Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsabar kuka, “Haba Bongel meye na kuka”, Cewar Asiya tana nuna rashin jin dad’in ta, “Muje kimun bayanin lecture da akayi” Tana kawar da zancen kukan, “Yanzu muna da wata lecture, muje idan mun fito sai na miki”, Bongel ta jinjina kai.



************************************

4:30 daidai suka fito makaranta zuwa gida, Daidai k’ofar gidan suka ga dallelliyar mota fake, Asiya tace “Wane bak’o ne mukayi” tana mamaki, Bongel bata ce komai ba, amma a zuciyarta tana mamakin waye, suka nufi shiga gida, Horn da suka ji na cikin motar na musu yasa suka tsaya, suna bin motar da kallo, baka ganin na ciki saboda tent, K’ofar motar aka bud’e Hisham ya fito, ganin sa yasa gaban Bongel fad’uwa “Me ya kawo sa?, me yazo yi?”





OUM MUHRIZ
[2/14, 15:55] Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

  *HASKE WRITERS ASSO...*

SHAFI NA TAKWAS


Murya a sanyaye tayi sallama, Yana zaune yana duba wasu textbooks, sallamarta ta sauka cikin kunnen sa, jin muryar mace bai d’ago kansa ba, Sai gyaran murya yayi alamar meke tafe da ita, Bongel cikin rawar murya tace “Dan Allah kayi hak’uri ka karb’i assignment d’ina”, Yana jin haka yasan yarinyar nan ce, “So she have the gut na biyoni office d’ina, tana tunanin nima irin mazan nan ne”, Ya fad’a a ransa, A zahiri yace “Kinzo kiyi seducing d’ina ne kome, rashin kamun kan naki har ya kai ki biyoni office d’ina, ni ba irin lecturer bane masu neman yan tasha irin ki, So out”, Ya k’arasa cikin tsawa,


Bongel jiki a sanyaye ta juya ta fita, zuciyarta na k’unar maganganun sa, idan tasan haka zai d’auka da bata zo ba, gara ta rasa assignment data k’ara rasa mutuncin ta a wurin sa,

“Ina fatan ya karb’a”, Asiya ta tambaya cike da kulawa, Bongel ta girgiza kai tace “A’ah”, “Ya salam gaskiya yana da tsaurin ra’ayi”, “Allah yasa hakan shine mafi alkhairi”,
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

  *HASKE WRITERS ASSO...*

ASHIRIN DA D'AYA


Dube dube suka soma na hanyar da zata sada su zuwa cikin gida, kasancewar gidan ya kasu kashi kashi,

  Haidar ne ya fito yaje wurin Ammi bata nan, kan maganar auren da ake shirin yi masa, ko akwai wata hanya da za'a bi dan ganin ba'a yi ba,


  Idon su k'yam a kansa tun ba Feedo ba data kasa b'oye zalamar ta, kamanin sa da Hisham ya tabbar musu Yayan sa ne, har ya k'araso kusa dasu Feedo idonta na kansa, "Ina wuni" Suka gaishe sa suna d'an duk'awa, "Lafiya lau" Ya amsa ba tare da ya kalle su ba, da zumar wucewa, Ihsan tace "Dan Allah wurin Ammi muke tambaya", "Bata nan" Ya basu amsa kai tsaye,


  Feedo ta tab'o ta da yi mata alama da kai, Ihsan tace "Tunda bamu sameta ba, bara mu sanar da kai, dan ina da tabbacin kai Yayan Hisham ne", Haidar gabansa ya fad'i yana fatan ba wani abun kunya Hisham d'in ya jawo musu ba, dan yana kyautata zaton yan' matan sa ne, Haidar ya gyara tsayuwar sa  yana cusa hannun sa cikin aljihun riga yace "Ina ji",


"Ina ce kowane dan'uwa burin sa yaga dan'uwan sa ya auri mace ta gari, toh Hafsah yarinyar da ake shirin auren su da Hisham, ba kowa bace face karuwa, wacce bata tsayar da kanta kan namiji d'aya ba, taxi no garaje ce, idan banyi b'atan lissafi ba ta zubar da ciki ya kai sau biyar, har asibitin da take zuwa ana zubar mata na sani, so taya mace irinta zata zama uwa ta gari ga yaran da zasu haifa gaba", Haidar sai da ya gama sauraren zantukan Ihsan tas, Yayi gyaran murya yace "Ina da tabbacin kema budurwar sa ce, wanda zafin zai auri wata yasa kika zo kina fad'in zantukan nan, so you are not welcome here" Ya nuna mata hanyar wucewa, Ihsan tayi shu'umin murmushi tace "Idan ma hakan ne ba laifi bane, soyayyar sa tasa nake k'ok'arin kub'utar dashi", Haidar yayi murmushin takaici dan ya tuna fuskar yarinyar itace suke rigima da Bongel ranar a makaranta, wato dukan su taron yan bariki ne, abunda bai gane ba shine yaushe aka soma zancen auren Hisham da yarinyar bashi da masaniya, idan kuwa gaskiya ne in dai yana numfashi a doron k'asa ba zai tab'a bari jininsa ya had'a jini da ita ba,

  Ihsan ta wuce, Feedo na take mata baya.


************************************

Dada ta shirya komai na zuwa neman auren Bongel, yayyen Abba su biyu, k'annen sa su biyu, sai yayyen Ammi su uku, Komai da ake buk'ata na zuwa neman aure an tanada, kama daga goro, sweets da sauran tarkace, goro kanshi k'warya ashirin, su sweets kuwa carton carton da kud'i naira dubu d'ari biyu, wanda da gayya Dada tasa kayan suyi yawa haka,


Bongel ta samu a d'aki tana karatun wani littafin addini,

   "Yanzu za'a tafi neman auren ki Bongel", Dada ta fad'a da murmushi d'auke a fuskar ta, K'irjinta ya doka sai take jin fargaba, Dada ta k'ara da cewa "Suna da kwatancen gidan ku zaki fad'a mun", Ta sanar da Dada, Ta jinjina kai tana ficewa,

Nauyayyen ajiyar zuciya ta sauke tana addu'ar Allah yasa komai ya tafi lafiya lau.



***********************************

Jabeer ya gaji da yawon hankalin da Hamma Siddiku ke masa, yasa an kama shi zuwa police station, Hamma Siddiku sai had'a gumi yake ganin sa a station, Ansa yayi report kan cewa nan da kwana biyu zai kawo kud'in ko a rufe sa, Da tsananin b'acin rai da haushin su Nene ya dawo gida wanda yake ganin sune silar komai, da mutuncin sa a kai sa ofishin yan' sanda, tun a hanyar sa ta dawo gida yake masifa, Yana shigowa gida kai tsaye wurinsu Nene ya nufa,


  Tukunyar dake tsakar gida, yasa k'afa yayi wurgi da ita, labulen dake sak'ale bakin k'ofar d'akin su ya d'age da cewa "Ku fito yau wallahi sai kun bar gidan nan, zama daku bashi da wani amfani, Bongel ta tafi yawon karuwanci ba zaku ja mana zagi a gari ba, dan ina da tabbacin Ramla ma ta kusa bin sahun ta, waya sani ma ba gidan aiki take zuwa ba, yawon shashanci take zuwa, dan inda naggen gaba tasha ruwa nan saura ke bi", Nene ta fito rik'e da hannun Abu, ta zube gaban Hamma Siddiku tana rok'on sa,

  "Dan Allah Dan girman Allah ka rufa mana asiri, kaji tausayin marayun nan ka barmu mu zauna, wallahi bamu da wurin zuwa", Hamma Bala yace "Dole ku bar gidan nan wallahi, babu amfanin zama daku", Hamma Siddiku da Hamma Bala suka shiga d'akin suka soma yi musu wurgi da kaya, Nene tana kuka, Ramla da Abu suma suna yi, Fatsuma da Dije na gefe na murna cike da tsantsar farin ciki,


  Sa'ade da Habiba ne suka shigo gidan sun dawo daga gidan kitso, Sukace "Ga manyan motoci nan masu kyau sosai sun tsaya bakin gidan nan", Jin haka Hamma Siddiku ya tsaya da abunda yake, Yace "Kun tabbata nan gidan", Suka ce "Eh dan sai da suka tambaye mu nan ne gidansu Bongel muka ce Eh", "Ahaf ai sai ita, na tabbata cikin kwartayen ta ne, wani ya biyota", Yayi hauri da kayan dake gabansa, yana nufar hanya fita, Hamma Bala yabi bayan sa,


  Turus suka yi ganin motoci har uku, masu azabar kyau da had'uwa wanda a tsawon rayuwar su basu tab'a ganin irin su ba, Suka kalli juna, A tare suka bud'e motocin suka fito, Ganin manyan mutane cikin shiga da kamala, sanye da shadda wanda kallo d'aya zaka yi kasan mai tsada ce,  jikinsu yayi sanyi, kowannen su ya basu hannu suka yi musabaha, Alhaji Yusuf yace "Ko zamu samu masauki", Hamma Siddiku yace "Eh eh bismilla", Hamma Bala yayi saurin shiga ciki ya d'auko tabarmi ya shimfid'a musu, Suka zazzauna, da yawa a zuciyar su, suna mamakin irin gidan da Haidar ya nemi mata, duba da arzik'in sa da na gidansu, da kuma irin gidan da matar sa ta fito,


    Alhaji Yusuf yayi bayanin daga inda suke kafin daga bisani yace "Mun zo ne nemarwa dan' mu auren yar' ku Hafsah", Hamma Siddiku sai da cikin sa ya juya saboda tsananin mamaki da tashin hankali mai k'unshe da hassada, Hamma Bala shima kusan hakan, dan sai da tarin dole ya taso masa, suka soma yi masa sannu, Cikin k'arfin hali da son b'oye bak'in cikin sa yace "Ai an mata miji", Kallo kallon suke wa junansu da mamaki, Alhaji Nasiru wanda Yayan Ammi ne yace "Toh ya haka, da amincewar yarinya muka zo nan, anya kuwa tana son zab'in da kuka mata", Alhaji Yusuf yace "Maganar tana son sa bata taso ba, dan da tana son sa, ba zata bari muzo ba", Hamma Siddiku ya had'iye yawun b'acin rai, Alhaji Nasiru ya cigaba da cewa "Ni dai ina baku shawara ku bar yarinya ta auri wanda take so, auren dole bashi da wata fa'ida, Hamma Siddiku kwarjinin da suka masa ya kasa musawa, Yayi shiru, ganin haka Alhaji Yusuf ya umarci a fito da kayan da suka zo dashi, kasancewar shi babba mai shekaru da yawa, wanda yayi mu'amala da mutane kala kala,  ya fahimci akwai hassada a lamarin,


   Hamma Siddiku da Hamma Bala ganin kayan da ake shigo dasu, Mamaki ya cika su, basu k'ara tsinkewa ba sai da Alhaji Nasiru ya ajiye kud'i a gaban su, Hamma Siddiku ai tuni ya soma washe baki da kuwa ya had'e rai, "Ashe arzik'i ke kirana ina neman shure sa da k'afata" Yayi zancen zuci, A fili yace "Ai dama yaron ne ya matsa kan yana sonta, ita bata son shi, mutuncin baban yaron yasa da za'a aura mata shi, amma tunda ga wanda take so ai shikenan, dama rashin tsayayye yasa", Kowa mamakin shi ya kama sa, ganin yadda ya canza lokaci d'aya dan abun duniya, Hamma Bala yace "Toh yaushe kuke ganin ya dace a saka ranar bikin", Alhaji Yusuf yace "Mu a shirya muke ko yaushe", "Muma haka" Cewar Hamma Siddiku, Suka musu sallama suka tafi.


****************************

"Ku kwashe kayan ku, ku mayar ciki" Hamma Siddiku ya fad'a, Da mamaki Nene ta d'ago ta kalle sa, Da sakin fuska kamar ba shine ya gama juye musu kwandon rashin mutunci ba yace "Neman auren Bongel aka zo, ashe mune bamu fahimceta ba yawon karuwanci ta tafi ba" Duk yana yi ne dan ya kwashe kayan da aka kawo da kud'in, Nene mamaki ya cikata neman auren Bongel, yaushe ta samu miji a can kuma waye zata aura, sune suka fara zuwar mata a rai, ba kayan da taga an shigo dasu bane gabanta, Hamma Siddiku dubu goma kad'ai ya bata, bai fad'a mata ainihin yawan kud'in ba, su alawa ma carton d'aya d'aya ya bata, da goro k'warya d'aya, Nene bata damu ba, duka ta tarkata ta ajiyesu wuri d'aya ba zata tab'a har kud'in ba, sai taji daga Bongel,


Fatsuma da Dije hassada fal zuciyar su kamar su had'iye zuciya su mutu.


Hamma Siddiku har majalisar su Jabeer yaje ya watsa masa kud'in sa dubu ashirin, yace ga tsiyar sa nan, abun ya so zamar musu rigima, mutanen wurin suka raba su.


**********************************

Daga Ammi har Abba har yau basu san yarinyar da Bongel zata aura masa ba, Wanda suka je neman aure bayan sun dawo, da yawansu sun nuna rashin dacewar Haidar da neman aure irin gidan, Dada ta musu tas kan cewa babu ruwansu da gidan, Dan dole suka ja bakin su suka yi shiru.


Bongel tayi farin cikin jin su Hamma Siddiku sun amince, yanzu tasan babu zancen auren Jabeer, kuma Nene zata samu kwanciyar hankali, sai taji hankalinta ya karkarta gida, tasan Nene na son jin k'arin bayani daga gareta.



*****************************

"An je neman auren ka kuma an basu", Ammi ke sanar da Haidar, Haidar wanda ke zaune Irfan na kan cinyar sa ya manne masa kan ya kai sa wurin Aunty, anyi hutu kwana biyu bai je gidan Dada ba, Kansa kawai yayi nodding ba tare da yace komai ba, k'asan zuciyarsa yana jin zafi, Ya rik'e hannun Irfan suka fito, Yace driver ya kai sa, baya jin zuwa gidan Dada, haushin had'in auren da ta masa yake ji.


********************************
Dada ta yanke shawarar auren nan da sati biyu, bata so a d'auki lokaci, gudun abunda zai je ya dawo, Kud'i masu yawa taba Bongel kan ta fara gyara, Bongel ita kunya ma taji, Asiya ta samu mai gyaran jiki tana zuwa gida kullum tana mata, wanda gyaran ba k'aramin kyau yake k'ara mata ba, tana glowing,


   Hisham kullum yazo sai yace ta k'ara kyau, yana k'ara jin masifar sonta na shigar sa, Abunda ke bata mamaki shine ko sau d'aya bai tab'a mata zancen auren ba, wanda ta rasa gane dalilin sa na hakan, itama kuma bata tab'a d'auko masa maganar ba.


******************************

Ammi yau ta yanke shawarar tambayar Dada wacece yarinyar, ganin bikin na matsowa ba tare da sun san ta ba, kuma ta soma had'e lefe, tana son ganin yarinyar ko a hoto ne dan sanin taste da ya dace da ita, Ta shirya taje gidan Dada,


**************************

"Dada an soma had'a lefe, gashi bamu san amaryar ba, balle mu san kayan da suka dace da ita", Cewar Ammi, Dada tayi dariya tace "Bongel ce ba kowa ba", Ammi lokaci d'aya taji sanyi a ranta dan ita kanta ta yaba da hankalin yarinyar, da kuma duba da yadda suka shak'u da Irfan, Tace "Au itace", Dada tace "Eh", "Mashaa Allah Allah ya sanya alkhairi", Dada ta amsa da "Amin"

*******************************

Bongel tana gidansu Asiya, tunda akace su Hamma sun amincewa auren ta, ta fara zuwa gidan ba tare da fargabar komai ba, Bayan sallar la'asar ta dawo har lokacin Ammi na gidan, Har k'asa ta duk'a ta gaisheta ta amsa da sakin fuska, tana k'ara yaba hankalinta da jin son kasancewarta surukar ta.


*********************************

Hisham yaji zancen nemawa Haidar auren, wanda Dada ta nemar masa mata, sai dai bai damu da sanin wacece ba, dan a ganinsa ba hurumin sa ba ne, Yau ma yazo wurin Bongel sun jima suna hira kafin ya tafi.


******************************

Bongel ganin kwanaki na k'ara matsowa na bikin, Dada bata yi maganar zuwanta gida ba, wanda a ganinta mutuncin ta shine a d'aura aure a gidansu, a d'auko ta daga gidansu cikin mutunci, Ta yanke shawarar samun Dada kan maganar,


 
Cikin sanyin murya da ladabi tace "Dada Dan Allah ina so na tafi gida a d'aura aure na a can", Dada ta jinjina kai tace "Kinyi tunani Bongel, hakan shi ya dace, zan shirya tafiyar ki, amma ina so ayi walima anan kafin ki tafi can", Ta amsa da "Toh", tana jin kamar kar ayi walima, tafi so a d'aura aure kawai.



***************************

Dada ta shirya walima babba a gidanta, wanda hadda ango zai zo da abokan sa guda biyu, a decoration da aka yi an ajiye wurin zaman Amarya da Ango.


*******************************

"Wow wallahi kinyi masifar kyau Bongel, gaskiya yau Ango Hisham dole ya rud'e" Cewar Asiya tana faman yi mata hotona, Bongel tayi murmushi, Tayi kyau sosai cikin bud'addiyar gown fara, wacce yadin ta mai tsada, Ammi tasa aka d'in ka mata, Ta fito sak Amarya.


**********************************

Yayi tsaki yafi a k'irga sam baya son zuwa walimar, amma Ammi ta nuna dole yaje, Farar shadda ce a jikinsa mai d'inkin babban riga da yasha aiki, hular sa  ta zauna daram a kansa, Yayi kyau matuk'a ya fito sak ango, banda k'amshi ba abunda ke fita a jikinsa, Hisham ne ya shigo yana cewa "Ango Ango" Cikin zolaya, Kallon da ya jefa masa yasa ya tsaya da wasan Yace "Su Fahad na waje kai kad'ai ake jira", Bai ce komai ba, yana gyara takalman sa covered wanda designer ne,


Yana fitowa abokan sa suka soma fad'in "Ango Ango" Ya d'aure fuska kamar bai tab'a dariya ba, ya shiga mota, Abokansa suma suka shiga tasu, aka jera tafiya cikin convoy.





OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

  *HASKE WRITERS ASSO...*

ASHIRIN DA BIYU


Bongel da sauran k'awayenta sunyi kusan minti talatin da zuwa gidan Dada, dan ta koma gidansu Asiya saboda bak'i wanda dan halatar walimar suka zo, Ango bai zo ba, Bongel na cikin mota bata fito ba, Kanta sunkuye k'asa cikin lullub'in da ta sha na mayafi mai net shara shara, "Ango ya iso" Ta soma jin muryar yan' matan dake wurin na fad'a,


Da saurin escort d'insa ya fito ya bud'e masa k'ofa, Haidar ya fara zura k'afar sa d'aya waje, yana jin kamar yayi zaman sa cikin motar kar ya fita dan sam baya maraba da auren, a ganin sa wanda yayi auren soyayya ya cancanta ya halarta event bashi da ake neman k'ak'aba masa ba, "Shin yarinyar tana son sa ko itama auren dole za'a mata", Ya tambayi kansa, "Ko tana sona ko bata sona it won't change anything, ba zata samun gurbi a zuciyata ba" Yayi assuring kansa, "Ka fito mana Haidar, kai kad'ai ake jira, Amarya ta dad'e da zuwa", Iska ya fusgar daga bakin sa, ya fito,

A tare suka jero da Hisham zuwa k'ofar shiga gidan, Asiya ta hango su tare cikin da mamaki tace "Dama Hisham da Haidar sun san juna, kai anya basu da alak'a ta jini dan kamaninnasu yayi yawa", Sam bata kawo ba Hisham bane ango, saboda shima shigar tasa tamkar ango, shadda ce fara a jikinsa d'inkin babban riga,

Asiya ta bud'e murfin motar da Bongel ke ciki, Tace "Amarya fito, Ango is here, angon ki yayi kyau sosai, na riga ki ganin sa", Bongel tayi murmushi, Asiya ta kamo hannun ta, suka fito cikin motar, Kanta na sunkuye k'asa, ta jata zuwa wurin dasu Hisham suke,


"Ina wuni angon mu" Cewar Asiya, Hisham da kallon mamaki yake bin ta dama tasan Amarya, sai kuma wata zuciyar tace mishi duniya da fad'i, watak'ila k'awarta ce duba da yadda ta rik'o amaryar, Murmushi yayi yace "Lafiya lau k'awar Amarya", Ta mayar masa da murmushi,


"Amarya da Ango sai su jera su shigo tare" Cewar Dattijuwar mace wacce take matsayin Yayar Abba, Jin haka Fahad ya jawo hannun Haidar tamkar yaro, yana saita shi gefen Bongel, Asiya mamaki had'i da al'ajabi ya kamata lokaci d'aya, me hakan ki nufi, ko kamanin su yasa ya kasa tantance ango, Ta kalli Hisham taga bai nuna wata alama nacewa shine ango ba kuskuren aka samu, sai far'a da taga yana yi, yabi sahun abokan ango, Kanta ya k'ara k'ullewa ta kasa tunanin komai, balle ta aiwatar da wani abu,


Bongel k'amshin turaren da taji yana ziyartar k'ofofin hancin ta ya bambamta da na Hisham, wanda kuma taso sanin me irin k'amshi sai dai ta kasa tuna ko waye, A jere suka shigo farfajiyar wurin ana saka wak'ar larabci ta tarbar Amarya da Ango, Kujerar da aka tanada dan zaman su, suka zauna, aka kashe wak'ar, Babban malamin da aka gayyata ya soma wa'azi kan ma'aurata mai ratsa zukata, ya fad'i hakk'ok'in miji kan matar sa, da hakk'ok'in mata kan miji, Bongel a zuciyarta tace "Ba k'aramin nauyi ba ne ke shirin hawa kaina, wanda sai nayi taka tsantsan dan samun aljanna ta",


Awa biyu malamin ya d'auka yana wa'azi, kafin aka soma rabon abinci, har lokacin Bongel kanta na sunkuye k'asa, Asiya wacce mamaki had'i da tashin hankali ya dabaibaye ganin Haidar ne angon yasa ta kasa sakewa, wuri d'aya ta samu ta zauna shiru, taso magana da Hisham ko zata ji wani bayani daga bakin sa bata samu damar haka ba, kasancewar yana kusa da ango,


Mutane suka fara tasowa ana hotona, D'aya daga cikin coursemate d'in ta tace "Tashi a mana a tsaye" Ta kamo hannun Bongel, tazo mik'ewa ta take gown d'inta ta baya, tayi suu ta fad'a baya mayafin ta na yaye wa, idon su ya sark'e cikin na juna ita da Haidar, Hisham ma daidai lokacin ya kai duban sa, jin muryar mutane suna fad'in Subhanallah ganin ta fad'i,


Bongel numfashinta ya d'auke na wucin gadi, yayin da zuciyarta ke dokawa da tsananin k'arfi kamar zata fasa k'irjinta ta fito, Haidar sandarewa yayi wurin dan ya kasa gaskata abunda idanun sa ke gane masa, yayin da wata zufa ta tashin hankali ta shiga tsattsafo masa,

Hisham kuwa idon sa ya sake murzawa dan tabbatar da ba gizo suke masa ba, Ganin Bongel ce matsayin amaryar Haidar, kansa ya mugun sarawa tamkar an sara masa takobi, yana jin wani abu ya daki k'irjin sa,


Bongel ganin idon mutane yasa tayi saurin mik'ewa tana gyara mayafinta tare da k'ok'arin tattaro natsuwa, sai dai ganin natsuwar ba zata samu ba, ta rik'e k'afarta alamar kamar taji ciwo tace "Auchh", Sannu aka fara mata, Waleeda ta jata zuwa mota, Jinginar da kanta tayi jikin kujerar mota, kanta na tsananin sara mata, bugun zuciyarta na tsananta, Asiya take buk'atar gani a yanzu,


Asiya na ganin an fito da Bongel, ta biyo bayan su, motar ta bud'e ta shiga, Hamza driver ta umarta ya kaisu gida, ba wanda ya d'aukowa wani maganar ganin bai dace suyi gaban Hamza ba, amma kowa yasan dan' uwan sa na cikin rud'ani.



********************************

Haidar bai k'ara minti biyar a wurin ba ya fita zuwa gida ba tare ya jira sauran abokan sa ba, Yana shiga d'aki ya cire hular sa da babbar riga yayi wulli dasu, Da fad'in "How is that possible, taya ta zama yarinyar da Dada ke son aura mun, wallahi ba zai tab'a yiyu ba, i must ruin everything bazan tab'a bari hakan ta faru ba" Ya fad'a idonsa na kad'awa su koma jajir.


**************************************

"Asiya kaina ya k'ulle, bana gane komai taya Haidar ya zama mijin da zan aura ba Hisham ba, meye alak'ar Dada da Haidar, taya Haidar ya zama mahaifin Irfan", "Nima sune abunda suka d'aure mun kai Bongel, amma ina jin Hisham ya kamata mu nema ko zamu samu wani bayani", "Bana tunanin Hisham nada masaniya a kai", Ta k'ara da cewa "Shiyasa kenan bai tab'a mun zancen auren ba", Ta k'arasa da dafen kanta da take jin tamkar zai rabe biyu, Asiya ta bud'e baki zata yi magana kiran Hisham ya shigo, wanda tun ganin Bongel matsayin matar da Haidar zai aura ya rasa natsuwar sa,

Ta d'auka, Cikin sanyi murya yace "Ina waje", Tace "Toh" tana kashewa ta kai dubanta ga Bongel tace "Hisham ne" Da sauri ta tashi, tana riga Asiya fita waje, Cak ta tsaya dan kallo d'aya ta masa ta hango tsantsar tashin hankali a fuskar sa da tarin tambayoyi, Kafin tayi wata magana yace "Taya haka ta faru Bongel, ki gaya mun taya, dama yaudarata kike kin shirya auren Yayana", Jin kalmar Yayansa ta kalle sa a razane da cewa "Haidar Yayan ka ne", "Kada ki raina mun hankali Bongel, tsawon zaman ki gidan Dada ba zaki ce baki san Haidar yaya na bane", Kuka ta fashe da shi tana cewa "Wallahi ban sani ba Hisham, hasalima kai nake wa kallon mahaifin Irfan, shiyasa ko da Dada tazo da zancen auren mahaifin Irfan na amince, bansan Haidar ba ne" Ta k'arasa tana kuka kamar ranta zai fita, Hisham natsuwa ya d'an ji na jin cewa Bongel bata san da maganar auren ba, Ya numfasa yace "Ki daina kuka Bongel, In Shaa Allah i will try wurin ganin auren ya dawo kaina", "Please try Hisham, ba zan iya auren yayan ka ba", Jin haka ya k'ara sa zuciyarsa tayi sanyi, Sai da ya tabbatar ya lallashe ta, ta daina kuka, sannan suka shiga cikin gida da Asiya, wacce tun fitowar ta bata ce komai ba.


****************************************

Hotonan walima da ake ta sawa a status Rauda ke kallo cikin tsananin b'acin rai da tafasar zuciya, hoton k'arshe da ta kai tayi jifa da wayar k'irar iphone 13, ta fashe, Kuka ta fashe dashi da cewa "Wallahi sai na aure ka Haidar, tun kafin Yaya Hafsah ta rasu nake wa kaina sha'awar miji irin ka, yanzu ga damar samun ka bazan tab'a bari wata ta mallake ka ba", Ta k'arasa da fad'awa kan gado tana kuka tana wulla k'afa kamar k'aramar yarinya.



***********************************

Alhaji Sani ne zaune jigum, ya zurfafa tunani, abincin da Hajiya Mariya ta zuba masa har ya soma sandarewa,

Hajiya Mariya ta shigo tana cewa "Ahh Alhaji baka ci abincin ba",

Please Login or Register in order to submit comment