Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

are, you are deep inside my heart 😍😍😍*





*page 43-44*





Tun daga wannan lokaci Hydar yakasa gane kansa,kullum bashida ayki sena tunanin Yasmeen yarasa dalili gaba d'aya yabi ya susuce yafita hayyacinshi.



Sosai Khairat taga canji daga megidannata wanda tasan da ba haka yakeba, koda ta tambayeshi meke damunshi, murmushi kawai yamata yace shima besaniba amman ta tayashi da addu'a.



Khairat bata da zab'in daya wuce ta tayashi da addu'ar kamar yadda ya buk'ata.





*Bayan shekara bakwai.*





Al-amura sun Faru da dama aciki harda komawar Fatima da Khairat makaranta inda a halin yanzu sungama degree d'insu Master's sukeyi yanzu.



Hydar yabiya musu makkah Fatima da Khairat d'in harda kamal sunje har sun dawo.



Rayuwa taci gaba da tafiya inda dukansu sun sake haihuwa duka mata suka haifa,inda y'ar gidan Fatima akasa mata Khairat suna kiranta meemee,itakuma Khairat sunan mahaifiyar Hydar akasa suna kiranta meema.



Yasmeen da Iman yanzu sunkai matakin ss2 a makaranta, shak'uwace me k'arfi a tsakaninsu bata wasaba.



Hydar kuwa so da k'aunar Yasmeen yanzu sungama kamashi dan beda kwanciyar hankali ko kad'an yaso yacireta aranshi amman abun ya gagara dan yasan duk ranar da zancan ya fito akwai tashin hankali bad'an kad'anba amman ya barwa Allah zab'i





Wata budurwa na hango wacce shekarunta basu wuce 16 ba sanye cikin wasu riga da wando farare, wandon and'an yagashi daga dede gwuiwa wato crazy rigar body hug ce itama fara se wata bak'ar boy friend jacket data d'ora asaman kayan takalmin k'afarta dogone irin me igiyoyinnan shima bak'i se farin gyale data nad'a akanta ta rataya bak'ar jaka fuskarta sanye cikin wani k'aton glass irin me rufe rabin fuska,kai me karatu duk yadda zan fasaltamaka kyau da had'uwar budurwarnan bazan fad'a maka daidai ba sede abu guda zan iya cewa, k'arshece gurin had'uwa,ba kowa bace wannan budurwa face *Yasmeen.*





Sakkowa take daga step cikin tafiyarta me d'aukar hankali har ta k'araso falon gidan, jikin Khairat ta nufa ta kwanta wacce ke zaune ita da hydar suna tattaunawa game da al-amuran siyasarsa dan tenure d'inshi tak'are har yasake maimaitawa.



Tunda Yasmeen tashigo falon gaba d'aya Hydar yay loosing control, hankalinshi nakanta tsawon wannan shekaru da sonta da k'aunarta yake kwana yake tashi, ya jima da amincewa zuciyarshi tabbas son Yasmeen yakeyi,muryartace ta dawo dashi daga tunanin daya tafi.



"Aunty zamuje shan ice cream nida Iman kuma we don't have enough money so please abamu don Allah",ta fad'a cike da shagwab'a dan ita koda wa zatayi magana a shagwab'e takeyi ya zama nature d'inta.



"Au yau kuma ni zaki tambaya? ki tambayi daddyn ku mana gashinan yana jinki danni ko sisi bazan bakuba, ko jiya about 50k kuka amsa a hannuna zakuyi ankwan k'awarku to yaude kam bazan bayarba".



"Tunda bazaki bamuba shikenan munfasa zuwan"Yasmeen ta fad'i ranta a b'ace ta mik'e zata wuce dan ita in akwai abinda ta tsana shine ace tayiwa Hydar magana gaisuwace kawai take had'ata dashi itama bata wuce ina kwana,daga haka bata k'arawa.



Wannan hali na Yasmeen shi yake sawa Hydar yarasa taya ze sanar da ita abinda ke damunsa aransa,yarasa gane me yay mata data tsaneshi haka dan tabbas tsanace tunda shi kad'ai takewa hakan.



"Au Yasmeen daki tambayi daddy gwanda kifasa zuwa duk wannan wankan sikarin dakika sha?".



Ko kallonta batayiba taci gaba da tafiyarta, cikin in ina Hydar yace.



"Yasmeen!!!"



Cak ta tsaya a inda take don jin sunanta a bakin wanda be tab'a furtawa ba,kuma batajin akwai wani mahaluki daya kaishi iya furta sunan.



Shima kanshi yayi mamakin yadda ya iya kiran sunan nata kai tsaye haka, danshi har tsoronta ma yakeji, daurewa yayi yaci gaba da cewa.



"Zo muje na siyamuku ice cream d'in kar kiyi Kwalliyar a banza, kyale Auntyn ki so take takashemiki kasuwa don taga kinyi kyau, kyaleta kizo muje dama nima fita zanyi".



Ba Khairat da Yasmeen ba shi kanshi mamakin kansa yakeyi,don magana makwatanciyar wannan bata tab'a had'ashi da ita ba,itako Khairat farin ciki ne yakamata yau Hydar ya nuna kulawarsa ga k'anwarta dan sam batajin dad'in rashin kula Yasmeen dayakeyi dan haka yanzu murnarta tagaza b'oyuwa shima yagani.



Yasmeen kuwa wani killer smile tasaki,dan yau tayi imani addu'arta ta tsawon shekara takwas tafara amsuwa, seda ta dedeta natsuwarta sannan ta juyo fuska a had'e tace.



"Ni nafasa zuwa kabarshi kawai dama kuma Iman ma bata shiryaba"ta fad'i cikin salon datasan dole ta d'auki hankalinsa.



"Banason irin haka Yasmeen taya da girmansa zece kizo kuje yasaimiki amman sewani abu kikeyi kamar wani sa'anki, banason iskanci kizo kiwuce kutafi kya tahowa da Iman d'in nata,tunda bata shiryaba, haba,yarinya se shegen kafiyar tsiya"Khairat ta fad'i cikin b'acin rai.



Killer smile Yasmeen tasake yi aranta tace,"wow I love that, da kanki kika bani dama gaskiya nagode miki" Amman a fili tafiya tayi da gudu ta rungume Khairat d'in tana dariya tace.



"Wayyo my sweet three in one kiyi hak'uri banason ganin b'acin ranki".



"Bangane three in one ba, mekenan hakan ke nufi?"inji Khairat.

Murmushi Yasmeen tayi sannan tace.



"One kece marik'iyata kinga you are my mum, two ke my blood sister ce me sona, three se ranar da aka kaini gidan mijina zan fad'amiki"da gudu tamik'e ajikinta tayi waje tana dariya.



Khairat ma dariyar tayi tace.



"Kai yaran zamani ba kunya wai Yasmeen ce ke zancan gidan mijinta Allah yakawomu zamani".



Mik'ewa Hydar Yayi yana sa hularsa yace, "madam keda wannan sister taki se Allah, bansan Wanda yafi wani son wani a cikinkuba" ya fad'i yana dariya.





"Ay gaskiya kam koni bazance ga wanda yafi son waniba a cikinmu, kaje ku tafi karta botsare kasan halinta".



Rakiya taimishi har gurin mota koda driver d'inshi yataso key kawai ya amsa, yace dakanshi zeja motar,tuni Yasmeen ta k'ace a gaban mota,duka Khairat ta kaimata tace.



"Zaki dawo ki samenine nikike cewa gidan mijinki ko?".



Dariya dukansu sukayi Hydar yaja motar suka tafi, Khairat takoma cikin gida zuciyarta cike da farincikin Hydar da Yasmeen yanzu Sun shirya dan batajin dad'in yadda sukewa juna.





Maman Yusuf.

[5/1, 21:31] Zahra Surbajo: 📓📓📓📓📓📓📓📓📓

*CIN AMANA KO FANSA*

📓📓📓📓📓📓📓📓📓





Zahra Muhammad mahmud



*Friends are like fishes, You have to sit patiently for a long time To catch a nice one Just like I caught you*

*Better stay nice or I’ll fry you,Maman Gidado*





*page 45-46*





Tafe suke bamecewa kowa komai Yasmeen se chatting take da friends d'inta hankalinta kwance, shiko Hydar rabi hankalinshi na kanta har suka iso wani ostrich inda zasu sayi ice cream d'in.



Yasmeen da zata sakko a motar seda tayi wani juyi wanda ko waye yagani se ya koka,Hydar Kasa motsawa yayi a inda yake seda tayi gyaran murya sannan ya dawo tunaninsa.



Jerawa sukayi suka shige gurin basu jimaba suka fito me makon taga yayi hanyar gida setaga yayi hanyar millonium park da ita, bata damuba har suka k'arasa gurin ice cream dinta kawai take sha,koda suka isa gurin bece su fitaba Illa adjusting d'in seat d'inshi da yayi itama mik'a hannu yayi yamata adjusting d'in kujerar wanda hakan ya tilastawa jikinsu had'uwa da sauri ya d'auke hannunshi.



jingina yayi da kujerar yana kallon Yasmeen wacce se shan ice cream d'inta takeyi kamar batasan Allah yay ruwanshi agunba,mik'a hannu yayi ya kwace robar ice cream d'in ya rik'e a hannunshi, da sauri ta d'ago tana kallonshi,kwab'e fuska tayi zatayi kuka,tace.



"Haba daddy yazaka kwacemin ice cream inacikin sha ko dama ba ni kasiyamawaba?".



"Naga ice cream d'in yafini muhimmancine shiyasa na amshe domin inason kibani aron hankalinki zamuyi wata magana".



Kallonshi take da idanuwanta masu k'ara sashi fad'awa kogin sonta,tace.



"Daddy I hope ba laifi de naimakaba?"ta fad'i harda wani juya ido.



"Ba laifi kikaminba".ya d'ora da cewa.



"Yasmeen inaso ki fahimceni da kyau karkimin wani kallo na dabam,tunda Allah ya kawoki gidana da zama na fad'a cikin wani yanayi wanda ni kaina tsoronsa nake, na rok'i Allah akan inba alkha'iri bane yacireminshi a raina amman ina kullum kamar k'araminshi ake a zuciyata tsawon shekaru bakwai kenan Yasmeen na kamu da ciwon sonki me tsanani don Allah ki taimakamin".



Wani farincikine ya lullub'e duk wani sassa najikin Yasmeen,harta rasa wacce irin godiya zatayiwa Allah,amman afili zabura tayi tace.



"What!!!,Daddy kana sonafa kace? kamanta yadda muke da Aunty Khairat ne?gaskiya wannan zancan bame yiwuwa bane yakamata kayi tunani ni don Allah karma kasake furta irin wannan maganar,ashe abinda ke ranka kenan yasa kace inzo kasiyamin ice cream?".



Kan Hydar ne yafara d'aukar zafi dama abinda yaguda kenan tun farko shiyasa yak'i bayyanamata,dan yasan bazata aminceba Amman ya ya iya? cigaba yayi da rarrashinta kamar wani yaro yadunga zayyana mata irin son da yake mata,dad'i kamar yakasheta Amman afili se ignoring take.





Daga k'arshe de dataga yana shirin zubda hawayene yasa ta turo baki gaba tace, "to naji kabari zanyi shawara abinda nasamu daga shawarar zansanar dakai".



"Dawa zakiyi shawara Khairat ko Iman?".



"Da zuciyata".



"Don Allah yayin shawarar ki kwatantamin adalci, dakwan soyayya tsawon shekara bakwai it not easy pls".



Bata bashi amsaba haka yagaji ya ja motar suka dawo gida.



Khairat murna kamar anmata albishir da aljannah don murnar Hydar da Yasmeen Sun shirya.



Ranar dukansu suka had'u gurin cin abinci Yasmeen da Hydar se satar kallon juna sukeyi har aka gama cin abincin kowa ya watse.



Yasmeen d'akin Khairat taje tasameta fitowarta daga wanka kenan tana kwalliya Yasmeen tashigo d'akin, Khairat tayi mamakin zuwan nata adede wannan lokacin dan da zaran anyi magrib basa hawa sama ma bare suzo d'akinta.



Tasowa tayi daga gaban mirror ta koma kan godo ta zauna Yasmeen na k'arasawa kan cinyarta ta kwanta tace.



"Am sorry Aunty nazuwa gurinki yanzu,wlh wata friend d'inace take cikin mawuyacin hali tanemi nataimaka mata da shawara yazatayi, to nikuma kinsan bawani wayo ne daniba shine yasa nace ta Bari intambayar mata Aunty na".



Murmushi Khairat tayi tace.



"Allah sarki, shawarar me take nema? Allah yasa na iya bata".



"Wlh Aunty mijin marik'iyartane kesonta kuma ba k'aramin soba tak'i amincewa amman inkinga yadda yake mata magiya ko ke sekin tausaya masa kuma itama tanasonshi,amman ganin mijin marik'iyartane yasa tak'i amincewa wlh dukansu suna cikin wani hali abin a tausaya musu,dan cewa tayi inde tarasashi to ita da aure har abada shine take neman shawara".



Ajiyar zuciya Khairat tayi sannan ta shafo kan Yasmeen tace.



"Wannan ba abin tada hankaline ba inde akwai fahimta ita da marik'iyartata tanasonta tsakani da Allah inaga bazata damuba dan hakan takasance, duba da cewa bazataso taga yarinyar batayi aureba kamar yadda tayi ikirari,inaga ta amince kawai inde marik'iyar nasonta tsakani da Allah bazata hanaba sede zataji zafi amman ba kamar akawo mata bareba wannan shine kawai".





Murmushi Yasmeen tayi bayan ta kashe recording d'in datasa tad'au muryar Khairat sanda take bata amsa sannan tace.



"Wlh bahaushe yayi gaskiya dayace aykin me shawara baya b'aci,da saura kad'an ta guntulawa kanta,wajan hana zuciyarta abinda takeso, Kai wallahi zama da Manya masu zurfin tunani,masu sowa d'an uwansu abinda suke sowa kansu da dad'i mungode Aunty da shawara kuma insha Allahu zan fad'a mata wannan shawarar,mukwana lfy".ta mik'e da gudu tabar d'akin tana dariya.



Khairat itama dariyar tayi aranta tace,

"kai Yasmeen wlh akwai hankali bata abu kai tsaye seta nemi shawara Allah de yay mata zab'i da miji nagari".





Yasmeen ko tunda ta koma d'akinsu inbanda dariya ba abinda takeyi, Iman har haushi taji dan ta d'auka ita takewa dariyar akan ba'a je da ita shan ice cream ba.



WhatsApp Yasmeen tahau tana chatting da k'awayenta cike da farinciki da annashuwa.



muje zuwa readers



Maman Yusuf.

[5/2, 09:17] Zahra Surbajo: 📓📓📓📓📓📓📓📓📓

*CIN AMANA KO FANSA*

📓📓📓📓📓📓📓📓📓





Zahra Muhammad mahmud





*Some People Have Nice Eyes, Some Have a Nice Smile & Some of Them Have a Nice Face But You Have All of Them Including a nice Heart.INNAH IBRAHIM KIME.*





*page 47-48*





Washe gari da safe dukansu sukayi breakfast,a tare Hydar se mamakin irin wani kallo da Yasmeen take watso mishi yake, kallone dake nuna tsantsar soyayya.



Yanason magana da ita Amman ba hali tunda yau weekend ne yana gida kuma tare da Khairat,dan haka fakar idon su yayi ya Kara hannunshi a kunne,Yasmeen na kallonshi alamar tabashi number wayarta.



Ho Yasmeen!!!halinki seke.



Tunda ta fahinceshi ay kawai setayi murmushi ta waiga gurin Khairat tace.



"Aunty don Allah d'an karantomin number na naga kamar kin rik'e, ni wlh ban rik'eba gashi wanine zanturamawa yadameni da tambaya yanzu haka gashi nan online,kuma kinsan number danake whatsApp bada ita nake receiving calls ba".



"Lalle Yasmeen yanzu number nakine baki rik'eba? sannunki da shiririta, niko ko daga bacci kika tasheni zan karantomiki numbar ki danna rik'e"daganan tafara karanto number Hydar yana rubutawa batare da Khairat ta ganeba tana gamawa Yasmeen tace.



"Yeeeeh thanks my sweet three in one,you are perfect that's why you deserve a perfect surprise when the time comes".



Duka Khairat takaimata tace.



"Niko na k'osa naji wannan sabon sunan nawa na ukun, dannasan dole zeyi dad'i tunda my sweet two in one ce tasaminshi".



Fuska Yasmeen ta b'ata tace.



"Kai Aunty don Allah taya zaki cemin two in one? wlh nima three in one ce a gurinki,ranar dazan sanar dake d'ayan sunan naki kema seki zab'i wanda yadace kisamin, amman gaskiya niba two in one bace a gurinki ba".



Sosai Khairat taji dad'in kalaman Yasmeen,rungumeta tayi tace.



"Wlh Sis bansan irin sonda nake mikiba komai naki burgeni yakeyi wlh, Allah de yahad'aki da miji na gari daze rik'eminke amana".



"Aunty na kenan ay wlh nafi sonki,sabida kinga nide yarinyace ko?to wlh bazan tab'a yarda Inga Daddy yashigo da wata bare a matsayin kishiyar muba, dan in yamiki kishiya ni yayiwa dole mutashi mud'au mataki, shiyasa ma Nafad'i a gabansa dagamu bak'ari inde ya amince to muma mun amince".



"Wlh Sis tunda muke baki tab'a farantamin rai irinna yauba,gaskiya nayarda da soyayyarki gareni tunda har bakyason ayimin kishiya gaskiya nagode".



Hydar zan iya cewa kusan suman zaune yayi dan abinna Yasmeen yafi k'arfin tunanin shi,cikin hikima tana magana dashi amman Khairat bata ganeba,se shid'in data.keyi dashi shine yaganen,dank'ari lalle akwai bala'i a gidanshi, sede addu'ar Allah ya yayyafa mishi ruwan sanyi.



gyara murya yayi sannan yace.



"Lalle ma mutanennan wato abin y'ar son kaice?,ina laifinma kuce kun yarda na k'aro wata a wajen bayan ku, Amman seku rik'eni ku kad'ai gaskiya bakuyi adalciba".



Yasmeen turo baki gaba tayi sannan tace.



"wlh muddin bayanmu kana tunanin k'ara wata to wlh kadena danmu aka yika kamar yadda kaima dankai aka yimu, koya kikace Auntyna?"ta waiga tana kallon Khairat wacce ta d'auki zancan Yasmeen a matsayin irin wasan da akeyi tsakanin miji da k'anwar matarsa cike da farinciki tace.



"wannan zance naki gaskiyane my Sister".



"To inde hakane yazama wajibi kudage da nunamin so da k'auna kamar yadda nima nake nuna muku,ma'ana kurik'eni amana inde kukamin haka to Hydar nakune ku kad'ai dan lokaci, yayi da zan shida muku kune zab'ina dana jima ina nema yau gashi kun tabbatarmin da hakan, gaskiya innace banji dad'iba nayi k'arya, nagode sosai wlh Allah yabarmu tare yasa mucinye duk wani k'alubale dazamu fuskanta".





Da sauri Yasmeen tace,"Ameen Ameen".





Oh my God jama'a kuna ina sunmaida Khairat banza.



A gabanta suna musayar magana amman bata ganeba, Dan k'arshema da gudu taje ta rungume Hydar dan ita zatonta da ita yake wannan dad'ad'an maganganu shima rungumeta yayi ya Kalli Yasmeen yace.



"Wannan shine fatana wata rana"yana nuna mata yadda Khairat ta rungumeshi.



Kunyace ta kama Yasmeen da gudu tabar gurin ita da Iman wacce tun d'azu dariya kawai takeyi.



Khairat ranar wani tattalin Hydar takeyi da bashi kulawa jin yace daga ita ba k'ari, itako dama ba abinda ta tsana irin kishiya, Tunda ko yace baze mataba itako bataga abinda bazata iya yimasa ba don ta faranta masa.



Hydar besamu damar kiran Yasmeen ba seda yafita masallaci, bayan an idar da sallah ya tsaya a garden d'in gidan yakirata a waya,bugu biyu ta d'auka cikin muryarta me kwantar da hankali tace.



"Ran hydara na yadad'e,karkayi mamaki, sanin zaka kira shiyasa na kama suna dannasan kaid'inne".



Murmushi Hydar yayi sannan yace.



"Such amazing My heart,d'azu kin rikitani wlh, wai dagaske kin amince dani to be your husband kode wasa kikemin?".



"Bana wasa da abu me muhimmanci kamarka tunda nace na amince I mean it babu wani wasa aciki".



Nande infad'amuku, suka kwashi soyayarsu me dad'in saurare, dan basu denaba seda aka kira sallar la'asar,yakashe yatafi masallaci.



koda yadawo gida Khairat tacemishi meya zaunar dashi, amsa yabata da wa'azi akeyi a masallacin shine yazauna ji se yanzu aka gama.🤣🤣



Kai Hydar, kai tun kafin kayi mata biyun kafara shirgota.



Muje zuwa readers.



Maman Yusuf.

[5/2, 15:18] Zahra Surbajo: 📓📓📓📓📓📓📓📓📓

*CIN AMANA KO FANSA*

📓📓📓📓📓📓📓📓📓



Zahra Muhammad mahmud



*The value of life does not depend on the length of time on this Earth but rather on the amount of love given and shared to the people we care about.am really appreciate the way you care about me Safina Sulaiman(Maman sultan)*



*page 49-50*



Soyayya fa tayi k'arfi tsakanin Hydar da Yasmeen kullum cikin nunawa juna kulawa suke koda kuwa a gaban Khairat ne,sun iya takunsu babu ta yadda zata gane.



Su Yasmeen sun gama makarantar su lafiya ita da Iman, se murna sukeyi Hydar kuwa harda party ya shirya musu,anyi taron tayasu murna lfy gami da musu fatan alkha'iri.



Yau asabar kowa yana gida dayake weekend ne zaune, suke a falo suna kallon casset d'in party da sukayi,Hydar ne yay sallama yashigo daga training ya dawo,da sauri Yasmeen ta mik'e taje taryarsa,suka tsaya a bakin k'ofar,tace.



"Sannu da zuwa me gidan Aunty na dafatan kadawo lfy?".magana take tana juya ido.



"Nadawo lfy Amarya ta, yakike ya Auntynki? dafatan kina kulamin da ita? kinsa itace heart beat d'ina".



Murmushi tayi sannan tace.



"Ka tambayeta kaji kullum ina kulawa da ita sabida sanin muhimmancinta a gurinka dan itama nasan kullum da tunaninka take kwana take tashi, kaide karik'e ta amana kuma ka gaggauta bata mulki na sarauniyar zuciyarka shine zesa tak'ara yadda ita d'in itace heart beat d'in taka".



Khairat ce tak'araso gurinsu tana dariya tace.



"Ikon Allah, wlh shiryawarka da Yasmeen ba k'aramin rana tayimin ba tunda gashi a sanadin hakan kana fallasamin sirrin zuciyarka wanda da baka tab'a fad'aminba, yanzu ne nake sanin matsayina a zuciyarka"dafa Yasmeen tayi sannan taci gaba da cewa.



"Ay wlh kede Sis sede ince Allah ya rabaki da bak'in cikin duniya da lahira Allah ya d'aga darajarki a idon mijin dazaki Aura fiye da duk wata mace afad'in duniya yazamana yana hannunki se yadda kikayi dashi".



Wata shegiyar dariya suka kwashe da ita Hydar da Yasmeen atare suna kallonta itama dariyar takeyi,Yasmeen tace.



"Wai Aunty anya wannan addu'ar batayi tsauri da yawa ba kuwa? kide sassauta dan inason inkin tashi bani sunana na uku agurinki kibani me dad'i amman wannan zazzafar Addu'a haka Aunty, ay seki jamin zagi a idon duniya ace na mallakeshi yazama mijin tace".

Carab Hydar yace.



"Ay ni wlh da za'a kiran mijin kan tacema akan Antynki so zanyi,dan matsayine babba agurina faruwar hakan".



Rungumeshi Khairat tayi sabida jin dad'i,tana jikinshi take ba Yasmeen amsa.



"Addu'a ce me kyau namiki Sis bazaki san amfaninta ba se ranar dakikayi auran, bazakiso ki koma komabaya a gurin mijinki ba dan haka kedai kawai kice ameen".



"Ah to tunda kika ce hakan nasan abune me amfani danhaka ameen ameen Aunty na daddy kai baka tayani cewa ameen d'in ba"ta fad'i tana kallon idonshi.



Murmushi yayi yak'ara rungume Khairat sosai ajikinshi sannan yace.



"Wacce ameen zance anan nida har a Sallah ina fad'awa Allah yabaki Wanda yake sonki kema kuma kike sonshi kuzauna lfy, amman tunda Auntyn kice tayi addu'ar kuma kinsan irinsu addu'ar su na amsuwa nima nace ameen d'in".



Janshi Khairat tayi suka haura sama suka bar Yasmeen da b'acin rai dan ta tsani taga Khairat ta rungumar mata Hydar.



Tofa kuji k'arfin hali don Allah.



Soyayya kullum se abunda yayi gaba koda wasa Khairat bata gano bakin zaranba, ita ta d'auki alak'arsu a matsayin wasan miji da k'anwar matarsa,ko shan ice cream yanzu duk Sunday se sunfita shida Yasmeen, wani time d'in suje da Iman wani lokacin da Khairat, ko su tafi da meema da Arfat dayake sun iya takunsu bawanda yaganosu.



Hydar ne yamatsama Yasmeen akan shifa yanaso tabashi dama yatura gidansu neman auranta,hak'uri tadunga bashi akan yad'an k'ara hak'uri ba yanzuba.



To yaude ko shawartarta beyiba da asubar fari ya kama hanyar kaduna shida drivern sa,yafiso ayita tak'are yagaji da b'oyewar dayakeyi shi ba mak'aryaciba Amman duk yagama zama mak'aryaci a gurin Khairat sabida hakan, shiyasa shi yak'osa ayita ta k'are Tunda yasande d'ayan biyu ne ko nasara ko akasin hakan.

Tafe suke shide se addu'a yake akan Allah yabashi nasara.



Yasmeen yau tun safe takejin gabanta nafad'uwa tarasa dalili addu'a kawai tayi akan Allah yasa alkha'irine,a kitchen suka had'u da Khairat gaisheta tayi ta amsa fuskarta d'auke da walwala.



Yasmeen tace, "Aunty yau ina soulmate d'in naki naga kinsakko da wuri haka?".



Murmushi Khairat tayi sannan tace.

"Wlh yau tun asuba yatafi kaduna shida driver yace ya kwana biyu beje ya gaishesu ba shine yau yatafi gobe ze dawo yace".



Hankalin Yasmeen ne yay mugun tashi tabbas tasan zuwan Hydar kaduna ayau nanufin tayi bankwana da farinciki a rayuwarta, meyasa yatafi be sanar da ita ba?.



Khairat ce ta tab'ota ganin gaba d'aya lokaci guda ta firgice tashiga damuwa,a rud'e ta waigo tana kallon Khairat,tambayarta tayi.



"Lafiya kuwa Yasmeen?meke faruwa haka?daga cewa Hydar yatafi kaduna duk kin tada hankalinki".

K'irk'iro murmushi tayi sannan tace.



"Wlh dama naso nabishine duk lokacin dazeje shine kuma naji yatafi bansaniba shiyasa kikaga nashiga damuwa amman bakomai wlh".



"To kidena damuwa in ze koma wani lokacin sekuje tare kinji my Sis".



Kai ta d'aga mata sannan tafice a kitchen d'in takoma d'akinsu,rasa me zatayi tayi addu'a kawai tashigayi dan tasan halin Ummanta in zancannan yafito zata iya nakasata da duka ita yau yazatayi,?wata zuciyarce tashiga k'arfafa mata guiwa da cewa "ay ba ke kad'aice cikin tashin Hankalin ba Khairat ma tana ciki in har da gaske kina da burin fansa a ranki dole kicire tsaron komai a ranki dan dole sekin daure zuciyarki".



shawara da zuciyarta ta bata itace ta k'ara mata kwarin gwuiwa yazamana memakwan tashiga tashin hankali sema wata natsuwace take shigarta.



Had'a kayanta tayi guri guda tayadda bame ganewa dan tasan zamanta a gidan yakusa zuwa k'arshe data fita ba shiri gwanda ta shirya.



muje zuwa.



Maman Yusuf.

[5/3, 07:49] Zahra Surbajo: 📓📓📓📓📓📓📓📓📓

*CIN AMANA KO FANSA*

📓📓📓📓📓📓📓📓📓



Zahra Muhammad mahmud



*Never say gud bye 2 sum1 who luvs u.Never say thanx to sum1who really needs u.Never blame a person who really trusts u.Never 4get a person who think u as LIFE,Juwairiyyatu(Anty Arfat)*



*page 51-52*



Hydar ya isa Kaduna lafiya kai tsaye gidan iyayensa yanufa.



Sunyi murna sosai da ganinsa dan ba k'aramin so suke masa ba kasancewarshi shikad'ai Allah yabasu,shiyasa suke tattalinsa, kuma koba dan hakaba Hydar mutumne dayasan daraja da girma na iyayensa dole ko zuciya taso me kyautata mata.



Part d'inshi nagidan yasauka, bayan yayi wanka ya kintsa fitowa yayi yanufi b'angaren iyayennasa, gaishesu yasake yi sannan yace.



"Alhaji dama akwai wata magana data kawoni inaso kufahinceni kunsan bazan tab'a yin abinda yasab'awa addini ba,shiyasa wannan ma inaso ku d'aukeshi a matsayin k'addarata ce tazo a haka".



Natsuwa sukayi suna sauraraonsa dan sun fahimci zancannasa me muhimmancine,cigaba yayi da cewa.



"Bakomai bane dama illah inason Yasmeen k'anwar Khairat kuma inaso kashigemin gaba gurin neman auranta".



"Innalillahi wainna ilaihirrajiun, Hydar kanka d'aya kuwa?,kasan abinda kake furtawa kuwa?,so kake kazama abokin shaid'an wajan tarwatsa zumunci?ina katab'a ganin haka?to wlh tuntuni inma bacci kake ka farka,wannan zancan bame yiwuwa bane",inji Hajiya wacce ke magana cikin fushi.





"Ah Hydar naji duk bayaninka kuma nagamsu dashi tunda nasan a addinancema ba laifi bane,sede Hydar iyayen yaran bazasu aminta subaka aurannanba dan ze tab'a zumuncinsu,kuma in akayi hakan kamar da cutarwa aciki, duba da ganin Khairat itace ta rik'e yarinyar harta girma,bawai nace bazan maka jagora bane aa kod'aya shawarace zanbaka inda hali ka hak'ura da wannan maganar kaji",Alhaji ya fad'a cikin sigar rarrashi.



Afusace Hajiya ta amshi zancan.

"Au lalle ma Alhaji koda yake ay duk sunanku maza,amman taya zaka goyawa yaro baya akan abinda kasan badede bane? tonide wlh ba hannuna aciki, dan bazan goyi bayan cin amana ba".tana gama magana tabar gurin tana huci.



Hawayene suka zub'o a fuskar Hydar na rashin kwarin guiwa, Mahaifiyarsa ma bata goyi bayansaba bayajin iyayen Su Yasmeen zasu amince subashi auranta,Alhaji ne ya katse masa tunani tahanyar dafashi yace.



"Haba Aliyu Hydar zakin fama namijin mazaje,karka bani kunya mana, taya akan wannan maganar zaka tada hankalinka?katunafa yak'i kad'auko bedace tundaga farko kanuna ka gazaba, dole seka nuna juriya da jarumta kuma dama su mata haka suke, sekaga abu al-adace kawai amman sesu fifitashi fiye da addini kuma kosu gidan yaran inaga ko za'a samu matsala to daga matanne,kaide kadage da addu'a yanzu katashi kaje da kanka kafara yi musu maganar in yaso yadda kukayi dasu zuwa gobe semuje tare".



Maganganun Alhaji sune suka k'ara masa kwarin guiwa, godiya yayi masa sosai sannan ya fita yanufi gidan iyayansu Khairat.



Da isarsa k'ofar Gidan Abban Khairat yasamu ya fito daga gida zashi masallaci, da sauri yafito a motor ya nufeshi, shima Abban ganin

Please Login or Register in order to submit comment