Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tana kallon plate dake gabansa, Ya sauke ajiyar zuciya da cewa "Wallahi ba zan iya ci ba Mariya, komai yana neman rushe mun lokaci d'aya, tarin burikana na neman wargajewa", Hajiya Mariya ta dafa kafad'ar sa da cewa "Ka daina fad'ar haka Alhaji, In Shaa Allah sai mun cimma burin mu", "Taya kina ganin an soma bikin Haidar", "Somawa akayi ba'a d'aura ba, ka bari kawai ka gani sai na tabbata auren bai yiyuwa ba", "Taya hakan zai kasance", Shu'umin murmushi tayi tace "Ka bar komai a hannu na",



******************************

Bongel sam bata runtsa ba, raba daren tayi Sallah, tana rok'on Allah zab'in alkhairi a rayuwar ta, Da safe kasa karin kumallo tayi, ruwa kad'ai ta sha, ba yadda Asiya batayi da ita ba, taci abinci tak'i, Yau ya kamata ta tafi malumfashi amma jiran ta bakin Hisham taji ko ya samu nasarar wargaza aurenta da Haidar ya dawo kansa, yasa ta fasa tafiyar.



*********************************

Dada tsaf ta gama sauraren buk'atar da Hisham yazo da ita, nacewa suna son junansu da Bongel, Dan Allah ta maida auren kansu, Ta kalle sa tsaf ta kira sunan sa "Hisham" Ya amsa da "Na'am", "Kayi kuskure tun farko na b'oye soyayyar ka da Bongel, bakin alk'alami ya riga ya bushe, Bongel na riga na zab'ar mata Haidar a matsayin mijin aure dan sunfi dacewa", Zubewa yayi k'asa yana had'a hannayen sa biyu yace "Dan girman Allah Dada ki taimake ni ki aura mun Bongel", Duk da tausayin sa ya kamata, bata jin zata tab'a canza akalar auren zuwa kansa, Tace "Kayi hak'uri Hisham, Allah ya baka wacce tafi Bongel", Kasa tashi yayi da gurfanen sai hawaye da suka soma sauka kan kumatun sa, yana jin kansa na juyawa, a yadda soyayyar Bongel ta kamasa baya jin zai iya jure rasa ta, Dada mik'ewa tayi ta bar falon cike da tausayin sa, dan ba zata iya jure ganin sa a wannan hali ba.



*********************************
Haidar dare d'aya amma duk ya canza kasancewar rashin bacci da bai samu jiya ba, had'i da damuwa da tunani da suka taru suka masa yawa, Kansa ke tsananin ciwo yasha pain relief amma tamkar k'ara masa ciwon kan ake, a daren jiya sai da ya samu hanyar sub'ucewa auren kafin ya d'an samu natsuwa,


Wayarsa ya d'auka ya kira Hisham, Hisham wanda tun fitowar sa gidan Dada, ya samu wani wuri da babu mutane, yayi parking motar sa ya d'aura kansa kan sitiyari cikin tsananin damuwa, Kamar ya share kiran sai kuma ya d'auka, "Kazo guest house kai daa budurwar ka Hafsah", Yana fad'ar haka ya kashe wayar, Hisham ajiyar zuciya ya sauke yana fatan kiran ya zama alkhairi, Motar sa yaja zuwa gidansu Asiya,


Bongel da take jiran zuwan sa, tana jin yana waje, ta saka hijab ta fito, "Ki shigo mota zamu je wani wuri" Shine kad'ai abunda yace mata, Kanta ta girgiza alamar "A'ah", "Zuwa yanzu ya kamata kisan bani da wata manufa a kanki face ta alkhairi, so pls kizo muje", Ta d'an yin jim, kafin ta bud'e murfin motar ta shiga, Yaja su zuwa guest house, Ganin gidan da suka zo gabanta ya fad'i ta kai dubanta gare sa cikin fargaba, "Wallahi tallahi bani da niyyar cutar dake Bongel", Jin haka ta d'an samu natsuwa, Ta fito tana bin bayansa,


Turus tayi k'irjinta na dokawa ganin Haidar hakimce kan kujera, tayi saurin ja baya, Hisham ne ya mata alama da ta tsaya, Cak ta tsaya,


Haidar hannun sa ya soma tab'awa yana tafi, ya mik'e Yace "Wow despite ana shirin auren ki da wani amma kike iya  bin saurayi zuwa wurin sharholiyar da kuka saba", Hisham da mamaki ya bud'e baki zai yi magana ya dakatar dashi da hannu "Nasan me kake shirin fad'a, idan bata saba biyo ka nan ba, babu macen data san k'ima da darajarta da zata biyo saurayi gida ko da babu kud'in auren wani a kanta","No Yaya Haidar ba haka ba ne", "Idan baka sani ba Hisham, ina so yau ka sani da idona na ganku", Hisham k'irjin sa ya doka, "Hakan na nufin Yaya Haidar yaga Bongel ranar kenan" Yacewa kansa, Haidar ya juya kan Bongel

"Haidar ba sa'an auren irinki ba ne mai cike da d'auda da dattin zina, Taya kike tunanin zan auri macen data had'a shimfid'a da k'anina, macen data zama tamkar motar haya kowa hawan ta yake, Ni HAIDAR ABBAS MAISHANU bazan tab'a auren karuwa wacce ta had'a shimfid'a da k'anina ba", Cikin zafin rai da hasala da maganganun sa tace "Banyi ba, ban tab'a had'a shimfid'a da kowa ba, ka daina danganta ni da kalaman da ban dace dasu ba" Ta juya kan Hisham tace "Ka fad'a masa gaskiya, ka gaya masa abunda ya faru ranar", Hisham yayi shiru ya kasa magana, Cikin d'aga murya tace "Kayi magana Hisham, ka fitar dani daga mummunan zaton Yayan ka, na gaji na gaji" Ta k'arasa cikin karaji.


FOLLOW, VOTE AND COMMENT



*OUM MUHRIZ*
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

*HASKE WRITERS ASSO...*

ASHIRIN DA UKU

Hisham ya bud'e baki zai yi magana wani tunani yazo mishi yace "Yes mun had'a shimfid'a dake Bongel, bana tunanin akwai amfanin b'oyewar haka", Ya fad'i hakane sanin Yayan sa ba zai tab'a amincewa auren ba matuk'ar yaji sun had'a shimfid'a, shi kuma ya samu mallakar Bongel,


  Ba Bongel kad'ai ba hatta Haidar zancen ya dake sa, duk da yaga Hisham a kanta, amma ji daga bakin sa, ya k'ara hasasa wutar tsanarta a zuciyar sa, ita komai ta had'a k'arya, iya makirci banda makirci yadda take yi zaka rantse babu abunda ya shiga tsakanin ta da Hisham d'in, taso ayi manipulating d'in sa kenan Hisham ya bayar da shaidar k'arya, Ya fusgar da iska mai zafi daga bakin sa a fili yace "Mak'arciya makira"


Bongel kalmar "mun had'a shimfid'a dake Bongel" ke wa yawo a k'wak'walwa, dishi dishi ta soma gani, jiri na d'ibar ta, tuni ta zube k'asa.


  A rud'e Hisham yayi kanta, Haidar har yayo kanta shima sai kuma ya tsaya cak kamar wanda aka rik'e, ya juya ya fice falon.


Hisham a rud'e ya d'auko ruwa a fridge yana watsa mata, ta bud'e idon ta suka sauka kan Hisham, tayi saurin runtse su tana jin tsananin haushin sa, "Am sorry please Bongel, ki.....", Da hannu ta dakatar dashi da cewa "Enough Hisham", Ta mik'e ta nufi hanyar fita, da sauri ya sha gabanta yace "Dan Allah ki saurareni Bongel, wallahi tsananin k'aunar ki yasa nayi haka", Wani banzan kallo ta watsa masa mai cike da takaici, tana jin kamar ta zabga masa mari, k'auna zata sa ya zubar mata da daraja,

  "Kiyi hak'uri Dan Allah, i have to do this dan ganin mun mallaki juna" Hisham ya fad'a a marairace, A fusace tace "Bana buk'atar mu mallaki juna in har sai mutuncina ya zube a idon wasu, kasan yadda jifar mutum da kalmar zina take da zafi da rad'ad'i, kasan shaidar zina illar da take wa mutum, meyasa ka zab'i wannan hanya ta zama ta silar auren mu", "Ita kad'ai ce hanya Bongel", "Bani hanya na wuce" Ta fad'a cikin b'acin ran ganin bashi da niyyar gyara mistake d'in sa, Ba dan rai yaso ba ya matsa, Ta fita tana bin hanyar zuwa titi, Bak'in ciki da damuwan suka had'u suka cunkushe zuciyar ta wanda ba zai bayyanu ba, shikenan zargin Haidar a kanta zai k'ara tabbata, watak'ila ma yaje ya sanar dasu Dada dan kub'ucewa auren ta, shikenan mutuncin ta ya zube wurin Dada, Hawaye suka soma ambaliya saman fuskarta, wasu na bin wasu, har ta isa gidansu Asiya, taci sa'a bata tarar da kowa a tsakar gida ba, har ta shige d'aki, Asiya kad'ai ta tarar,


  "Lafiya kike kuka, me ya faru?"Asiya ta tambaya cikin damuwa, Kanta ta girgiza  tace "Ba komai, kawai auren Haidar ke d'aga mun hankali", "Ki kwantar da hankalin ki, kiyi ta addu'ar zab'in alkhairi" Kanta tayi nodding, Ta jawo kayanta ta soma had'awa, ta yanke shawarar tafiya yau, gaba d'aya hankalinta ya karkata gida, tana son jin d'umin jikin mahaifiyarta, ko zata rage wani rad'ad'i, Haka bata son sake had'a ido da Dada, bata san da wane ido zata kalleta ba, zata koma gida ta amincewa auren Jabeer su Dada a mayar musu kayan su, tafi son auren Jabeer akan Haidar, haka ba zata tab'a iya auren Hisham ba, danginsa na mata kallon mazinaciya wanda tasan abu mai wuya ne su amince ya aure ta, ba wanda zai so dan' sa ya auri mazinaciya.


***************************************

Haidar daga guest house kai tsaye gidan Dada ya nufa, da k'udurin lalata auren sa da Bongel, Sama
Sama ya amsa gaisuwar masu aikin, Dada na kishingid'e kan kujera bacci na son d'aukar ta, Ganin Haidar tace "Ka gama fushin, tunda kaji na nemar maka mata ka d'auke k'afar ka daga gidan nan", "Ina wuni?" Ya fad'a yana kawar da zancen, "Lafiya lau Ango kasha mai", Fuska ba yabo ba fallasa ya zuana saman carpet yace "Dada Dan Allah ina neman alfarma a wurin ki", "Ina jin ka", "Dan Allah ki janye zancen aurena da yarinyar nan, budurwar Hisham ce", Murmushi tayi irin na manya tace "Haidar kenan, idan kasan alkhairin da na hango maka tattare da Bongel da baka ce haka ba, shin ko dan yaron ka ba zaka amincewa auren ba", Da mamaki yake kallon Dada, dama itace Auntyn Irfan, itace Irfan ke yawan magana, taya d'an sa ya shak'u da karuwa, Dada ta katse masa tunani da cewa "Kyau, nasaba, tarbiya, natsuwa da halayya nagari ake nema wurin mace ta gari, Bongel duka ta had'a, ina maka sha'awar auren ta dan tarbiyar yaron ka, da kai kanka ka samu natsuwa da kula a tare da ita", Ya bud'e baki zai sake magana Dada ta dakatar dashi da cewa "Auren ka da Bongel kamar anyi an gama, idan kaga ba'a yi ba to bana numfashi a doron k'asa, kai ko bana raye zan bar wasiyyar tabbatuwar auren ku",

Kansa ya dafe, wacce irin masifa ce ya tsinci kansa a ciki, Taya yaron sa zai samu tarbiya wurin wanda ta kai k'arshe wurin tsantsar rashin tarbiya, taya zai samu natsuwa a tare da Karuwa, ko shakka babu ta zama fuska biyu, macijin sare ka nok'e, Dada kallon kitso take wa rogo, ta b'oye ainihin kalar ta, ta nunawa su Dada ita ta kirki ce, matuk'ar ya aure ta sai ta gwammace gidan yari akan nasa, da k'afafun ta zata bar gidan, Ban da baya son jefa Dada da iyayen nasa a damuwa, da cire k'imar k'anin nasa a idon iyayen su, da ko shakka babu yau zai fasa k'wan dan gujewa auren ta, sai dai girman soyayyar dake tsakanin sa da k'annin sa, da gudun b'acin ran iyayen su, dole ya bar abun a ransa, Ya mik'e ya fita ba tare da ya ma Dada sallama ba, tabi bayan sa da cewa "Watarana da kanka zaka yi mun godiyar gatan da na maka",


******************************

"Kina ganin ya dace ki tafi ba tare da kin sanar da Dada ba" Asiya ta fad'a, Bongel ta numfasa tace "Bana son abunda zai mun shamaki da tafiyata yau", "Ni sai nake ganin ba zata tsayar dake ba", Bongel ta girgiza kai tace "Bar ni kawai na tafi, idan na isa zan kirata", "Shikenan Allah ya tsare ya kai ki lafiya", "Amin", Aina'u ce ta shigo tace "Ga napep din an samu", "Yawwa Aina'u zo ki tayani da wannan" Ta mik'a mata k'aramar jakar ta,

  Asiya ta mata rakiya har waje, tana cewa sai mun zo.


****************************

Dada ke had'a kayan fitar bikin Bongel, kala biyar masu kyau da tsada, komai ta saka hadda jewelries, su takalmi da mayafi, alkyabba mai kyau wacce za'a saka mata idan za'a kawota, Anty Mami itama yar' Dada ce tace "Gaskiya Dada kina ji da wannan auren, ban tab'a ganin auren da kika dage a kansa ba irin wannan", Dada tayi murmushi tace "Alkhairin ciki nake hangowa", Anty Mami tace "Allah ya tabbatar da alkhairin sa", "Amin, ki kira Basira kuzo ku tafi, ku biyu kun isa ba sai anyi gayya ba", Anty Mami tace "Toh" tana mik'ewa ta nufi sashen Inna.


*************************

Su Aunty Mami suka dawo suke sanar da Dada, Bongel ta wuce, Dada bata nuna musu bata san wucewar Bongel ba, gudun su ga laifin ta, Tace "Au na manta yau ne tafiyar ta, ku ajiye kayan goben sai a kai mata can garin su, tare da katin gayyata da sauran abubuwan da ya kamata a kai", Aunty Mami tayi dariya tace "Dada tsufa ya soma kama ki", "Kinci gidan ku" Cewar Dada, Suka yi dariya ita da Basira,


  Dada mamakin tafiyar Bongel d'in take ba tare da ta sanar da ita ba, bayan sunyi kan idan ta shirya ta kirata, zata aika Hamza direba ya kai ta, duk yadda akayi wani uzurin babban yasa tasan Bongel ba zata tafi haka kawai ba, Ta tabbatarwa kanta da k'ok'arin hana zuciyarta ganin laifin Bongel.


***********************
Bongel sun iso garin malumfashi lafiya, Direba da ya d'auke su ta buk'aci ya kaita gida, ta k'ara masa kud'i, Har ya sauketa ta shiga gidan bata ci karo da kowa d'an gidan su ba, Abu ne yazo da gudu ganin ta ya rungumeta, Ramla ma yau bata je gidan aiki ba ta tashi da ciwon kai, Ta taso ta rungume ta,


  Nene dake dakan yaji, ta tsayar da dakan tana duban yar'ta cike da farin cikin ganin ta, "Nene jam bandu", "Jam Bongel", Ramla da Abu suka karb'i kayan hannun ta suna shigar mata dashi ciki, Itama tabi bayan su, Nene ta ajiye dakan ta shiga ciki, ba abunda take buk'ata kamar ji daga bakin Bongel, Nene tace "Su Ramla su fita waje zasu yi magana",


Ta kai dubanta ga Bongel da cewa "Bayan tafiyar ki wasu sun zo kan neman auren ki, da kaya hadda kud'i, ina son jin k'arin bayani", Bongel ta bud'e baki da niyyar cewa Nene bata son auren, ba da amincewarta ba, sai kuma tayi shiru da tunanin gara ta fara samun Hamma Siddiku da maganar, "Kinyi shiru", Bongel ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da yatsun hannun ta alamar kunya take ji, Nene tayi murmushi tace "Na manta jinin fulani kike, shikenan  Allah ya tabbatar da alkhairi", Bongel a ranta tace "Kiyi hak'uri Nene da na soma b'oye miki abubuwa masu muhimmanci akan rayuwata, bana son k'ara miki damuwa kan wanda kike ciki",



****************************
Ammi itama bakin rai take wurin ganin auren Haidar da Bongel ya tabbata, haka kawai Allah yasa mata k'aunar Bongel, duk abunda tasan mace na buk'ata a kayan lefe ta had'a akwati goma sha biyar, Haka komai na buk'atar gida ta siya kama daga gadaje, kujeru, kayan kitchen da sauran kayan amfanin gida, yau take son yi ma Hajiya mariya  kan su turo a kwashe kayan Hafsa, tun rasuwarta basu kwashe ba, a cewarsu tunda Rauda zata maye gurbin ta, a barsu.



*********************************

"Yanzu rashin ta idon har ta ka ga ki kirani kina cewa azo a kwashe kayan Hafsah" Hajiya Mariya ta fad'a cikin masifa, Ammi cikin sanyin murya tace "Kiyi hak'uri ba haka bane, dangin amaryar ne suke son yin jere, kwanaki na matsowa", "Dangin Amarya ko dangin tsiya, mai aikin Dada ce fa za'a aura masa, me suke dashi da zasu jera mata, ina jin k'warya da ludayi su za'a cika d'akunan dasu dan naji ance fillo ce", Ammi tace "Ni dai ba wannan ba, kuma ban kira ayi tashin hankali ba", "Tashin hankali ai kun neme shi, tunda kuka k'i jinin mu, kaya dai ba zamu kwashe ba, dan bamu da buk'atar su, aba Amarya dangin tsiya, sannan abu na k'arshe ku fara had'a kayan Irfan, zan zo d'aukar sa, ba zamu tab'a amincewa kulawarsa ta koma hannun bagidajiya dangin tsiya ba", Ta kashe wayar, Ammi ta bi wayar da kallo tana maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un", Su Hajiya Mariya na neman su zamar musu masifa,



*******************************

Washegari bayan sun gama karin kumallo wanda Bongel tayi sa ne kawai ba dan tana jin dad'in ci ba, Taje b'angaren Hamma Siddiku,


  Tayi mamakin ganin sauyi a tare dashi, wanda wannan karon ya sakar mata fuska sab'anin lokutan baya, wanda sakin fuskar ba har zuci ba ne, dan yaci amfanin ta ne, Ta numfasa tace "Kayi hak'uri Hamma da tafiyar da nayi ban dawo ba", "Ah ba komai ai, na fahimce ki Bongel gashi ana shirin auren ki", "Idan ba damuwa ina son a mayar da auren kan Jabeer, bana ra'ayin wancan", Wani mugun kallo Hamma Siddiku ya watsa mata yace "Yau ga yar jakar uba, ke k'undun uban ki, ni zaki mayar mutumin banza, har na bayar da auren ki kizo da wani zance, ban da kina sakarya ga inda arzik'i yake zaki nemi tsiya, toh idan kinga ba'ayi auren ki da dan' birni ma, mutuwa kika yi, tashi ki bani wuri kafin na shure ki", Jiki na rawa Bongel ta fice.



*******************************

An shirya komai na kayan aure da za'a kawo gidan su Bongel, hadda lefe, katin gayyata, goro da sauran tarkace, Mutum biyar mata kad'ai suka shirya tafiya, Cikin motoci biyu jeep prada, kowannen su yasha sutura mai kyau da tsada, Dada wanda tasan basu da gutsiri tsoma ta zab'a, dan kar aje aga gidansu Bongel a dawo ana gulma.



Bongel dake tsakar gida tare da Nene dasu Ramla, Akwati suka ga an soma shigowa dasu, Bongel gabanta ya fad'i hakan na tabbatar mata daga danginsu Hisham, sai dai abunda ta kasa ganewa auren ta da Hisham ne ko Haidar zai tabbata, Da tunanin haka tayi saurin tashi ta shiga d'aki, Nene ma tabi bayan ta, dan tana gani tasan kayan auren Bongel ne,

Dije da fatsuma suka kasa suka tsare, suna yak'e wanda yafi kuka ciwo, ganin uban kaya ya k'ara shaida musu ba k'aramin attajiri Bongel zata aura, ko shakka babu gidan daula da hutu zata, wanda ko a mafarkin su basu zatar mata haka ba.


Su Aunty Mami basu jima ba, suka tafi, bayan wucewar su Nene ta fito, lokacin har Ramla taje da sanar da Goggo Hajjo sunzo, da sauran yan' uwan Nene na garin, mak'wabta ma sun soma cika gidan, kowa na fad'in albarkacin bakin sa, na had'uwa da yawan kayan, Nene tsoro ne ya shiga zuciyarta, su ba kowa ba, basu da komai, taya yarinyar su zata yi auri cikin irin wannan ahalin, hasalima basu da komai da zasu mata kayan d'aki, Data samu Goggo Hajjo da maganar, ta kwantar mata hankali da cewa, Allah ne yayi wannan had'in, ba iyawar su ko dabara ba, kuma su san irin gidan da suka nemi auri, ba zasu buk'aci wani abu daga garesu, kawai suyi k'ok'arin yi daidai k'arfin su, Da haka Dada taji k'arfin gwiwa,



  Bongel kuwa kwana tayi juyi kan gado, da tunanin waye ango ta tsakanin Haidar da Hisham, a halin yanzu duka bata sha'awar auren d'aya daga cikin su, Haidar yana munana zato a kanta, da nuna mata k'iyayya k'arara, Hisham haushin sa take ji sosai na d'aura mata zina dan kawai cikar burin sa, hakan na nufin bai san darajarta ba, idan ya sani gara yayi hak'urin rasa ta, akan rusa mata darajar ta, Ta k'arasa da cusa kanta cikin pillow tana hawayen bak'in ciki.




OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

  *HASKE WRITERS ASSO...*

ASHIRIN DA HUD'U


Haidar tashin sa daga bacci kenan wanda da k'yar ya samu runtsawa a daren jiya saboda damuwa da tunanin auren Bongel da suka hana zuciyar sa sukuni, gaf da sallar asuba bacci ya d'auke sa K'aramin agogon dake kan bedside drawer ya kalla, 9:30 daidai salati yayi ya sanar da ubangiji, yana mamakin nauyin baccin da ya d'auke sa, Toilet ya shiga yayi brush ya d'auro alwala ya fito, ya kabbara sallah, yana idarwa kiran Abba na shigowa wayar sa, sai da ya kammala azkar, kana yabi kiran Abba, ya d'auka yace yazo yana son ganin sa.



   Ba tare da ya tsaya wanka ba, ya nufi sashen Abba dan sam baya wasa da abunda ya danganci iyayen sa,  Kamar ko da yaushe a falon sa ya same sa, Yace "Abba barka da hutawa", "Yawwa Barka", Ya zauna kujerar kusa da Abban, K'aramar jaka ya mik'a masa yace "Katin auren ka ne a ciki, gasu nan sai ka rabawa yan'uwa da abokan arzik'i, ina fatan kasan an kai lefe jiya", Haidar zancen Abba ya k'ara masa damuwa a kan wanda yake ciki, hakan na nufin auren sa da ita babu fashi tunda har an buga kati an kai lefe, taya zai fahimtar dasu wacece ita, da yasan haka da tuni ya amincewa auren Rauda, dan gara ita akan auren Karuwa, Abba ya katse masa tunani da cewa "Kayi shiru", "Toh In shaa Allah" ya furta, yana d'aukar jakar ya fita.



Kan gado ya jefar da jakar, ya shiga band'aki ya sakar ma kansa ruwan shower ko hakan zai rage masa damuwa.



*********************************

Bongel cikin bacci ta soma jin muryar Goggo Hajjo na fad'in "Ina Amaryar take?", Idonta ta mutsitssika tana tashi zaune, baccin bai isheta ba, kasancewar bata samu runtsawa ba sai bayan sallar asuba,


   "Au Bacci kike yi, to tashi ga ruwa can na had'a na wankan ki", Cewar Gwaggo Hajjo, Ta yamutsa fuska alamar bata so, wanda Hajjo ta d'auki hakan matsayin kunya, Ba dan rai yaso ba, ta mik'e ta shiga wanka da ruwan turare da had'in wasu itatuwa masu gyara jiki, tayi tsarki da wasu ruwa a buta da ta bata, Ta fito tana k'yalli tana k'amshi, ta shafe jikinta da mai, ta saka atamfa d'inkin riga da skirt cikin kayan fitar biki, tayi matuk'ar  kyau, yan Allah sanya alkhairi nata faman kai kawo gidan, Su Dije kuwa bak'in ciki da hassadar fal zuciyar su.


   Bongel kuwa tunanin ta ya tafi kan son sanin wa zata aura, tana jin kunyar tambayar d'aya daga cikin yan' gidansu, zuwan k'awayen ta wanda sukayi primary tare, yasa ta d'an ware suna hira dasu a kai kai, Hajaru d'aya daga cikinsu tace "Bongel kin more samun miji Allah ya bamu danshin ki", Saura suka ce "Amin", A zuciyarta tace "Da kunsan irin auren da zanyi babu mai marmarin irin sa, in dai har ya kasance Haidar zan aura", Tana rufe baki, Mairo tace "Hafsah amaryar Haidar", A razane ta d'ago ta kalleta da cewa "Ina kika san sunan angon", Dariya tayi tace "Gashi nan rubuce a katin gayyata", Wasu miyau ta had'i na bak'in ciki had'i da fargabar wacce irin rayuwar aure zatayi da mutumin da ya nuna mata k'iyayya fiye da kowa a duniya, A zahiri tayi k'ok'arin b'oye damuwarta but a bad'ini damuwa ce shimfid'e a zuciyar ta.



*****************************

Alhaji Sani maigoro ya kalli Iv d'in ya k'ara kalla, Cikin tsananin b'acin rai yace "Yanzu dan cin fuska ni Alhaji Abbas zai aikowa katin gayyata hadda goro", Hajiya Mariya tace "Ka daina mamakin halayyar su, ni duk abunda zasuyi yanzu ya daina bani mamaki", Ya jinjina kai yace "Wallahi ko ta halin k'ak'a sai na cimma burina, na daina tsoro ko fargabar komai", "Haka nake so naji kace Alhaji, nima yanzu zanje na d'aura musu nawa", Ta karb'i IV a hannun sa, tana fita.



************************

Ammi na zaune tare da k'annen ta, suna shirye-shiryen yinin biki da d'auko amarya jibi idan an d'aura aure, Hajiya Mariya ta shigo kamar an jefo ta babu sallama, Kowa ya kai duban sa gare ta, Ammi tace "Sannu da z.......", Ta katse da d'aga hannu tace "Dakata ba wannan ya kawo ni ba, ina irfan shi nazo tafiya dashi", Ammi tace "Haba Mariya abun duk bai kai haka ba", Hajiya Mariya ta k'ara gyara tsayuwa tace "Ni fah babu sauran mutunci tsakanina daku, jikana nazo a bani", Anty Binta d'aya daga cikin k'annen Ammi tace "Haba Maman Hafsah, bai kamata ana jin kan ku ba, ina ce an zama d'aya", "Wallahi ba'a zama ba, idan an zama ba zasu k'i jinin mu ba, dan haka kawai a bani Irfan",


  Abba ne ya shigo rik'e da hannun irfan, yace "Gashi mun yarda kulawar shi ta koma hannun ku", Kowa yabi Abba da kallo mamaki, Ammi ta bud'e baki da zumar yin magana ya mata alama tayi shiru, Ita kanta Hajiya Mariya was shocked ba haka tayi tsammani ba, jiki a sanyaye taja hannun Irfan d'in tana ficewa ba

Please Login or Register in order to submit comment