Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

firgici ya dabaibaye su lokaci d'aya, Kafin d'ayansu yayi magana Haidar ya shige ciki ba tare yace musu uffan ba, D'akin ya shiga ya kwanta, ciwon kai sosai ya dawo dashi gida, wanda tunani da stress ya haddasa masa,


Hisham ya sauke ajiyar zuciya da cewa "Wai! Na d'auka yaji zancen mu", Rauda tace "Wallahi nima har hantar cikina ta kad'a", Hisham yayi dariya da cewa "Sarkin tsoro, bara na tafi sai na kira ki", Tace "Ok sai anjima", Ta tashi ta nufi d'akin,


Ganin Haidar kwance tasan ba lafiya ba, bakin gadon ta zauna tace "My dear ina fatan lafiya", "Headache" ya bata amsa a dak'ile, "Ayyah sorry kasha magani", Ya mata nodding kai, Ta kwanta gefen sa tare da saka hannayen ta ta rungume sa, ba dad'in hakan yaji ba but bai hana ta ba, sai idonsa da ya runtse yana jiran zuwan bacci.


******************************

Bongel sun soma exams, kullum bata da lokaci tana makaranta sai yamma lik'is take dawowa, ko jarabawar safe suka yi sai ta tsaya cikin school tayi karatu, Idan ta dawo haka zata yi aikin gidan, dan Rauda da kanta tayi wa Haidar magana ya raba musu girki, ta gaji da yi ita kad'ai, Haidar ba musu yace kowaccen su ta rik'a yi kwana biyu biyu dan shi kansa yana buk'atar girkin Bongel na Rauda cin dole yake masa, Bongel babu musu ta karb'a, duk da k'asan zuciyarta taji babu dad'i wane irin raba girki ne wanann, babu miji ba dan tana son kusancin su da Haidar ba, sai dai a saninta ranar girki kai ke da miji, amma ita hatta ranar girkin nata Haidar yana wurin Rauda, wane irin rayuwar aure ne ta tsinci kanta, ta kan yiwa kanta tambayar lokuta da dama,



Yau ma ta dawo gida a gajiye, ta shiga kitchen tayi girki, kana ta koma d'aki, Bak'uwar number taga na kiranta, Ta d'auka, "Assalamu alaikum Adda" Taji muryar Ramla, "Wslm Ramla ya gida?", "Lafiya lau Adda", "Ina kika samu waya", Tana dariya tace "Yaya Hisham ne ya siyan mun wai mu rik'a kiran ki kullum", "Hisham" Bongel ta maimaita a ranta tana mamaki, Ramla ta katse tunanin ta da cewa "Ga nene", Nene ta karb'i wayar da yin sallama, Bongel ta amsa tace "Nene ina wuni?", "Lafiya lau, ya mutan  gida da karatu?", "Alhamdulillah", "K'anin mijinki yana k'ok'ari sosai, ki mishi godiya kullum baya gajiya da mana hidima", Bongel tace "In Shaa Allah" K'asan zuciyarta mamakin Hisham d'in take, hakan na nufin soyayyarta har yau na cikin zuciyar sa shiyasa yake kyautatawa ahalin ta, ko kuwa yana yi ne kawai dan kyautatawa shine ta kasa ganewa, Ta katsewa kanta tunanin da cewa "Nene ya shirin Bikin saude", "Alhamdulillah yanzu ma ai saura sati biyu, zaki zo dai ko", Tace "In Shaa Allah" tana jin natsuwa a ranta dama ta tambayi Nene ne dan son jin ko Hamma Siddiku ya sameta kan zancen kayan d'aki, sanin k'aramin halin sa ne ya tadawa Nene hankali, abunda bata k'auna, Sukayi sallama ta kashe wayar.


***************************

"Ya kamata muje asibiti dan sanin lafiyar cikin ki", Cewar Hajiya Mariya, Rauda dake kange da waya a kunne tace "Toh Mummy", "So ki shirya gobe zan zo na d'auke ki mu tafi", Tace "Toh", "Yawwa sai anjima", "Bye Mummy", Ta kashe wayar tare da shafa cikinta tace "Babyna nasan ma kana lafiya" Tayi murmushi dan ba k'aramin son cikin take yanzu ba.


*****************
"Wai ke ba zaki hak'ura da Hisham ba, mutumin nan fah ba son ki yake yanzu ba, kullum cikin wulak'anta ki yake" Cewar Fido, Ihsan tace "Hmm Fido kenan kina tunanin zan bar sa yaci bulus, wallahi idan kin ga na hak'ura da Hisham to mutuwa nayi", Ta jinjina kai tace "Shikenan Allah ya taimaka", Ihsan ta amsa da "Amin", Tana taunar chewing gum kamar tsohuwar karuwa.


***********************

Yau ranar girkin Rauda ce, hakan yasa dan dole ta tashi da wuri ta shirya Irfan, ta shiga kicin had'a breakfast, ruwan shayi tayi da irish, dan sune mafi sauk'i, Haidar kad'ai yaci a cewarta zuciyarta ke tashi, Bayan ya kammala ci ya mik'e zai fita, Tace "My dear anjima Mummy zata zo muje asibiti duba lafiyar babyn ka", Kansa yayi nodding yace "Ok" ya saka hannu a aljihu ya zaro kud'i masu yawa ya bata sanin asibiti dole a buk'aci kud'i, Tasa hannu ta karb'a tace "Thanks",


***********************

Likita bayan ya gama gwaje gwajen sa ya buk'aci ganin sa office d'in sa, Suka shiga, Ya gyara zaman madubin dake idonsa ya kai dubansa gare su da cewa "A bisa bincike da mukayi gaskiya bata da ciki", "What" Suka fad'a a zabure, Dr ya jinjina kai yace "K'warai bata d'auke da juna ba, face infection wato cutar sanyi wacce ta mata mugun kamu, shine dalilin da yasa period d'inta ya d'auke na tsawon lokaci", Rauda tuni hawaye suka soma zirya kan kumatun ta tace "Na shiga uku wayyo ni Allah na", "Subhanallah ba wani babban matsala bane ai, za'a d'aura ki kan medication wanda In Shaa Allah zaki samu sauk'i, sai dai ki kiyaye inserting abubuwa a gabanki, ba komai za'a baku mata ku cusa a gaba ba, mafi yawa shi ke jawo muku matsala", Hajiya Mariya kad'ai tayi k'arfin halin amsa sa, Rauda kuwa kuka tamkar wacce akayi wa mutuwa,

Dr ya rubuta musu magunguna da allurai da zata rik'a karb'a, Suka fito, Rauda na kuka, a mota Hajiya Mariya ke lallashin ta tace "Ki daina kukan, ai ba cewa akayi ba zaki haihu ba, yanzu ki fara treating infection nasan kina gamawa ciki zai shiga", "Mummy me zan cewa Yaya Haidar yanzu bayan na gama fad'a masa ina da ciki, ga shegiyar can sai tamun dariya", Hajiya Mariya taja ajiyar zuciya da cewa "Kiyi shiru kar ki fad'awa kowa yanzu har sai mun gama maganin infection d'in, ki barsa a cewar kina da ciki", Ta jinjina kai da cewa "Toh", K'asan zuciyarta zallar bak'in ciki ne, har suka isa gida tana kuka, Ta sauka aka wuce da Hajiya Mariya gida.



Tana ganin kiran Hisham tak'i d'auka, b'acin rai da damuwar da take ciki bata jin magana da kowa, yanzu ita bama ta fitar Bongel gidan take ba, jin cewar bata da ciki ga infection yafi komai d'aga mata hankali.


Hisham yayi tsaki yana cillar da wayar gefe, "Ko gidan uwar wa ta ajiye wayar oho" Ya fad'a cikin takaici, yaso samunta yanzu dan aiwatar da plan d'in sa, a yadda yake ji tamkar yaje ya fitar da Bongel daga gidan Haidar ta dawo gidan sa.



FOLLOW, VOTE AND COMMENT


OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

*HASKE WRITERS ASSO...*

ARBA'IN DA SHIDA

SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298


Alhaji Sani maigoro ya yarce zufar data keto masa a goshi jin zancen Hajiya Mariya, Fuska d'auke da zallar damuwa da bak'in ciki yace "Ban tab'a jin labari mara dad'i irin wannan ba, wai ma taya za'a ce babu ciki, shin dama ba asibiti ya tabbatar ba hasashen ku kawai ba tare da wani gwaji ba", Hajiya mariya ta marairaice fuska tace "Wallahi ranar da naji, naga alamar ciki tare da ita", Tsaki yayi yace "Burina da nake ganin ya gabato, yanzu ya k'ara nisa", Ta d'aura hannu kan kafad'ar sa tace "Kayi hak'uri Alhaji, Sannu bata hani ga zuwa sai dai a dad'e ba'a je ba, kuma ai wani jinkirin alkhairi ne", Ya jinjina kai yace "Ko nawa ne ni zan bada dan ganin an kawar da cutar sanyin dake jikin ta, ta samu d'aukar ciki", "In Shaa Allah zan yi k'ok'arin ganin haka", "Allah yasa" Ya fad'a yana fusgar da iskan baki mai zafi.


*************************

Rauda ta d'auki shawarar mahaifiyarta sam bata nunawa Haidar alamar babu ciki ba, Yau ma tashi tayi da kakarin amai, ta shiga toilet tana yi kamar zata amayo yan' cikin ta, Haidar yabi ta ya rik'e ta yana mata sannu, Bayan ta dakata, ya jawota suka dawo d'aki, Ta kwanta jikinsa tana jan numfashi da k'yar kamar da gaske,


  "Da kuka je asibiti me Dr yace, banji kimun wani bayani ba" Cewar Haidar, "Yace Babyn lafiya lau, ba wata matsala", "Ina result?", "Ai bai bayar da komai ba, sai magani da ya rubuta mun muka siya", Ya bud'e baki  zai yi magana, yayi shiru, Ajiyar zuciya ta sauke da yin hamdala a zuciyarta bai d'ago ta ba.


**************************

Bongel bata da exam sai bayan sati d'aya wacce itace jarabawar k'arshe ta semester, Yau tana gida bata fita school ba, sha'awar waina ta tashi dashi, Hakan yasa tun da asuba data tashi sallah ta jik'a shinkafa, Ana kiran azahar ta kammala ta zuba a kuloli, har da Ammi ta d'ibarwa, ta jere a k'aramin basket, ta yafa mayafinta zuwa kai mata, sam Haidar bai mata iyaka da zuwa b'angaren Ammi ba, duk lokacin da taga dama take zuwa ba tare da ta tambayi izinin shi ba, Fitowar ta d'akin akan idonsa, yana zaune falon tare da Rauda, Kyau yaga ta k'ara masa sosai, ya tsinci kansa da kasa d'auke idon sa kanta, yana jin wani yar, K'arasowar cikin falon yasa yayi saurin kawar da kansa, Cikin sanyin murya tace "Ina wuni?", "Lafiya" Ya amsa ba tare da ya kai dubansa ba,


Har ta kai k'ofa, Ta jiyo muryarsa "Ina zaki?", "Wurin Ammi" Ta bashi amsa, Bai sake cewa komai ba, Jin shiru ta bud'e k'ofar ta fita, Rauda kuwa ta cika tayi fam ganin irin kallon da yake wa Bongel, Bai bi ta kan Rauda ba sai ma mik'ewa da yayi, ya nufi dining, Ya hau ci wainar wanda ta masa masifar dad'i.


*******************
Ammi sosai taji dad'in wainar da Bongel ta kawo mata, Tayi ta saka mata albarka, Tana k'ara yaba hankalinta, Ko shakka babu Dada babban gata tayi wa Haidar data had'a sa da ita, Rauda tun zuwanta gidan bata tab'a kawowa Ammi ko ruwa ba, Bongel ta jima a sashen kafin ta koma, Ammi ta bata kyautar humrah mai masifar k'amshi, ta mata godiya sosai.


*********************

Rauda kwata kwata tak'i ba Hisham damar su had'u, a ganinta sai ta gama da matsalar cikin da akace babu, kafin ta dawo kan fitar Bongel gidan, Hisham ba k'aramin haushin hakan yaji ba, amma ya d'auki alwashin shawo kanta, dan yana ganin da taimakon ta zai cika burin sa, Yanzu ma kiranta yake tak'i d'auka bai fasa kiran ba,


Haidar dake zaune gefen Rauda yace "Ba kiran ki ake ba", "Eh wayar bata da amfani", Ta fad'a tana k'ok'arin kashe wayar wanda kiran ya sake shigowa, Haidar ya kai dubansa sunan Hisham rubuce kan screen d'in, Ya kawar da kansa tamkar bai gani ba, yana cigaba da danna wayar sa.



****************************

"Alhamdulillah yau mun kammala jarabawar level one" Cewar Asiya, Bongel ta nisa tace "Lokaci na gudu kamar jiya muka shigo makarantar gashi har mun kammala level one", Asiya tace "Wallahi kuwa, haka watarana makarantar zamu gama baki d'aya", "Allah ya nuna mana lokacin yasa mu gama a sa'a da nasara" Cewar Bongel k'asan zuciyarta tana fatan ganin wannan ranar, ranar da zata cika burin sa, Asiya ta amsa da "Amin Amin, mu tafi gida ko?", Bongel ta dan' yi jim tace "Jibi za'a fara bikin Saude, jiya Nene ta kirani kan batun zuwana sai dai abu biyu ne zasu katange ni ga zuwan", "Me zai hana ki zuwa bayan kullum kina damuna kan cewar kinyi kewar su", Bongel taja numfashi tace "Na farko ban san ta yadda zan tambayi Haidar zuwan ba, na biyun had'uwata da Hamma Siddiku, nasan ba zatayi kyau ba, nayi mamakin tsawon lokacin da aka d'iba ma bai waiwayo ni ba, nayi imani da Allah matuk'ar naje ba tare da kayan d'akin da ya buk'ata ba sai nayi dana sanin zuwa na", Cike da tausayin ta Asiya tace "Tambayar Haidar zuwan ki ba matsala ba ne, matsalar itace Hamma Siddiku, amma ina so ki sani addu'a bata bar komai ba, ita zamu dage da yi", Bongel ta jinjina kai duk da tana jin karaya, amma tayi imani da Allah, yana sane da ita, shi zai kawo mata mafita a rayuwarta da tayi mata d'aurin goro.



****************************

Bongel tana dawowa gida, tayi wanka ta saka doguwar riga mara nauyi bayan ta shafe jikinta da humra da Ammi ta bata, K'amshi mai sanyi da dad'i na fita jikinta, gashinta tayi bakin, jelar sa ta sauka kan gadon bayanta, bata saka d'ankwali ba, Ta zauna k'asan carpet tana had'a handout d'inta na level one wuri d'aya tana sakawa a ghana must go,


Haidar yayi kusan minti biyar tsaye yana k'are mata kallo, a zuciyarsa ya shaida tana da kyau, had'i da komai ake buk'ata a jikin ya' mace, Sai dai kyan nata a wurinsa yake ganinsa kyan dan' maciji, "Fure a cikin juji" Ya furta wanda caraf a kunnen Bongel, Ta d'ago ta dube sa, ta mayar da kanta k'asa ba tare da ta fahimci me yake nufi da kalmar ba, Hannun ta tasa ta jawo dan' kwalinta dake kan gado, ta rufe kanta, Haidar k'arasowa yayi cikin d'akin, K'amshin humra ke dukan hancin sa yana sake jefa sa wani yanayi, Gaf da ita yazo yasa hannu ya d'agota, K'irjinsu tamkar zai manne da juna, ta runtse ido tana saukar da kanta k'asa, Hannu d'aya yasa ya tallabo hab'arta, bakinsa kawai taji cikin nata, yana tsotsar labb'anta na k'asa, Kasa aiwatar da komai tayi sai k'afafunta dake rawa, Haidar kissing d'inta yake kamar zai cire mata lips, Soma fita hayyacin sa yayi, Yayi k'ok'arin controlling kansa, ta hanyar tureta, tayi baya kamar zata fad'i, Idonsa ya runtse ya girgiza kai, Kana ya bud'e su gaba d'aya sun canza launi,  Muryarsa na fita da k'yar yace "Ki shirya gobe kije gida", Ya juya ya fita d'akin,


K'irjin Bongel yayi mummunan dokawa, kar dai ya shirya rabuwa da ita, Kanta taji ya mugun sara mata, Ta soma ambaton Allah, a iya saninta babu soyayyar Haidar a zuciyarta, but ta rasa dalilin jin fad'uwar gaban rabuwa dashi, ta danganta hakan da damuwar Nene da k'annen ta bata son ganin fuskokin su d'auke da damuwa, amma tana fatan rabuwar tasu ta zama alkhairi, tana fatan samun sauyi ne a rayuwarta, "Shin Dada da Ammi sun san ya yanke hukuncin kuwa, da amincewar su ko sab'anin haka?", take wa kanta tambayoyin da babu mai bata amsa, Da sak'e sak'e kala kala ta had'a kayanta a akwati guda d'aya, komai na buk'ata ta saka ciki, Daren ranar bata runtsa ba, k'iyamul laili tai tayi, tana sanar da ubangiji damuwarta.


***********************

Tun tashinta komai sukuku take yin sa, tayi wanka ta shirya, ta saka hijab d'inta jalbab, Ya mata kyau sosai, komai ta kasa sakawa cikinta hatta ruwa, Zaune take bakin gado tayi jigum, Irfan ya shigo yace "Aunty ina kwana?", "Lafiya lau my boy" Ta amsa tana murmushin dole, "Kizo inji Daddy", Mik'ewa tayi taja akwatin ta sanin kiran nada alak'a da tafiyarta,

  Haidar na tsaye, Rauda na gefensa, Bongel ta fito, Ta gaishe sa cikin ladabi ya amsa, "My dear bara na gyara maka necktie d'in ka" Cewar Rauda cikin salo tana gyara masa tana wani shafo wuyansa wanda da gangan take yi, Bongel kallo d'aya ta musu ta kawar da kanta, Bai hana Rauda ba, sai hannu da ya saka a hannu ya fiddo envelope ya mik'awa Bongel,


Kanta yayi mummunan sarawa sanin ko shakka babu takardar sakin ta ce, tasa hannu ta karb'a, ya jefa cikin k'aramar jakarta, "Direba na jiranki waje zai kai ki", Ya fad'a, Kasa ce masa komai tayi sai akwatin ta da taja tayi gaba, Irfan yabi bayanta da cewa zan bi ki, Haidar ya jawosa yace "Dawo, school zamu je na kai ka", Bongel na fita, Haidar shima ya fito tare da Irfan,


  Rauda tsalle tayi ta fad'a kan kujera da cewa "Wayyo Allah na dad'i, shikenan ya rabu da yar' iska, wai mafarki nake ko gaske", Ta mari kanta, "Wallahi da gaske ne, Allah ya hutar dani, ya rabu da ita ba tare da na wahalar da kaina ba, dole na kira Hisham na sanar dashi wannan labari mai dad'i", Ta taka rawa kana ta soma kiran wayar sa, Bugu d'aya ya d'auka da cewa "Haba Rauda, ya zaki mun haka, tun yaushe nake kiran ki", "Maida wuk'ar, yau dai Allah ya hutar damu Haidar ya saki Bongel", "What, bana son wasa" Ya fad'a da k'arfi, "Wallahi tallahi a gaban idona ya bata takardar ta", Hisham ihun murna yayi ya jefar da wayar gefe, ya fad'a kan gado ta baya, farin ciki yake ji na ratsa shi wanda bai tab'a jin irin shi ba.


**********

A mota Bongel shiru tayi ta jingina kanta kan window k'ofa, ta lumshe idonta zuciyarta cunkushe da damuwa had'i da tunanin kala kala, Jin parking d'in mota da hayaniyar yaran unguwarsu da suka dabaibaye motar ganin mota mai tsada da kyau ya tabbatar masa sun iso, Ta bud'e idonta tana jin fad'uwar gaba na da wane baki zata furtawa Nene aurenta ya mutu Haidar ya saketa, tasan zasu sha gori kala kala da habaici wurin yan' gidansu, amma ya bawa ya iya da k'addarar ubangiji, Allah ya riga ya rubuta faruwar hakan, Da tunanin haka ta k'arfafawa kanta gwiwa ta aro jarumta ta sakawa kanta, Ta saki ranta da k'ok'arin b'oye damuwarta, ta fito motar zuwa cikin gida, Tuni yara sun shiga da akwatin ta.



  *Hmmm bakina da goro*🤐😷



OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

*HASKE WRITERS ASSO...*

ARBA'IN DA BAKWAI

SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298


*MAMAN INYASS SHAFIN YAU NAKI NE❤️*


Ramla da Abu da gudu suka zo suka rungumeta, haka sauran yaran gidan, mamaki ya cika Bongel ganin wannan shine karon farko da ta samu tarba daga yaran gidan su, ko da tana makaranta idan ta dawo hutu ko kallon arzik’i bata ishe su ba, Hassan da Hussein kad’ai take samun sauk’i daga gare su,


Nene na zaune d’akinta tana jera kayan ta da aka kawo daga wurin d’inki cikin akwati, Bongel ta shigo, Cikin ladabi ta gaishe da Nene, ta amsa da farin cikin ganin yar’ ta, “Ga tuwo can da miyar kub’ewa busasshiya na miki”, Da kallon mamaki tabi Nene dama tasan da zuwanta, Nene ta katse tunaninta da cewa “Ko baki ji ba”, Tayi saurin cewa “Dama nayi kewar miyar ki”, Nene tayi dariya, Ramla ce ta shigo rik’e da kwanukan abincin ta ajiye gaban ta, “Sannu”, Cewar Bongel, Ramla tace “Kai Adda wai sannu kamar nayi wani aiki”, Bongel tayi murmushi, Bongel taci abincin ne ba dan tana son ci ko jin dad’in sa ba, sai dan kar su Nene su gano akwai wani abu, duk da cewar ya zama dole ta sanar dasu, sai dai ba yanzu ba sai an gama hidimar biki,


“Ai baki wani ci tuwon ba”, Cewar Nene, “Gajiya ce tamun yawa, kwanciya kawai nake buk’ata”, Nene tace “Kamar wacce tayi tafiya mai nisa”, Tayi murmushi tana kwanciya kan katifar dake shimfid’e a farfajiyar d’akin, baya ta juya musu ta yadda ba zasu gane ba baccin take ba, duniyar tunani ta tafi, yayin da idonta ke hasko mata fuskar Haidar a lokacin da ya mik’o mata takardar, tana jin b’acin rai da damuwa na sake shigarta, tana jin kiran Asiya na shigowa wayarta, tak’i d’auka, dan bata san me zata ce mata ba, bata son d’aga mata hankali a halin yanzu.


******************************

Haidar yau yaje makaranta yayi handing over ya tashi daga matsayin lecturer, ko shakka babu ya samu experience sosai, Abba yayi gaskiya da yace ta hanyar lecturing zai k’aru da abubuwa da dama, Daga makarantar company ya wuce, Tun shigar sa office d’insa ya kasa aikata komai sai tunanin Bongel da yazo masa, Meyasa idan yaga yarinyar ko suka keb’e tare da ita sai yaji ya kasa controlling kansa, jiya daga zuwa sanar da ita zuwanta gida ya bige da kissing d’in ta, “Ko shakka babu tana amfani da wani lak’ani dake jawo maza zuwa gareta, dashi take mun amfani” Ya tabbatarwa kansa, Idanunsa ya lumshe ya jingina da kujera yace “I have to get rid of her”, Jin bud’ewar k’ofa yasa ya bud’e idon sa yana kallon k’ofa, Hisham ne ya shigo fuska d’auke da far’a,


“Barka da hutawa Yaya”, Cewar Hisham, “Yawwa barka”, “Ya aiki?”, Haidar ya amsa “Alhamdulillah”, “Papers na kawo maka kayi signing”, Ya fad’a yana mik’a mata, Haidar ya karb’a yana duba takardun, kana ya saka hannu, ya mayarwa Hisham, Hisham ya sauke ajiyar zuciya da cewa “Ashe abunda ya faru kenan, Allah ya kiyaye gaba, banji dad’i ba kwata kwata ba amma haka Allah ya k’addara”, Haidar da tsantsar mamaki yake kallon Hisham sam bai fuskanci inda zancen sa ya dosa ba, Ganin irin kallon da Haidar ke masa, yasa bai sake cewa komai ba, dan a zaton sa maganar ce Haidar baya so, Ya mik’e ya fita ba tare da Haidar yace masa komai ba, sai mamaki da ya cika sa.



**************************

“Ina Bongel d’in naji ance tazo” Cewar Dije, “Eh gata nan bacci take”, Nene ta fad’a, “Idan ta tashi na dawo”, “A’ah zata zo ma da kanta”, Dije tace “Toh” tana murmushin da bai kai zuci ba, Bongel kuwa jij shigowar Dije ya k’ara d’aga hankalinta tana kyautata zaton ko Hamma Siddiku ya aiko a kiranta, amma a yadda tasan halin shi da kanshi ma zai iya zuwa d’akin, but ba abun mamaki ba ne, dan ya aiko Dije.


Bongel bata tashi ba sai ana kiran sallar azahar, ta fito tsakar gida tayi alwala, ta koma ciki tayi sallah raka’a biyu, tana idarwa ta jiyo muryar Hamma Siddiku daga waje, hantar cikinta ce ta kad’a, Ta ambaci sunan Allah,


“Kizo inji Hamma Siddiku” Ramla ta fad’a, Bongel da k’yar ta iya amsawa da “Toh”, Jiki a sanyaye ta fito tsakar gidan, Kanta sunkuye k’asa ta gaisheta, “Lafiya lau Bongel ya hanya?” Ya fad’a da far’a, Jin muryarsa yasa mamaki ya kamata, ya akayi yake amsa mata haka ko ya zata tazo da kayan d’akin ne,


“Kin kyauta, kin zama ya’, auren ki yayi man rana, ashe zaki ji maganata”, Cewar Hamma Siddiku, Bongel tayi shiru kanta na sake k’ullewa sam bata fahimci ina zantukan sa suka nufa ba, Ya cigaba da cewa “Allah yasa ki d’ore haka, idan kina mana irin haka ai babu wanda zai ji mu dake”, Bongel murmushi kawai tayi ba dan ta fuskanci komai ba, Yaja babbanr rigar sa ya wuce, Ta juyo suka had’a ido da Nene ta mata murmushi, D’aki ta koma da tunani birjik, Ramla ce ta shigo, Bongel ta kai dubanta gareta tace “Ramla meke faruwa a gida


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu

Please Login or Register in order to submit comment