Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faisal ban ganta ba, wacece? Faisal ya tambayeshi yarinyar da nace maka nahadu da ita a asibiti, to kuma shine zakazo kayita shan wiwi? Ai kamata yayi katsaya ka nutsu ka binciko inda take amma baka zauna kayita bunkawa cikinka hayaki ba lumshe idanuwansa tafida yayi yace nagode abokina insha Allah zan kokarta kwanciya yayi yafara hango kyakkyawar fuskar hanfa, Allah sarki kowa da yadda Allah yake jarrabarsa ita kuma haka Allah ya halittota kurma sannan kuma bebiya amma ya tsara halittarta yadda bazai kwatantu ba, dan tsaki yaja ni ba muryarta nakeso ba kuma ba jin maganarta nakeso ba ita kanta nake so kuma insha Allahu sai na mallaketa.
[5:09PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Zama jugum tafida yayi yana ta sake sake acikin ransa gamida tunanin yadda zai nemo sahibarsa hanfa daren ranar bashida wata walwala har gari ya waye, shiryawa yayi yadda yasaba cikin suit bakake yasa bakin takalmi yasa glass dinsa fari dan siriri yafito agurguje ya leka wurin mai martaba yafito yashiga wurin inno yana fitowa yanufi asibiti koda yaje tuni har ma'aikata sun firfito manyansu da kananansu, gakuma yan attachment suma duk sun fito, yana zuwa yawuce office dinsa yafito yashiga maternity jim kadan yafito yashiga female ward nanma bai fi minti biyar ba yafito yana fitowa yashiga antenatal,yana fitowa yadaga yan yatsunsa guda biyu yashiga office take dogarawansa suka furtsa aguje suka nufi office dinsa nanfa yan practical suka fara kace nace wato wannan daga yatsun dayayi ashe fadawansa yayiwa magana lalle sarauta sai me ita,basu farga ba sai ga wani bafade guda daya yazo inda suke yayi musu sallama yace wacece zara'u acikinku? Gani zara'u ta amsa, to kizo mai girma tafida yana son ganinki, hanzarta yanmata, tafida ikon Allah tafida mai jan doki, dasauri zara'u ta tashi tanufi office din dr tafida yayinda dogari yake biye da ita yana fadin takawarki lafiya yanmata, gyara kintsi bakuwar tafida alafiya dai gaba salamun baya salamun, ita dai zara'u gaba daya atsorace take domin bata san me zai biyo baya ba, yayinda kawayensu suna can suna ta gulmarta ita da hanfa to ko yanzu zara'u zai ce yana so? Inji wata acikinsu kudai jira muga dawowarta tukunna sakina tafada, zara'u suna zuwa office din tafida bafade yabude mata tashiga abinka ga jinin sarauta akishingide ta sameshi yana jiran zuwanta tana shiga yayi gyaran murya take fadawan sukayi waje suka ja musu kofa.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [6:39PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Fadawansa na fita ya kalli zara'u yana daga kishingide yace hv a seat zarah, babu musu ta zauna akan kujerar dake nesa dashi, kallonta yayi ina hanfa take? Hanfa tatafi gida, a ina gidan yake? Ya tambayeta, acan disina gidansu yake, dagaske ne ita kurma ce? Daga Kai zara'u tayi tace dagaske kurma ce sannan kuma bebiyace, murmushi yayi wanda yasake bayyanar da zahirin kyansa afili to yanzu ki taimaka min kibani address dinta zanje gidansu na sameta amma kuma naji tace min wai ita matar aurece hakane? Girgiza kai Zara'u tayi wlh bani da masaniyar hakan amma nima tabbas ta taba fada min cewar ita matar aurece amma ban yarda ba gaskiya, murmushi yayi hakane metake karanta a makarantar? Lab science take karanta, a school of nursing & midwifery dake cikin garin nan amma asalinsu yan garin disina ne, ok to ke tun wanne lokaci kika santa? Sanina da ita baifi shekara daya ba lokacin da muka shiga makarantar nanne kuma tunda muka fara kawance da ita har yau babu abinda ta taba yi min na bacin rai har gidansu naje itama taxo namu gidan, ok good yanzu ki rubuto min address din ki kawo min nagode amma zan kara nemanki idan bukatar hakan ta taso,daga kai zara'u tayi babu komai tashi tayi zata tafi murmushi tafida yayi nagode zarah amma agaskiya ina son kawarki sosai kuma zan aureta, murmushi zara'u tayi tace Allah ya tabbatar da alheri amin tafada tareda ficewa daga office din.
[6:56PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣7⃣
Na UMMI A'ISHA
Zara'u tana fita tafida yayi kishingide yazama tilas agareshi gobe yaje disina yabinciko gidansu hanfa, tashi yayi yafito daga office dinsa yanufi motarsa nan da nan su sarkin fada suka tattaso suka fara bin bayansu daidai lokacin zara'u tazo tamikawa tafida address din gidansu hanfa ko dubawa bai yiba yasaka takardar acikin aljihunsa ya wuce yana cewa thank u, ita kuwa zara'u tana komawa wurinsu sakina sakina tayi farat tace wai zarah me wannan gayen yake so awurinki ne? Dariya zara'u tayi address din budurwarsa ya nema kuma nabishi, dakyau sakina tafada cikeda bacin rai. Tafida yana zuwa gida yayi dukkan abubuwan da yasaba yi yafita kilisa yau kilisar tasu daga shi sai faisal, suna tafe ahankali akan dawakansu tafida yace abokina gobe zanje disina, me zakayi a disina? Akwai abinda zai kaini, ok to ko gidansu matar taka zakaje? Eh can zanje tafida yafada ahasale, dariya faisal yayi Allah yabaka hakuri abokina abin bana fada bane daga tambaya? Eh daga tambayar tafida yafada yana harararsa kasan Allah tafida? Ka nemi matarka ku sasanta tun wuri, tsaki tafida yayi haba faisal wayace adaura min auren da banine na bukata ba, wlh babu wani sasanci da za ayi ni yanzu ma aure zanyi wanda duniya zata san nayi aure amma wanccan auren ai na mai martaba ne murmushi faisal yayi to kuwa sai Allah ya tambayeka domin nauyin yarinya yana kanka tun daga ciyarwarta da shayarwata ga uwa uba hakkinta na aure tunda ita macece mace kuwa kasan tanada rauni, kuma duk duniyar nan kai kadaine zaka iya yi mata wannan domin babu wanda zai bata sai kai, uwar me zan bata? Tafida ya tambayeshi kafini sanin abinda zaka bata to ai kuwa sai dai ta mutu wlh dan banida lokacinta, dariya faisal yayi yace Allah ya shiryeka abokina, da haka suka juya suka koma gida.
[7:18PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣8⃣
Na UMMI A'ISHA
Suna komawa gida tafida yashiga dakinsu ya zauna yafara bincike acikin laptop dinsa wanda ni kaina ummi A'isha ban san me yake nema ba sai da ya dauki tsawon lokaci sannan yarufe laptop din nasa yanufi masallaci yana dawowa yadora daga inda ya tsaya yaci gaba da bincikensa har faisal yazo ya sameshi yafara yimasa hira amma shi tafida sama sama yake jinsa duk hankalinsa ya tattara akan binciken da yakeyi. Washe gari da misalin karfe 11 nasafe tafida yayi shirinsa tsaf cikin wani tsadadden boyel fari yasa hula yasha turaren fogg ya daura agogon azurfa kirar kamfanin omega yasa farin takalmi cover shoe yafito yayiwa mai martaba da inno sallama cewar yatafi disina duk babu wanda yasan abinda yatafi yi sai faisal amma su mai martaba basu tambayeshi me yatafi yiba kasancewar sun san garinsa ne shine yake mulkar garin, wata jibgegiyar jeep yashiga wadda akalla zata iya daukar mutum goma ita yashiga yazauna agidan baya sarkin fada yashiga gaba yazauna yayinda sarkin mota shikuma yazauna a mazaunin driver yaja suka tafi, tafiya sukayi ba mai nisa dayawa ba suka karasa garin disina, address din da zarah ta basu sarkin fada yarinka bi har suka isa wata unguwa mai suna gangare, anan sarkin fada ya tambayi wani yaro ko inane gidan su hanfa? Wancan mai koren fentin ne yaron ya nuna musu shidai tafida yana zaune abaya kishingide ajikin kujera yana latsa wayar hannunsa, adaidai kofar gidan sarkin mota yayi packing din motar yafito shima sarkin fada fitowar yayi ya isa bakin kofar gidan yafara kwada sallama sai da yayi sau wurin biyar sannan wani yaro yafito, yana amsa sallamar, yaro nanne gidansu hanfa? Eh nanne,tana ciki? Eh tana nan to kaje kace ana sallama da ita, to yaron yafada tareda juyawa cikin gidan da gudu, Jim kadan kuma sai gashi yadawo wai ance inji wa? Kace inji tafida, dagudu yaron ya sake komawa can sai ga wani mutum yafito daga cikin gidan waye yake nemanta? Mutumin yafada cikin fada, daidai lokacin tafida yafito daga cikin mota wazai gani? Sirikinsa yagani mahaifin matar da mai martaba ya aura masa.
[7:50PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣9⃣
Na UMMI A'ISHA
Bata fuska tafida yayi yasauko dakyau ya tsaya yana kallonsa dama shima sirikin nasa kallonsa yake, cikin murtukewar fuska mutumin yace, lfy kuka zo min gida? Cikeda isa tafida ya kalleshi amma baiyi magana ba sarkin mota ne yace barka da safiya dama yallabai ne yazo gurin yarinyar gurinka hanfa, wata harara mutumin yayi musu sai yanzu yasan da ita? Da lokacin da aka daura auren ya nemi inda take balle ace ya ganta, tunda aka daura auren nan bai san cinta ba bai san Shanta ba bai san sutturarta ba uwa uba bai san lafiyarta ya takeba dan haka nidai nayi dana sanin aura maka yata kuma nayi bakin cikin auran yata da kayi domin kai ba mutumin arziki bane bakada wata kama ta mutanen kirki,dan haka ina mai shawartarka da kadauki sahunka a likkafa tun dare baiyi maka ba kabar kofar gidana sannan kuma yazama tilas, dole ka saki yata domin bazan hada zuri'a da mutumin banza ba irinka dama na aura maka yatane dan mutuncin mahaifinka to yanzu nafasa, yana gama fadin haka yakoma cikin gida tareda doko kofar gidan da karfi, sai asannan tafida ya iya motsawa daga mutuwar tsayen da yayi dama hanfa itace matar da mai martaba ya aura masa? Wata zuface ta fara karyo masa kamar an kwara masa ruwa ga kafarsa tayi wani irin nauyi marar misaltuwa, ahankali ya zare gilashin dake idonsa yafara tafiya ahankali tamkar kazar da kwai yafashewa aciki, batare da tsoro ba yatura kyauren kofar ya shiga gidane na talakawa babu yabo babu fallasa komai na cikin gidan irin na talakawa ne,yana shiga ya fara sallama tamkar mai yin rada, zuruf masu gidan suka fito daga daki baban matarsa ne yataso cikin fada, waye yayi maka izinin shigowa cikin gidana? Kai kafita daga idona yanuna shi da yatsa nadade da sanin kai marar kunya ne kuma bakasan mutuncin nagaba da kai ba, kafitar min daga cikin gida tun kafin nayi maka kamun kazar kuku, cikin rawar murya tafida yace baba zan fita amma sai ka bani matata, kar ka kuskura kasake kirana da baba domin baka daukeni uba ba kuma nima duk cikin yayana babu mai wulakanta mutane wanda bai san darajar mutane ba, kayi hakuri baba amma dan Allah kabani matata tafida yafada tamkar zai fashe da kuka, wai wacce matar yake fada? Wata mata ta tambaya cikin fada, wannan akwai marar kirkin yaro, sai yanzu kasan da matar taka, yau auren naka yafi wata 6 ko sau daya baka zo kaganta ba saboda kana gadarar kuna da sarauta? Kai gaka dan gata to mu bamu da sarauta amma Allah shine gatanmu, nuna masa hanya baban hanfa yayi fice min daga cikin gida marar kunyar banza marar kunyar wofi, cikeda rashin karfin jiki tafida yajuya yafita yayinda mahaifin hanfa yabiyoshi yayi masa korar kare, dakyar tafida yashiga mota yacewa su sarkin fada sushiga su koma misau take suka bi umarninsa.
[8:28PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣0⃣
Na UMMI A'ISHA
Gudu sosai sarkin mota yayi amma tafida gani yake kamar ba tafiya sukeyi ba alla alla yake yaga sun isa garin misau, wani jiri yaji yana daukarsa wannan abin al'ajabi da yawa yake, tun farko dayasan wannan kurmar ce matarsa ai da ya amince, to ai sai da mai martaba yabaka hotonta amma kaki gani, shiyasa aka ce komai idan aka bishi a sannu yafi armashi zuciyarsa tafada masa, gefen kansa yaji ya sara kamar wanda zai tsage gida biyu, da sauri yasa hannunsa ya rike, sai yanzu yasan wulakanci bashida rana gashi yanzu yanaji yana gani yataho yabar hanfa batare da yaganta ba, amma da ace alheri yayiwa mahaifinta tun farko da bazai yi masa wannan cin mutuncin ba domin shi ALHERI DANKO NE! Baya faduwa akasa banza ko baka samu alokacin ba to agaba zaka dauki abinka watikil ma harda riba, wayarshi yadauka yafara kiran number faisal bugu biyu faisal yadaga abokina ya? Kana ina faisal? Ni gani a office kaifa kadawo daga disinan ne? A'a nakusa zuwa dai yanzu gamu acikin azare dan Allah kadawo gida nafi son da nazo nataradda kai agida pls abokina, ok dama nima nagama aikin da nakeyi yanzu zan koma gida, Allah yadawo daku lfy amin faisal, tafida yafada yakashe wayar, kansa yadafe yana ji kamar zai bar jikin wuyansa dakyar ya iya mikewa ya kwanta akan kujerar da yake, gudu sarkin mota yakara dan danan sai gasu acikin disina, suna isa gida tafida yatashi yafito anan yabar gilashinsa da wayoyinsa, sai sarkin fada ne ya dauko masa, yana shiga dakinsu yasamu faisal zaune yana waya kusa dashi yazauna faisal yagama wayar ya jiyo gareshi yace abokina kadawo? Kai tafida yadaga yace nadawo sai dai yau nayi dana sanin aikata kuskure da sharri arayuwata faisal hakika nayi kuskuren aikata sharri hakika faisal sharri jakada ne maishi yake dawowa yayinda shikuma ALHERI DANKO NE bazai taba faduwa abanza ba, kallonsa faisal yayi wai meya farune? Cikin damuwa tafida yace faisal yarinyar da nake baka labari ashe itace matar da mai martaba ya aura min sai yanzu da naje gidansu na tabbatar da hakan, dariya faisal yafara har da saukowa kasa daga kan kujera nan ran tafida yakara baci sai hawaye sharr! Cikin sauri faisal ya daina dariyar yace haba abokina be a man mana, ya zaka rinka kuka kamar mace, faisal ina sonta nd i can't do with out her! Hannunsa faisal yarike yace maza tashi muje wurin mai martaba mu rokeshi yabaka matarka, tashi tafida yayi yabi bayan faisal har suka isa fada kuma fadar acike take makil da alama sarki yana ganawa da yayun su tafidan ne, turakin soro shine yayi musu iso wurin mai martaba, a kasalance suka isa cikin fadar nan suka matsa gaban mai martaba suka yi gaisuwa caraf fadawa suka cafke,sarki ya gaisheku samarin alheri, sarki ya amsa gaisuwarku mazajen fama, tafiya dai sannu sannu kwana nesa.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:52AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣1⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikin fargaba faisal yace ranka yadade akwai abinda yake tafe damu, gyaran murya mai martaba yayi nan da nan fadawansa suka fice daga cikin fadar sai iya su chiroma da galadima da sa'i kawai aka bari awurin,cike da jin nauyi faisal yace ranka ya dade dama tafida ne yace yatuba yanzu yagane abinda yayi bai kyauta ba shine muka zo mu nemi afuwarka ayi hakuri abashi matarsa, cikin fada sarki yace kai! Idan ku shashasu ne to ni ba shasha bane, dama wannan ce maganar da ta kawo ku? Maza kutashi kubar wurin nan tun kafin raina ya baci, hakuri faisal yafara bayarwa yayinda shikuma faisal yakasa furta koda kalma daya in banda fararen idanuwansa da suka rine sukayi jajawur, cikeda fushi galadima yace kai! Akace kutashi ku bawa mutane wuri marassa kunyar banza, tashi faisal yayi yaja hannun tafida suka fice daga cikin fada, suka tafi wurin inno, afalo suka tarar da ita tana zaune kuyanginta zagaye da ita, rai abace tafida ya zauna kallonsu tayi ya akayi naganku duk kunyi wani iri, inno bukata ce take tafe damu inji faisal, kuyangunta ne suka tashi suka fita,meya faru? Inno ta tambaye su, inno daga wurin mai martaba muke dan Allah kisa baki adawowa da tafida matarsa ai abinda ya wuce ya riga ya wuce, au dama wannan ce ta kawoku? To maza ku tashi kubar min dakina kuma kar ku kara tunkarata da wannan maganar kunji dai na fada muku marassa kunya kawai, tana gama fadin haka ta mike tashige dakinta nanfa tafida yaji kansa ya sara, jan hannunsa faisal yayi taso muje wurin momcy bai yi musu ba yabi bayansa har fannin momcy, suna shiga lokacin tana kokarin fitowa ganinsu yasa takoma ciki suka bi bayanta, tafida me yafaru? Ta tambayesu faisal ne ya iya yi mata bayanin abinda ya faru nan tafara kwantarwa da tafida hankali, kar kadamu tafida insha Allahu komai zai zo da sauki kaji, kayi hakuri zanje nasamu mai martaba saboda dama yanzun nan wurinsa zanje jakadiya tace min yafito daga fada, kujirani naje nadawo yanzu, tashi tayi tafita zuwa sashen mai martaba.
[9:53AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Koda momcy taje wurin mai martaba hakuri tafara bashi akan maganar tafida ai kuwa nan mai martaba ya rufeta da fada baji ba gani, cikin fuskar alhini momcy tace to ranka yadade ni kayi min izini gobe sai naje disinan da kaina nataho masa da matarsa, hajiya mabruka muddin kikaje to wlh bada yawuna ba kuma babu hannuna aciki,aure dai ai nine nayi masa ko? To babu ruwanku aciki ku zuba min ido kawai, tashi momcy tayi tana fadin Allah yahuci zuciyar ka ranka yadade amma mai martaba sai fada yake ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, tashi momcy tayi ta koma sashenta tana shiga tasamu su faisal suna zaman jiranta, cikin damuwa tafara magana, nayi duk iya kokarina amma mai martaba bai saurareni ba asalima cewa yayi idan naje disina to bada yawunsa ba, amma abinda nake so dakai tafida shine kayi hakuri mujira muga nan da gobe ko Allah zai sa ya sauko, kai kawai tafida ya iya dagawa yamike faisal yabishi suka fita, suna zuwa dakinsu tafida ya zube akan gadonsu yafara fitar da numfashi mai zafin gaske shikuma faisal ya zauna yafara bashi baki, wunin ranar nan tafida yayi shine kawai amma acikin bacin rai yake shi kansa a matsayinshi na likita yasan bp dinsa yahau sosai ba kadan ba dan yaji alamun hakan ajikinsa, gashi ko ruwa bai sha ba bare yaci abinci har dare yayi. Wurin misalin karfe 10 nadare tafida ya kalli faisal yace abokina dan Allah kayi min wani taimako, ina jinka fadi injishi, so nake gobe katafi disina gidansu hanfa kasamu mahaifinta kuyi magana ta fahinta kaji ko ahaka aka haifeta da lalurar kurmanci da bebanci, idan ba haka aka haifeta ka dauketa ka kaita asibitin tafawa balewa teaching hospital akwai likitan kurame acan kuma insha Allahu akwai taimakon da zai bata, cikeda tausayawa faisal yace dama kurma ce? Kai yadaga wlh faisal kurma ce kuma bebiya bataji kuma bata magana amma tahadu fiyeda yadda baka zato gata da hazaka domin ahakan take karantar nursing, girgiza kai faisal yayi Allah sarki Allah yabata lfy ya daidaita tsakaninku, amin faisal sa'ar danayi ma da ban saketa ba tun da farko da matsalar da zan shiga sai tafi haka, kayi hakuri dai tafida ka kwantar da hankalinka tunda kasan illar saka damuwa acikin zuciya daga kai tafida yayi yashiga duniyar tunani har faisal yayi bacci amma shi faisal yadda yaga rana haka yaga dare ga wani azababben ciwo da kansa yake yi masa dakyar yatashi ya dauko brief case dinsa ya bude yadauki abin auna jini yafara auna jininsa nan yaga yahau fiyeda zatonsa ahankali ya mayar yakoma ya kwanta, alla alla yake gari ya waye dan faisal ya tafi disina.
[9:54AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Wayewar garin ranar faisal yashirya ya tafi disina alokacin tafida ko tashi zaune baya iya yi, lokacin da faisal yaje gidansu hanfa tarbar arziki mahaifanta sukayi masa, bayan sun gaisa yace baba dama zuwa nayi naji ko dama hanfa haka aka haifeta da wannan lalurar? Cikeda alhini mahaifinta yace wlh faisal da bakinta da kunnenta muka haifeta har ta girma ta xama budurwa, haduwarta da lalurar shekaru uku baya ne da suka wuce tayi wata rashin lafiya mai tsanani tun daga lokacin tadaina magana tadaina ji, amma da lafiyarta lau yakarashe maganar yana kwalla, ayya Allah ya rufa asiri faisal yafada yanzu tana ina? Tana ciki, dama ina sone zan kaita asibiti likita zai dubata, cikeda farin ciki mahaifinta yace Allah saka da alkhair madallah madalla nagode, tashi yayi ya shiga ciki bai jima ba sai gasu sun fito tare da ita kallonta faisal yayi agaskiya kyakkyawa ce sosai shiyasa tafida ya rikice da hannu suka gaisa ya bude mata mota tashiga yayiwa mahaifinta sallama suka tafi, suna zuwa asibitin faisal yafita yaje yabude mata polder aka nuna masa inda zai ga likita sannan yakoma yataho da hanfa suna zuwa tabi layi tazauna wurin ganin likita basu fi su biyar ba, tana nan zaune har layi yazo kanta suka shiga tare faisal, likitan da zai dubata bature ne nan yafara bincikarta yana wasu yan rubuce rubuce, tare da dauko wani zungureren almakashi yadauki audugu yatura a kunnen yafito dashi nan yacewa faisal gado zasu bata, za ayi mata aiki zasu biya kudi dubu dari bakwai da hamsin tashi faisal yayi yafita yaje banki ya ciro kudin yazo ya biya jifa jifa tafida yana kiranshi awaya yana tambayarshi halin da ake ciki, bayan ya gama biyan kudin ne yatafi gidansu hanfa ya sanar musu abinda zai gudana nan da nan mahaifiyarta tahada kaya suka nufi asibiti sai da faisal yagama yi musu komai sannan yayi sallama dasu yakoma misau sai yamma lis ya isa gida yana zuwa yasamu tafida kwance adakinsu ga ledar ruwa nan ana kara masa ashe duk wannan wayar da yake yimasa karfin hali kawai yakeyi shima yana kwance, sannu tafida yau likita ne dakansa ake kara masa ruwa? Murmushi tafida yayi faisal ya kukayi da hanfa? Cikin fara'a faisal yace an bata gado aiki zasuyi mata nan da kwana 3 fatan dai Allah yasa adace amin faisal nagode Allah yabar zumunci, haba tafida duk abinda nayi maka ai kaina nayiwa Allah yabaku lafiya, tashi yayi yafita saboda tsabar tausayin dan uwansa da ya shigeshi.
[9:54AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Acikin kwanakin kullum sai faisal yaje garin disina yayinda shikuma tafida yana nan akwance yana jinya jininsa ne yahau over gashi tunda yake bai taba yin hawan jini ba sai a wannan lokacin, ranar da za ayiwa hanfa aikin aranar faisal yatafi da sassafe dama duk abinda suke bukata shi yake kai musu, yana zuwa asibitin ya samu za ashiga da ita dakin da za ayi mata aikin ga iyayenta agefe ko wannensu zuciyoyinsu babu dadi haka shima faisal yatsaya suna nan tsaye har tsawon awa 2 sannan aka fito da ita kai daga ganinta kasan tawahala mutuka wani daki aka zarce da ita amma da alama ba ayi nasara ba, sai bakar wuya da tasha domin sai da aka fara yimata fanfo sannan aka yimata wankin kunne kai wuya dai kala kala tashata amma bata samu lafiya ba domin sauki daga Allah yake nan mamanta tafashe da kuka shi kansa faisal ji yake kamar yayi kukan domin bai san halinda tafida zai shiga ba idan yaji cewa bata warke ba, tashi yayi yashiga office din likitan dan neman karin bayani anan likitan yake sanar dashi cewa sunyi iya bakin kokarinsu amma ba adace ba kuma amma kunnenta lafiya lau yake dan haka agobe ma zasu iya tafiya gida godiya faisal yayi masa yafito yazo yasamu iyayenta yayi musu bayanin abinda likita yace, babu komai Allah yasa haka shine yafi alheri mahaifin hanfa yafada alokacin faisal yayi musu sallama yakama hanyar misau yana zuwa ya tarar da tafida yana jiransa nan ya zauna yafada masa dukkan abinda ya wakana, cikin damuwa tafida yace babu komai ni dama ita nakeso ba wani abu nata ba amma yanzu abinda nakeso dakai faisal dan Allah kaciri kudi gobe kaje kasiya musu gida mai kyau ka zuba musu furnitures kasiya musu kayan abinci domin babu amfanin ni ina zaune awuri mai kyau ina cin mai kyau amma matata tana cikin kuncin rayuwa kai faisal yadaga hakane Allah yakaimu goben. Acikin kankanin lokaci faisal yaje garin disina yasiyawa su hanfa hadadden gida mai kyau wanda yadace da zamani yazuba musu furnitures dama unguwar ba unguwace mai hayaniya ba babu bata lokaci suka koma gidan nan iyayenta da ita kanta suka shiga yiwa faisal addu'a domin duk atunanisu shine yake yi musu wannan hidimar, lokacin da faisal yadawo gida ya sanar da tafida ba karamin dadi yajiba anan yake sanar da faisal cewa an hadashi da wani malamin addini wanda yake taimakawa mutane dan haka zaije ya duba hanfa ko Allah zai sa adace, hakan kuwa akayi faisal yaje yadauki malami suka tafi gidansu hanfa, suna zuwa malamin yace taje tadauro alwala sannan ya bukaci da abashi ruwan zamzam original ba jabun ba

Please Login or Register in order to submit comment