Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kad'ai" Ta fad'a a marairaice, "A'ah kar mu fara da karya masa sharad'i, dama ce muka samu kada mu bari ta sub'uce", Bongel tace "Hakane kuma, kira sa naji ina zan same shi",


   Hisham fitowarsa daga wanka kenan, yana goge gashin kansa da k'aramin towel wanda ya taru kamar na mace sai dai gashin ya k'ara masa kyau,  Wayar sa ta soma ruri, ya kai dubansa ganin bak'uwar lamba yasa a ransa yarinyar jiya ce, dan baya expecting kira da sabuwar number yau a wannan lokacin, yayi receiving tare da saka handsfree,


  "Assalamu alaikum" Ta fad'a cikin natsuwa, "Wa alaikis salam", "Ina wuni?", "Lafiya lau", "Nice ta j.." Ya katse da fad'in "Na gane, mu had'u a bakin company", Ta amsa da "Toh", Ta mik'awa Asiya wayar, "A'ah kije da ita, ko da buk'atar amfani da ita zata taso", Tace "Toh",


  Kusan minti ashirin da tsayuwarta a wurin, dallelliyar mota tayi parking a gabanta, tented ce shi ya hana mata ganin na cikin motar, glass ya sauke ya mata alama da hannu tazo, Ganin Hisham ne ta k'arasa bakin mota, "Shigo" Ya fad'a, Kai ta girgiza tace "A'ah", "Baki shirya karb'ar admission ba kenan", "Na shirya" Ta fad'a da sauri, ganin yana shirin tada mota tayi saurin bud'ewa ta shiga, ba abunda ke tashi cikin motar sai kid'a, sam bata son kid'a, sai yatsina fuska take,


   Daidai wani k'aton gida taga yayi horn, security ya taso ya bud'e, tayi mamakin ganin gida suka zo, "Fito" Yace mata, Jiki a sanyaye ta fito, tana bin harabar gidan da kallo, dan ba k'aramin kyau ya mata ba,

  "Mu shiga ciki ku gaisa da Matata", Ya fad'a yana murmushi, tabi bayan sa, a ranta tana ayyana matar sa ta dace da miji mai tsantsar kyau, gayu had'i da dukiya,


  Falon sam bai nuna akwai d'an adam dake rayuwa cikin sa ba, "Bara na kirata" Ya fad'a yana shiga ciki, Few minutes ya fito, Yace "Ki sameta ciki, tace kanta na ciwo, kinsan masu laulayi", Bongel tayi murmushi a ranta tana mamakin kirki irin nasa, dama akwai masu kud'i masu sauk'in kai,


    Tana shiga d'akin ya rufa mata baya, tare da saurin saka key ya kulle ya zare mukullin,

   Jin an rufe k'ofa ta juyo a razane, "Dan Allah kar ka cutar dani ka barni na tafi", Murmushin gefe baki yayi yace "Kina tunanin a banza ake samun admission" Yayi dariya ya cigaba "Ki kwantar da hankalin ki, ki bani kanki yau kad'ai, ki samu admission cikin sauk'i da kud'ad'en kashewa", "Dan Allah kaji tausayina ka k'yaleni kada kamun komai, Dan Allah ka rufa mun asiri", Tana fad'a tana ja baya, yana biyota har ta fad'a kan gado kwance, ya hau kanta ya cire hijabinta da k'arfi ya wular, ya soma romancing d'in ta, hawaye ke ambaliyi saman fuskarta, tana nadamar kawo kanta, ko shakka babu tayi babban kuskure na biyo sa,


*********************


  Namiji ne da ya amsa sunansa namiji, yana cikin jerin maza ajin farko, mai jini a jika, kyau, had'uwa had'i da gayu duk ba'a bar sa a baya ba, Fari ne sosai wanda ya had'u da na halitta da hutu, fatar sa kad'ai zaka kalla kasan naira da hutu sun ginu a wurin, Tsaye yake bakin dressing mirror na tantsamemen gadonsa royal, yana combing kwantaccen gashin sa na fulani, comb d'in ya ajiye a ma'ajiyar sa, ya fesa turare sun kai kala biyar, ya gyara zaman necktie d'in sa, Ya fito d'akin cikin takunsa na k'asaita,

Da sauri escort d'in sa ya taso da zumar bud'e k'ofar mota, "Zan shiga gidan Ammi", Ya fad'a a takaice, yana bin wata k'aramar k'ofar da zata sada shi da gidan, ba tare da yabi ta gate ba, ganin babu motocin Abba, ya tabbatar masa ya fita aiki kenan,


   Dattijuwar mata yar' kimanin shekaru hamsin na zaune falo wanda aka narkawa dukiya, ta sha ado na matan manya, hutu da naira ya b'oye tsufanta zaka rantse ba zata haura shekaru arba'in zuwa da biyu ba,  yaro dan' kimanin shekara biyu yana zaune kan cinyarta tana bashi chips, "Ammi ina kwana?" Ya gaisheta yana russunawa, "Lafiya lau",Ta amsa da sakin fuska, Yaron  ya sauka jikinta yana nufar sa, yana fad'in "Daddy" cikin gwarancin sa, "Wato kaga babanka ko", Ammi ta fad'a tana dariya,

   D'aukar sa yayi ya soma masa wasa yana cilla sa sama, yaron kuwa sai dariya yake, ya jima yana masa wasa, kafin ya mik'awa Ammi shi, Yace "Ammi wai ba zaki samu mai tayaki hidimar yaron nan ba, kema kina buk'atar hutu", Ammi ta nisa tace "Yaran ne na kasa dacewa, kowacce da nata matsala, lokaci yayi ma da ya kamata ace ka k'ara aure, shekarar Hafsah biyu da rasuwa, ya kamata ace ka dangana, ka samar wa yaron ka wacce zata maye masa gurbin uwa da ya rasa", "In Shaa Allah" Shine kad'ai abunda yace yayi saurin fita, sam baya son ana masa maganar aure.


   Ganin fitowar sa, Escort d'insa yayi saurin tasowa ya bud'e masa gidan baya, ya shiga, ya mayar ya rufe, Driver yaja motar,

Wayarsa ya jawo ya soma kira, amsa d'aya ake basa a kashe, idan  ya kira wayarsa yaji a kashe yasan babu inda zai same sa sai guest house, "Muje guest house" Ya umarci driver, "Ok Yallab'ai" Ya fad'a cike da ladabi, Banda yana buk'atar takardun dan kusan akansu ne zasu zauna meeting da wasu yan china, zasu mishi signing da ba abunda zai kai sa can,

   "Ba sai ka shiga ciki ba" Ya fad'a, a bakin gate yayi parking, Escort yayi saurin fitowa ya bud'e masa, ya fita, Kai tsaye ya shiga cikin gida, alamun kamar kuka ya soma jiyowa daga d'akin, Yana sa kansa ciki daidai lokacin Bongel ta d'ago kanta, idonsu ya sark'e cikin na juna, da sauri ya runtse idonsa yana cizon pink lips d'insa na k'asa, ya fice d'akin, bai tab'a mummunan gani irin na yau ba, lokaci d'aya yaji tsanar yarinyar da yaga k'aninsa a kanta, ya tsani zina, yana k'yamatar ta, yasha yi ma Hisham wa'azi kan neman mata baya ji, bai tab'a gani da idon sa ba sai yau, "Meyasa mata basu da hankali, basu san daraja da martabar da Allah ya musu ba, suka zab'i zubar da mutuncinsu akan titi, mata da yawa kyaunsu ke cutar dasu, k'aramar yarinya ta lalata rayuwarta" Ya girgiza kai yana jin haushi da tsanar yarinya na k'aruwa a zuciyar sa, yana jin tamkar ya koma ciki ya mata tsinannan duka sai ya raunana ta,


   Hisham yaji shigowar mutum wanda yasan babu wanda zai shigo sai Yayansa Haidar, a daburce ya sauka kanta, ya fito d'akin,


  "Yaya kaine, ina fatan lafiya?" Ya fad'a murya na rawa, duk da yasan Yaya Haidar d'in yasan yana  neman mata amma bai tab'a kama sa red-handed irin na yau ba, Ko kallo bai ishi Haidar ba yace "Documents na jiya zaka bani", "Ai suna gida d'akina", Tsaki Haidar yayi ya mik'e ya fita, "Me ya hanani duba d'akinsa, da banga wannan k'azantar ba", Yana zancen zuci tare da yin tsaki,

   Drivern sa da Escort daga ganin yanayin sa suka san ransa ya b'aci, "Mu koma gida" Shine kad'ai abunda ya fad'a,


  Hisham zama  yayi falo ya kasa komawa d'aki, kunya ta ishe sa, Yaya Haidar ya kamasa da mace, bai tab'a ganin b'acin rai akan fuskar yayan nasa ba irin yau,

   Bongel ta fad'i Alhamdulillah yafi cikin kwando, zuwan wannan bawan Allah ya ceci rayuwarta, Hisham na gab da rabata da budurcinta Allah ya jefo sa, Hawayen idonta sun kasa tsayawa, tsantsar nadamar biyo sa ne shimfid'e a zuciyarta, meya rufe idonta ta kasa tunanin hakan zai iya biyo baya ta amincewa shiga motar sa, ta biyo sa gidan sa, ko shakka babu sunyi ganganci na saurin yarda dashi, "Meyasa maza tunanin su d'aya ne akan yaran talaka, suna ganin da kud'i zasu rud'e  su lalata su, ba'a taimako Dan Allah, sai yaushe rayuwar talaka zata inganta a k'asar nan?", Ta k'arasa da girgiza kanta tana saukowa  daga kan gadon, ta d'auki hijabin ta da ya jefar k'asa, ta saka tabi hanyar fita d'akin, jikinta ko'ina ciwo yake saboda fisge fisge data rik'a yi na k'wace kanta, Ganin Hisham a falo, tayi saurin juyawa baya, Ya ganta ya mik'e ya biyota,


  "Dan girman Allah kayi hak'uri, ka dubi maraicina, kada ka tona asirin mahaifiyata", Jin haka ya tsaya cak, yana bin ta da kallo, yadda take kuka sai yaji tausayinta ya shige shi lokaci d'aya, Karon farko da ya tab'a jin tausayin wata ya' mace ya shige sa, haka bai tab'a attempting raping wata ba sai akanta, itace macen farko da yaji masifaffan sha'awar ta, duk macen da ya kwanta da ita da amincewar ta, idan yayi sau d'aya da mace sai ta dawo, wasu yana cigaba da mu'amla dasu, wasu kuwa da ya cire kwad'ayin sha'awar sa na ranar baya sake waiwayar su,

  "Tashi tashi daina kuka", Ya fad'a tare da sa hannu a aljihu ya mik'a mata hanky, ta karb'a tana share hawayen ta, jikinta na kyarma, "Ki natsu bazan miki komai ba, and admission d'inki is ready, tun a jiya nasa a karb'a, da niyyar idan na samu abunda nake so daga gareki na baki, idan ban samu ba shikenan, kece mace ta farko da zan ba admission kyauta ba tare da na samu abu daga gareta ba", Ya mik'a mata takardar admission d'in, kamar tak'i amsa, tuna muhimmnacin karatun nata, da burin Bappa tasa hannu biyu ta karb'a da fad'in "Nagode" Godiyar bata kai zuci ba, dan babu yadda zatayi ne,

"Am sorry for everything ki yafe mun", Ya fad'a tare da had'a hannyen sa biyu, Mamakin canzawar sa lokaci d'aya ya kamata, duba da yadda ya zamar mata d'azu tamkar mara imani, tabbas ko shakka babu lokacin shaid'an ne ke kad'a masa ganga, ko ba komai yaji tausayin ta, kuma ya bata admission free, Ta tsinci kanta da cewa "Allah ya yafe mana baki d'aya", "Amin ko da wasa kada ki sanar da kowa abunda ya faru", Tayi nodding kai,

  "Muje na kai ki gida", Tayi saurin cewa "A'ah zanje da kaina", Kallon da ya jefata mata yasa tayi shiru, tana jin tsoron kar ya mata wani abu, tabi bayansa ta shiga motar sa ba tare da son ranta ba, gabanta nata fad'uwa tana ganin kamar wani wurin zai kaita ya lalata mata budurcin ta,

   Sunan unguwar da ya tambayeta yasa taji sanyi a ranta, har k'ofar gidan ya kai ta, ya bata kyautar kud'i wannan karon tak'i karb'a, Tana shiga gidan, Asiya ta taso da sauri wurinta, "Kin tada mana hankali Bongel, na kira waya yafi a k'irga baki d'auka ba","Wayar tana cikin jaka, kaina ya rik'a ciwo da jiri", "Subhanallah sannu kije d'aki ki kwanta, bara a aika a siyo miki magani", Cewar Mama, "A'ah nasha magani" Tayi saurin cewa, "Sannu kinji", Ta amsa da "Yawwa",

   Kwanciya tayi shiru tana tunanin abunda ya faru da ita yau, yayin da take godewa Allah da ya kawo mata mafita cikin sauk'i, hakan kuma ya zama izna gareta ba zata sake yarda wani yace su had'u ba taje, tsabar son admission yasa ta tashi rasa abu mai tsada da daraja a rayuwarta,

  Asiya tayi farin ciki sosai ganin Bongel ta samu admission economics, course d'aya da ita.


  Idonta ta runtse kamar mai bacci, mutumin data had'a ido dashi ya soma yi mata gizo, da sauri ta bud'e ido tana addu'ar kada Allah ya k'ara had'a ta dashi ko a mafarki.


    Haidar wunin ranar tunanin Hisham da yarinyar da ya gansa a kanta, ya kasa barin zuciya da k'wak'walwarsa, yayin da idonsa ke masa gizo da fuskar yarinyar, duk sanda zai tuna ta, sai yayi Allah wadarai da ita, tare da jin tsanarta da k'yamatar ta na d'arsuwa a zuciyar sa.



OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

*HASKE WRITERS ASSO...*

SHAFI NA SHIDA


Bongel kwanaki hud’u suka d’auka suna registration kafin suka kammala, Ranar farko da zasu fara shiga aji lecture, bakinta ya kasa rufowa saboda murna da zumud’i,

Asiya na tsaye gaban k’aramin madubi dake manne bango d’akin su, tana shafa janbaki, “Wannan kwalliya taki k’arewa kamar wanda zata gidan biki, sai kin ja mana latti”, Bongel ta fad’a cikin k’aguwa, “Yau ce rana ta ta farko a jami’a, dole na gyara kaina”, Bongel tayi murmushi tana girgiza kai, ita kam bata ga amfanin wata kwalliya ba, tunda karatu kaje, Hijabinta ta saka dogo har k’asa, Asiya kuwa mayafi ta yafa,

A tsakar gida suka sami Mama, ta musu addu’ar nasara, da jan kunne kan su tsare kansu, Suka amsa da “In Shaa Allah”


Napep suka tara zuwa jami’yar umaru musa, Yana ajiye su, Bongel tayi saurin fito da kud’in zata bayar, Asiya ta rik’e mata hannu tace “Baba ya bayar da kud’in zuwan mu da dawowa”, Bongel tace “Angode Allah ya saka da alkhairi” A zuciyarta tana jin ba zata zauna yana biya mata kud’in mota ko da yaushe ba, sanin su ba masu k’arfi ba ne.


Suna cikin mutane na farko da suka fara zuwa, seat na farko suka zauna, Bongel hakan ya mata dad’i sam bata son seat d’in, a ganinta marasa k’ok’ari ke zama baya, tafi son zama gaba tana jin duk abunda malami ke cewa.



*****************************


Kaya kusan kala uku yana sawa ya cire, tsaki yayi yana jawo wata shadda light blue, yasan students da raina malami, baya son yayi shigar da za’a raina sa, mutum ne shi mai son girma, ya tsani raini, duk abunda zai sa a raina shi baya yi, haka baya tolerating wulak’anci daga wurin kowa, yanayin k’asaitar sa zaka rantse jinin sarauta ne idan ba an fad’a maka ba, haka zalika mutum ne shi kaifi d’aya,


Shaddar tayi masifar kyau a farar fatar sa, ya d’aura hular sa kan gashin kansa da ya d’an taru, apple watch d’insa ya d’aura, ya fesa turaruka wanda tuni d’akin ya gauraye da k’amshin sa, wayar sa ya d’auka k’irar iphone 13pro max,

Hamma yayi alamun bacci, tsaki yayi dan daren jiya bai samu isasshen bacci ba, saboda research da ya dad’e yana yi na lecture da zai yi yau, Tabbas ya yarda da zancen Abba da yace ta hanyar lecturing zai yi research sosai, da abunda zai sa ya hana idonsa bacci daren jiya.


Agogon wayarsa ya duba, 7:20am, lecture 8:00am ce zai d’auka, “Definitely Ammi na bacci” Ya fad’a, Kai tsaye wurin motar sa ya nufa, ba tare da ya biya gidansu Abba ba,


Kamar kullum Escort d’in sa ya taso da zumar bud’e masa k’ofa, Da hannu ya dakatar dashi alamar ya tsaya, Ya tsaya cak cike da fargabar ba wani laifin yayi ba, “Am going alone” Ya fad’a yana mik’awa drivern sa hannu alamun ya basa key, ya mik’a masa cike da ladabi, ya karb’a ya shiga motar yaja,

Driver ya kalli escort yace “Yau oga da jan mota da kansa”, “Nima shi nake mamaki”, “Ina jin ya kusa kawo wata sabuwar amaryar ne”, Cewar Driver, Sukayi dariya.



Office d’in da aka tanadar masa da zai zauna na d’an lokacin ya fara nufa, ya ajiye wasu takardu, duka malaman department d’in cike da girmamawa suke gaishe sa, har da wanda suka girme shi, shima yana amsawa da sakin fuska.


***************************

“8:00 tayi nasan yanzu malamin zai shigo, bara na fiddo handout” Cewar Bongel, tana jawo jakarta,

K’amshi mai masifar dad’i da sanya zuciya natsuwa ya daki hancin ta, “Kai turaren nan ya had’u”, tayi zancen zuci,


Tuni ajin aka soma k’us k’us, wanda duk maganar had’uwar malamin da ya shigo suke, yan’ mata da yawa sai faman gyara jikinsu suke dan tuni ya tafi da imaninsu, hatta mazan ajin yaba had’uwa da tsaruwar sa suke, suna ganij yafi k’arfin zama lecturer, dan kallo d’aya zaka masa kasan yana tare da hutu had’i da daula, da yawansu suna ayyana a zuciyar su, meyasa yake lecturing,

Gyaran murya da yayi yasa kowa natsuwa, a lokacin Bongel ta d’ago kanta, idonta sai cikin nasa, muguwar fad’uwar gaba taji, tayi saurin sunkuyar da kanta k’asa tana fad’in “Innalillahi wa inna ilaihi raji’u” a zuciyarta,

Haidar lokaci d’aya yaji fad’uwar gaba, yayin da ranar da ya gansu da Hisham na dawo masa tar a idon sa, “Tasha hijabi kamar mutuniyar arzik’i” Ya ya fad’a a zuciyar sa, yana sake jin tsanar ta,

B’angaren maza ya koma kallo, Ya soma da cewa “Am Haidar Abbas Maishanu”, Mamaki ya cika fin rabin yan ajin jin cewa yaron Abbas Maishanu ne,
Ya cigaba da cewa “I have my rules, wanda ke son zama lecture na dole ya kiyaye, idan na shigo aji ba wanda zai k’ara shigowa, mobile phones off, surutu i won’t tolerate, if you miss two attendance baza ka zauna jarabawata ba”, Bai k’ara da komai ya soma lecture cikin natsuwa, da yawa yan’ matan basa fahimtar mai yake cewa suke ba, sunyi nisa wurin kallon sa.

Bongel kuwa tunda ta sunkuyar da kanta k’asa bata k’ara d’agowa ba, sai dai duk abunda yake fad’a a cikin kunnen ta, ganinsa ba k’aramin d’aga hankalin ta yayi ba, sam bata so ya zama malamin ta ba, ta tabbata ba zai tab’a ganinta da k’ima a idon sa ba,


Lecture awa biyu ya d’auke su, ya fita bayan ya basu assignment mai wuya,

“Nikam malamin nan yayi mun kama da Hisham baki ga kamar su ba” Cewar Asiya, “A’ah ban lura ba” Bongel ta fad’a a tak’aice, “Wallahi suna kama sosai”, “Muje library muyi assignment d’in kafin mu tafi gida”, Bongel ta fad’a tana k’ok’arin kawar da zancen Asiya, “Lecture d’aya ce damu yau?” Asiya ta tambaya, “Eh”,

Sun jima a library suna duba littafai kala kala, basu samu amsoshin assignment d’in ba, sai bayan sunyi sallar azahar sun dawo, suka samu amsar uku cikin biyar, Bongel ta nuna damuwarta k’arara, “Haba Bongel kiji dad’i ma mun samu ukun”, Bongel tace “Haba Asiya ai kamata yayi ace mu samu duka”, “Munyi iya k’ok’arin mu mun kasa ba sai mun hak’ura ba”, Bongel ta d’aga kai sama, rai babu dad’i suka fito makarantar zuwa gida, tana ganin kamar hakan fad’uwa ne gareta ta kasa amsa sauran biyun.



******************************


“Hy my boy” Rauda ta fad’a tana shigowa, Irfan yaje da gudu ya rungume ta, Ta d’auke shi, tana k’arasowa cikin falon, “Afternoon Ammi” Ta fad’a tana zama kujerar kusa da Ammi, Ta d’ago tana kallon ta cike da takaicin rayuwa irin nata kanta yasha attach gashin ta zuba shi har gadon baya, ta yafa k’aramin mayafi kan gashin, wanda dashi da babu d’aya, doguwar riga ce english wear a jikinta, k’atuwar ledar da ta shigo da ita, ta mik’awa Irfan tace “Your favorites” Ya karb’a yana bud’e ledar chocolates ne da sweets kala kala, ya fiddo d’aya ya mik’awa Ammi yace “Bud’e mun”, “Baka gajiya da shan zak’i Irfan”, “Ammi ai gara yasha abun sa”, Ammi murmushi kawai tayi, tana bud’e masa ya karb’a ya fara sha,

Rauda gyara zamanta tayi ta soma ba Ammi labari, wanda bashi da kan gado, Ammi sauraren ta kawai tana bata amsa ba dan ranta yaso ba.


******************************

Haidar daga school, company ya wuce direct, acan ya tarar da ayyuka da yawa, duk da haka bai hana masa tunanin yarinyar da ya gani makaranta ba, “Angel at face devil at heart, ina jin kamar na bar lecturing d’in nan, na tsane ta, i don’t want to see her face ever again, why yau na ganta, kuma zan cigaba da ganinta har zuwa lokacin da zan gama”, Hannun sa ya buga kan teburin dake gabansa cike da takaici.



**************************

Bongel tunanin ganin mutumin ranar ya kasa barin zuciyarta, “Shin yasan Hisham k’ok’arin raping d’in ta yayi, ko kuwa ya d’auka ita ta kawo kanta dan hakan ta faru?” Ta jerowa kanta tambayoyin da babu mai bata amsa, Shigowar Asiya d’akin, ta tashi zaune tace “Dan Allah na tambaye ki?”, Asiya tace “Allah yasa na sani” Tana tattaro dukkan hankalinta kan Bongel, “Kece kika ga saurayi kan wata budurwa a gidansa, shin wane hukunci zaki yankewa budurwar”, “Wani hukunci da ya wuce na yar’ iska, me zai kaita gidan nasa har ya hau kanta idan ba yar’ iska bace”, Bongel ta jinjina kai yayin da take jin tsoro na dabaibayeta wanda ta rasa na menene, tana jin tamkar ta mayar da hannun agogo baya, ta goge bin Hisham da tayi, “Amma meyasa kika tambayeni?” Asiya ta katse mata tunani, “Babu komai kawai jiya naji wasu na muhawarar a makaranta”, Asiya tace “Ohh gashi inji Baba yace na baki mu rik’a siyan abinci a makaranta duk ranar da zamu dad’e”


Bongel ta girgiza kai tace “A’ah Asiya, abun sai yayi yawa, Dan Allah ki mayar wa Baba da kud’insa yayi wani abu dasu”, Asiya ta watsa mata harara tace “Baba ya baki kud’i kice a mayar, lallai Bongel sai yau na shaida baki d’auki baba matsay….”, Tayi saurin sa mata hannu a baki tace “Dan Allah kar kice haka Asiya, wallahi ina jin Baba tamkar mahaifina, kawai ina duba yanayin rayuwar ne, idan bamu taimakawa Baba ba, bai kamata mu k’ara masa hidima ba, ga kud’in mota ga kud’in cin abinci sai nake ganin yayi yawa”, Asiya tace “Bai yi yawa ba Bongel, kuma shi yaji zai iya ai”, Bongel ta nisa tace nasan da haka, amma yau da gobe sai Allah shiyasa nake so na fara aikatau”, “Aikatau” Asiya ta fad’a da mamaki, “Eh aikatau”, “Aiki zakiyi ko karatu, kina tunanin aiki zai bar ki kiyi karatun”, “Haka zan lallab’a duk lokacin da bani da lecture, zanje wurin aiki”, “Dan Allah ki bar maganar aikin nan, ki tsayar da hankalin ki kan karatu, idan dan hidimar ki ce Baba ya d’auka”, “Ina son abunda zai rik’a taimakawa su Nene, Bappa ne mai nema rai kuma yayi halin sa, yanzu basu da mai basu sai Allah” Ta k’arasa da hawaye, Asiya ta soma share mata hawaye da fad’in “Kada kiyi kuka Dan Allah, Bappa addu’arki yake buk’ata banda kuka, Nene kuma Allah yana tare dasu”, Bongel ta jima tana kuka na kewar Bappa da ya taso mata, kafin tayi alwala tayi sallah raka’a biyu na nema masa rahamar ubangiji.



Mama da Baba sun so hana Bongel aikatau, ganin yadda ta nuna tana so suka k’yaleta, Mama tace zata samu mata gidan mutanen kirki, idan ba zata wahala ba ko su wulak’anta ta, taji dad’in kulawar Mama gareta.



**********************************

Har satin ya k’are Haidar bai sake d’aukar su lecture ba, hakan ba k’aramin dad’i yama Bongel ba, a ranta tana addu’ar Allah yasa ya bar makarantar gaba d’aya,


Kamar kullum yau ma suna cikin mutane na farko da suka fara zuwa, sai dai kafin 8 ajin ya cika, cikar da bata tab’a gani anyi ba irin wannan lokaci da wuri, wasu duk sai ana lecture suke zuwa, Bongel sam ta manta da dokar Haidar ta saka haka, Sam bata san shigowar sa ba, sai dai taji ajin yayi shiru, hankalinta na can wurin k’ok’arin jawo biro d’in ta da ya shige k’ark’ashin kujera, ta kai hannunta zata jawo ya datse da k’arfen kujera, “Auchh hannuna”
Ta fad’a da k’arfi wanda duka hankalin yan ajin ya dawo kanta, Haidar na kai dubansa yaga itace ba tare da wani ja ba, Yace “Out” Yana nuna mata hanyar fita, Jikinta ya soma kyarma na tsoro, ta mik’e ta fita, Ya juya ya cigaba da lecturen sa, a ransa yana jin dad’in korar ta, ganin haka yasa yan ajin kowa ya k’ara shan jinin jikin sa,


Bongel gefe d’aya ta rab’e, tana hawaye na bak’in ciki biyu, bak’in cikin korarta da yayi waje abunda ba’a tab’a mata ba tun fara makarantar ta, kuma ai ba laifi tayi ba, hannun ta ya datse ya kamata a mata uzuri, bak’in cikin rasa lecture ranar.


Ko da suka fito lecture idonta ya kumbura

Please Login or Register in order to submit comment