Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"duk naji kuma na gamsu amma beasty ba,anan gizo ke sak'arba,
abinda ke jefani cikin rud'ani shine rashin tarbiyyan yaya jameel sabida kwata kwata baida nutsuwa, rawarkai yayi mishi yawa.

"Au kinma san Wanda za'ahad'akun Ashe? "Eh nasamshi d'an wan Abba ne daya dawo daga turai karatu, watanni biyu dasuka wuce.

Kai ta jinjiga tace "to saiki k'ulla d'amaran cin maganin zama dashi tunda kin san wayeshi kuma kintabbatar da rabuwaku sai ikon Allah.

Muryanta narawa ta ce "beasty baza kigane abinda nake tsoroba amma bari kiji salon iskancinsa k'ila kyatayani jajircewa wurin k'in aurensa.

Sophy ta xuba mata idanu tana saurarenta.





*Mrs j moon*
[4/16, 4:04 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*23 to 24*

*©Safiyya*

*Dedicated to Hajiya Juwairiyyah Muhammad Aliyu DDY, Allah ya albarkaci zuri'arki Amin*
*Ina Alfahari da ke hajiya ta*😊





Ahankali tasoma magana.
"Jiya da safe Abba yafad'amin hukuncin da suka zartar akanmu, hankalina yayi matuk'ar tashi jin da yaya jameel za ahad'amu.
Sabida nasan halin shi na rashin kamunkai.
Atake nace ma Abba yataimakeni su warware wannan had'in don bana sonshi sam,aiko nasha fad'a hard a barazanar duka, nayi takuka ba mai rarrashina.

Ranar da hantsi ina barci umma ta tasheni wai inmaza inshirya inzo ga jameel yazo.
Duk raina ba dad'i nashiga wanka nashirya.
Yana zaune a d'ikin bak'i, nasa meshi, cikin girmamawa na gaidashi, nasami wuri na zauna.

Tunda na iso ke aikin kallona kamar maye, nahade rai ina hararanshi domin wallahi beasty kallo daya nayi mishi na kau da kai sabida shigarshi kamar wanda zashi gidan rawa.
Sanye yake cikin d'amanmun kaya irin na rashin d'a'a da rashin kamun kai.

Inacan ina tunani banji motsinsaba sai jin hucin numfashinsa nayi kusa dani, nayi saurin tashi na matsa zuwa dayan kujeran, ya biyoni zan tashi ya fizgemin gyale ya cukuikuye yayi jifa dashi, aiko na rufe Ido nasoma cin masa mutunci.

Abisa mamakina maimakon yayi fushi sai yasoma tafa hannayensa yana daria.
Cikin salon iskanci yasoma magana.

Waww baby kin had'u kina d kyau tare da kayan alatu, lallai zan kwashi romo, yaja wani numfashi irin na tacewa, yacigaba dole ink'ara godewa dady da yayimin albushir da samunki, washhh!! ni jeemee guy na caba sosai, jibeki Ai kece gama hawan ya shek'e da dariyan iskanci.

Cike da tsoro nake kallonshi, yasoma matsoni na arce da gudu.

Inakuka nake fad'ama Umma abinda yayi min wani amma domin bazan iya fad'a mata dukaba.

Umma tasomamin fad'a wai don ina k'insane, yasa na shirya wannan zance.

Duk yadda naso umma ta fahimceni tak'i saurarata.
Hakanan na yini kuka.
Da dare Abba dawo tare da yaya jameel, tare mukayi dinner dashi.
Muna gamawa nabar wurin.

Bantaba tunanin zai biyoniba, shiyasa ina shiga na tube nafad'a wanka.

Bayan nafito, "Allah beasty ban lura da mutum ciki d'akinba, sai da natsaya gaban mirror na hangoshi tsaye ya k'uramin idanu masu matuk'ar firgitani.

Da hanzari nayi gaggawan komawa toilet daku daya ya tsakumoni yana wani numfashi, mai ban tsoro.
Ihu na kwalla amma baza ajiniba sabida muryata ta dushe, inaji inagaji d'an iskannan yayi kissin d'ina tsawon lokaci, sannan yabarni yafice yana daria wai sadakinsa yasoma d'anawa.
Kinjimin dan duniya.
Taja numfashi ta kafe Sophy da Ido, alamun takawo k'arshen zancenta.

Shiru Sophy tayi tana tunanin wannan tabara na jameel, bata tabajin irin hakaba ko alabari, ace zuwan farko, kazo da tsinewa da lalacewa haka oooo

Tasan intabiyewa beastyn ta za'ami matsala don haka tasaita numfashin ta tana kallonta.

"Beasty tabbas bai kyautaba, amma kiyi masa uzuri k'ila gwadaki yakeyi.

Da fushi ta tare numfashinta gwadawa fa kika ce!!? Eh
Taja tsuka to Allah tsinewa wannan gwajinnan.

Shiru Sophy tayi, tana kallonta, taja filo ta kwanta tana dafe kanta.

Sudrex ta ballo tabata, bata musaba ta amsa tasha, bajimawa barci yakwasheta.

Ganin haka yasa Sophy fita zuwa kitchen taya mamie aikin girkin tarban Abba.

Suna aiki suna hira da mamie, wanda hakan yataimaka wurin kaucewa tunanin labarin beastynta, amma sosai takejin haushin jameel tare da maxa masu rashin kunya irinsa.

Bayan sunyi sallah mamie ta tasa Jamee zuwa gida.

Sudai suna d'aki basu san mi suke tattaunawa.

Mamie tashigo tasamesu suna hira.
Gefen Jamee tazauna tasoma magana cikin sigar rarrashi.
" jameela kiyi hak'uri kiyiwa iyayenki biyayya, sukansu sunsan rashin jinsa,amma sun tabbatar kece zaki iya dashi sabida kin wadatu da ilimin addini, komi yayi miki zakiyi k'ok'arin saitashi ahanya, sabida haka ki ba marad'a kunya kinji? Ahankali ta amsa "to mamie.

Sophy da mamie suka komo gida cike da jimamin lamarin.

La,asar sakaliya uataz ya duro zance.
Kamar wancen karan yasami tarba mai kyau.
Sunacikin hira Abba yadawo, atare sukab isa sukayi mishi sannu da zuwa.

Yana dariya yace "aa lallai yarnyar mamaie an girma.

Ta ruga ciki da gudu, ustax yabita da murmushi yayin da Abba yace "ja'ira
Atak'aice yayiwa ustax tanbayoyi yana bashi amma, yace "zannemeka muk'arasa inna huta, " to Abba ya ce cikin girmamawa

Barr shikan tunda yaga sun nufosu ya sulale.

Kwanar Abba biyu da dawowa, ya mallakawa Sophy key d'in wata k'aramar motar *206* tare da fad'a mata ranar Monday zata soma halartar hospital domin soma aiki.

Wowohoo!! Zokuga tsalle da murna wurinta, rasa wazata soma rungume cikin su mamie, Abba da Barrister.

Ak'arshe barr yaja hannunta "zo muje muyo d'ani mu dawo.


Sunsha yawo wanda ita ke Jan abinta, domin ta jima da iya mortar, barr yakoya mata.

Ahanyarsu nadawowa yasako mata maganar Jamee. Yace da ita "lil sis inafa jin son k'awarki jamee.
Kallonsa tasomayi cikin mamaki, sanna ta maida hankalinta bisa titi.

"Takusa aure ta ce dashi atak'aice.

Hararanta yakeyi tana sane tak'i kallonshi, saida yagaji don kansa sannan cikin fad'a yasoma magana, "kinga banson raini ko? Inbanda rainin hankali yaushe kika xomin dazancen in aureta amma yanxu don nine naso abin zakiyimin iskancinku na mata wai jan aji tsuttt!!!!
Yaci gaba "to kisani yau da dare zaki rakani gidansu, kuma banson ink'arajin maganar banxa yafito abakinki.

Sosai yabata dariya amma sai ta gumtse kada tajawo k'ilu.

Bata k'ara tam kashiba har suka isa gida.

Suna shiga parlour ta isa gaban mamie, tana duban barr tace "mamie don Allah ba beastyna Abbanta yayi mata mijiba? "Eh anyi haka, miyafaru? Ta nuna barr tace "shine keson aurenta wai, yau zan rakashi.

Ido waje mamie tace kul d'inka, ansamu ta hak'ura zaka tada wani ballin, to ahird'inka, kanemo wata.

Kai yasunkuyar cike dajin haushin Sophy.

Abba dake aiki a computer ya tsoma baki, "eh lallai anyi haka, jiya Abbanta kefad'amin, inagama tare da Nana za'ayi bikin ahuta, don haka Nana inkunyi waya da yaron dake juwa wurinki, kice yazo ina nemanshi,ta amsa a kunyace "to Abba.

Barr dayagama mutuwar tsaye, yacinkayi muryan Abba yana cewa" barr kaje Kano gidan surukan Bahijja kazabi mata, don nayi magana da Alhaji bello zakazo neman d'aya daga cikin 'ya'yansa.

Agigice yake kallon kowa na parlour n, suna had'a Ido da Sophy ta kwashe mishi da dariya
azuciye yayo kanta ta arce zuwa d'ankinta ta danna key.

Su mamie suka kwashe da dariya, "ba ita takar zomonba rataya aka bata, cewar mamie.








*Mrs j moon*
[4/18, 2:11 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*25 to 26*
*©Safiyya*


Ganin su mamie nayi masa dariya, yasa yabar patlourn da sauri.

Acikin room d'insa, yana zaune dafe da kai, yama rasa tunanin mai zaiyi.

Yana son lil sis d'insa kamar ransa, mamie tashiga tsakani tahanashi tasiri, yad'au dangana da tawakkali.
Yanzukuma yasa ransa a meelan umma, itama ga yadda takasance, ak'rshema wai Kano zaitafi neman aure.
"Kai haba bazai yuwuba!! 'ya furta afili.

Haka dai yayi ta sak'awa da warwarewa batare da yasamo mafitaba, ak'arshe yatashi ya fice zuwa masallachi.


Sophy da dare suna waya da ustax d'inta tafad'a mishi sak'on Abba, yayi ta murna yakuma tabbar mata da yanazuwa goben

Dariya tasa mishi jin yadda ke murna.

Tace dashi cikin zolaya "Kajika, sai murna kakeyi kamar ance dakai and'aura mana aure
Shima dariya yasa yace "uhmm ai inranar auren mune bakina bazai iya maganaba sai shiru domin yadda nake d'okin ranar bazai taba misiltuwa ba.

Itadai dariya abin yake bata, agefe d'aya kuma gabanta nayawan fad'uwa, dazaran taji haka sai tasoma istiggifari tare da fad'an lahaula wala k'uwwata illah billahil aliyul azim.

Jin kamar tanajin barci yasa sukayi sallama.

Washe gari barr yafice bai nemi kowaba, sabida haushin kowa yakeji agidan.

Office d'insa ya bud'e yashige ya kulle kansa ciki.

Ya kife kansa bisa table, yana jin ciwon kai sosai.




Sun halarta a dinning suna tajiran barr suci abinci basuji motsinsa ba.
Abba ya d'au waya yakirasa, ya tabbatar masa yafita.

Yana sanar da mamie ta zunkud'a kafad'a tana cewa shiyasani ai.

Bawanda yace k'ala suka soma karyawa, bayan sungama Abba ya dubi mamie yace "hajiya inganin yaronnan maganar zuwa kanon danayi masa shine yashi fushi yafice da sassafe.
"Shiyasa ni Ai, aure ne sai yayi ko yak'i ko yaso.

Sophy dake saurarensu tasa dariya tace kai mamie auren dole zakuyi mishi kamar wata mace.
"Bashi yajaba, tuntuni anyi anyi yayi aure yak'i sai hange hange to kinga yanzu kaiconsa ai don inajin wannan karan aure ba fashi da yardan Allah.

Cikin jimami takama hannun mamie, tace "ayya mamie ayi mishi sassauci yanemo da kansa, kinsan barrister nmu mai ajine da kwalisa, sabida haka abarshi ya zabo da kansa hakan zaisa yafi ganin k'ima da darajan matar.

Mamie tunda tasoma magana take watsa mata harara, tabude baki zatayi magana Abba yatari numfashinta " a,a hajiya aduba maganar Nana, abarshi yazabo da kansa zaifi kam.
Baki mamie tasaki tana kallonsu, ak'arshe Abba ya ja hannun sophy yana cewa "zo muje kifad'amin wani colour kike buk'ata d'akinki ya kasance? Tana murmushi tana kallon mamie wacce ke hararanta ta kauda fuska tabi Abba, mamie taja tsaki, tare da cewa yarannan so suke su haukatani.

Barrister bawan Allah.
Yana can ko breakfast bai iya yiba sabida tunani yasha mishikai ga ziga zirgan Neman transfer dayakeyi, bai sami nutsuwaba sai da yasami tabbacin cikin satin zaiga letter na transfer d'insa.

Bayan la,asar yadawo,can baya yayi parking inda bakowane zai sanda dawowanshi ba.
Ta k'ofar baya yashigo parlour n cikin ikon Allah kuma baisami kowa cikiba har yashige room d'insa ya murza key sabida sosai yakejin baison hayaniya.



Ranar Monday Abba yayiwa Safiyya jagora zuwa hospital d'in daza tasoma aiki.
Private hospital ne wanda yazamo had'in gwaiwa ne Abba da abokinsa suka yi suka gina, babban yaron abokin nasa shine ke rik'e da hospital d'in sabida shi cikakken doctor ne.

Bayan had'ata da dr sadam da yayi, yawuce wurin aikin wani company nasa da akeyi.

Taji dad'n aikin sosai, taji dama karatun likita tayi ba nurse ba, sosai ta fahimci al-umma nabuk'atar taimako musamman mata.

Agajiye ta iso gida, tana kyara parking motat barr ya danno kai shima.

Tafito ta jingina jikin motarta, tana jiran sa.
Yana murmushi ya iso, ya jingina shima yana fuskan tarta, cikin muryan wanda yagaji tace " yaya Deen sannu da dawowa "yawwa sannu kema lil sis ya sabon rayuwa? "Alhamdulillah "masha Allah.
Suka jera suna hira,wanda hakan bak'aramin dad'i yayi mataba.

Daren ranar barr yasanarma dasu Abba anyi mishi transfer zuwa Lagos sati na sama zai wuce.

Mamie tayi mishi fatan alkhairi hakama Abba yayi masa.

Amma Abba kallonsa kawai yakeyi domin duk shige daficen da yayi na neman transfer yasani kyale shi yayi kawai.

Yasan bazai wuce maganar aure yakema guduba.

Lil sis d'insace dai suka kwashi daru domin sanda yafad'a mata kuka tasa mishi sosai yayi ta rarrashinta tak'i saurarenshi a k'arshema tabar mishi wurin cike da jin fishi.

Ana gobe zai wuce iyayen ustax sukazo, Abba tare da Baffan mamie sutayi musu tarban girma, bayan gaishe gaishe suka tsaida nan da wata nakwai za'ayi biki Wanda haka aka tsaida na beastynta.

Barr yak'ara tabbatar da cewa yarasa lil sis d'insa, domin haka daren ranar ya kwana sallah tare da addu'ar Allah yabashi juriya kuma Allah yayi mishi zabi nagari.

Washe gari yatafi cike da kewar gida yayinda yabar lil sis d'insa da kuka Wanda takasa zuwa asibiti sakamakon zazzabi da ciwon kai da take fama dashi, kuma kukan datasha ne yahaifar mata da hakan.

Haka ta yuni a kwance, zuciyarta ba dad'i sam tarasa mike damunta.
Sosai takejin kewar barrister zuciyanta namata shafi.

Ita kanta mamie sukuku take, sabida halin da babienta yafad'a yataba mata zuciya kuma tafad'a cikin tunani wanda yak'ara sanyaya mata jiki.

Da kyat tasamu tayi wanka, tasha magani.
Bayan tatashi barci tasami sauk'i sosai har ta sauka taya mamie girki, hakan bak'aramin yiwa mamie dad'i yayiba, tayi tajanta da hira har ta ware, sai gata tana kwasan dariya.


Bikinsu yana tamatsowa, kowani ban gare sai shirye shirye akeyi, yayin da Ammin ustax ta tubure sai dai ya auri mata biyu, shikuma yace bazanyiwa abincin ruhinsa kishiyaba, aiko ta kunnoshi tahana mishi sik'it.

Dama indai fagen tsiya ne ta haddace shi kusfa kusfa.

Sotake ya auri d'aya daga cikin yaran yayarta wato uncle d'insa dake zaune gidanshi.

Domin tasami labarin Nafisa nasonshi shikuma yak'i amincewa da ita sai wata bare can.
Dalilin haka ita kuma tace tunda ya dage sai bare to dole ya had'asu biyu.
Yayi ta rok'onta tak'i saurarenshi, yarasa yadda zaiyi, wanda hatta sophy ta fahimci yana cikin damuwa, amma tayi tambayar duniya yak'i fad'a mata sai dai yayi tacewa bakomi.


Zaune suke a d'akin Jamee, umma ta kawo musu had'in zuma kowa cike da cup.
Jikin Jamee har rawa yakeyi sanda takesha, sophy ta zuba mata idanu, har tashanye tana tsotse baki

"Malama miye kika samin Ido haka? Tabe baki tayi sannan ta yi k'asa da murya tana cewa"beasty bakijin tsoron shan kayannan wai? "Eh banjin komi sabida yaya jameel baxaiyi sauk'iba, nima bazan raga mishiba

Dariya sosai sophy ke mata har da ruk'e ciki, "wallahi beasty kina da abin daria, kintabajin inda Amarya tace baza tad'agawa Ango k'afa ba?

"Ansoma akaina daga yanxu.
" uhmm lallai alamomin harijanci yabayyana gareki, k'ara.
duka ta kaimata tana dariya.tace

" Kedai beasty bari kawai, yaya jameel baida kunya Sam, ko kinsan ranar damukaje gidan Dada( kakarsu) muna hanya dawowa don rashin ta Ido wai intai makeshi muje gidansa yarage mara, minti biyar zaiyi, niduk ban gano nufinshiba, saida yayimin baro baro wai baby bazanmiki da zafiba kowa bazai saniba.

Jinayi kamar in shak'eshi, don haushi wato kallon 'yar iskama kemin.
Tundaga ranar
nasoma taka mishi burki, yanasomamin tabara zan ce mama zan had'ashi da ita, sai kiga yayi lak'was, domin nafahinci yana jin shakkanta.
Kuma shiyasa na ku'dura sai na bashi mamaki, sai na caja mishi tunani,badai shi d'an iskaba toni kuma 'yar guguwa ce.
Dariya sophy keyi kamar me, tace "zanso ganin wannan game d'in.

Ta amsa "zadai kiga game a d'akinki da ustax.

Dukan wasa takai mata,ta goce tana dariya.

*ina labarin barrister Deen bawan Allah*
*...............*






*Mrs j moon*
[4/19, 6:35 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*27 to 28*
*©Safiyya*


*Barrister nuruddeen* ya kama aiki cike danasarori.
Yana da k'wazo tare da hazak'a, shiyasa baijima awurinba yayi suna, al-umma nasonahi sosai musanman wurin kare mai gaskiya.

Yayi fama da kewar gida tare da jinyar zuciyarsa, daga baya ya fawwalawa Allah lamarinsa.

Haryanxu yakasa manta lil sid d'insa.
azuciyarshi.

kuma yak'i bawa 'yammata fuska dazasu bayyana mishi k'aunarsu gareshi, hasalima shakkan yimishi magana sukeji.

A tsawon lokacinnan sau biyu yazo Kaduna ganin su mamie.

Yayi kyau sosai yanayib garin ta amshe shi saidai kuma rama yakeyi kad'an kad'an

A binda yafi danunshi shine yawan mufarkin sex da yakeyi ako dayaushe,
gashi yanxu in yayi sai abin yak'i wuce mishi, yini zaiyi yana tunanin abin
Asakamakon haka yasa yasoma fuskantan ciwon mara.

Yanxu haka shirye shiryen zuwa Kaduna keyi ,inyazo sai yanemi imam suwaid'i.
Limamin masallacin juma'arsu.
Sabida abin yayi yawa, *atunaninsa* ko matsalar junnu ne. Oho!!


**** Sallama yayi ababbar parlourn, suka amsa masa tare da gaishesa, ya ansa yayin da ke nufar dinning area.

Yana k'ok'arin zuba abinci a plat, nafisat ta iso tayi hanxarin ruk'e saving spoon d'in tana cewa haba yaya saif ina gidannan ace ka zuba abinci da kanka. Ta soma zuba masa tana yimishi magana ahankali wanda shikad'ai ke iyaji.

Baice da ita k'alaba, ya xubawa kayan ruwanta idanu, sakamakon duk'awar datayi d'inki ya zazzago shine bayashi damar kallonsu yana jan ta'awiyyi azuciyarsa.

Lallai mata had'arine kam. Cikin zuciyarsa yafad'i haka.

Bayanta gama zuba mishi taja kujera ta zauna daf dashi, tana kallon idonsa, yace turaren humranta mai d'ankaren k'amshi na dukan hancinshi

Hak'ik'anin gaskiya tana shirin jefashi wani yanayi sabida k'anshin turare nada dire sosai

Ta ce dashi "oya cinye kabani plat d'in yanxu, harara ya dalla mata "ga yaronki ko? Ta girgiza kai"a,a.

Bai k'ara cewa komiba har ya k'oshi ya d'au ruwa ya korawa mak'oshinsa.

Zama ya gyara yana dubanta, rai had'e. Yace da ita
"Amma kinsan baidace dake irin wannan shigannanba ko?
bakyajin magana Nafee tun tuni ina gargad'inki da suturce jiki ink'iji.

Ya nunata da yatsa "don Allah duba yadda d'inkinnan ya matseki, kalli sket d'inki, keba kyajin zafi ak'irjinki ne? dibafa yadda yamatse miki kayan ruwa.

Idanu waje take dubanshi, takasa cewa komi, itadai iya saninta bai taba ce mata nafisat kibar d'inki matsatstsuba, amma yau ya fitittike yana yimata wasu zantuttuka marasa tushe harda wani fad'an kayan ruwanta a,a kayan wuta ne.

Ta bata rai tana dubansa ido cikin ido, "tace to ina ruwanka kuma, tunda bajikinka bane, sai ka sa ido kayi kallon arziki kabar arziki.

Azuciya yakai hannu ya murd'e mata kunni tana shirin kwalla k'ara yayi hanzarin toshe mata baki da d'ayan hannunshi, hannayenta tasa tana k'ok'arin kwatan kunnenta amma ta kasa, aiko don azaba tasoma zubar hawaye.

Ahankali yasaketa yana murmushin mugunta, tako kife kai bisa table tasaki kuka mara sauti domin sosai takejin kunnenta nayi mata rad'ad'i.
Yace badai tak'amarki rashin kunyaba to zansoma gyara miki zama 'yanmata
Tana shirin bashi amsa mamata iso.

ta tashiga kitchen tafito, taja ta tsaya tana kallonsu wanda bakomi cikinsa sai harara.

Cikin alamun fad'a tace "nafisat Allah zansaba miki da son shigewa wanda bai damu dakeba, yace baya sonki sai bare, sabida haka munkusa sa k'afar wando daya dake a gidannan, ta k'arasa maganar tana dokawa ustax harara.

Ya sosa sumar kansa, "uhm mama nifa bance bansonta ba, nace abari inna auri Safiyya ko da da shekara ne sai in auri nafisat.
Yaci gaba "to tayama za'ayi ink'i jinina? Ta tari numfashinsa "gashinan ka k'i kuwa!! tunda har sai nan da shekara zata jiraka, to kayi kad'an saifullah, ba masoya ta tasaba don haka kayi tayin aurenka, itama zatayi nata bada jimawaba.

Ganin tad'au zafi yace "a'a mama kadakice haka, kiyi hak'uri zan auresu duka amma.... Amma me? Tace Magana tak'are tunda ka amince zaka auresu rana d'aya Ai bamatsala, intafi insanar da Abbansu.
Tawuce da sauri.
Tayi hanyar room d'in uncle d'insa.

Kansa yadafe yana jimamin subul da bakan da yayi.

Nafisat ta mik'e cike da tsiwa tana cewa "nibazan had'a miji da kowaba, don haka wallahi da sake ehe.
Kamar ya mangareta yakeji, amma sai yamik'e kawai yabar wurin cikin k'unar rai.
*Atunaninsa* yazaiyi da sophynsa, kuma yana tunanin anya zai iya adalci a tsakaninsu kuwa? Kai abin dakamar wuya.
Yana ta sak'e sak'e kiran Amminsa yashigo, gabansa nafad'uwa yad'auka, amai makon yaji tana fad'a kamar kullum sai yaji akasin haka wannan karon Albarka tayi tasa mishi akan yaji maganarta ya amince da auren nafisat, shi dai amsa yake da Amin Amin kawai jikinsa ba k'wari.


A inda suka saba zama, Safiyya,saif tare da jamee da oga jameel suke zaune suna tatttauna yadda tsarin bikin zai kasance, sudai amaren sunfad'a musu walima zasu gabatar kawai ana gobe.
Ustax yace hakanma yayi amma oga jameel yace dole ayi lunching kafin walimar bayan d'aura auren da dare ayi dinner.

Hakan suka amince ganin zaisoma mitan, wai kada subata mishi show abokansa har da masu jan kunne fa.

Sophy tayi tama jamee dariya ganin yadda tayi fitifitik da fuska.

Sun rakosu zasu shiga mota, motar barr ta kunno kai.

Dukkansu suka isa wurinsa bayan yafito, suka gaisa tare da musabaha da juna, yayi musu fatan Alkhairi ya wuce ciki zuciyarsa nak'ara jadda masa yayi hak'uri da lil sis d'insa baarabonsa ba ce.


Yasami imam suwaid'i yakuma yi masa gamshasha shiyar bayani.

Matsalarsa da junnu dakuma sa'abu arai yana haifar da mufarkin sex amma mafi inganci zance junnu ke haifar da haka.

Yabashi magani na wanka tare da sha, sannan yarubuta mishi nafilfili masu inganci da kariya daga sharrin shaid'anu, yakuma k'ara jadda mishi duk runtsi kada yayi sakaci da yin arollah kafin ya kwanta.
Yayi ta godiya tare da ajiye mishi sadaka.


***** biki budiri bured'e
Gobe d'aurin aure.
Amare amsha gyara ansha kyau kam ba'a maganarshi.

Sosai kuke haskawa.
'Yan Maiduguri sun iso tun ana saura kwana biyu wato ranar dasu gabatar da lunching.

Yau kuma ranar walima ce.
Don haka awani katafaren gidan Abbansu Safiyya akashirya gabatar da walimar Wanda gaba daya amaren sun had'u agidan.
Jamee,sophy tare da nafee.

Wacce dole ta hak'ura da zama da kishiya.

Sosai walimar ya k'ayatar malama mamie waru ta gabatar da wa'azi mai tatsa jini da jijiya, domin tayi k'ok'arin tabo zancen manzo SAW akan falalar da mace mai biyayyar aure take samu arayuwarta tare da nasarori.

Bayan ta gama malama Hameeda ta d'ora da tata akan tsafta da kula tare da kuma rik'e sirrin miji sai uwa uba hak'uri jigon zaman aure.

Tunda akasoma gabatar da lectures hankalin Sophy yake kan wata matashiyar mata tare da wata budurwa mai tsananin kama da ita sosai.
Suma tafahimci hankalinsu na kanta domin tana hago yadda suke kallonta suna k'usk'us akanta.

Gawani fad'uwa da gabanta keyi akai akai tun jiya.
Agefe d'aya kuma bak'in cikin rashin zuwar barr Deen bikin ke damunta.

Bama tasan anyi addu'ar tashiba sai dai tacinkayi maganar beastynta tana cewa" beasty mamie tana kiranki gatacan tare da k'anwar baban ustax d'inki, zaku gaisa, taja hannunta tana cewa amma beasty kunyi kama da budurwancan mai siffan larabawa.










*Mrs j moon*
[4/20, 1:57 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*29 to 30*
*©Safiyya*

*Page d'in nakine my Sahiba(Aisha' Ashmee) banmanta dakeba,Allah yabarmu tare cikin Aminci Amin.*




Mamie ce ta kamo kafad'anta tana cewa "yarinyar mamie ga surukanki Ku gaisa, k'anwar Abban Saifullah ne.

Cikin jin kunya ta russuna tace "inayini? Lafiya lau Amaryanmu, tana murmushin kunya tafad'a jikin mamie.

Abayanta ta cinkayi maganar budurwan tana cewa "Aunty Allah sai data matso sannan nak'ara ganin kanarta da mum sosai domin hatta kwayar idanunta na mum ce, ta kama haba "kai amma wannar kama harta baci.

Mamie tayi yak'e kawai, batare da tace komiba,domin ita kanta gabanta fad'uwa yakeyi tun sanda tayi arba da photocopy n yarinyarta.

Aunty ta ja ajiyar zuciya tace "kai eshat kinfiye surutu, to Ai kema mumyn ki kika kwaso, tasa dariya eh, hakane aunty amma abin ya jefani cikin matsanancin mamaki, kuma bros kada wasa bai taba cemin matarsa kamatake damuba, ko miya hanashi fad'a oho.
Zuwa lokacin ita kanta mamie ta jinjinawa surutu irin na eshat.

Su dai su Sophy da Jamee Ido suka zuba mata, tana magana tanawani lunshe idanu kamar mai jin barci.
*haka idanun meena yake lol*

Aunty ta kaimata duka kad'an tace kin balle da surutu kamar aku, ko gaisawa da

Please Login or Register in order to submit comment