Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zance, Baba ke sanar dani wannan karon admission yana matuk'ar wahala sai kana da hanya, amma yace mu had'o takardun mu ya rok'i VC ya taimaka", "Amma nagode sosai Asiya, kiyi wa Baba godiya, In Shaa Allahu gobe zan zo da kaina na kawo", "A'ah ba sai kinzo ba, ki aiko ta mota kawai", "Toh shikenan nagode",

Da murna ta koma gida tana sanar da Nene da Ramla, "Kai yarinyar nan da iyayenta mutanen kirki ne, Allah ya saka musu da aljanna" Nene ta fad'a, "Amin Amin".



Sati biyu da tura takardun ta, suna zaune tsakar gida suna hira, suka jiyo sallamar Asiya, Bongel ta mik'e da fad'in "Asiya zuwa ba sanarwa", Asiya tayi murmushi tace "Tare muke da Baba", "Kice zuwan ba naki bane ke kad'ai", Nene tace "Ki masa iso ya shigo" Ta shiga d'aki ta d'auko hijabin ta,


Bayan an gama gaisawa sun sha ruwa, Baba ya numfasa yace "Da farko dai ina fara baku hak'uri, kuyi hak'uri Dan Allah komai kuka gani muk'addari ne daga ubangiji, kamar yadda Asiya ta sanar da Bongel ta tura takardunta, ni na buk'aci haka da niyyar taimaka musu su samu admission tare, amma sai dai hakan bai yiyu ba, d'aya ta samu d'aya bata samu ba" Bongel k'irjinta ne ya duka, jikinta yayi sanyi ta gama sarewa, Baba ya cigaba da cewa "Wallahi ba da son raina haka ta kasance ba, Asiya suka ba admission, itama VC cewa yayi dan tana yar' cikina shine zai taimaka, kuma ko da yara biyu ne nawa d'aya zai d'auka, nayi k'ok'arin aba Bongel admission d'in, Asiya ta hak'ura dan tana gaya mun burin Bongel na son karatu, wallahi sam yak'i yarda da cewa admission ya riga ya fito da sunan Asiya, kiyi hak'uri Bongel wallahi bani da wata hanya, k'asar tamu ce sai dai muce Allah ya sawwak'a"


Tuni hawaye suka wanke fuskar Bongel, ta kasa cewa komai, Nene duk da yadda zuciyarta ke soya tayi k'arfin halin cewa "Haka Allah ya k'addara, mun gode sosai da k'ok'ari baban Asiya Allah ya bar zumunci", "Amin" Ya amsa, Ramla ma jikinta yayi sanyi matuk'a, gaba d'aya hope d'insu akan Bongel yake, yanzu komai ya yanke, Baban Asiya ya jima yana basu baki kafin suka tafi, Asiya ma rai babu dad'i ta tafi.


"Wannan k'asa tamu Allah ya kawo mana sauk'i, na kasa cika burin Bappa na son ganin Bongel tayi ilimi mai zurfi, kayi hak'uri Bappa bani da wata hanya, talaka bashi da galihu a k'asar nan" Ta k'arasa da hawaye, "Ki daina d'aurawa kanki laifi Nene, haka Allah ya k'addaru bazan yi ilimi mai zurfi ba, watak'ila haka zamu k'are rayuwar mu duk da bawa baya yanke rai ga rahamar ubangiji", Abu duk da kasancewarsa yaro ya nuna rashin jin dad'in sa, "Yanzu shikenan nima bazan shiga makaranta ba"
Ya fad'a a sanyaye, Bongel ta jawosa jikinta "Idan da rabo zaka yi ilimin boko Abu", "Allah yasa", Tace "Amin" cike da tausayin sa.



Bongel ta koma sukuku, walwalarta ta rage, rashin samun admission ba k'aramin tab'a ta yayi ba, gashi kullum rayuwa k'ara wuya take musu, babu mai taimaka musu, dangin Nene ba masu k'arfi bane, suma suna fama da kansu, iyayenta ma suna rugar ard'o can wurin funtua.


Asiya wurin printing takardar admission d'inta taji wasu yan' mata na hira, "Wallahi kin taimakeni da kika kaini wurin Hisham, gashi na samu admission cikin sauk'i" Cewar d'aya daga cikin yan' matan, "Ai Hisham sai idan baka je wurin sa ba, admission kamar ka samu amma fah..." Bata k'arasa ba sukayi dariya da shewa, Jin haka Asiya ta k'arasa wurinsu, ta musu sallama suka amsa, "Dan Allah kuyi hak'uri na saurari hirar ku, wata yar'uwata zaku taimakawa itama ta samu admission", Suka kalli juna, D'ayar tace "Ba damuwa bane", "A ina zamu samesa Dan Allah", K'aramin kati ta fito dashi daga jaka ta mik'a mata, Ta karb'a tana mata godiya,

Ta kasa bari ta koma gida, nan take ta soma kiran wayar Maman Jabeer, anci sa'a Bongel ta shigo itama ta kira Asiya kwana biyu basu yi waya ba, "Kinga yar' halak na kira" Cewar Maman Jabeer, Bongel tace "Aikuwa" tana karb'ar waya,

"Albishirin zan miki, na samu wata hanya da zaki samu admission" Cewar Asiya da k'arfi kamar zata fasa mata dodon kunne,"Da gaske?",  "Wallahi da gaske nake, idan zaki iya ki shigowa katsina gobe", "Ko a yau kike so zan shigo", "Toh sai kinzo", Ta kashe wayar cike da farin ciki,


Nene farin cikin daya bayyana kan fuskarta ba k'arami bane, haka Ramla da Abu, tun a daren Bongel ta had'a kayanta kala uku da abunda zata buk'ata cikin jaka, Tunda safe ko kari batayi ba, ta shirya tafiya, Nene tabi ta addu'o'i na nasara da kariya, wurin maman jabeer ta ari dubu biyu da zatayi kud'in mota, Fatsuma da Dije nata yada habaici bata ce musu komai ba suna fad'in haka za'a je a dawo.



Tafiyar awa d'aya da rabi ya d'auke su, suka isa garin katsina, suna isa tasha, ta ari waya ta kira Asiya, ta mata kwatancen unguwar su, mai napep ta samu ta fad'a masa unguwar, ya kaita har k'ofar gidansu Asiya, ta sallame sa ya tafi, gida ne k'arami sosai, kana gani kasan suma basu da hali, d'akuna biyu ne sai band'aki a tsakar gida, da k'aramin kicin, Cike da far'a mutanen gidan suka tarbeta, Asiya ta sauketa d'akinsu ita da k'annenta mata uku, haka suke gwamatsawa,


Asiya ta sanar da ita komai, ta fiddo katin ta nuna mata, hakanan Bongel ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, "Amma Asiya kina ganin babu matsala", "Wacce matsala Bongel, zuwa zamuyi mu rok'esa mu fad'a masa buk'atar mu In Shaa Allah zai taimaka ki samu admission", "Toh shikenan yaushe zamu je?", "Yanzu ba zamu tsaya b'ata lokaci ba", Bongel tace "Toh" tana mik'ewa, ta d'auki k'aramar jakarta da takardun ta ke ciki, fuskarta kad'ai ta wanke da ruwa, saboda zufar da tayi, kasancewar lokaci ne na zafi,


"Daga zuwa ba hutawa sai fita" Cewar Mama dake tsakar gida tana yankan alayyahu, Asiya tace "Mama da zafi zafi ake dukan ice", Mama tayi dariya tace "Allah ya bada sa'a", Suka amsa "Amin",




H&H GLOBAL RESOURCES

Shine sunan da suka gani manne a tafkeken ginin dake gabansu, wanda jikinsa  duka glass ne yana walk'iya, Bongel ta kalli Asiya tace "Anya bamu kawo kanmu inda yafi k'arfin mu ba", Asiya duk da tasha jinin jikinta ganin girman ginin, ta dake tace "Ki cire tsoro Bongel bakya son shiga jami'a ki cika burin Bappa", Bongel tayi saurin gyad'a kai, Tare suka jera zuwa building d'in, Bongel na ambaton Allah a ranta,


Securities dake tsaye bakin wurin sukayi checking d'insu, suka k'arasa, suna zuwa wurin shiga k'ofa ta bud'e, Karon farko a rayuwarsu da suka ga k'ofa na bud'ewa da kanta, a tare suka zaro ido, Suna shiga sanyin Ac mai rab'a ya soma dukan fatar jikin su, kalle kalle suka tsaya yi, basu san ina zasu yi ba, suna tunanin wacce duniya ce suka kawo kansu, tsabar had'uwar wurin sai suke jin tamkar ba'a k'asar suke ba,

Wata mata ta nufo su da fad'in "May i help you", Cikin daburcewa Asiya tace "Wurin Hisham muka zo", "This way floor 2" Ta nuna musu hanya,


Elevator ne a wurin sukayi tsaye suna faman k'wankwasawa a zaton su nan ne office d'in sa, K'ofar suka ga ta bud'e, budurwa mai ji da kyau da gayu kanta yasha attach ta baza su shi har baya, da fixed nails, zaka rantse ba musulma bace, ta fito banzan kallo ta watsa musu ta wuce, Asiya taja tsaki , Bongel tace "Mu muka kawo kanmu",


Wani babban mutum ne yazo shiga, suka gaishe sa har k'asa ya amsa, a ransa ya yaba da natsuwar su, Yace "Wa kuke nema?", Asiya tace "Hisham", "Muje" Ya fad'a, Suka bi bayansa,

Mamaki ya kama su ganin inda suka shiga, suka ga ya danna abu wurin wasu numbers, sama suka ji ana yi dasu suka had'iye yawun tsoro tare da k'ank'ame juna, dariya suka so su bashi yadda yaga sun tsorata,

Suna ganin k'ofar ta bud'e, suka fito a guje, "Can zaku je nan ne office d'in" Mutumin ya fad'a yana nuna musu wata k'ofa, Mun gode Baba", Asiya ta fad'a,

"Meye muka shiga yanzu mai kamar jirgi" Cewar Bongel, Asiya tace "Nima ban sani ba, ban tab'a ganinsa ko jin labari ba", "Allah yasa mu koma gida lafiya idan ba mun kawo kanmu inda za'a yanka mu ba", Asiya tayi dariya tace "Har kin bani dariya, duniyar ce da fad'i, Allah ne bai tab'a kawo mu ba, wuri ne na masu naira", Bongel bata ce komai ba, har suka kai bak'in k'ofar, Knocking sukayi, Suka ji wata murya tace "Yes", A hankali Asiya ta murd'a k'ofar suka shiga, wata mace suka tarar zaune tana rubuce rubuce a takarda, Ta kallesu tace "Ku k'arasa ciki",


Asiya na gaba Bongel na bin ta a baya, kusan mutuwar tsaye sukayi ganin had'uwar office d'in, hankalinsu bai k'ara tashi ba, sai da suka ga wanda ke zaune kan kujerar dake nuna shine mallakin office d'in, had'uwar sa da kyansa yasa suka k'ara shan jinin jikinsu,

"Ku k'araso mana" Suka tsinci muryar sa, wanda basu tsammaci jin haka ba, A sanyaye suka k'arasa, ya nuna musu kujera su zauna, k'amshin turaren sa mai dad'i ke ziyartar k'ofofin hancin su, idonsa k'yam akan Bongel, duk ta tsargu da irin kallon da yake mata,


Asiya tayi k'arfin halin cewa "Dan Allah taimaka mana muka zo kayi", "Wane irin taimako kenan?", Ta nuna Bongel, "Ita ke neman admission, wallahi munyi iya k'ok'arin mu ta kasa samu shine aka ce muzo wurin ka", Murmushin gefen baki yayi yace "Admission kamar ta samu ta gama but akwai sharad'i", Bongel tayi saurin cewa "Ko wane sharad'i ne zan bi", "Ki dawo gobe ke kad'ai, ga numberta i will let u know inda zamu had'u" Ya k'arasa yana ajiye mata k'aramin katin sa, tasa hannu ta d'auka tana masa godiya, Suka mik'e zasu fita har sun kai k'ofa ya kira Bongel, ta dawo, bandir na 500 ya mik'a mata, Tayi saurin cewa "A'ah mun gode", a tsawon rayuwarta bata tab'a ganin kud'i masu yawan su ba,


"Bana kyauta a mayar mun" Ya fad'a cikin dakewa, Kwarjini taji ya mata ta kasa k'ara musa masa, Hannu biyu tasa ta karb'a da fad'in "Allah ya saka da alkhairi", "Amin" Ya amsa, Ta juya zuwa k'ofar fita, yabi bayanta da kallo, yayi juyi kan kujerar sa yana murmushi.


Har suka isa gida suna jinjina kyautar kud'in da ya musu, suna zuwa suka nunawa Baba, ya musu fad'an karb'a da sukayi, yace kada su k'ara daga yau, suka ce toh, Bongel baccin farin ciki tayi na jin zata samu admission, tana alla-alla safiya tayi sai wani b'angare na zuciyarta na saka mata tunanin meyasa zai ce tazo ita kad'ai.






OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

  *HASKE WRITERS ASSO...*

SHAFI NA BIYAR


Safiyar yau Bongel sukuku ta tashi, duk da tana k'ok'arin b'oye damuwar ta, Asiya taso ta fahimta sai dai bata tambayeta ba, sanin mutum ce mai zurfin ciki, idan ba ita tayi niyyar fad'a maka abunda ke damunta ba, tambayar duniya amsar d'aya ce babu komai,

   Ita ta taya Asiya suka gyara gidan suka dama kunu wanda dashi kusan kullum su Asiya ke karin safe, Bongel kad'an ta sha tace ta k'oshi, bata jin sawa cikinta komai,

  "Ina tunanin yau zan koma", "Kai haba ba zaki bari ki mana kwana biyu ba", "Ina so na koma na sake shirin dawowa makaranta, naga saura sati d'aya a fara registration, kuma banda abun ki ni da zan dawo garin ku", "Hakane, bama garin mu kad'ai ba gidan mu, dan anan zaki zauna, jiya Baba yace na fad'a miki", Murmushi tayi tana jin dad'in yadda Asiya da iyayenta ke nuna k'auna gareta.


    12 na rana ta shirya wucewa, a tsakar gida ta samu Baba da Mama, Bongel har kin shirya wucewa" Baba ya fad'a, Tace "Eh Baba", "Toh ga kud'in da mutumin nan ya baku, kunfi mu buk'atar su, ki kaiwa mahaifiyar ki kwa rage wani abu", Saurin girgiza kai tayi tace "A'ah Baba", "Ki karb'a Bongel, reg na makaranta kina buk'atar kud'i, naira ba zamu tab'a cikin kud'in nan ba wallahi" Ya k'arasa yana mik'awa Asiya "Karb'a ki sa mata a jaka", Asiya ta karb'a ta bud'e jakarta ta jefa, Godiya ta musu sosai, ta tafi da tunanin karamci irin nasu, Asiya da K'anwarta Aina'u suka rakata har tasha, sai da suka tabbatar ta shiga mota, suka taho gida.


***************

Tsaye yake bakin balcony na office d'in sa, hannun sa rik'e da k'aramin mug yana sipping hot tea, ta glass na wurin yake hango motocin dake wucewa ta titi, Kallo d'aya zaka masa kasan akwai abunda ke damun sa, Komawa yayi cikin office d'in, ya zauna kan kujerar sa, ya jawo drawer dake manne da teburin dake gabansa, wani file ya d'auko yana dube dube a ciki,


    Hisham cikin  sanyin jiki ya tura k'ofar office d'in ya shigo da sallama, Haidar yaji sallamar yayi tamkar bai ji ba, har ya k'araso ya zauna kan kujera tare da fad'in "Yaya Haidar sannu da aiki", takardun ya cigaba da dubawa ba tare da yabi ta kansa ba, Jikin Hisham ya k'ara yin sanyi, bai tab'a masa irin haka ba,


  "Yaya Dan Allah kayi hak'uri", Still bai tanka sa ba, "Yaya kada kayi fushi dani", A fusace ya d'ago yace "Tashi ka fita Hisham, is your life ka cigaba da duk abunda kaga dama", "Yay...", Yayi saurin katse sa "I said out", Hisham ya mik'e yana jin duniyar ta masa zafi, So shak'uwa da k'auna ce mai k'arfi tsakanin su,  tun tashin sa bashi da abokin shawara kamar Haidar, duk wata matsalar sa shi yake kawowa, basa k'aunar b'acin ran junan su, fushin Haidar a gare sa yasa komai ya jagule masa.


  "Ya zama dole na nuna masa fushina wannan karon, ko hakan zai sa ya shiryu, ya gyara halayyar sa" Haidar ya fad'a yana cigaba da duba takardun,

   Ya d'auki lokaci yana dube dube kusan kowacce drawer a office d'in sai da ya duba, kansa ya dafe ya furta "Ya Allah" ganin bai samu abunda yake so ba, "Ya zama dole naga Abba", Mik'ewa yayi ya fita office  d'in nasa, elevator ya shiga zuwa floor 3,


   Wata aljannar duniya kenan ba k'aramin tsaruwa da had'uwa floor d'in yayi ba, Kai tsaye office d'in Abba ya shiga ba tare da ya jira an masa iso ba, Yaci sa'ar samun Abba shi kad'ai yana karatun newspaper,

  Ya gaishe sa cikin ladabi, Ya amsa da sakin fuska, Bayan ya zauna, Abba ya ajiye newspaper dake hannun sa yace "Tunda  na ganka a irin wannan lokacin nasan  akwai dalilin zuwan", Kansa ya gyad'a sama yace "Eh ina da magana Abba", "Ina jin ka" Abba ya fad'a yana tattaro hankalinsa kan Haidar,


   "Abba ina tunanin lokaci yayi da ya kamata mu cirewa Maigoro share d'insu ya zama business d'inmu babu share na kowa a ciki", Haidar ya fad'a, a ransa yana addu'ar samun goyon baya daga mahaifinsa, Abba ya gyara zaman sa yace "A ko da yaushe tunanin mu yakan zo d'aya da kai, na dad'e ina wannan tunanin sai dai bansan ta yadda zan b'ullowar al'amarin ba", Yaji dad'in jin haka sai dai zancen Abba na k'arshe ya sa shi fargaba,


  Abba ya cigaba da cewa "Before muyi hakan dole sai munyi tunanin wata hanya na bunk'asa kasuwancin mu ta yadda raba business d'inmu dasu ba zai tab'a mana kasuwanci ba, duk da cewa munfi so k'arfi a ciki, mu muka fara kafa business d'in, ya zama dole mu k'ara ilimin yadda zamuyi running business d'in mu individual", Haidar ya numfasa yace "Wane irin ilimi Abba,  ina da PHD akan business admin, degree da masters on economics,

  Abba yace "You still have to learn more", "How?" Ya tambaya, "You have to be a lecturer in economics department", "Lecturer" Haidar ya fad'a a razane, "Yes" Abba ya fad'a yana d'aga masa kai, "Amma Abba taya zan zama lecturer, ba zan iya lecturing ba", "Haka zaka daure, ta hanyar lecturing zaka k'ara samun ilimi kan kasuwanci, lecturer dole zai rik'a research kullum da zurfafa tunani, ta lecturing zaka k'ara samun experience", Shiru yayi yana nazarin yadda zai zama lecturer, gaba d'aya yana jin hakan ba ajin sa bane, gashi sam baya son hayaniya, "Kayi hak'uri ka bi abunda nace, ta haka zamu cimma burin mu In Shaa Allah, idan kayi hak'uri na dan' lokaci ne zaka yi", Abba ya fad'a yana assuring nasa, "Allah ya shige mana gaba" Ya furta yana jin sarewa a tare dashi, Abba ya amsa da "Amin".


************************

Har k'ofar gidansu driver ya kawota, tare da wata tsohuwa ya kawo su unguwar, tun daga can aka biya ya kawo tsohuwar har gida, ita ya fara ajiyewa kana ya kawo Bongel,

  Tana fitowa cikin motar sukayi ido hud'u da Hamma Siddiku mugun kallo ya jefa mata ya wuce cikin gida, jikinta yayi sanyi, tayi wa mutumin godiya yaja  motar sa ya tafi, Ta d'auki k'aramar jakarta zuwa cikin gida, tun daga k'ofar gida take jiyo muryar Hamma Siddiku yana zuba ruwan bala'i,


   Tsaye yake kan Nene yana sauke mata bala'i, "Iskancin yarinyar taki har ya kai k'ato ya ajiye ta da mota bakin gidan nan, dama nasan ba wata makaranta data tafi nema katsina, yawon karuwanci kawai kika tura ta, toh ba zai yiyu ba, ba'a k'ofar gidan nan ba, taje can tayi yawon karuwancin ta", Nene har cikin ranta take jin zafin kalmar karuwanci da yake jifan yar'ta dashi, hak'uri irin nata yasa ta kasa ce masa uffan, sai d'aki da ta shige abunta, Ramla suka rufa mata baya, "Au shigewa kika yi baki da lokacina ko, toh wallahi bara na shaida miki duk ranar da tayo abun kunya sai kun bar gidan nan ku dukan ku",

  Bongel bata san sanda zuciya ta d'ibeta tace "In Shaa Allah ba zanyi abun kun..." Bata k'arasa ba ya kife ta da mari, kafin ta d'ago ya k'ara mata, Da gudu Abu da Ramla suka fito daga d'akin suna kama Yayar su, Hamma Sidddiku ya cigaba da zage zage, Bongel duk da zafin marin da yadda zuciyarta ke k'unar b'acin rai, ta dake bata bar d'igon hawaye ya zuba kan fuskarta ba, bata son ganin damuwa kan fuskar mahaifiyarta da k'annen ta,


   Tana shiga d'akin tayi saurin fiddo jamb admission letter d'inta ta mik'awa Nene da fad'in "Na samu admission" Tayi hakane dan kawar musu da b'acin ran da Hamma Siddiku ya saka su, Nene a take murmushi ya sub'uce mata tace "Alhamdulillah Alhamdulillah Allah abun godiya bazan iya misalta farin cikin da nake ciki ba" Abu ya tashi yana ta tsalle, Ramla ma bakinta ya kasa rufowa,


   Ta fiddo kud'i cikin jaka ta ajiye kan cinyar Nene, "Ina kika samu wannan kud'i masu yawa?" Nene ta tambaya tana zaro ido, "Wanda ya bani admission ne ya bani yace nayi hidimar shiga makaranta", Karon farko a rayuwarta tayi wa Nene k'arya dan sam bata son abunda zai tada mata hankali, "Toh ai sai ki karb'a ki ajiye wurin ki", "A'ah Nene dubu ashirin kad'ai zan karb'a na lallab'a dasu, sauran ayi cefane da sauran hidimar gida, ki cire ko dubu goma ce ki fara k'aramar sana'a", "Allah ya miki albarka, yasa ki fara karatun a saa", "Amin Amin",


   Bongel a ranar data cika kwana biyar gida, ta shirya komawa katsina makaranta, a cikin kwanakin babu irin bak'ar maganar da basu sha ba wurin su Fatsuma, a cewar su Bongel yawon karuwanci taje katsina, ta samu kud'i, gashi har sunyo cefane, idan ba yawon banza ba, ina zata samu kud'i, Daga Nene har Bongel ba wanda yabi ta kansu.

  
   Bongel ta had'a kayanta tsaf na tafiya, Goggo Hajjo ta kawo mata yaji, k'uli k'uli da garin kwaki tace ta k'ara, Ta mata godiya sosai da nuna jin dad'in ta, Haka Nene ma ta yabawa Goggo dan tafi k'annen mahaifinta da ko abunda ba'a so basu bayar ba, kuma dukkansu ta musu sallama, amma ba wanda ta samu amsar kirki daga gare sa,

 
"Maganar zaman ki gidansu Asiya sai nake ganin rashin dacewar haka, suna fama da kansu kije ki k'ara musu lalura, babu wurin kwana ne a makarantar taku" Cewar Nene, Bongel tace "Akwai Nene", "Toh me zai hana ki zauna a can", "Sai nake ganin kamar idan nayi haka ba zasu ji dad'i ba, dama ina tunanin neman aikatau na d'aukewa kaina wasu lalurori", "Kinyi tunani mai kyau, rayuwa tayi tsada yanzu, kowa yana ji da kansa, baka k'arawa mutum d'awainiya ba", Ta jinjina kai alamar gamsuwa da zancen Nene, "Allah ya tsare ki ya kare ki, Allah ya baki ilimi mai amfani da albarka", "Amin"


   Har k'ofar gida suka mata rakiya, ta tafi da burin watarana zata kawo sauyi a rayuwar ahalin ta.


**********************

  Bongel ta koma katsina da kwana biyu suka soma registration na makaranta, ranar farko ba k'aramar wahala suka sha ba, kasancewar su sabon shiga, ko'ina sai sun jira layi bana wasa ba, sunyi applying scholarship gwamnati zata rik'a biya musu kud'in makaranta,

  "Wai Allah! wallahi na gaji, haka zamu rik'a fama kullum", Asiya ta fad'a tana tsayawa, Bongel tace "Nima na gaji, amma ya muka iya tunda ilimi muke nema", Asiya tace "Hakane amma Dan Allah tsaya mu huta", Bakin wata bishiya suka zauna, sun d'auki kusan minti ashirin kafin suka tashi,

  Sai yamma suka dawo gida a gajiye, wanka suka fara yi, suka ci abinci, kowacce ta kwanta tana huce gajiya,


********************

"Ya kamata zuwa yanzu an kai k'arshen komai, amma kullum babu wani bayani, idan ra'ayi ne bakwa yi ku fito ku fad'a" Ammi da wayar ke kunne ta tana sauraran mai maganar tace "Ba haka bane Hajiya Mariya, ina so ku bamu nan da sati d'aya", "Kullum maganar d'aya ce dai, a baku lokaci kaza, idan lokacin yazo kuma babu wani bayani", "In Shaa Allah wannan karon hakan ba zata faru ba", "Allah yasa, Ina Irfan banji motsin sa ba", "Gashi nan", Ta mik'a masa wayar yana mata gwaranci, kafin ta kashe,


   Ammi shiru tayi damuwa d'auke a fuskarta, har Haidar ya shigo bata ji shigowar sa ba, "Ammi barka da dare", Sai muryarsa kawai taji, "Barka kadai" Ta fad'a a sanyaye, Yana zama Irfan ya d'are cinyar sa,

  "Ammi ina fatan lafiya?" Ya tambaya cike da kulawa, Ta sauke ajiyar zuciya tace "Hajiya Mariya ce ta kira k..." Saurin katse Ammi yayi ta hanyar yin tsaki yace "Suna nema su zamarwa mutane liability, ana dole ne", Ammi tace "Wallahi bani da damuwa sai su", "Ki daina damuwa Ammi, kada ki sawa kanki wani ciwo, In Shaa Allah ba da jimawa ba zamu kawo k'arshen komai", "Allah ya yarda", "Amin In Shaa Allah",


   Hisham ne ya shigo da airpods a kunnen sa yana jin wak'a, sai dai yazo saitin Ammi ya cire ya gaisheta, ya juya kan Haidar yace  "Yaya barka da dare", "Yawwa" Ya amsa ganin Ammi, sanin rashin amsarwa zata so jin ba'a si, Hisham sanyi yaji a zuciyarsa na amsarwa Yaya Haidar, tun ranar ya daina masa magana, ko yayi baya amsa masa, yasan ganin Ammi ne, dan haka da gangan ya rik'a jan Haidar d'in da hira, dan dole ya rik'a amsa masa, har ya saki jiki suna hira har Ammi.



OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

  *HASKE WRITERS ASSO...*

SHAFI NA HUD'U


  Ta shirya tsaf cikin atamfar ta d'inkin riga da skirt, sai hijabinta iya gwiwa, "Bazan gaji da cewa kinci sunanki Bongel ba, wallahi ke kyakkyawa ce Hafsah", Cewar Asiya, Bongel tayi murmushi tace "Kema ai kyakkyawa ce", "Ban kama k'afarki ba, kefah kafin a samu mai kyau irinki sai an tona", "Uhmm ni dai muje ki rakani bana son zuwa ni

Please Login or Register in order to submit comment