Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KURSUM
Na Xarah Bukar
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com


Kursum 1 to 20 Posted by XARAH ABUBAKAR on
NOVEMBER 13, 2016 KURSUM by ~Xarah Bukar Page ~
Sauko wanshi kenan daga jirgin sama,daka ganshi kaga
dan hutu ne,dago ne fari kakkyawan gaske,ga dara daran
sexy eyes dinshi……….driver yaxo airport ya dauke shi
sai cikin garin bauchi,har hotel din daya sauka driver ya
kaishi…. Bayan awanni kalilan harya shirya cikin kanana
kaya masu kara fito da ainuhin kyawun shi,ya kira
abokinshi huzaifa dan ya yadan zaga dashi yaga gari, sun
gama zagawa suka biya wani eatery dan cin abinci……
Tafe suke suna dan hira,kursum na cewa kawarta itafah
ta gaji da wannan wahala su kenan kullum yan Aike suka
zama, sauran dalibai na hostel amma su suna nan suna
supervising kayan abincin makaranta har sai an shigar
da komai kitchen,Sumy tace haba kursum miye aciki toh
ai aikin lada ne kuma koba komai ai mun ga
gari…………..kursum taja tsaki tace to ai sai kije ke kadai
saboda ni xan dan leka gurin masu wasa da monkeys
(biri). Sumy tayi kwafa ta wuce abunta inda sabo ai ta
saba da halin aminiyarta…….. Kursum kenan,yarinyar
yar kimani shekara sha bakwai a duniya,ga kyau, sam
batason hayaniya, amma idan ka tabo ta sai inda karfin
ta ya kare Wannan kenan…. *Xarah Bukar* *Dedicated
to Bady social* ~Luv u all~ KURSUM By ~Xarah Bukar
Page ~ Gaskia garin nan fah akwai mata hadaddu, ya
kamata ace kafin in bar garin nasamu babe (yarinya)
wanda xan huta da ita, huzaifa yaja tsaki ya kalle shi
kaidai yazid kana nan da halinka na playing mata bansan
randa zaka natsu ba, Ina fatan Allah yakawo wacce za
tayi maganin ka……….Yazid yace aini babu macen data
isa tayi magani na, asali ma ban dauki su abakin komai
ba face rigar canxa wa Sumy ta gama aikin da take ta
biya eatery cin abinci, shiganta kenan tayi ido hudu
dashi, wow ta fada cikin xuciyan ta gaskia kiya guy
dinnan is hot ya hadu iya haduwa…. bata ida xancen
xuci ba kawai taji ya mata sallama ai ba shiri ta saita
kanta ta amsa ta gaishe shi, da fara’arsa yace mata ni
sunana habib acewar yazid Ina fatan baza kimin rowar
sunanki ba… tayi murmushi tace sumayya suna na yace
nice name sumy Ina kike xama ne naganki da school
uniform, tace aikina director dinmu yayi school din
bayan wajen nan yake ma, yace okay nagane skull din.
Yayi murmushin mugunta yace naga kinmin ne gashi
you are so quite Ina fatan dai xaki amsa min tayina,
sumy ta sunne kai xuciyan ta fal da farin ciki, yau dai ta
samu prince charming din da take mafarki…….. yazid ya
dauko wani hadadden xoben azurfa mai shegen kyau da
tsada ya zurawa mata a hannunta amatsayin son dayake
mata sumy tayi godiya tace zata wuce dare ya farayi
yace yaushe xamu sake haduwa, tace ko xuwa gobe
muna iya haduwa anan yace toh Allah kaimu ta wuce.
……. yayi murmushi mugunta da alaman yarinyan bata
da wayo, tabbas zan samu abunda nake sha”awa tattare
da ita..ya wuce waje wajan abokin kinshi daya cika yayi
fam dan jiran ya dawo su wuce huzaifa yace Allah ya
shirye ka yace Amin suka wuce……. Ina Kursum take ne?
Waye yazid ? Wace kuma sumy ? Mai yakai kursum da
sumy makarantar boarding wanda babu marabarta da
gidan marayu ? Ku buyoni dan jin asalin labarin *Xarah
Bêê* *Dedicated to Bady social* ~Luv u all~ KURSUM By
~Xarah Bukar Page ~ Har kusan yamma sannan ta dawo,
ta tadda sumy kwance sai faman murmushi take tana
lumshe idon ta kursum ta daka mata duka tace lafiya ki
kike wani murmushi kaman wata charisma goat (akuyar
krisimeti) ko dai baba ne ya shigo gari, sumy tace kedai
yau nayi new catch fah guy din ya hadu iya haduwa ba
karya, wani irin so da kaunan shi ke ratsamin
zuciya……….. Kursum ta yatsane fuska taja tsaki, kedai
raba kanki da soyayya tun yanxu saboda maza basu da
tabbas kila ma dan iska ne, sumy tace haba banda habib
dina dan kuwa nasan yana sona, munyi dashi ma xamu
hadu gobe dan Allah kursum ki taimaka ki rakani gobe
kinji my cwt sis:| Yazid kwance a tafkeken dakin hotel
din daya sauka da alama waya yake, yace haba xee kiyi
hakuri mana nace makin nan na 4days xan dawo duk kin
dakamin hankali….xee tace haba ya yazid tun jiya fa
yakamata ace ka dawo wlh nayi missing dinka sosai gaba
daya garin kano yamin zafi, jiya har wajen ummanka
naje na mata wuni ko zan kanga amma shiru kuma gashi
wayoyin ka duka akashe…..kiyi hakuri my love zan dawo
dana gama aikin dana ke abubuwa sun min yawa ne,
tace to amma dai kayi promising nan da 4days ko yace
eh ya kashe wayan……xee rigiman ki yayi yawa wlh
amma dole in koma saboda dad bai san bana gida ba.
Makaranta ce babba nagani nafada mai tsadar gaske
wanda sai dan wane da wane, ita ba gidan marayuwa ba
kuma bawai makaranta jeka ka dawo bane ko boarding,
yawan ci student (dalibai) din dake makarantar iyayensu
basu da lokacin kula dasu, tun yara na kanana ake kai su
har sai sun gama senior year sunkai 18 years old
(shekaru goma sha takwas) Sannan iyayen su ke zuwa
daukan su…….Gimbiya Hafsatu itace director din
makarantar gata da zalama dason abun duniya,babu
ruwanta idan kakai 18years iyayenka basu zo daukan
kaba saita aurar dake acewarta iyayenka sun manta
dakai ne…… Yau ta kama weekend fito wansu kenan
daga hostel zasu shiga gari, daka gansu kaga aminan
juna ….kursum tace kin tabbata saurayin nan naki zai zo,
ina fatan dai ba jirga ki zai yiba sumy tayi dariya tace
haba dai aini na yadda dashi dari bisa dari, maybe ma
yana can yana jirana ma Sun iso wajen haduwan kenan
sumy tace wayyo na manta da xoban daya bani jiya akan
gado kuma gashi namai alkawarin bazan cire shi ba dan
Allah kursum kiyi hakuri ki jirani anan barin koma hostel
in dauko. Kursum ta wurga mata harara, tace kedai
wallahi baki da wayo sam, dan wahala shine xaki koma ki
dauko toh ai sai kije ni ina nan idan kuma kin dade in
kara gaba abuna, “sumy tayi murmushi ta bar wajen da
sauri ta. Tana nan tsaye har kusan minti goma, taji wani
lausassan murya yana mata sallama ta juyo sukai 4 eyes
saida numfashin ta ya kusa dauke wa saboda ya hadu iya
haduwa, ya sakan mata wani irin yaudararen murmushi,
ta hade rai tace malam nasan kane, yazid yace a’a baki
sanni ba, asalima ni bako ne yau Nashigo garin suna na
kabir yana murmushi yana shirin jawota jikin shi, ai bai
ankara ba ta wanke shi da mari an gayama ni yar iska ce,
waye ma kai dahar xaka naimi tabani………kallon ta
kawai yake yana shirin magana sumy ta iso wajen fuska
a murtuke tana tambaya meke faruwa taja kursum gefe
tace shine saurayin nawa fa naga kina shirin yimai rashin
mutunci kursum tace sis ki raba kanki da guy dinnan
kabir ban yadda dashi ba da alama yana da wani hidden
agenda tattare dashi. Sumy ta daure fuska tana mata
kallon bakida hankali wato bakin ciki kike min danke
baki da saurayi toh baki isa ki rabani dashi ba yanxu
nafara sonshi kuma harda aure xamuyi, sunan shi habib
not kabir tayi tsaki ta bar kursum nan tsaye da mamaki.
Yazid yace amma kawarki bata da mutunci tana ganina
tafara zagina, sumy tace dan Allah kayi hakuri kar kayi
fushi bata sanka bane, yace to ya wuce ya kike me zan
samu ne yana magana yana rike da hannunta yana lashe
lips dinsa sai lumshe ido yake, tace lafiya kalau nake”
anan garin kake zama ne yace eh ai gidanmu bai da nisa
daga nan, iyayena sun rasu, wajen kawuna nake tun ina
karami tace wayyo Allah yaji kansu da rahma ta
tausayamai sosai wani irin sonshi ke kara shiga zuciyar
ta….. Ni yanxu bani da kowa sai kawuna sai kuma ke, “ya
kara janyo ta jikinshi yaxe plz sumy karki kujeni I love
you with all my heart, xaki aureni ? “Ba shiri sumy tace
eh kaman dama jira take ( I pity u sumy) , yace to yanxu
ya zaai Kince parent dinki suna kano kuma ni inaso in
mallake ki amatsayin mata ta, tace babu damuwa
babana sau daya yake zuwan min visting a shekara kuma
yana sona sosai idan yaga na auri wanda nakeso shima
zai ji dadi, yanxu kawai director din makarantar mu
Gimbiya Hafsatu xaka samu sai kuyi magana saika turo a
naimi auran ko gobe kakeso ana iya daurawa….. Shi kam
sai kallonta yake azuciyan shi yace lailai yarinyan nan
bata da wayo ko kadan, burina kawai in samu abunda
nasamu in tattara in gudu bazama ta kara gani na ba.
Yazid yace kina ganin babu matsala danni acikin kwana
uku nakeso ayi auren dan baxan iya rayuwa bake ba,
tace babu matsala gimbiya Hafsatu tasan abunda ya
kamata…ya rakota har gaban makarantar sannan sukayi
sallama ta wuce ciki shima ya tafi yana farin cikin da
baisan na miye ba. Hmmmm Muje xuwa dan jin cigaban
labarin *Xarah Bêê* *Dedicated to Bady social* ~Luv u
all~ KURSUM By ~Xarah Bukar Page ~ Tangareren
Mansion (gida) ne mai girman gaske kaman estate, da
ganin gidan kasan dukiya ta zaunawa masu shi…….
Hajiya hadiza ce zaune acikin kataferen parlour din
gidan wanda yasha dukiyar gaske da kayan alatu….
Fuskan nan nata ba annuri :evil::evil::evil: ko kadan, tasha
uban shade (tabarau) a ido….taja dauri har goshi irin no
respect dinnan, tana jiran sauko wa Alhaji Tanimu danta
zazzaga mai masifar data saba. Alhaji ya sauko yana wlh
hadiza baki isa ki hanani xuwa ganin yarinyan nan ba
kuma dole in dawo da ita nan da xama tunda gidan
ubanta ne, haba wai yaushe xaki canza halin ki ne tunda
na aurenki bance Alhamdulillahi ba saboda bakin cikin
da kike shuka min. Ta ja tsaki tace indai ka dawo da
sumy gidan nan toh saidai nafita in bar maku gidan,
kawai dan ya’ta ta rasu shine ka samo yarinya a titi ka
kawo gida kana rainonta shekara da shekaru, gaskia
Alhaji ka canxa Shawara. …:evil::evil::evil: Alhaji yayi
kwafa ya fice daga gidan, yana mamakin halin rashin
imani irin na hadiza, “duk da ta makance, amma babu
halinta daya canxa. Alhaji tanimu da malam habu
(baban hajiya hadiza kenan) aminan juna ne sosai, kafin
malam ya rasu ya roki Alhaji ya auri hadiza tunda bai
sake aure ba tun bayan mutuwar matar shi ta farko,
yace hadiza ta manya ta ga shekaru sun ja amma shiru
babu manai ma….dalilin auren alhaji da hadiza kenan.
Hadiza ta tsani alhaji sosai, ita aganinta ta wuce ajin da
zata auri tsoho kusan sa”an ubanta..koda tayi rashin
yarta wajen haihuwa bata damu ba, amma sai ta
nunawa alhaji ta damu sosai har a sanadiyar haka
tasamu ciwon ido ta makance Wacece kursum ? Kursum
marainiyar Allah ce bata da kowa sai sumy , ranar da
uwarta ta haife ta tayi niyyan jefar da ita atiti tare da
ajiye mata 17 white diamonds (lu’u lu”u) da pink
daimond guda daya tare da rubuta kursum ajikin wani
hankecheif pink mai kyau amatsayin sunan data ba yarta
acewarta duk wanda ya tsince ta bazaiyi wahalan
rainonta ba tunda ga dukiya……….amma aminiyar
uwarta mairo ta tausayawa jaririyar ta bada shawaran
kaita inda xaa raineta harta girma, shine mairo ta kaita
makarantar da take yanxu ta damka ta hannun gimbiya
hafsatu sannan tabata 18 diamonds din acewarta duk
shekara adauki diamond daya a biya mata kudin
makaranta da abubuwan da zata bukata, sannan idan
yarinya ta cika shekara goma sha takwas sai abata pink
diamond din dan tasamu na rike kanta a rayuwa.
Wacece sumy ? Sumy diyace ga Alhaji tanimu da hajiya
hadiza, asali yan kano ne, tun tana karama alhaji yaje
gidan marayu yayi adopting dinta arashin rasa yarsa da
yayi tun haihuwan ta, shiyasa ya dauki son duniya ya
dorawa sumy, sabanin hajiya hadiza data tsane ta kaman
mutuwan ta……dalilin da yasa ma alhaji ya dauke ta tun
tana shekara hudu a duniya ya kaita makarantar da take
yanxu haka, wajen shekara goma sha uku kenan hajiya
bata sata a ido ba Wanene Yazid ? Yazid Imam Ambrusa,
dan kimanin shekara 29 a duniya, “da tilo ne ga alhaji
imam da hajiya mairo, cikakken haifefen dan kano ne,
abunda yaga dama yakeyi iyayensa basu wani damu
dasa masa ido ba shiyasa bai dauki mutane da
relationships abakin komai ba…….. huzaifa ne kadai
abokin shi tare suka yi school of aviation dake kasar
England, yanxu haka shi yazid din cikakken pilot
(matukin jirgin sama) ne, shine manajan company din
babansa na jirgin sama….Ambrusa & Sons Airline.
Wacece xee Zainab diya ce ga baba shehu (kanin hajiya
hadiza)…..mamanta ta rasu tun tana karama, shiyasa ita
da baba shehu suka dawo Mansion din alhaji tanimu da
zama….zee irin yammatan nan ne mara sa kamun kai da
aji duk girman mutum haka zata kalle shi ta shuka mai
rashin M,”ga ubanta da shegen son abun duniya burin
shi kawai alhaji ya mutu suci gado.. Babu wanda take so
a duniya kaman yazid Ambrusa, asalima ita ta makale
mai harya fara bata attention…..babu wanda bai sansu
tare ba, burinta kawai ta aureshi yaxama nata. *cigaban
labarin* Kursum da takaici ya isheta haka taja jikinta ta
dawo hostel tayi kwanciyan ta, gaba daya duniyan tai
mata zafi wato akan saurayi shine sumy zata ci mata
mutunci hmmmm……amma fa guy din ya hadu ba
karya, fuskan shi kawai take gani, wani irin nishadi take
shi, “taja tsaki Allah ya rabani da irin shi dagani ma dan
iska ne, tunda naga alama suna biyu gareshi. Turowan
kofan dakin ne ya dawo da ita daga tunanin da take,
sumy ce ta shigo ko kallon gefen kursum batai ba……
haka dai suka kwana suka tashi babu wanda ya cewa
wani uffan. Gimbiya hafsatu taga kudi sai washe baki
take, tace indai sumy ce nabawa danka halak malak,
kawu jamilu (wanda yazid yayi hayan sa ya bashi
makudan kudi yaxo amatsayin kawun sa ya naima mai
auren sumy) sai zuba godiya yake kaman dagaske, yace
yaron nawa fa yafiso adaura auran nan da kwana
biyu……gimbiya hafsatu tace ai angama, ya mika mata
dubu ashirin amatsayin sadaki ta amsa tana Dariya.
Hmmmmm *Xarah Bêê* *Dedicated to Bady social*
~Luv u all~ kursum 21 to 35 Posted by XARAH
ABUBAKAR on NOVEMBER 13, 2016 KURSUM By ~Xarah
Bukar Page ~ Haba sumy yanzu da bakinki kika aminci
da auran stranger din da baki ma san halinsa ba, ko aure
baki sani ba balle iya zama da miji asalima ma ko
dadewa bakuyi da haduwa ba…… Dan Allah kursum ki
kwantar da hankalinki kema kinsan banda wani option
daya wuce in aure shi tunda har muna son junan mu,
kuma nidai akan in koma gurin momy da zama na
gwamma ce in auri stranger dinnan cause hankalina yafi
kwanciya dashi I don’t want to lose wannan opportunity
din dana samu, kursum tace to mai zaki cewa daddy
kinsan nan da wata biyu zaizo ganinki, tace dad ba
matsala bane, na tabbata sai yafi kowa murna da auran
nan. Kursum tace toh Allah yasa hakan yafi alkhairi, duk
jikinta yayi sanyi ranta abace ta rasa dalili,:|:|:| tana
ganin dan zata rabu da aminiyar ne shine yasa ta jin
hakan. **************************** A yau ne
aka shaida daurin auran yazid (habib) da sumy, babu
wani event da akayi illa abinci da gimbaya hafsatu ta
bada a dafa, anci an koshi jama’a sun watse kafin dare
kuma akai amarya Ango kam sai washe baki yake,
:mrgreen::mrgreen::mrgreen: babu wani aboki ko
dan’uwa dayasan da batun auran face kawu jamilu daya
tsaya mai akai komai cikin kwanciya hankali… Ko huzaifa
abokinshi bai san abunda. Ke faruwa ba, dan yasan idan
ya gayamai plans dinshi xai ruguje kenan, asalima yamai
karyan ya koma kano. Amarya sumy sai shiri take tana
hada kayanta cikin akwati, farin ciki fal fuskan ta, lokaci
kawai take jira akaita gurin heart beat dinta. Ta kalli
kursum data takure karshen gado, daka ganta kasan tana
cikin tashin hankali….tace haba sis muna nan tare fa
bawai guduwa xanyi in bar kiba, kursum tace dole
hankalina ya tashi bani da kowa sai ke sumy, idan kin tafi
maraicina zai dawo sabo ta fashe da kuka mai tsuma
zuciya, sumy ma tana kuka tazo ta rugumeta tana kara
bata baki akan tayi hakuri suna nan tare, mutuwa ce
kadai xata iya raba su. Da daddare kawu jamilu da
kanshi yazo dauka amarya, gimbiya hafsatu da kursum
kadai suka mata rakiya har gidan mijinta, Gida ne dan
karami, mai dauke da room & parlour sai kitchen daga
gefe sai dan karamin tsakar gida, cikin dakin kuwa babu
wani abun kirki aciki sai kafifa kawai da stool na zama,
dama baa jera mata komai ba tana jiran idan daddy ya
zo sai ya siya mata komai da komai. Gimbiya hafsatu da
kursum sun mata nasiha sosai, sanna suka mata saida
safe suka wuce abunsu. Kamshin turaren sane yasa
tagane yashigo dakin, yaxo ya xauna kusa da ita ya jawo
hannuta ya sumbata yana kare mata kallo, yarinyar so
innocent………. Sakonnin soyayya ya aika mata a
darenan da kyau,masu rikitarwa, har ya samu biyan
bukatan shi, saida yaji kukanta na yawa sanan ya dan
saurara mata…… Koda ta farka da safe baya cikin dakin,
dakyar ta tashi ta shiga toilet ta tsarkake kanta tayi
wanka ta fito tayi sallah harta koma bacci, sai wajen
10am ta tashi, tayi mamanki still baya na,ta tashi ta leka
ko ina a gidan amma bayanan kuma babu alamunsa……
Ta koma daki dan duba kayan sa, nan ma wayam tagani
sai wata wasika daya ajiye mata kamar haka Matata mai
sona, Allah yayi miki albarka kin biyani ni
arayuwa…….amma dan Allah ina naiman gafararki da ki
yafemin dan bawai na aureki dan ina sonki bane face
sha’awarki danayi, kuma ni bazan iya zina ba shiyasa na
aureki, amma kiyi hakuri sumy, na sakeki saki biyu
sannan ga kudade masu yawa nabar miki ki kula da
kanki, karma kice xaki naime ni dan kuwa baxa ki taba
ganina ba. Sannan kina iya zama acikin gidan na wata
daya kafin kudin hayan ya kare…………..ina miki fatan
alheri. Bissalam Innalillahi wa inna’ilaihi rajun kawai take
fadi, ta fadi kasa tana rusa uban kuka shi kenan taga ta
kanta kursum ce ta shigo gidan da abincin karin su, ba
karamin girgiza tayi ba da taga kawarta cikin yanayin nan
tace miya faru? Kukan mai kike yi? baki da lafiya ne, a
gigice take jero mata tambayo yi……… sumy kam kasa
cewa komai tayi, ta mika mata wasikar daya ajiye mata,
kursum ta girgiza matuka data karanta kasa cewa komai
tayi, itama ta zauna sai kukan suke babu mai rarrashin
wani. kaico Daga bisani suka tashi suka dau kayan sumy
da makudan kudin daya bari suka bar gidan….. Yazid
kuwa tunda ya tashi yawuce Airport yana sauri baya son
missing flight dinshi na 7am, Allah yasa yana xuwa dama
shi kawai ake jira, jirgi ya daka sai kanon dabo…….
Umma ce da kanta taje dauko shi a airport, dan kawai
yasan ta damu dashi, suna cikin mota umma tace, son
wato ka gujemu ko, wajan wata daya kenan bansa ka a
ido ba idan nakira wayan ka saika ga daman dauka……
Yace to umma ya kikeso inyi, keda kika fi bawa aikin ki
(fashion designer ce) mahimmanci, ko a gida baki da
lokacin kowa saina aikin ki, ki wuni kina aiki a office
kuma ki dawo gida kinayi, har Abba ma yafiki samun
lokaci na, “tace my son kamin uzuri dan Allah, aikin
nawa ne dole saida attention sosai in ba haka ba komai
bazai yi daidai ba, ni kaina inason kasance wa da family
dina shiyasa ma nakeson daukan hutu kona wata biyu
ne……yace toh shikenan umma duk yadda kikai yayi
daidai, shidai arayuwan shi yanason ummansa bai
hadata da komai. Koda gimbiya hafsatu ta karanta
wasikar sumy, sai cewa tayi karta damu dama maza basu
da tabbas, itama tayi mamaki yadda yayi ta zubar da
kudi kaman bai san ciwon suba, indai aure takeso zata
iya naima mata wani ta aura kodan ta huce haushi.
Kursum tace haba gimbiya kamata ace kin naimo mijin
nata ayi magana,tunda da hadin bakinki akayi auren nan
kuma ai kinsan kawunsa, gimbiya tace tab aini yanxu ko
nayi trying number kawun bai shiga kashe wayar take
kuma yarinyan ita da kanta ta nuna shi take so kuma
xata aure shi, toh miye laifina aciki…….ki fice min yanxu
nan marar kunya, wato kece da bakin magana ita da aka
saka bata zoba sai ke, wawiyar banza. Kursum ta fice
ranta abace,bata taba ganin zalamar miyar mata irin
gimbiya ba, ita dai kanta kawai tasani…… Ta koma
dakinsu, har lokacin sumy kuka take duk ta rame ta fita
hayyacinta lokaci daya, kursum tace mata dan Allah ki
bar kukan nan haka, indai ina raye a duniya toh saina
naimo shi na daukar miki fansar abunda ya miki, koda
kuwa zaiyi causing life dina, dat is a promise, sau daya
nataba ganinshi amma bazan taba mantawa da face
dinshi ba…… Tana taba sumy baki hardai ta hakura ta
barwa Allah komai.. *Bayan wata biyu* Sumy sai rashin
lafiya take ga zazzabi da weakness da take ji ga yawan
amai , shiyasa gimbiya ta kaita asibiti, doctor ya mata
gwaje gwaje ya gano tana dauke da cikin wata
biyu…….aka sallamo su suka dawo. Gimbiya ta kirawo
kursum ta gayamata sumy na dauke da cikin wata biyu,
sai data girgiza da jin wannan xancen, yanxu ya sumy
zatayi idan tasan tana dauke da cikin wanda yama manta
da zamanta, gimbiya tace ga test result din saiki bata ki
kara kwantar mata da hankali, kinsan mai karamin ciki
batason tashin hankali gudun kar ciki ya zube. Ta karba
sum – sum ta fice, tasamu sumy na karatun al-qur’ani,
sai da tajira ta idar sannan ta mika mata test result din,
sumy ta karba ta duba saida gabanta ya fadi tace wake
dauke da ciki ? Kece kowa? Kursum tace kinsan dan
Adam ajizine, duk yadda ubangiji ya tsara aka ke faruwa
babu wanda ya isa yaja da ikon Allah, komai na duniyan
nan jarabawa ce, Dan Allah kiyi hakuri ki yarda da
kaddaran da Allah ya daura miki, sumy tace meke
faruwa ne ? kinsani a duhu fah. Ciki gareki na wata biyu
sumy, kece keda cikin ba kowa ba, hawaye kawai sumy
take tana addu’an Allah yasa hakan yafi alheri agareta,
kursum tace amin. Daddy ne ke tuki hankali kwance,
yana murnan yau zai ga diyar shi tilo a duniya, wajen
shekara guda rabon daya ganta.. Ya iso makaranta, har
visitors lodge (inda iyaye ke zama idan sunzo ganin
ya’yan su) aka kaishi, aka tura kiran sumy tazo dad dinta
yaxo…..ita da kursum suka je wajen daddy suka gaishe
shi, gaban dad sai da yafadi ganin yadda sumy ta rame
sai haske data kara sosai, yace kursum, sumy bata da
lafiya ne? Kursum tayi shiru ita dai tarasa dalilin daya sa
idan tana gaban baban sumy take jin wani iri, kaman
akwai wani connection tsakanin ta dashi………kukan
sumy ne yadawo da ita daga tunanin da take, tana kuka
tana ba daddy labarin abunda ya faru tun daga auran ta
har izuwa yanxu da take dauke da ciki, daddy kasa
magana yayi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment