Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zarah data jingina kanta a jikin kujerar bayan motar tace.

"Zarah kina ganin ba muyi ganganci ba wajen shiga cikin wannan case ɗin daya shafi Alhaji Nura Mai Riga.?"

"Banason halinki na saurin karaya Jidda, kada ki manta Allah yana tare da msi mai gaskiya." Ta faɗa tana mai ɗagowa daga jinginawar da tayi jikin kujerar.

"Waye ne Alhaji Nura Mai Riga.?" Saleem ya tambaya hankalinshi na kan hanya.


*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸

*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.

*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️


... Jidda ce ta gyara zama tare da fara magana.

"Wani sanannen ɗan siyasa a ciki da wajen Bauchi, anyi mishi shaidar rashin arziki da wulaƙanci gami da cin zarafin na ƙasa dashi, baya ragama kowa kasancewar yana da muƙami ga dukiya kuma daya tara, shiyasa yake taka kowa ya zauna lafiya daga shi har ɗan nashi. Ana faɗin cewa zai iyayin komai akan yaronshi ko da kuwa kisa ne. Shiyasa nake tsoron kar wani abu ya haɗa su da Zarah saboda baza'a haifar da ɗa mai ido ba."

Kai Saleem ya girgiza kana yace.
"Gaki a haka kamar Jaruma amma zuciyarki fal take da tsoro, ni a gani na wannan ba wani abu bane da za'a tsorata har ayi shakkun yin shari'a dashi. Insha Allah zamu zauna anan har sai munga an kwatar ma yarinyar nan hakkinta. Kuma ni zan zame mata lauya."

"A zahiri bakai bane zaka zame mata lauyan amma a baɗini kai ne." Zarah ta faɗa idonta a lumshe kamar ba ita tayi maganar ba.

Ɗan juyuwa Saleen yayi yana son fahimtar abinda take nufi.

"Wani lauyan zamu nema yanzu a matsayin wanda zai kareta, saboda zai iya siye duk wani lauya da zamu ɗauka da kuɗi. Bayan mun gama yarda muna da lauya sai ranar da za'a shiga kotu mu rasa mafita. Shiyasa a yanzu dole mu ɗau wani lauyan na ganin ido, amma a baɗini zamu cigaba da gudanar da bincike tare da haɗa shaidun da zamu gabatar a kotu." Cewar Zarah

Sosai suka ƙara mamakin fasahar ta wajen yin tunani abinda masu laifi zasu aikata.

"Sam banyi tunanin haka ba da farko, kuma tabbas nasan Alhaji Mai Riga zai aikata haka." Faɗin Jidda tana mai haɗe hannayenta alamun jinjina ga Jidda.

Haka suka cigaba da tafiya suna hira jefi-jefi har suka ƙaraso gidan.

Ɗakinta ta wuce kai tsaye tare da shigewa banɗaki, wanka tayi sannan ta fito ɗaure da towel a jikinta. Zama tayi da nufin yin shafa amma ta kasa illa kwakwalwarta dake tariyo mata irin matsalolin da take dasu a gabanta, riƙe kanta tayi da hannu biyu bayan ta kifashi a jikin mirro ɗin.
Saitin zuciyarta ta kuma dafewa da hannu ɗaya tanajin yadda take bugawa da sauri, tabbas tasan watarana matsalolin ƙasar nan zata haddasa mata bugawar zuciya saboda yadda ta ɗau matsalolin tamkar yadda take ɗaukan duk wani abu da ya shafeta ko danginta.

Miƙewa take shirin yi ta nufin saka kaya batare data shafa man ba, turo ƙofar da akayi ne yasata dakatawa tare da maida kallonta ga Baaba dake shigowa bakinta ɗauke da sallama. Amsa wa tayi tare da faɗin.

"Wannan tsohuwa me zakiyi min a ɗaki ne haka daya saki haurowa sama, dan wannan zuwan naki kam akwai abinda ta kawoki tunda nasan ba haurowa sama kikeyi ba."

"Yo idan ba wani abu ba mai zanzo nayi a bene nikam salon watarana na faɗi a garin sauka." Baaba ta faɗa tana mai zama a gefen gadon Zarah.

Sai da suka gama barkwancin jika da kaka sannan Baaba tayi gyaran murya tace.

"Zara'u."

Ɗagowa tayi ta kalleta, gani yanayin fuskarta ne yasa tagane magana ce mai mahimmanci zasuyi.

"Na'am Baaba."

"Kin sani Zara'u kin kai mun zalin daya kamata ace kema kinyi aure kamar ƴar uwarki Jidda, aure shine darajar duk wata ƴa mace koda kuwa tana da tarin dukiya, kyau, muƙami ko nasaba. Ba mu da yawan zuri'a Zara'u kune muke fatan ku hayayyafa ku sama mana masu yi mana addu'a damu daku gaba ɗaya koda bama a raye, shekarunki na haihuwa fa yanzu 23 yakamata ace kinyi aure kin sama kanki daraja musamman a irin yanayin aikin da kikeyi da ake tunanin duk wata mace da takeyin shi bata da kamun kai. Dan Allah ki siya mana mutunci da kanki kar a fara maganar a gari ana cewa mun barki sakaka."

Shiru Zarah tayi batare da tayi magana ba, Baaba ce ta kuma cewa.

"Munyi magana da babanku Sulaiman yace nagaya miki ki turo mishi wanda kika tsayar domin manya su shiga maganar."

"Baaba bawai auren ne banaso ba, akwai burika na da nakeson cikawa wanda nasan va kowani namiji dazan aura bane zai bani damar cikasu, shiyasa ma bana saka auren cikin lissafina a yanzu amma idan lokaci yayi zanyi insha Allahu." Ta faɗa alamun maganar Baaba bata wani dame ta ba.

"Toh akwai wani wanda kuka sasanta ne ko kuma kukeson ku sasanta tsakaninku dashi.?"

"Dan Allah Baaba ki barni ni babu wani da nakeso ko muke soyayya, aikina shine a gabana yanzu." Cewar Zarah da ta miƙe ta nufi gaban durowar kayanta.

"Nima ai ina fatan ki kasance tare da aikinki kodan kawo ƙarshen waɗanda azzaluman mutanen, amma ki dawo ki zauna muyi magana domin bankai ga faɗin sakon da aka aikoni na isar ba."

"Waye kuma ya aikoki.?"

"Toh da farko dai mai saƙon yace bazai zo da kanshi bane gudun kada kiji nauyin shi kiyi abinda bashi ranki ke so ba, alfarma ce yake nema a gurin ki nason haɗa zuri'a dake, ma'ana dai yana neman alfarmar ki akan yanason ya haɗaki da ɗansa ku raya sunnar manzo S. A. W a ƙarƙashin inuwa ɗaya. Kuma yana fatan ace wani bai riga shi ba sannan yace a barki kiyi shawara kafin ki bada amsa."

Wani kallo Zarah ta mata kafin tace.

"Waye da wannan doguwar wasiƙa kuma Baaba."

Miƙewa tayi kana tace.

"Doddon ku mana Sulaimanu yace yana neman alfarmar ki amince da auren ɗan sa Muhammad Jawwad."

Dariya sosai Zarah tayi jin yadda Baaba ta kira Daddy wai Doddo kana ta tsagaita ganin har Baaba takai kusa da ƙofa, ƙarasa wa tayi inda take sannan tace.

"Ban fahimce ki sosai ba Baaba."

"Ke dai ba kurma bace sannan kuma ke ba mahaukaciya bace bare nace bakya fahimta, abinda dai kikaji shi nake nufi idan kuma kina tantama ne to ki ɗau waya ki kirashi ya miki ƙarin bayani." ta faɗa tana mai ficewa a ɗakin.

Ta daɗe tsaye a inda Baaba ta barta tana sakawa da kuncewa akan maganganun Baaban, lokaci ɗaya kuma ta watsar da zance daga tunaninta sannan ta nufi durowar ta ɗauko wata doguwar rigar atamfa super ta zura. Mai kawai ta shafa a leɓanta kana ta zura takalmi ta fice zuwa falo inda tasan Jidda na jiranta.

A zaune ta same su ita da Saleem sun tasa laptop a gaba da alama abu suke gani a ciki mai mahimmanci.

Jidda ce ta ɗago ta kalleta tace.
"Madam ASP tun ɗazu muke jiranki anan munkawo ƙara.''

Kyaɓe baki tayi kana ta gaishe da Saleem sannan ta kalli Jidda ta kuma cewa.

"Ace mutum shi kullum cikin zolaya kamar mara damuwa."

"Wace damuwa ne dani nikam, ga mijina a gefe ai sai farin ciki ko da yaushe." Jidda ta fada.

Bata kulata ba sakamakon abinda Saleem yake nuna mata a cikin laptop ɗin, shiru sukayi gaba ɗaya suna mai maida hankalinsu kan laptop ɗin.

"Na rigada na gama bincike kuma na tabbatar shi ne mai laifin shaidune kawai suka rage mana, sannan nayi magana da babban likitan asibitin da yarinyar take akan Jidda zataje ta gudanar da duk wasu bincike da rahoton likita da za'a buƙata a kotu, yanzu binciken ya rage na ɓangarenki daga nan kuma a shigar da ƙara kotu." Cewar Saleem

"Abun zaizo da sauƙi ai, nima yanzu nake so na fita na gudanar da wasu bincike na saboda gobe nakeson a shigar da ƙara kotu." Faɗin Zarah.

"Yanzu baiyi yamma ba Zarah.?" Cewar Jidda.

Kaɗa kai tayi kana tace.
"Inason zuwa ofishin ƴan sanda da suka fara kai ƙara ne domin haɗuwa da Inspector ɗin wajen, na samu labarin yafi zama a office a irin wannan lokaci."

"Ki tsare shi ya faɗa miki gaskiya fa Zarah kuma ya gayamiki nawa a bashi ya danne gaskiya." Jidda ta faɗa cike da takaicin abinda aka aikatawa Fahima.

Dariya Zarah tayi sannan ta maida kallonta ga Saleem tace.

"Gaskiya Sa.Jid ina tunanin kwanan nan zan shigar da matar ka aikin ƴan sanda ita ma, naga alama ta fini zaƙewa akan aikin nan."

"A'a ki rufamin asiri, ai aikin ƴan sanda sai irinkj jajirtattu bana su Jidda bane." Faɗin Saleem cike da zolaya.

Dariya suka yi duka kafin Zarah ta miƙe ta koma ɗakinta inda ta ɗauko mayafi da jaga, sallama ta musu sa'an nan ta fice domin zuwa inda ta faɗa musu.

A hankali take driving har ta iso bakin ofishin, kallon gurin tayi wanda ke tsabtace sosai sai ƴan sanda da mutane dake shawagi ɗaɗɗaya.

Kasancewae gilashin motar mai duhu ne yasa jami'an basu gane wacce ke ciki ba har saida ta fito, nan tsirarun da suke farfajiyar wajen suka ƙaraso gabanta da hanzari suka sara mata.

Kai kawai ta jinjina sannan ta fara tafiya a hankali inda suke take mata baya har zuwa ofishin Inspector ɗin.

Miƙewa yayi da sauri daga kishingiɗen da yake tare da miƙewa...... *MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*📚🖊️
*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers face_
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
___________________________________

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸

*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.*
*Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*

*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.

*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Free Page 7*

... "Barka da zuwa ranki ya daɗe." ya faɗa cike da ladabi.

Zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun office ɗin sannan ta umarce shi ya zauna shi ma.

"Ina son sanin gaskiyar binciken da kayi game da case ɗin fyaɗe da aka kawo maka kwanaki biyar da suka wuce." Zarah ta faɗa tana mai zuba mishi idanu.

Daburcewa yayi alamun rashin gaskiya, take kuma zufa ta keto mishi duk da iskar fanka dake kaɗawa a ofishin. Kana yace.

"Dama ranki ya daɗe ƙazafi ne ake yiwa yaron amma bai aikata laifin ba."

Bata ce komai ba ta ciro wata paper daga cikin jakarta ta miƙa mai tana mai cewa.

"Ka cire mana hular mu da belt ɗin mu, sauran kayan kuma idan kaje gida ka aiko mana dasu. Sannan duk wani abu daya kasance mallakin hukumar mu ka dawo mana dashi, karɓi wannan takardar korarka daga hukumar mu ta ƴan sanda ne."

Durƙosawa yayi akan gwiwan shi tare da faɗin.

"Ki rufamin asiri ranki ya daɗe wallahi zan faɗi gaskiya, wannan aikin dashi nake ci da iyali na da mahaifiyata idan kika rabank dashi bansan ya zanyi ba. Sharrin shaiɗan ne yasa ni karɓa kuɗin toshiyar bakin daya bani."

Shiru tayi batare da tace komai ba, hakan ya bashi damar cigaba da magana inda yace.

"Bayan an kawo case ɗin ni da kaina naje har gidansu wanda ake zargin, bayan mun zauna da mahaifinsa ne yake gayamin cewatabbas ɗan sa ya aikata abinda ake zarginsa dashi amma yana so a kori case ɗin inda ya bani kyautar kuɗi naira dubu ɗari uku, dalilin dayasa na kori case ɗin kenan. Dan Allah ranki ya daɗe ayimin afuwa bazan ƙara ba, nayi alƙawari."

Tsaye ta miƙe kana ta mayar da takardar cikin jakarta sannan tace.

"Ka shirya zama shaida a kotu."

"Nagode ranki ya daɗe insha Allah zan kasance mai faɗar gaskiya."

Nan ya rakota har bakin motarta yana mai ƙara yimata godiya.

Gida ta wuce kai tsaye tana mai tuƙi cikin nutsuwa.

"Har kin dawo." cewar Jidda dake tsaye a dinning tana shirya kulolin abinci bayan Zarah ta shigo cikin falon.

"Ehh sannu da aiki fa Madam."

Hararar wasa ta aika mata sannan tace.

"Yauwa ASP."

Tsayawa tayi a bakin bene da zai sadata da ɗakinta jin maganar Jidda dake cewa.

"Jirani mu haura tare."

Hannunta ta riƙe kana suka haura sama inda suka shige ɗakin Zarah wanda yake farko a jerin ɗakunan dake saman.

Tsalle Jidda tayi ta faɗa kan gado tare da yin juyi sannan ta fuskanci Zarah dake ƙoƙorin rage kayan jikinta.

"Ɗazu Baaba ke tsegunta min wani zance."

"Wani zance kenan."

"Zancen auren ki da Muhammad Jawwad mana."

"Uhmm."

"Meyasa ba zaki amince ba Zarah, babu wani fa da zaki aura ya riƙe ki da daraja kamar shi. Idan ma aikin ki kike tunani ai shi ɗan uwanki ne dole zai barki ki cigaba aikin ki batare da tsauwalawa ba, nikam bana tunanin akwai aibu a cikin wannan haɗin."

"Kema kinsan dai Daddy uba ne a gare ni ko da ace Abba na yana raye shi mai zaɓa min miji ne, bazan iya cewa a'a ba kawai dai zaɓin Allah nake nema a cikin al'amura na."

"Toh Allah ya shige mana gaba baki ɗaya ya kuma zaɓa mana abinda yake mafi alkairi."

"Ameen" Zarah ta faɗa tana mai shigewa banɗaki.

Duk wasu bincike daya kamata a gudanar sun gama haɗa shi, zuwa yanzu mai laifin ya daɗe da kasancewa a bayan kanta a kulle sai jiran ranar shiga kotu duk da yaƙi amsa laifin nashi.
Har zuwa yanzu kuma Zarah bataje office ba tun bayan ranar sa takaiwa C. P rahoton abubuwan da suka faru.

Yau dai ta shirya domin zuwa ofishin nata bayan tayi sallama da jama'ar gidan.

Kyawawan motoci guda uku ta gani a harabar ofishin nasu wanda ya tabbatar mata da sunyi baƙin manyan mutane.

Tun kafin ta ƙarasa ta hango Alhaji Mai Riga zaune a inda suka tanada domin zaman baƙi.

Bata ko kalle inda yake ba lokacin da ta ƙaraso kusan shi saima shigewa ofishin ta da Sergent Bala ya buɗe mata ƙofar.

Saida ta zauna kafin Sergent din yace.

"Ranki ya daɗe wannan mutumin shine wanda yake ta ziryar son ganinki a kwana biyun nan, yau ma tun ƙarfe bakwai yazo saboda na faɗa mai zaki zo office yau."

Kai ta gyaɗa sannan tace.

"Ka shigo dashi."

Fita yayi bada jimawa ba kuma ya ƙara shigowa inda a bayan shi Alhaji Mai Riga ne da wasu body guards dinsa da suka sha baƙaƙen kaya guda biyu.

Kujerar da Sergent Bala ya nuna mai ya zauna.

Shikuwa Bala sara mata yayi tare da ficewa a office ɗin.

"Alhaji a tunani na kaine wanda keson zantawa dani." Faɗin Zarah

Washe baki yayi tare da faɗin.

"Ehh nine ranki ya daɗe."

"Toh tsayuwar me waɗannan keyi anan."

Umarni ya basu da su fita waje, nan suka nufi ƙofar fita bayan daya ys ajiye wata brief case a kan teburin........ ✍🏼

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸


*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.

*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️


.. "Na kwana biyu ina zuwa nan ranki ya daɗe bana samun ki." cewar Alhaji Mai Riga.

"Ayya." ta faɗa a hankali.

Zama ya gyara sannan yace.

"Dama nazo ne akan maganar case ɗin yaron waje na da aka ce ke kike riƙe dashi, duk da naga wannan case ɗin na ƙananun jami'ai ne ba manya irin ku ba."

"Akwai kundin tsarin daya ce babban jami'i kar ya karɓi case ne.?"

"Ba haka nake nufi ba ranki ya daɗe, nazo ne kawai muyi magana akan case ɗin ne."

"Ka samo mana wata shaidar ne.?"

"Ba shaida ba dai ranki shi daɗe, kawai inason ayi wani abu akai ne."

"Bangane wani abu ba."

"Ehhm nace dama ko za'a bar maganar shiga kotun a sasanta a gida kawai."

"Bai aikata abinda ake zarginsa dashi bane.?"

"Ranki ya daɗe kinsan halin yara basa tunani kafin su aikata wani abin."

"Tambaya ce kawai nayi bai aikata bane."

"Ehh toh gaskiya yace min ya aikata amma...''

Hannu ta ɗaga mai alamun batason jin sauran zancen sannan tace.

"Toh Alhaji ya aikata ya kakeson ayi kenan."

"Yauwa nace a sasanta kawai anan inyaso sai abiya kuɗin da mahaifan yarinyar suka kashe akan nema mata lafiya."

"Baka gudun ya kuma aikatawa."

"Toh kinsan halin yaran zamani su komai sukayi gani suke daidai ne."

"Yanzu kana nufin a janye ƙarar kenan.?"

"Ehh haka nakeso ranki ya daɗe, ni ɗan siyasa ne hakan zai iya jawomin cece kuce a tsakanin jam'iyun adawa. Yanzu ga wannan." Ya ƙarasa faɗa yana mai buɗe jakar da body guard ɗin ya ajiye, kuɗi ne maƙil a cikin jakar rafar dubu ɗaɗɗaya an jere su.

Murmushi tayi har saida dimple ɗinta ya lotsa sosai kana ta sa hannu ta taɓa kuɗi tare da ɗaga rafa ɗaya ta jujjuya sannan ta aje.

Cikin ƙwarin gwiwa alamun nasara Alhaji Mai Riga yace.

"Shiyasa ban turo kowa ba nace bari nazo da kaina ayi maganar zamu fi fahimtar juna."

Gyaɗa kai tayi kana tace.

"Zan iya tambayan ka idan babu damuwa."

"Bakomai ranki ya daɗe yi tambayarki."

"Kana da ƴa mace.?"

"A'a babu yarona ɗaya ne dai wannan da muke magana akan shi."

"Ohk to kana da Yaya ko Ƙanwa mace."

"Gaskiya babu dake dukkan mu maza ne iyayen mu suka haifa. Amma lafiya kike min irin tambayar nan ranki ya daɗe."

"Ban kai ga ƙarasa tambayata ba idan na gama zan amsa taka tambayar. mahaifiyar yaron nan yakake jinta a ranka a matsayinta na waccw nake tunanin tun auren ƙuruciya shine har yanzu."

"Gaskiya bazan iya misalta miki yadda nake jinta a raina ba, wannan dalilin ne ma yasa har yanzu banyi mata kishiya ba."

"Masha Allah, yanzu Alhaji misali wani ya shiga gidanka yayi wa matar ka fyaɗe sannan da akayi bincike aka gano mai laifin, wani irin mataki zaka ɗauka.?"

"Wallahi da hannu na zan kashe shi, idan ban samu damuwar haka ba kuma zan tsaya da dukiya da ƙarfina har sai naga an yanke mishi mummunan hukunci akan laifin daya aikata min."

Dariya Zarah tayi sosai sannan lokaci ɗaya ta gimtse kana ta jawo jakar kuɗin gabanta ta zuge zip ɗin kamar yadda yake tare da tura jakar gaban Alhaji Mai Riga kana tace.

"Kamar yadda kakejin zaka tsaya da ƙarfi kuma da dukiyarka ni idan akayi qa matarka fyaɗe, toh ni inajin fiye da hakan wajen ganin na tsayawa kowace mace da aka ketawa haddi domin abi mata haƙƙinta. Wannan kuɗin da ka kawo bazai taɓa canzamin ra'ayi domin na saba riƙe fiye da irinsu, cin hanci koh? Toh kasani cewa bakayi kuɗin da zaka iya bawa Zarah cin hanci ba, wannan kuɗin ko albashin ma'aikatana na wata ɗaya bazai iya biya ba. Shin kasan girman laifin da ka aikata na baiwa ƴar sanda cin hanci.? Tabbas zan baka mamaki kuma dole a yankewa yaron ka hukunci daidai laifin daya aikata. Banason na ƙara jin ko da kalma ɗaya ce ta fito daga bakin ka idan kuma ba haka ba, hmm kulle ka ba wani abu mai girma bane a wajena sannan babu wani jami'in dayasa isa ya saka ni buɗeka idan nayi hakan. Dan haka kaɗau tarkacen kuɗinka ka ficemin daga office." taƙarasa faɗi tana mai buga teburin, wanda hakan ya ƙara ɗarsa tsoro a zuciyar Alhaji Mai Riga domin dai dama ƙarfin hali kawai yakeyi yake iya mata magana amma ba ƙaramin kwarjini take masa ba.

Batare da tanka ba kamar yadda tace yaɗau jakar tare da ficewa daga office ɗin yana mai banko ƙofar da ƙarfi.

Murmushi Zarah tayi sannan tace.

"Mai Riga kenan, ba shirin wasa nayi a kanka ba duk wani motsin ka yanzu a tafin hannu na yake.".

Kiran wayar daya shigo ne yasa ta saka hannu ta jawo wayar daga inda take, numbar Daddy da tagani ne yasa bata ɗaga ba har saida ta yanke sannan ta maida kiran.

"Assalamu alaikum."

"Wa'alaikumus salam daughter barka da safiya."

"Daddy ina kwana."

"Lafiya lau kun tashi lafiya koh.?"

"Lafiya kalau Daddy ya Momi."

"Gata nan lafiya lau, yasu Baaban dai da mutanen turai."

"Duk suna lafiya Daddy."

"Kin fita aiki ne yau.?"

"Ehh ina office."

"A'a toh bari na bari ki koma gida kar na katse miki aiki, dama nayi tunanin kina gida ne shiyasa na kira muyi magana."

"Bakomai Daddy ba aiki nakeyi ba dama, zamu iya magana babu damuwa."

"Toh Masha Allah, nace ko Baaba ta isar miki da saƙo na.?"

"Ehh Daddy ta gayamin kuma na

1 Comments On ASP ZARAH
avatar
zainab-3-7-9

1 year ago

Reply

I need complete Asp zarah

Please Login or Register in order to submit comment