Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hydar ya nufoshine yasa ya tsaya fuskarsa d'auke da fara'a.



Hydar tsugunawa yayi har k'asa yagaisheshi,yana d'aya daga cikin halayansa dayake sawa surukannasa ke sonsa shine girmamasu dayakeyi batare da yayi la'akari da matsayinsaba,ruwan alwala Abban yasa aka kawomishi yayi alwalar suka nufi masallacin tare.



Bayan an idar da sallah kai tsaye cikin gidansa yaja Hydar d'in suka gaisa da Umman Khairat, daganan sit room suka koma suka zauna aka kawo musu abinci Abban tilastawa Hydar yayi suka ci tare, duk kunyar Abban ta gama kama Hydar bayan sungamane Hydar yace yanada maganar data kawoshi,murmushi Abban yayi yace.



"To Hydar ina sauraronka".



Rasa Ta inda ze fara yayi gaba d'aya Abban yamasa kwarjini,amman bashida zab'i dole ya furta,cikin rawar murya yafara maganar.



"Abba don Allah ku fahimceni wlh k'addarace ta hau kaina bana nufin kawo tarnaki acikin familynku banida yadda zanyine don Allah kugafarceni".



Mamakine yakama Abban to me Hydar yamusu da yake neman gafarar su haka.



"Hydar ka natsu ka sanar dani abinda yake faruwa, ni mahaifinkane zanmaka duk abinda uba yake wa d'ansa, meyasa kake shayin sanar dani damuwarka?ni na maka alk'awari kowacce irice insha Allahu zanyi k'ok'arin taimakamaka, Danhaka kasanar dani ina sauraronka"Abba yayi maganar cikin yanayin k'arfafa guiwa agareshi.



"Abba Yasmeen nakeso ka auramin idan har da gaske kai ubane agurina, inaso kayimin ranar da uba yakewa d'ansa yayinda d'an yashiga tashin hankali"ya k'arasa maganar yana kuka tamkar anmasa mutuwa.



Tashin hankali ba'a samaka rana.

Abba jiyayi kansa na shawagi a sararin samaniya gaba d'aya kalma ta gudu daga bakinsa gumi se karyo masa yakeyi.



Hydar zuwa yayi yakama k'afarsa yana kuka yake fad'in.



"Abba naso hak'ura tun kan kuji maganar amman nakasa, wlh Abba inbaka auramin Yasmeen ba zan iya rasa raina, don Allah katausayamin kuma wlh bazan wulak'anta muku y'ay'aba".



Dakyar Abba yasamu abin cewa.



"Hydar ka kwantar da hankalinka bana tunanin zaka wulak'antasu,kawai zumuncinsu ake dubawa,amman ba komai gobe dama munada family meeting,zamu tattauna maganar a gurin kaje ka kwantar da hankalinka Hydar kanada uba tsayayye,idan har inada iko akan Yasmeen inkuma Allah yayi matarkace koda duka dangi basu yardaba ni zan auramaka ita,kuma inda Hali inaso taron dazamuyi gobe da azahar yazamana Khairat da Yasmeen su halarta".



"Insha Allahu zasu halarta Abba nagode Allah yasaka da alkha'iri Allah yak'ara girma",godiya Hydar yakeyi kamar zeyi sujada.



Abba k'arfafa masa guiwa yayi sosai gamida alk'awari.



Hydar gidan su Yasmeen yashiga suka gaisa da iyayanta sannan yamusu sallama ya wuce gidan iyayensa.



Maman Yusuf.

[5/4, 08:38] Zahra Surbajo: πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

*CIN AMANA KO FANSA*

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““





Zahra Muhammad mahmud



*People Live, People Die. People Laugh, People Cry. Some Give Up and Some Will Try. Some Say Hi and Some Say Bye!. Others May Forget You! But Never Will i,Hassana Amadou.*





*page 53-54*





Hydar yana isa gidan iyayensa yakwashe yadda sukayi da Abban yafad'awa mahaifinsa,fatan alkhairi yamasa sannan yak'ara da cewa yaci gaba da addu'a Allah yatabbatar da alkha'iri.



Part d'inshi yawuce a falo yazauna yakira Khairat a waya,bugu d'aya ta d'auka tace.



"Sanyin idaniyata yanzu nake zancan ka araina ashe kana kusane shiyasa".



"Kai ammafa naji dad'in hakan,to ya kuke I hope komai normal?".



"Lafiyarmu k'alau sede kewarka da take damunmu".



"Sorry zamu kasance tare har abada,dama ashe kunada family meeting gobe amman shine baki sanar daniba,?se d'azu da muka gaisa da Abba yake sanar dani,kuma yanemi alfarmar keda Yasmeen ku halarci taron a goben,so dan haka na turo driver yadawo tun d'azu seku shirya da wuri gobe kutaho da sassafe kinjiko? keda Yasmeen zakuzo Iman kubarta dasu meema tunda akwai masu gadi".



Dad'ine yakashe Khairat yau gashi akaron bati zata kaduna cike da murna tace.



"Ayya kayi hak'uri ban sanar dakai bane sabida nasan ba lalle ne kabarmu mujeba, amman kayi hak'uri kuma insha Allahu gobe zamu iso akan Kari".



Sallama sukayi zuciyarshi cike da tausayinta da'ace ze iya hak'ura da Yasmeen dayayi kodan farincikin Khairat to baze iyabane amman harga Allah yana tausayinta.



Washe gari da sassafe suka shirya dan Yasmeen Khairat nasanar da ita zancan Hydar murmushi kawai tayi,dan tasan bomb ne ke shirin tashi da d'aya daga cikinsu.



Kayanta data had'a su tayi saurin kaiwa boot batare da Khairat taganiba driver yasaka mata sannan takoma ta d'auko na Khairat d'in shima akasa.



Har mota Iman tarakosu suka shiga driver yajasu zuwa kaduna.



Sun iso kaduna lokacin danginsu sungama taruwa kwansu da kwarkwatarsu, kowa se murnar ganinsu akeyi nan aka shiga hirar yaushe gamo kamin a zauna taron.



Ita ko Yasmeen gidan su Khairat takai jakarta d'akin Maman Khairat d'in ta b'oye,basu jima da zuwa ba su Abba suka kirasu aka had'u a tsakar gidan su Khairat dan yafi fad'i.



Bayan bud'e taro da addu'a se gaishe gaishe dasuka biyo baya, daganan kowa yashiga kawo matsalarsa ana warware masa,wa'inda sukayi fad'a da junansu aka shiryasu, kowa fuskarsa inbanda annuri ba abinda take fitarwa,Abban Khairat ne yace a saurara yanada magana me muhimmanci.



Gabad'aya natsuwa sukayi suna sauraron abinda zece,gyaran murya yayi sannan yafara da cewa.



"Munada wata magana me matuk'ar muhimmanci dazamu tattauna akanta, wacce kowa cikinku nakeso yamata duba na tsanaki dan inba hakanba abin ze haifar da gaba me tsanani acikinmu, dan haka kowa yabani hankalinsa" .



K'ara natsuwa sukayi sosai suna sauraronsa.



"Ba wata magana bace illah Hydar mijin Khairat yana son yak'ara aure, kuma bakowa yakesoba illah Yasmeen k'anwarta".



A gigice Khairat ta mik'e tsaye jikinta inbanda rawa ba abinda yake da kyar tace.



"K'aryane wlh,wannan zancan k'aryane, taya Yasmeen zata iya auran mijina wannan hirace".



Tsawa Abba yadakamata yace takoma tazauna, yayinda gaba d'aya falon yakaure da hayaniya kowa nafad'in albarkacin bakinshi.



Seda kowa yayi shuru sannan ya d'ora da cewa.



"Jiya Hydar yazo har gida yasanar dani buk'atarsa nason Auran Yasmeen,wanda kunsani nasani wannan al-amari ba haramun bane shiyasa nace yabari zamu shawarta akan zancan".



Abban Yasmeen ne yamik'e ranshi ab'ace ya damk'o Yasmeen d'in yafara duka,da kyar aka kwaceta a hannunshi cikin fushi ya fara magana.



"Kaiconki Yasmeen wlh kinyi asara,mijin y'ar uwarki zaki aura to wlh matuk'ar nina haifeki baki isa kisani jin kunyaba".



"Kai har Kana da iko da Yasmeen sama dani? da zakace in kaine mahaifinta? to inso Kake ka tabbatarmin da yanzu ka haihu bisimillah Nasiru nunamin iyakata".Abban Khairat yafad'i cikin tsananin b'acin rai dan maganar Abban Yasmeen d'in ta b'atamasa rai.





Kubiyoni taku har kullum.





Maman Yusuf.

[5/4, 10:02] Zahra Surbajo: πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

*CIN AMANA KO FANSA*

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““





Zahra Muhammad mahmud





*Earth may stop rotating, Birds may stop flying, Candles may stop melting, Fishes may stop swimming, Heart may stop breathing,But i will never stop Missing you my friend.ESHAT MUSTAPHA insha Allahu your forever start now between you and your Husband,Happy marriage life*





*page 55-56*





Hak'uri Abban Yasmeen ya durk'usa yana ba yayannasa,sauran family ma suka sa baki sannan ya hak'ura aka ci gaba.



Yasmeen se kuka takeyi sabida ta daku a zuciyarta ko fad'i take,"wlh ko kasheni za'ayi sena aureshi".



Khairat gaba d'aya komawa tayi kamar wata mahaukaciya se zare ido kawai take tana soshe soshe, abin gwanin ban tausayi, duk da bata gama yarda da abinda ake fad'inba.



Abba ne yaci gaba da magana.



"Yasmeen inaso kitashi kiyimana bayani kinason Hydar ko bakya sonshi? domin shi ya tabbatarmin inbake baze iya rayuwaba shin ko kema hakan take a gurinki?".



Mik'ewa Yasmeen tayi without fear tace.



"Tabbas Abba inason Hydar kuma nima a shirye nake narasa rayuwata matuk'ar ban sameshi a matsayin mijinaba".



Wani kukan kura Khairat tayi ta shak'e Yasmeen kamar wata me aljanu idonta sunfito waje sosai bakinta har kumfa yake tace.



"K'arya kike Yasmeen wlh baki isa kihau shimfid'ata ba,bakiji kunyataba kike furta kinason mijina agabana da kuma iyayanmu?menayimiki haka dakika rasa me zaki sakamin dashi se cin amanata? me nayi miki?Yasmeen me nayimiki?".kuka take sosai tana jijjiga Yasmeen d'in, itako Yasmeen ko ajikinta illah ma kwace jikinta a hannunta datayi sannan tace.



"Ina kiranki da babbar murya dakiyi gaggawar cire kalmarki tacewa naci amanarki,ni banci amanarkiba hasalima abinda nayi ay bakaina farauba,nide abu d'aya nasani shine ni bazan hana zuciyata abinda takesoba akan farincikin wani,kamar yadda Aunty Fatima tayi a k'arshe ta b'ige da ciwon zuciya, niba haka nakeba Hydar mijinki yayimin kuma inasonshi".



jikake tass Fatima ta d'auke Yasmeen da mari tasake k'ara mata cikin kuka ta fara magana.



"How dare you Yasmeen?i said how dare you?!!,karki k'ara jingina wannan maganar da abunda yariga ya wuce,inma Danni zakiyi ni najima da yafewa,ke bama hakaba waye ya baki labarinnan da kike rik'e dashi tsawon wannan lokacin? Tell me who told you our secret"Fatima rik'e take da Yasmeen tana hawayen tausayin Khairat.





Yanke jiki Khairat tayi ta fad'i k'asa sumammiya,dagudu akayo kanta ana mata fifita kan kace me gida yakaure da hayaniya masu kuka nayi, dan basu tab'a fuskantar tashin hankali irin wannan ba, ruwa aka yayyafawa Khairat ta farfad'o ay kamar jira Yasmeen take ta farfad'on tace.



"Wlh Aunty Khairat ba suma ba ko mutuwa zakiyi sena auri mijinki,tunda kema baki tausayawa Aunty Fatima ba kika iya rabata dashi bayan kinsan shine buri da fatanta kamar yadda shima Yaya Hydar d'in Aunty Fatiman ce burin ransa kika rabasu, a sanadin hakan har ciwon zuciya ta kamu dashi kamar zata mutu Amman baki tausaya mata ba, to wlh nima kam banajin zan tausayamiki matuk'ar Yaya Hydar yana Raye kuma nima ina raye sena Aureshi dan tun shekaru bakwai dasuka wuce nake da burin karantar dake illar *cin amana*shiyasa natashi da burin *fansa*banajin akwai wani yanayi dazaki shiga dazesa na janye k'udirina,dan haka ki shirya zama dani a matsayin kishiyarki nanda wasu kwanaki".



Faskaren itace Umman Yasmeen ta d'auko ta jefeta dashi Allah yasota ta kauce,mik'ewa tayi zata bita Umman Khairat ta dakamata tsawa da cewa.



"Ya isheki haka nace,wlh kika sake kika kuma dukanta wlh sena shayar dake mamaki, meye naku na ganin laifinta bayan ga babbar algungumar can da yadace ku daka,ay dama Khairat na fad'amiki akwai ranar k'in dillanci kuma gata Allah yakawomu,wlh inde inada iko akan Yasmeen seta auri Hydar koda kuwa babu wanda ya amince acikinku".



Gaba d'aya kansune ya kulle sunrasa gane inda maganganunsu suka dosa, kamar hakan na nufin akwai sa hannun Khairat game da ciwon zuciyar Fatima kenan.



Abban Khairat ne yadakawa kowa tsawa suka natsu sannan yakai dubansa kan Fatima yace.



"Fatima ki dubi girman Allah ni mahaifinkine kidaure kisanar dani dalilin kamuwarki da ciwon zuciya kiji tsaron Allah ki sanar dani gaskiya".



Cikin kuka Fatima tafara magana dan bata da ikon b'oye mishi tunda ya d'aureta da jiniyoyin jikinta dan Allah ba abin wasa bane.



"Tabbas Abba Hydar ni yake so kuma nima haka, akwai soyayya da shak'uwa me tsanani tsakaninmu har zuwa ranar daka kiramu akan mu fitar da mijin aure,se jinayi Khairat tace ita Hydar yakeso hankalina yatashi shine ma abinda ya hanani magana har muka baro gurinka, bayan mundawo d'aki ne tasameni tacemin yazama dole nabarmata Hydar sabida a matsayinta na kyakkyawa da ita yadace baniba, sabida ikrarinta nacewa ita matar manyace, tajamin kunne akan idan har ban barmata shiba zata kashe kanta kokuma taje tayo cikin shege tace shi yayi mata, Ta yadda dukanmu zamu rasa tunda tasan inde tayi hakan bazaku yarda ku Aura minshiba, haka dole nabar mata shi badan banasoba sedan samamata farinciki"ta k'arasa zancan cikin matsanancin kuka.



Umman Khairat ce ta amshi zancan.



"Kuma nima shaidace dan Fatima ce Ta matsawa Hydar har ya yarda ya auri Khairat dande kawai ya faranta ran fatiman"daganan ta kwashe duk abinda tasani ta shaida musu.



"Kuma kamin na amince da auran Khairat seda mukayi yarjejeniya da Fatima akan duk sanda nasamu zab'ina ko a inane zan aureta, kuma ita kanta Khairat d'in tasan da zancan kuma tayi na'am da hakan,sede ta amincene aganinta da zaran munyi aure zata d'auki hankalina"inji Hydar wanda ke k'ok'arin k'arasa shigowa cikin tsakar gidan, dan tunda aka fara cece kucen Yasmeen tayimishi text a b'oye akan yazo kar akasheta a banza shiyasa yazo yanzu.



Dukansu sunyi mamakin ganinsa har yasamu guri kusa da kamal ya zauna basu dena kallonshiba.



muje zuwa.



Maman Yusuf.

[5/4, 16:52] Zahra Surbajo: πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

*CIN AMANA KO FANSA*

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““



Zahra Muhammad mahmud



*Long, long afterward, in an Lake I found the arrow, still unbroke,And the song, from beginning to end,I found again in the heart of a friend."The rain may be falling hard outside,But your smile makes it all alright.I"m so glad that you"re my friend.I know our friendship will never end."Hafsat Dahir*



*page 57-58*



Kowa hankali atashe suke kallon Hydar.



Abban Khairat ne yasoma magana cikin fushi wanda basu tab'a zaton yana dashiba.



"Khairat kinyi asara wlh duniya da lahira yanzu duk yadda kuke da Fatima seda kika ci amanarta, to ke wacece da baza'a d'au fansa akankiba wlh kinyi kad'an kece silar komai kinso zumunci yab'aci to da yardar Allah zumuncinmu daga Allah yake ku baku isa ku tarwatsamana shiba".

Zasuyi magana yadakatar dasu da cewa.



"Bana buk'atar jin komai daga gurinku, Hydar inaso kamik'e ka shaidawa kowa abinda ke ranka buri da kuma fatanka".



Mik'ewa Hydar yayi cike da kwarin guiwa Khairat binshi kawai take da ido kamar mujiya fatanta Allah yasa yafasa Auran Yasmeen.

"Salamu Alaikum jama'a ni Hydar inason Yasmeen da aure kuma banida wani buri daya wuce inga faruwar hakan shine fatana zanrik'esu duka bisa gaskiya da rik'on amana inde har kun amince kun bani".



Gaba d'aya gurin kaurewa yayi da hayaniya wasu nacewa Sun yarda wasu nacewa basu yarda ba.



Abban Khairat ne ya tsawatar musu ta hanyar cewa.

"Ba shawararku muke soba abu d'aya nasani ko duka duniya gatan Khairat ne sena aurawa Hydar Yasmeen yanzu batare da bata lokaciba, ko kunaso ko bakwaso tunda nidasu munaso ya wadatar"yana gama fad'in haka yasa hannunshi a aljihu yaciro bunch d'in d'ari biyar dubu hamsin kenan ya d'aga sama yace.



"Ni Alhaji Mukhtar Abubakar uba ga Hydar ina nemarwa d'ana Hydar auran y'arku Yasmeen abisa sadaki naira dubu hamsin,idan kun amince waliyyin Yasmeen yafito ya bani auranta".

Ihu Khairat tasa ta je ta kama k'afar Abban nata tana kuka tana fad'in.



"Abba karka tarwatsa farincikina wlh bazan iya kishi da Yasmeen ba tafini komai, Abba kishi da ita azaba kawai zansha mace irin Yasmeen aka had'ata da kishiya wlh seta kashe kishiyar da bak'in ciki don Allah karka yimin haka natuba kagafarceni don Allah".wani kyakkawan mari Abba yasakarmata wanda yatilastamata ganin wucewar wutar nefa a waya, agigice tasaki k'afarshi takama ta Abban Yasmeen tana rok'onshi,rasa yazeyi da ita yayi kawai rungumeta yayi yana rarrashinta dan zuciyarshi tafi tata k'una kawai de anfi k'arfinsane.



Abban Khairat ne yasake nanata buk'atarsa tanemawa Hydar auran Yasmeen inda yabuk'aci waliyyin Yasmeen ya fito Amman gaba d'ayansu ba wanda ya motsa hakanne yasa yace.



"Hydar da Yasmeen kuzo muje masallaci a d'aura muku aure nan banida wata darajar daza tasa su bani auran kutaso muje" ya mik'e yana shirin ficewa.

Da gudu Abban Yasmeen yaje ya kama k'afarsa yana fad'in.

"Yaya don Allah karka tonamana asiri kayi hak'uri karkayi fushi damu inde waliyyine gani zanmata walicci don farin cikinka kawai badan suba kayafemana don Allah".

Dakyar Abban ya hak'ura yakoma yazauna nandanan aka fara karanto sharudd'an aure yana amsawa daga k'arshe yamika sadaki aka d'aura auran Hydar da Yasmeen cikin k'ank'anin lokaci.



Khairat tana ganin angama d'aura auran ta yanke jiki ta fad'i k'asa sumammiya da gudu sukayo kanta Zasu Kawo mata agaji Abba yadaka musu tsawa yace.



"Duk Wanda yasake ya tab'ata wlh senayi Shari'a dashi,dukanku ku watse a gurinnan na sallami kowa kubarta ta mutu ma intaso, mugun iri zamu rage" ya fad'i cikin tsananin fushi wanda ke nuni da abinda yafad'a ze iya aykatawa.



Jiki a sanyaye d'aya bayan d'aya suka dunga ficewa a gidan har kowa yafice amman Hydar na tsugunne a gabanshi kallonshi yayi yace.



"kai me kake jira dabaka fitaba?".

Kukane ya kubcewa Hydar sabida yayi imani duk abinda Abba yakeyi dauriyace kawai dason k'arfafa zumunci amman ba wanda za'awa y'arsa haka komai laifin da tayi beji zafiba,cikin kuka Hydar yace.



"Abba kayimin dukkan hallacci kuma nagode kuma zan kasance me maka biyayya akowanne al-amari sede yanzu Abba zuciyata tagaza yimaka biyayya kayi hak'uri wlh bazan iya ganin Khairat cikin wannan yanayin natafi nakyaleta ba" yana gama fad'in hakan ya nufeta d'aukarta yayi kamar gawa yafice agidan motarshi yanufa da ita ya kwantar da ita abaya yashiga yatada motar yanufi asibiti da ita.



Abba ko zuciyarsa da tayi bak'ik'k'irin abisa abun da yafaru tabbas dauriyace kawai yakeyi Amman kulawar da Hydar yanuna ga Khairat a gabansa yasa duk wani b'acin Ransa yanemeshi ya rasa tabbas ya yarda Hydar k'addarace ta fad'a masa nason auran Yasmeen amman bawai dan ya shirya wulak'anta Khairat ba, wani farinciki yaji yana shigarsa tabbas yayi abinda yadace Allah yabasu zaman lfy.



Yasmeen ko duk inda tashiga se gulmarta akeyi ana kyararta,wasu suyi agaban idonta wasu kuma suyi abayan idonta.

To kunsan halin mutuniyar taku ba tsaron kowa takejiba dan haka Bud'ar bakinta se cewa tayi.



"Ayyiriririy ni Amarya a Gidan Hydar tunda bak'inciki yasa kun Kasa yimin y'ar gud'ar da akewa Amarya yayinda aka d'aura mata aure toni nayiwa kaina,kuma wlh komai zakuce daga bayane tunda nariga nazama mallakinsa Wanda ku baku isa ku rababa dan haka kun dade baku zageniba"ta fad'i cikin isa ita duk zatonta iyayenta basa cikin gidan shiyasa tazage ta karkad'awa masu gulmar tata rashin kunya.



Wuf taji an damk'ota ta baya Umman tace kan tayi wani yunk'urin guduwa tariga ta rik'eta nanfa tashiga dukanta kamar zata kasheta dangin suna kallo bawanda yazo ya ceceta ita kuma takasa gudu Umman ko cigaba take da dukanta iya k'arfinta Yasmeen tun tana kuka har muryar ta dusashe da sauri Fatima tazo ta kama Umman Da kyar takaita d'akin da ba kowa tace cikin kuka.



"Haba Umma meyasa kike hakane?dukan dakike matane ze warware auran da aka riga aka d'aura? koko shine ze shafe abinda yafaru,?kidubafa kiga ko kara cikinsu bawanda yamiki kina dukanta amman bawanda ya ceceta wanda aka'ida hakan ba dede bane,Umma duk abinda kayi se anmaka, meyasa baki dauki hakan a matsayin sakayyace Allah yayimin ta wannan hanyarba? nide gaskiya kidena dukanta haka shi kanshi mijinta inyaji kindaketa wlh girmanki ze zube a idonshi tunda son da yake mata banawasa bane Amman kiyi hak'uri inna batamiki rai".

Ajiyar zuciya umman tayi sannan tace.

"Fatima rainane yab'aci badan komaiba sedan ruk'on da Khairat tayimata na tsakani da Allah amman bawai ina Jada hukuncin Allah bane, bakomai bazan kuma dukantaba,matuk'ar batazo inda nakeba".



Kamal ne yace Fatima ta fito su tafi gida Abba yace su wuce gida shiyasa da zasu wuce ta kama hannun Yasmeen suka tafi tare dan bazata barta ummansu ta Illa tata ba itama lokaci yayi dazatawa Y'ar uwarta rana, tunda tasan komai Yasmeen tayi Dan ita tayishi.



wannan kenan



Maman Yusuf.

[5/4, 22:46] Zahra Surbajo: πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

*CIN AMANA KO FANSA*

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““



Zahra Muhammad mahmud



*Nobody is like you Nobody is like u, nobody cares 4 u, nobody misses u, nobody wants to see u good, nobody is ur best fr, nobody is happy with u.... dont cry.......my name is nobody.Rumaysa Lego's am always with you, take care*



*page 59-60*





Ko a mota kamal da Fatima se rarrashinta sukeyi da kalamai masu dad'i a haka har suka iso gidan.



Kaitsaye ruwan wanka me zafi Fatima ta had'awa Yasmeen sabida ta gargasa jikinta abinka da farar mace ko ina shatin dukane ajikinta yayi jawur, Da kyar tasamu tayi wankan kayan Fatima tasa dan ba tazo da kayantaba.



Indomie Fatima ta dafa mata wacce tasha had'in kayan lambu da hanta da kwai,Yasmeen duk soyayyarta da indomie wannan kasa ci tayi tanajin zafin abinda mahaifiyarta tamata wanda take kallonsa amatsayin rashin k'aunane yakawo hakan, tunda ko ita Khairat uwar laifin ay nata iyayen basuyi mata hakaba,kuka tasa sabida abun na cimata rai sosai.



Fatima ce tajiyo sautin kukanta tashigo d'akin da sauri ta dafata tace.



"Yasmeen wannan kukan ya isa haka inde baso kike kirasa hawaye gabad'ayaba, yadace kiyi shuru haka,inma akan abinda umma tayimikine namata magana kuma ta fahimci bata kyautaba Danhaka ki share hawayenki kinji k'anwata".



Share hawayen tayi tana kallon Fatima tausayinta nadad'a kamata,fatima ta fahimci hakan dan haka dariya tayi kawai tajawo kwanon abincin tashiga bata abaki harta cinye.





Hydar suna isa asibiti emergency ward aka kaita likitocine suka rufu akanta seda suka kwashe awa biyu akanta sannan ta farfad'o amman jininta yayi mugun hawa fiye da tunani, kwantar da ita sukayi awani d'aki namusamman anyimata allurar bacci dan haka bacci takeyi anason kwakwalwarta tasamu hutu.



Hydar ganin asibitin akwai kulawane yasa yabaro asibitin yadawo gidansu Khairat d'in anan yamusu bayanin abinda ke faruwa jiki na b'ari Umman Yasmeen ta d'auko mayafinta ita da wasu acikin y'an uwa tabishi zuwa asibitin lokacin dasuka je Khairat ta farka se kuka takeyi Hydar ne yashawarci likitocin akan ko zasu sake yimata allurar baccin ba musu suka sake danna mata wata takoma baccin.



Ganin dare yafarayine yasa Hydar mik'ewa ze tafi gida sabida Umman Yasmeen ce zata zauna da ita a Asibitin,sallama yamata bayan yaajiye mata kud'i koda buk'atarsu zata taso kamin yazo gobe sannan ya wuce.



Se yanzu yatuno da Yasmeen amman d'azu sam yamanta da ita sabida tashin hankalin dayake ciki gameda rashin lafiyar Khairat,waya yaciro yakira number d'inta ga mamakinsa Fatima ce ta d'auka bayan sun gaisa yace mata.



"Ina Yasmeen d'in take?".



"gatanan a gidana bata danjin dad'ine shiyasa"inji Fatima bayan sun had'a ido da Yasmeen d'in dake zaune tana jinsu.



"Oh my God gashi bansan gidanki ba Fatima turomin address Amman de jikin da sauk'i ko?".



"Eh to ba laifi da sauk'in zamuce bari na turo maka address d'in"



Amsawa yayi agaggauce dan gaba d'aya hankalinshi yatashi fiye da wanda yayi alokacin Khairat d'in,kallon wayarshi kawai yakeyi har text d'in address d'in yashigo da sauri ya Karya kan motar yanufi unguwar su fatiman besha wuya ba yagane address d'in,yana isa yakira yashaida musu gashi a k'ofar Gidan.



Yasmeen dariya kawai take kyalkyalawa lokacin da Fatima ke zuba masa K'aryar wai bata da lafiya har zuwa yanzu da Fatiman ke koyar da ita salon siye zuciyar miji.



Kissa da kisisina Fatima tashiga koyawa Yasmeen ta yadda zata zauna Lafiya da Khairat dan tasan Khairat farin sani badaga baya bace wajen wannan fannin,wani abun in Fatima ta fad'i Yasmeen dariya take harda hawaye, itade Fatima bata bi takanta abinda ze fishsheta take koyamata.



Wani turare Fatima ta shafawa Yasmeen sannan ta dunga jaddada mata abinda zata ce in Hydar d'in yashigo dade duk abinda yakamata seda takoya mata sannan tasa ta kwanta akan gadon ita kuma taje d'ayan d'akin inda kamal keta wasa da meemee ta sanar dashi zuwan Hydar yaje yashigo dashi.



Ba musu kamal yaje yashigo dashi cikin gidan kai tsaye har d'akin da Yasmeen d'in take yakaishi sannan suka sake gaisawa da Fatima daganan suka basu guri,a rud'e ya isa kan gadon yazauna rasa me zemata yayi kawai se yamik'a hannu ya d'agota cak yad'ora akan cinyarsa, itako kamar yadda Fatima Ta koyar da ita langabewa tayi ajikinshi tana kuka mara sauti sosai tana wani d'an zazzamewa ajikinshi.



Hankali atashe yasake rungumota yace.



"Babyna meyasameki haka? fad'amin abinda ke damunki"yatambaya cike da nuna kulawa.



Kamar yadda Fatima ta koyamata,narkewa tayi ajikinshi dakyar tace.

"K'irjinane yake wani irin abu nima bansan komeyeba"ta fad'i cikin lafazinta med'auke da tsabagen kissa aciki.



D'agota yayi yana kallon k'irjin yace, "dede inane yake miki ciwon?".



Ho y'ar nema,ay seta nuna masa dede saman na shanunta,da sauri yacire hijab d'in dake jikinta yanak'arewa gurin kallo,hankalinshi ne yafara tafiya ga wani asirtaccen k'amshi dake fitowa ajikinta yana k'ara tadamishi da hankali.



Dakyar ya iya kai hannunshi kan gurin πŸ™„jinin jikinsu duka seda yadena ayki na wani lokaci bama kamar Yasmeen da tsoro yakamata, dan ita inbanda ita ba wanda hannunshi yatab'a kaiwa wannan gurin se yau Hydar daya kai,ya lura da tsoronnata Amman seyayi kamar be luraba yaci gaba da shafa gurin duk azuwan yana ganin inda ke ciwonne da kyar ya iya d'auke hannunshi,koda yace tazo suje asibiti k'i tayi dan haka shantakewa yayi agidan se shad'aya yabar Gidan.



washe gari da safene yasamu damar yiwa iyayensa bayanin komai murna mahaifinshi yayi masa daga bisani yatafi gurin Abban yasake yin godiyar,gida yadawo yad'auki mahaifiyar Hydar d'in sukaje asibiti gaida Khairat.



Me gyaran amare Fatima ta d'aukowa Yasmeen tashiga gyara Yasmeen gyara bana wasaba dan Fatima cewa tayi ak'ure maneji wajen gyarata, ayko me gyaran ba ha'inci nanda nan Yasmeen tafara haskawa ciki da waje.



Maman Yusuf.

[5/5, 08:52] Zahra Surbajo: πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

*CIN AMANA KO FANSA*

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““





Zahra Muhammad mahmud



*Never cry for those who donot deserve ur tears but who deserve your tears never let you cry,AMINA SANI, MAMAN SAHIBA,MAMAN MUALLIM. am much more appreciate your care and support thanks stay nice.*





*page 61-62*





Kwanan Khairat bakwai a asibiti sannan aka sallameta bayan an kafa mata dokoki game da kula da lafiyarta.



Kai tsaye gidan su Yasmeen Umman Yasmeen d'in ta wuce da ita,jama'a se zuwa gaisheta akeyi gamida kwantar mata da hankali, dayake sanda tana asibitin anhana kowa ganinta

Please Login or Register in order to submit comment