Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata maganin ciwon mp.
" mamie tace,, tana shafa mata sumar kanta, cikin tausayawa.

Tam mamie ya amsa tare d fice cikin Sauri, jikinshi narawa,, baison ganin ciwonnan, nta,, yasan tana jin jiki inyazo, duk atunaninsa yazaci tawarke ganin ciwon yadade bai motsaba.

Bayan d'an wani lokaci d shan mgnin, tasami sauk'i,, sukar maran d cinyar ya lafa.

Ganin barci yad'auketa, mamie ta umurci barr yadauketa yakaita bed room d'inta.


Washe gari ras ta tashi, batajin ciwon komai sai d'an abinda ba,arasa ba.

'Dakin mamie tashiga d sallama

Tasameta tana waya d Abba

Yana sauraren hiransu
Sosai take murmushi jin tsofaffi d soyayya

Mamie natafi makaranta" OK yarinyar mamie har kin warke d zaki iya fita? Eh mamie,, to Allah k'ara lapia" Amin.

Har tafita ta kuma dawo,, mamie ayimin dambun cuscus
To Nana, za,ayi miki " yawwa mamiena tafice d gudu.

Daria mamie tasa, tana jijjiga kai.

Abakin step sukaci karo d juna,, shi ya hayo d sarsarfa ita kuma zata sauka

'Yar k'ara tasaki, tana liliya k'irjinta.

ya dan batarai tare da cewa lil sis miyasa baki d natsuwa ne ?

Kwalla yaciko mata a idanu,, tabi gefenshi ta wuce batare d amsa mishiba.

Bayanta yabi d kallo.

Hijabin ya manne mata sbd robane, amma dogone don yawuce gwaiwarta.

Awaya takira Jamee, bata jimaba tafito suka wuce.

'Karfe daya saura suka tashi.

Suna fitowa get suka sami ustax zaune bisa motarshi,, yana ganinsu ya duro.

Amincin Allah yatabbata agareku abincin ruhina"tare d amuniyarta" atare suka sa, da'' Amin tare d kai.

Yayi daria, kuzo inkaiku gida, basu musaba, sbd sun gaji sosai.

Ya sauke Jamee sannan ya wuce d Sophy.

Kafin su isa gida yanata janta d hira, tak'i sakewa, wani matsancin kunyarsa takeji.

Yana ajiyeta,, ta shige gida d sauri.

Ya jingina d site ya dannamata kira,, lokacin tana daf d shiga parlour.

*Matar ustax* kin gudu ma ustax d ruhinsa,, cikin dan daria tace to dayamma ustax yazo amsar ruhinsa wurin Matar nashi,,

da daria ya kyal kyale dashi sannan yace kijirani zanzo kuma sai kinban Abita,, Tam ina jiranka.

Cikin nushad'i sukayi sallama.

Ta doka tsale kad'an ta furta " inasonka ustax duk d d'an gemennan naka.

Tana d'agowa suka had'a Ido d barr,, yayi kincin kicin d fuska,, ta bi gefenshi zata wuce
" ya daka mata tsawa" kedawaye haka kike daria kamar kwancen haukaciya?

Ta batarai, tana kallon hanyar gudu,, nikam ya Deen kabar cemin mahaukaciya,, ya zaburo zai maketa ta kwasa d gudu tashige parlour.

Kai ya gyad'a zan d'au mataki akanki yarinya.






*Mrs j moon*
[4/12, 8:32 AM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*15 to 16*
*©Safiyya*



Turare take aikin fesawa, sai atishawa takeyi
Murace ta kamata bisa gadikkan alamu.

Parlour tafito tazauna,, lokaci lokaci tana kallon wayarta tana sakin murmushi.

Mamie ce ta shigo parlour n
Baki ta kama, cikin,, lallai yarnyr mamie kinaji d wannan suruki nawa, wannan irin kwalliya tare d k'amshi kamar agidan khady k'amshi.

Ta sa hannunta a fuska" mamie kinsani jin kunyafa, tafad'a cikin sigar shagwaba.

Aikece 'yar gidan mamie, dole ayaba irin wannan kwalliya taki.

Kwalliya tayi Nagani na fada duk don xuwar ustax saif.

Wata tamfa tasanya mai kyau d tsada, mai dauke d fulawowi jajaye tare d ratsin bak'i.
Ta bata lokaci wurin kyalkyale fuskanta, sannan taja d'aurin d'an kwali irin ta 'yammata 'yan kwalisa.

Sosai tayi kyau,, gawani haske data k'ara.

''Wayarta tayi k'ara, saida ta ja class sannan ta d'auka.

Matar ustax ga ustax yazo" OK ganinan.

Mamie yazo,, to yarinyata adawo lafiya banda rawar kai,, akame kai duk da nasan bakya d matsala tanan wurin.

Tam mamiena, tace" yayinda ta yafa gyalenta k'arami maroon ta zura takalminta mai tsini kad'an shima maroon
Tapito fes abinta.

Cikin nutsuwa ta isa wurinsa, yana jingine jikin motarsa.

Sanye yake cikin yadi mai laushi ruwan coffee d hularsa kalan kayansa sai shoes dinsa cover black.

Tundaga nesa suke jifan junarsu d murmushin k'auna.

Tunkafin tayi mgn ya tareta
" Ran Matar ustax yadade,, murmushi tayi,, tare danaka ya ruhina.

Tajashi zuwa k'asan mango tree dake gefen parking space.

Wurin d kujeru masu kyau zagaye sai table mai fad'i a tsakiyarsu.

Wurin xaman barr ne d abokanshi.

Cikin jin kunya ta gaidashi,, ta koma ciki ta dauko mishi kayan motsa baki, dangin su snacks d drinks sai farfesun kayan ciki mai dadi.

Yaci sosai, nata yabama girkinta,, tana daria tace mamie tayi maka musamman, ah" lallai mamie tanaji dani,sosaima kuwa, tam ngd da kulawanku mata ta, ta kauda fuska wai matarka,, eh man, inaji ajikina kwanan nan zamuyi aure, tasa daria,, uhmm lallaima, to saina gama tantance halayyanka, kuma sai nasoma zuwa aiki hospital.

Aw kedin doctor ce? A,a nurse '' OK Allah yataimaka, Amin.

Yaushe zakisoma xuwa hopl d'in? Dazarar Abba yadawo daga tafiyar nan.
Aha, Allah dawo dashi lpia "Amin.

Kinsa me? Sai kafad'a

Ace karatunki ba kan kiwon lapiya kikayiba, to da bazan barki kiyi aikiba in mukayi aure, koda kuwa a gida kinsoma aikin.

Kai hava " sabida mi?

Inada kishi kuma mace irinku agida yadace akillaceku,, sabida yanayinku.

Idanu waye take dubansa,, ya runtse nasa yana jan hailala.

Mud'in mike garemu to?
Uhmm matar ustax mubar zancen, a,a sai kafad'a.

Intambayeki man? Eh" ina saurarenka.

Antaba fadamiki kina da kya kuma jikinki na d'auka hankali?

Ta bata rai tana hararanshi,, yasa daria, ehmm inajiran amsarki

Cikin tsiwa tace bansaniba,, Ashe kaima d'an sa idone? Ya kama baki yi hkr abincin ruhina.

Ta tura baki,alokaci d'aya tamik'e, zatabar wurin.

D sauri yasha gabanta,, cikin marairai cewa, yace soryy please bazan k'ara kallonkiba, na tuba' fushinki kukan yaro, ta sassauta fuska, tana kallonshi k'asa k'asa, yaja numfashi, zomu k'arasa hiranmu,

tadawo ta zauna. Tana d'an hararan sa.

Wallahi d kikayi fushi kina mgn sai kikatunamin d artabunmu ranar d ruwa ya zanemu.

Ta kunkuyar dakai, sakamakon tuno tsiwan datayimasa ranar.

Yasa daria, Allah tsiwarki na burgeni sai kuma kunyarki mai ban sha'awa.

Murmushi takeyi kawai batare datace komiba.

Sunsha hiransu sosai, daf d magrib sukayi sallama.

Yabawa mai gadi ledoji biyu manya cike d kanyan kwalam, d kayan Shafa, yabi bayanta d su.

Tanashiga parlour ta fad'a jikin mamie tana daria,, mamie yana da kirki Allah, ina sonshi, yace agaisheki next time zaizo gaidaki.

Allah ya kaimu lapia"Amin.

Baba mai gadi yayi sallama yabata sak'on,,mamie tayi ta yabawa, ita kam murmushi takeyi tana jinjina k'aunar d ustax keyi mata.

Barr yayi sallama suta amsa mishi"
Ya kai dubansa kan Safiyya.

Sarkin yawo, yau kuma ina kikaje, don nasan wannan kwalliyar, unguwa kika fita, tayi mishi banza, ganin tak'i amsashi, ya dubi mamie" yanxu mamie kina kallonta tafita ahaka d wannan ficicin gyalen, salon ta jefa mutane a halaka.

Cikin kuka Sophy ta tari numfashinsa" wlh y Deen ya isheka dangantani d shaid'an

Ta k'amk'ame mamie,, mamie kishiga tsakanina dashi, ya daina min haka.

Da kyat mamie ta rarrasheta, ta bar kukan,, ganin tasake yasa cikin zolaya mamie tace tapi daki huta yarinyata, Allah barki d ustax musha biki

Tana daria ta mik'e ta haye sama.

Mamie tana ganin ta haye ta dawo da dubanta kan barr.

Ka fita idona Deen , nace kafita sha,an in yarinyata, bansan irin wannan abin da kake mata tam,
kakiyaye ko in saba maka.

Kanshi sunkuye ya amsa to mamie,zan kiyaye.
Dadai yafi maka kam.
Ta mik'e tare d barin mishi parlour n.

Kai yadafe, cikin matsanancin damuwa.

Zanbarki har abada, yazamamin dole inyi nesa dake.

lokaci yayi dazan nemi transfer.
inbarmuku gidan Ku wataya.

Cikin zuciarsa ke zancen.

Ya mik'e yadoshi d'akin Sophy.
Xuciarsa kamar wuta don tsabar rad'ad'in datake mishi.











*Mrs j moon*
[4/12, 4:33 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*17 to 18*

*©Safiyya*


*Dedicated to bebeelo*



Ya tura k'ofar, yashiga.
Kwance ya hangota, tayi rufda ciki.

Ya k'urawa k'ugunta Ido, kina da kyau tare da diri sosai lil sis, cikin zuciyarsa yake fad'a.

Tun shigowarsa, tanaji tayi biris dashi.

A sannu ya tako zuwa wurinta, gefen bed ya zauna
Hannunsa ya dora bisa gadon bayanta, taji wani yarr, amma tak'i motsawa, domin yayi matuk'ar bata haushi.
Yasan tanajinsa, sabida haka sai ya lalibi zip d'in dake bayan kayanta ya soma ja ahankali.

Cikin fushi ta juyo tana kallonsa, rai hade.

Murmushin yak'e yayi, ya kyara zama ya damk'e hannunta cikin k'aramin murya yasoma magana " lil sis kiyi hak'uri ki fahimceni, banson ganinki cikin dinkuna mai nuna tsiraici, alhalin kinsan kina da shape mai d'aukan hankali, to tunasar dake nakeyi ki kyara, bance kibar sa kayanki ba amma kitabbatar d kinsa hijab wanda zai suturta jikinki, Wanda zai yaboye niimar d Allah yayi miki.

Yaja numrashi kad'an yaci gaba

"ku mata hadarine wani lokaci,musanman inkunga kuna da siga, dirri,tsari tare d kuma kyau, sai kuyi ta fidda shi ako ina batare da tunanin kuna cutar dawasu maza masu raunin imani ba.
Shi yasa ake yawan keta muku mutunci, abarku da cizon yatsa, domin anriga angama daku. Sabida haka nake yawan yimiki fada, akan suturce jikinki.

" dafatan yanxu kinfahimceni, ba takuraki nakeyiba sai son tunasar dake dokokin Allah SWA.
" duk danasan kinsani, sai dai kintake ne, sabida haka yakamata ki kyara tun wuri.

Jikinta yayi sanyi sosai, muryanta na rawa tak'ara k'amk'ame hannunta da ya ruk'e" yaya Deen kayimin affuwa akan rashin fahimtarka da banyi ba.
" natuba ya Allah kayafemin inna d'au hankalin wasu mazan batare da sanina ba.
Ta cije banba.
"Nagode da kulawanka yaya deen, Allah yabarmu tare da k'aunar junanmu.

"Ya amsa Amin ya Rabbil Alamina.

Yana jin wani sanyi na sauka a heat d'insa sosai.

"Lil sis mubar fad'a kenan daga yau ko?

Yafad'i tare da
kashe mata Ido d'aya
Tasaki murmushi mai nuni da tana cikin farin ciki, "eh yaya Deen munshirya, kuma dama kaine ke fushi dani ai.

Idanu yazuba mata yana kallon maganarta cike da shagwaba, sannan cikin natsuwa takeyinsa.

Zame hannunta tayi, ta hura masa iskan bakinta bisa fuskanshi.
Yaja numfashi.

" kallonfa? tace da shi.
Ya hai hannu ya murd'e mata kunni, tasaki k'ara, yak'i sakinta saida yaga tasoma kwalla sannan ya saketa, lokaci d'aya kuma ya gintse fuska.

" banson raini, kinji ko, kai ta gyad'a tana liliya kunninta.

Ya mik'e yana cewa "kishirya bayan isha'i zaki rakani dubiya, matar abokina bata da lafiya.
" to tace, yasakai yafice, tabi bayansa da kallo, sai kuma tasaki k'aran murna, "wayyo dad'i kasheni, mun shirya da barr.

Sai ta hau rawa tana karkade karkade, kamar wata mazari, duk cikin farin ciki.

Saida tagaji don kanta sannan ta zauna tana dafe ciki.

Sosai takejin zuciyarta namata dad'i, wani nushad'i takeji aranta.

Bayan isha'i tasanja kwalliya, tayi kyau cikin material pink da ratsin white.

Ta sa hijab fari dogo, wanda yasauka har gwaiwanta, sai k'amshin turaren insidex takeyi.

Tana zaune a parlour, yashigo.

" lil sis kinsha kyau' yace da ita.
" nagode
"Kaima kayi kyau, ga gemunka yak'ara fitowa.

Ganin yana hararanta, tasa daria" yi hak'uri barr,nabari.

Murmushi yayi tare da cewa "kin riga kingama rainani lil sis, hatta da k'awarki meelah ta rainani, kun maidani abokin wasanku.

Jin yakira beasty d'inta, yasa ta tuno da alkwarin datayi mata na had'a ta dashi.

** bari mufita sai infad'mishi,Allah ya d'orani akasa, Amin. Duk cikin zuciyanta takeyi zancen.

'Danki mamie suka shiga da sallama.
Tana zaune bisa sallaya, tayi musu gyaran murya.

Suka sami wuri suka zauna jiranta ta idar.
Bata d'auki lokaciba ta sallame.

Baki bud'e take kallonsu,, kamar ba d'azun suka sami sabaniba, uhmm yaran zamani sai abarsu da halinsu.

Atare sukace "mamie inayini? "Lapiya lau
" saikuma ina haka? Barr yabata amsa rakiya zatayimin zuwa gidan abokina Ahmad, matarsa bata da lafiya.
" OK to kudawo lafiya, agaidamin da ita, kuma kada kuyi dare.
" to mamie bazamu yiba, insha Allahu.

Safiyya ta rumgume mamie tace "mamie yimin addu'a sabida bakin mutane, tana d'an daria ta ja addu'ar kariya daga mugun abu ta tofeta dashi, "Allah yayi mini Albarka "Amin mamie, tarema da yaya Deen.
Tana kallonshi, murmushi yayi tare da ficewa, tamanwa mamie kiss a kumatunta, tabi bayansa barr da d'an gudu.

Jijjiga kai mamie tayi tana maijin dad'in ganinsu cikin walwala.

Sun isa gidan lafiya, ahanya suna ta hiransu, saitayi kamar zatayi masa maganar beasty n ta saikuma ta kasa, ita ta lurama wani kunyarsa takeji yanxu.

Laluran ciki ke wahalar da fadeela, Matar abokinsa Ahmad.
Ta tausaya mata sosai, kwance take kamar ruwa, bata iya komi, muryanta tayi rauni, sai juya kai takeyi.

"Yaka mata Kuje hospital abokina, barr yace da Ahmad.
"Dole zamuje gobe kodon yawan aman da takeyi, da jiri.
" dayafi kam.
" sannu fadee, ta motsa kai tana lumshe Ido, alamar barci takeson yi.

Suka ajiye mata kayan dubiya suka yi musu sallama.

Tare da yimata fatan samun lapiya

Sun d'au hanyar komawa, gida duk sunyi shiru kowa da tunanin da yakeyi cikin zuciyarsa.

Itadai yadda zata yimasa maganar beastynta take sak'awa, sai kuma tausayin fadeela fal cike da zuciyarta.

Yayin da barr nasa tunanin yadda zai yi nisa da su mamie yakeyi inyasami transfer.

Ta muskuta tare da katse shurun nasu

"Uhmm yaya Deen don Allah alfarka nake nema a wurinka.
Ya kallota sosai, " inajinki lil sis, zanyi miki komiye indai baifi k'arfina ba.

Cikin kwarin gwaiwa tasoma magana a hankali...






*Mrs j moon*
[4/14, 5:18 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*19 to 20*
*©Safiyya*

*Dedicated to my family, LATE ALHAJI HARUNA MAIRIGUNA*
*Allah yajik'an mahaifinmu da rahama, Allah yacigaba da k'ara had'a kanmu, muzamo tsintsiya mad'aurinki daya Amin*👏🏻




"Ya Deen don Allah inason ka auri beasty na jamee.
Dam!!! K'irjinsa yabada sauti.
Kan motar yanemi kwace mishi, yayi gaggawan dawowa hankalinsa tare da damke sityarin da kyau.

Jin yayi mata shiru, yabata daman cigaba da koro mishi kyawawan d'abi'un sahibanna ta.

"Allah ya Deen tana da kirki d hankali ga natsuwa, sannan ma'abociyar kyalliyace d tsafta ga iya girki mai dad'i da gamsarwa, sosai nakeson tazamo daya daga cikin zuri'armu, sabida d'abi'unta na garine kuma ina buk'atar dank'on zumuncimu ya cigaba da d'orewa na har abada.
Ta numfasa sanna tacigaba da cewa
"Inhar hakan yafaru zanfi kowa murna don nasan big bros d'ina yayi dace da mata tagari mai matuk'ar so da k'aunarsa.
Takai hannu ta d'ora bisa cinyarsa tad'an matsa, ya d'an zabura yana watsa mata wani mugun kallo,

idanunsa sun canza launi,gawani jijiyoyi akansa sunfito rad'a rad'a.

Ita kam bata ko lura da hakanba tacigaba " banajin beastyna akanka, tabbas zatazamo maka inuwa mai matuk'ar dad'i, zata kare martabanka ako ina kake sabida ta wadatu da ilimi mai nagarta.
"Allah sai kayi alfahari dazaman towarta uwar 'ya'yanka,, ta sanyaya muryanta tace"barrister nmu please kada kak'i amincewa kaji?

Banza yayi mata yana cigaba da kallon hanya, zuciyarsa tamkar yata futo k'irjinsa don tsananin bugawar data keyi mishi.

Cikin shagwaba ta dafa kadanshi tana mai cewa " uhmm ya Deen say sme thing please.
Batare da ya kalletaba ya daka mata tsawa" live me alone!!

" ko in taka miki wuya yanxu.

Cikin zare idanu ta matsa can nesa dashi, tana kallon yadda yake gwama numfashi.

Har suka isa gida bata k'ara motsi mai k'arfiba.

Ko gama gyara parking bai yiba ta bude k'ofar zata fita
"Gidan uban wa zaki? Yace da ita, yana jifanta da mugun kallo, wanda ya haifarmata da rawan jiki.
Asanyaye takoma ta zauna, tana kallonsa da darara daran eyes d'inta.

Tsawon lokaci baice komiba, ta sunkuyar da kanta zuciyarta na tsoron jin abinda zaifurta.

'Dan k'aramin tsuka yaja, cikin kaurin murya yakira sunarta
"Nana Safiyya!! Ta d'ago cike da mamakin jin yakira ainihin sunarta, wanda iya tsawon rayuwarta bata tabajin yakirata da shiba sai yanzu.

Sai da yak'ara mai matawa, sannan ta amsa acan cikin mak'oshi " Na'am

Saida yakirata sau uku tana amsawa, ya gyara zama yana duban ta fuska d'aure.

" Daga yau sai yau dazan k'arajin kiyimin magana makamancin wannan.
Ya cije bele yana jijjiga kai " inkuma kika kuskura kika k'ara abinda zanmiki sai kinyi mamaki, don zir zanmiki inzaneki, ciki da bai, wanda inaga sai kin hau gadon asibiti jinya.
Idanunta waje tace "zir fa kace yaya Deen?
"Yawuce nace,, aikatawa zanyi, inkuma kina da ja, ki yi gigin maimata shirmanmun zantun tukanki kiga aiki da cikawa.

Ta batarai, tana tura baki, "to kayi hak'uri bazan sakeba, amma masoyi Ai yafi mak'iyi
Abazata ya buge mata baki da bayan hannunsa, ta dafe wurin tana kallonsa Ido waje.

"Kad'anma kikasoma gani yace da ita.

Idanunta yakawo ruwa, ta kwabe fuska, tanason sake magana tanajin tsoron tasaki layin dazaisa yayi mata zir, cewansa.

Ya bude k'ofar yafice yana cewa " bari Abba yadawo zan fad'a masa arabaki da shegen ustax d'innan, sabida naga alamar yafara koya miki rashin kunya, don gashinan kusoma bin maza kunafad'an kuna sonsu

" k'ila shima cewa kikayi kina sonshi don rashin kamunkai da zubda aji.

Da gudu takamo hannunsa,idanunta na zubda hawaye, " wallahi Allah yaya Deen bani nace inasonshiba, shine yaganni ya yaba kuma na...

Kallon dake mata yasa tayi saurin tsuke bakinta.

Kai yakad'a kawai batare da yace da ita komi ba, ya wuce tabiyo bayansa jiki asanyaye, wanda gaba daya tarasa mike mata dad'i.

Aparlour suka sami mamie tana sauraren channel d'in Saudi QUR'AN
hannunta d'auke da wani littafin addu'o,i.

Tafad'a jikinta tana mai kallon barr ta gefen Ido, suna had'a idanu ta girgiza mishi kai, ga mamakinta sai taga ya gyad'a kai yana murmushi.

Tasauri ta tashi tana daria, duk suka zuba mata Ido domin k'arin bayani

Tarasa mizatace musu, tasoma daburcewa, sabida hak'i k'anin gaskiya ita dai ganin barr yayi mata murmushi alamun yahuce shine ya saukar mata da jin sanyi azuciyarta, har yasata daria.

Ganin yadda takeyi kamar tayi k'arya gaban Alk'ali, yasa mamie tasoma yi mata daria tama mai cewa " yarinyar mamie ko surukina kika tuna yasaki darawa? Cikin kauda fuska tana murmushi ta gyad'a kai alamar eh.

Tsaki barr yaja tare d barin wurin.
Mamie tabishi da Idanu. Tana tunanin miya batamishi rai kuma, ta zunkud'a kafad'a alamun shi yasani.

Itama bata jimaba tayiwa mamie sai da safe.

Ta gama shirin barci ta kwanta cike da tunanin yadda zasu kwashe da beastyn ta gobe intaji zancen yaya Deen yak'i amincewa soyayyarta.

Cikin talatainin dare barr ya farka, yana jimamin wannan bak'on al-amari da yake faruwa shi cikin kwanakinnan.

Duk inya kwanta barci da dare sai yayi mufarkin yana saduwa da lil sis d'inshi cikin jin dad'i da yadda.

Ko yauma abinda yafaru kenan.

Ahankali ya furta "ya salamu kayomin agaji ,ka iyakancemin wannan laluran.

Wani shashi nazuciyarshi ya amsa, kayi aure shine k'arshen matsalarka, jinjina kai yayi alamun amincewa da shawaran xuciyarshi.
Alokaci daya ya bawa kanshi zabi, zai nemi lil sis tayi mishi jagora zuwa wurin meelah.

Sai kuma ya sosa kai, alamun kunya, tuno da yadda ya ma lil sis d'insa fata fata akan zancen.
Yamik'e yafad'a toilet, domin tsarkake jikinsa.

*my Berry low*
Ayi hkr d wannan, insha Allah gobe zakujini.





*Mrs j moon*
[4/16, 8:21 AM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*
*21 to 22*
*©Safiyya*


*Wannan page nakune 'yammata adon gari*
*Zainab('yar gata)*
*Fauxah(Matar saraki)*
*Maryam Rano('yar mama)*
*Duk kumatso domin kai gaisuwa wurin auntyn ku BEBEELO* *Lol*


Break suke gabatarwa cikin nushad'i.
Barr yafara tashi, yana goge bakinsa da tissue.

"Mamie sai nadawo, inaga daga office zan wuce d'auko Abba, yacemin jirginsu k'arfe biyar zai sauka.

"OK Allah saukesu lafiya,"Amin.

Har yakusa fita parlour n ya dawo, yana kallon sophy yace "lil sis innadawo zakirakani zance,
amamakance ta kama baki "kai barrister nmu? 'Dan hararanta yayi ina miki k'arya ne? Ta girgiza kai tana daria, tace "tam sai kadawo Allah yatsare ya kareka, ina jiranka, inga auntyna mai sa'a.

Shima darian yayi yana mai cewa"zako kiga surukan mamie yau. Mamie ta tabe baki, tace kamar gaske," Allah mamie dagaskene, "uhmm naji, wuce office kada ka makara, "tam mamienmu, yafice yana yiwa Sophy alama da hannu, na kishirya fa, kai ta gyad'a masa tana murmushi.

Tana kitchen tana wanke kayan dasuka bata, mamie tashigo.

"kiyi sauri kixo in aikeki wurin umman jameelah, "to mamie bari inyi wanka, "aha k'awar agwagwa, daria tasa tana cewa "mamie garinne da zafi duk da ana ruwa sama amma zafi yayi yawa.

Tashirya cikin doguwar riga tayi rolling, har ta fito parlour sai takoma dasauri domin sanyo hijab, gudun kada ta had'u da barr. yasata agarejin hak'ora arasa mai taunata.

Bayan tasanyo hijabin, wayarta tayi k'ara tazauna bisa stool tana fuskantan mirror.

Cikin murmushi ta d'aga tare da fad'in
"Amincin Allah ya tabbata agareka ya
Sweet ustaz d'ina.

Ya amsa "tare dake abincin ruhina.
Tasaki murmushi"ya office?" Alhamdulillah.
Sosai suka bata lokaci suna hira cikin annashuwa da jin dad'i
Ak'arshe ya sanar da ita zaizo bayan la,asar, sukayi sallama cike da d'okin son ganin juna.

Jamee ce ta turo k'ofar tashigo tare tafad'a bisa gado ta saki kuka cikin dusasshiyar murya.

Akid'ime sophy ta isa wurinta tana jeramata tambayoyi

"Mi'akayi miki beasty? Umma ce ko Abba? Ko kuma yaya munir ne? Shiru ba amsa sai kuka takeyi,ta jijjigata please beasty tashi kifad'amin inji miye matsalarki.

Ta tashi hawaye na zirarowa, itama zuwa lokacin idanunta sunciko da kwallah suna son zubowa.

Mai makon tayi magana sai ta rungumeta tana k'ara sautin kukanta. Atake itama tasaki nata kukan.

Mamie ce tashigo sakamakon jin Sophy ta dade bataxo amsar sak'onba, sam bataji shigowar Jamee ba.

Kallonsu takeyi cike da mamaki.
Cikin fad'a tace "kuna da lafiya kuwa? Mi akayi muku kuka maidamana da gida kamar sansanin zaman makoki?

Sophy ta dubi mamie tana jan hanci, "nima bansani ba, tashigo ne tana kuka, ta tari numfashinta "shine don shashanci kika biye mata kunayi?

maimakaon ki rarrasheta.

Ta sunkuyar da kai batace komiba.

"Jamilah mi yafaru? Mamie tace da ita.

Cikin dushewar murya ta amsa tana gyara zama
"Abbane zaimin aure kuma ni ina da wanda nakeso,na fad'a mishi, yace ban isaba, nikuma wallahi inason zabina, tacigaba
"Kuma wanda zai auramin sam baida tarbiyya.
Tasaki kuka ta rungume mamie"don Allah mamie kije kifahimtar dasu Abban, k'ila su janye inkinsa baki domin wallahi ban sonsa ban k'aunarsa Sam araina.

Ta k'ara tashewa da kuka mai ban tausayi.
Sophy tayi tagumi tana tsiyayar hawaye.

Ahankali mamie tasoma magana tana shafa bayanta

"Kiyi shiru hakanan, kibar kuka, zanje in gwada sa'ata ingani
amma kisani inhar sukak'i janye k'udirinsu to abinda zan umurceki dashi shine, yazamo da kiyi dangana tare dayi musu biyayya.

"domin iyaye ba aja da lamarinsu, duk d'a nagari burinshi yagama dasu lafiya, sabida haka ina rok'onki ki yadda da k'addara,kiyima mahaifanki biyayya, zakiga ribarta nan gaba kinji ko? Ta gyad'a kai tana Jan hanci.

"Yawwa 'yar albarka, Allah yabaki juriya da dangana "Amin
mamie nagode.

" kuma zanyi hak'uri da duk abinda yakasance, inhar sunk'i yanjewar.

Cikin jin dad'in kalamanta, mamie tace "yawwa meelan umma mai hankali d tawakkali insha Allahu Alkhairi na tare dake.

Ta kalli Sophy "tace k'awa ta garin ansanta da kwantarwa da abokiyarta hankali ne ba k'ara tunxuta ba, sabida haka ki rarrasheta ba kibiyemata kina wannan kukan banza da wofinba.

Tana share hawaye ta amsa da "to mamie zanyi k'ok'arin hakan.

"Allah yataimaka tace yayinda ta fice daga d'akin tana mai jaddadawa jamee lallai yakamata tabar kukannan haka.

Hayowa bed d'in Sophy tayi ta damk'e hannun jamee, tasoma bata baki tare da k'ara nusar da ita muhinmancin yiwa iyaye biyayya da kuma amfaninsa.

Jamee ta nisa

Please Login or Register in order to submit comment