Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun yana ɗan shekara 14.

Jirgin ƙarfe tara Zarah zatabi zuwa garin Abuja yayinda jirginsu Muhammad Jawwad zai sauka ƙarfe takwas da rabi.

"Daddy ina jin ku wuce kawai zanbj ta ofishin kwamishina kafin mu wuce." Zarah kenan ke faɗi bayan ta gama amsa wayar da Sergent Bala ya bugo mata.

"Babu rabon zaku haɗu da ɗan'uwan naki kenan saboda shima kwanaki biyar zaiyi ya koma saboda inaso ya dawo ƙasarshi ya cigaba da aiki." cewar Daddy

"Banji daɗin haka ba gaskiya amma tunda zai dawo ƙasar gabaɗaya zamu ga juna."

"Shikenan Allah ya kiyaye hanya."

"Ameen Daddy."

Sauran iyayenata ma addu'ar sauka lafiya suka mata kafin ta shige motarta ta fice a gidan.

Daddy, Momi da Ammi sune sukaje airport tarbar ɗan nasu domin Baaba batada damar fita saboda halin takaba da take ciki.

Basu jima da isa ba jirgin ya sauka, dubawa suke domin ganin ta inda zai ɓullo amma basu ganshi ba.
Wani kyakkyawan bature ne suka ga ya nufo inda suke tsaye, basu ankara ba suga ya rungume Daddy tare da faɗin" Nayi kewarka Daddyna."

Salati Ammi ta shiga rafkawa tana faɗin.

"Jawwad kaine haka.? Shikenan masu jajayen kunnuwa sun canja ka, ka koma jinsinsu."

Dariya sukayi gabaɗaya sannan suka nufi gurin da motarsu take, ita kuwa Momi kunyar fulani da kawaicin ɗan fari ne ya hanata magana.
Mota suka shiga tare da nufar gida.



A ɓangaren Zarah kuwa koda kwamishina ya gama zayyana mata tsarin yadda taron zai kasance saita miƙe domin tafiya, har ta kama hannun ƙofar da nufin buɗewa ta fasa tare da waiwayowa ta kalli kwamishinan da hankalin shi ya koma kan takardun dake saman teburinsa tace.

"Yallaɓai nace ba."

Kallonta yayi batare da yace komai ba.

Murmushi tayi mai cike da ma'anoni kafin tace.

"Yallaɓai idan ba damuwa ka faɗawa wanda ya baka umarnin wakiltani a matsayin wacce zata halarci wannan taron cewa _Babu ma'ajiyar CCTV a ofishin ASP Zarah sannan baya buƙatar na'ura mai ɗaukan sauti domin sanin abubuwan da nake gudanarwa a cikin ofishina._

Bata jira mai zaice ba ta buɗe ƙofar tare da ficewa a ofishin........ ✍🏼

*Jasmine*🌸🌸


*TALLA*! *TALLA*!! *TALLA*

*Uwargida!!! Shin ko kinsan zaki iya magance matsalolin da suka daɗe suna ci miki tuwo a kwarya cikin gidan aurenki.???*
*Uhmm riƙe sirri sai mai sirri, shin kinada labarin shahararriyar matar nan wacce ta shahara wajen ganin cewa mata basu wulaƙanta a gidan mazajensu ba.!? Wacce ta kware wajen gyara amarya har ma da uwargida.? Ita ɗin dai dake siyar da kayan gyara na musamman masu sauƙin kuɗi amma akwai aiki, mai kawo muku sirrika da dabarun gamsar da miji ta kowani fanni.*😍

*Kardai na cika uwar gida da surutu, nice dai HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA. A wannan karon nazo ne da zafafan darussa da zan gabatarwa mata tare da kayan gyara na musamman. Bari dai na lasa muku zuma a baki, kaɗan daga cikin darussan da zan gabatar a wannan karon:*

*Sirrin TomTom*
_Shidai tom tom da kika sani uwargida, matsalar ki ta wajen kasa gamsar da mai gida ta ƙarw idan kika riƙe wannan sirri._

*Zuba ki lashe*

_Bazance komai ba a wannan fannin idan kinason sani to ki kasance tareda ni a cikin sati ukun dazan gabatar da darussa_.

*Kayan gyara na musamman zai iso ki har garin da kike idan kinyi odarsu, domin sanin kalar su da amfaninsu to ki kasance dani cikin zazzafan darussa na sati uku da zan gabatar a Special Group na ASP ZARAH FANS.*

*Kada ki bari ƙaramin kuɗi ya saki zama mara gata gidan mijinki.*

*Ki tuntuɓi wannan number 07048961623 domin samun damar shiga ASP ZARAH SPECIAL FANS GROUP, Inda ni HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA zan kasance daku.*
*Kada ki bari ƴar uwarki ta baki labari*.
*SAI KUNZO*

Ya kasa koda motsa yatsa ne saboda kaɗuwa da yayi da zancenta, yanzu kam ya fara zargin ko Zarah tana da aljanu masu faɗa matan idan anyi maganarta.
Kiran wayar sirri sukayi da Alpha lokacin da yake shaida mishi ya tura Zarah garin Abuja domin halarta taron ƙarin ilimi a fannin aiki, hatta da wayar da yayi amfani da ita tana killace a ɗakin barcinshi na gida.
Duk tunanin dayayi bai samar mishi da amsar inda Zarah taji labarin za'a sanya CCTV a ofishinta ba, yanke shawara yayi na kiran Alpha domin shaida mishi abinda ya faru.

Saida ya kira sau biyu kafin aka ɗaga kiran.

Cike da jimami kwamishina ya karanto mishi abinda ya faru a ofishin nashi kusan mintuna goma da suka wuce.

"Ya akayi tasan da batun CCTV.?" Alpha ya faɗa cike da masifa

"Kayi haƙuri Alpha nima bansan ina ta samu labarin ba." Ya faɗa kai a sunkuye tamkar yana gabanshi.


Shiru ya biyo baya na wani lokaci kafin Alpha yace.
"Ku bar batun saka camera ɗin tukunnan zanji da lamarinta a garin Abujan."

Ya kashe wayar batare da yayi magana ba.

Ƙayataccen ɗaki ne wanda yaji kayan alatu masu matuƙar kyau da tsada, tsaruwar ɗakin kaɗai zaisa mutum yayi tunanin na wani hamshaƙin shugaban ƙasa ne amma idan aka ƙurewa fitilun dake kawowa da ɗaukewa idon za'a gane mamallakin ɗakin sakamakon sunan Alpha da suke rubutawa a kowani kawowa da suke yi. A tsakiyar ɗakin wani haɗaɗɗen gilashi ɗauke da kyawawan kifaye a saman shi cikin ruwa suna ta shawagi yayinda ƙasan gilashin ke ɗauke da wasu kyawawan halittun ruwa da bazan iya tantance sunayensu ba.

Maganganun ke tashi a cikin falon saidai banga alamun ta inda nake jiyo maganar ba, muryar namiji ne ke maganar inda yake cewa.
"A matsayin marainiya mai neman aiki domin tallafawa mahaifiyarki zakije gidan, sannan ki tabbatar bata cikin gidan yayinda zakije neman aikin saboda kaucewa matsala."
Har zuwa wannan lokaci mai maganar bai bayyana ba illa wata matashiyar yarinya da tafito daga wata kusurwa a cikin falon, kyakkyawa ce daidai gwargwado sannan fatarta ta kasance kalar chocolate.
Kallo ɗaya mutum zaiyi mata ta gane tana cikin damuwa sosai sakamakon idanunta da sukayi jazir saboda kukan da tasha.

Ƙofar dazata sadata da farfajiyar gidan ta buɗe tare da fita a falon, babban fili ne sosai dake ɗauke da gine gine a wani gefe sannan shukoki kala daban daban da suka ƙawata wajen ciki harda manyan bishoyin kwakwa wanda su sukafi yawa a wajen. Sai ƙananun shukoki da aka tsarasu tamkar a ƙasar turai, a ƙasa kuwa wasu kyawawan duwatsu ne masu haske da sheƙi waɗanda ke ƙara bayyana kyawu da tsarin farfajiyar wannan gida da ya kasance tamkar na sarauta. Jefi-jefi mutane na shawagi a farfajiyar inda yawancinsu suka kasance mata sa'an masu ƙananun shekaru.

Tafiya tayi sosai kafin ta iso wani keɓaɓɓen guri da ruwa ke gudana tsakanin waɗansu matsakaitan duwatsu, wasu mata ne ke zaune su uku suna ɓare kwakwa. Ta farko keyin hanya a jikin kwakwar, ta biyu kuma ke ƙarasa barewa yayinda ta ukun cikinsu ke ɗauraye jikin kwakwar bayan a ɓare tare da jerasu cikin wani kyawawan kwando.

Zama matashiyar yarinyar tayi a gefe tare da jingina kanta a jikin wata ƙaramar bishiya.

Gabaɗaya suka maida hankalinsu kanta, kafin wacce ke wanke kwakwar tace.

"Meke faruwa ne Raliya, wani abinda ya miki ne.?"

Ɗago kanta tayi tare da maida kallonta garesu tace.

"Zanso ace wani abu ne ya shiga tsakanina dashi saidai babu abinda yamin illa aiki dazai turani a gidan da waƴannan lu'u lu'un suke."

"Raliya wani lokacin kina saka mana shakku akanki, dukkan mu anan fata muke mubar cikin wannan azzalumin gida ke a lokacin ne keki fatan kasancewa da mai gidan ki dinga aikata haramtaccen abu dashi." Fadin ɗaya daga cikinsu bayan ta maida hankali kan ɓarar kwakwar da takeyi bayan jin furucin Raliyan.

"A yanzu bana fatan barin wannan wajen saboda waƴanda nayi fatan ƙara kasance dasu basa duniyar zan fiso na cigaba da kasance anan saboda ko bana nan ɗin zaiyi wuya na tserewa *ALPHA* tunda na rigada nasan wasu sirrika nashi, bazai taɓa barina a raye ba tunani zaiyi asirin shi zan tona." Faɗin Raliya

Ɗayar da tun fara maganar bata tofa ba tace.

"Ki dinga yiwa kanki kyakkyawan fata Raliya idan ba haka ba zuciyarki zata iya rikeɗewa ta koma irin tasa na marasa imani."

"Hauwa kenan ai yanzu haka banajin akwai abinda zuciya da gangar jikina zasu kasayi indai umarnin Alpha ne. Ku da iyayenku kawai ya rabaku ya kawoku nan amma nifa? Da hannayena guda biyu yasa na kashe iyayena, zuciyata ta gama bushewa tun a waccan ranar. Zan iya raba kowaye da jindaɗin sa kamar yadda akasa na raba kaina da nawa jindaɗin." Ta faɗa tana mai maida kanta ga kishingiɗar da tayi a jikin bishiyar.

Babu wanda ya kuma tankawa a cikinsu domin dai sun saba da jin kwatankwacin wannan furuci a bakin Raliyan tin bayan da tasamu kusanci da Alpha lokacin da tayi nasarar ganin yatsun hannunshi, mutum ne shi mai matuƙar taka tsantsan kasancewar shi wanda jami'ai ke nema ido rufe shiyasa baya taɓa bada damar a ga wani sashi na jikinshi koda kuwa farce ne. Idan kuwa kayi nasarar ganin wani abu nashi to daga wannan lokaci zaka zama makusancin shi bayan an shiga dakai wani ɗaki mai taken _Kusanci da Alpha_, wata ɗaya cur ake kwashewa ga duk wanda ya samu nasarar shiga wannan ɗakin saidai mutum yakan fito ne a galabaice. Idan mai tsawon kwana ne zaiyi dogowar jinya, idan yazo da ƙarar kwana kuma saidai a wuce da mutum kabari. Babu wanda yasan abinda akeyiwa mutum a cikin wannan ɗakin domin hatta Raliya da aka shigar da ita tace bazata iya tuna komai da ya faru ba.
Ko bayan mutum ya samu kusanci dashi bazai ƙara samun damar ganin wani sashi na jikinshi ba saidai zai kasance yana kasa saɓa umarnin Alpha ɗin koda kuwa umartarka yayi da kashe kanka.

*Abuja*

Cikin kwanciyar hankali da tsari ake gudanar da taron na ƙarawa juna sani a harkar aiki inda Zarah tayi zarra kwarai wajen baiyana dabaru da koma salon aiki da kowani jami'i ya kamata yayi amfani dasu, a cikin kwana huɗun da tayi a gari Abuja an samo nasarar zaƙolo manyan masu laifi da aka daɗe ana nema, hakan yasa aka shirya karramata a ranar ƙarshe da za'a kammala taron a matsayinta na jajirtacciyar ƴar Sanda da hukuma ke son irinta.

Kasancewarta mace kuma kyakkyawa yasa manyan masu muƙami a rundunar Ƴan Sanda ke ƙoƙarin janta a jiki amma taƙi bada damar hakan, domin hatta ɗakin da aka kama mata a hotel ɗin da aka sauki baƙi irinta wanda sukazo daga wani gari taƙi karɓa. Gidan wata abokiyar karatunta na sakandire dake zaune da mijinta a cikin garin Abujan nan ta sauka.


*Bauchi*

A yau ne akayi addu'ar kwana bakwai na rayukan da aka rasa a farfajiyar gidan marigayi Alhaji Abdul_Jalal, inda akayi saukar alqur'ani mai girma tare da yiwa mamatan addu'o'i.

Ƙarfe biyu jirginsu Ammi ya ɗaga zuwa Cairo ita da maigidanta da kuma Rahma da suka wuce da ita domin cigaba da duba lafiyar saboda har zuwa wannan lokacin bata magana tun bayan farfaɗowarta.

Daddy da Momi ma bayan sallar la'asar suka ɗauki hanyar tafiya Bauchi. Sai gidan ya ragw daga Baaba sai Muhammad Jawwad da wata tsohuwa da Daddy ya samu domin tayasu zama sannan jami'an tsaron da Mustapha ys ɗauki nauyin ajiye musu guda biyar.

Shima Muhammad Jawwad a washegarin ranar zai wuce Abuja ya ziyarci wani abokinshi dake aiki acan, sa'an nan daga can ya wuce ƙasar England domin haɗo takardunshi tare da takardar shaidar aiki da yakeyi acan saboda samun sauƙin cigaba da aikinshi a Nigeria.

Washegarin kuwa shima ya wuce garin Abuja, kasancewar su Daddy basuyi mishi batun Zarah ba shiyasa baisan tana garin ba.
Ƙarfe 12:30nr ya isa garin Abujan inda abokin nashi yazo ta taryeshi a airport ɗin, daga nan kai tsaye gidanshi suka nufa.
Bayan yaci abinci ya huta ne ya buƙaci su fita domin zaga gari.


Ta fito da nufin tafiya gurin da suke ƙaddamar da taron kiran wata abokiyar aikinta Toyin wacce suka haɗu wajen taron ya shigo wayarta inda ta buƙaci ta biyo ta hotel ɗin da take domin su wuce tare.
Agogon hannunta ta kalla taga akwai sauran mintuna 45 kafin a fara taron hakan yasa ta yanke shawarar tsayawa a wani resturant da tagani domin siyan burger da ta tashi da marmarin ci a yau.

Suna ƙoƙarin fitowa daga *Koise Delicies* ita kuma tana ƙoƙarin shiga waya kare a kunnenta, karo sukayi da Abdallah wanda ke gaba yayinda Muhammad Jawwad ke bayan shi.

"Sannu dan Allah." shine abinda ta furta sannan ta cigaba da tafiya tana mai magana a waya inda takw cewa.

"Jirani a reception na hotel ɗin bansan ɗakin ba."

Dogon tsaki Muhammad Jawwad ya saki bayan sun shiga mota kafin yace.

"Suna fakewa da aikin ƴan sanda suna abinda suka ga dama, yanzu menene abin burgewa ga mace a aikin ƴan sanda kuma musulma.?"

Dariya Abdallah yayi sannan yace.

"Nikam naga abin burgewa sosai, ka dubi yadda tayi shiga cikin kamala ba kamar wasu matan dake irin aikinta ba, sannan maganar hotel da kaji tanayi ƙila wani aikim zai kaita can kasan su aikinsu babu inda bayakai mutum."

Baki kawai ya taɓe batare da ya kuma magana ba....






*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸

*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.*
*Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*

*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.

*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩‍✈️
👩‍


Free Page

Alhamdulillahi taro yayi kyau an watse lafiya bayan kyaututtuka da aka rarrabawa jami'ai tare da karrama wasu daga ciki inda Zarah ta kasance cikin waɗanda aka karrama.

Saida ta ƙara kwana biyu cikin garin Abuja sakamakon jirginsu Jiddah dazai sauka ta garin bayan ya taso daga ƙasar Malasia.

*_Jiddah ƙawace ga Zarah tun zamanin ƙuruciya, tare sukayi makarantar firamari da sakandire inda bayan sun kammala Jidda ta wuce jami'a yayinda itakuma Zarah ta wuce makarantar bada horo na ƴan sanda. Duk wasu sirrika na Zarah Jidda tasansu kamar yadda yake a ɓangaren Zarah itama._
_A shekarar data gabata ne Jiddah tayi aure inda mijin data aura ya kasance Barrister wanda yake aiki a ƙasar Malasia wato Bar. Saleem, dakyar aka rarrashi Jiddah tabi Saleem ƙasar a waccan lokacin bayan tayi iƙirarin ita bazata iya tafiya wata ƙasa batare da Zarah ba, shima dai Saleem ɗin bawai yana ƙaunar aiki a wata ƙasa bane illa dai kawai yanason ƙarasa yarjejeniyar aiki da sukayi da ƙasar. Tun bayan tafiyarsu kuma basuzo gida ba sai wannan karon da suka tattaro gabaɗaya suka dawo ƙasarsu ta gado._"

Sallama tayi da ƙawarta ta tare da yimata godiya sannan ta wuce filin jirgi inda tanan zasubi wani jirgin zuwa Bauchi.

Tana tsaye jirgin ya sauko daga sararin samaniya, bayan wadu mintuna kuma matafiya suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya, sam bata kula ba sai ji tayi an rungumeta gam tamkar za'a tsaga ta.

"Nayi kewarki sosai sahibaty.''
Jiddah wacce ita ke da alhakin rungumar ta faɗa cike da farin ciki, kana ta saketa tare da ƙamewa ta sara mata kana tace.

"Na gaida ASP da kanta."

Murmushi kawai tayi tare da maida hankalinta ga Saleem dake cewa.

"Zan shigar dake ƙara fa Zarah, ganinki kawai yasa ta mance dani ma gabaɗaya."

Dariya sukayi duka sannan suka nufi gurin da aka tana da domin zaman ma tafiya.
Mintuna kaɗan jirgin dazai sadasu da garin Bauchi ya keta hazo.

*England*

Tsaki yaja a karo na ba adadi cike da takaici, tashinsa kenan daga bacci sannan kamar koda yaushe yau ma mafarkinta ya ƙarayi wanda ya haddasa wajabcin wanka ya hau kanshi. Ya rasa dalilin dayasa tun ranar daya ganta kullum dare sai yayi mafarkin yana wani abu da ita wanda hakan ke silar dole idan ya tashi sai yayi wankan tsarki.
Wannan shine dalilin dayasa yake jin wata muguwar tsanarta a cikin ranshi.

Miƙewa yayi tare da shiga banɗaki, bai jima sosai ba ya fito cikin shirinsa na farar riga da baƙin wando.
Wayoyinshi ya ɗauka da niyar ficewa a ɗakin, saidai missed calls din Ammi daya gani a cikin wayar ne yasa shi dakatawa tare da zama a gefen gadonshi yana ƙoƙarin kiranta.

Bugu biyu ta ɗauka tana mai sallama, amsawa yayi tare da gaisheta.

"Har yanzu banga wani alert ba fa Jawwad." Ammi ta faɗa.

Cikin son gane mai take nufi yace.

"Ammi wani irin alert kuma na mene ne."

"Zan saɓa maka fa, ka maidani sa'ar wasan kace. Ko ba dakai mukayi magana zaka turo kuɗi a fara haɗa lefen ba.?" Ta ƙarasa magana cikin hassala.

Dafe kai yayi saboda tunawa da abinda take nufi, gaba ɗaya ya manta da batun aurenshi da Daddy yace zai haɗa da ƴar marigayi wacce bai ma santa a fuska. Shi a tunanin shi girman kai ne ya hanata zuwa ta gaidashi ko tabari su haɗu lokacin da yaje Nigeria, shiyasa yaji baya ƙaunar yin auren duk da matsalar da yake fama da ita na ƙarfin sha'awa.

"Ayi haƙuri Ammi zan turo insha Allah." Ya faɗa cike da biyayya.

"Toh ina jira kada ka sake na ƙara kiranka akan wannan batun idan ba haka ba kuma ranka ɓaci zaiyi." Ta faɗa gami da kashe wayar.

Dafe kai yayi cikin damuwa, shifa yana da ra'ayin irin matar da yakeson aura, amma gashi yanzu Daddy ya ruguza mai duk wasu tsarin shi.

Miƙewa yayi jiki babu laka ya fita domin yana a farkon sabuwar wata da za'a yakeson komawa gida gaba ɗaya, shi da ƙasar turawa kuma sai ziyara ko hutu ko kuma wani abu mai mahimmanci.


.......................

A bakin gate su Zarah suka tarar da wasu mutane biyu da alama dai miji da mata ne sannan marasa ƙarfi.
Ganin motar ne yasa su miƙewa daga durƙusun da suke a gefen gidan.

Tsayar da motar Saleem yayi kamar yadda Zarah ta buƙata, buɗe ƙofar baya ta fito ta nufi inda suke tsaye.

Da sassafar matar ta ƙaraso tare da durƙusawa akan gwiwoyinta tace.

"Ranki ya daɗe ki taimake mu, kwana uku kenan muna zuwa gidan nan amma anƙi bamu damar shiga. Hatta ofishinku ma an hanamu ganinki dan Allah ranki ya daɗe ki sauraremu."

Ɗagota Zarah tayi kana tace.

"Kada ki bani kunya ta hanyar durƙusawa a gabana domin neman wata alfarma, hakan zai sa nayi tunanin ko baki ɗaukeni a matsayin ƴa ba. Ku tashi mu shiga daga ciki muyi magana a nutse."

Ta ƙaramar ƙofa suka shige bayan su Saleem sun shige da motar tuni.

Falon saukar baƙi ta kaisu kana taje kicin da kanta ta kawo musu ruwa da lemo.

"Bismillah ga ruwa ku sha sai muyi maganar abinda ke tafe daku."
Fadin Zarah bayan ta aje tiren dake dauke da gorar ruwa da lemu a kan ƙaramin teburin dake tsakiyar falon.

"Ranki ya daɗe ba zamu iya shan komai ba ahalin da muke ciki." Faɗin mijin

"Meke faruwa ne.?" Zarah ta faɗa tana mai zama a kujerar dake fuskantarsu.

"Ranki ya daɗe ƴar mu akayi wa fyaɗe, sannan mun tabbatar da wanda ya aikata laifin. Yaron wani ɗan majalisa ne dake maƙobtaka damu amma bayan mun sami mahaifin yaron da batun ya ƙaryata lamarin tare da faɗin zaiyi shari'a damu duk sanda muka nemi ɓata masa suna ko ɗan shi. Yanzu haka yarinyar na gadon asibiti ana neman kuɗin aiki sannan bamu da halin biya." Ya faɗa yana mai fashewa da kuka inda matar ke taya shi.

Sosai zuciyarta ta tsinke da lamarin musamman da taga manyan mutanen da suka haifeta a shekaru suna zubar da hawaye.

"Amma meyasa baku kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa ba.?" Zarah ta tambaya a raunane.

"Tun faruwa lamarin muka kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa damu, saidai bayan sun gana da mahaifin yaron suka fatattake mu tare da faɗin sharri mukeson ƙullawa ɗan sa. Wannan dalilin yasa muka garzaya ofishinki bayan wani maƙocin ya bamu shawarar yin hakan, tun kwanaki uku da suka wuce muke zirya a ofishin an hana mu shiga shine mai gadin wajen ya bamu adireshin ki." Matar ke wannan bayanin.

Kai kawai ta jinjina tare faɗin.

"Ina zuwa." kana ta miƙe ta fita.


Bata daɗe ba ta shigo tare da Saleem da Jidda, zama sukayi tare da gaisa.

"Wannan shine Bar. Saleem tare da matarsa Dr. Jidda, za muje asibitin tare domin ganin halin da yarinyar take ciki kafin shigar da ƙara a kotu." faɗin Zarah bayan tayi nuni da kujerar da Saleem ke zaune shida Jidda.

Godiya su kayi sosai kana suka miƙe gaba ɗaya suka nufi waje.

Motar Zarah suka shiga duka inda Saleem ke tuƙin.

Mintuna kaɗan suka iso asibitin, kasancewar Zarah ƴar sanda shiyasa basu wani sha wuya ba wajen isa ɗakin da yarinyar take.

Ita kaɗai ke kwance a gadon jikinta rufe da zani yayinda acan kusurwar dakin wata ke zaune kan dadduma da alama dai itace mai jinyar.

Bayan sun mata ya jiki ne suka zazzauna inda Saleem ya ciro ƙaramar sound recorder tare da jan kujera ya ƙarasa bakin gadon yace.

"Baiwar Allah da farko dai ina ƙara jajanta miki akan wannan lamari da ya afku dake sannan inason sanin ko ke wacece.?"

"Da farko dai ni suna na Fahima ina zaune ne tare da iyayena a anguwar bakin kura dake nan jihar Bauchi. Sannan mahaifina mai ƙaramin ƙarfi ne." magana take a hankali alamum dai tana jin jiki.

"Meya jawo afkuwar wannan lamarin a gareki."

"Ina aikine a gidan wani ɗn majalisa dake nan anguwar mu wato Alhaji Nura Mai Riga. Tun lokacin da nafara aiki a gidan ɗan sa Kabeer ke yawan shigemin tare da nuna alamun yanaso muyi sabo sosai saidai ban bada damar hakan ba. To a ranar larabar data gabata ne bayan na kai masa abincinsa na rana kamar yadda na saba kowani lokaci bayan na gama girki ina kai masa nashi bangarensa. Bayan na ajiye abincin ne ya miƙomin kofin dake hannunshi wanda ke ɗauke da lemu ya umarceni da na shanye, naso nayi jayayya saidai yace idan ban sha ba bazai barni na tafi ba shiyasa na karɓa na shanye tare da miƙewa da nufin tafiya sai ya kuma cewa na share mai falon shi yayi ƙura. Tunda nafara sharar nakejin bacci na fizgata kafin nagama kuma bansan inda kaina yake ba sai farkawa nayj na ganni akan gadonshi ya ketamin haddi..." Ta ƙarasa faɗa tana mai fashewa da wani marayan kuka wanda ke nuni da ciwon abin da takeji.

Kashe recorder ɗin Saleem yayi kana ya miƙe ya fita yana musu alama da ido.

Zarah da Jidda ma miƙewa sukayi kana Zarah tace.

"Insha Allahu za'a bi miki haƙƙinki sannan kafin mu tafi za'a sa hannu a shigar dake aikin da za'a miki na matsalar yoyon fitsari da kika samu."

Godiya suka ƙara yi musu sosai.
Sanna su Jiddan suka bar ɗakin.

Saida suka biya kuɗin aikin da za'ayi wa Fahima sannan suka bar cikin asibitin.

A hanyarsh da zuwa gida ne Jidda dake gaban motar ta waiwayo ta kalli

1 Comments On ASP ZARAH
avatar
zainab-3-7-9

1 year ago

Reply

I need complete Asp zarah

Please Login or Register in order to submit comment