Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya dawo da waɗanda suka rasu ba, idan kace baka da kowa toh mufa ko baka ɗaukemu a matsayin iyaye bane dama, ƴan uwanka mata fa, bawai ina nufin bazan iya riƙesu bane tamkar ƴaƴan da na haifa amma suna buƙatarka a kusa dasu a matsayinka na wanda zasu dinga gani tamkar ɗan'uwana da ya rasu, kaine kaɗai zaka iya rarrashinsu musamman Zarah da ita bata kukan fili saina zuciya wanda yafi ƙuna, kayi haƙuri ka shirya mukoma gida tare dan Allah ina neman wannan alfarmar."

"Daddy kai ubane a wajena baka da buƙatar neman alfarma a wajena, umarni kawai zaka bani na aiwatar, insha Allahu zuwa ƙarshen shekara zan tattaro na dawo gida."

"Me zaka tsayayi anan har ƙarshen shekara? Bayan haka ma bikin ƴan uwanka za'ayi nan da wata ɗaya da sati biyu ka shirya kawai mu tafi tare."

Idanunshi da suka fara washewa ya waro wanda hakan yayi mishi kyau matuƙa, kafin yace.
"Wasu ƴan uwan nawa kuma Daddy."

"Ehh ƴan uwanka Zarah da Jawwad, insha Allah nan da wani lokaci za'a ɗaura aurensu."

"Amma ita Zarah ce ta amince da auren Bro Jawwad ɗin? Ko dama suna soyayya ne ban taɓa sani.? Amma yarinyar nan batada hankali duk ana maganar nan shine bata taɓa faɗamin ba ɗazu ma fa munyi waya da ita amma take cemin babu komai, yanzu ina ita ina miskilancin M.J mut..." lura da yayi da wanda suke maganar ne ya sashi yin shiru batare da ya gama maganar ba tare da sunkuyar da kanshi ƙasa cike da kunyar maganganun daya yiwa Daddyn.

"Kada kaji kunyata Son, ko nine a matsayinka tambayar da zanyi kenan yanzu tamkar uba kake a garesu kanada damar yin bincike a duk wani lamari daya shafesu."

"Kayi haƙuri Daddy, zan shirya mu wuce tare."

"Toh nagode Son, Allah yayi albarka".

"Ameen" yace kana ya tsiyayi ruwan dake ajiye akan teburin wajen yasha, nan suka zauna suna hira kafin daga bisani suka miƙe tare da barin wajen.

👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️

Saida ta kammala duk wasu mahimman abubuwa da duka dace game da case ɗin kafin ta nufi gida cikin hanzari saboda jiran da ake mata .

Da sallama ta shiga falon, ganin Baaba a zaune ta sha kunu ne yasata faɗin
"Dan Allah ayimin afuwa Baabata aikine mai matuƙar mahimmanci ya tsayar dani."

"Zaki wuce kije ki samesu ko yaya."

"Haba ko wanka bazaki bari nayi ba, da kayan aikin zanje ne wai"

"Wallahi idan baki wuce ba zan saɓa miki, yo menene ai gwara suka ganki da kayan aikin su san ba ƙarya na musu ba, ki wuce kafin raina ya ɓaci"
Babu yadda ta iya haka ta nufi ƙofar falon Abban saboda batason tayi abin da zai ɓata ran Baaba tunda yanzu ita kaɗai ta rage musu.

Abbdallah na kishingiɗe a doguwar kujera yayinda M.J ke zaune yana danna waya, sallamar da akayine tasa ya miƙe daga kwancen yana amsawa shikuwa M.J. ko ɗago kanshi baiyi.

"Amaryar..." maganar Abdallah ce ta katse lokacin daya kalli Zarah lokaci ɗaya kuma ya waro ido, kallonta ya ƙarayi sosai tana sanye da abaya amma hakan bazai hana mutum ganin kayan Ƴan sanda dake jikinta, dariyarshi ya ƙunshe tare da amsa gaisuwar da take mishi.

"Amaryarmu kin shanya mu har mun bushe."

"Ayi haƙuri dan Allah aiki ne ya tsayar dani shiyasa ." ta faɗa tana zama a kujera.

"Toh gaki ga angon dai domin yayi fushi kinga ko kallonki yaƙi."

Kallon shi tayi kana tace
"Barka da zuwa ayimin hakuri na barku kuna ta jira."
Kusan second goma dayin maganar kafin ya ɗago da nufin kallonta, ido ya waro sosai domin tabbatar da abinda ya gani, miƙewa yayi tare da nufu inda take zaune yana tafa hannayenshi......✍️


_Tammat Bi hamdulillah! Nan na kawo ƙarshen free pages, ga maison cigaba da karantawa sai a tuntuɓeni. Nagode sosai da addu'o'in ku da soyayyarku a gareni, sakallahu khairan._

*By*
*Jasmine*🌸🌸
07048961623
*ASP ZARAH*

Tsayuwa yayi a gabanta na wasu sakonni kafin ya durƙusa a gabanta yace.

"Naji mamaki matuƙa sannan nayi farin ciki da wannan zaɓin na mahaifina, a ɓangare guda kuma ina takaicin haɗani aure da karuwa da za'ayi, sannan mace mai fuska biyu. Albishir da shawara zan miki a yanzu.."

Maganar shi ta katse saboda dafashi da Abdallah yayi yana cewa

"Haba M.J wane irin magana kakeyi ne haka.?"

"Kayimin shiru Abdallah bana buƙatar jin komai daga gareka, ka zuba ido kawai."

Baice komai ba ya kuma ya zauna cike da takaicin abinda M.J din yakeyi.

Sunkuyawa ya kuma yi tare da dafa kujerar ta take kai da hannunshi biyu ta yadda suna iya jiyo numfashin juna.

"Ina baki shawarar ki shirya tarban kowani ƙalubale da zaki fuskanta a zaman da zakiyi a cikin gidana domin zai kasance tamkar maƙabartarki domin zakiso ki tsince kanki cikin kabarinki fiye da gidana, sannan ina miki albishir cewa bazan dakatar dake daga aikin naki ba wanda kike rufarufa dashi kina aikata saɓon Allah amma ki sani bazan lamunta ba ace kina aurena kina yawon karuwanci. Banza, ballagaza, karuwa kawai mazinaciya."

Ba iya Zarah ba hatta Abdallah saida yaji zafin kalaman M.J akan Zarah, sunkuyar da kanshi yayi cike da jin kunyarta amma uban gayyar ko a jikinshi illa ma zama da yayi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tare da tsiyaya ruwa a kofi yana sha.

Tun bayan rasuwar iyayenta bata sake tsintar kanta cikin baƙin ciki da ɓaci rai irin na yau ba, zuciyarta takeji tamkar xata tsago ƙirjinta ta faɗo, a yau tanaji duk wanda zai kirata da kalmar _Marainiya_ bazata ƙi amsawa ba, kamar ko da yaushe idan ranta ya ɓaci bata taɓa iya yin kuka na hawaye saidai na zuciya.

Abdallah ne yayi ƙarfin halin magana ta hanyar faɗin

"Dan Allah Zarah kiyi haƙu...."

"Karka ƙarasa Abdallah mutane masu daraja ake baiwa haƙuri idan anyi musu ba daidai amma ba marasa tarbiyya irinta ba, tashu mu tafi."

Bai kuma tankawa ba saboda tsananin ɓacin rai illa bayanshi da yabi bayan shi suka fice a falon.

Tafi mintuna talatin a zaune ta kasa ko da motsawa, bakin ciki tamkar zai kashe ta, murmushin yake tayi ƙoƙarin yi saboda muryar Baaba da taji a bakin ƙofar falon.

"Me kikeyi anan kuma Zara'u bayan sun tafi." cewar Baaba daga bakin ƙofar.

Miƙewa tayi cikin fara'ar da ta aro tace

"Tunanin masoyina nakeyi, inajin tamkar na kai kaina gidanshi mu cigaba da rayuwa."

Kaucewa tayi daga dukan da Baaba ta kawo mata tana dariya.

"Allahu ya shiryaki Zara'u, muje kici abinci nasan wunin yau duka bakisa komai a cikinki ba."

Nan suka fice a falon tana ta ƙoƙarin biyewa zolayar Baaba cikin dauriya gudun kada ta fahimci wani abu, sai da ɗan tsakuri abincin kafin ta barta ta wuce ɗakinta.
Gaban hoton iyayenta ta isa tare da ɗauka ta rungume a ƙirjinta, sai a wannan lokacin kukan yayi nasarar zuwa mata, batayi jayayya ba domin itama tanason yin kukan ko zai rage mata raɗaɗin da takeji a zuciyarta, nan ta shiga rera shi mai taɓa zuciya. Ƙarar da wayarta keyi ne yasa ta tsagaita da kukan tare da miƙa hannu ta ɗauki wayar , ganin mai kiran nata ne murmushin da batasan dashi ba ya kwace mata, da sallama a bakinta ta kara wayar a kunne, sai da ya amsa sallamar kafin ya fara jero mata tambayoyi.

"Meyasa kika amince da auren Bro Jawwad.? Dama kuna soyayya? Meya hanaki sanar dani halin da ake ciki har kina shirin yin aure amma kin kasa sanar dani? Meke damunki ne?"

"Duk wannan tambayoyin Bro wacce kakeso nafara amsa maka ne.?" Ta faɗa cikin marairaicewa

"Duka nakeso ki amsamin, haba mana little wannan zurfin cikin naki yayi yawa."

"Toh ya kakeso nayi Yaya, me kakeso nace maka."

"Gaskiya nakeso ki faɗamin tsakaninki da Allah, kada ki ɓoyemin komai dan girman Allah baki da wanda ya fini a halin yanzu kinji."

Cikin sanyin jiki ta amsa mishi da "Toh".

"Kuna soyayya da M.J ne.''

Tambayar tazo mata wani irin amma ba yadda ta iya tunda tayi alƙawarin faɗar gaskiya duk da bataso wani yasan halin da take ciki.

"A'a Yaya"

Numfashi yaja mai ƙarfi kafin yace.

"Ya akayi kuma kuke shirin yin aure?"

Shiru tayi batare da tayi magana ba.

"Ki amsamin banason nadawo nayi abinda bai kamata bane."

"Dear zakazo ne." cikin ɗoki tayi tambayar.

"Ehh" ya faɗa a takaice sannan ta cigaba da cewa.
"Ki amsamin tambayata, kun haɗu da juna ne."

"Ehh basu daɗe da tafiya ba ma yazo Bauchi"

"Ya kukayi dashi."

"Yaya..."

"Shikenan tunda bakyason magana idan nazo zan nemi mafita da kaina ko da kuwa dakatar da auren ne.''

''Haba Bro...."

Bai jira ta ƙarasa ba ya kashe wayar gabaɗaya, zama tayi ta dafe kanta da hannuwa biyu, lallai ya kamata tasan yadda zatayi ta rarrashi ɗan uwan nata akan maganar auren nan duk da itama a yanzu tana dana sanin amincewa amma ƙaddara ta rigayi fata.

🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢

Babu wanda ke magana a cikinsu har suka isa masaukin nasu, sun daɗe a zaune kafin Abdallah yace

"Yanzu M.J abinda kayi kana ganin ka kyauta kenan.?"

"Mene abin rashin kyautawa anan."

"Oh kai kana gani kayi daidai kenan, ya za'ayi kaje kana zagin baiwar Allah batare da ka tabbatar da abinda kake zargi ba, ina faɗa maka aikin ƴan sanda babu inda baya iya kai mutum daga inda ya dace har inda bai dace ba, amma kaje kana cin zarafin yarinyar nan, baya ga haka ma fa ƴar uwarka ce, why M.J?"

"Idan ka gama saika faɗamin, look Abdallah wannan rayuwata ce and yarinyar nan ni zan zauna da ita ba wani ba, banason ka kuma yin magana akai babu ruwanka da lamarin dake tsakanina da yarinyar nan."

"Kamar yadda kace zan fita a lamuranka da yarinyar nan amma inaso ka saka a ranka cewa ranar da zakazo kana neman alfarmata na shiga lamuran bazan shiga ba."

"Bazan buƙace ka bama" yana gama faɗin haka ya shige bandaki, shikuwa Abdallah miƙewa yayi yaje reception da nufin binciken tun yaushe Zarah suka kama ɗakin, saidai hirar da wasu matasa sukeyi ta ɗauke mai hankali, nan ya zauna can gefe yana sauraron su, mata biyu ne da namiji ɗaya.
Ɗaya daga cikin matan ne tace.
"Wallahi bantaɓa jin ƴan sanda sun matuƙar burgeni kamar yau ba, kiga yadda yarinyar nan ta kama munafikin mutumin nan cikin sauƙin da babu wanda zaiyi tunanin."

"Ai baku ga komai ba indai ASP Zarah ce, idan ta zaƙolo muku wani mai laifin sai mamaki ya kusa kar ku, wanda kake tunanin bazai taɓa aika wani mummunan laifi ba idan kaji laifin shi sai kayi ta mamakin yadda yake aikatasu." cewar saurayin.
Hirar Zarah suka cigaba dayi wanda yawanci yabonta ne sukeyi tare da jinjina ma yanayin yadda take aiki da gaskiya da riƙon amana, gabansu Abdallah ya ƙarasa tare da baiwa saurayin hannu suka gaisa sannan yace.....✍️


*By*
*Jasmine*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

"Dan Allah naji kuna magana akan wata ƴar sanda shine nace bari nazo naji gaskiyar batun."

Dake saurayin irin masu surutun nan ne bai tsaya wani dogon nazari ba ya fara labarta mishi abinda ya faru awanni uku da suka wuce, na yadda Zarah ta jagoranci jami'i sukayi basaja suka kama mutumin da babu wanda zaiyi zaton mai laifi ne, ya daɗe yana zayyano mishi kyawawan halinta tun daga kan shiga har fannin aiki, ganin saurayin bashi sa niyar dakatawa ne yasa Abdallah miƙewa tare da ajiye musu rafar kuɗi akan teburin da suke zaune ya wuce sama.
Murmushi yayi mai cike da ma'anoni, tabbas bazai gayawa M.J wani abu da ya sani akan Zarah ba, zai barshi har zuwa lokacin da zai gano da kanshi, a wannan lokacin zai taya Zarah ramuwar abinda ya mata amma duk da haka yana fatan ya saduda da wuri kafin dare yamai nisa.

Ko da ya kuma ɗakin bai nuna mishi wata alama dazai gane yana cikin wani yanayi akan abinda ya faru ba, hirarsu suka cigaba dayi har zuwa lokacin da aka kira sallar magrib suka fito masallacin dake farfajiyar hotel ɗin domin sauke farali.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Duk yadda taso taƙi saka abin a ranta ta kasa, kusan kwana tayi a zaune tana tunanin mafita babu shawarar da zuciyarta bata raya mata ba daga mai kyau har wanda bai dace ba, daga ƙarshe dai ta yanke shawarar ɗaukar lamarin a duk yadda yazo mata, zata karɓi tayin kowane irin zama da yakeso suyi, damuwarta ɗaya ce kuma ya magance mata wato cigaba da aikinta, bata da wani sauran abinda zata damu dashi matuƙar zai yarje mata cigaba da aiki.
Washe gari idonta yayi luhu-luhu saboda rashin baccin da bata samu ba ga kuma kuka da tayi sosai, hakan ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani har taji bazata iya fita gurin aiki ba, tana kwance akan sallayar da tayi sallar asuba ta kasa miƙewa ta koma kan gadon.

Ganin har ƙarfe takwas Zarah bata sauko ba yasa Baaba miƙewa da kanta ta haura saman domin duba lafiyarta, da sallama ta shigo saidai duhun dake ɗakin bai barta ta hangi komai ba, lalubawa tayi har Allah ya bata sa'ar samun switch ɗin ta kunna haske ya gauraye ɗakin, kalle-kalle ta farayi ganin bata ganta kan gadon ba har Allah yasa ta hangota acan kusurwar da take sallah. Da hanzari ta ƙarasa inda take tare da tattaɓa jikinta ganinta a duƙunƙune.

"Subhanallahi Zara'u baki da lafiya shine baki faɗa ba tuntuni a kaiki asibiti, saiko zauna da ciwo a jikinki haba sai kace ƙaramar yarinya."

Cike da juriya da ƙarfin hali tayi ƙoƙarin miƙewa zaune tare da jingina bayanta a jikin gado tace.

"Ba wani abu ke damuna ba fa Baaba, kawai ɗan ciwon kai ne daya haddasa min zazzaɓi amma yanzu zanyi wanka nasha magani."

"A'a Zara'u ban yarda da wannan ba ki lallaɓa kiyi wankan sai a rakaki asibiti, ko kuma zaki jira su Muhammadu suzo ne saisu kaiki naga kamar zaifi."

"Baaba nace miki karki damu ba wani abu bane fa zansha PCM yanxu zai sauka."

"Tunda haka kikace ai shikenan Allah ya baki lafiya, dama naga baki sauko bane nazo faɗamiki cewa ɗazu Babanku ya kirani wai sun fasa bari sai wani sati saboda Sadiku ya matsa sai sun dawo shine yau zasu biyo jirgin yamma su dawo."

Wanj irin zabura tayi kamar ba mai jinya ba tace.
"Da gaske Baaba.?"

"Mtsww! Iskancin banza, ni ina nan na ɗaga hankali na baki da lafiya ashe ƙarya kike yi tunda har zaki iya wannan zaburar."

"A'a fa Baaba, kinsan daɗewar da nayi banga ɗanuwana ba dole nayi ɗoki yanzu da naji zai dawo."

"Shikenan ai kiyi wanka kizo ki karya saiki sha maganin."

"Toh yanzu zan sauko."

"Karma ki sauko yanzu inkin so." Ta faɗa tana mai ficewa daga ɗakin.

Miƙewa tayi dakyar saboda sarawa da kanta keyi ta shige banɗaki, ruwa mai ɗumi ta tara ta shiga ciki, ta daɗe a kwance cikin ruwan kafin ta canja shi ta tare wani kana ta ɗauki sponge ta fara murzawa jikinta a hankali har ta gama ta ɗaureye jikinta kana ta fito a ruwan ta ɗaura towel tare da ficewa a banɗakin.
Zama tayi gaban dressing mirro tana ƙarewa kanta kallo ganin yadda damuwar dare ɗaya ke neman ramar da ita, ya zama dole tayiwa kanta alƙawarin cire duk wani damuwa dake ranta akan wannan auren ta maida hankalinta wajen binciken inda zata nemo _Alpha_ domin zuwa yanzu tanajin wani irin kwarin gwiwa akan binciken da take a kanshi, tana iya gudanar da komai batare da tsoro ko shakkar wani abu zai faru da ita, hakan na ƙara bata tabbacin cewa lallai ta kusa tozarta Alpha a idon duniya. Abu ɗaya yanzu takeson sani shine haƙiƙanin inda yake rayuwa, zata iya riskar kowani haɗari matuƙar zata gano inda yake, hanya ɗaya gareta yanzu, hanya ɗaya tak! Wato Raliya. Ta hanyar Raliya ne kawai zata iya gano inda Alpha yake, dole tasan yadda zatayi ta samu duk wasu bayanai a gurin Raliyar.

Tunanin damuwar Alpha da tayi ne ya mantar da ita badakalar auren dake gabanta, mayukanta ta shafa tare da wadata duk wata gaɓa na jikinta da turare, gaban wardrobe taje ta tsaya tare da kallon tulin kayanta dake ciki, idonta ne yakai kan kayan sports ɗinta dake can gefe a ninke, zaro su tayi tare da ƙura musu ido tana tuna lokacin baya da kowace ranar lahadi sai sunyi wasanni kala-kala da yayarta Rahama saboda haka ma Abba ya saka aka ƙawata musu wani sashi na cikin garden dinsu da kayan wasanni, wasu lokutan ma hatta Abban yakan kasance tare dasu domin shima yana matuƙar son wasan Table Tennis. Wasu marayun hawaye ne suka zubu daga idonta, hannu tasa ta share tare da yiwa iyayen nata addu'ar samun Rahamar ubangiji, kayan ta mayar ma'ajiyarsu kana ta ciro wata material kalar blue da golden, ɗinkin riga da skirt ne wanda ya matuƙar karɓan jikinta.
Wayarta kawai ta ɗaukan sannan ta fice a ɗakin.
"Ya jikin dai" Baaba ta tambaya bayan saukowarta cikin falon.

"Da sauƙi." ta faɗa a hankali.

"Allah ya ƙara afuwa, ga kalaci akan dinning idan kin gama saiki sha magani."

"Toh" ta faɗa tare da miƙewa ta nufi dinning ɗin da Raliya ke gurin tana ƙara ƴan goge-goge, kujera ta jamata ta zauna tare da cewa.
"Ina kwan Anty."

"Lafiya" ta amsa a taƙaice kana ta kuma cewa.
"Jeki kawai." ganin Raliyan na ƙoƙarin zuba mata abincin.
Tea kawai tasha sha sai dankali da ta ɗan tsakura, sannan ta miƙe ta koma cikin falon ta kwanta a doguwar kujera, tana daga kwance take ƙarewa Raliya dake zirga-zirga kallo, tabbas akwai abinda take ɓoyewa domin tun zuwanta gidan bata taɓa ganinta babu hijabi ba kullum cikin saka hijabai take kowani irin aiki da takeyi ko yanayi da ake ciki. Toh mene ne Raliyan bataso a gani??? Ta tambayi kanta, shiru tayu na wasu mintuna kafin ta saki wani murmushi mai sauti wanda har saida ya jawo hankalin Raliyan dake moping, tabbas ta samu amsa.
Lallai akwai tatto ɗin Alpha a wuyanta wanda batason a gani shiyasa ko da yaushe take cikin hijabai.
Wayarta da tayi ringing ne ya katse mata tunanin da takeyi, da murmushi a fuskarta ta ɗaga tare da karawa a kunnenta.

"Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida." Jidda ta faɗa daga ɗaya ɓangaren.

"Dama nasan idan bake ba babu mai kirana da sanyin safiyar nan."

"Saboda baki da aurene yasa kike ganin yanzu yayi safiya, toh yakike ya angon namu? Kun gana dai koh?"

"Yanzu wace tambaya zan fara amsa miki maganaɗisu."

"Duka nake buƙatar sani."

"Alright to duka lafiya lau."

"Hmm to ya angon kun sasanta dai koh."

Shiru tayi batare da tace komai ba, hakan yasa Jidda cewa.
"Wato ɗan iskan maganganu yazo ya faɗa miki koh? Kuma shine kika zuba mishi ido batare da kin ɗau mataki ba, wai ke wace irin mace ce habibaty."

Batayi mamakin jin abinda ya fito a bakin Jiddan ba domin idan da sabo ta saba da wannan halin nata, sau da dama ko bata faɗa mata abu Jidda na iya fahimtar hakan a yanayinta, da fari tayi tunanin ko Jidda nada aljanu akanta ne masu gayamata sai daga baya ta gano nature ɗinta ne hakan da kuma tsantsar ƙaunar da takeyi mata shiyasa take iya karantar ko wani yanayi nata, ƙwafa tayi kana tace.
"Toh madam mai gani har hanji ya kikeso nayi idan ba shirun ba."

"Wato abinda ya faru kenan dai, ke kuma saboda gaki mai biyayya kika zura ido kina kallonshi yana gasa miki maganganu, toh wallahi ki kiyayeni tun kafin nakai maƙura na shiga lamarin da bai shafeni ba."

"Kiyi hakuri Mama" Zarah ta faɗa cike da zolaya.

"Toh na haƙura ƴar nan, yanzu ya ake ciki wasu event zamu shirya ne naga alaman idan aka biyewa ra'ayinki bazamu gwangwaje."

Dariya tayi sosai kana tace.
"Kinsan nifa ustaziya ce."

"Matar uztazu koh, shikenan ma bazan kuma yi miki magana ba zanjira Ammi su shigo next week sai mu tsara komai da Sis Rahama."

Miƙewa tayi zaune daga kwancen da take tace
"Wace Ammi."

"Ammi nawa muke dasu dama.?"

"Wato saboda anjireni a cikin dangi yasa duk wanda zaizo kasar ba'a faɗamin koh".

"Ke kika sani nikam na tafi gurin habibi na."
Kafin ta kuma magana kashe wayar, miƙewa tayi da nufin zuwa ɗaki sai....✍️


*VIP ayimin haƙuri dan Allah jiya banji daɗi ba shiyasa banyi typing ɗin ba. Sorry dan Allah*👏


*ASP ZARAH*👩‍✈️

Shigowarsu ce ta dakatar da ita daga ƙoƙarin miƙewa da take domin zuwa ɗakinta, sallamar da Abdallah keyi ta amsa ɗauke da murmushi a fuskarta.
Bakj M.J ya kyaɓe lokacin daya zauna a kujera tare da faɗin
"Mutum a fuska kamar na Allah saidai a baɗini ɓarnar da ake aikatawa ko kare bazai shinshina ba, Allah dai ya shirya wanda ya mayar da kanshi kwarkwar."

"Ameen kuma gani kuturwar uwa zama dani dole." ta faɗa cike da basarwa kamar ba ita tayi zancen ba.

"Amaryarmu ni dai yunwa nakeji ki rabu da wannan angon naki ki ceto rayuwata."
Taƙaitacciyar dariya tayi har kyawawan haƙoranta suka bayyana sannan dimple ɗinta ya lotsa, ta gefen ido ya kalleta cikin rashin sanin dalilin dazai saka yaji haushin fara'ar da takeyi ma Abdallah.
Kallo ya bita dashi lokacin data miƙe har ta shige kicin, tsaki ya kuma ja sannan ya kalli Abdallah yace
"Akan wani dalili zaka dinga sake mata fuska haka.?"

Dariya yayi harda buga ƙafa kana yace.
"Ikon Allah! Tunda baza kayi mata fara'a ba ai saika bar masu yimata koh bawai ka dinga jin haushin mu ba."
Bai kulashi ba sai miƙewa da yayi ya nufi ɗakin Baaba, shima miƙewa yayi tare da bin bayan shi domin zuwa gaida Baabar.
Ganin basa cikin falon yasa ta shirya musu komai a dinning, ɗakinta ta kuma ta ɗau mayafi da makullin mota ta fita domin zuwa kasuwa tayi cefanen abubuwan da zata buƙata na girkin tarbar ɗan uwanta da kuma mahaifinta. Yayanta nason masa sosai shiyasa zata fita da kanta ta siyo sauran abubuwan buƙata na miya da basu dashi.
Tare suka fito falon da Baaba inda suka nufi dinning table yin breakfast.
"Bari na kirata ta zuba muku, Zara'u" cewar Baaba, Raliya ce ta taho da sauri ta iso gabansu tare da cewa
"Hajiya Baaba bari na zuba musu, Anty Zarah ta fita."
"Ina taje kuma."
"Wallahi bata faɗamin ba amma kaman ba nisa tayi ba, naga batayi shiri ba."
"Ai shikenan zuba musu, amma zata fita shine bazata sanar da ni ba."

Ranshi ne yaji ya ɓaci saboda mummunan zaton da shaiɗan ke kitsima mishi na cewar gurin wani ta tafi domin suyi lalata, baice komai ba ya cigaba da cin abincinsa batare da ya kula Abdallah dake cewa.
"Ko dai anyi mata kiran gaggawa ne."
"Ina tunanin haka nima, kasan Zara'u da ƙulafucin aiki bataji bata gani idan aka kira ta wannan aikin nasu duk wani abu da takeyi saita ajiye ta tafi."

"Yanayin aikin nasu kenan Baaba sunyi rantsuwar kare haƙƙin mutane."

"Toh Allah dai ya tsare."

"Ameen" Inji Abdallah

Ko da suka gama cin abincin falon suka dawo suka zauna, hira suka cigaba dayi da Baaba wanda yawanci akan dawowar da su Daddy zasuyi ne.
"Gashi shigowar yamma zasuyi kuma mu yau mukeson tafiya saboda aiki."

"A'a ku tsaya mana dai ku gana duk da ma zaku haɗu acan amma ya kamata ace kun tsaya an tarbesu da ku."

"Shikenan saidai muma muyi tafiyar jirgin kenan, bari na duba ko za'a samu jirgin dare."

"Mezai hana ku ƙara kwana?."

"Baaba nace miki fa akwai aiki."

"Ku zama na'ura saboda aiki idan kun so."

Dariya M.J yayi yace
"Duk rashin son magana da nakeyi sai kinsa ni."

"Yo me za'ayi da mutum miskili."

"Ba zaki gane bane ai Baaba, babu fa'ida ace mutum ya kasance mai yawan surutu."

"Shiyasa ma aka haɗa ka da wacce ta dace dakai gurin rashin son magana."

Bai kuma magana ba illa cigaba da danna wayar shi da yayi, itama Baaba miƙewa tayi ta nufi kitchen.

💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

"Raliya! Raliya!! Raliya!!! sau nawa na kiraki?" ya faɗa cikin fusata.

Cikin shessheƙar kuka ta amsa mai da "Sau uku ranka ya daɗe."

"Wai ke wace irin daƙiƙiyar yarinya ce da batasan abinda takeyi ba, duk tsawon lokacin nan da kika ɗauka a cikin wannan gidan aikin me kikeyi da har yanzu kika kasa samo wani gamsasshen bayani .?"

"Kayi haƙuri yallaɓai wallahi ina ƙoƙarin ganin na samu masaniyar inda lu'u lu'un suke."

"Kullum abinda kike faɗamin kenan, amma sai yaushe ne zaki kawo min wani bayani mai amfani eye.?"

"Fashi da makami."

"Ke Raliya! Baki da hankali ne, kada ki kuskura ki fara aikata wannan mummunan kuskuren, wannan hanyar ba mai billewa bace. Da mai amfani ce bazamu kai war haka batare da mun mallaki wannan kadarar ba, ko

1 Comments On ASP ZARAH
avatar
zainab-3-7-9

1 year ago

Reply

I need complete Asp zarah

Please Login or Register in order to submit comment