Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώ[1/9, 7:53 PM] +234 901 554 3771: _*DEEN MARSHALL*_
_Mamuhgee_

*_ZAFAFA BIYAR_* πŸ”₯πŸ”₯
_*So Da Zuciya*_
Miss xoxo
_*Halin Girma*_
Hafsat Rano
_*Dabi'ar Zuciya*_
Safiyya huguma
_*Takun Saka*_
Billyn Abdul
_*Deen Marshal*_
Mamuhgee

_Pay @08184017082 Or 09134848107_


*1*

*_BismillahirRahmanir-Raheem_*

Ahankali ta dago kanta dake 'dan Sara Mata ta kalli kofar office din nata da aka kwankwasa batareda ta motsaba ta dauke idonta akan kofar tana sake boyayyan numfashin dake bayyanarda qosawarta da halin ABBAS LAMIDO sbd ko ba'a fada ba tasan koba shi bane to koma waye to al'amarine daya shafi sunan Abaas aciki.
Turo kofar akai tareda shigowa ko Bata dagoba Jin takun takalma yasa ta fahimci Sarah ce Dan Haka ta sake lumshe ido tana dago Kai ahankali tareda dauke hannunta daga kan aikin datakeyi a laptop ta aje gefe tareda gyara zama ta Kai hannu ta dauki ruwan data fitar a fridge tun dazu sbd su huce daga sanyi ta bude robar ruwan Tasha kusan rabi ta ajiye sauran tana cewa"

Sarah akwai wani abune?

Sai alokacin Sarah ta matso ta zauna kan kejerar hutawar dake kallon waddaΒ  *_NAJMA_*Β  ke zaune tana jiran abinda zata fada,
Saidata Dan sauke numfashi itama kafin Kai tsaye tace"

Naj dazu kafin isowarki zuwan chairman Abaas biyu office dinnan Kuma Banga alamar lafiyaba a yanayinsa
Zan iya cewa dai yanayin da aka Sabane.

Sai alokacin _*NAJMA ABDULLAHI BELA*_ ta dago da fararen idanuwanta dasukai laushi da gajiya tareda damuwar Jin abinda aka fada din ta kalli Sarah tsawon lokaci kafin ta sauke nata numfashin itama ta bude Baki da muryarta me taushi dake kokarin boye damuwarta tace"

Meyene matsalar Abaas Kuma yanzu?

Cikeda kulawa Sarah tana kallonta tace"

A yanda nakega inaga bazai wuce akan maganar jiya bace da Dr Sa'id yazo gurinki sbd zuwansa biyu Ana cewa kunfita tareda Dr Sa'id din.

Sai alokacin ta tuno da zuwan Dr din jiya da fitar da sukai zuwa taron makarantar yaronsa a wata private school dake kusa bama nesa ba.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana daukan wayarta Dan kiransa Dan kuwa ma wannan karon yayi kokarin rashin binta gida tun Daren jiyan yayi abinda ya Saba.

Ringing wayar ta ringa yi harta katse Bai daga ba ta sake saka Kiran Bai dagaba har lokacin
kusan Kira uku Tai Masa baya dagawa ta kashe wayar tareda ajewa gefenta ta waiwayo ta kalli Sarah tace"

Bai dagaba
Baya office dinsa ne?

Banajin yafita Dan ko kafin nashigo Naga wucewar secretary dinsa hanyar zuwa office dinsa.

Juyar da fararen idanuwanta tayi ta maidasu kan wayarta da tadau ringing taga sunan Hanifa ne akai ta lumshe idanu ahankali tana sauke ajiyar zuciya tareda Jin sanyi aranta sbd Hanifa Marshal Alfa Bata Bata lokaci komai kankantarsa batareda takirata ba idan taji wani Abu yafaru da ita.
Kallon Sarah tayi da alamar tambayar cewa"
Kinfada Mata yawon da Abaas yayi na nemana yanzu da safe kenan?

'yar dariya Sarah tasaki tana miqewa ta nufi hanyar fita tana cewa"

Sorry ma'am itace takirani da kanta ta tambaya.

Ficewa tayi tareda rufo kofar office din har lokacin da sauran dariya akan fuskarta saidai ta baro jikin kofar sukai kusan Karo da Abaas daya qaraso office din sanye cikin suits ash dasukai Masa kyau matuka kasancewarsa kalar ruwan tarwada Kuma cikakken kyakkyawan namiji meji da lokaci da kuruciya da nera.

Da sauri Sarah ta matsa gefe tana sake sake fuska da tace"

Barka chairman.

Ko kallonta beyiba ya bude kofar office din dake daukeda sunan NAJMA BELA ajiki ya shige tareda rufo kofar.

Tana zaune a inda Sarah ta barta bakuma ta juyoba sbd tariga tagane shine yashigo Dan Haka saima Dan lumshe ido datayi Wanda yake tamkar dabi'a gareta.

Kureta yayi da kallo daga tsayen kyawunta da dabi'unta masu sanyi suke taruwa su sace zuciyar mutum wainda shima sune suke dawo dashi gareta Koda yace ya rabu da ita,
Duk neman matansa yakasa samun wadda tafi Masa Naj kyau da sanyin dabi'u tareda wani irin aji Wanda ko jinin sarauta zai shafa Mata lafiya
Daya samu da tuni ya rabu da Naj sbd gabaki daya tagama Cinna Masa hauka bayan yanada tarin mutunci da dukiyarda yake iya shimfida duk abinda yakeso Amma gashinan yaqare da aiki a ALFA'S sbd ita 'yarΒ  daba 'yar kowaba face wadda ke amatsayin babbar Aminiya ga 'yar Marshal alfa Wanda sbd hakan ne take anan din shikuma yafiso ko ruwa idan zatasha tafada Masa Amma duk yabi yazama wani zararre akanta Wanda abin ke matuqar Kona Masa Rai duk da yasan tana tsananin hkr da dauke ido akan abubuwan dayake Mata Amma shima duk son dayake Mata bazai zauna Yana zuba ido tana yanda takeso ba Dan gwara ta Saba ko bayan aurensu tasan dokarsa baya daukan reni.

Jin shirun yayi yawa yasa ta dago ahankali ta Dan kalli gefensa da idanuwanta ta bude Baki cikin muryarta me taushi da nutsuwa tace"

Akwai wani Abu ne?

Rintse ido yayi wani takaici na taso Masa ya budesu akanta tareda qarasa matsowa gabanta ya fige wayar hannunta ya dangwareta kan kejera da qarfi cikin bacin Rai yace"

Akaro da danban adadiba Ina sake tambayar meye asalin boyayyar alaqarki da wannan likitan sbd bazai yiyu ko yaushe nayi tambayar mu'amalarku kinamun shiru sbd bansan meyake bakiba Wanda Ni bazan iya bakin ba da kinkasa rabuwa dashi,
Kyanki kike rudarsa dashi?
Kokuwa wani abun ne Wanda bansaniba ni......

Kashesa tayi ta hanyar zuba Masa manyan idanuwanta farare dasukai jajir atake da zallar takaicin kalamansa da basuda mutantawa ko darajantata amatsayinta na wadda zai aura din.

Miqewa tayi tsayi tareda daukan wayarta ta batareda tace Masa ko kala ba ta nufi table din office din da Jakarta ke Kai ta dauka ko kallon inda yake bataiba ta nufi kofa ta bude ta fice tabarshi tsaye Yana bin bayanta da kallo zuciyarsa na Kuna Kamar zai cinnawa kansa wuta yakeji.

Tana fitowa Sarah ta taso daga kan table dinta na matsayinta na secretary dinta ta qaraso tun kafin Tai magana ta lura da yanayin Naj din Wanda tasan dama za'ai Haka indai Abaas ne Wanda kullum ne qaida sai sunyi fada da Naj da Abaas din duk da dai kullum fitinar da tashin hankalin na Abaas din ne.

Batareda ta kalletaba da murya me 'dan nauyi tace"

Sarah ki tattara takardun Dana Bari a table da laptop Dina ki kawomun gida idan kintashi.

Ok Naj Allah yatsare hanya.

Tana saukowa qasan building din ta nufi gate zata fita tahau taxi sbd dama Abaas din yawanci ke daukota daga gida Kuma idan sun tashi ya maidata idan Kuma suna fada taxi take hawa wadda dama tafi hawanta shiyasa ma takeda me taxi dinta na musamman Wanda kiransa kawai takeyi yazo Dan kuwa ranaku daddayane basa samun matsala da Abaas Wanda take Jin wani lokacin Kamar zuciyarta zata Gaza bazata iya cigaba da hakuri tana hadiye halayen Abaas ba dan kuwa gabaki daya Babu inda sukai dace da juna dazasu iya rayuwar aure bayan aurenba,
Ta Yaya zata auri mutuminda baisan darajarta,mutuncinta,qimarta ba tareda mutunta alaqarsu,
Tariga tasani tsananin kyawuntane yasa Abaas yake son aurenta Dan tazama tasa abin ado agaresa Wanda Bata saniba ko tsananin zafin ransa da zafin kishinsa zai Bar kyan nata ta tsufa da abunta Dan ita shakkar aurensa yafara mamaye zuciyarta sbd a dukkanin halayensa Babu Wanda baya Bata mamaki.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana sake shanye damuwarta Kamar yanda ta Saba akan al'amarin Dan kuwa fasa auran Abaas gareta babbar matsalace dazata sake sako Kai tsakaninta da mahaifiyarta dama Dada kakarta uwa uba Dattijo Wanda yake mijin mahaifiyarta Kuma tawainiyan mahaifinta daya auri mahaifiyarta bayan rasuwar mahaifinsu.
Fasa aurenta da Abaas idan tayi shine zai zama Karo na hudu biyar kenan Ana fasa aurenta...

Mun iso hajiya" me taxi din yafada daidai Yana parking bakin Babbar kofar gidan Marshal Alfa Wanda sojojiΒ  hudu ke zaune kofar gidan suna gadi.

Fitowa tayi ahankali cikin nutsuwa wadda zallar ilimi da wayewartane tareda ajin datake dashine yasa komai nata yake cikin nutsuwa ta bude jeka ta fiddo nera dubu daya ta miqa Masa tana cewa"

Nagode Mal Hafiz.

Juyawa tayi ta nufi gefen gidan daya bangaren dake gefen gidan Alfa wani 'dan madaidaicin gidan gado Wanda yakeda Dan zurfi daga cikinsa sbd 'Dan yawan dasuke dashi a gidan danma kusan duk Yan Matan gidan sunyi aure duk da bawai yawane dasuba sosai.

Cikin sabo sojojin dake zaunen dasukaga dawowarta sukace"

Welcome Ms Naj.

Dan murmushi tasaki tana waiwayowa tace"

Barkanku da aiki da hutawa.

Gidansu ta qarasa Wanda yake gefen da 'yar tazara da gidan Alfa din ta shige Wanda ba gate bane koface irin ta gidan me 'dan rufin asiri.

Gefen Dattijo ne a farko Dan Haka ta wuce Kai tsaye kuryar gidan inda taci Karo da Umma habiba zaune a kofar nata sashen kan kujera tana duba kayan 'yan kananan atampopinta datake saidawa tana waya autarta Asmau na gefenta tana jera kayan cikin qatuwar ledar da aka kawo kayan.

Cikin girmamawa asma'un ta dago tana cewa"

Anty Naj sannu da dawowa.

Yauwa sannu Asmau
Ina yiwa umma sannu idan tagama wayar.

Hannu kawai umma habiban ta daga alamar amsawa tana bin bayan Najma din da kallo tana yamutsa Baki cikeda shaguben Naj din sbd aikin datakeyi Amma aure ya gagara.

Tana Isa sashen mahaifiyarta ta taddata a tsakar gida zaune itama tana lissafin nata kudin na turarukan wuta datake saidawa duk kwalaben turarukan a gabanta baje sai wani irin kamshi Mai qarfi ke tashi ta kalli umman tana nufar dakinta tace"

Ummi sannu da aiki.

Itama Bata wani dagoba tanaci gaba da aikinta gabanta tace"

Yawwa,
Lafiya dai Naga kin dawo yau da wuri.

Tana qarasa shigewa dakin nata tace"

Lafiya kalau hutawa nakeson Yi jiya bansamu bacci sosaiba.

Dama Ina Zaki samu maganar bacci me Dadi bakida abokin Hira acikin gida kowa Yana dakin aurensa,
Dayake Kuma ga wata babbar kwabon Nan kinsamu" taqarasa fada tana kallon gefen Anty Amina dake gefe tana yiwa babbar 'yarta zainab bayanin karatunta da Bata ganeba.

Kallon umman tasu anty Amina tayi tana cewa"

Umma Dan Allah ki daina cewa"

Naqi zaman auren Nan a gaban zainab zata ringa daukan abin aranta tana ajewa da wata fassarar.

Wani mugun kallo ta watsawa Anty aminan kafin tace"

To Yaya kukeson na bayyanarda damuwata da halinda nake ciki akanku?
Ke zaman auren ya gagara kin tattara kindawo gida da budurwar 'ya,
Ita wannan aurenma ya gagareta Yi kwata kwata ta koma ta zama wata ma'aikaciya mutane na qarqashinta ta Yaya zata iya auren
Shiyasa nake sake cewa Hanifa wannan aikin na Najma bazai Bari tayi aureba matuqar tana ganin mazan daidai take dasu..

Lokacin auren ne baiyiba umma" cewar Hanifa data shigo gidan tana qarasowa gurin umman fuskarta daukeda murmushi tace"

Umma Naj zatai aure kamar kowa lokacine kawai Allah Bai kawoba.

Cigaba da aikinta umman tayi tana cewa"

Duk da hakan dai ta rage ganin girman kanta ta sallamawa duk namijin daya samu tayi aure Dan shine mutuncinta da nawa Nima Dan ko Nima na huta da gorin dattijo da Dada dasuke ganin da saka hannuna aΒ  riqewar datai Kamar rake.

Murmushi Hanifa ta saki tana barin gurin umman tana cewa"

Umma Naj zata auri namijin daya kamaceta bawai ko wanne ba gskia
Kumafa ba riqeqa tayiba kawai dai Wanda zai Mana ciki da itane Bai bayyana ba haryanzu
Idan ya bayyana shikenan muma mun huta da damunta da kowa keyi da maganar aure,
Ni wlh bansan meyasa kuka sakamun Naj Dina a gaba ba duk kun damarmun ita.

Qarasawa kofar dakin tayi ta shige tana cewa"

Anty Amina barka da hutawa.

Da 'yar dariya anty Aminar tabi hanifar sbd ganin Kamar ta kunna umma databi kofar dakin da harara kamar zata hadasu su duka Tai musu duka ko zasu fahimci ciwon ranta na rashin auren Naj din wadda ita Sam kamarma abin baya damunta.
#Mamuh#


*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*

*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada'dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡

09134848107
[1/9, 7:53 PM] +234 901 554 3771: *_DEEN MARSHALL_*
_Mamuhgee_


2
Da wani irin kallo Hanifa kebin Naj dake tsaye bakin wardrobe daure da towel me kauri da girma brown color fuskarta fayau Kamar ko yaushe Babu wata damuwar abubuwan dake addabe da rayuwarta Kamar fitinar ummanta data su dattaji uwa uba ta Abaas datafi ta kowa zama abin baqin ciki da takaici.

Sake kallon fuskarta Hanifa tayi tana zaunawa kan gadon tareda ajiye wayarta gaban madubi tana cewa"

Nayi waya da Sarah dazu.

Batareda ta juyoba tana zare Yan kunnayenta tace"

Kada ki damu da abinda tafada Miki
Idan Akan Abaas ne zuwa yanzu kema kinsaba da halinsa,
Abinsa ya daina damuna yanzu saidai kawai yanda Naga kamar abin nasa kullum rikidewa yake zuwa ga zargi
Zarginma me muni Wanda nake dannewa Ina sharewa sbd Umma dasu Dattijo...

Sai alokacin Hanifa ta katseta da cewa"

Meyesa Zaki daure sbd su umma bayan su dinma da zasu bude ido da kyau su duba dabi'u da wasu abubuwan tako Ina Abaas Bai cancanta ba bama Haka ba yaushe Kika fara damuwa da abinda ake fada na cewan kece Kika qi aure da har Kika zabi auren Abaas lamido Wanda Ni kwata kwata baima kwantaminba
Gabaki daya Banga halayen maza masu hakuriba ko iya tattala mace atareda Abaas.

Ajiyar zuciya Naj din ta sauke Jin ran Hanifan yafara baci da zancen ta waiwayo ahankali ta kalleta tareda sakin wani irin lafiyyan murmushi Wanda kusan Arayuwarta tunda tazama budurwa cikakkiya kaf kannenta sukai aure aka sakota gaba tako Ina Hanifan ce kawai take iya ganin murmushinta me fidda asalin kyawunta Wanda yafito daga ainihin cikin zuciyarta sai kuwa Dr sa'id Wanda yake tamkar 'dan uwa Kuma aboki agareta shima idan tana tare dashi takanji nutsuwa da kwanciyar hankali sbd ya fahimceta tareda sanin halayyarta fiyeda 'yan uwanta na jini duk da kuwa Bata hada komai dashi ba face kasancewarsa likitan Hanifa tun suna yara har yanzu dasuka girma.

Zama tayi gefen Hanifan tana kallonta tace"

Ba abun damuwa bane basai kin saka damuwan Abaas ba aranki
Mubar maganan ma sunan Harya fara sakamun ciwon Kai.

Hanifa Sam ko sunan Abaas din tafi kowa takaicin saurara sbd tun ranar farko da zancen Yana son Naj din ya sauka a kunnenta ta qarewa background dinsa da halayyarsa bincike bataga ta inda ya cancanta Naj ba kafin daga baya taji fara aikinsa da zuba hannun jarinsa a ALFA'S dinsu Wanda Sam bataso hakan ba Amma sbd zagayen da yayi akai Masa Hanya ya bullo ta gurin JALALUDDEEN qaninta Wanda dukiyarsa tafi ta kowa yawa acikin ALFA'S din hadda kuwa mahaifinsu da shine me asalin companies din na Nan portharcourt dama na wajenta.

Miqewa Naj din tayi tana cewa"

Bari nayi wanka nafito zamuyi mgna akan Isma'eel ya kirani dazu akan maganar zuwanki ganin likita A Jamaica.

Kallon kyakkyawar fuskarta Hanifa tayi tana murmushi tace"

Allah sarki Zawj.

Da yanayi na sanyi Naj ta kalleta zuciyarta na yin sanyi da dukkanin wata damuwar Hanifa ko ciwonta.

Toilet din dakin nata ta shige Dan dama wanka zatayi Hanifan ta shigo.
Bayan shigarta wanka miqewa Hanifan tayi ta sauko daga kan gadon ta zura flat slippers dinta na _Jimmy choo_ ta fita dakin ta nufi gurin umma dake zaune har lokacin tana aikin zuba wasu turaren wuta masu tsananin qamshi ta zauna gefen umman tun kafin ta qarasa zama umman tace"

Kun gamo shawaran yanda zaku fuskanci Dattijo da Dadah idan Maganar aurenta da Abbas ta fasu Dan nasan wannan doguwar fuskar da Kika shigo da ita bata lafiya bace Dole akwai abinda yake faruwa tsakaninta da Abbas.

Dan guntun murmushi Hanifa ta sauke tana Taya umman rufe kwalaben turarukan tace"

Umma meyesa kuka kasa gane irin taurin zuciya da qarfin imanin da Naj take dashi sbd ba kowane zai iya hadiyewa ba yakuma danne irin Gori da takura tareda cin fuskan da ake Mata akan rashin yin aure ba?

Umma kowa Yana yiwa Naj kallon taqi aure sbd zurfin ilimi da karatun bokon datayiba a cikin gidan Nan hakama Ana Mata kallon wadda ta Raina maza sbd ganin Kamar matsayinsu da nata daya ne Wanda umma keda Kika haifi Naj kinsan ba Haka takeba kawai dai ita Allah Haka yayita miskila me halin ko oho ga abinda ake fada akanta bayan Haka shi fa aure nufi ne na Allah Kuma ba lallai ne ita lokacin nata auren yayi ba idan lokacin yayi zatayi.

Hmmn Hanifa nagaji da bin bayan Najma akan maganar fasa aurarrakin Nan nata da akeyi kusan Kashi biyar tun Ina yadda da qaddarane a gaskia yanzu na yadda da hadda halinta na miskilanci Wanda kesa mazan ganin Kamar tafi karfinsu ne kokuma tana tuna tafi karfin nasu,
Kunfi kowa sanin yanda Dadah da Dattijo suka sakoni gaba a cikin gidan Nan akan Najma
Kullum fa qara shekaru akeyi ba ragewa ba yanzu ke da Allah yakawo rabo na haihuwa aurenki da yanzu ba kinada yara biyu ko ukuba koma hudu idan anyi haihuwar ritsa Amma Sam Naj ko 'yar damuwar Nan Bata nunawa kullum itace a nutse a kammale saikace wata lissafi ahaka takeson qarewane saidai aiki kawai..
To ku zauna ku dasa sabuwar shawara wannan karon wlh Dattijo rantsuwa ce a bakinsu shida Dadah matuqar aurenta da Abbas ya fasu to wlh bazata rufa sati ba agidan zasu aura Mata duk Wanda ya samu ciki kuwa hadda sojojin dake gadin gidanku yace zai kaiwa tayi idan hakan ta faru Ni kaina danake mahaifiyarta wlh zuciyata zata iya bugawa bare ita Dan Haka ki zaunar da ita kuyi shawara koma menene matsalar su zauna suyi sulhun abarsu itada Abbas din asamu ayi auren Nan ta tafiyarta ta huta Nima na huta da zancen kullum din.

Batasan wane bayani zata yiwa umman ta fahimta ba sbd matsuwar su dattijon tariga tasaka umman itama gajiya tana kasa fahimtar 'yar tata,
Tana tsananin qaunar Naj tamkar 'yar uwarta ta jini dasuka fito ciki daya Dan kuwa tsananin qaunar datake Mata har kasa tantance cikin su biyun tsakanin ita da marshal batasan waye tafiso ba duk da shi din jinintane dasuka fito ciki daya,
Bazata iya Bari Naj ta cutu takowane irin Hanya ba Dan Haka ita da kanta zata nema Ganin Abbas lamido suyi magana idan har yanason Naj da dukkanin zuciyarsa da gaskia to yakamata ya sauya su fuskanci rayuwar aure zasuyi su fahimci juna tun yanzu.
Idan har zai qaunaci Naj da gaskia zaifi Mata ace Dattijo yabada auren Naj wa duk Wanda yasamu.

Wanka ta fito taga Hanifan Bata dakin tasan tana gurin umma ko anty Amina Dan Haka Kai tsaye ta nufi gaban mirror ta zauna ta kalli fuskarta zuwa kirjinta da kafadunta dake bayyane suna wani qyallin haske da samun lafiyar fata ta maida kallonta kan fuskarta datafi komai kyau da daukan ido atare da ita ta lumshe fararen idanuwanta ahankali tareda sauke numfashi kadan kafin ta janyo lotion na jagggins tana shafawa kadan kadan Dan batason Mai da yawa Ta miqe bayan ta shafa turaren POSSES ajikinta tareda mist na Rednight ta zare band din kanta ta gyara daurin gashinta tayisa sako sako sbd Taji dadin kan nata ta nufi wardrobe ta Ciro doguwar riga Mara nauyi zata saka wayar Hanifa data bari kan mirror din nata takawo haske tana vibrating ahankali ba qara sbd Wanda Dabi'arsune rashin sakawa waya qarar ringing Dan kusan itace ta koyawa Hanifan hakan qarar waya na damunta shiyasa Sam wayarta Bata qara idan Ankira saidai vibrating shiyasa itama Hanifan ta koya sbd Naj din.

Ahankali ta waiwayo ta kalla wayar taga sunan dayake Kai _MARSHAL_
dauke Kai tayi tana cigaba da saka kayanta Dan tunda takeda Hanifa Bata taba daga wayar 'dan uwanta ba idan yakira Wanda shi kadaine kawai Bata daukan wayarta idan shine yakira idan har Bata kusa tun kuwa tasowarsu suna qananu haryanxu.

Sanin baya Kira biyu 'daya yakeyi yasa ta sake waiwayo wayar tana kallon sunan destination dinda caller ID ta rubuto _HAWAII US STATE_
Hanifa Babu wani Abu a duniya dayafi Mata qanin nata Wanda su biyu kacal mahaifiyarsu ta Haifa ta bar duniya Wanda tazarar shekara uku ce a tsakaninsu yanayin aikinsa da girman matsayinsa yasa baya tareda ita wayama sai yasamu lokaci suke iya Yi Dan Haka Babu abinda Hanifan Bata Wasa dashi irin waya da marshal din Dan Haka bazata so ta rasa kiranba takai hannu a natse ta dauka tareda nufar kofa ta bude ta fito ta kalli zainab dake kusa tace"

Miqawa Hanifa wayarta Ana Kiranta.

Karba zainab tayi ta nufi Hanifan da sauri ta miqa Mata cikin sa'a kuwa har lokacin Kiran Bai katseba tana ganin me Kiran ta dauka tana Kiran sunansa cikin tsananin kaunarsa da kowa ya shaida kaunace me girman gaske a tsananinsu.
#MAMUH#




*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*

*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada'dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡

09134848107
[1/9, 7:53 PM] +234 901 554 3771: *_DEEN MARSHAL_*
_Mamuhgee_



3
Komawa Naj din tayi Dan tayi sallah tana Shiga dakin tun kafin Hanifan ta qaraso dakin ta tayar da sallarta Dan tasan Babu ranar da zasuyi wayan Hanifan Bata hadasu ba suka gaisa Wanda daga ita harshi din basa buqatan gaisawar sbd shi dai Bai taba gaidata ba hakama itama batajin zata iya gaidashi din tun koba komai shine qani Amma gabaki daya matsayi dayake dashi da jin yazama billionaire yasa baya iya gaida mutane kokuma tace wasu mutanen tunda Yana gaida Hanifa da hajjo kakarsu,itadaima gabaki daya Bata wani buqatan shiga rayuwar kowa musamman irin tasa rayuwar wata iri

1 Comments On DEEN MARSHAL
avatar
hindatu-5

3 months ago

Reply

The novel is nice

Please Login or Register in order to submit comment