Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da ta nuna musu ba haka taso ba,



  Bayan fitar ta Abba ya wuce d'akin Ammi, tabi bayan sa, sanin hakan na nufin yana son magana da ita,


  Bakin gado ta same sa a zaune, ta kalle sa rai babu dad'i tace "Meyasa ka zab'i bata Irfan, kasan irin shak'uwar dake tsakanin sa da mahaifinsa, da ahalin gidan nan", Abba ya numfasa yace "Ina mai tabbata miki Irfan ba zai wuce kwana biyu a gidan su ba, zasu dawo dashi", "Meyasa kace haka?" Ta tambaya da mamaki, Yayi murmushi yace "Ki kwantar da hankali, kuma bana so ki sanar da Haidar komai, idan ya tambayi Irfan, kice yaje kwana biyu", Tace "Toh" tana gamsuwa da mijin nata, tasan ba zai tab'a kawo abunda zai rusa farin cikin su ba.

  


***********************************

Hajiya Mariya cike da bak'in cikin plan d'in ta bai yi ba ta dawo gida, sam ba haka taso ba, Falo ta bar Irfan wurin yan' aiki, ta shige d'akin ta cike da takaici, taso tada rigimar a bata Irfan, ta yadda hakan zai sa Su Ammi suji tsoron rabuwa da Irfan, a fasa auren da Bongel, ace ya auri Ramla dan Irfan ya zama wurin su, sai gashi tashi d'aya Abba ya damk'a mata shi, zirga zirga take a d'aki, ta kasa zama tana tunanin hanyar b'ullowa al'amarin.




***************************

Hisham walwalar sa ta rage sosai, office ma ya daina zuwa, kullum yana gida, he is depressed, abu biyu suka taro suka jagula masa lissafi Bongel na fushi dashi, ta kasa tsayawa ta fahimce shi, ganin yana gaf da rasata, duk iya tunanin sa na yadda zai hana auren yiyuwa ya kasa, Bai tab'a zaton Haidar zai amincewa auren ba jin sun had'a shimfid'a, yasan ko shakka babu saboda shi ya kasa fallasawa su Dada, anya ba zai samu Dada da kansa ya gaya mata sun had'a shimfid'a da Bongel ba, yana jin ta haka kawai zai samu mallakar ta, yayin da wani b'angare na zuciyar sa ke hana sa.


***************
Rauda ta sawa ranta ko ta wacce hanya sai tabi dan ganin ta mallaki Haidar, zuciyarta ba zata tab'a iya hak'ura dashi ba, ko a lokacin da ta soma ganin su taso ita yake so ba yayar ta ba, yanzu kuwa ba zata bari wata mace ta samu gurbi a zuciyar sa idan ba ita ba, ado tasha sai dai wannan karon ta b'oye gashin kanta da yasha attach, ta saka mayafi madaidaici dan ta fuskanci hadda yanayin shigarta ke sa yake shunning d'in ta, tayi simple makeup tayi kyau dan itama kyakkyawa ce, Mukullin motar ta, ta d'auka ta fice gidan ba tare da sanin Hajiya Mariya ba.




****************************
Haidar yau tun zuwan sa office ba abunda ya aikata, bashi da natsuwar yin komai, gashi tun shigowar sa ma'aikatan wurin ke masa Allah ya sanya alkhari wanda bai ga abun fatan alkhairi ga auren Karuwa ba, takardun dake gabansa kallon su kawai yake ba tare da ya aiwatar da komai ba, shigowar Rauda yasa ya d'aga kai ya kalli k'ofa, ta sakar masa murmushi tana shigowa cikin yanga da yauk'i kamar zata fad'i, Haidar ya d'an kawar da kansa gefe, zama tayi saman kujera tace "Yaya ina wuni", "Lafiya lau" ya amsa da sakin fuska, "Ya aiki?", "Alhamdulillah", Ta soma jan sa da hira, ya d'an sake mata, a zuciyar sa yana jin yayi amfani da ita wurin kaucewa auren sa da Bongel, ko auren ya tabbata ya rabu da ita cikin sauk'i.



*************************
Rauda cike da tsantsar farin ciki ta dawo gida, ta tarar da Irfan yana zaune falo yana kallon carton, ta jawo sa da cewa "Yaushe kazo?", "D'azu granny tazo dani", Ta shafa kansa da cewa "Bara ina zuwa", D'akin Hajiya Mariya ta nufa, cikin tsantsar farin ciki take sanar da ita, irin tarbar data samu daga Haidar yau, Sam zancen bata d'auke sa da muhimmanci ba, a ranta tace "Ya samu wacce zai aura ai dole zaki ga far'ar sa, tunda ya gujewa auren ki", A zahiri kuwa ta nunawa Raudah ta cigaba da basa kulawa, ta haka zata samu gurbi a zuciyar ta, bata son Rauda ta cire rai ga samun sa, dan ba zata yi k'asa a gwiwa ba wurin ganin ta zama surukar gidan Maishanu a karo na biyo, Ta gamsu da zancen mahaifiyarta ta fito tana murna taja Irfan zuwa d'akin ta.


***************************
Ana saura kwana biyu d'aurin aure Asiya tazo malumfashi, Bongel tayi farin cikin zuwan ta, zata samu wacce zata rik'a fad'awa damuwar ta, tana rage nauyin k'irjin ta, ana gobe d'aurin aure Asiya da sauran k'awayen Bongel na garin suka shirya fulani day, Bongel taso hana su, suka ce sai sun yi, a farfajiyar gidan suka shirya, k'awayen amarya sukayi ankon kayan fulani, kowacce rik'e da k'warya da nono, Amarya tayi ado cikin kayan fulani tayi kyau sosai, ta fito sak fulani, kid'an k'warya kawai ke tashi a farfajiyar gidan, k'awayen amarya na chashewa sai dare kowa ya watse, Bongel tun kafin su watse ta koma cikin d'aki, fargabar d'aurin auren ta gobe yasa sam bata walwala, Asiya ta fuskanci haka, ta sameta dan k'ok'arin kwantar mata da hankali.



"Bongel" Asiya ta kira sunanta, "Na'am" ta amsa tana tashi daga kishingid'en da tayi, "Nasan damuwar ki akan auren Haidar ne, ina so ki cire damuwar komai a ran ki, In Shaa Allah Haidar zai zama abokin rayuwar ki nagari, da sannu zaku so juna, baki shan jin labarin wanda sukayi auren da babu soyayya daga baya ya koma soyayya ba, baki san labarin auren Fetta da Suraj ba, sunyi aure babu soyayyar junan su, daga k'arshe suka mutu a soyayyar juna", "Kada ki had'a aurena da na wasu, nawa yasha  bambam da saura, Taya kike tunanin mutumin da ya nuna mun k'iyayya fiye da kowa a duniya ya zama abokin rayuwata, ya kike tunanin k'iyayyar sa gare ni ta koma soyayya, hakan ba zai tab'a yiyuwa ba, ki rik'a auna zantukan ki a ma'auni kafin ki furta su", Asiya tayi murmushin takaici, tasan Bongel ba zata fahimce ta yanzu ba, amma tana da kyakkyawan zaton gaba zasu so juna ita da Haidar.



********************************

K'ofar gidansu Bongel ya cika da al'ummar Annabi yan' d'aurin aure, wakilan amarya da ango duka sun hallara, wanda Hamma Siddiku ne wakilin ango sai washe baki yake ganin sa cikin manyan mutane an karrama shi matsayin shi na wakilin ango, Haidar na zaune gefe d'aya, kallo d'aya zaka masa kasan ango ne daga shigar sa, kusan ince yafi kowa shiga mai kyau da tsada a wurin, blue shadda ce d'inkin babbar riga, tayi masa matuk'ar kyau, hular sa zanna ta zauna daram a kansa, sai dai sam babu walwala a fuskar sa, kowanne ango yau ranar farin cikin sa ce, sab'anin shi da aka k'ak'aba masa karuwa da sunan zata kula da tarbiyar yaron sa, ya samu natsuwa a tare da ita, ganin gidansu yasa a ransa yace "No wonder take neman maza, ta kasa rik'e talaucin ta, sai ta samu kud'i ta k'azamtacciyar hanya", Yaja siririn tsaki dashi kad'ai yaji abun sa.


*******************************

Hisham yau kwata kwata bai fito daga d'akin sa ba, balle yasa ran zuwa d'aurin aure, ba zai iya halarta ba, kwance yake k'udundune cikin bargo, zazzab'i mai zafi ya rufe sa, k'asan zuciyar sa yana jin ba zai tab'a hak'ura da Bongel ba, ko anyi auren yana da tabbacin sai ta fito ta aure sa, sanin Haidar ba zai tab'a son ta ba, ya d'arsa abu a zuciyarsa mai wuyar gogewa, yasan mu'amalar aure ba zata tab'a shiga tsakanin su ba, ga sanin halin da yayi wa yayan sa.



*******************************
Bongel tunda taji muryar Hassan na fad'in an d'aura aure, ta nemi natsuwarta ta rasa, zazzab'i ya soma rufe ta, sai dai tayi k'arfin halin rashin barin ya kwantar da ita, Farin cikin data hango zalla a fuskar mahiafiyarta da k'annenta guda biyu ba zata bari ya gushe ba, Haka tayi ta k'arfin halin danne damuwarta, k'asan zuciyarta kuwa zallar damuwa ce had'i da fargaba, yayin da gangar jikin ta ke amsar gashin zazzab'i.


****************************

Haidar daga wurin d'aurin aure, gida ya umarci drivern sa ya kai sa,


    Kayan ya cire, ya rage daga shi sai boxer da singlet, wayoyinsa ya jawo da zumar kashewa, baya son damuwa, yana buk'atar keb'ewa shi kad'ai, Kiran Raudah ya shigo, ya d'auka yan sawa a kunne,


Kuka ta fashe mishi dashi tana cewa "Haba dear kasan irin son da nake maka amma ka auri wata, kana so zuciyata ta buga in mutu ko", Kuka da kalamanta haushi suka soma basa, amma ya dake yace "Am sorry kinji, ki daina kuka, ki samu kiyi bacci ki huta, will call u later", Tana shesshek'a kuka tace "Ok, Ina sonka Yaya Haidar please ka tausaya ka auren ni", "Is Ok" ya fad'a yana kashe wayar, tare da dan' dafe kansa, "Anya zaka iya kuwa", Zuciyarsa ta ayyana masa,


  Rauda taji sanyi a ranta na ganin alamar soma shawo kan Haidar, duk da k'asan zuciyarta tana jin tsananin kishi da haushin auren nasa.


*NOT EDITED*

*OUM MUHRIZ*
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

*HASKE WRITERS ASSO...*

ASHIRIN DA BIYAR


Yan' uwa da abokan arzik'i nata kai kawo gidan su Bongel, Abinci ya wadata, kowa yaci ya k'oshi, Ammi ta aiko da kayan abinci da komai na buk'atar hidimar bikin sanin su Bongel ba masu k'arfi ba ne, Nene farin cikin ta ya kasa b'oyuwa, duk wanda ya kalleta zai san tana cikin farin ciki, Ramla da Asiya sai kai kawo suke, suma kallo d'aya zaka musu ka hango zallar farin ciki,


   Ana gama sallar la'asar aka soma shirye shiryen kai Amarya, Dan tuni motocin d'aukar Amarya suka zo, da dangin ango kusan mutum sha biyar, kowa ya k'ara shaida Bongel ba k'aramin dangi zata shiga ba, masu taya ta murna nayi, yan hassada suma suna yi.


***************************

Bongel ta rasa meke mata dad'i ko tunanin me zata yi, zuciya da tunanin ta ya cunkushe wuri d'aya, idan taga yadda mutane ke taya ta murna sai taji itama murnar ya kamata tayi Allah yayi mata rahamar yin aure, yayin da ta tuna waye mijin sai taji komai ya tsaya mata cak, ta nemi natsuwa da farin cikinta ta rasa, Zaune take shiru a d'akin Su Asiya nata faman tsokanar ta, bata tanka su, sai ma niisa da zurfin tunani da tayi,


  "Ku fito, a tafi kai Amarya" Taji muryar Goggo Hajjo na fad'a, K'irjinta ya doka, tana jin tamkar ace akwai wata hanya mai sauk'i da zata zillewa auren, ba tare da  tayi hurting kowa, sam bata sha'awar had'a inuwa d'aya da Haidar, Shigowar Nene ya katse mata tunani, Cikin sanyin murya da kulawa Nene tace "Bongel yanzu kin tashi daga budurwa kin shiga sahun matan aure, wani nauyi ya hau kan ki, ina so ki rik'e gaskiya da amana, ki zama mai ladabi da biyayya ga mijin ki, ki sa hak'uri a rayuwar ki kiyi ta hak'uri da addu'a, Allah yayi miki albarka ya baku zaman lafiya mai d'aurewa", Rungume Nene tayi ta fashe da kuka, tausayin yar' ta taji ya shige ta sosai, amma ya zasuyi dole dama rana irin ta yau na zuwa da aure zai raba su, ko babu aure akwai mutuwa,

Bongel na kuka haka Goggo Hajjo ta raba ta da jikin Nene, aka ja ta zuwa mota, Motocin kai Amarya suka d'aga zuwa garin katsina, Cikin yan' kai Amarya hadda Fatsuma da Dije wanda gulma zata kai su.



**************************

Gidan Dada suka soma zuwa wanda shima cike yake da yan'uwa da abokan arzik'i, Hannun Goggo Hajjo rik'e da na Bongel suka shiga gidan, ana ta faman gud'a, Bongel mamakin al'amarin ubangiji take yadda ya juye komai lokaci d'aya, daga matsayin ta na yar' aiki a gidan, yau gata ta shigo matsayin surukar su, Har gaban Dada aka kai ta, wanda Dada ta buk'aci kowa ya basu wuri, Har su Goggo Hajjo suka mik'e suka fita, Dije da Fatsuma rai bai so ba sun so jin me Dada zata ce.


Dada ta numfasa da cewa "Yau na d'aya daga cikin ranaku mafi farin ciki gareni, ganin auren ki da Haidar, ina da tabbacin had'in nan zai zama alkhairi" Bongel tayi shiru k'asan zuciyarta tana k'ara gaskata soyayyar da Dada ke mata daga Allah ne,


  "Bongel kada ki dubi auren nan a matsayin wanda babu soyayya a ciki, kisa a ranki tamkar auren soyayya kuka yi da Haidar, a zamanin mu mace bata ganin mijin da zata aura sai ranar da aka kaita, kuma haka zasu yi hak'uri da juna su zauna, har su fara son junan su, Mace ita ke taka muhimmiyar rawa wurin ganin soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin ta da miji, Namiji da kike ganin sa tamkar sakarai ne akan mace, Bongel kina da komai da zaki iya jan hankalin namiji dashi, kada kiji tsoro ko shakkun rashin samun soyayyar sa, Namiji na son kula, kyautatawa, ladabi da biyayya, uwa uba ki rik'e ado, kwalliya, tsafta da girki, Su kad'ai sun isa su sa ki gina k'auna a tsakanin ku", Bongel shiru tayi tana sauraren Dada, tana kyautata zaton dan bata san irin k'iyayyar da yake mata ba ne take fad'ar haka, watak'ila da babu k'iyayya zata iya shawo kansa ta hanyar abubuwan da Dada ta lissafa, sai dai mutum irin Haidar ba irin wanda mace ke samun kansa ba ne cikin sauk'i, ita sam ma bata sha'awar zaman su inuwa d'aya, kowa yayi rayuwar su, har zuwaa lokacin da Allah zai kawo hanyar rabuwar su cikin sauk'i, Dan tana da tabbacin Haidar ba zai tab'a amsarta matsayin matar sa ba, Hisham ya goga mata bak'in tabo a wurin sa, wanda babu mai fitar da tabon sai Hisham.


Dada ta cigaba da cewa "Zan sanar dake tak'aitaccen tarihin mu, dan kisan family da zakiyi rayuwar aure, kuma kisan waye mijin ki", Bongel ta jinjina kai, Dama ta dad'e tana son sanin hakan, Hisham tana tare dashi ne,  ba tare da tasan ainihin tarihin sa ba,


  Alhaji Dikko Maishanu(a shafin da ya gabata nayi kuskuren suna na saka Ard'o matsayin mijin Dada) shine mijina wanda matsayin kakan Haidar yake, bafullatani ne gaba da baya, mutum ne mai halin dattako, yana da tarin dukiya wacce ya mallaka da gumin sa, dan' kasuwa ne sosai wanda kowacce sana'a tab'awa yake in dai zata kawo masa kud'i, Mu biyu ne matan sa ni da Salamatu(Inna), yaranta bakwai, ina da biyar Abbas shine babba(baban su Haidar), sai Mu'azu, Rabi'a Mami, Sadiya, Aisha, Duka yaran gidan kansu a had'e yake,


   Abbas auren zumunci aka musu da Ammi wacce da mahaifinta da Dikko uwar su d'aya uban su d'aya, tun tana k'arama bata da wurin zuwa hutu sai gidan nan, haka yasa suka shak'u da Abbas har zuwa girman su, soyayya ta shigo ciki aka musu aure, Abbas duk cikin yaran Dikko yafi kowa zafin nema, wanda hakan yasan cikin k'ank'anin lokaci yayi kud'i, kowacce sana'a shima yana yi kama daga man fetur, kwangila, sarrafa masarufai da sauran su, arzik'insa ya shahara ta yadda manyan yan' siyasa suke huld'a dashi, mutane da dama kan biyo ta hanyar sa ya samar musu alfarma, yayi wa mutane silar samun aikin sun fi a k'irga ciki hadda Vice councilor na makarantar ku", Bongel a zuciyarta tace "Shiyasa Hisham yake da damar admission kenan, dan Babanshi ya samar wa VC matsayin shi",



   Dada ta cigaba da cewa "Auren su da shekara d'aya Ammi ta haifi Haidar, bayan shekara biyu ta k'ara haihuwar Hisham, daga su bata sake haihuwa ba, sunyi ta neman haihuwar har sun gaji sun daina, Haidar ya taso miskila wanda bai cika son hayaniya da shiga mutane ba, Hisham ya bambamta dashi yana da son mutane, surutu da barkwanci, Duk da bambamcin halayyar  su akwai shak'uwa mai k'arfi tsakanin su, kasancewar su kad'ai ne wurin iyayen su, suna k'aunar junan su, d'aya baya son b'acin ran d'aya, Makaranta d'aya aka saka su, Haidar yafi Hisham da aji, Haidar yana da k'ok'ari sosai tun shigar sa makaranta yake ta d'aya, Da suka kammala secondarya ya kai su london wanda a can sukayi degree, bayan dawowar su, Abbas ya yanke shawarar bud'e babban company, Haidar ya bada k'arfin gwiwa sosai wurin ganin ya tabbata, cikin ikon Allah ya gina katafaren company wanda ya zuba mak'udan kud'i, ya jawo Haidar da Hisham ciki, hasalima ma sunan su ya saka ma Company H&H global resources, Ya bud'e da shekara biyu Alhaji Sani Maigoro shima shahararren dan' kasuwa ne wanda abokin sa ne tun yarin ta, yazo masa da buk'atar yana so su had'a kasuwanci, ya bada kud'in sa a saka masa ciki, Girma da nauyin sa da Abbas ke ji yasa ya kasa cewa a'ah amma sam baya son had'a kasuwancin sa da kowa, daga lokacin ya zama Alhaji Sani shima yana da share a ciki, Haidar da Hisham kowane ya bada himma wurin ganin cigaban company, wanda kowannen su Abba ya cire masa share d'in sa, a shekara ana lissafi a gaya wa kowa ribar sa,


   Ana haka Alhaji Sani yazo wa Abbas da tayin had'a auren Haidar da yar' sa Hafsah, Abbas bai musa ba, sai ma dad'i da yaji na ganin yana son had'a zuri'a dashi, Daga haka suka tsara Hafsah ta rik'a zuwa gida wurin Ammi, ko Haidar zai ganta su daidaita, Haka kuwa aka yi kusan kullum Hafsah na gidan, har sun saba da Ammi sosai, itama Ammi taji sha'awar Hafsah ta zama surukar ta, kasancewarta mai hankali, natsuwa da ladabi da biyayya,  ba zaki ji yar' Hajiya Mariya dan ko kusa bata d'auko halayyar ta ba, Haidar a hankali ya soma sabawa da Hafsah, shak'uwa ta shiga tsakanin su daga baya ta juye zuwa soyayya, ba'a d'auki lokaci ba aka yi auren su, zaman lafiya da kwanciyar hankali ne tsakanin su, Wata tara da auren su Hafsah ta haifi Irfan, wanda yana zuwa duniya, Allah ya d'auki ranta ba tare da tasan me ta haifa ba, Irfan bai san dad'in uwa ba, bai tab'a jin d'umin mahaifiyar sa, ina so ki cike masa wannan gib'in, Haidar ya shiga tashin hankali na rashin Hafsah, ya jima bai dawo daidai ba, rashin Hafsah yasa har yanzu ya kasa bud'e k'ofa ga kowacce mace, Bongel ina so ki maye gurbin Hafsah a rayuwar Haidar, ina so ki fitar dashi daga k'uncin rashin ta, you should make him love again, ina neman wannan alfarma a wurin ki",


  Bongel gaba d'aya ji tayi Dada ta d'aure ta, Tausayin Irfan ya k'ara ninkuwa a zuciyarta, haka Haidar shima taji tausayin sa dan rasa mata ta gari ba k'aramin abu ba ne, sai dai abunda Dada ke nema a wurin ta bata jin zai tab'a yiwuwa, ta sani har abada ba zata samu gurbi a zuciyar Haidar ba, ta zama tamkar mujiya a idon sa, baya ganin hasken ta, mummunan zaton da yake a kanta, ba zai bari ya tab'a ganin hasken ta ba, har ta samu soyayyar sa, "Ya Hayyu Ya Qayyum" Ta furta a ranta, ba k'aramin aiki ne a gabanta ba,


   Dada ta tashi ta d'auko wani turare ta zuba mata a jikin alkyabbar ta, Tace "Allah ya haskaka rayuwar auren ki Bongel, Allah yaa baku zaman lafiya da zuri'a ta gari, Allah yasa kuyi alfahari dani sanadiyyar had'aku da nayi", Bongel a ranta ta amsa da "Amin" Ba dan tana sa ran yiwuwar haka ba.


Dada ganin lokaci yaja sosai tace azo a tafi kai ta gidan ta.


*********************************
Rauda ta fito d'akin ta tana mik'a da hamma alamar bacci bai ishe ta ba, Ta kalli Hajiya Mariya dake faman gyangyad'i kan kujera tace "Mum kema baccin kike", Hajiya Mariya ta bud'e ido da cewa "Ba dole ba, tun zuwan yaron nan bama samun bacci", "Toh ai kece kika d'auko sa Mummy, gashi kaina ciwo yake mun" Ta fad'a tana tunzura baki, Hajiya Mariya tace "Bansan haka abun zai juye ba, nayi ne dan a fasa auren ya dawo kan ki, ban da kunyar kada suce na kasa da tun ranar zan mayar da shi, amma yau zai koma", Rauda tace "Idan kika mayar dashi still zasu ce kin kasa ne just 2days yayi fah", "Yanzu ne lokacin da ya kamata na mayar dashi", "Saboda me?" Rauda ta tambaya da son jin k'arin bayani, "Ina mayar dashi gidan Haidar za'a kai sa, kinga zai hanasu sakewa yadda ya kamata balle bagidajiyar can ta samu shiga wurin Haidar", Raudah tayi dariya tace "Kaii Mummy ina son ki", Sukayi dariya.


***********************************

"Shigo da k'afar dama kiyi bismilla", Goggo Hajjo ta fad'a, Bongel k'irjinta ke wani irin dokawa, tsoro da fargaba suka dabaibaye ta, zata shiga gidan mutumin da ya tsane ta, baya ganin ta da k'ima ko kad'an a matsayin matar sa, ya rayuwarta zata kasance a auren da babu soyayya, Jifa k'afarta take ba tare da tasan ina suke nufa ba, sai jin zaman ta tayi kan lumsassan katifa, d'akin ya gauraya da k'amshin turaren wuta mai masifar dad'i,


  "Gida har gida kam, Allah yasa dai a samu zaman lafiya", Ta tsinkayi muryar Fatsuma na fad'a, Dije tace "Amin dai", Sai kuma taji sun koma magana k'asa k'asa wanda ko shakka babu gulma ce.


   Kusan awa d'aya tana jin hayaniya, kafin ta fara jin shiru alamun mutane sun soma tafiya, Goggo Hajjo ta zauna kusa da ita tace "Toh Bongel mun kawo gidan ki, Hak'uri da addu'a sune gaba, kibi mijinki sau da k'afa, Allah ya baku zaman lafiya, mu zamu tafi", Ta mik'e, Bongel na jin fitar ta, ta fad'a kan gado ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.


***********************************

Haidar wanda tun dawowar sa d'aurin aure yake d'akin sa, yana sak'a da warwara shi kad'ai, tunanin sa gaba d'aya kan yadda zai fitar da Bongel rayuwar sa, hayaniyar yan' kawo amaryar a kunnen sa, yayi ta faman tsaki, Bayan wucewar su ya fito kitchen ya d'auki yoghurt a fridge ya zauna a falo yana sha a natse, Sip na k'arshe yayi, ya ajiye kofin kan centre table dake gaban sa,  Ya mik'e da cewa "Tun yau ya kamata  ta fara sanin matsayin ta, ta fara dana sanin auren HAIDAR", Ya d'an ciza lips d'in sa na k'asa, ya nufi d'akin da yake kyautata zaton nan aka kai ta.



*******************************
Sai mu had'u gobe ko😂 nasan kun baza idanu karatun me zai fara mata dashi🤣toh sai gobe🤪





OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*

Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad

*HASKE WRITERS ASSO...*

ASHIRIN DA SHIDA

  *BANYI EDITING BA*

Bongel wacce tun tafiyar su Goggo Hajjo take kwance tana kuka, ta kasa tsayar da kukan balle ta aiwatar da wani abu, Haidar kai tsaye ya murd'a handle na k'ofar ya shiga, Bongel jin an bud'e k'ofa ta d'ago kanta da addu'ar Allah yasa wani daga cikin yan' uwan ta ne ya dawo, idonta ya sauka kan fuskar sa, k'irjinta ya doka tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa,


"Da kin adana hawayen ki zuwa gaba zasu miki amfani", Haidar ya fad'a ba tare da ya sake kai duban sa gareta ba, Bongel wacce kanta ke sunkuye k'asa sam bata fahimci mai yake nufi da hakan ba,


Gyaran murya yayi jin shiru babu alamar taji zancen nasa, Ya nisa yace

"Duniya da kowa ya shaida an d'aura auren mu, a idon mutane kike matata, amma ki sa a ranki bakiyi aure ba, igiyar aure ko d'aya bata hau kan ki ba, dan bazan tab'a karb'ar ragowar wasu matsayin Matata ba", Ya k'arasa da cewa "And one last thing turaren da kika yi amfani dashi dan seducing d'ina, ba maza irin Haidar ake wa haka ba, ki canza salo", Yana fad'ar haka ya fice, tun shigowar sa yake shak'ar k'amshin turaren, wanda dad'in sa da k'amshin sa yasa yake jin tamkar ya manna jikinsa da nata, wanda hakan yasa yake kyautata zaton tayi amfani dashi ne dan jawo sa gareta,


Bongel hawaye ta cigaba da yi wasu na bin wasu, dama tasan tunda ta aure sa, ta bud'e kofa da wulak'anci kala kala, bata gidan sa ya mata, balle yanzu da take k'ark'ashin sa, Ganin kukan ba zai mata maganin komai ba, ta shiga band'aki ta d'auro alwala, ta soma nafilfili tana rok'on Allah zab'in alkhairi a rayuwar ta, Raka'a goma sha biyu tayi, Kafin tayi shirin bacci ta kwanta, cikin minti biyar bacci ya d'auke

Please Login or Register in order to submit comment