Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke fad'in haka tare da Jan hannun Abbansa.

Biye mishi yayi suka doshi wurin da kukan kefita, bakinsu d'auke d addu'a,, ganin haka ita hajia Aisha tabisu.

Tafiyan 'yan secns suka isa inda kukan kefitowa.

Cikin wani d'an rami dake gefen titin kukan yake

Bissimillah Alhaji Ibrahim yayi, yad'auko babyn, saida yatsaya yayi addu'a mai tsayi sannan suka dawo, chikin motarsu.
Chikin gaggawa sukabar wurin.

Hajia Aisha ta k'urawa babyn Ido, tanajin tausayinta na ratsata,, shima Alhaji Ibrahim tausayin babyn yakamashi sosai.

Har zuwa lokacin kuka takeyi, muryanta har ya dushe.

Tagumi Deen yayi, cikin jimami
"yace mamie kubata nono tasha, kozatabar kukan.
Da kallo suka bishi zuciyarsu yana bugawa!!

Shirun nasu yayi yawa, yamike.

Yad'auko madara yace to kubata wannan tunda nonon mamie baruwa
" ko Abba? Yana kallon Abban nasa, kai ya gyada mishi yace.

"Mamie bata mana ga ruwan zafi na debo

"Deen natsu, kaji" qanwartaka wannan madaran tayi mata k'arfi,
" to miza' abata tabar kukan?

Rikemin ita kagani
Ruwa mai zafi ta d'ebo tayi mata wanka, zuwa lokacin tabar kuka sai ajiyar zuciya.

Kayan jikinta ta mayar mata da shi.

Kayane masu k'yau tsada, hannunta har da azurfa. Kunnenta d'ankunen zinare ne,, showel d'in da aka nad'eta ma abin kallone.

Mamie ta kakkabe showel din domin sakata, sai gawata takarda ta fad'o,, Abba ne yad'auka yasoma karantawa kamar haka:::

*Dukwanda ya tsinceta,to yatafi da ita,Allah ne yabashi. Kuma abar yankinnan da ita,saboda wa'yan da sukasa, ad'auketa,kasheta sukeso ayi!!. Amma Nina satota tun kafin su kasheta, kuma insunsan tana raye, to tabbas zasu nemota su rabata da duniyar baki d'aya,, 'yar halasce gaba da baya, ina rok'on Allah yasa tafad'a hannu nagari Ameen*
*kuyimata hud'uba, Inda hali nan da kwana uku ayimata hakika,,"" Allah yatayaku ruqo Amin bissalam*

Tsit sukay, suna jinjinawa rashin imani na wasu mutanen.

Nayi alk'awarin zamemata uwa ta gari, bazan bari kisan asalinkiba, sai bisa larura" balle mugaye su samu nasaran kashemin ke.
Hajia Aisha kefad'in haka cikin zubar hawaye.

Tana rufe baki Alhaji Ibrahim ya amshe""
Nima zanzame mata uba abin alfahari.

Deen dake rungume d ita, yace nima nazama yayanta
Ina sonta mamie

Murmushi iyayen sukayi, suna jinjina wayau irin na Deen

Shekaransa 9 lokacin.

Washe gari sukabar Maiduguri, tun da subahi,, ko mutane masu zuwa musu sallama, sai dai suka sami sak'on wucewarsu a bakin mai gadin gidan.

Ranarda tacika sati a duniya sukayi mata hakika tare da sa mata suna *Nana Safiyya*

Bahijja tazo, lokacin tana d'auke da k'aramin chiki d'an wata biyu.
Ita kad'ai mamie tafad'awa ainihin yadda suka sameta, kuma tagargad'esu da kada Wanda sukafad'awa tsintarta sukayi.

Tasamusu son Safiyya aransu, Wanda har suna mancewa itadin ba jininsu bace.

Sun shak'u da Deen sosai

Shike wanke mata kashi in mamie na aiki har goyo ya iya, yana bata kulawa matuk'a.

Sanda yagama secondary Abba yaturashi karatun law Germany, lokacin Safiyya nada 7yrs

Sunsha kukan rabuwa
Wanda daky'ar akasamu tadawo cikin walwalanta.

Shekaransa 10 yadawo gabad'aya, sabod tunda yatafi baizo ganin gidaba saidai su Abba suje ganinshi

Lil sis d'insa kuwa saidai suyi waya ko taga pic d'insa awayar mamie ko Abba, badon hakaba, da baza ta ganeshiba.

Sanda yayi arba da ita yasha mamakin girmanta.

Yayi ta tambayar mamie meta bata tayi tsawo haka, don itaba mai k'iba bace kuma baza' akirata siririya ba.

Ba abinda yak'ara firgitashi da ita sai chikan halittan da Allah yayi mata, sosai tajefa zuciyarsa chikin rud'ani.

Ita agefenta tayi mamakin k'yau da tsari irin nashi

Nandanan suka saba, tayi tayawo da shi gidan yan uwan mamie da k'awarta jameelah.

Yadawo da yan watanni, yasoma aiki a kotu.

Ita kuma Safiyya ta wuce school of nursing.

Yanxu haka tana watanta biyar da kammala karatunta.

Dama tayi saukan ALQUR'ANI tanagama primary, tayi hadda tare da wasu littafan ilimi.

Duk ranakun asabar, lahadi, da littinin take xuwa makarantar addarsu ta koyar, haka takan lek'a islamiyar su.

Ahanyarta na zuwa makarantar addarsu tahad'u da uztax d'inta, wanda yace sai yaga abinda ya turewa buzu nad'i.

Agefe d'aya kuma barr Deen yana azabtuwa d begenta, mamie tace kul! Kar ya sake yafurta, saboda zai zama fallasa abubda suka jima da binnewa, wanda sam bata buk'atar hakan ta faru. Yayi yayi tace a' a, bazai taba yuwa ba, A tunaninta zai zama sanadin rabuwarta da Safiyyah.

Atunaninta intasan asalinta zata gudu neman iyayenta kuma inhar tatafi mutanen da suka so kasheta tuntana jaririya zasu ganta

Duk tsawon lokacinnan mamie batak'ara yadda sunbi hanyar da suka tsincetaba duk da angyara hanyar, ansami sauye sauye. Bata barinta fita ita d'aya kuma basa dad'ewa a garin koda sunje.
Sosai take kaffa- kaffa da ita, Tana ji da ita sosai.





*dawowa labari*


*Mrs j moo*
[4/8, 4:53 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA* 🤔
*7 to 8*
*®Safiyya*

*Godiata agareki bazai taba k'arewaba bebeelo'' Allah yasakamiki d Alkhairi,, Allah yak'ara miki lafia Alfarmar Annabin rahama SAW Amin*


Tana tsaye tana addu'ar shiga barci, taji wayarta na naiman agajin adauketa,, bata kulaba hat saida tagamaga addua'ar tashafe jikinta d shi,, zuwa lokacin ankira sau uku,, dafda zai tsinke ta dauka tare d sallama, duk d batasan number ba

"Barka d dare abincin ruhina'' tayi jim tana tunanin aina tasam voice dinnan" hlo kina jina kuwa? Uhm barka kadai,, waye don Allah''
Daria akayi mai sauti,, Saifullah ne ko ince Ustaz" dafatan kin gane mai kiran naki''

Jin batai k'ara maganaba,, yace nabarki cikin amincin Allah
Allah yatashemu lafia, sannan ina addua Allah yasa kiganni cikin mufarkinki muna hiran k'auna.

Bai jira cewarta ba yakatse kiran yana mai farin cikin jin muryanta.

Sororo tayi baki bude, xuwa can tasaki murmushi,, tanajin wani abu cikin ranta.

Adduar tak'ara sabuntawa, sannan ta hau bisa bed ta ja bargo ta rufe k'afafunta zuwa k'ugunta.


6:30am
Zaune take bisa sallaya, tana lazimin safe,, tana shafa addu'a wayarta ta dau ringing
Ustaz d'ina,, sunar dake yawo bisa screen d'in kenan,, jim tayi tana kallon sunar" jia tayi save d'in sunar bayan sungama waya"

Tadaure ta d'auka"

Aminchin Allah ya tabbata agareki ya hasken ruhina'' mgnr data doki dodon kunnenta kenan,, saida taja ajiar zuciya sannan ta amsa" tare dakai ya ustaz,, yasa daria itama murmushi tayi mai sauti

Can k'asa k'asa taji yace nabarki lapia,, komaki barchin sunna domin samun falalar d ke chikin varci a,irin wannan lokacin" kit ya katse kiran, batare d yak'arajin maganar taba.

Wayar tabi d kallo tana jin wani farin chiki a ranta.

Voice dinsa namata dadi sosai, tun farkon had'uwarsu,, muryansa nadaga chikin abinda ke burgeta, sai kuma gayunshi, d kuma yawan nutsuwarshi, gemunsa ne kawai kebata haushi d shi d yawan kallonsa, domin tatsani ayi ta kallonta kamar tv.

Ahankali ta furta zanyi manage dakai hakanan *ustax d'ina* domin inajin kamar INA sonka a ruhina.

Saikuma tasa daria,tasa hannu ta kulle eyes d'inta wai taji kunya.


A kitchen******
Ita d mamie sai aikin break fast sukeyi, chinkin k'warewa.

Mamie ta dubeta, taga sai doka murmushi takeyi ita 1,, yarinyar mamie wani albushir kike daukemin dashi?

Cikin rashin fahimta ta kallo mamie n tace" mikigani mamie? Komima na gani babyna,,, miye sakaki chikin nushad'i d sanyin safian nan? Uhmm uhmm mamie ustaz ne " saida tafada sai kuma takama baki tana zare idanu, alokaci daya kuma tafice dga kitchen din d gudu.

Daria sosai tabawa mamie,, ja'ira mara kunyar qarya.

Saikuma ta d'aga hannu tana mai cewa' Ya Allah kasa abokin rayuwarta na har abada ne kuma Allah yasa yazamo nagarine, Amin.

9:00pm
Abba
Mamie
Barr.Deen
Sophy
Suna zaune bisa dinning, bakajin matsin komi sai k'aran spoons,, mamie tadage sai turawa sophy food,, ita kuma sai shagwaba take zubawa,, Abba nayi musu daria,, barr.yawani hade rai,, sophy ta dubeshi taji wani irinn faduwar gaba,, ta ja innalillahi chikin ranta

Zama tagyara cikin son tsokana tace ya Deen hala daren jia auntyna ta kunno kane kake shanmana k'amshi tare d chin magani,, bai kulataba,, ta matsa ta kamo hannunsa, tamarai raice, hava ya Deen miye haka, komi yayi zafi mgninsa Allah

Ya k'ura mata Ido, batare d yace komiba ya zare hannunsa cikin nata.

Zuwa lokacin idanunta, ya ciko d kwalla, d kallo mamie" mamie n ta girgiza mata kai,, ta ja hanci d sauri tamik'e tabar wurin ta haye sama.

Mamie ta dalla mishi harara,,vya kauda kanshi

Abba ya dubeshi chin kulawa, yace mi yahadaku d k'anwar taka? Kamar baison mgn ya amsa bakomi Abba, to mike damunka? Nanma amsar 1 ce bakomi,,
Ganin yaki bad'amishi damuwarsa, sai yasoma yimasa nasiha akan yayi hkr d rayuwa,, sosai ya nusar dashi lamura na zaman dunia.

Mamie barinmusu wurin tayi don jin haushin antaba 'yar lelenta.

Koda tashiga dakinta, kuka tasa mai taba zuciya

A iya tunaninta bata tunano komiba wanda zaisa barr.yayi mata wulak'anci don kawai tadamu d lamuranshi batason ganisa cikin damuwa.

Tana cikin haka mamie ta shigo,, fada tasoma yimata, na akanmi zatayi kuka" kinsan Allah kifita idanuna d saurin kukannan kamar wata ita ciyar baure.

Jin mamie ta kwatantata d baure yasa tasa daria ga hawaye na zuba, mamie ta rungumeta tana Shafa bayanta,, sundade ahaka sannan mamie ta saketa, tafice.

Itama barci ne yazo mata, ta bi lfiar Kati fa,, bata jimaba sarkin data ya sacewa zuwa birnin kebbi garin fish, cikin fish dinsu harda masu bada hikayar soyayya hhh lol.


K'amshinsa ne yatasheta a barci.

Tana bude Ido kuwa tayi arba dashi zaune gabanta yana danne danne a wayatshi

Tura baki tayi, tace miyasa kashigomin daki? Wani mugun kallo ya dannamata, bashiri ta kauda kai

Mgnrsa taji nacewa oya tashi kiahirya kirakani unguwa,, yamik'e,, kisameni a falo, kuma banson ki shanyani,, yasakai yafice yana wani haderai.

Cikin jin haushin sababbin dabi'un d yatsiro mata dashi, tamik'e. Tafada toilet

Sosai taci kwalliya chikin doguwar rigar shadda marun colour ta ja daurin dankwali,, sosai tayi kyau, sai k'amshi ketashi ajikinta.

Falo n tayiwa tsinke

K'amshinta yayi musu sallama" mamie ce zaune tare d qanwarta, yarinyar baffanta.

Cikin far in ciki mamie tasoma jijjigakai alamun wankar nata ya burgeta,, ko kefa babyna" kinyi wasai abiki, d sarsarfa ta iso tafada jikin mamie, ta rungumeta tanayimata rad'a cikin jin kunya ta zame,,

Sai lokacin ta lura d bakuwar mamie,, ina yini umma? Ta amsa cikin fara,a " lpylau Safiyya.

Kinyi kyau,, " cewar umman,,tadubi mamie inaga Sadiq zaishigo neman iri kam" caraf ackin kunnen barr. Dam!!! k'rjinsa ya bada sauti

A,a hajia Amina, wannan kayan ustax ne,, daren jia yasata nushadi,, daria umman tasa tace hajia Aisha baki da dama, yanxu idanu kikasama 'yartaki? Murmushi mamie tayi tanacewa bawani sa Ido ko *Matar ustaz* tace haka tana duban safiyya,, idanu ta kulle tana murmushi k'asa k'ada.

Sallama yayi, suka amsa,, yagaida umma sannan yadubi mamie" sai mundawo mamie,, kudawo lpy,, kada kudade, kasan zata makatanta dala'asar" tam mamie zamudawo d wuri Ai,, aha agaidamin d baffan " zaiji.

Daganan sukafice,, tanama su ummie bye bye.

Sunyi tapia mai nisa natare d yace d ita komiba,,
K'amshinta yacika mishi hanci,, zuwacan ya dubeta,
Kibar sa gyle k'arami, sbd gudun fadawar wasu masu raunin sha'awa cikin halaka,, idanu waje take dubansa,, wato nazamo shadan kenan ko barr? Oho miki komadai miye ki kiyaye,, uhmm tace kawai sbd tagama zuwa wuya d zancenshi.

To mikedamun y Deen dake jifanta d kalmomi masu tunzura zuciya,, uhmm saikace ba lil sis dinsa wanda keso d kaunaba.

Tayi lamo tanata sak'awa ta warwarewa

Fito muyi musu tsaraba,," yace d ita bayan yagyara parking awani super market.

Bayansa tabiyo, sosai suka zamo abin kallo acikin super market d'in

Sanye yake cikin shadda milk yaci hula, sajennan nasa d Dan gemunnan yasha gyara.

Basu jimaba suka fito

Hy my hasken ruhina" ita kalmar d yadoki kunnenta,, kallonsa take cikin fara'a,, ustax kenan.

Yak'araso wurinsu, ya mik'awa barr hannu bai amsaba yadai d'aga mishi nasa hannun, tare d cewa barkanka.

Ustaz d'ina ya xafin rana? Baisamu damar amsa mataba, barr ya figo hannunta yasa ckin mota, ya lek'o kasameta agida, nan bawuri shiririta bane, yaja motar yafice d gudu.

Dan tsalle ustaz yayi najin dadi ya mai maita *ustaz d'ina* wawwww so xuma sunar.

Yajuya gida batare d ya yi abinda yakawoshi ba duk murna yacikashi.







*Mrs j moon*
[4/8, 4:53 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*
® *Na Safiyya*

*Nasara tana ga Allah, komi mai k'arshene amma banda ikon Allah, da sannu lafia zai dore miki,,, BEBEELO"" da yaddan Allah SWA*

*9 to 10*


*Waye ustaz?*

Ambassador Ja,afar Salis Sharif,, shine mahaifin Saifullah(ustaz)

Haifaffen garin maiduguri.

Shi daya tillo Ammin sa tahaifa.

Amminsa kanurice yayin da Abbinsa shuwa,
Shiyasa yake d kyau sosai, kyawunnasa yakuma hadu d gyara.

Da girmanshi Abbinsa yak'aro aure, yanyi ta tashin hankali kafin auren d Ammi,, and cewa tayi baxa ayi mata kishiyba ita yaronta bazai zauna d yan uba ba

Barinma dataji Armaryan danginsa ce,, hankalinta yak'ra tashi.

Lokacin saifullah na dan shekara 8

Abbi ya jajirce yace sai da yayi,, yayi mata barazanar'' sai dai inzata fice ga hanyanan abude take, yagaji da tashin hankali.

Jin haka yasa Ammi saduda don tana matuk'ar son mijinta,, batason kowa ya rabeshi hatta d danginshi amma ita tanason nata suzo, sumadin sai wanda suke daki daya.

Cikin ikon Allah akayi auren Abba d Hajia Sadiyya.

Mace mai karamchi d tarin ilimi, zamani d na addini,, sosai suke shiri d saifullah, dukda hudubar d uwarsa ke mishi akan yarik'a yiwa Amaryan Abbanshi rashin kunya amma yak'i dauka,, tayi tayi tarabasu takasa,, dole k'anwar nak'i,, yasa tabar saifullah d mum" sunar dake kiran Amaryan dashi kenan.

Yayi karatunsa na primary a naija, dganan aka turashi Cairo dora har zuwa master d'insa.

Afannin kasuwanchi yayi karatunsa,, sbd haka sanda yadawo Abbinsa yace yazaba daya dga chikin company ninsa dazai rik'e

Yazabi garin Kd,, amatsayin zai zo na'yan watanni, yakoma, amma yazo d sati biyu yahadu d hasken ruhinsa,,, Nana safiyya

Yace bai komawa sai yaga abinda yaturewa buzu dad'i.

Yana zaune a gidan yayan Amminsa ne,
Alhaji Adam.
Layi biyu ke
tsakaninsu d gidan Su Safiyya.



********* Barr.gudu yakeyi sosai,, go slow yasashi tsagaita gudunsa.

Safiyya duk ta tsorata d yanayinshi,, tunda suka baro super market din bawanda yayi magana chikinsu.

Sosai akahada go slow, yakashe motar, suka zauna zaman jira.

Sophy ta kwana sosai a site d'in ta lumshe idanu, kamar mai barchi

Tana ta sak'e sak'e cikin zuciyarta. Sosai takejin haushin abinda barr.yayi mata, iya tunaninta tarasa gano mike damunshi. Yake daddaure mata haka.

Tagefen Ido yake dubanta,, sosai tayi mishi kyau, yasaki murmushi yana duban hanya.

Ganin tayi lamo kamar mai barchi yabashi damar kallacheta tsaf batare d sanintaba.

Sanda suka sami hanya,, ya firza motar d gudu,, ta farka a firgice tana fad'in ya salam!! Dai dai sunshigo kwanar d zai sadasu d unguwar su Baffa,, yak'ara taka buki d k'arfi,, tazabura ta k'am k'ameshi bakinta d'auke d sunar Allah.

Sai suka tsaya bakin get din gidan sannan tasakeshi,, ya dallah mata harara,, ta kauda fuska batare d tamaida mishi d martaniba,, sbd yanxu tsoro kebata, mutum kamar shafan junnu.

Atare suka jera zuwa chikin gidan.

Iyalan gidan dukkansu suna zaune afalon Baffa sunata hira wasu na kallo yayin dawasu ke danne danne awayarsu.

Gdn cike yake d 'ya'ya d jikoki,, domin Allah yawadata Baffa d zuri,a masu dama.

Anyi murnan ganinsu, sukayi ta gaisawa d mutane,,

Baffa yayi tasamusu Albarka,, suna amsawa d Amin.

Agdn suka gabatar d sallar azuhur.

Misalin 3:00pm
Suka yi sallama dasu.

Yana zaune abisa mota, yana jiran fitowarta su wuce,, ya hangota tafe chikin yauk'innan nata, k'irjinta yadauki hankalinsa

Tana tsakiyar 'yammatan gidan sa,anninta,, su hudu itace cikon na biyar dinsu.

Baimasan sun k'arasoba saijin maganarsu yayi
" ya Deen Allah saukeku lafia,, Amin ya amsa,,suka dawo gefen Sophy, sis munanan zuwa wani satin kigaidamana d mamie, zataji insha Allah, sai kunxo.

Yafice tana d'agamasu hannu.

Sunsoma tafia, ta kai hannu ta kunna k'ira'ar AL-QUR'AN cikin muryan Abdul Rahman Ahmad bin Sudex.

Ta lumshe idanunta tana bin karatun chikin k'warewa.

Take tanemin wani malolo d yatokare mata zuciya tarasa.
Sai murmushi take dokawa tana jijjiga kawai.

Lokaci lokaci barr na kallonta, shima yana murmushi don sosai yakejin sanyi naratsa ruhinsa.

Ahaka suka iso gida.

Tafada jikin mamie, washh!! Mamie na, duk nagaji, don haka bazan lek'a makarantar nanba,, hutawa zanyi yau.

Mamie na Shafa kanta, ta amsa,to yarinyar mamie ki huta jiki d jini Ai, amma ki kira malaman kifada musu, kada suyi tajiranki badu gankiba,, to mamie zankirasu. Allah yayi Albarka" Amin.


Bayan kwana biyu d yammaci,,
Suna tare d Jamee,, Sophy nabata lbrn ustax d'inta, sai daria take mata.

Suna cikin haka wayarta tayik'a,, tana murmushi ta dubi Jamee '' uhmm hala ustaz ne? Kai ta gyada tana daria k'asa k'asa.

Hy my honey ustaz" abinda tafada kenan sadda ta d'aga,, tuni hira ya balle cikin shak'in so d k'auna.

Jamee ta saki baki tana kallonta

Tana mamakin wannan shak'uwa nasu,, du du basufi sati d soma mgnr arzikiba amma inkajisu suna waya d juna tamkar sun shekara.

Duka ta taskawa Jamee bayan gama wayarta.
Tunanin mikikeyi haka bestty? Tunanin masoyuna " ta amsa mata.

Waww bestty waye mai sa,arnan haka?
Tadan batarai sannan ta amsa da " baisan inayiba, hasalima a k'anwa yadaukeni, baimin duban komi bace haka.

Jikin jimami Sophy tace wage shi? Besty!! sharekawai'no bazan shareba sai kinfadamin kowaye

Zanfad'amiki amma not now" Allah sai kinfad'a kinji narantse,, to innafad'a zaki temakeni insameshi? Eh zanyi indai nasan inda yake.

Bakowa bane nake makuk'ar axabtuwa d so d k'aunar shiba illah *ya Deen*
Idanu waje Sophy ke kallon Jamee,, ganin tazuba mata ido yasa ta daidaita
Bugun d zuciuarta keyi,, Wanda tarasa miyakawo shi.

Muryanta na rawa tasoma magana....






*Mrs j moon*
[4/11, 5:28 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*11 to 12*
© *Safiyya*

*page d'n naka ne new babynmu,, Allah yarayaka, yayi Albarka arayuwarka Amin. Allah ya qaramiki lpiar shayar dashi sweet Jamee*


"Besty zantaimakeki insha Allahu, ya Deen zaisoki kamar yadda kike sonshi.
Saidai ina cikin rud'ani, bansan taya zanfara yimishi maganarba.

Idanu kawai jamee ta zuba mata tana kallon yadda jikinta ke rawa, tana gwama numfashi

"Kamar ya besty bakisan taya zaki fad'a mishi ba?
Alhalin nasan kedin ta dabance agareshi.
"Uhmm besty kenan, adaba' yanxu Barr ya canzamin sosai,
kodayaushe cikin hade fuska yake, keni yanzuma tsoronsa nakeji, yakomamin wani damisa mai ban tsoro, kuma ni 1 kemawa haka, don shidasu Abba lapialau.

Amma dazaran sun bar wurin to zai yi fuskan shanu, mutum kamar mai almatsutsai bisa kai.

D'an dariya Jamee tasa, sannan tace topa! Besty yaushe hakan yafaru ban saniba?
Baifi 2wks ba da somamin atattalan junnu.

Koba junnuba, ta doki kafad'anta.

"Nidai besty ki taimakeni, insami abinchin ruhina ta fad'a tareda rike hannuwanta gam

Murmushi ta mata,
" kada kidamu zan yi k'ok'ari kisami cikar burinki,da yardar Allah
" nagode tace tareda rungumeta.

Basu jimaba suka bar wurin.

Bakin get tarakata, tana jaddamata, gobe tashirya akan lokaci, zuwa hadda,

" kada kidamu tace zan shirya, bazan batamana lokaci ba insha'Allahu.

" Ok sai munhad'un.

Ta juya kenan domin
komawa ciki,
Horn din Barr taji zai shigo, yasa taja ta tsaya jiran shigowarsa, tafara gwada sa'arta tun yanxu.

Yana fitowa ta k'arasa wurinsa.

"Sannu da dawowa ya Deen,
ya office?

Cikin sakin fuska ya amsa "yawwa Alhamdulillah

Ta amsa ledar hannunsa,, yayi gaba tabi bayansa, har d'akinsa ta kaimishi ledar, tasamu wuri tazauna.

Shikuma yana shiga ya ajiye phone d'insa tare d key, ya fad'a toilet.

Tananan zaune yafito d'aure d towel a k'ugunshi yana goge sumarsa d k'aramin towel

Yaji mamakin ganinta zaune,, ya tako gabanta ya tsaya, yana dubanta, fuskanshi ba yabo ba fallasa.

"Ya akayi?
"Wani Abu kikeso?
Ta sunkuyar d kai gabanta nafad'i, sabida ganinshi haka.
Sumar k'irjinsa sun kwanta lup lup, azuciyarta tace Barr nada k'yau sosai, in besty tasameshi tagama morewa kam, a fili kuwa d'an wani guntun murmushi ta sake, wanda Barr ya kasa gane na meye.

"Uhmm ina saurarenki...
ya katse mata tunani, cikin sark'ewar murya
" tace dama.. dama.. inaso inbaka hak'urine akan laifin danayi maka, kake shareni d yimun fushi.

Ta canja maganar d tazo yi masa kuma, tarasa dalilin ta na kasa fuskantanshi d zancen, alhali yau taganshi cikin salama.

Murmushi yayi mai sauti,
"yace nibakimin komiba lil sis, kawai yanxu banason takura ne.
k'irji ta dafe tana kallon shi cike da mamaki sanan ta furta
" nike takuraka kenan?
Yayi mata shiru...
Bata rai tayi lokaci d'aya kuma ta d'an sake murmushi wanda ya k'ara jan hankalin shi,a shagwabe tace
" ya Deen to kayi hkr zankiyaye bacinran naka.

sai da yad'auki 'yan dak'ik'u sannan ya durk'usa gefenta

" lil sis wani Abu nake nema, kuma mamie tak'i bani goyon baya akai.
To kafad'awa Abba mana,
"Aa;
Ya furta
" banason yasani har sai mamie ta Amince.

"Uhmm to wai miye wannan abin ne?

"Hajace mai daraja d tsada,ya fad'a yana dalla mata kallon canko mana....

Murmushi tayi itakam sanan ta dube shi tace
"aw kace akan kasuwanci ne, aiko dole sai dai mamie tashiga lamarin,, kayita lallabata har ta amince maka, ai nasan tunda wanan ne yazo da sauki

Sororo yayi yana kallonta,a ranshi ya furta'wanan anyi subulluwa.A fili kuwa cha yayi "amma dai lil sis ke wata mashirmanciya ce, dagajin ance haja sai kikawo zancen bussiness tsuttt!!!
Yaja tsuka yana hararanta.

"Nice ke shirmen barr?
ta fad'a tana mai mashi kallon rashin jin dadin kalamin shi
" Eh kinma fi shirme har d dolanci ma. Zuwa lokacin, zuciyarta yazo wuya batak'ara maganaba,
Tamik'e tafice cikin fushi, har d buga mishi door d k'arfi

Daria yasa mai sauti, yana sosa sumar kanshi.

"Lil sis rigima, zanfice lamarinki tunda naga mamie tana adawa d buk'ata ta, Zan ci gaba d d'aukanki k'anwata na jini. Daganan
Ya fice zuwa masallaci. Yana addu,ar Allah yasa ya iya kauda kai akanta, yakuma barjin kishinta.

Amma yasan abin d kamar wuya.






*Mrs j moon*
[4/12, 8:32 AM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*
*13 to 14*
© *Safiyya*

*masoyana inaji daku aduk inda kuke,, inayimuku godia d k'aunar ku akan novel d'ina, Allah yabarmu tare cikin aminchi" AUNTY KHADY har dake chikin masoyana,, Sophy na godia sosai* *Allah yacika miki burinki, addu'armu tayi ta tafiya kamar ruwa"Amin*👏🏻

Koda Sophy ta fice daga d'akin barr, bed room d'in mamie tashiga, ta haye bisa bed, ta k'udun dune cikin bargo.

Tana jin sadda mamie tafito toilet.
Har ta idar d sallah bata motsaba.

Sai tufka d warwara takeyi cikin ranta.

Sosai takejin bestynta ta had'ata d aiki.
Agefe d'aya kuma yawan fad'uwar da gabanta keyi, ya jefata cikin rud'ani,, shin mike damunta akan barr,, uwa d'aya uba 1 amma sai shaid'an yarik'a raya mata wasu abubuwa masu wuyar fassaruwa.

Zuwa yanxu tagano bata son jin wata na son barr

Wayyo raina,, Allah yashiryaki zuciata d barrin dauko abinda bazai taba yuwuwaba.

Tabbas zan jajirce besty tasami barr.

Don da ita yadace sosai.
Afili taja gajeran tsuka.

Mamie dake bisa sallaya tana lazimi,, tayi saurin duban inda tsukan yafito.

Tacika da mamaki, ganin Safiyya kwance bisa bed d'inta.

Saida ta shafa addu'arta sannan ta iso gefen gadon,, cikin kulawa ta janye bargon d tarufa.

Bakya d lafia ne? Eh mame,, inajin marata tanamin ciwo d cinyata ta dama.
Ayya sannu.
Tashi ki wanka sai Deen ya amso miki mgni, don nasan mp ne zai wahalarmin d ke.

Batace komiba ta mik'e zuwa d'akinta.

Sosai taji ciwon maran d cinyar na k'aruwa,, duk da ita k'arya tayiwa mamie kawai don tasan inta rutsata d tambaya bata d amsar d zatabata.

Yana shiga toilet taga d'igon jini, ta gyara jikinta,, ita kam Sam ta manta date d'inta yayi.

A dinning ta samesu, suna jiranta.

Bisimillah kowa yayi sannan suka soma cin abincin.

Bata wani ci ba, abin kirkiba ta koma parlour.

tazauna dafe d Maran ta, xuwa lokacin har idanunta sunyi ja.

Subbahanallahi!!! Deen yi hanzari kasamo

Please Login or Register in order to submit comment