Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamu kuma aikata hakan ba nan kusa ba akwai sauran lokaci."

"Amma yallaɓai naji kamar batun aurenta akeyi."

A kishingiɗe yake amma jin wannan batun yasa shi miƙewa batare da yasani ba, cin hargagi yake faɗin.
"Aure! Aure dai? Meyasa baki faɗan hakan tuntuni ba Raliya, sai zuwa yaushe ne ƙwaƙwalwarki zata dinga yin abinda ya kamata ne."

"Kayi haƙur..."

"Hell with this fucking word Raliya! Hakurin me zanyi, abubuwa na shirin lalacemin kice wai nayi hakuri."

"Amma yallaɓai naga wanda zata aura ɗan gida ne shiyasa banyi tunanin komai."

"Wanene wanda zata aura ɗin."

"M.J ne."

Wani murmushi yayi mai sauti kana yace.
"Woow! Komai ya kusa zuwar mana da sauƙi, kin tabbata shine wanda zata aura."

"Na tabbata ranka ya daɗe yanzu haka ma yana garin Bauchi yazo ganinta."

"Ki tsaya ki saurareni dakyau Raliya, wannan ne lokacin mu na samu ko rashi, a yanzu ne muke da damar yin duk wani abu da muka daɗe muna shiryawa, inaso ki lura sosai da duk wani motsinta daga yau, saboda inada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za'a nemi sauyawa diamonds ɗin nan wajen zama, ki sanar dani duk wasu bayanai da zaki samu, zan organising team ɗin da zakuyi aiki tare da zarar angano inda suke kiyi ƙoƙarin samu mana bayanai kawai."

"Zan kula sosai yallaɓai."

"Ohk" kawai ya kuma faɗa tare da kashe wayar.

Shiru tayi bayan gama wayar tasu tana tunani, tabbas wannan ita kaɗaice damar da take da ita domin ƙara samun kusanci da Alpha, ya zama dole yanzu ta shirya ɗamarar yin fito na fito da Zarah akan Diamonds ɗin nan, ba damuwarta darajarsu ba ko kuɗin da za'a samu akansu, babban abinda ya dameta shine ta wannan hanyar ne kaɗai Alpha zai dinga ganin ƙimarta har ta samu nasarar cusa soyayyarta a cikin zuciyarsa, saboda sanin yadda yake da babban buri akan Diamonds ɗin.
"Lokaci yayi da zanja ragamar wasan nima." ta faɗa cikin wani shu'umin murmushi.

💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫

Gefen hanya ta samu tayi parking motarta saboda kiranta da Jidda keyi a waya, hannu tasa ta ɗauki wayar tare da maida kiran daya kuma katsewa.

"Ina kika shiga ne nake kiranki bakya ɗagawa."

"Toh shugabar masu ƙorafi tuƙi nakeyi."

"Kin fita aiki ne?."

"Aa cefane naje yi inaso na shiga kitchen da kaina na shiryawa Big Bros abincin."

"Nima ai naso zuwa wallahi Sa.Jid ne ya hanani wai saura kwana nawa ne ma da duk zaku dawo Gomben."

"Saboda ke gaki mai ƙafar yawo ko.?"

"Hmm! Kin cika ni da surutun ku na ƴan sanda baki barni na faɗi dalilin kiran nawa ba."

"Wato surutu ma na cika ki dashi ko.?"

"Baza dai ki barni na faɗi abinda zan faɗa ba kenan.?"

"Ohh sorry ina jinki."

"Akwai matsala fa"

"Wacce irin matsala kuma."

"Jiya naje gidan Momi take gayamin wai a ɗaya part ɗin nan zaki zauna kafin a ƙarasa muku gyaran gidan da zaku zauna."

"Yanzu ya za'ayi kenan."

"Baki zaki buɗe ki gayawa Daddy kin fiso a gyara muku gidan tukun, idan babu hali ma sai a ɗaga bikin tunda kinga abu ne mahimmaci zamuyi."

"Haka za'ayi zamuyi maganar."

"Toh shikenan sai anjima ki gaishemin dasu idan sun sauka."

"Ok bye."

Motar ta kunna bayan ta ajiye wayar sannan ta nufi gida kai tsaye, M.J kaɗai ta tarar a falon bayan shigarta ciki da sallama, bata kulashi ba ta nufi hanyar kitchen, juyuwa tayi tare da aika mishi wani sihirtaccen kallon jin abinda yake faɗa.
"Allah yasa dai kin wanke najasar tun a waje baki dawo dashi cikin tsarkakken gidan nan ba."
Shigewa tayi batare da tace komai ba, shikuwa tsaki ya furzar mai sauti tare da miƙewa ya bar cikin falon.

A zaune ta tadda Baaba a kitchen ɗin tana yankan ɗanyar kuɓewa, ledojin hannunta ta ajiye tare da faɗin
"Me zakiyi da kuɓewa kuma Baaba.?"

"Babanku ne yace yanaso a mishi shine nafara gyarawa kafin ki dawo, ina kikaje ne.?"

"Kasuwa naje na siyo sauran abubuwan da bamu dashi a kitchen ɗin."

"Gashi ki ƙarasa wannan bacci ne yaketa ƙoƙarin kamani tun ɗazu zanje na ɗan kwanta, saiki kira Raliya ta kama miki wasu aiyukan."

"Toh" tace tare da karɓar rubar da kuɓewar ke ciki, ita kuma Baaba ta fice a kitchen ɗin, saida ta gyara komai tare da fitar da duk wani abu da zata buƙata kafin itama ta wuce ɗakinta tayi wanka da sallah kafin ta fara aikin.

Tun ƙarfe biyu ta shiga kitchen ɗin tafara hada-hadar haɗa abincin tarbar baƙin nasu, ita kaɗai takeyin duk wasu aiyuka ba kamar yadda Baaba tace ta nemi taimakon Raliya ba, a dole ne kawai take haƙuri Raliy na kusantar inda take bawai dan tanaso ba, saboda tsanar da takeyiwa Alpha da duk wanda ya dangance shi.
Kasancewarta mai saurin aiki yasa kafin la'asar harta gama haɗa komai illa kawai masa ɗin da bata soya ba wanda shima rashin tashin da baiyi ba ne ya hanata soyawa. Baaba ce ta kuma shigowa kitchen ɗin da sallama tana faɗin.
"Yanzu Zara'u da nace ki kira Raliya ta kama miki wannan aikin shine kika ƙi koh.?"
Sai a lokacin Zarah ta lura da Raliya dake bayan Baaba, kau da kai tayi tare da faɗin.
"Naga aikin ba mai yawa bane shiyasa."

"Allah ya kyauta wannan halin naki, saka min tuwon nikam idan kin gama."

"Toh kije zan kawo miki."

"Ban yarda ba sakamin na tafi dashi ko kibawa Raliya ta kawomin."

Ba yadda ta iya haka ta saka mata malmalar tuwon guda biyu a plate sannan miya a ƙaramin glass bowl, a wani ƙaramin faranti ta jere mata tare da ɗora mata kwalbar soyayyen man shanu ta miƙawa Raliya farantin suka fice tare.
Saida ta wanke abubuwan da tayi amfani dasu kafin ta nufi ɗaki saboda kiran sallar la'asar da akeyi, cikin sauri ta watsa ruwa ta fito bayan shigarta banɗakin sannan ta shimfiɗa darduma tare da tayar da sallah.

Ko da ta idar gaban dressing mirro ta nufa domin shiryawa, saboda ƙarfe biyar jirginsu Daddyn zai sauka, simple makeup tayi wanda ya matuƙar yi mata kyau saboda yadda ta tsara shi, wardrobe ta kuma tare da zaro wasu rantsattsun riga da siket na wani dark blue ɗin less mai ratsin fari, cikin hanzari ta saka kayan ganin lokaci na ƙurewa, ba ƙaramin karɓar jikinta kayan sukayi ba musamman data yafa farin gyale mai duwatsu sanna ta saka farin takalmi, wayarta ta ɗauka ganin har ƙarfe 4:40pm yasa ta fita da sauri, bata tarar da Baaba a falo ba hakan yasa tabarwa Raliya dake ƙoƙarin shiga kitchen sallahun soya mata sinasir ɗin tare da faɗama Baaba cewar ta wuce airport.

A farfajiyar gidan ta gansu suna ƙoƙarin shiga mota wanda tana da tabbacin suma airport ɗin suka nufa, inda motarta take itama ta nufa batare da ta kuma kallon inda suke ba.

"Amaryarmu irin wannan kyau haka kamar wacce ke shirin zuwa gasar kyau na duniya gabaɗaya." cewar Abdallah daya leƙo da kanshi ta window yana magana.

"Banda zuga dai."

"Da gaske fa, kizo mu wuce tare mana ko ba airport ɗin kika nufa ba kema."

"A'a kuje kawai yanzu zan biyo bayanku."

"Sai tayi yawon dandin nata kafin nan, kaga bazata haɗa hanya damu mu hanata aikata kudurinta ba." cewar M.J yana taɓe baki kamar yaga wani abin kyama.

Hawaye taji......✍️


*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

...Hawaye taji masu zafi suna ƙoƙarin silalo mata, da sauri ta buɗe motar ta shige domin batason M.J ya gano lagonta.
Ta rigasu isa airport ɗin dan haka ta samu guri tayi parking sannan ta fito da jingina da motar ta yadda waɗanda take jira zasu iya hangenta, batayi minti goma da tsayuwa ba jirgin ya fara ƙoƙarin sauka ƙasa daidai lokacin kuma motarsu Abdallah ta iso gurin inda sukayi parking a kusa da tata motar.
Matafiya ne suka fara saukowa cikin takon isa na hamshaƙan da suka baro ƙasar turawa, ɗaya bayan ɗaya suka jero akan matattakalar da zata sauko dasu daga jirgin, ido ta baza sosai ta inda zata gano ɗan'uwan nata. Duk da yawan video call da sukeyi amma dakyar idanuwanta suka iya ganeshi saboda kyau daya ƙara, nufowa suke domin ƙarasowa inda suke tsaye ita da su Abdallah, saidai bazata iya jira su ƙaraso ba dan haka ne ta ruga a guje ta ƙarasa inda suke tare da rungume ɗan'uwan nata cikin tsantsar farin ciki, shima hannayensa biyu yasa ka ya maida mata rungumar tare da ɗan bubbuga bayanta jin tana shessheƙar kuka.
"Bakyason ganina ne na koma inda na fito ko.?" ya tambaya cikin son yaga ta daina hawayen.

Da sauri ta sakeshi tana saka bayan hannunta ta goge hawayen kana tace.
"A'a dear murnar ganinka ce kawai ta saka hakan, idan kace zaka koma to nima binka zanyi mu koma tare."

Daddy dake tsaye yana kallonsu ne yace.
"Wato ni ko sannu fa zuwar ma bazan samu ba duk da ni naje na taho dashi, ai babu damuwa nikam naga warayya ƙarara a fili."Cikin zolaya ya ƙarasa maganar.

Ɗan durƙusawa tayi da hanzari tana faɗin
"Sorry Daddyna ai nafi kowa murnar son ganinka, barka da dawowa ayimin afuwa."

"Babu komai daughter mu hanzarta mu wuce gida naga hadari ya haɗo."

Hannushi ta riƙe kamar wata yarinya suka ƙarasa wajen motocin, cikin fara'a suma sukayi musu barka da dawowa, nan aka ɗanyi raha irin wacce ke tsakanin uba da ƴaƴansa kana suka fara ƙoƙarin shigar da kayansu mota domin shigewa gida, Zarah kam hannun Sadiq taja zuwa motarta ta buɗe mishi gidan gaba ya zauna sannan ta dawo domin ɗaukar wasu kayan ta saka a tata motar, daidai lokacin daya sunkuya domin ɗaukar wata jaka itama lokacin da sunkuya zata ɗauka, a hankali yayi magana ta yadda ko Daddy dake tsaye agun bazaiji mai ya faɗa ba yace.
"Wato ke a ko ina saikin bayyana salon karuwancin naki ko, saboda asan kin shahara a bariki ne zaki rungume mutum a bainar nasi kuma ki ƙi sakinsa saboda ke ga ƴar bariki ko? Toh Allah yasa dai rungumar iya ta ƴan'uwan taka ta tsaya bata kauce hanya ba."

Da sauri ta ɗaga idonta da sukayi jazir saboda ɓacin rai ta kalleshi, wato cin mutuncin nasa har yakai matakin dazai iya zarginta akan ɗan'uwanta da suka fito ciki ɗaya, abubuwan da M.J yake mata idan ta mutu bata rama ba toh tabbas bata yafe mishi ba, batace komai ba ta ɗauki jakar ta nufi motarta.
Cikin ƙoƙarin danne ɓacin ran da take ciki ta buɗe mazaunin direba ta shiga motar tana faɗin
"Sorry dear na barka kana jira."

Kasa amsawa yayi illa idanunshi daya kafeta dasu yanason gano wani abu tattare da ita.
"Zarahty kina kallon kanki a madubi kuwa.?" ya tambaya da alamun mamaki a tattare dashi, leƙawa tayi kaɗan ta kalli madubi motar sannan ta ɗan juya ta kalleshi tana cewa.
"Nifa Yaya banga inda kwalliyar nan ta ɓaci ba, kawai ka saba da ganin fuskar turawa ne shiyasa komai kake kallonshi sabo."

Wanj murmushi yayi da iyaka fuska ya tsaya yace.
"Ba batun kwalliya nakeyi ba, ke baki taɓa tsayuwa a gaban mirro kin fahimci how not ok are you ba, baki ga irin ramar da kikayi ba kamar wacce ta fito a prison, wai meke damunki ne haka little."

"Ka dawo kenan ai Yaya, toh nidai aikine sukemin yawa bana samun lokacin hutu shiyasa kaga ina ramewa, ni banga ramar danayi ba ma fa."

"Ke kam ai bazaki gani ba, amma nasan tabbas bayan aiki akwai wani abu daban a cikin ranki."

"Uhmm nidai babu komai fa"

"Shikenan I'll figure out myself tunda nadawo ƙasar, ja mota mu tafi gida gashi harsu Daddy sun wuce sun barmu."

"Toh" ta faɗa sannan ta tayar da motar suka bar farfajiyar wajen, suna tafe suna hira tamkar wasu sa'anni ko kuma abokai saboda yanayin yadda suke hirar cikin raha da tsokanar juna, wannan na ɗaya daga cikin tarbiyar da iyayansu suka basu a zamanin da suke raye, son juna da kulawa ba tare da la'akarin babba ko yaro ba.
Cikin Mintuna ƙalilan suka iso gidan horn tayi aka buɗe ƙofar sannan ta nausa kan motar zuwa ciki, a farfajiyar gidan suka tarar da Baaba tsaye tana jiran ƙarasowarsu.
"Sannu da zuwa angona na kaina." tace lokacin data ƙaraso jikin motar, Sadiq ne ya fara buɗewa ya fita ta gefen da take tsayen, baki ta riƙe tare da zaro ido kamar tsohuwar da ta kama kwarto a ɗakin suruka, saboda mamakin yadda jikan nata ya sauya gabaɗaya duk kuwa da yawan ganinshibda takeyi idan suna video call, dariya yayi mai sauti ganin yanayin Baaban da kuma irin tsayuwar da tayi yace.
"Haba amaryata irin wannan kallon haka, ko kina tsoron ayi saurin kwace miki ni ne.?"

"Kwacewa ta nawa kuma Habu, ai yadda ka rikiɗe ka kuma bature nasan baza'a rasa wata baturiyar data kwace ka ba."

"Toh ki kwantar da hankalinki ni ɗin naki ne ke kaɗai kinji my one and only kakaty."

"Nifa banason wannan salon iskanci, daga dawowa zaka fara zagina tun daga kan iyaye da kakannina da wannan ɗan iskan yaren."
Dariya yayi sosai kafin ya dakata yace
"Toh yi haƙuri rabin raina, mu ƙarasa ciki sai muyi magana."
Juyawa yayi yana waige-waige yace
"Little ta shige ta barmu a tsaye ashe."

"Wannan mai baƙin miskilancin ai ba tsayawa zatayi ba."

"Ohh tana nan da halin ashe."

"Sai abinda ya ƙaru."

"Little ba dama Allah ya yaye mata."

"Amin idan mai barin ta ne."

Nan suka shige falon suka samesu idan Zarah ke zaune a ƙasan kujerar da Daddy yake kai ta ɗaura kanta akan cinyarshi, Abdallah da M.J kuwa suna zaune ne a kujera two seater. Zama sukayi aka shiga gaisuwar yaushe gamo da kuma ƙarin ta'aziyar da aka yiwa juna, sun jima suna hirar kafin Baaba ta umarci duk su miƙe domin zuwa dinning, Zarah ce tayi serving kuwa da abinda yakeso sannan suka fara cin abincin cikin nutsuwa da yadda addini ya koyar.
Ko da suka gama ita ta tattare gurin ta kimtsa shi yabkoma kamar ba'aci abinci a gurin ba, falon ta kuma inda ta samu Daddy ya wuce sashin baƙi domin hutawa, zama tayi a gefen Baaba akan doguwar kujera tace.
"Dear ba zakaje kayi wanka ka huta ba kaima."

"Ke Zara'u kowa saikin ɓata mishi suna ne, mene ne kuma giya ɗin da kike kiranshi dashi."
Dariya sukayi gabaɗayan su har M.J da hankalinshi yake akan wayarsa saida ya ɗan murmusa, tsagaitawa Sadiq yayi yace
"Gaskiya ba ƙaramin wauta nayi ba na barin Nigeria ko wannan comedy ɗin da kike cirewa ai ya ishi mutum farin ciki na sati guda, Little jeki haɗamin ruwan wanka ganinan zuwa."
Miƙewa Zarah tayi cikin dariya tabar falon.

"Turanci bai yi muku rana ba tunda kun zubar da al'adun ku."

"Kakaty kenan, bari naje nayi wanka na huta sai na dawo mu cigaba."
Shima miƙewa yayi tare da bawa Abdallah hannu sukayi musabaha, hannu kawai M.J ya ɗaga mishi lokacin daya miƙa mishi hannu da nufin yin musabahar, baiyi mamaki ba domin tun zuwanshi ya fahimci ɗabi'un M.J ɗin musamman a gareshi da yake ganin tamkar baiyi farin ciki da dawowar tasa bane, kaɗa kai kawai yayi sannan ya nufi hanyar side ɗinshi.
A tsaye ya tadda ta tana ƙara kimtsa mishi ɗakin, murmushi yayi mai sauti yace.
"Ke dai bakya iya zama bakiyi aikin komai ba."

"Tab! Ina hutawa mana, kawai naga baka da wanda zai maka ne shiyasa nakeyi."

"Ai kuwa nagode na kusa kawo miki Anty ki huta."

"Da gaske Yaya." ta faɗa da ɗoki

"A'a bance ba karki kaini gaba." dariya sukayi duka sannan ya shige banɗakin yana faɗin.
"Idan kin gama ki ɗaukomin fresh milk."

"Toh"
Sai da ta kimtsa ɗakin sosai duk da jiya ta shigo ta gyara amma tana ganin abubuwan da yakamata ta gyara musu waje, fita tayi domin zuwa ɗauko fresh milk ɗin.
Baaba kaɗai ta tarar a zaune tana kallo sai Raliya dake ƴan goge-goge a gefe.
"Yauwa Zara'u yanzu nake shirin aika Raliya ta kiramin ke."

"Me zanyi miki kuma."

"Bani ke nemanki ba, Abdullahi ke nemanki zakuyi sallama domin daga masallaci zasu wuce."

"Ayya bari na haɗo saƙon Momi naje muyi sallama, suna ina ne."

"Suna can falon baƙi."

"Ina zuwa."

Ta faɗa tana haurawa sama da gudu, ɗakinta ta shiga tare da nufar inda ta ajiye jakar tsaraba data tanadar musu da wacce takeso a kaiwa Momi, rufuwar jakunkunan ta gyara sannan ta ɗaukosu ta fito falon, kallon Baaba tayi tace.
"Dan Allah Baaba Raliya ta kaiwa Yayana fresh milk karya fito yaga ban kai mishi ba."

"Ɗaukomin ni na kai mishi."

"Yauwa" ajiye kayan tayi akan kujera sannan ta nufi kitchen ta ɗauko fresh milk ɗin da cup ta miƙa mata, kayan ta ɗauka ta nufi falon baƙin ita kuma Baaba ta miƙe ta nufi ɗakin Sadiq ɗin.

"Ahh Baaba da kanki kuma, ita little ɗin me takeyi da bazata iya kawomin ta koma ba.?" cewar Sadiq dake ƙoƙarin fitowa daga bedroom sanye da farar jallabiya.

"Bakaji daɗi bane da ni na kawo."

"A'a kawai naga kamar ba aikinki bane."

"Sai kuma kayi idan bazaka sha bane na maida, ita wacce kake magana tana gurin mijin da zata aura zasuyi sallama domin zai koma inda ya fito."

"Yi haƙuri Baaba, dama Bro ɗin yau zasu wuce shine basu faɗan ba."

"Gashi ni na faɗa maka ai."

"Ehh to nima inaga yakamata naje muyi sallama ko."

"Yakamata gaskiya."

"Bari naje na dawo sai muyi hirar soyayya."
Dariya tayi kawai shi kuma ya fice a ɗakin.

Ƙoƙarin riƙe handle ɗin yake domin shiga falon saidai maganganun dake tasowa yasa ya jinkirta domin jin cigaban zancen, muryar M.J ya kuma ji yana faɗin.
"Idan kinsan da kuɗin karuwanci kika siyama uwata waɗannan tarkacen ki tattara kayanki ki koma dasu domin rashin arzikina bai kai matakin da zan iya barin uwata tayi amfani da abin haram ba."

"M.J wai meke damunka ne akan yarinyar nan, wai ko mantawa kake itace wacce ake ƙoƙarin ɗaura muku aure nan da satikai uku masu zuwa.?"cewar Abdallah.

"Abdallah kenan ina sane da duk abinda nakeyi, wannan da kake magana akanta bana mata wanj kallo da ya zarce na mazinaciya, karuwa, sannan kuma fasiƙa mai aikata abinda Allah ya haramtashi, bana mata kallon matar da nake shirin aura domin bata cancanci a alaƙanta ta dani ba bare kuma aje batun aure, ina mata kallo ne na wacce ake ƙoƙarin kawomin domin na horata akan abinda da ta daɗe tana aikatawa." sannan ke kuma, ya waiwaya ga Zarah dake zaune zuciyarta na barazanar faso ƙirjinta ta fito saboda baƙin cikin daya turnuƙeta
"Ina ƙara jan kunnenki tare da baki shawara da ki zubar da duk wasu mugun nufinki nason cigaba da bin maza a gidana domin bazan lamunci hakan ba, a cikin gidana dana gina da tsarkakkun kuɗi bana haram ba a dinga aikata saɓon Allah a ciki, mazinaciyar banza mazinaciyar wofi, wa ya sani ma ko a gada kikayi kika tsotso a no..."

Tasss!!! Ta katseshi ta hanyar baiwa fuskarshi wadataccen mari zazzafa domin zuwa yanzu bazata iya jure cin mutuncin nasa daya bar kanta ya koma kan iyayanta da basa duniyar ba ma.
Baki buɗe suke kallonta, a ɓangaren Abdallah tsantsar farin ciki da mamakin abinda Zarah tayi ne ya hanashi magana, shikuwa M.J baƙin ciki da mamakine suka turnuƙeshi lokaci guda.
"Ni kika ɗaga hannu kika mara.?" Ya faɗa yana huci.

"Na mare ka kuma in gab da yi maka abinda yafi mari zafi matuƙar zaka taɓa mutuncin iyayena, banza kaw..."
Bata ƙarasa ba itama ya wanke mata fuskarta da mari kafin ta kuma ankara ya ƙara wanke mata ɗaya ɓarin da mari mai zafi, saidai ko kaɗan Zarah bataji zafin shi a fuska ba saboda zafin zagin iyayenta da yayi yafi komai ƙuna a gareta.

"Kina karuwa har kin isa ki ɗaga wannan hannun naki mai cike da ƙazantar zina ki mare ni, wallahi baki isa ba kuma ƙunci yanzu kika fara shiga cikinsa nonsense."

A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shigo duk da halin da yake cike bai hanashi yin sallama ba, kai tsaye inda take a durƙushe ya nufa batare da yayi magana ba, hannu biyu yasa ya miƙar ta ita tsaye tare da riƙe hannuwanta suka nufi ƙofar fita daga falon, ɗan tsayawa yayi sannan yace
"Dama sallama nazo yi muku, idan kun tafi Allah ya kiyaye hanya."
Yana gama faɗin haka ya ja hannunta suka fice a falon, daga Abdallah har M.J babu wanda ya tanka, shikam Abdallah baƙin ciki yakeji na abinda abokin nasa ya aikata tare da dana sanin wannan rakiya da yayi, a ɓangaren M.J kuwa babu wani abu da yakeji a ranshi face ɓacin ran da Zarah ta sakamai ta hanyar marinshi.
Miƙewa Abdallah yayi tare da ɗaukar kayan da Zarah ta ajiye mai ya fita batare daya kula M.J ɗin ba, bayanshi ya bi ganin bai kulashi ba suka fita tare, sun rigada sun sanar da direban dazai kaisu airport ya shirya dan haka bayan motar suka shiga yajasu zuwa airport ɗin.
Ko da suka isa basu yima juna magana ba har zuwa lokacin da suka shiga jirgi ya keta hazo dasu.
Kuka take me matuƙar ban tausayi da sosa ran duk wani mai sauraro har suka isa ɗakinta, kan gadon ɗakin ta faɗa tana cigaba dayin kukan, shikuwa Sadiq nufar inda hoton mahaifansu dake gefe yayi ya ɗauka tare da rungume hoton a ƙirjinshi, sai a lokacin kukan daya danne ya hanashi fitowa yayi nasarar bayyana kanshi batare dayayi ƙoƙarin dakatarwa ba shima ya fara kukan yana faɗin

"Meyasa zai rabamu daku, me muka mishi zai rabamu daku ya barmu cikin gararin rayuwa da rashin gata, Abba! Mami kuna ganin yadda rayuwarmu ta tagayyara da bakwa tare damu, Abba meyasa bakace mutuwar ta ɗaukeni ba ta barka ka kula da ƙannena, Abba inajin kamar na gaza riƙe amanar ƴan'uwana da kullum kake daɗa jaddadamin, Mami kina gani koh? Ki tayani roƙon Allah yayi gaggawar ɗaukan raina bazan iya jure ganin ƴan'uwa cikin halin baƙin ciki da ƙunci ba alhalin ina raye. Kaicona dana kasa riƙe amanarka Abbana yau ga ƴar'uwata tana zubda hawayen baƙin ciki dana maraici sannan ina kusa na kasa aikata komai, Ya Allah kayi gaggawar ɗaukan ra...."
Hannu aka saka tare da rufe mishi bakinshi, bashi da ƙarfin dazai iya hana hakan shiyasa ya cigaba da rera kukan shima mai ban tausayi.
Zama Baaba tayi a gefen gadon ta ɗora hannun hagunta a bayan Zarah tana bubbugawa alamun rarrashi hannunta na dama kuma na kan Sadiq tana shafawa a hankali.
Sun ɗauki tsawon mintuna a haka batare da sun daina kukan ba, ganin haka yasa Baaba tace.
"Idan rai ya ɓaci ambaton Allah akeyi ba kuka ba."

"Baaba na gaji bazan iya jure wannan baƙin cikin ba, na gaji ta dalilinsu fa muka shiga wannan halin amma abinda zasu saka mana dashi kenan, bazan iya jure wannan cin mutuncin da akeyiwa iyayena ba zan maida musu da Diamonds ɗinsu ko zamu huta da wannan takaicin." Zarah ta faɗa cikin fitar hayyaci, da sauri ta miƙe ta nufi gaban dressing mirro ɗinta tana watsi da duk wasu abubuwa dake kai batare da ta kula da irin ɓarnar da takeyi ba. Sai da zuba komai na kan wajan a ƙasa kafin da fara ƙoƙari tura dressing mirro ɗin gefe.

"Me kike ƙoƙarin aikata ne haka Fatimah?" Baaba ta faɗa a fusace.

"Bazan iya ba Baaba zan basu Diamonds ɗinsu kawai na huta." ta ƙarasa fada lokacin da tayi nasarar tura dressing mirror ɗin gefe, tsugunnawa tayi a gaban wani tiles a wajen, hannu takai da nufin taɓawa sai dai kamar a danna mata remote ta dakata saboda jin kamar anayi mata raɗa a kunne.
"Raliya!!! Batula Raliya na waje." haka taji a kunnenta tamkar wani ke magana, da hanzari da nufi ƙofar fita bata ko ganin gabanta saboda tsananin tashin hankali, da mugun ƙarfi ta buɗe ƙofar.

Rasss! Rasss!! Rassss!!! Haka ƙirjin Raliya ya bada sauti wacce ke tsaye a jikin ƙofar riƙe da sound recorder da kuma ƙaramar camera tana ɗauka duk wani abu dake faruwa ta ɗan ramin ƙofar data buɗe kaɗan ganin mutanen ɗakin basa cikin hayyacinsu bare su lura da ita, tsananin tashin hankali da firgici ne ya ziyarceta lokaci guda ta fara ɗika saboda zufar da tayiwa jikinta ƙawanya lokaci ƙanƙani..

Wata irin shaƙa Zarah takai mata........✍️

😱😱😱😱😱😱😱
*YANZU NE FA ZA'A FARA ASALIN LABARIN _ASP ZARAH_👩‍✈️ MATAR MUHAMMAD JAWWAD KAWAR JIDDAH MATAR SALEEM. LOKACIN DA ZAMUGA ƁOYAYYEN SIRRIN DAKE TATTARE DA JIDDAH YAYI FA🤔*

*SHIN ZARAH ZATA MAIDAWA DADDY DIAMONDS ƊINSA KO KUWA ZATA BARSHI A WAJENTA HAR SAI ZUWA LOKACIN DA ZATA KAUDA ALPHA.???*

*ME ZAI FARU TSAKANIN ZARAH DA RALIYA NE A WANNAN FITO NA FITO DA SUKAYI.???*

*WANI MATAKI DADDY ZAIYI NE IDAN YAJI LABARIN ABINDA ƊANSHI YAKE AIKATAWA GA YARINYAR DATA SADAUKAR DA KOMAI NATA DOMIN KARE DUKIYARSA WACCE TA DALILIN HAKANE TA RASA IYAYANTA SANNAN ƳAR'UWARTA TA FICE A HAYYACINTA.???*

*AURAN MUHAMMAD JAWWAD DA FATIMAH ZARAH

1 Comments On ASP ZARAH
avatar
zainab-3-7-9

1 year ago

Reply

I need complete Asp zarah

Please Login or Register in order to submit comment