Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin danyen boyel yasa bakar hula takalmin kafarsa ma baki yaafito sai zuba kamshin turare yake take fadawansa suka bude masa motarsa yashiga suka rufa masa baya driver yaja sai disina, suna zuwa suka zarce wani dan madaidaicin gida daga ganin gidan gidan talakawa ne masu rufin asiri, cikeda yatsina fuska tafida yafito daga motarsa yanufi cikin gidan fadawansa suna take masa baya, babu ko sallama yakutsa kai cikin gidan yana rayawa aransa wai dan abin kunya nanne gidan sirikansa kai Allah ya kiyaye, atsakar gida yahango mahaifin matarsa da mahaifiyarta tana hura wuta, kafarsa yasa yayi bol da wata buta ta farin karfe atsakar gidan da alama butar mai gidan ce, dayake gwanine wurin kwallo take butar tawuce tasaman kan mai gidan taje tadaki bango tadawo baya tafadi atsakar gidan ta tankwashe yanda bazata moruba har abada.
[10:07PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikin tashin hankali mahaifiyar matarsa tafara magana suwaye ku? Me kukazo yi anan gidan? Cikin yayyatsina fuska tafida yadubi wannan mitumin yace bawan Allah yadda kasa aka daura min aure da yarka to tun wuri kaje kasa awarwareshi domin bazan zauna da itaba kuma bazan taba sonta ba, banda tsabar son zuciya tayaya zaka dauki yarka ka kaiwa mai martaba rallarta har alika min ita, to bana sonta kuma sai nasaketa sai asannan suka gane ashe shine mijin yarsu sirikinsu duk cikinsu babu wadda yayi masa magana kawai tsayawa sukayi suna kallonsa fadawansa kuwa sai fadi suke hutawarka lafiya tafida wannan sako naka ya je inda kakeso yaje, abi tafida a zauna lafiya tafida buhun karangiya ko an zazzage dole sai ya makale, gaba salamun baya salamun dan sarki jikan sarki, gunbar dotse, icen kan kabari titi kafi karfin a tsallakaka dole sai an waiga, takawarka lafiya toron giwa dawisu da ado aka sanka, ragayar dutse namijin fama, juyawa tafida yayi yafita daga cikin gidan fadawansa suka rufa masa baya kai tsaye fadarsa yawuce inda wakilinsa yake, anan ya tambayi wakilin nasa wacce gonace tafi kowacce girma agarin? Cikin washewar baki wakili yace ranka yadade gonar sirikinka malam faduluddeen gonarsa tafi takowa girma cikin rashin damuwa tafida yace ok to inaso nan da sati mai zuwa agyara min domin zan turo masu aiki zasuyi min ginin gidan shakatawata awurin, cikin mamaki wakili yace yallabai sirikinka fa, ka iya bakinka wakili fadawa suka fada lokaci daya, shiru wakili yayi yace tuba nake yallabai tashi tafida yayi yana bawa sarkin fada sallahun ginin da za azo ayi masa, cikeda farin ciki yakoma gida domin yasan abinda yayiwa mahaifan matarsa dole zasuji haushi kuma kila zasu samu sarki suce yasashi yasakar musu yarsu amma abin mamaki shiru yaji ba wani batu alokacin har ansoma fara yimasa ginin gidan da yabada umarni acikin yanayin yashirya yanufi kasar india yana cikeda haushin auren da yake kansa.
[10:45PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Lokacin da tafida ya tafi india ya samu damar mantawa da auren dayake lankaye akansa sai dai kusan kullum idan sunyi waya da faisal yana yawan yimasa maganar amaryarsa dariya kawai tafida yakeyi domin yanzu ya daina damuwa idan faisal yana yimasa tsiya, cikin ikon Allah yasamu yagudanar da course dinsa cikin kwanciyar hankali da nasara wata 5 daidai yayi yafara shiri ysdawo Nigeria. Ranar da yadawo ranar fada ta cika makil da yan sannu da zuwa faisal kuwa sai zolayarsa yakeyi amma yashareshi har sai da suka koma daki sannan yakalli faisal yace mekake cewa dazu? Dariya faisal yayi abokina kayifa kyau sosai kayi fresh kodai kabi hanyar ne? Tsaki tafida yayi kai wai baka da wata magana sai kwaya daya? Ai ni nafada maka ko zanbi hanyar da kake fada to ba yanzu zan bitaba, dariya faisal yayi to malam yakamata fa kasan inda dare yayi maka dan wlh nakusa korarka daga dakin nan? Wazaka kora? Kai zan kora tunda yanzu Kai magidancine so sai kakoma wurin iyalinka, kamanta zurriyya ba iyaliba tafida yafada tareda mikewa yafara cire rigar jikinsa domin shiga wanka. Washe garin ranar da tafida yadawo yakwanta yayi baccinsa ranar bai je office ba sai wurin 11 sannan yashirya cikin suit milk colour yasa milk colour din takalmi yasha turare yafito dan zuwa asibitinsu yana so yaje yakai report, agidan baya yazauna acikin motarsa fadawansa suna tareda shi har asibitin yana fitowa daga mota wasu yanmata wanda zasu kai kimanin su 20 suna sanye da unifoam suka fara kallonsa da alama yan practical ne aka turosu asibitin duk cikinsu babu wadda tafida bai tafi da imaninta ba nanfa suka fara tattauna maganar a tsakaninsu. Sai da tafida yayi hutun sati 2 sannan yafara zuwa office aranar dayaje yana tsaye acikin office dinsa yana daddanna wayarsa wata nurse tashigo masa office akidime pls sir ka taimaka mana munada patient wadda take neman taimakon gaggawa kamar baijiba yayi har saida ta sake maimaitawa sannan yace yaji yabi bayanta har zuwa female ward can gadon karshe takaishi tace gata sir wannan ce, gaban gadon yakarasa wata yar budurwa yagani wanda shekarunta zasu kai 23 aduniya tana sanye da farar riga da bakin dark blue din wando daga gani yar practical ce domin yaganta da unifoam din yan lab science.
[11:12PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Kallon fuskar ta yayi kyakkyawa ce ta daukar hankali shidai yana ganin mata masu kyau amma baiga wadda ta kai wannan kyau ba duk kuwa da cewa baka ce amma bakinta mai kyau ne har wani shining take kallon nurse din yayi me yasameta? Cikin inda inda tace let me go and call her friend she's d one dat brought her here, dasauri tafita Jim kadan sai gata dawata budurwa itama tana sanye da uniform irin na wadda take kwancen kallonta tafida yayi meya sameta? Dr wlh kawai muna zaune mukaga tafadi, sai alokacin yasa hannunsa yatabata amma da bai taba koda hannunta ba ya salam! Yafada saboda jin laushin fatar jikinta, nan yafara jin wani yanayi ajikinsa daurewa yayi yafara checking dinta anan yasamu yagano matsalar tata yayi mata allurai har guda hudu alokaci guda, kallo yabita dashi dama wannan ai dole tasamu matsala saboda tahadu sosai shiyasa takamu da ciwon mara mai tsanani wanda bazata taba warkewa ba har sai tasadu da namiji, fita yayi yakoma office dinsa sai 3 yashiga round yana shiga yan practical suka fara gulmarsa wannan likitan duk asibitin nan yafi kowa kyau, ai duk misau ma babu mai kyanshi inji wata aciki, yana tafiya yana duba patient har yazo gadon karshe inda yanmatan nan suke, waje yace sufita yafara duba patient dinshi wadda har ta wartsake kallonta yayi doguwa ce baka tanada manyan idanuwa da dogon hanci gata da dan tsukakken karamin baki, gashin girarta mai yawane batada kiba dayawa amma tana hips da cikar kirji sosai, yanmata kin tashi? Ya tambayeta, biron hannunsa ta karba da takarda tayi masa rubutu kamar haka, bana jin abinda kafada ni bebiyace kuma kurma ce, mika masa tayi yakarba ya karanta cikeda mamaki ya rubuta mata, ayya sannu, amma ko kin san ke kyakkyawa ce? Mika mata yayi takarba tagani takaranta tayi masa reply nagode amma Kayi hakuri ni matar wanice, karba yayi yai murmushi nima mijin watane, murmushi tayi wlh inada aure, bai gasgata ta ba saboda yaga tana fama da matsalar ciwon mara sperm yataru dayawa a mararta gashi har ya haifar mata da ciwo shi kuma yasan da ace tanada aure da hakan bazata faruba kallonta yasakeyi waye zai mallaki wannan a matsayin mata yatsaya yazuba mata ido yana kallonta? Kai karyane gaskiya budurwa ce cikakkiya kuma.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Wani tsadadden murmushi tafida yayi mata yace ok koma dai menene bari na rubuta miki maganin dazai taimaka miki, wata yar takarda yadauka ya fara rubutu yana gamawa ya mika mata gashi Allah yabaki lfy, duk wadannan maganganun da yakeyi bata jinshi murmushi yayi mata kinyi min kinyi daidai da tsarina hannunta tadaga tayi mai nuni ma'ana me yake nufi, murmushi ya sakeyi wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana kumatunsa na dama ya lotsa kusan ko magana yakeyi sai yadan lotsa kallonsa tayi taji gabanta yafadi wannan likitan yanada kyau tafada acikin zuciyarta astagfurullah tayi saurin tuba saboda tunowa datayi itafa matar aure ce, fuskarsa ta kalla lokacin da yake yin rubutu ajikin takarda yadan dunkuyar da kansa yanayi yana lasar lebenshi nakasa wanda suke jaja jaja duhu duhu domin tabar wiwin da yakesha tahadu da jan lebensa sai tabada wata irin kala mai kyau kamar yana shafa jan baki gashi farinsa irin mai dan jan nanne kura masa ido tayi kai wannan saurayin yana yimata kama da Seth rollins dan wrestling domin har tsayinsu ma zai zo daya gashi manyan idanuwansa ma irin nasane sak, dagowa yayi yana murmushi yamiko mata takardar yayi mata wani kasalallen murmushi yajuya yafara tafiya ita dai nurse tana tsaye tana kallon ikon Allah domin tunda take acikin asibitin nan bata taba ganin dr tafida yayi irin haka da wata patient ba babu ruwansa da kowa tsakaninsa da kowa gaisuwa ce amma sai gashi yau har dasu bude hakora taf lallai wannan tacika mai nasara.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣7⃣
Na UMMI A'ISHA
Yana juyawa marar lafiyar tafara kallonsa yahadu sosai ta kissima aranta sai da yafita tabude takardar da yabata tafara karantawa kamar haka Yake kyakkyawa agaskiya yau idona ya yi duban da be taba yiba hakika banyi kuskure ba idan nakiraki da suna tauraruwa kigodewa mahaliccinki domin ya tsara halittarki irin tsarin da har yau banga wadda takaiki ba, ina sonki zuciyata takamu da kaunarki alokaci guda,ina taredake aduk inda kike luv u! I. T. Tana gama karanta wasikar kawayenta suka shigo dukkaninsu kowacce tana sanye cikin unifoam nanfa wata daga ciki tafara yimata tambaya da hannu alamar meya ce mata murmushi kawai tayi bata fargaba taji sun fizge takardar hannunta karantawa sukayi take kuma bakin ciki ya mamaye zuciyoyinsu domin agaskiya wannan likitan bai dace da ita ba dasu yadace mutum dayace bataji haushin hakanba asalima murna tayi sukuwa sauran ji sukeyi kamar su shaketa dan haushi. Dr tafida yana fita daga female ward yanufi office dinsa zuciyarsa cikeda tunanin yarinyar da yagani sai dai yana jin tausayinta har cikin ransa domin abin atausaya matane gata budurwa har budurwa kyau iya kyau amma dayake Allah alhakimu ne sai ya iyota kurma kuma bebiya, duk da haka zuciyata tana sonki yanmata ni babu ruwana da jinki ko maganarki ke kawai naji ina so, zama yayi yafara kiran fadawansa minti kadan sai gasu kayansa yace su hada masa zai tafi gida babu bata lokaci suka harhada duk wasu abubuwa nasa suka fita,tashi yayi yacire bakar coat din jikinsa yabar iya tacikin wadda take light green mai dogon hannu da neck tie baki da green, ahannunsa yariko rigar idonsa yana sanye cikin farin glass yana tafe yana daddanna wayarsa.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣8⃣
Na UMMI A'ISHA
Fadawansa na hango shi suka zabura suka zo suka fara take masa baya suna tafe suna zabga kirari, takawarka lafiya, alafiya dai tafidan alheri, gaba salamun baya salamun namijin fama, babban goro sai magogin karfe, karo da karo sai rago, wani Kaya sai amale wane jaki, buhun kaya kake mai daukarka sai wanda ya shirya, kogi ba ayi maka katanga, kaga katangar sukari kowa ya jingina sai ya lasa, sauka lafiya dan ahamadu jikan sani, farin wata sha kallo, lafiya dai mai dogon zamani, gaba salamun baya salamun,shi dai tafida tafiya kawai yakeyi yana yin waya da faisal amininsa kuma dan uwansa har ya isa gun motarsa suka bude masa ya shiga ya zauna, daliban nan duk akan idonsu hakan tafaru har motar tafida tafita daga cikin asibitin, daya daga cikinsu mai suna sakina itace ta tabe baki wai kuga haduwar wannan gayen amma yarasa wacce zai so sai waccan kurmar,bebiya dukansu baki suka tabe wayaga abinda rai keso inbanda haka me zaiyi da ita kuma kunji ma dan gidan sarki ne ashe, daya daga cikinsu ce ta katsesu haba sakina meye amfanin haka? Ina ruwanku dasu, wannan abun da kukeyi babu kyau hassada ce ita kuma hassada Annabi yayi hani da ita domin akwai wani ingantaccen hadisi da manzon Allah s.a.w yake cewa iyyakum wal hasadu, fa innal hasadu ta akulul hasanati kama ya akulul narul hadabe, ma'ana nahaneku da hassada domin ita hassada lallai tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cinye itatuwa ko kuma karare, dan haka wannan abin da kukeyi wlh bashida amfani ko kadan,soyayya ta Allah ce idan kukayi hakuri kuma zaku samu rabonku, tana gama fadin haka tabar wurin takoma cikin female ward, tsaki sakina taja wannan damuwarki ce amma wlh bazai yiyu ace mu masu baki da kunne yakimu yaso kurma ba. Tafida jinsa yake kamar bashiba har yaje gida,shidai bai taba soyayyaba asalima ko budurwa bai taba yiba saboda shi miskili ne nagaske kai kallon mata ma bai dameshi ba, baya hulda da mata ko kadan amma yau yayi gamo, gamo wanda za a iya cewa kyakkyawan gamo.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣9⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikeda farin ciki ya isa gida sai wata walwala yakeyi marar kan gado domin babu wadda ya saba ganinshi cikin wannan yanayin su kansu fadawansa mamaki sukeyi yadda yau yake cikin nishadi da walwala, suna isa tangamemen gidansu yafito daga cikin mota fadawan dasuke tsaron kofar suka mimmike tsaye suka fara gyara kintsi gaba salamun baya salamun barka da shigowa tafidan zamani tafida ba akawo maka wargi, takawarka lafiya dan toron giwa, dan zaki kafi karfin rainon kura, ko kura ta mutu tafi karfin kare yaja gawarta, namijin dawa kake mai kayan alfarma, barka da shigowa zaki dangin sikari, tsawo dangin rama, takawarka lafiya gaba salamun baya salamun, cikeda jin dadi tafida yadaga musu hannu kamar yadda yasaba yanufi zauren dazai sadashi da lungun mai martaba yana zuwa kansa tsaye yawuce cikin dakin mai martaba yasameshi zaune yana kallon labarai atashar CNN zubewa yayi yafara diban gaisuwa, sannan yatashi yafita yanufi wurin inno itama a falonta ya taradda ita tana kishingide jikin tumtum ga bayi zagaye da ita sunayi mata firfita ka kayan motsa baki a gabanta shiga yayi yazauna a kan kujera bayinta suka tashi suka fiffita anan ya zamo kasa ya gaida ta yatashi yafita yau gaba daya jinsa yake kamar wani sabon mutum dan tsabar nishadi, yana isa dakinsu yashiga toilet yayi wanka yafito yasaka kayan yan kwallo jar riga mai number 1 ajikin rigar da wando dogo,adaki yayi salla yana idarwa yafito yanufi wurin dawakansa yasamu har an daura masa sirdi domin fita kilisa shi kadai kawai ake jira baiyi wata wata ba ya haye dokin shima sarkin fada yahau nasa da alama yau su biyu zasu fita kilisar, tafe suke ahankali kowannensu rikeda linzamin dokinsa har suka isa wasu manyan gonaki, tafida ne yayi yar magana ahankali kamar yadda yasaba, sarkin fada wannan gonar idan baka mantaba nataba fada muku zatayi daidai da tsarin danakeso wurin gina business suit dina, Allah ya taimakeka tafida sarkin fada ya fada,amma yallabai wani hanzari ba gudu ba wannan gonar itama ta sirikinka kace idan ban mantaba, yatsina fuska tafida yayi koma tawaye a cikin satin nan za afara yimin aiki, Allah yaja kwana,Allah yasa kafi haka, sarkin fada yafada amma acikin zuciyarsa cewa yake wannan wanne irin mutum ne ace duk gonakin sirikinka sai bi kakeyi kana karbewa kana gini marassa dalili.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣0⃣
Na UMMI A'ISHA
Haka suka karaci shawaginsu suka koma gida lokacin magriba tana daf da kawo jiki, suna isa gida tafida yasauka daga dokinsa a gajiye ya shige gida afalonsu ya zube akan carpet ya kwanta gaba daya ya gama gajiya, jinsa yake kamar yayi wani gagarumin aiki, fuskar wannan yarinyar ya hango take yayi wani murmushi insha Allahu sai na auri wannan yarinyar yafada azuciyarsa domin kyakkyawa ce ajin karshe, amma mamakinsa shine yadda take karatun science alhalin kuma bata ji kuma bata magana hakika ta cika yar baiwa gashi komai nata mai kyaune tamkar ita tayi kanta saboda yadda halittar ta tatsaru sosai, lumshe manyan idanuwansa yayi oh ko meye sunanta? Tsabar yarude yamanta bai tambayi sunanta ba shigowar faisal cikin falon ne yasashi dago kansa yakalleshi abokina daga ina? Zama faisal yayi daga dambam nake kasan garin nawa kullum basa rabo da rikicin manoma da makiyaya, murmushi tafida yayi uhm dakyau hakimi, dariya faisal yayi kaima dai dadinta hakimin ne, murmushi tafida yayi masa wadda har saida faisal yayi masa magana yau naga kana ta fara'a kodai? Murmushi tafida yayi babu abinda yafaru amma nazo maka da albishir nasamo matar aure dariya faisal yafara yi bakada seti tafida yaushe kayi aure da har zaka fara neman wani? Tsaki tafida yayi kaga babu ruwanka malam ni namanta ma wlh da wani auren da mai martaba yayi min, kallonsa faisal yayi to wlh kafadawa yarinya gaskiya tunda wuri ka sanar da ita gaskiyar lamari kai bazawari ne ba saurayi ba dan kanada mata yakarasa maganar cikeda dariyar mugunta,shiru tafida yayi masa bai bashi amsaba amma yatsani faisal[truncated by WhatsApp]
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣1⃣
Kallon faisal yayi malam banida lokacinka yanzu yana gama fadin haka ya mike yanufi lungun inno zuciyarsa fes domin yana cikeda farin ciki a wannan rana. Daren ranar bacci kadan yayi domin alla alla yake gari ya waye yaje yaga wannan yarinyar, asuba tana yi yatashi yafita masallaci yayi salla yana dawowa ya dauko alqur'aninsa ya buda yafara karantawa har karfe 6 tayi sannan yaje yayi wanka yafito ya shirya cikin suit ash colour hatta takalmin kafarsa ash colour ne yadaura agogon Gucci na azurfa duk wannan budurin da yakeyi faisal yana kwance yana kallonsa sai da yagama shiryawa tsaf faisal yace gaskiya kayi kyau mitumina wlh babu wanda zai ganka yace kai ba saurayi bane kamar ba kayi aure ba, tsaki tafida yayi Allah yasa kaima asatin nan dai ayi maka auren inyaso muga ta tsiya, dariya faisal yayi gaskiya kam gara mai martaba ya taimaka min yayi min aure tunda gashi har Kanina zaiyi mata 2 ina zaune niko daya banyi ba dariya tafida yayi yajuya yafita bai ce komai ba yana fita yashiga gurin inno ya gaidata yafito yaje wurin mai martaba shima ya gaidashi sannan yayi haramar tafiya office lolacin karfe 8 saura minti 20. Yana zuwa office yazauna akan table dinsa yadauki yar farar takarda yayi rubutu yasa agaban rigarsa yafito yanufi female ward, yana shiga nurses suka fara gaisheshi morning sir! Morning kawai yake cewa yawuce, da haka har yaje last bed inda budurwar nan take, kallon kyakkyawar fuskarta yayi yai mata murmushi ita dinma shi take kalllo wata farar takarda ya miko mata takarba yana bata yajuya yafita dama abinda yakawo shi kenan, theatre ya hara dan yanada aiki acan, yana fita ta bude takardar tafara karantawa rubutunsa kyau kadai kamar wadda aka buga ajikin computer, sakon nasa takaranta kamar haka "some people hv a nice smile, some hv a nice eyes,and some hv a nice faces, you u hv all of them & nice heart Good morning & hv a nice day! I. T, tana gama karantawa sai kuma tasoma hawaye wanda nikaina ummi Aisha ban san ko na menene ba.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Kuka take sosai wannan wanne irin abune da aurenta ta rinka son wani mutum nadaban, istigfari tafara yi ba kakkautawa acikin yanayin kawarta zara'u sulaiman tazo ta sameta zama tayi gefen gadon tafara tambayarta da hannu meyafaru? Dakyar tadauki biro zara'u yau zan bar asibitin nan dama kin san acikin satin nan zan gama practical dina gida zan koma idan kingama naki ma hadu a sch dariya zara'u tayi to kijirani zanje nadawo tana gama rubuta mata ta tashi tafita, hawayenta tagoge tadauki takardar taboyeta acikin rigarta, tana nan zaune aka kawo wata mata marar lafiya agadon kusa da ita aka kwantar ta Jim kadan sai ga likitanta yazo wato dr tafida idonsa akanta yaje yagama duba matar nan yabata dukkan taimakon daya kamata sannan yadawo inda take, da ido yayi mata alama wai meya sameta idonta yayi ja, murmushi tayi takada hannu alamar babu komai takarda yadauka yarubuta mata meye sunanki? Da babban baki tabashi amsa sunana HANFA yana karantawa yayi murmushi meye ma'anar hanfa? Dan ni ban taba jin wannan sunan ba, murmushi tayi yakamata ka rinka bibiyar tarihi amma nabaka assignment go and find out d meaning of hanfa murmushi yayi yace zan kuwa baki mamaki domin zan samo miki ayau basai gobe ba yana gama rubutawa yabata yafita daga masu jinyar har nurses din kallonsu suke tayi to kodai sun san juna wannan abin mamaki ya isa domin ada ibrahim tafida (I.t) baya tsayawa yayi magana da patient amma gashi yau yatsaya yanata rubuce rubuce da kurma gulma nurses din suka fara yi agefe daya duk dai sun san ita wannan marar lafiyar yar practical ta hadu ta cancanci hakan.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Agurguje yagama abinda yakeyi ya koma gida abinda bai saba yiba tashi karfe biyu amma yau yayi saboda yana so yasamu damar binciko ma'anar sunan hanfa, yana zuwa gida yasamu sirikinsa yana fitowa daga fada ko kallonsa bayi ba balle yasa ran zai gaisheshi tafiyarsa yayi cikeda takama fadawa suna biye dashi suna takawarka lafiya dan toron giwa gaba salamun baya salamun dahaka yashige gida dakinsu yaje yabaje ya jawo laptop dinsa yafara searching din hanfa sai da yadade yana nema sannan ya samo cikeda farin ciki yatashi yaje dakin inno bata cikin dakin dan haka kan gadonta ya haye yayi dai dai yana tunanin hanfa ba shakka sunanta ya dace da ita kuma ya cancanceta ganin inno bata shigoba yasashi mikewa zai fita daga dakin sai gata kuma ta shigo,a'a tafida dama kana nanne? Kai yadaga mata ina nan inno ai tun dazu nadawo amma sake fita zanyi, to amma dai sai kaci abinci ko? Murmushi yadanyi to inno abani kadan naci dakanta tafita ta hado masa abinci takawo masa harda kayan marmari agefe zama yayi yadanci abincin kadan yatashi yafita yakoma dakinsu yayi wanka yafito yashirya tsaf cikin blue colour din jeans da riga dark brown mai gajeren hannu yana fitowa yahadu da faisal ya yau da wuri zaka fita kilisar ne abokina? Faisal ya tambaye shi, no zanje asibiti ne amma bazan wani jimaba zan dawo, ok sai kadawo faisal yafada yawuce ciki shi kuma tafida ya fita, yana zuwa su sarkin fada suka bude masa kofar mota ya shiga ya zauna sai asibitin kwararru na rasheed shekoni wanda yake da xango acikin garin misau.
[4:08PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Suna isa asibitin ya nufi female ward yashiga nurses din dake ciki sai fadi suke welcome sir! Last bed ya hanga amma babu kowa cikin rudewa ya tambayi daya daga cikin nurses din ina patient din dake last bed? Ahankali tace dr dazu tatafi, ahargitse ya kalleta are you mad? Danme zaku barta tatafi ban sallameta ba, meye amfaninku agurin? Wannan ya nuna min cewar baku san aikinku ba, sai kun karbi query saboda sam bakuda hankali hakuri suka soma bashi we are sorry sir! Ko kulasu bai yiba yafice daga cikin ward din, to shi yanzu ina yanufa? Tunda bai san inda yarinyar nan takeba sa'arsa daya yasan sunanta, fita yayi yashiga motarsa fadawansa suka rufa masa baya, ransa abace yake yau sanadiyar rashin ganin hanfa da wannan bacin rai suka karasa gida yana zuwa dakinsu ya fada akan gado ji yake kawai kamar ya fashe da kuka, tabar wiwi ya janyo ya kunna ya fara zuka nan fa ya turnuke dakin da hayaki kamar salansar babur, faisal dake kwance kusa dashi yana bacci ya bude ido yafara kallonsa dan ganye ka fara zuke zuken naka ne? Shiru tafida yayi masa domin bacin ran dayake ciki baxai barshi ya iya yin magana ba tabarsa yaci gaba da busawa batare da yace komai ba tuni idonsa ya kada yayi jajawur kamar jini ganin abin bana kare bane yasa faisal kwace sauran wiwin ya boye yana cewa kai meyasa wani lokacin baka da saiti ne? Sai kaje kajawa kanka wata cutar, kana likita amma baka san abinda zai illataka ba, dakyar tafida ya iya bude baki yace

Please Login or Register in order to submit comment