Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Da manyan harufa HAJIA SAMIRA daga wyr tayi

daga daya bangaren hajia samirace zaune tadaura kafa daya kan daya fa'iza ta kwantarda kanta acinyarta cikin Dan murmushi tace hajiata ykk?

Itama momy murmushin tayi tareda fdn lpy q Aminiyata ya iyalin naki?

Lpy q ya shirye 2n tarbar shugaban kasa ?

Gashinan munatayi aminiya yame gdn naki?

Lpy q shima baya kasar


Allah yadawo dashi lpy


Amn

Hajia samira takarada cewa wai ya maganar tamune aminiyata wlhy diyarki dukta damu kullum cikin yimin kuka itade *annur*


Murmushi hajia hassana tayi tareda fdn ki kwantar matada hnkl wannan maganar bata waya bace sedai munhadu

Hajia samira ta amsa da ok

Daganande sukayi sallamah cikin SO da amincewar junah

hajia hassana taci gabada bada odar abinda za ayi mata kan kace kwabo an hada mata komai adaining tabla din babban falon me gidan an kammala komai cikin tsafta sewani daddadan kamshin turaren wuta yake tashi aduk ilahirin gdn. Wani wanka hajia hassana tadauka cikin wata danyar shadda doguwar riga me fitin din jiki agaskia bakaramin hatsabibin kyau tayiba sewani zuba kamshi takeyi na tsadaddun humra yan dubai (aiseta koma kmr yarinya yar shekara 25) nan aka zauna cikin shirin tarbar me gdn


Kwance yake akwanakin nan tunaninta yana addabarshi dayawa babu abinda idanuwanshi suke kwadayin gani kamar kyakyawar fuskarta harwani rama yayi tsaboda tunaninta betaba jin hknba akn wata diya mace waishin mekeneman samunshine??? Gaba daya yasusuce kullum addu 'arshi Allah yasake nuna mishi kyakyawar fuskarta datunaninta fal azuciyarshi tarados yayi wnka tareda dauro alwala yagabarda sallar azahar tareda addu'ur insa daya saba shiryawa yayi cikin kananan kaya sunyi matukar amsar jikinshi fadima batawa sajennan daya kewaye kyakyawar fuskarshi ya kwanta luf 2 feshe jikinshi yayida turare taresa manna dan tsiririn agogon gwal atsintsiyar hannunshi



Manyan mutanene cikeda airport din don tarbar me girma shugaban kasa adalin talakawa wanda suka hada da me girma gwamnan Abuja Da gwamnan kaduna dame girma sarkin kano Allah yajada ranka iya wadanda na (iya hangowa kenan)tako ina sojojine da yansanda anbaza tsaro cikin isada kasaita yafito daga katon jirgin da aka tanada danshi nan da nan yansanda suka mara mishi baya nan yabi gwamnonin da sarakunan yabi kowa sukayi musabaha sukayi mishi murnar dawowa lpy yaji dadn hkn yashiga motarshi suma yansandan suka mara mishi baya gabanshi yansanda da sojoji hk bayanshima hk katafaren gidanshi akayi dashi


Dai2 lokacin jiniya tafara tashi akatafaren gdn cikin katsaita yafuto acikin mota nan da nan *annur* yafito cikin murnar dawowar Dadyn nashi dasauri sauri ya isa yarungumeshi cikin kewar juna shiko Dady se kare mishi kallo yake ya hango damuwa a idanunshi daganan suka dunguma cikin katafaren bangarenshi momyce zaune tana jiran isowarshi cikin murna tamike tareda fdn wlcm my dear daganan *annur* yace Dad kahuta lpy yabar flon yakoma bangarenshi dan barinshi yahuta


Yana fita hajia hassana tarungume Mijin nata taredayi Masa kalaman love tajashi suka shiga cikin bedroom dinshi tataikaka mishi yarage kayan jikinshi tataimaka mishi yayi wanka tashiryashi cikin kaya marasa nauyi yayi sallah sannan taja hannunshi tacika mishi cikinshi yakoshi sosai sannan tatayashi bacci suka huta matuka sannan tabarshi yahuta sosai


Kafin yatashi taysake wani wankn tashirya cikin rigada siket na cot lace me matukar tsada tayi matukaryin kyau


Shima yatashi yayi wanka tasake shiryashi

Hajia hassana macece wadda tasan hannunta ta iya tafiyarda mijinta yadda yakamata shiyasa yake matukar santa tana kyautata masa matuka



Zaune suke akatafaren falonsu wanda yamatukar kayatu tana bashi kayan fruit abaki suna dan taba hira yadaga daya daga cikin woyoyinshi dake gefenshi yakira *annur* tareda fdn kana inane inason ganinka my son cikin Jin dadi *annur* ya amsada ganinnan my dady

Dady yadawo da knshi kan hajia hassana tareda fdn hajia waimeke damun son dinane ? naga yarame

cikin alamar damuwa itama tace wly naga hkn nima natambayeshi yacemin bkm naga almar bayamason hayaniya kwanan nan

Dady yabude baki zeyi magana kenan yaji sallmarshi

Atare suka amsa mishi yashigo wurin dady yanufa da murmushinshi ya kwantarda kanshi acinyar dady

Dady yadan shafa mishi kanshi tareda fdn my son naga karamene meke damunka ? pls karka boyemin


Murmushi *annur* yayi tareda dago kanshi cikin nuna alamar bakomai yace dady bakomai

Dady yadanyi murmushi tareda fdn Allah yasa hk ne yadago mishi kai tareda fdn waini yaushe my son zeyi aurene?......

Kubiyoni asannu zakusha lbr πŸ˜‰
LUV U ALL 😍😘


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI πŸ“
[7/12, 9:26 PM] Sis Grp: πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘

{7/7/2017} 1: 30 pm


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“


PAGE1⃣9⃣

Cikin mamaki yajuyoda fuskar tashi ga dadyn nashi fuskarshi daukeda alamar tmby

Kamar dady yasan abinda yake sakawa azuciar tashi yadaura mishi bayani

Dady cikin nusuwa yace tareda kallon kofar gidan wannan gidan malaminane dayakeyimin saukar alqur'ani aduk abinda zanyi don samun haske

Shide annur yayi mamaki matuka da HK yafito tareda budewa mahaifinnashi murfin motar yafito cikin shigar alfarma zauren gidan suka nufa nande almajiran sukace masa yana cikin gidannashi daya daga cikinsu ya mike yashiga gidan yafada mishi yanada baki yace ayi musu iso cikin dakin har dakin yanuna musu sukashiga cikin sallama yana zaune akan katuwar daddumarshi yana rubutu da tawada a allo da fitilar kwai agefenshi

Yayi musu izinin suzauna Dan yagane adalin talakawane mutumin kwarai nande suka gaisa cikin girmamawa dasanin darajar junansu annur yasugunna yagaidashi ya amsa cikin jin dadi

dady yace mishi tilon dannawane Malam sunanshi sulaiman

Malam yace masha allahu Allah takwaranane ma allah yakara mishi albarka

Dady yaji dadin addu'ar tashi ya amsada amin

Malam ya cigabada cewa yaushe kadawo daga tafiyar?

Dady ya amsada kwanana 2 Malam nagode da addu'ur'i wlhy ina ganin cigaba Allah yakara kusanci da shugaban halitta

Malam ya amsada amin amin

Sukade cigabada tattaunawa akan cigaban da dady yake samu asanadin addu'ur'in da akeyi mishi shi kuwa dady se godia yakeyi taredayiwa mlm addu'a

Shiko annur kawai binsu yakeyida ido


Batasanda mutane adakin baban nataba kasancewar sun shigada takalmansu tadan ciki dakin

Sallama tayi tareda shigowa dakin abban nata

tanasako kannata cikin dakin idanuwannashi suka dira azukekiyar surar tata sanye take cikin atamfa me ratsin fari da pupple rikada siketne dinkin shoki yayi matukar fitoda surar jikinta dinkin tayane kanta mayafi black (hmmm yanda kukasan inkashe mata selfie) daidai kan hips dinta idanuwannashi suka sauka wani shokin yaji yaratsashi dasauri yakai idanuwannashi har zuwa kirjinta nanma wata duniyar yafada nanda nan yakai idanun nashi masu Neman gusar mishi da hankalinshi zuwakan fuskarta (hmmmmmm) ainanma kara gigicewa yayi Dan fuskar tata se sheki takeyi don kyau gawani annuri tana fitarwa

Cikin sauri tajuya dabaya zata koma don batasanda mutaneba aciki

Malamne yadakatarda ita da fadin ..............

*inajiran shawarwa warinku*


LUV U ALL😍😘


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“
[7/12, 9:26 PM] Sis Grp: πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘

{7/7/2017} 4:pm


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“


PAGE2⃣0⃣

Shigo mana me nasara

Dawowa tayi idanunta akasa tasugunna ta gaidasu kasancewar bawadaccen haske adakin batamasan kosu wayeba

Cikin jin dady ya amsa mata tareda tambayarta yakaratu

Ta amsada alhmdllh

Malam yace yatace sunanta *inteesar*

Dady yasa mata albarka

Taji dadin albarkar dayasa mt

Malam yadawo da idanunshi kanta cikin kulawa yace ya akayine me nasara?


Cikin ladabi tace abbah dama zan tambayekane akawo maka abinci?

Malam yace ehh takawoma bakinshi

Tacew tohnm tareda mikewa tafice

Ba afi minti 5 ba tadawo tadire musu katon tire me daukeda kuloli guda 2 da pleats 2 spoons 2 da juk medaukeda kofuna 2

Malam yasa mt albarka

Tafice abunta

Malam yace bismillanku kuci abincin

Dady yace alhmdllh

Malam yadawoda kanshi kan *suleiman* tareda fadin bismillah dan albarka

Haka kawai yatsinci kansada son cin abincin

Katuwar kular ya bude tuwone annadeshi aleda yadau pleat yasa Leda daya yabude dayar kular miyar kubewa danyace yasa yadau spoon yafara kai lomar tuwun hmmm nanfa yagigice da dadin girkin agaskia dande kada ace yayi santi daseyace betaba cin abinci me dadin wannanba be ankaraba yacinye tuwunnan tsaf ya ajiye pleat din tareda godia ga Allah yabude juk din yabude yazuba ruwan adan karamin kofin yasha shi kanshi ruwan dadinshi dabanne

Sukuwasu Mlm da dady sunata hirarsu kasancewar dady baya boyewa mlm komi

Yanata santin girkin harsuka kammala suka fito mlm yarakosu har kofar motarsu

Dady yaga wasu almajirai sunzo fitowa yakirawosu sukazo cikin ladabinsu

Yabude musu but din motar sukarinka fitoda buhun shinkafa babban buhu buhu 5 katondin Talia 10 da macaroni 10 shima se babban galandin mangyada galan 2 se manya shima galan 2 dady yabasu izini sushiga dashi cikin gidan

Shide Malam yasaki baki yasaba mishi irin wannan kyautar bayaso amma

Bayansun gama shigarda dakayan

Mlm yace agaskia hidimar nan tayi yawa karage

Dady yace ko daya aikawuce hk awurina

Mlm yayita godia dasa albarka

Dady yasa hannu a aljihu yaciro kudi yan dubu2 bandir 3 yabama mlm

Nanfa mlm yaki amsa

Seda dady yace ayi sadaka sannan mlm ya'amsa yayita samasa albarka

Suka shiga cikin motar *annur* yatada motar sukabar unguwar shikuma mlm yakoma gida yaci gabada rubutunshi a allow

Ahankali yayi hon cikin hanzari get man yawangale mishi get din yafaka motar a inda aka tanada don faka motocin gidan yabudewa dady yafuto yanufi bangarenshi shima *annur* yanufi nashi bangaren

Wajan karfe 12 nadare Kwance yake akatoton gadonnashi juyi kawai yakeyi amma zuciarshi cikeda tunaninta surarnan tatase gizo takeyi mishi

YASALAM! Waini meke neman samunane kullum cikin tunaninta meyasa bantabajin sha'awar wata diya maceba se ita? Abinda yaketa tmbyr kanshi kenan har wajan asubahi da hk yamike yadauro alwala yayi raka atanil fajir sannan yatafi masallaci yayi sallar asubahi yadawo yakwanta ba jimawa bacci yayi awon gabadashi

Ringing din phone dinshine yatasheshi daga daddadan baccin dayakeyi tareda daddadan mafarkinta

Cikin bacci ya kara wayar tashi akunnenshi muryar dayajine tabakanta mishi zucia cikin lokaci kankani yabata fuska cikin matsifa hadida bala'i yace................

*kubini asannu kusha lbr*πŸ˜‰

*ina jiran shawarwarinku* ga number dina 08106462493


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘

{6/7/2017} 4:54 p.m.


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“


PAGE1⃣8⃣

Dady yadanyi murmushi tare da fadin Allah yasa hk ne yadago mishi dakai tareda fadin waini yaushe my son zeyi aurene?

Cikin jin kunya yadan sosa keyarshi tareda kara sunkuyar da kanshi kasa alamar kunya amma azuciarshi tunanintane yafado mishi zucia ita kadai yataba jin yana fatan kasancewa da ita har abada muryar momyce tadawo dashi daga tunanin daya afka

Momyce ta amsheda alhaji kenan nima kullum cikin son inga jikokina nakeyi kumaga yarinyarnan Yar aminiyata hajia samira semuyi yar gida

Wani malolon bakincikine yatokare mishi zucia ko sunanta bayason a ambata mishi

Dady yace au hakane my son kunma shirya kanku kenan ?

Dasauri ya amsheda nifa dady banasonta wlhy batada tarbiy.........

Dasauri momy tatari numfashinshi tareda fadin toh wakakeso? Inde kaga baka auri yarinyarnanba toh bana rayene shirmen banza kawai tanakaiwanan tamike tabar flon tahaye sama zuciarta acushe

Dadyne yadawo dakanshi ga tilon dannashi tareda fadin fadamin kanada wadda kake sone my son?

Cikin jin kunya yace dady inada wadda nakeso amma bamu daidaitaba

Dady yace Allah yadaidaitaku

Annur ya amshe da amin

Nande sukaci gabada hirarsu cikin soda kaunar juna kafin DG misani se dady yahaye sama shikuma annur yanufi bangarenshi

Yauma kmr kullum juyi kawai yakeyi akatafaren gadon nashi kyakyawar surar tata se gizo takeyi mishi kullum tunanin nata kara yawa yakeyi azuciarshi {hmmmm nidai ina tunanin wani Abu πŸ€”} da kyar bacci yayi awon gaba dashi amma zuciarshi cikeda kaunarta

Yau kwanan dady 2 da dawowa da daddare bayan sallar isha'i dady yakirashi awaya tareda neman yashirya suje yarakashi ya amsa da toh

Cikin manyan kaya yashirya yafito se zuba kyau yakeyi da kamshi
Daidai lokacin daya fitoma mahaifinnashi yafito atare suka shiga katuwar mota me bakin gilashi annurne yake tuka motar shikuma dady yanayi mishi kwatance

Cikin mamaki yaga ya iso kofar gidan nasu dady yabashi izinin yafaka motar tashi

Hmmmmmmm koda abacci yatashi baze manceda gidannasuba cikin mamaki yajuyoda fuskarshi ga dadyn nashi fuskarshi daukeda alamar tmby............


Karku gaji kubini asannu kusha lbrπŸ˜‰


*kuyi hkr masoyana narashin jina wajan 2 mouth don Allah kusani a addu'arku *

Luv u all😍😘

πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘


{23/7/2017} 8: 2 AM


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“

PAGE2⃣2⃣

Zaro idanu inteesar tayi tareda fadin nashiga ukku meyakaini grp din manya hk gaskia fita zanyi

Khausar tace wlhy idankika fita koh hmmmmmm...........

Inteesar tasanme hmmm din aminiyar tata yake nufi don hk tace shikenan yi hkr zanzauna amma GRP dinna yayan masu kudine *ukti*

Khausar tace da talaka da me kudin wayayisu?

Inteesar tace Allah

Khausar tace tokingani karkifita pls

Inteesar tace toh shikenan

Khausar taci gabadacewa kiyi introducing kanki a GRP din harda pic dinki zaki tura

Inteesar takara zaro ido kirufamin asiri wlhy ko mgn baniyi a GRP din

Khausar tayi tayi da ita taki hk takyaleta

*Abangaren gidansu khausar*

Kwance yake zuyi kawai yakeyi adoguwar gujerar dake dankareren falon dayasha kayan alatu kudi sunyi ihu afalon.
Kullum tunaninta kara daduwa yakeyi azuciyar AHAMAD wlhy yanaji akasan zuciarshi inya rasata zeshiga wani hali yasalam dama HK son yake yahana mutum sukuni ya ubangiji ka taimakamin in sami kyakyawar bbyn nan wayarshi yadauko yafara kallon pic dinta koze samu sassaucin sonta azuciarshi hmmmmm wani turiri yakara tasowa nasonta ganin kirar jikinta agaskia Wanda yamallaki bbynnan bashi ba bakin ciki ko kallon wata wayar ya manna agirjinshi yana murmushin kaunah( nima hk nakewa Aunty Bilkisu murmushin so da kauna)

*BARI IN WAIWAYI INDA BANTABA WAIWAYABA S@UDI@*

Wata zukekiyar matace kyakyawa me karamin jiki ga diri komi yaji ajikinta tanada gashi matuka yala- yala irinna larabawa tana sanyeda kayan barci pink sun amsheta tana kwance amalelen gadonsu agefen damarta wani farin balarabene yana sanyeda kayan bacci bacci sukeyi bilhakki

Afirgice matarnan tafarka tana fadin wayyoni diyata karku tabamin ita kutaimaki rayuwata jininace wlhy ita kadai namallaka shikenan sunason kasheta wayyoni allah nah! dukcikin harshen larabci taken fadin hkn

Jin ihunnatane yafarkar dashi daga barcinshi afirgice yafarka yakamota yarungumeta ajikinshi yanayi mata addu'ur'i haryana samu tadawo daidai

Tana zubda hawaye tace cikin harshen larabci wlhy abbu hummaira diyata bata mutuba wlhy tananan daranta katashi yanzu muje anemomin diyata kar akashemin ita wlhy nima mutuwa zanyi tafashe dawani kuka meratsa zucia

Cikin muryar rarrashi yace haba aneesaty khalbi kwantarda hankalinki kisamu nusuwa pls

Takara fashewa da kuka nizanje innemota tafadi hkn tareda zare kanta daga jikinshi...............


*tirkashi abun babbane ni @DEH kubini asannu kusha lbr*

*Gaisuwar ban girmaga masoyana bazaku lissafuba akullum inasamun kiranku dasakonninku kuyimin hkr bawanda banasamun dmr replying amma kusani kuna ran sa'adah duk zanhadaku da ANNUR amannama kowa koda 1 million ne kuyi manage*πŸ˜œπŸ˜‚

LUV U ALWAYS 😍😘


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘

{21/7/2017} 6:43


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“


PAGE2⃣1⃣

Wani irin rashin hnkl ne yake damunki Lpy zaki Kira mutum da sassafannan?

Adaya bangaren ta amsa cikin kissada iya salon mgn haba habibi danna kiraka lefine?

Wani uban tsaki yaja hadi da fadin ina sammanin kinada tabun hnkl fa'iza yana gama fadin hkn yakarajan wani tsakin hadida kashe wayar gaba daya kaitsaye bathroom yafada

Wani uban kara tasaki me daukeda kuka hadida jefi da wayar tata

bashiri hajia samira tasauko asaba'in kdn yarage taci tuntube wurin saukowa daga benan karasowa hadida rungume diyar tata fa'iza mekikewa wannan uban ihun da sassafennan?

Wani kuka nabakin ciki ta sake saki cikin kukan tace momy wlhy mutuwa zanyi! Wlhy momy mutuwa zanyi!! Nanma takara sakin wani sabon kukan

In hnkln hajia samira yafi dubu toh yatashi taka a diyar tata ta girgizata don atunaninta bata hayyacinta kee dawo hanklnk fadamin menene?

Cikin kuka taci gabada fdn wlhy mom idan banmallaki zuciarshiba idan bn aureshiba wlhy zaku rasani don rayuwata batada amfani shine rayuwata tana kaiwanan takara fadawa jikin uwar tata

Hajia samira tagane inda diyar tata tasa gaba kamota tayi tarungumeta ajikinta akunne take rada mata kwantarda hankalinki autata Ai kmr kinsamu abinda kikesone inde kinadani kibar zubda hawayanki inyasan wata besan wataba nande tayita kwantar mata da hnkl tareda wani mugun kudiri azuciyoyinsu *shin wani kudirine???*(kubini asannu zakusha lbr)

Kwance take adakinsu kasancewar gidan babu kowa ynx iya sunsami wata dabi'a tafita yawo itada hafsat tana danna wayarta tahaukn yanar gizo kawai taganta awani GRP sunan grpdin tama rasa gane meyake nufi $.$.$. harzata fita grp din taga Number din *ukti* sekawai tafasa fita tabi *ukti* dinnata ta prvt taci sa'a tana online suka gaisa tajefo mata tmbyr wai *ukti* naganni awani GRP ne?

Khausar tace nice nabada lambarkmki yaron shugaban kasane yabude grp din.....................

*kuyi manage da wannan*


*gaisuwa ga masoyana ina ganin sakonninku da wadanda bana samun dmr reply duk ina gdy Allah yabar kauna*

LVU U ALL😍😘

πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIπŸ“
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘



{31/3/2018} 3: 47 pm


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI✍🏻




*Am back*πŸ’ƒπŸ» *ina masoya BOYEYYEN AL'AMARI gani nadawo muku da cigabanshi*



*Wayyoni wayyo allahnah ina zansa kaina masoya novels dina kuna nunamin kaunah wlhy kuna raina ina tabbatr muku ana mugun tare*😁🀝🏻



*Kut Dana mance dake ai gwara na mance komima kece sanadiyr cigaban wannan novel dakuke nunama kauna wannan page din nakine Mmn Jiddah ina yin ki over*❀



PAGE32⃣3⃣

Cikin hnzari yabita yariketa yana tofa mata addu'ar tareda lallashi ranarde azaune suka karasa kwana kowa hankalinshi atashe


*** ****
*Bari mukoma gida Nigeria*
**** *****


Yakasa gudanar da komi yinin yau ba dadi duk tunanin ta ya addabi zuciar gwarzon maza

Tashi yayi yashiga yadaura wanka yau ya kudiri aniar zuwa gareta

Cikin kananan kaya yashirya jeans blue riga white yayi matukr yin kyau tmkr akasar turai yafeshi jikin shi da turare yadauko mukullin motrshi yanajin wani irin nishadi

Futowa yayi kai tsaye bangaren mum yanufa

Tana gishin gide tana waya cikin harshen larabci dagaji da ummanshi ta saudia suke waya amma duk yanayin mum dinshi ya chanza

Seda yajira sukayi sallama sannan yagaidata ta amsa tareda manna mishi kiss akumatu

Cikin damuwa yake tambayrta mum menene naga duk yanayin ki ya chanza?

Cikin wani yanayi tace ummahnka ta saudia ce bata da lafia hawan jininta yatashi tanama kan gadon asibiti akan tunanin 6tr dinka


Cikin wani irin yanayi yace mum meya sameta ai 6tr dina tarasu


Kmr zatayi hawaye tace son kullum mum dinka ta saudia takasa hkrn rashin Humairah kullum cewa takeyi ita wlhy bata mutuba ta tabbatr tana raye😭


Shima damuwrce ta bayyana atashi fuskar ji yakeyi dama ace 6tr dinshi bata mutuba da yayi mata gata gata me tsanani amma kash ! Allah yafi mu sonta ya amshi kayan shi

Zaunawa yayi yana lallashin mum dinshi domin kuka tashiga yi sosai da kyar yasamu hawayen dake ambalia afuskarta suka tsagaita
Yadauki waya da niyar yakira ummanshi ta saudia mumta dagatr dashi tareda fada mishi tasamu barci kabari zuwa anjuma ka kirata


Ya amsa da tohnm mum pls kar kisa damuwa kinji mum

Ta daga mishi kai cikin wani yanayi


Ahaka yayi mata sallama yanufi hanyr layinnasu tin kafin yakaiga shiga layin ya hangota sanye da uniform din islamiyya da jakarta arataye tana tafia ahnkali fuskarta dauke da murmushi dukda ba kwallia tayiba tayi matukr kyau

Faka motr yayi dai2 saitinta domin yau yashiryama tararta yagaji da Rashin barci

Burki taja tatsaya don ganin wani me karfin halinne yasha gabanta amma takasa ganin na cikin motar domin bakin gilashi da aka kewayeta dashi tasaba ganin hkn domin babu ranar da zata fito bata hadu da samariba batade sauraransune


Bude marfin motr yayi tareda ziro hadaddun kafafunshi irinna yan Hutu

Tin kafin yakarasa fitowa kamshin turarenshi ya ruda dukkan lissafinta

Karasa futowa yayi nanda nan idanuwansu suka sarke dana juna wani irin kallo suka shiga yima juna kowa yakasa kauda idanuwanshi

Kallon sani *Inteesar* takeyi mishi kmr ta Taba ganin fuskar tashi

Kallon juna sukeyi tamkr masoya kowa yakasa kauda idanuwanshi.......


*kude yi manage din wannan kubini asannu zakusha lbr*πŸ˜‰


LUV U ALL😍😘


πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI✍🏻
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘



{4/4/2018} 3:35 pm



πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI ✍🏻



*Masoyanah masu yimin mgn da masu kirana dukna gode da kaunah*πŸ‘„


*Maman Shaheed nagode da novel dina yazama na farko dakika fara karanta littafin Hausa arayuwarki ngd da kaunar da kike nunamin*πŸ’ž



PAGE2⃣4⃣

Wani irin sako me wahalar misaltuwa *Annur* yafara aikama *Inteesar* ta kwayr idonshi


ita kanta tarasa gane dalilin dayasa taji wani Abu nabin jinin jikinta wani irin yanayi takeyi

Sun dau lokaci a haka



Wucewa yazoyi ya hangota Faka katuwar motarshi yayi yafito zuciarshi na wani irin bugawa isowa yayi inda suke yace cikin wani irin yanayi *Lafia inteesar kika tsaya naganki da uniform?


Afirgice suka dago atare kowannensu ba hk yasoba

Dagowar daza tayi wazata gani inba ya Ahamad ba dasauri cikin fara'arta tace ya Ahamad ina wuni?


Yace lpy q domin muryarta taratsa dukkan tsassan jikinshi


Yakara dacewa *Intee* time yawucefa me kikeyi anan baki tafi islamiyya ba muje nakarasa dake islamiyyan koh?

Tace tohnm ya Ahamad

Yawuce gaba yana yima *Annur* kallon uku saura gwata (nidai nace Ahamad adebi ahankali🀣)


Sauri takeyi tabishi abaya bata Ankara seji tayi jakarta ta islamiyya ta subuce tafadi


*Annur* dayake tsaye bakin ciki da tsanar Ahamad yayi mishi dirar mikia akahon zuciarshi. Yatsugunna yamika mata jakar ranshi adaure hakama fuskarshi adaure


Ta amsa tareda kallonshi cikin idanunta tace nagodeh tana fadin hkn tabar gurin tashige motar ya Ahamad yaja sukabar wurin


Yana tsaye ranshi adagule yama kasa daukar kafarshi bakin ciki ya cika zuciarshi wanene daze dauketa amota? Meye hadinsu? kode yana sontane?😒 yakasa lalubo amsa tambayarshi amma acan kasan zuciarshi tana fada mishi saurayintane domin beyi kama da saurayintaba

Da kyar ya iyajan jikin shi jiri na dibarshi yashiga motar yajawo murfinta ze rufe ya hango pos adan gefen motarshi nan tunani yafado mishi ya tabbatr da sanda jakarta tafadi yar pos din tafado

Fitowa yayi yadauki pos din yakoma mota yayi mata key

Kai tsaye gidansu yanufa yayi hon me gadi yayi saurin Bude mishi get din yana kwararo gaisuwa

Faka motar yayi aharabar gidan yafito yana tafia ahnkali zuciarshi ba dadi

Nanfa duk ma aikatan gidan sukazo suna kwararo gaisuwa kmr maroka ciro bandir din yan dubu daya2 yayi bandir hudu yamika musu Nanfa suka shiga jero godia cikin jin dadi kowa na yabon kyautrshi da kyaun halin shi (Nazunguro Mmn shaheed tare da fadin Halina yabiyo aiπŸ€“πŸ˜œ Saura kice karya nakeyi😎)


Be saurari dumbin godiar dasuke shararo mishi ba kai tsaye bangarenshi yanufa amma da kyar yake daga kafarshi

Yana shiga yahaye sama yafada bed room dinshi yanajin wani irin yanayi yafada katafaren gadonshi

Dakyar ya iya jan jikinshi yashiga wanka yafito yasa kaya marasa nauyi dai2 lokacin anfara kiran sallar la'asar yafito yatafi masallacin dake manne acikin gidansu



Tafia sukeyi bame yima wani magana shide Ahamad kishintane yadanne mishi kirji cande yace *wai menene hadinku da wanda naganku a tsaye?


Bata ankaraba se kawai jin tambar tashi tayi domin ta zurfafa atunanin tayi lattin zuwa islamiyya domin yau karfe biyu suke shiga makarantr yanzu tanada tabbacin karfe ukku tayi


Dawowa tayi daga duniar tunanin data afka tace *Ya Ahamad shine Wanda yataba bigeni kwana ki


Yadanji sanyi tareda fadin kin tabbata ba abinda ke tsakaninku?


Tace *eh bakomi ya Ahamad

Yadaura da cewa ammm pls karki kula kowa kinga ynxu karatu kikeyi koh?


Tace toh insha allahu ngd


Yace tayi mishi kwatancen mkrntr tasu tayi mishi yakaita yaciro dubu Dari yabata yace tahau keke napep yayi2 da ita taki amsa hakanan ya hkr yaja motrshi yabar harabar mkrntr


Karfe shida dai2 aka tashesu

Kai tsaye gida tanufo

Ta iso da sallamarta malam na zaune azauro tagaidashi ya amsa taredayi mata ban gajiya

Ta isa cikin gidan da sallamarta

Iya na zaune kan tabarma hafsa na kwance akan cinyarta tasa waka tanaji

Nashigo ko sallamarma sun kasa amsamin

Natsugunna nagaida iya ko amsa wa batayiba takara cokalo dangwalinta gaba2 tace *ke dan kan ubanki matsonan


Jikina har rawa yakeyi namatsa

Iya ta daga hannunta ta yarfamin mari

Seda na zauna domin marin yashigeni

Takara kaimin rankwashi tana fadin shigiya fuska kmr ta aljanu dan ubanki dazu hafsat tace ki wanke mata dan kanfanta da rigar mama kikace bazaki wanke ba waye ubanki yau senaci ubanki kuma kinjama kanki wlhy

Kuka kawai nakeyi domin ni yau hafsat batace nayi mata wankiba

Iya taci gaba da cewa *se an fara mgn kirinka tsun2 da kai kmr mumina to wlhy yau se kinyi wankin gidan nan duka harda nawa maza hafsat tashi ki kwaso kayan naki wlhy ko zatakai biyun dare seta wanke kayan nan maza tashi..........


*Ko a ina masoyi yake yafi makiyi don hk ina mugun sonku masoyanah*πŸ‘„



LUV U ALL😍😘



πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI✍🏻
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘



{10/4/2018} 5:02 pm



πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI✍🏻





*Gaisuwar ban girma gareki YAR MUSA ngd da kulawarki wannan page din nakine kina raina ina kara tabbatr miki ana mugun tare* πŸ€πŸ»πŸ‘„



PAGE 2⃣5⃣

Mikewa Hafsat tayi da uban matsassan wando se uban fari takeyi da idanu kmr wata me kyau tace *wlhy ko zaki mutu sekin wankemin kayannan shegia mayyahπŸ˜‚ tana fadin hkn tafada dakin nasu tana murgude murguden duwawu😜


Nidai bnce komiba ina tsugunne hawaye nazuba a gwayr idanunaπŸ˜₯


Iya nafadin kozaki mutu dan kuka sekin wanke kayannan *INTEESAR*

2 Comments On BOYEYYEN AL'AMARI
avatar
nafeesat-yusuf

1 year ago

Reply

Continuenation pls

avatar
shuraihu

1 year ago

Reply

Replying to nafeesat-yusuf

We will complete it soon Insha Allah

Please Login or Register in order to submit comment