Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiyasa yanzu aketa tururuwar zuwa ganinta.



Fatima da Yasmeen ma ba'a barsu a bayaba suma sunzo dubata,ko kallo basu ishetaba, da Fatima ta isheta da maganane kawai seta taso mata da masifa.



"Kinga malama banason tsohon munafunci tunda kinsa Yasmeen ta d'aukar miki fansa kuma tayi yadda kikeso ay inaga seki fita harkata haka, kuma wlh daga ke har ita sekunyi danasanin wannan d'aukar fansar,sabida ni Khairat wlh nafi k'arfin irin wannan agurin kowa bare ku,ke kuma Yasmeen I salute you, yardar danayi dakene yasa kikayi nasara Amman wlh dana farga da wuri ke kinsan kinyi kad'an kimin haka, Amman yanzuma ban makaraba muzuba nidake".



Tsananin mamakine ya hana Fatima magana gamida takaici, hawaye ne kawai suka shiga biyo fuskarta, Allah yasani bata da masaniya akan abinda Yasmeen tayi,amman Abu d'aya tasani tunda har Yasmeen ta auri Hydar a matsayinta na y'ar uwarta da bata da kamarta bazata barta tazama bora agidan mijiba, muryar Yasmeen ce takatseta.



"Allah yayi gaskiya dayace inbaka da kunya kayi abinda kaga Dama,yanzu har kece zaki bud'i baki kice anmiki ba dedeba? Dank'ari to kibud'e kunnenki dakyau Khairat nima Yasmeen ba tsoronki nakejiba, muzuba nidake aga wanda ze hak'ura yabarwa wani kuma albishirinki, kishirya zama dani amatsayin kishiyarki ba k'anwa ba dan najima da datse wannan dangantakar".



Da sauri Fatima taja Yasmeen suka fice a d'akin gurin ummansu sukaje suka gaisheta daganan suka shiga gidansu Khairat,a falo suka samu Abba da Umma durk'usawa sukayi suka gaishesu suka amsa cike da walwala Abba yace.



"Ke Fatima waya baki damar fita da matar mutum bada izininsa ba? wannan ay shashancine kibarta anan inzaki tafi sabida asan meza'ayi gameda tarewarta kinjiko?".

Kai Fatima ta d'aga tana murmushi.



Umman Khairat tace cikin dariya.



"Hala koda kika tafi da ita bawani shiri dakika mata dan shashanci?".



Shuru Fatima tayi hakan yasa umman d'auka bata ba Yasmeen magungunaba.



Haka Fatima ta tafi tabar Yasmeen agidan umman Khairat d'in.



Umma wata mata y'ar Sudan ta d'auko tace ta gyara mata Amarya,ayko Yasmeen tasha wuya dansu basu d'auka anmata agidan Fatima ba sosai suke d'irka mata magunguna har kuka take in aka bata wani Maganin ko tsarki zatayi da ruwan Magani take yinshi inde ba sallah zatayiba,ta jima da dena shan ruwa pure sede na Magani shiyasa duk abin ya isheta.



Shiko Hydar ya koma Abuja sabida yanayin aykinshi se ranar Friday zezo domin tafiya da Khairat kamar yadda Abba ya umarceshi.



Ranar Friday ko se bayan an sakko masallaci ya iso kaduna gidan iyayensa yafara zuwa suka gaisa sannan ya wuce gidan su Khairat inda Abba yace yasameshi inyazo.



A sit room Abban ya saukeshi bayan sungaisa nasiha sosai Abban yamasa akan yarik'e musu y'ay'a amana dan duka d'aya suke agurinsu ba banbanci.



"Insha Allahu Abba zanyi iya bakin k'ok'arina wajan ganin ba'a samu matsalaba".



"To Allah yabaka ikon kamanta adalcin, yanzu katafi da Khairat Yasmeen kuma zaka d'an bamu lokaci mud'an kintsa tunda kaga ayadda abun yazo bamu shiryaba".



"Abba wannan bawani abun damuwa bane duk abinda uba yakeyiwa y'arsa yayin auranta nine dama meyiwa Yasmeen koda bani Ta auraba tunda a hannuna ta taso, dan haka bana buk'atar ko tsinke a hannunku ni zanyimata inhar kun amince nan da sati biyu se ayi bikin tarewarta, Abba Tunda budurwace ba bazawaraba be kyautu amata aure bawani biki ba".



Kalaman Hydar sunshigi Abba tabbas abinda Hydar yafad'i gaskiyane dan haka dole itama ashirya mata taron auranta kamar kowacce y'a.



"Maganar ka Hydar gaskiyane kuma naji dad'in wannan shawarar taka insha Allahu kuma nan da sati biyu za'ayi kamar yadda ka buk'ata,maganar kayan dakace zakayi kuwa bazan hanakaba danshima kafimu gaskiya tabbas uba kake a gurinta munbaka wannan damar Allah ya had'a kanku baki d'aya ku zauna Lfy,bari inturo maka Yasmeen d'in kugaisa kamin Khairat d'in tafito ku wuce".



Godiya Hydar yay tayi kamar baze denaba har Abban yafice daga gurin,cikin gida Abban yanufa yakira Yasmeen yace taje sit room Hydar najiranta, Umman Khairat ce tasake gyarata sannan tace taje to,tafiya Yasmeen take jiki a sanyaye dan bak'aramin kunya Umman Khairat take bata ba ahaka har tak'araso k'ofar shiga sit room d'in,kasa shiga tayi ta tsaya tana tunani shiko ya hangota ta labule danhaka sejitayi an kamota anjata zuwa cikin d'akin a tsorace take kallonshi dan ita tsoronshi takeji tun abinda yamata rannan.



"Baby yanzu kuma ni kikejin tsoro har baza'a shigo gurinaba?"yafad'i yana k'ok'arin had'a bakinshi da nata,k'ank'ame jikinta tayi guri guda ta rufe idonta shi abunma dariya yabashi danhaka cakulkuli yashiga yimata ayko takasa daurewa tashiga kyalkyala dariya tana gaggantsarewa seda ya wahal da ita sannan ya kyaleta.



"Baby jikinki yak'ara laushi gawani k'amshi dakikeyi fad'amin meyene sirrin?".



Cusa kanta tayi a k'irjinshi tayi lamo tak'i bashi amsa se murmushi takeyi.



"Baby zanyi missing d'inki wlh yau zan wuce da Auntynki ke kuma senan da two weeks sabida za'ayi taron biki kamin ki tare,yanzude kije ki kawomin passport naki ko guda d'ayane da national I'd card d'inki kinji da indigen d'inki".



Akunyace tashiga cikin gidan dan kayanta duk sunyi squeeze haka ta daure ta shiga taje ta d'auko duk abinda ya buk'ata ta kawomishi.



Mik'ewa yayi suna sallama, ay mutuniyar taku yi tayi kamar zata fad'i hakan yasa Hydar ya rungumeta da sauri ita ko tai amfani da wannan damar Wajan manna bakinta a k'irjinshi jambakinta yafito ajikin shaddar jikinshi kamarde kiss, shiko bemasan tayiba,kwacewa tayi ajikinshi takoma gefe, kud'i yabata masu yawa yace tarik'e kamin yazo next week a haka sukayi sallama yafice itakuma takoma cikin gidan tana dariyar muguntar bomb d'in data had'a.



muje zuwa.





Maman Yusuf.

[5/6, 18:57] Zahra Surbajo: πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

*CIN AMANA KO FANSA*

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““





Zahra Muhammad mahmud



*Only the open heart receives LOVE Only the open mind receives WISDOM,Only the open hand receives GIFTS, and Only the CUTE 1 receive MESSAGES From ME!,MAMAN IZZUDDEEN, MAMAN ABULKHAIR,QUEEN HASSANA GWAMBE,MAMAN HANIF,am really appreciate your support thanks you all*



*page 63-64*





Mota Hydar yaje yazauna yana jiran fitowarta dan tuni ansaka kayanta a booth.



Koda tazo tana shirin shiga motar yadakatar da ita dacewa yakamata taje tawa iyayenta sallama, ko kallo be ishetaba tashige motar abinta tana doka masa harara.



Be kulataba yatada motar suka bar harabar gurin,tafe suke bame cewa kowa k'ala har suka zo unguwar mu'azu junction inda yashiga wani gidan mai domin yak'ara mai,angama zubamasa, mik'a hannun dazeyi cikin aljihu yad'auko kud'in idon Khairat yasauka akan kiss d'in jambakin Yasmeen.

Wohoho bala'i ba'a samaka rana.



Wata kururuwa tayi takaima gurin damk'a dasauri Hydar yabada kud'in yaja motar suka fice daga gidan man dan takusa tara masa jama'a.



Itako ashar data dunga zundumawa Yasmeen bazasu fad'uba kamin daga bisani tadawo kan Hydar d'in.



"Wlh kaji kunya Hydar kazama bunsuru kabi ya kabi k'anwa, wato iskancinnaku yakai hartayimaka kiss a riga dankazo kanunamin? to wlh baku isaba daga kai har itan dede nake daku,cin amanar tawa dakukayi bata ishekuba sekun bini da haka,waya sanima ko tuni kagama saninta awaje watak'ila ma Allah kad'ai yasan yawan cikin dakuka zubar dan amaryar da bata saba da mijin tun awajeba bazatayi hakaba, nide ba abinda zancemuku se Allah ya isa munafukai kawai, wlh wutarku daban take ko fira'una yafiku matsayi a jahannama".



Tass Tass Tass!!!.



Hydar yad'auketa da wasu zafafan mari har guda uku,tuni idanuwanshi suka rine gashin jikinshi suka tashi jikinshi har rawa yake yasamu gefen titi yayi parking sannan yasake kifamata wani Marin sannan yace cikin b'acin rai.



"Ke Khairat ya isheki haka!!,how dare you dazaki sani agaba kina fad'amin magana son ranki? ni d'anki akace miki?,shasha dak'ik'iya wacce batasan abinda yadace ba,inna santa a wajen ina ruwanki? ayba jikinki bane,kuma kiss dakike fad'a akan tayishi tayi d'in ba Matata bace? koko kin isa kisa mata dokar tab'a jikinane? to Bari kiji infad'amiki ba kiss ba wataranama sucking zatamin seki mutu inkin so, wawiya kawai wlh wannanne nafarko na k'arshe dazaki kuma yimin haka"yana gama fad'an ya fisgi motar da matsiyacin gudu.



Itako Khairat kumatunta har sun tasa sabida marin datasha, tayi danasani fad'amishi maganar dan bata tab'a ganin b'acin ranshi irin hakaba,kuka tadungayi na d'umbin tausayin kanta, waima Yasmeen d'in bata tareba kenan inaga kuma ga ta tare,haka taci gaba da kukanta har suka isa gida ficewa yayi yabarta a motar,a sanyaye tafito itama tabi bayanshi zuwa cikin gidan.



A falo tasameshi rungume da yaransa suna masa sannu da zuwa,tana shigowa yazare jikinsa ya haura sama.





A b'angaren Yasmeen kuwa k'awayenta taita kira awaya akan zancen shagalin bikinta,suma su Fatima gayyata sukayi sosai dasu Umma.



Gyara ko Yasmeen tashashi harta godewa Allah,jikinta sewani kyalli yake yana santsi ga laushi dayayi,me k'unshi aka d'auko tayimata abin gwanin Sha'awa,Ranar alhamis sukayi bridal shower abin sewanda yagani kyau de kam Yasmeen tayishi bana wasa ba.



Dukiyar da Hydar ya narka ma Yasmeen a b'angaranta sewanda yagani ba abinda besaba haka kayan lefenta seda yahad'amata akwati guda ishirin shak'e da kaya na alfarma.



Ranar jummaa za'ayi dinner dan haka tun safe Hydar da aminansa suka bar garin Abuja zuwa Kaduna domin halartar taron.



Khairat ko abin duniya ya isheta dan tun ranar dasuka dawo daga kaduna Hydar bek'ara bi takantaba fushi yake da ita bana wasaba danko abincinta yadena ci,tarasa yadda zatayi gashi yau kuma yawuce kaduna ko sallama babu wanda tasan bazata sake ganinshiba se ranar Saturday kuma da Amarya zasu taho fashewa tayi da kuka na bak'inciki fad'i take, "Allah ya isa Yasmeen kincuceni bazan tab'a yafemikiba".



Dinner fa takai dinner abin sewanda yaje yagani Hydar da Yasmeen sun had'u kamar bagobe sosai dinner tak'ayatar anci ansha anyi hotuna abinde no easy.



Washegari dasafe aka kawo motocin d'aukar Amarya jama'a sunyi dafifi zasu shiga Abban Khairat yadakatar dasu sannan yace kowa yakoma gida babu me zuwa kai amarya,abun be musu dad'iba dangama kowa yasa rai zeje kuma yazo ya hana.



Hydar yakira awaya yace yasameshi a gida yanzunnan,ayko be b'ata lokaciba yazo, tare da Yasmeen yasameshi zaune a sit room kanta aduk'e alamun kuka takeyi,yayi sallama yashiga shima yazauna.



Abbane yafara magana da cewa.



"Hydar ga Yasmeen nan zaka tafi da ita dakanka kayi k'ok'arin tarbiyantar da ita duk dacewa dama tarbiyarkace to kad'ora zaman aure se hak'uri Allah yabaka ikon yin adalci a tsakaninsu, kayi hak'uri da shirman dazaka gani daga Khairat wata rana zezama tarihi kaji".



Godiya sosai Hydar yayimasa itako Yasmeen kuka take harda majina.



Hannun Yasmeen Abban yakamo yasa a hannun Hydar yace.



"Kutashi kuje Allah yayi mumu albarka".



Hydar ne ya amsa amma banda Yasmeen, kamata yayi suka fito tana ta kuka Fatima suka samu da Umman Khairat awaje suna jiransu, hannun Yasmeen suka ja zuwa cikin gida gurin Ummanta, kuka Yasmeen take wanda ya tilastawa Umman yin kukan itama, rungume juna sukayi Umman na fad'in "nayafemiki Yasmeen Allah yabaku zaman lfy da hak'uri da juna keda y'ar uwarki".



Gurin Abban ta suka kaita shima yasa mata albarka daganan umman Khairat zama tayi Fatima ce da sauran dangi suka raka Yasmeen gurin Hydar dake tsaye yana jiranta.



Fatima kamo hannun Hydar tayi tasa na Yasmeen tana hawaye tace.



"Hydar kaso Fatima Allah bebakaba Ashe akwai manufarsa dayasa yay hakan, sabida da kasamu Fatima da yanzu bazaka samu Yasmeen ba,Hydar Yasmeen itace Fatimarka ta baya kayi k'ok'ari ka rik'emin ita amana, Allah yabaku zaman lfy da hak'uri da juna",tana gama fad'in haka ta juya da sauri tashige gida tana kuka.



Hydar bud'e motar yayi yasa Yasmeen sannan shima yazagaya yashiga yatada motar suka d'au hanya, dangi se d'aga musu hannu suke harsuka b'ace.



Gidansu yafara kaita Iyayensa suka musu fad'a sosai Dan yanzu Hajiyar shi tadena fushi dashi addu'o'i suka musu, sannan suka kama hanyar Abuja.



Maman Yusuf.

[5/7, 08:46] Zahra Surbajo: πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““ *CIN AMANA KO FANSA*

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““





Zahra Muhammad mahmud



*Someone somewhere dreams of your smile.and while thinking of you says life is wortewhile.So whenever you"re lonely,remember its true,someone somewhere is thinking of you,Maryam Murtala Mahmud, Aisha Jumey,Fiddah,thanks you all*



*page 65-66*



Tafe suke Yasmeen nata rusa kuka shiko Hydar inbanda tsokanarta ba abinda yake danshi kukanma dariya yabashi, itako wannan dariya dayake mata ay kamar ya zugatane k'ara k'aimi tayi gurin cigaba da kukan.



Ganin kukannata bana wasabane shine yasa yay parking agefen hanya,to dama glass d'in motar tinted ne shiya bashi damar rungumota gaba d'aya jikinshi yafara rarrashi.



"Haba Baby na meyasa kike wannan kukan kamar anmiki dole gurin aurena?ninefa Hydaranki amman kike wannan kukan dan zankaiki gidana ko yanzu kindena sonane?".da sauri ta girgiza masa kai,cigaba yayi dacewa.



"To kiyi shuru banason kukan haka dan kar kanki yayi ciwo anjima inaji ina gani ki cuceni".yak'arasa zancan yana dariya.



Ita ko kunya zancan yabata dan haka zamewa tayi daga jikinshi takoma gurin zamanta tana murmushi,tada motar yayi suka ci gaba da tafiya yana janta da hira ba Laifi tana bashi amsa har suka iso gidan.



Ga mamakinshi k'ofar shiga gidan duka akulle yayi nucking Amman tak'i bud'ewa shikuma mantawa yayi betafi da key d'inshi ba,nurking yacigaba dayi zuwacan yaji muryar Khairat tana fad'in.



"Wlh baka isa kashigomin da wannan bak'ar kadararba sede kamaida ita inda ka d'aukota Amman wlh bazata kwana agidannanba".



Cikin fushi yace.



"Kibud'e k'ofar nan nace inba hakaba wlh sakamakon daze biyo baya baze miki dad'iba".



"To namijin hotiho wlh bazan bud'eba sakamakon kuma inyatashi fitowa Inga f-nine kaine kadamu baniba, munafukai kawai maciya amana, masu maida sharri ga alkha'iri,wlh sekunci wutar Allah".



Ran Hydar yagama b'aci kuma shi baze biyemata sunayiba har masu gadin gidan su fuskanci abinda ke faruwa,juyawa yayi yanufi gurin drivernshi ya amshi mukullin wata mota yaje yabud'e yad'auko wata envelop y'ar babba meruwan k'asa yajuya yaba drivern key d'in,jan hannun Yasmeen yayi suka koma mota yaja suka bar gidan.



Hilton transcop hotel suka nufa suna zuwa yakama d'aki aka basu key suka wuce d'akin.



Suna shiga kan gado yaje ya kwanta dan har yanzu ranshi ab'ace yake,Yasmeen ko rab'ewa tayi daga bakin k'ofar tana kallonshi shima ita yake kallo sun kwashe mintuna ahaka, daga k'arshe hannu yamik'a mata alamar tazo,ba musu ta tafi a hankali cikin takunta na k'asaita ta iso bakin gadon a tsorace takama hannunnashi janta yayi tafad'a kanshi, mirgina yayi yazamana takoma kasanshi Rabin jikinshi na samanta.



K'ureta yayi da ido yana kallonta gaba d'aya tabashi tausayi ace Amarya amman anhanaki shiga gidan mijinki sede hotel bakomai ze d'aukar mata fansar wannan rashin adalcin.



Hancinta yaja duk tayi wik'i wik'i sabida tsoro,murmushi yayi yace.



"Nide Babyna nasanta bata da tsoro amman yanzu naga nema take takoma matsoraciya gabad'ayanta wannan zare ido haka"ya fad'i sanda yakai bakinshi dede nata jira kawai yake tai magana, dayake ta fahimceshi setak'i yin maganar bedamuba yafara kissing d'inta a hakan da kanta da dad'i ya ratsota ta bud'e bakin suka shiga kissing d'in junansu seda yaga suna k'ok'arin fita a hayyacinsune yazame jikinshi yashige toilet, dan yasha alwashin ba a nanne yadace ya kusanceta ba ya tanaji guri na musamman, wanka yayi yad'auro alwala yamaida kayan jikinshi itama zuwa tayi tayo alwalar tabi bayanshi sukayi sallah.



Abinci aka kawo musu suna gama ci aka kirashi awaya bayan yagama amsa wayarne yamik'e, yace ta taso su tafi ba musu tabi bayanshi suka kulle k'ofar suna zuwa reception yabada key d'in suka fice,mota suka shiga yatada suka bar harabar hotel d'in,hanyar Airport taga yanufa batamasa maganaba har suka isa wani mutumne yazo yatarbesu yana fara'a yace.



"Ranka yadad'e ay tuni boarding pass d'inku yafito to amman ban anso ba sabida passport d'inku yana hannunku yanzu passport d'in zaka bani inje in amso muku".



Envelop d'in yabude yad'auko masa passport d'in yabashi yaje, bejimaba yadawo musu dashi, ihsani Hydar yamasa mutumin se godiya yake daganan suka fita a motar Hydar ya kulle yaba mutumin key ,yace yarik'e drivernsa zezo ya amsa, waya yaciro yakira drivern yace yazo Airport zega motarsa a dede setin departure zega wani najiransa ya amshi key a hannun mutumin yamaidar masa da motar gida.



Yana gama wayar yaja hannun Yasmeen wacce tun dasuka zo gurin kanta yakulle dan mamaki,to ina zasuje? Dama passport zeyimata shiyasa yace tabashi su I'd card d'inta? lalle Hydar Aliyunne.



Dayake yanada alfarma kuma basuda kaya ko na hand bag shiyasa basu sha wahalaba suka shiga jirgi basu jimaba jirginsu yad'aga zuwa k'asa me tsarki.





Saukar dare sukayi shiyasa suna isa masauki sallah sukayi suka ci abinci suka kwanta,basu tashiba seda asuba,dan sunso su makarama, dasauri Hydar yajasu sallah suna idarwa fitowa yayi wajen hotel d'insu shagunane birjik anata hada-hada sabida su larabawa ba ruwansu ko cikin dare suna kasuwanci,wani shago yanufa inda yaga suna saida kayan sawa yasiyo musu shida Yasmeen, ita dogayen riguna yasiya mata dasu pant da brezia da takalma irin flat shoes d'innan, haka shima yasiya jallabiyoyi da kuma k'ananan kaya da takalman Dade duk abinda yasan zasu buk'ata dan akwati biyu yayi na kayan yabiya suka bashi wanda zekaimasa har masauki.



Suna zuwa k'ofar d'akin ya sallami wanda yakawon,shi yak'arasa shiga dasu cikin d'akin lokacin Yasmeen na zaune tana lazimi, dasauri tamik'e ta tayashi shigo da kayan.



Wanka sukayi suka canja kaya sannan suka nufi masallacin Annabi,murna da farincikin Yasmeen abin baze fad'uba ,sunyi addu'o'i sosai gameda Allah yabasu zaman Lfy.



Kwanansu biyar a madina suka wuce makkah nan ma Yasmeen harda kukanta sunyi ibada sosai,shiko dama Hydar bakomai yasa suka zo saudiyyaba sedan yama kansa alk'awarin agarin makkah ze fara kusantar Yasmeen shiyasa sukazo.



Yau jumma'a ana rana sosai agarin makkah me zafi danma suna ta'ammali da AC da abin yafi haka, ana idar da sallah Hydar yaja Yasmeen sukayi d'awafi suna gama d'awafin sukayi sallah raka'a biyu sukasha zamzam sannan suka nufi gida, a hanya suka tsaya yase musu kaza dan masaukinnasu kana wuce bindau ne basu da nisa da harami.



Suna shiga d'akinsu yadda Yasmeen taga yadda yake rawar k'afa tasan da bayani.



muje zuwa.



Maman Yusuf.

[5/8, 11:18] Zahra Surbajo: πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

*CIN AMANA KO FANSA*

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““





Zahra Muhammad mahmud





*Munga shekaran jiya tare, muka ga jiya tare, kuma munga yau tare,munasan ran ganin gobe tare da ikon Allah, my sweet talatsuruwa,😝Ussaina Muhammad Lawan, Naibawa Kano,since 2005 up to now you are deep inside my heart,stay nice*





*page 67-68*





Tunkarota yakeyi ita kuma tana jada baya harsuka kai k'arshen bango,runtse idonta tayi dan batason kallon idonshi.



D'aukota yayi yad'ora agado yashiga sarrafata,ido kawai Yasmeen take kwalowa dan abin na Hydar yawuce tunaninta,shiko gogan naku be ji be gani yake romancing d'inta.



Kuka takemishi sosai akan ya kyaleta amman ina ay kamar mayan k'arfe ya had'u da k'arfe,ay Abu daya kai abu ma shima kukan yasa(Anwar na biyu)yadda take rusa kuka shima haka yakeyi dan harseda Yasmeen ta saurara tana kallonshi dan fahimtar meyakewa kuka harda hawaye.



Dukansu sunji jiki dan Hydar jiyake dad'in kamar ze janyeshi zuwa cikin Yasmeen, dakyar ya saurara mata,fuskarta tayi luhu luhu idonta sun kumbura gwanin ban tausayi kuka kawai takeyi,shima kwance yake yakasa motsawa yana sauraron sautin kukanta yana tab'amishi zuciya, dan se yanzu ne yatabbatar yana sonta da duk hauka yakeyi.



Dakyar yajawota jikinshi yarungume soyake ya rarrasheta amman yakasa dan abinda yaji daga gareta ba maganarsaba har ji da ganinsa seda yatafi dashi, don be tab'a jin abinda yaji ajikin wata maceba bayan ita.



Jijjigata yake kamar yarinya yana d'an bubbuga bayanta alamar tayi shuru,zuwacan Allah yataimakeshi kalma ta dawo kan bakinshi yace.



"My soulmate kiyi hak'uri don Allah kidena kuka, Allah yamiki baiwar da mutum baze iyamiki shaf shaf ba dole se an d'au lokaci wlh bada son raina naimiki hakaba kiyi hak'uri, yau kinbani abinda kud'i da mulki basu isa su semin shiba wato virginity d'inki Allah yamiki albarka, yakaremin ke daga sharrin duk abin k'i I love you so much more my Baby".



Yana gama fad'amata yasake rungumota jikinshi yana mata kiss a goshi,



Wani sanyi Yasmeen taji aranta tabbas ta yarda budurcin mace shine mutuncinta a gurin mijinta, babu wata daraja ga budurwar data zubar da mutuncinta awaje bazata tab'a kima a idon mijinta ba har abada, koda kuwa sune Laila majnun afagen soyayya,kwantar da kanta tayi akan k'irjinshi tana godewa Allah daya bata ikon yiwa mijinta kyauta mafi girman daraja.



Toilet yashiga ya had'a musu ruwan wanka sannan yazo ya d'auketa suka shiga wankan Yasmeen se kunyarshi takeji shiko ko ajikinshi.



Satin su uku a saudiyya suka d'aga zuwa Dubai acanne aka dagargaji soyayya harta tsawon sati biyu,daga can kuma suka sauka k'asar Masar itama anyi soyayya kamar ba gobe gaba d'aya Sun sauya Kana kallonsu kasan suna cikin kwanciyar hankali,Hydar yaso suje UK Yasmeen ce tak'i yarda itade sukoma gida haka ya isa,tsawon wannan lokutan dasuka share basa Nigeria gaba d'aya sim card d'insu ciresu sukayi suka sa sabo shiyasa ko a Nigeria annemesu baza'a samesuba.



Waiwaye adan tafiya.



Tunda Hydar suka fice agidan hankalin Khairat yatashi tunaninta, "to Ina zasuje",ranar wuni tayi tunani,har zuwa sanda driver yakawo mata key d'in motar Hydar daya d'auko a Airport,agigice take sauraron bayanin drivern,da gudu ta haura sama inda d'akinta yake ta fad'a kan gado tana kukan takaici fad'i take.



"Why Yasmeen? meyasa koyaushe kece kike winning akaina?,naso k'untatamiki gashi k'arshe kaina nayiwa,nashiga uku ni Khairat Hydar ya auromin ajalina",cigaba tayi da kukanta.



Tundaga ranar dasuka tafi kullum ta Allah se Khairat tayi kuka na bak'in ciki musamman inta kira wayarshi tak'i shiga ko abinci yanzu dakyar take ci, kallo d'aya zaka mata kasan bata da kwanciyar hankali danko kwalliya Ta dena, kunsan ko tashin hankalin daze hana Khairat kwalliya ba k'arami bane,Fatima ce abokiyar shawararta to itama Sun b'ata rasa inda zatasa kanta tayi.



Watansu Hydar biyu a yawon honey moon sannan suka nufo gida niger cike daso da k'aunar juna,Yasmeen yanzu sam batajin kunyar Hydar har rawa take agabanshi ba kaya sosai take tsula tsiyarta, dan ita yanzune ma tagane meyasa mata suke damuwa in za'a musu kishiya ashe suna da gaskiya dan ko ita yanzu yadda takejin Hydar aranta inyace zemata kishiya za'a kwashi y'an kallo.



Saukar dare sukayi dan haka hotel Hydar yakama musu me kyau d'akin daya kama babbane da falo sannan dakuma d'akuna biyu aciki ga dinning area komai ya had'u gashi kuma hotel d'in ba'a cikin mutane yakeba sabida akasari turawa ke sauka acikinshi,bakowa ze gane kana gurinba dankowa akwai hanyar fitarsa ta baya base wani yaganshiba.



Wanka sukayi suka ci abinci suka rama sallah,sannan Yasmeen tasamishi rigimar seya goyata bashida zab'i tunda shi yasaba mata da goyon, mik'ewa yayi yagoyatan yana zagaya d'akin da ita suna dariya se da taga da gaske yagaji sannan ta kyaleshi suka nufi gado, acanma seda suka sha soyayyarsu bayan komai yalafa sukayi wanka sannan suka kwanta rungume da juna.



Kwanansu goma da dawowa Hydar ya d'auki Yasmeen da tsaraba suka nufi garin kaduna,Iyayensu sunyi murna da ganinsu rasa inda zasu sasu sukayi kowa Yasmeen.



Fa'eeza k'anwar Khairat ce takira Khairat tasanar da ita zuwansu Hydar Kaduna, dan ita batama san sundawoba,ayko Khairat jikinta har rawa yake Tamik'e tashiga d'akinta Ta d'auko gyalenta da jaka da takalmi da key d'in mota ko hoda bata tsaya shafawaba tayiwa Iman sallama akan ta kula da gida sannan tafice daga Gidan acikin motar ta k'irar kamfanin Toyota mesuna venza bak'a, ta harbata kan titi zuwa garin Kaduna.



To Khairat fatan alkhairi.





Maman Yusuf.

[5/9, 07:38] Zahra Surbajo: πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

*CIN AMANA KO FANSA*

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““





Zahra Muhammad mahmud





*This page is dedicated to my sweet friend Fatima Zahra Katsina (Maman Mahmoud)in sha Allahu we are together now and forever.*



*page 69-70*





Ta iso Kaduna lafiya,tunkamin tagama parking ta tabbatar da zancan Faeexa sabida motar Hydar da tagani a k'ofar gidansu.



Da gudu tashige cikin gidansu har ta wuce sit room sekuma ta dawo sabida jin muryar Hydar da tayi aciki shida Abban ta,da sauri ta fad'a cikin d'akin tana kuka jikin mahaifinta ta nufa ta rungumeshi.



Gaba d'ayansu sunyi mamaki da zuwanta,babu ma kamar Hydar, cikin kuka Khairat take magana da mahaifinta.



"Abba wlh Yasmeen da Hydar so suke su kasheni,Hydar bashida adalci ko kad'an rabona dana sashi a idona,ko naji muryarsa tun ranar da yataho da Yasmeen sekuma yanzu dana ganshi tare da kai, Abba kataimakeni kar na mutu don Allah".



Maganganun Khairat tabbas sunshigi mahaifinta dan ko a ido ka kalleta kasan bata da kwanciyar hankali,duba da ganin yadda tarame tayi bak'i tafita hayyacinta.



Hydar ko ji yayi kamar k'asa ta tsage yashige don kunyar da yaji,gaba d'aya rasa yadda zeyi yayi,se yanzu ya gane beyi mata adalci ba,natafiya da yayi batare da ko kud'in cefane ya bata ba,kunyar idon Abba gabad'aya ta dabaibayeshi,so yake yay magana Amman yakasa.



Abban ranshine ya b'aci game da abinda Hydar yama Khairat,ko wanne irin laifi tamasa,be dace ya kwashe sama da kwanaki saba'in batare da yaje inda take ba, sosai abun ya b'ata masa rai dan har akan fuskarsa se da fushin shi ya nuna.



Hydar zeyi magana Abban ya dakatar dashi da cewa.



"Kar kacemin komai Hydar, nagama fahimtar komai, nide abu d'aya zance maka shine kayi hak'uri idan kuma kagaza hak'urin dasu

Please Login or Register in order to submit comment