Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jawo mana tashin hankali sosai adanginmu don Allah kayi hakuri kamaida ita dakinta batare da iyayenmu sunji ba dan tunda ta taho a gidana tasauka gudun bacin zumunci".



"hmm Fatima kenan,yanzu duk laifin da Khairat ta aykata min kikeso namanta naci gaba da zama da ita to wlh dasake inda kin tilastani yin abinda bansoba to yanzu ni ba yaro bane dazaki tilastani,ko wancan lokacin ma yarintace tasa naamince, dan haka inzaki iya sa ido kiyi kallo kisa kicire kanki acikin wannan maganar",yana gama fadamata haka ya kashe wayar gaba daya.



Hankalin Fatima tashi yayi dajin kalam Hydar hakan na nufin dole se zancan yakai ga iyayensu kenan.



Yasmeen kwananta biyu da dawowa gida Amman bataga Khairat da yarantaba, koda ta tambayi Hydar cemata yayi taje Kaduna ne,be sanar da ita komai,fatan Allah yadawo dasu lafiya tayi.

Yasmeen ce zaune gaban computer tana latse latsenta,a dakin Hydar,kamar ance taba kawai seta shiga inda mutum zega abinda ke faruwa a gidan wato CT camera old videos tashiga.



Hydar tagani yana dukan Khairat,har zuwa lokacin dayace yasaketa,har batun zubewar cikinta duk seda taji.



Tashin hankali baa samishi Rana.



Ita bata cikin takeyiba sakin da akayiwa Khairat a dalilinta shi yafi daga mata hankali,da sauri taciro wayarta takira Fatima tana bata labari gami da tambayar ina Khairat din take.



Kwashe duk abinda yafaru Fatima tayi tabata labari har yadda sukayi da Hydar,Yasmeen bataji dadin abunba sam,kamin suyi sallama seda Fatima ta roki Yasmeen akan ta roki Hydar yadawo da Khairat dakinta.



Hydar yana dawowa daga gurin ayki yaga Yasmeen atsaye tana kallonshi babu alamar walwala a fuskarta, karasawa yayi inda take ze rukota da sauri ta bige mishi hannu sannan tasa mishi kuka tana fadin.



"wanne kalan suna kakeso duniya takirani dashi,sokake zumuncin gidanmu ya rushe a tsakanin iyayenmu,mene naka na sakin Khairat dan munyi fada,kana tunanin wai dan na aureka bana son tane,cikina da ya zube daga Allah ne ba ruwan Khairat wacce nayi imani da tasan inada ciki bazata dakeniba,".tacigaba da kukanta.



Hydar ya rasa abinyi wato yanzu Yasmeen tasan abinda yafaru kenan waya fada mata,rasa amsane yasa yawuce dakinshi, da shigarshi dakin ya fahimci inda Yasmeen taji zancan ta hanyar ganin computer dinshi a bude.

Dakinta ya nufa domin ya rarrasheta, Duk magiyar dayake mata taki sauraronshi karshema cewa tayi itama Kaduna zata tafi.

Hydar yaga daru gurin Yasmeen dan bata kyaleshi ba har seda ya furta yamaida Khairat Amman darajarta taci.

.Waya tasashi yayiwa Fatima dan ta sanar da Khairat Hydar yamaida auransu ba musu yakira Fatima ya sanar mata.



Wani dadine yakama Fatima da Khairat dan har kuka sukayi name farinciki.

Fatimace ta maida Khairat gidanta sannan tamusu waazi sosai akan illar tarwatsa zumunci suyi hakuri su zauna Lafiya.

Bata kwanaba a ranar ta koma kaduna ranta da zuciyarta sunyimata sanyi.

Yasmeen har kasa ta tsugunna tanemi gafarar Khairat,cikin kuka itama Khairat ta tsuguna tana neman Yasmeen ta gafarta mata abinda taimata, dukansu kuka sukeyi suka rungume juna.

Hydar yaji dadin ganinsu a haka zuwa yayi ya rungumesu duka yana sa musu albarka da fatan zaman lafiya a tsakaninsu.



Bayan wata goma.



Yasmeen naga Hydar ya dauko da tsohon ciki tana kuka Khairat na binshi da wani akwati suka shiga mota basu zame ko ina ba se asibiti,ananne naji ashe nakuda take.



Labor room aka shigar da ita abin gwanin tausayi bata jimaba ta haihu tasamu yan biyu duka maza kamarsu daya da Hydar.



Murna da farincikin dasukayi baya misaltuwa barinma Khairat har kuka tayi na farin ciki.



Ranar suna yara suka amsa sunan Abban Khairat da Abban Yasmeen.suna kiransu da Fadeel da Nabeel. Fadin bidirin da akayi baze yiwuba Amman fa taro yakai taro.

Khairat da Yasmeen yanzu ba wani fada a tsakaninsu dan yanzu Khairat tagama gane albarkacin Yasmeen taci Hydar yadawo da ita,Yasmeen tana mutunta Khairat sosai itama haka.



Taron family Hydar ya kaisu Kaduna ananne Hydar yabada labarin abinda yafaru tsakaninshi da Khairat da kuma tsakanin Khairat da Yasmeen, fada dekam sun shashi bana wasaba daga karshe fatan zaman lafiya akayimusu taro yawatse kowa yatafi.



Yasmeen ta koma makaranta inda take karanta bangaran likitanci,Iman tayi aure itama inda ta auri wani dan majalisa itama abin gwanin Shaawa.



Bayan shekara ashirin da biyar.

Abubuwa sun faru da yawa a tsawon wannan lokaci aciki harda rasuwar Granny da Abban Khairat, da iyayen Hydar gaba daya sunyi jimami daga baya suka fauwallawa Allah.



Taron jamaa na hango a cikin masallacin sultan Bello dake anguwar sarki Kaduna,ko baa fadamaba taron na daurin aurene,kunne nasa dan inji auran wa akeyi ayko najidin domin ji nayi ana fadin.

An daura auran *Hydar Kamal mukhtar, Da Amaryarsa Fatima Hydar Jibreen,*ikon Allah Ashe da rabon Hydar da Fatima suyi aure.

[5/12, 22:25] Zahra Surbajo: 📓📓📓📓📓📓📓📓

*CIN AMANA KO FANSA*

📓📓📓📓📓📓📓📓



Zahra Muhammad mahmud



*Dedicated to all wainda bansamu damar yimusuba,kuyimin uzuri next time daku zanfara ngd*





*last page*.



*page 81-82*





Zumuncinsu se kara karfi yakeyi ta kowacce siga.



Yasmeen yanzu yaranta biyar hudu maza mace daya me sunan Khairat,itama Khairat ta haifi yara uku mata aciki da mesunan Yasmeen suna kiranta princess.



So da kauna tsakanin Yasmeen da Hydar sede hamdala har zuwa yanzu bashida wani farinciki se nata,kuma yana yin adalci atsakaninsu dan koda wasa baya bari yafifita wata a gaban wata, duka daya take daukarsu.



Arzikinshi se karuwa yakeyi ba dan kadanba, haka shima kamal mijin Fatima yasamu babban matsayi a gurin aykinsu dan haka tuni ya tamfatsa gini a garin Abuja yamaida Fatima can.

Yasmeen da Hydar one love with Khairat.





*Alhamdulillahi ala kulli hali.*



*Godiya ga Allah Subuhanahu wata ala,daya nunamin wannan rana dana gama littafin cin Amana ko fansa.*



*Tsokaci!!!!*



*Littafin cin amana ko fansa true life story ne dole a yadda yazo zan tafi dashi.*



*Yana jan kunne ga mata masu raayin snatching ga aminansu.*



*Kuji tsaron Allah kudena dan ba dabia bace me kyau.*



*yana koyar da mata masu kishiyoyi yadda zaki yi kissa ki kwaci miji batare da kinbi boka ko Malam ba.*



*Sannan yana fatan makaranta dasuka karanta suyi koyi da kyakkyawar zuciya irin ta Fatima dason zumuncin Allah.*



*Mahaukacin kishi ba inda zekaiki dana sanice karshenki, kikama kissa kidena shashanci dan mahaukacin kishi shashancine.*



*Don Allah duk Wanda na batawa rai yagafarceni,nima nayafemuku,ina mana fatan Allah yasa muga Ramadan lafiya yasadamu da daran lailatun qadri,Yasa muna cikin jerin bayin da zaa y'anta,Ameen,nagode taku har kullum.*



*Zahra Muhammad mahmud (SURBAJO)*



Maman Yusuf 🙏


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment