mafarkin ba gaskiya ban.." bata ƙarasa ba ta ƙara sulale wa.

"Yallaɓai kasa hannu anan munason mu wuce da gawarwakin asibitine domin gudanar da bincike." cewar likitan da aka damƙa case ɗin binciken gawarwakin a hannunshi yana miƙawa Alhaji Sulaiman wasu takardu.

"Babu wani binciken da za'a gudanar saboda a yau ɗinnan nakeson a sadasu da gidansu na gaskiya, ku taimakawa waɗannan dake sume kawai." Yafaɗa cike da rauni.

Nan ya ciro waya ya fara bugawa ƴan uwa da abokan arziki, abu da zamani nan da nan anguwar ta cika maƙil da jama'a domin sallartar mamatan.
Da taimakon likitoci aka samu damar kimtsa su a cikin likkafani Saidai kafin wani lokaci gabaɗaya sun rine daga kalar fari zuwa Ja saboda jinin dake zuba da jikin gawarwakin.
Sau uku ana canjawa amma babu wani sauyi hakan yasa aka barsu a haka.

Acan falon baƙi kuwa Limamin masallacin Juma'a na gwallaga ne tare da su Momi da aka samu suka farfaɗo dakyar, saidai har zuwa wannan lokacin Rahma bata farka ba hakan yasa aka wuce da ita asibiti.

Nasiha ya musu mai ratsa jiki hakan yasa suka sassauta da koke koken da sukeyi, nan suka miƙe suka nufi falon inda baƙi suka fara cika. Nan aka fara gaisuwa da jajantawa.

Kwamishina ne ya kalli Zarah dake zaune a kujerar dake fuskantar shi yace

"Zarah ta wace hanya kike ganin zamu iya magance matsalar tsaro a ƙasar nan.?"

Zuwa yanzu Zarah ta fara zargin akwai wani abu a ƙasa domin duk lokacin da tayi nufin tafiya sai shugaban nata ya tsayar da ita ta hanyar yi mata wasu maganganun da ba ita ya dace a faɗawa, cike da ƙosawa tace " Yallaɓai a tunani na wannan matsala ce da zamu taro mu samu mafitar ta, matsala ce data shafi jaharmu da ƙasa baki ɗaya don haka muna buƙatar mu tattauna da sauran manyan jami'ai domin samun mafita.?"

Kafin ya samu damar amsa mata wayarsa dake gefe tayi ƙara, hannu yasa ya ɗauku wayar tare da karawa a kunnenshi batare da yayi magana ba.

"Zaka iya bata damar tafiya yanzu mun gama aikinmu sannan ka duba wayarka akwai saƙon kuɗi dana turama a asusun bankin ka."
Abinda aka faɗa kenan daga ɗaya ɓangaren sannan aka kashe wayar batare da jiran amsar da kwamishinan zai bada ba.

Kallon shi ya maida kan Zarah yace" ASP zaki iya tafiya. "

Cike da mamaki ta miƙe tare da sara mishi sannan tafice a ofishin, jikinta taji ya mata wani iri ga zuciyarta dake bugawa da ƙarfi tamkar zata faso ƙirjinta.

Shigarta cikin mota yayi daidai da katsewar kiran wayarta dake ringing kafin shigowarta, sai da ta zauna kafin ta sa hannu ta ɗauki wayar.
Ido da zaro ganin anyi mata kira har 66, take ta duba domin ganin masu kiran, 35 missed calls daga Rahma, 6 missed calls daga Mustapha, 15 missed calls daga Daddy sai sauran kira 10 daga mutane daban daban.

Da sauri ta shiga danna kiran Rahma saidai har ta gama ringing ba'a ɗaga, haka tayi ta kira ba'a ɗagawa kafin ya danna kiran Daddy sai dai wayarsa bata shiga.
Ganin haka yasa ta canja akalar kiran ga wayar Mustapha.

Bugu biyo ya ɗaga tare da faɗin" Zarah kina inane haka ake ta kiran wayarki bakya ɗagawa."

"Na shiga ganawar sirri ne da kwamishina kuma wayar na cikin mota, meke faruwa ne.?" tafaɗa cike da zaƙuwar son jin abinda ke faruwa domin a lokacin bugawar da zuciyarta keyi ya ƙaru.

"Babu komai ki taho gida anason ganinki." yafaɗa gami da kashe wayar baki ɗaya.

Cikin sauri ta taɗa motar tare da harbawa kan titi bakinta ɗauke da kalmar hasbunallahu wa ni'imal wakil saboda yanayin da take jinta a ciki.
Tun daga farkon shigowar anguwansu take ganin jerin motoci har zuwa gaban gidansu data tara cike da jama'a, nan zuciyarta ta ƙara tsinkewa gami da tabbatar mata lallai wani abu ya faru, horn ta danna a ƙofar gidan saidai a maimakon taga mai gadinsu sai taga Alhaji Sulaima na buɗe mata ƙofar.
Bata ko gama parking ɗin motar ba ta fito da sauri, hannunta taji an riƙo hakan yasata tsaya wa daga tafiyar data fara tare da waigowa Daddy ta gani a tsaye.
Kallo ɗaya ta mishi taga alamun kuka a fuskarshi.

"Daddy meke faruwane dan Allah ka faɗamin."

Batare da yayi magana ba yaja hannunta suka koma jikin motar, ƙofar baya ya buɗe mata tare da gyaɗa mata kai alamun ta shiga sannan shima ya shiga ya zauna.

"Zarah." ya faɗa bayan ya zauna

Cike da rauni ta amsa da" Na'am Daddy".

"Nasan kinyi karatun islamiyya har zuwa matakin da kika sauke alqur'ani koh.?"

Kai kawai ta iya gyaɗa mishi.

"Inaso ki nutsu wasu tambayoyi zan miki."

"Toh Daddy."

"Inaso ki gayamin abinda Allah yace a cikin suratul Baqara a ƙarshen aya ta ɗari da hamsin da biyar zuwa aya ta ɗari da hamsin da shida(2:155-156) tare da ma'anar shi."

Kai ta jinjina sanna tace" Allah maɗaukakin Sarki yana cewa

و بشر الصبر ين(155) لَّذِينَ إِذَآ أَصَٰبَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوٓا۟ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيْهِ رَٰجِعُون(156)
Fassarar shine
"Kuma kayi bishara ga masu haƙuri(155) Waɗanda suka kasance idan wata masifa ta same su sai su ce _Lallai ne mu ga Allah muke, kuma lallai ne mu, zuwa gare Shi muke komawa._

A taƙaice ayar na nufin idan Allah ya jarabci bawa da wanu abu na baƙin ciki sai ya kasance mai yawan furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".

Murmushi yayi wanda iyakar shi fuska sannan yace" Masha Allah, to me Allah ya sake cewa a cikin suratul Ankabut aya ta hamsin dashi.?"

Allah yace"

كُلُّ نَفْسٍ ذَآئِقَةُ ٱلْمَوْتِۖ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ
Fassarar ayar
"Kowani rai mai ɗanɗanar mutuwane, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar daku."(Q29:57).

"Alhamdulillahi tunda kin kasance mai ilimi, kinga kenan duk abinda yasamu bawa to ƙaddararre ne sannan da mutuwa da rayuwa duk na Allah koh.?". Daddy yafaɗa yana mai yimata kallo irin na tausayawa.

"Ehh hakane Daddy."

"Toh Zarah inaso ki kasance mai haƙuri tare da rungumar ƙaddarar data same mu duka, kiyi haƙuri ƴan fashi sun shigo gidannan sannan sunyi kisan kai kafin su tafi."

A ruɗe ta kalli Daddy tanason gane inda maganarshi ta dosa.
Tace" Ƴan fashi, kisan kai.? Wa suka kashe mana.?"

Ganin tana shirin ficewa a hayyacinta ne yasa ya riƙo hannayenta biyu tare da faɗin" Ki nutsu Zarah sannan ki cigaba da faɗin kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."

Haka yayi ta maimaita mata har zuwa lokacin da ta ɗan nutsu kafin ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofar motar ta fito sannan yajata zuwa inda aka ajiye gawarwakin kafin a fita dasu a sallace su domin farfajiyar gidan bazata ɗauki mutanen da sukazo jana'izar ba.
Dangin mamatan ne a gurin kowa yana karantu musu addu'a tare da kallon ƙarshe.

Abinda ta hangone ya sata sulalewa a ƙasa batare da sun ƙarasa ba, da sauri Ammi data hango lokacin faɗowarta ta nufi inda butar Baba me gadi take ta ɗauko tare da watsa mata ruwan ciki a fuska.
Shidai Daddy yana tsaye yakasa koda motsawa domin zuwa yanzu shima ya fara rasa jarumtar shi.

Tsiyaya mata ruwan Ammi ta farayi ganin bata farfaɗo ba.

Cikin sa'a kuwa taja numfashi mai ƙarfi.

_Cigaban labari_.

Zuwa ƙarfe bakwai na dare gidan ya ƙara cika sosai saboda ƴan uwa da abokan arziki na nesa da suka ƙaraso, domin hatta dangin Babansu Shahid dake Taraba duk sunzo kasancewar dayawa daga cikinsu jirgi suka bi.
Haka akayi ta koke koke kafinan suka saurara aka cigaba da karɓan gaisuwa.

A daren ranar dai babu wani daga cikin wannan ahalin daya samu damar runtsawa, kwana sukayi suna raya wannan dare da yiwa matattun addu'o'i tare da fatan Allah ya basu juriyar rashin da sukayi.

Daddy ne ya hana a sanar da Sadiq dake ƙasar Singapore yana rubuta jarabawarshi ta ƙarshe na zama cikakken likitan zuciya wato *Cardiologist Consultant* sakamakon asarar shekaru da zaiyi inhar baici jarrabawar.

Muhammad Jawwad kuwa sai ranar da akayi sadakar uku Daddy ya sanar dashi, shima dai kuka yayi tayi saida Daddy ya rarrashe shi. Nan yace ma Daddyn zai nemi biza ya taho bayan yayi ƙorafin rashin faɗa mishi da ba'ayi da wuri ba.

Bayan kwanaki ukun ne baƙi suka rago a gida amma kullum wuni suke karɓar gaisuwa daga mutane daban daban, masu kwana ne dai babu.
A cikin kwana ukun nan duk wanda yaga halin da suke ciki saiya kuka, Baaba kawai mai ƙarfin hali a cikin su.
Ga Rahma da har yanzu bata farfaɗo ba.

Gabaɗaya suna zaune a falo a daren ranar ukun harda Daddy da Mustapha da shima kullum baya rabo da gidan.

Zarah na kwance saman dogowar kujera yayinda tayi filo da ƙafar Baaba.
Lokaci ɗaya ta miƙe a firgice.

Kallonta Daddy yayi tare da faɗin" Lafiya kuwa Zarah.?"

"Daddy CCTV , na jona CCTV a duka falon dake gidan nan." Ta faɗa lokacin da ta miƙe sannan da gudu ta nufi hanyar ɗakinta......

Da gudu ta nufi cikin ɗakin tare da nufar inda ƙaramar na'urarta take ajiye, sashin abubuwan da suka faru a cikin satin ta shiga tare da playing daga ranar farko.

Daddy da sauran mutanen gidan ne suka shigo ɗakin, gabaɗaya suka zauna domin kallon abinda ke wakana a cikin na'urar.
Saidai gabaɗaya babu abubuwan da suka faro a kwanaki uku da suka wuce wanda hakan ya tabbatar mata da cewa akwai wani wanda ya shaidama Alpha na'urar da ta saka.
Cike da takaici ta rufe na'urar tare da kwanciya akan gadonta.

Babu wanda ya tanka duk suka fice a ɗakin.

Babu daɗewa kira ya shigo wayar Zarah, hannu ta kai ta janyo wayar tare da kallon fuskar wayar domin ganin mai kira. Ɓoyayyiyar number ce ke kira, tamkar bazata ɗaga kiran ba saida ta kusa yankewa kafin ta ɗaga tare da karawa a kunnenta batare da tayi magana ba.

"Na tabbatar yanzu kin fara gaskata abinda Alpha yake da damar yi ga duk wanda ya shiga gonarsa." Daga ɗaya ɓangaren aka faɗa

Zaune ta miƙe batare da tayi magana domin ta gane wanda yake maganar.

Magana ya cigaba dayi ta hanyar faɗin "Kada kiyi saurin karaya ta hanyar ajiye aikinki Zarah domin kin riga kin shiga wasan da baki da damar fita, ba'ayi komai ba tukun. Kin shirya bada kadarar ko baki shirya.?"

Mamaki ne ya cikata jin abinda ya faɗa, tabbas Alpha ba ƙaramin shiri yayi akanta ba domin da Daddy kaɗai tayi maganar ajiye aiki kuma shiɗin ma bai goyi bayan hakan ba sannan tanada tabbacin cewa ba wajen Daddy yaji wannan batun ba. Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye kafin tace

"Bana zuwa akan lokaci amma tabbas idan na iso waje ina jan ragamar kowani wasa tare da kasancewa mai nasara, ka faɗama kowaye ya sanar dakai cewa Zarah zata ajiye aiki da yaje ofishinta a gobe ranar litinin domin ya samu maka cikakken bayani."

Bata jira mai zaice ba ta kashe wayar gabaɗaya.
Takalmi ta zura tare da fita zuwa falo, dukkan su suna zaune kamar yadda suke da farko.

Zama tayi kusada ƙafafun Daddy tare da faɗin
"Daddy inaso gobe zan koma bakin aiki."

"Zara'u wace irin magana kikeyi haka, kodai kema ƙwaƙwalwarki ta taɓo ne kamar yadda ƴar uwarki ta samu.?" Faɗin Baaba wacce maganar da Zarah tayi ya tadata Zaune daga kishingiɗen da take.
Sunkuyar da kai tayi batare da tayi magana ba.

Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.
"Baaba ina ganin mu barta ta koma bakin aikinta ƙila akwai wani muhimmin abu da zata gudanar ne bayan haka kuma zamanta a gida bashine zai dawo mana da waƴanda muka rasa ba. Hasalima aikin nata zai taimaka wajen binciko da masu hannu akan wannan lamarin."

Jinjina kai Baaba tayi cikin gamsuwa da maganganun Daddyn sa'an nan tace.
"Toh yaya batun Rahmatu kuma.?"

"Ehh Amminsu zata wuce da ita can Cairo a cigaba da duba lafiyarta tunda maigidan nata ya amince, Zarah kuma zata zauna anan saboda binciken da zata cigaba da gudanarw. Sannan ina neman alfarmarki Baaba da ki cigaba da zama anan tare da ita, kasancewar mace bai kamata ta zauna ita kaɗai ba saboda kare mutuncinta. Insha Allahu kuma zamuyi ƙoƙarin ziyartar ku lokaci lokaci kamar yadda muka saba." Cewar Daddy

"Babu damuwa Sulaimanu Allah yayi albarka ya albarkaci zuri'a."

Da Ameen sika amsa gabaɗaya kafin kowa ya miƙe domin zuwa kwanciyar bacci wanda a zahiri ba haka bane domin raba dare suke gaban mahalicci suna kai mishi kukansu.

Washegari tun ƙarfe bakwai Zarah ta fito cikin shirinta sanye da kakinsu na ƴan sanda, baƙin wando da shuɗiyar riga, inda ta ɗora baƙar Abaya mai ratsin shuɗi a saman kayan sannan tayi rolling da gelen rigar.

Ammi kaɗai ta tarar zaune a falo tana jan carbi, ƙarasawa tayi tare da zaunawa a ƙasan kujerar da Ammin ke zaune.

"Barka da safiya Ammi."

Kanta Ammin ta kwantar akan cinyarta tare da shafawa a hankali.

"Ina fatan kintashi lafiya.?"

"Lafiya lau Ammi, zan wuce aiki ina barar addu'a." cewar Zarah lokacin da take gyara kanta a cinyar Ammin.

"Allah ya kareki daga dukkan sharrin masu sharri, Allah ya nesanta zuciyarki da aikata abinda ba daidai ba, Ina roƙon Allah ya baki nasara ga duk abinda kikasa a gaba. Allah ya albarkaci rayuwarki."

Cike da jindaɗin addu'o'in Ammin take amsawa da Ameen kafin ta miƙe tare da mata sallama ta nufi hanyar fita daga cikin falon.

Gurin motarta da yaran Mustapha suka wanke mata ta nufa domin masu yi musu aiki tun bayan faruwar wannan lamarin suka aje aiki saboda tsoron kada a ƙara kawo wani harin a haɗa dasu tunda na farko dai hodar saka bacci aka shaƙa musu basusanai zai iya faruwa ba nan gaba.

Cikin mintuna ƙalilan ta isa ofishin nasu, tun kafin ta ƙarasa parking sergent Bala ya iso inda motar take ya buɗe mata ƙofa bayan ta gyara tsayuwar motar.
Ƙamewa yayi har saida ta fito sannan ya kulle motar.

"Ranki ya daɗe barka da safiya. Ya ƙarin haƙurin mu."

"Barka dai Bala, haƙuri mungode Allah." ta faɗa tana mai fara tafiya domin isa ofishinta.

Karbar jakarta yayi bayan yace" Allah ya gafarta musu."

"Ameen." tace a taƙaice.

Haka ƙananun jami'an suka jigaba da mata gaisuwa harta ƙarasa cikin ofishin ta.

Tana ƙoƙarin ajiye wayarta akan tebirinta kira ya shigo, ganin mai kiran ne yasata sakin wani kyakkyawan murmushi.

"Assalamu alaiki ya habibaty." abinda aka faɗa kenan bayan ta kara wayar a kunnenta

"Wa'alaiki salam Dr. Jiddah amaryar Bar. Saleem." Zarah ta faɗa tanamai zama a kujerarta

''Ki faɗawa wanda bai sani ba, naga alama tsokanar da bakiyi kwana biyu ba kikeson yi kuma ba kulaki zanyi ba. Dafatan kin tashi lafiya yasu Ammi."

"Lafiya lau suke duka."

"Ya ƙarin haƙuri kuma."

"Alhamdulillah."

"Allah ya musu Rahama."

"Ameen Ameen. Ina kika baro maƙalematan naki banji motsinsa ba." Zarah ta faɗa cike da barkwanci.

"Ke dai bari habibaty, jiya kwana nayi ina mishi kukan nagaji da zama a cikin masu jajayen kunnuwa shine yau ba shiri ya fita domin fara haɗa tarkacensa." Jidda kenan take maganar cikin sanyi murya.

"Babu kyau abinda kike aikatawa fa, ki dinga damun bawan Allah yana miki abinda kikeso koda shi bayaso ɗin."

"Auren kenan ai kema kiyi kigani ko baza'a miki abinda kikeso ba."

Kafin tayi magana aka kwankwasa ƙofar ofishin nata da haka tace.

"Zamuyi magana anjima SA.JID zan fara aiki a ofis."

"Innalillahi! Yanzu Zarah tun ba'a sadakar bakwai bama har kin fara fita wannan ƙaddararren aikin, so kike ki jama kanki zance a gari."

Shiru Zarah tayi na wani lokaci kafin tace" Jiddah ya zanyi to, *Alpha* kinsani Idan ban kasance a ofis ba na wani lokaci mutane da dama zasu rasa abubuwa masu mahimmanci sanadin wannan mutumin."

"Shikenan Allah ya taimaka, nima dai Insha Allah zuwa wani watan zamu dawo." Jiddah ta taɗa cike da tausayin Zarah.
Sallama sukayi sannan suka katse kiran lokaci guda.

Umarni ta bada a shigo lokacin da take ajiye wayar a kan teburinta.

Sergent Bala ne ya kuma shigowa hannunshi ɗauke da farar takarda, saida ya sara mata kafin ya fara magana.

"Ranki ya daɗe wannan saƙo ne daga ofishin mai girma kwamishina, jiya da yamma ya aiko tare da bada umarnin lallai akai miki saboda abune mai mahimmanci. Dama yau nakeson kawo miki idan na tashi a aiki sai kuma gaki kinzo."

Kaɗa kai Zarah tayi kafin tace" Sau sa dama Bala ina gayamaka ka koyi saka maganganu a cikin kalma ɗaya, basai kayita dogon sharhi ba a matsayinka na ɗan sanda. Anaso maganar jami'i ta banbanta dana sauran mutane, anfiso idan kayi magana sai mutane sunyi nazari sosai kafin su gane ainahin abinda kake nufi ba kamar yadda kake magana yanzu ba."

Ƙamewa ya kuma yi kafin yace.

"Ayimin afuwa ranki ya daɗe zan gyara."

Bata kula da maganarshi ba tace.

"Me takardar ta ƙunsa."

"Ranki ya daɗe bani da damar buɗewa saboda a kulle take cikin envelop."

Hannu tasa ta karɓi takardar tare da buɗe envelop ɗin ta cirota.
Mintuna biyu ta ɓata wajen nazartar abinda ke cikinta.

Ɗagowa tayi daga kallon takardar tare da maida kallonta ga Sergent Bala sa'an nan tace.

"Taron ƙarawa juna sani a harkar aiki ne ake umartana naje wanda za'a gudanar a garin Abuja. Cikin sati ɗaya za'a gama gudanar da taron wanda zai fara ranar alhamis, sannan kaida Jennifer ne zamu kasance tare."

Bata jira mai zaice ba ta bashi umarnin tafiya.

Jingina kanta tayi da jikin kujerar sannan ta lumshe idanuwa.

Haka ta wuni a ofishin sam takasa taɓuka komai bayan kuma da shirin yin aiki ta fito saidai ta danganta hakan da saƙon kwamishina daya risketa.

Cikin kwana ukun ta kammala duk wasu shirye shiryen ta na tafiyar.

A gefe guda kuma su Ammi na shirye shiryen tarban Muhammad Jawwad da shima zai iso ƙasar ranar Alhamis wanda rabonshi da ita

1 Comments On ASP ZARAH
avatar
zainab-3-7-9

1 year ago

Reply

I need complete Asp zarah

Please Login or Register in order to submit comment