Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nassn inteesar yarinyar kirkice ai amma kinsan wannan marikiyar tata muguwace naji labarin malam yabace ankai inteesar aikatau ince dai ko ke yar uwartace koh? (kunsan wasu tsofaffi da surutu fadi ba a tambayekaba)

Innalillahi wa'inna ilaihirraju'unπŸ™†πŸΏβ€β™€khausar ta ambata hawaye nafin kuncinta😒 cikin sauri tamike tabar gidan tsohuwar nata kwala mata kira amma ina bata cikin hayyacinta

Kai tsaye gun motarta ta nufa cikin sauri tafigi mottar hankalinta atashi idanuwanta nata barin kwalla😭



** ** **
Dukkansu atsaye suke agaban bokannasu suna bashi bayani Hajiya samira ce tadaura dacewa *Boka nifa abun yana bani mamaki nasan aikinka kmr yankan wuka yake amma ka kasa aiki akan yaronnan anayi tamkar ba'a yiba

Wata uwar dariya bokan yayi tareda cewa ai ansamu matsalane adawowarshi be sauka agidan da kukasa layoyinba ko kafarshi be bari yataka gidanba shiyasa aikin ya warware

Marairaice fuska fa'iza tayi tareda cewa *ka taimakamin boka wlhy inasonshi sonshi ajinina yake

Bokan ya kwalkwale da uwar dariya yace *Karki damu yarinya........ nan yashiga wani kirari irin nasu na yan tsubbu cikin minti biyar sega wata kwalba tafaďo akan hannun bokan nanma yakara tin tsirewa da dariya kana yamikawa fa'iza turaren yace duk randa zasu hadu dashi tashafe jikinta da turaren kuma ta tabbatar yaji kamshin turaren inhar yaji kamshin turaren shikenan ze zama rakumi da akala

hannu na rawa fa'iza ta amsa tashiga jero godiya nan suka aje mishi uban kudade kana suka kama hanyar inda sukayi parking din motarsu



** ** **
zaune yake akayataccen office din baturen dake wani katafaren asibiti akasar America cikin harshen turanci suke magana yana zayyano mishi yaddda yakejin mararshi na kullewa.......nan likitan yasa akayi mishi gwaje2 toh abu na kudi cikin kankanin lokaci result yafitoh likitan ya tabbatar mishi da yanada matsananciyar sha'awa sperm yatarun mishi amara yana bukatar mace yayi gaggawar nemawa kanshi mafita tin kafin abin yakaishi ga kwanciyar asibiti

Shide *Annur* kallon likitan kawai yakeyi amma zuciarshi na tunanin tohshi wace mace zai tare da ita mace dayace kullum take tada mishi feeling ko tunata yayi seyaji sha'awarshi tamotsa ita yake fatan mallkawa sirrikanshi........... sosai yayiwa likitan godiya sannan yawuce gidanshi cike da tunani nan ya zartar kawai gobe gida zaije idanuwanshi nakwadayin ganinta....... nan yasa masu tsaronshi suka fara shirya mishi komi nashi a pilot dinshi

Haka kawai ya tsinci kanshi cikin nishadi nan yakira mommy awaya yasanar da ita gobe zai diro nigeria

Mommy taji dadi sosai nan tashiga mishi addu'ar allah yakawoshi lafiya

cikin farin ciki yakatse wayar yakira umminshi ta saudiya nan suka shiga hira ita kanta tayi mamakin yadda taji *annur* din nata cikin farin ciki se itama ta tsinci kanta cikin farin cikin



** ** **

su *inteesar* anzama yan gida acikin kwanaki kowa yazo gidannan zai gane ansamu canji sosai domin *inteesar* ba bayaba wajen iya gyaren gida ga tsafta uwa uba iya girki tinda tayima Mommy wani drinks mommy tasha taji bata taba shan drnks me dadi ba kmrshi aiko nan mommy ta tambayi baba talatu wayayi baba talatu tace *Inteesar* ce aiko nan mommy tace taji dadi sosai tace daga yau ita zata rinka mata girki da wadannan lemukan masu dadin gaske nan mommy tabada kudi dubu hamsin direba da baba talatu sukaje kasuwa suka siyo mata kaya masu matukar kyau atampopi da shaddoji da dogayen riguna aka bada dinki seda aka dinko sannan baba talatu tawaba *inteesar* din aiko tarinka godiya taje tayiwa mommy godiya sosai mommy takejin yarinyar dukda ta tsani talaka amma tana dan jin yarinyar awani bangare na zuciarta

Abu dayane yake damun *Inteesar* takasa mancewa akullum setayi kukan rashin ganinshi da batayiba hnkalinta akullum yana kanshi wato mahaifinta takan kebance kanta tayita kuka in baba talatu taganta tayita rarrashinta domin itama allah yasa mata son yarinyar hakan yasa suke kwana daki daya da ita bata barinta cikidamuwa kullum cikin debe mata kewa take dukda bata san labarintaba amma tanaji ajikinta itadin ni'imace

Allah yasama *inteeaar* son baba talatu saboda bata barin zubar hawayenta takan kwantar mata da hankali aduk lokacin data ganta tana tunanin wani abu dukda tasha tambayarta meke damunta amma *Inteesar* takasa sanar da baba talatu damuwarta

acikin kwanaki biyu *Inteesar* takara fari tayi yar kiba hips dinta yakara fitowa kullum tana sanye da hijjab koda tana aikine da hijjab dinta ajikinta baba talatu tayi2 da ita amma bata cire hijjab hatta barci in zatayi da hijjab take kwana

Dukda haka allah be hana baba talatu gano irin ni'imar kyaun da allah yama surar jikin *inteesar* dinba domin hips dinta baya boyuwa ko ahijjab din suna bayyana kyansu

Sanye take cikin doguwar riga kalar yellow da ratsin baki da fari ajiki daya daga cikin rigunan da aka siyo matane tasa hijjab baki da ratsin fari ajiki ba wata kwalliya tayiba amma tayi masifar kyau

tana shirya abincin yamma baba talatu tana zaune se dayar me aikin wadda ake cewa ma'u ita kuma tanata wanke2 tana goge kwanukan sauran masu aikin suna bangarensu suna dan hutawa wasu kuma suna cikin gidan suna gyaro gidan

sanye take da riga da siket na material me ratsin green da white ajiki kayan sun matukar mata kyau hannunta rike da wayarta iPhone10 Shigowa cikin kichin din tayi ......da sauri baba talatu tamike tare dacewa ranki ya dade dakin kirani ai

Mommy tace no bakomi kujera mommy tasamu tazauna nan masu aikin suka shiga gaidata harda Inteesar cikin isa ta amsa tareda musu barka da aiki

Kana takai dubanta kan baba talatu tace *talatu gobe shalelen naki zai dawo da allah kibada mukullin bangarenshi me gyaran bangarenshi zaizo ya amsa dama shekaran jia aka canza komi na bangaren da allah kiduba komi yatafi dai2 kinsan halin kayannawa beson kazanta

Baba talatu cikin murna tace *toh ranki ya dade mutan amerika allah yakawosu lafiya

Mommy tace amin and ahada mishi abinci sosai kinsanshi baya wasa da cikin shi don allah kada abata mishi rai amishi me dadi ina wannan yarinyarnan me take da suna

Baba talatu tace *inteesar*

Yauwa dan allah tamishi abincinnan nata me dadi da drinks din datake hada mana

Baba talatu tace angama ranki ya dade

Mommy tamike tare dabude friji tadauko drinks din da inteesar ke hada musu arobar faro mommy tabude tasha kana ta daura dacewa ki duba abinda babu kiyiwa direba magana yasiyo muku (tana fadin hakanne tareda niyar barin kichin din)

Baba talatu ta amsa da toh ranki ya dade.......



LUV U ALL😍😘



πŸ“šSA'ADATU BINTU BINTU ABDULLAHI✍🏻
[12/7, 10:11 AM] mmn usman grp: πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYE AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘



{19/7/2018} 6: 47 pm



πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI✍🏻



*comments dinku yana karamin karfin guiwa nagode rabbih yakara dankon love* *one love*πŸ’‹



PAGE 3⃣9⃣

Nan tashiga duba abinda babu taje tasanar da direba cikin mintuna ashirin aka kawo komi aka yi mishi mazauni amazauninshi nama kuwa kowanni nama da frizarshi komi na bukata seda aka tabbatr da an tanadeshi

Sannan baba talatu ta tsaya aka gyare bangaren *annur* din aka sanya turaruka

*inteesar* tagama hada abincin dare aka kwashe aka kai kan daining ta dibar musu nasu itada baba talatu tasawa sauran masu aikin nasu suka kwashe suka kai nasu bangaren aka gyare kichin din tsaf lokacin an fara kiraye kirayen sallar magrib nan kowa yawatse yanufi bangarenshi don gabatar da salla

Suna shiga bangarensu kai tsaye drowar kayanta *Inteeaar* tanufa tadauko riga da siket din atamfa me ratsin orange da blue ta dauko hijjabi blue tanufi bandakin dake manne abangon dakin

Baba talatu ta kalleta ta girgiza kai taredacewa allah ya kyauta miki yannan kedai ko kayan bakya iya cirewa agaban mutane sedai kiyi wanka abayi kisa kaya abayi kullum kina fama da uban hijjabi sekace matar liman.......

itadai *Inteesar* tana jinta harta karasa shigewa toilet din....... cikin minti goma tagama tayi alwala tafito sanye da riga da siket din atamfar ta zumbula hijjabinta har kasa sekace me shirin zuwa unguwa...... 🀣 Akan dadduma tasami baba talatu tana lazimi wadda tafita tayialwala atoilet din dake waje

Shafa mai *Inteesar* tayi tadan shafa powder kadan tareda man baki ta dan fesa turare kana tadauko dayar daddumar tashimfida akusa da baba talatu tagabatr da sallar magrib tareda jero addu'ur'i aciki harda addu'ar allah yahada fuskarta data mahaifinta 😒

Seda suka gabatr da sallar isha'i da shafa'i da wutiri sukayi lazimi kmr yadda suka saba sannan *Inteesar* tazubo musu hadaddiyar jalop din shinkafa da wake wadda taji kifi bushashe se kamshi take zubawa ta zubo musu farfesun naman kazan asaman shinkafari

Sunaci suna hira sama2 *Inteesar* ce tafara cire hannu tasha lemun kwakwar data hada musu

kallonta baba talatu tayi kana tace kai yarnan bade kin koshiba?

*inteesar* tayi murmushi tareda cewa nakoshi baabaa

Taba baki baba talatu tayi tareda cewa ke kam yarinyar nan kinada abun haushi kwata2 bakyason cin abince kedai gakinan ne

Itada batace komiba taje bandaki tawanke hannunta kana tadawo tazauna kusa da baba talatun tana jira takarasa takwashe kwanonin

Seda baba talatu taci takoshi tayi nak takora da sansanyan lemun kwakwar me dankaren dadi tanasha tana santi tace * Waini kam yarnan kodai kinyi makarantar girki ne? gaskia kin iya girki wlhy in takaice miki ban taba cin abinci me dadiba seda kikazo gidannan ke kam kin godewa allah ga kyau kmr yar larabawa
ga iya girki kuma

Dariya *Inteesar* tayi sosai harda rike ciki sannan tace *kai baabaa seda kika gama cin abincinki ashan drinks sannan kike santi ko insa miki waigine 🀣

Itama dariya tayi sosai *wlhy kuwa yar nan da gaske nake miki ke nifa tin tini naga kinamin kama da wata adangin hajiya amma wlhy na mance wacece

Dariya inteesar tasakeyi sosai dan ita kawai tasan santi baabaa takeyi...... seda tagama tsaf sannan takwashe kwanukan takaisu kichin din dake nan bangarensu ta wankesu tsaf sannan tadawo suka cigaba da hira da baabaa talatu tana bata labarin yadda hajiya da alhaji keji da dansu tilo *Annur*

Da aka ambaci sunan seda gaban *Inteesar* yayi wani mummunan faduwa amma takasa gano meye dalilin faduwar gabannata...... haka kawai tatsinci kanta dason jin hirar guy din

Aiko kmr tana ziga baba talatu se zuba mata labarin *Annur* din take tareda rokonta tashirya mishi abinci me dadi in allah yakaimu gobe......... se wajen goma suka kwanta domin gobe tashin asuba zasuyi saboda bakaramin girke2 za ayima shalelen gidanba

aiko tin asuba suka tashi sukayi salla inteesar tayi wanka suka shiga kichin da dukkan yan aikin gidan kowa yakama nashi aikin

Nan inteesar tashiga hada abun brkfst amma tariga ta rarraba duk wani abu datake bukatr ayanka mata na fannin girkin *Annur* sauran yan uwanta masu aiki sunata tayata hatta baba talatu seda tasa hannu anata aiki bakama hannun yaro

Ruwan lipton wanda yaji kayan hadi Yanata tafarfasa se kamshi ke tashi a kichin din tajuye a plast tashiga soya dankalin turawa da wainar kwai da kunun gyada da kosai da doya da kwai kai harda abincin turawa wanda ni kaina ban sansuba

Se wajen goma aka gama komi aka hada akan daining table

Goma da minti goma mommy tafito daga bangaren dady kai tsaye kichin tanufa nan ta tadda aiki kace2 anata kiciniya masu aikin suka shiga koro mata gaisu tana amsawa cikin isa da kasaita

Baba talatu takalla tareda cewa ashirya komifa da allah yama taho yana hanya amma yacemin zai biya gun wani abokinshi dan haka zai kai 2 na rana sannan zai iso plx ayi komi atsanake

Baba talatu ta tsugunna tareda cewa toh ranki ya dade allah ya tsareshi

Mommy tace amin... kana tajuya tanufi hanyar fita se kuma tajuyo tareda cewa *Naga an aje mana brkfst afalona kisa akawo mana falon Dady

Baba talatu tace angama gimbiya........ cikin minti biyar tasa aka kwashe komi aka kai bangaren dady

Kana suka dawo suka karya amma seda baba talatu tayi da kyar sannan *inteesar* ta tsaya takarya

Seda inteesar tayi iya bakin kokarinta tahada mishi abincin gargajiya kala biyar irin na gani na fada dinnan sannan abincin turawa kala bakwai se abincin larabawa kala hudu ga drinks iri daban2 kala goma (nasan masu karatu zasuyi mamakin yadda *inteesar* ta iya girki toh karku mance tana karance2 na littafin girke2 hkn yasa ta kware agirki iri2)

Zuwa karfe daya da rabi an shirya komi a daining area abangaren mommy (seda baba talatu ta tambayeta tace ashirya komi abangarenta)

aka turare ko ina na gidan da turare hatta kichin seda aka wankeshi da sinadarin kamshi akasa turare irinna sudan me dankaren jamshi ko ina agidan seda yayi tsaf hatta mommy sedata jinjinama *inteeaar* domin taji dadi sosai

Dukkan masu aiki kowa yakoma bangaren dayake domin su gabatr da sallar azahar hk suma su *inteesar* itada baba talatu kai tsaye ban daki *inteesar* tafada domin duk tagaji wankan take bukata ita dama baba talatu tafison bayin tsakar gida shi tanufa don yin alwala



Sanye yake cikin yadi ash colour wanda yaji aiki awuya da hannu kayan sun matukar fito da kirar jikinshi da tsantsagwaron kyawunshi yayi kiba se sheki yakeyi babu hula akanshi gashin kanshi har sajen fuskarshi ya kwanta yayi luf wayyo allah nah naso ku ganshi fans😜

Ahankali yake saukowa daga matakalar jirgin yana wani barin murmushi sosai yake kallon gidan tamkar yashekara dari baya gidan

Masu take mishi baya sunata kwasar kayanshi suna kaiwa bangarenshi

Kai tsaye bangaren mommynshi yanudfa domin yana kwadayin ganinta

Taji alamar saukar pilot dinshi dan haka tana shirin saukowa kenan daga matakala yakaraso da gudu ya rungumeta yanajinshi tamkar jariri

Momy taji dadin ganinshi tankar ta maidashi ciki takeji gashi taga yayi kiba ta manna mishi kiss agoshi tareda mishi ban gajiya takama hannunshi suka nufi bangaren dad dinshi shiko babu abinda yake kallo se yadda tsarin gidan ya canza ga wani sihirtaccen kamshi me rasa zuciya yana tashi shakar kamshin yake yana lumshe ido zuciyarci na mishi wani irin bugu ahaka har suka isa bangaren dad dinshi



πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI✍🏻
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYE AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘



{26/7/2018} 4:37 pm




πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI ✍🏻



*Plx auntynah zuwairat ummu maryam kiyi hakuri ki kara hakuri ta hannun damana ni nasan kedin kainuwace dashen allah........*πŸ˜πŸ’‹



PAGE 4⃣0⃣

Daddy yana zaune yana kallon news atashar aljazera suka shigo falon da sallamarsu

Da gudu *Annur* yakarasa yarungume dad dinshi cikin murna

Daddy cikin murna ya rungumeshi...... sosai suka shiga murnar ganin juna itadai mommy tana zaune tana kallonsu tana murmushi azuciarta tana addu'ar allah yanuna mata ranar dazataga jikokinta..... Sun dau kusan minti ashirin suna hira shida daddy akan compan dinsh na kasar dayaje nan *Annur* yashiga bashi labarin cigaban daya samu...... seda mommy tayi mishi magana yaje yayi wanka yasauko abincinshi najiranshi

Mikewa yayimi yanufi bangarenshi.... cikin 30 mnt yayi wanka yashirya cikin kananan kaya yagabatar da sallah kana yanufi bangaren mommynshi

Yana isa kai tsaye daining area yanufa nan kamshin abincin tin kafin yabude kulolin sun fara kai ziyara ahancinshi sosai yakosa yafara cin abincin domin ya tabbatar abincin zaiyi dadi...... daya daga cikin kujerun yaja yazauna tareda danna lambobin mommynshi yasanar da ita yakammala komi yana falonta

Cikin minti biyar ta iso falon wurin dayake tanufa taja kujerar kusa dashi tazauna tana kallonshi cikin so da kauna

Shagwabe fuska *Annur* yayi tareda cewa * mommy wazaiyi saven dina?

Murmushi tayi tareda cewa * Waya saba saven dinka inba baba talatu ba bari akira maka ita. tadauki wayarta tayi dailing lambar baba talatun ringin daya ana biyu *Inteesar* tadauki wayar takara akunne

Mommy tace *Ina baba talatun?

*Inteesar* tace yanzu ta tada sallah

Kai tsaye mommy tace toh *Annur* ne zatazo tayi saven dinshi gashi yanajin yunwa inta idar ki sanar da ita

Cikin girmamawa *Inteesar* tace toh ranki ya dade...... kit mommy takatse wayar

Kallonta *Annur* yake tayi tin farkon fara wayar tata tana katsewa yayi charab yace *Wai mommy bata nan ne?

Mommy tace *No son tana sallah ne bari ni nayi saven dinka koh? tafadi hakan tareda mikewa tadauki plate

Sosai yaji dadin hakan domin tin tasowarshi mommy bata taba saven dinshiba se yau *No mommy ki barshi zan jirata ta idar barima naje bangarenta dama idanuwana na mararin ganinta nayi missn dinta

Komawa mommy tayi tazauna tareda cewa Toh son adawo lafiya

Mikewa yayi tareda daukar wayarshi yanufi bangaren baba talatun amma yarasa dalilin dayasa kirjinshi ke mummunan harbawa...... da sallamarshi yatura kofar dakin aiko seya jita abude kai tsaye yashiga

Tana zaune akan dadduma ta idar da sallar kenan ita kuma *Inteesar* tana tolet

da sauri yakaraso kusa da baba talatu cikin mrnarshi

tashafa addu'arta ta waigo gareshi cikin farin ciki tace *Barka da zuwa ranka ya dade

Murmushi yayi tareda zaunawa akan gefen gado wanda yasha gyara agun *Inteesar* yana fuskantar baba talatu yace *Baabaa kinki zuwa kiyi saven dina inatajin yunwa

cikin hanzari baba talatu tamike taredacewa ranka ya dade tashi muje ina zanso kaji yunwa

Murmushi yayi tareda mikewa yanabin dakin da kallo amma yana jiyo karar ruwa atoilet yakasa dauke idanuwanshi akan kofar toilet din

baba talatu tayi gaba yabita abaya har suka isa bangaren mommy tana zaune a inda yabarta tana latsa wayarta

Baba talatu tagaidata cikin ladabi ta isa taja mishi kujera yazauna tashiga bude mishi kulolin abincin tareda tambayarshi abinda zata zuba mishi

hmmm aifa gogan dukya rikice domin kamshin abincin yagama dashi duk yakosa yafara cin abincin

Mommy kanta seda kamshin abincin yasa ta aje wayarta agefe tana hadiyar miyau

Shiko gogan da kyar ya iya zabar chainis rice baba talatu tazuba mishi hadi da farfesun naman kasa ta aje mishi agaban shi


Mommyma tace azubo mata dukda ba yunwa take jiba amma kamshin abinci kawai yasa tafarajin yunwaπŸ˜‚ nan tashiga aunawa cikinta ba kama gannun yaro


Aifa shima gogan nan yafara kai lomar abincin yanajin wani ni'imataccen dadi na shigarshi yanaci yana sambatun dadi baba talatu nata mishi dariya domin itama mommy bakunne se baka

kan kace chass gogan yacinye chainis rice dinnan da farfesunnan nan aka kara zuba mishi abincin larabawa nanma sambatu yayi tayi seda yaci yakoshi yama mance dashan ruwa sannan ya kalli baba talatu yace *Toh baba abani exotic

Nan baba tace ranka ya dade aiga drinks nan an hada maka...... tazuba mishi kunun aya wanda yaji kayan hadi ta miko mishi

Yana kallon kunun ayan yanaso amma ba hali domin yasan zai shiga yanayi dan haka yakalli baba talatu yace *Baabaa kisamin wani in akwai se asamin kunun ayan afirij zansha anjuma

Aiko mommy tayi charab ta amshe tashanyeπŸ˜‚

Baabaa tazuba mishi lemun kwakwa tabashi aiko nan yashiga sha seda yashanye tass sannan ya aje kofin aka kara mishi yanata santi hmmmmm awannan fannin yakasa jurewa sedai kawai ya tsinci bakinshi yana cewa *Wai baabaa waye yayi girkinnan gaskia yayi dadi sosai ga drinks dinma irin wannan in kana samunshi ai bazaka sha na kwaliba gaskia yayi sosai

Mommy tayi tariya tareda cewa baabaa dauko waigi kisama Babana karya fadi wannan santi haka🀣

Aiko baba talatu tadauko karamin fillo tasa mishi tana dariya

Shima dariyar yayi tareda kara maimaita tambatar tashi

Mommyce tabashi amsa *Bakanan ai ankawo mana sabuwar me aiki itace taketa shagwabamu da girkinta me dadinnan

Wow gaskiya mommy ta iya girki dole nabada tukuici..... yasa gannu a aljihu yadauko bandir din dubu daya daya bandir biyu yamikama baba talatu yace daya nata daya na dayar me aikin

Sosai baba tashiga kwararo godiya

Mikewa yayi ya nufi gun mom yayi mata kiss tareda cewa *Mommy zan dan fita in dawo bazanyi nisaba

Abbanah ina zakaje haka kaida yakamata ka kwanta ka huta

Mukullin mota yadauka seda yakai bakin kofa sannan yace yanzu zan dawo bazan dadeba

Mommy tace allah ya tsare tareda mikewa ta haye sama itako baba talatu seda ta tsaftace gun takara sa turare sannan tanufi bangarensu tabawa *Inteesar* kudin nata da *Annur* yabata

Kallon mamaki *Inteesar* tayima baba talatu cikin wani yanayi tace *Ni nabar miki baba mezanyi da wannan uban kudin

Harara baba talatu tayima *Inteesar* tareda cewa *aiko baki isaba dole ki amfana da kudinki zan dauki dubu ishirin asiyo miki abubuwan dakike bukata zuwa gobe in aiki yayi mana sauki se in rakaki amiki saloon kinga seki fito sharr sauran se in adana miki ko atura kauye ase miki akuyoyi

itadai *inteesar* godiya tayima baba talatu sosai domin ta tabbatr da baba nasonta da wannan shawarar suka shiga kichin don gabatar da girkin dare........


Hmm ai yana fita kai tsaye yanufi ma ajiyar motocin gidan yashiga daya daga cikin manyan motocin gidan yamata key nan da nan yabar harabar gidan

kai tsaye unguwar tasu yanufa zuciyarsa cike da mararin son ganin gimbiyar tashi wadda sonta yahanashi kwanciyar hankali

Tafiyar 20mnt ya isar dashi kofar gidannasu yafaka motarshi yafito ya karasa zuwa zauren gidannasu..... shi kanshi azuciyarshi yayi mamakin ganin zauren gidan bakowa kmr anshareshi ba kamar adaba kullum cike yake da almajirai

Da wannan tunanin yadawo zuwa jikin motarshi yajingina nan da nan bakon yanayi yaziyarceshi addu'ar yakeyi azuciarshi allah yasa yaganta ko kadanne domin yasamu natsuwa......... seda ya dauki kusan 10mnt yana tsaye akofar gidan aiko se yaga giftawar wani yaro yakira yaron yaron yakaraso ya gaidashi Ko amsawa *Annur* yakasayi burinshi kawai ya aiki yaron yakira mishi ita aiko be bata lokaciba ya aika yaron zuwa gidan shiko yaro da gudunshi yanufi gidan

Suna zaune a tsagar gida akan tabarma iya tayi male2 Hafsat tana gefenta wadda tayi wata irin mahaukaciyar kiba sekace zata fashe {ko kibar meye ohoπŸ€·πŸ½β€β™€} sun tasa gasasshen naman kaza agefe sunata yaga musammanma iya data dade bata sa naman kazar abakintaba🀣

Da sallmarshi yaron yashigo gidan...... cikin sauri iya taboye naman kazar abayanta πŸ˜‚πŸ€£ita duk azatonta bako sukayi seda duk suka dago sukaga yaron sannan iya ko amsa sallamar batayiba ta tambayi yaron cikin zaro idanuwa *Kai lafiya zaka shigomin gida kmr tsohon barawo

shidai yaro be tanka mataba saboda duk wanda ke layin babu wanda besan halin matarba da ruwan matsifa

Hafsat takara zare mishi jajayen idanuwanta sekace gauta *Kai bakai ake tambayaba? kagamin dan bura uban yaro

Turo baki yaron yayi tarexa cewa wai wanine me mota yake sallama da wata yarinya agidannan yace wai fara

Hafsat taji ance me mota aiko nan tayi zumbur tamike cikin sauri tareda cewa au ashe mani ake nema kai kayi hakuri kaji πŸ˜‚tafadi hakan tareda mincino naman kazar tamikawa yaron

Girgiza kai yaron yayi alamar bazai amsaba sannan yafice dagudu daga gidan

Cikin matsifa *Hafsat tace aikin banza tsiyata da yayan matsiyata kenan toh ohon maka dai...... tafadi hakan tareda nufar dakinnasu

Itadai iya cewq takeyi ke kiyi sauri ki fito kilama alhaji usman sabo ne kiyi sauri yannan karki mana bukulun samun kudi🀣

Cikin minti biyar Hafsat tayi tsaka tsami rabonta da wanka tafi sati dayaπŸ€ͺaiko nan ta zabga uwar kwalliya tasa dogon wando matsastse se riga iya cibiya kai yaji uban gashin doki sekace diyar arna🀣aiko tana fitowa iya tashiga koda diyar tata harta fice

Tin bayan dawowar yaron daya sanar dashi tana zuwa yadauki dubu daya yamikama yaron nanko yaron yashiga murna yana godiya harya bar gun

Ya kudirci aniyar koda zai kwana agun zai jirata harta fito shidai burinshi yasata a idonshi

Hmm karasowa gun tayi be ankaraba yaji anata taba mishi hannu aikocikin hanzari yadago idanuwanshi sukayi tozali da ita dominshi bemaji tafiyartaba

Kallon sama da kasa yayi mata ga wani karni dake dukan hancinshi cikin bacin rai yace *ke lafiya zaki tabani?

Fari tashiga mishi da idanuwa kana tace *Haba Malam kaifa ka aiko akirani toh nazone naga kanata tunani bakasan nazoba shine na tabaka

Kara kallonta yayi kana yace *da allah malama kiyi hakuri bake nake nemaba dayar yarinyar gidanku nake nema plx help me ki kiramin ita

wani irin uban kallo ta watsa mishi domin tafara tunanin rainin hankali zaiyi mata tace *Ni nikadaice budurwa agidan ai dan allah malam inni kazo nema gani kwana kakeso kayi dani ko wuni ko sati duk zan yarda kaini har wata inhar zaka biyan...........




πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI✍🏻
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYE AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘



{12/8/2018} 8:6 am



πŸ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI✍🏻




πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘πŸŒ‘

{7/4 / 2017} 10: 30 p.m.

πŸ“š SA'ADATU BINTU ABDULLAHI πŸ“


PAGE 1⃣


Tafe yake cikin sauri acikin tsaleliyar 🚘 yana sauraron kidin turawa ahankali yakebin wakar cikin san-sanyar muryarshi daka ganshi kasan yana cikin nishadi shan kwanarshi keda wuya be ankaraba yayi ciki dawata yarinya😳 cikin hanzari yaja wani burki jikake kiiiiiiiiiii.....πŸ™†πŸ»β€β™‚ agigice yafito daga motar yana furta INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU UN... kan kace kwabo mutane sun taru fam kowa yana alhinin abun cikin hanzari yadauketa kantase zubda jini yake agaskiya taji rauni fiye da tunaninshi πŸ˜₯ cikin hanzari yabude gidan baya yasata yashiga mazauninshi yatada motar gudu

2 Comments On BOYEYYEN AL'AMARI
avatar
nafeesat-yusuf

1 year ago

Reply

Continuenation pls

avatar
shuraihu

1 year ago

Reply

Replying to nafeesat-yusuf

We will complete it soon Insha Allah

Please Login or Register in order to submit comment