Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da rashin arzikinku shin kinsan cewa shi so baruwanshi da talauci koda akan bola kike rayuwarki wlhy nidai inasonki

Yasauke gwauron numfashi kana yadaura dacewa kece rayuwata wlhy inasonki pls ki yarda kisoni

Nidai sebinshi nakeyi da idanu dukda bansan wayeba amma nasan iyayenshi masu kudine

Dayaga nayi shiru seya tsugunna har kasa yace Dan Allah kisoni wlhy rashinki dai2 yake d rasa rayuwata tin farkon ganinki nakamu d kaunarki

Waige2 nashigayi domin naga alamar mutuminnan zai taramin mutane

Nace Dan Allah katashi atsugunne kada mutane su zaci ko wani abune pls katashi

Kara tsugunnawa *Annur* yayi yace inhar bakice kina sonaba bazan tashi daga nanba

Nazaro idanuna nace nashiga ukku๐Ÿ™†๐Ÿฟโ€โ™€ Dan Allah katashi

Yace Dan Allah kice kinasona

pls katashi zance

Yamike tare dacewa toki fadi


Da sauri nabar gurin nashige mota


Dasauri *Ukti* taja motar tanata turo baki๐Ÿ˜‚

Shiko tsayawa yayi yadau lokuta atsaye sannan yaja tashi motar jiki babu kwari domin gani yakeyi kmr bana sonshi


Nakalleta nace *Ukti* turo baki kikeyi to menayi miki?

Tayi banza dani

Niko *Ukti* ?

Nanma tayi banza dani

Nace pls *Ukti* kiyi hkr nabata miki lokaci

Tace bakomi aiduk abinda kukeyi ina kallonku

Nayi murmushi

Tace *Ukti* gaskia guy dinnan yana sonki wlhy kuma yahadu

Nace koh *Ukti*?

Tace yes *Ukti* ammafa banason yature govenatinmu

Nace kmry

Tace yayanama yana ciki fah

Nace cikin rashin fahimtar inda tadosa Bnganeba

Tace Ya ahamad ma yatsunduma asonki wlhy *Ukti*

Naja numfashi azuciata ina tunani dominni ban dau ya ahamad amatsayin masoyiba dominni gaskia aya nadaukeshi bana tunanin kunyarshi zatasa na iya soyayyah dashi

Amma afili nace Allah yazaba mana abnda yafi alkhairi

*Ukti* tace ameen amma insha allahu ya ahamad ne alkhairin

Nidai murmushi kawai nayi

Muka isa wurin saloon din aka gyara kowa nan take bani kudin da ya ahamad yabata yace takawomin

Nakalli uban kudin data ajemin nace *Ukti* yazanyi da wannan kudin nidai kawai ki ajiye agunki


Tayi2 dani na amsa naki amsa nace ta ajiyemin


Tace toh akwai lokacin dazan baki kayanki

Se wajan yamma muka dawo gida tasaukeni akofar gidanmu tawuce gida itama


Kai tsaye gidansu yanufa zuciarshi dauke da tunani2 gaba daya zuciarshi cike take da damuwar anya zata soshi?


Hon yayi akatafaren gidannasu cikin hanzari baba me gadi yazo yabude mishi get din yadanna kan motar

Wurin da aka tanada dan parking yanufa yafaka motar

Yafito kai tsaye bangarenshi yanufa

Fadawa kan katafaren gadonshi yayi yakwanta rigingine yana kallon silin zuciarshi naraya mishi shin inya rasata yazaiyi da rayuwarshi

Ya tabbata inya rasata bazai rayuba domin itace rayuwarshi

Dawannan tunanin yadauro alwala yanufi masallaci

Ana idar da sallah yanufo gida nanma bangarenshi yanufa

Lambobin Baba talatu yadannan

Cikin ladabi ta dauka tareda cewa ranka ya dade barka da hutawa

Yace brkadai baba talatu

Tace kana bukatr wani abune agaggauta yimaka

Yace tumbinane yayi kasa asamamin abinci cikin sauri

Tace angama yallabai

Seda yafara ajiye wayar sannan itama ta ajiye


Cikin Sauri tashiga kitchen tashirya mishi tuwan shinkafa miyar kubewa danya dominshi yanason abincin gargajia

Da talia da miyar kwai wadda taji nama da kwai

Tahada mishi da farfesun kayan ciki

Da farfesun naman sa

Dana kan akuya

Tayi mishi drinks din gwanda

Dana kwaiba Dana kankana da kunun aya


Nan cikin minti uku tasa aka shirya mishi abangarenshi akan daining table

Yana zaune afalo yanata aikin tunaninta ta iso ta tsugunna har kasa

Allah yataimakeka angama shirya maka komi akan dainin table

Yace okay sannu da kokari


Yadauko kudi akusa dashi dubu dari yamika mata

Ta amsa tanata godiya tanasa mishi albarka harta bar falon

Seda yadau kusan 5 mnt sannan ya iya Jan kafarshi ya isa kan daining din

Da kanshi yazuba tuwan shinkafar yadanci ya ci ferfesun naman sa kadan yadan kora kunun aya

Yakirata tazo ta kwashe kwanukan

Nan da nan ta tsaftace gurin takunna mishi turaren wuta

Kana tabar bangaren

Komawa bed room dinshi yayi yashiga duba hotunanta zuciarshi cikeda dumbin kaunarta

Turiri se tashi yakeyi wuta nata ruruwa bom nashirin tashi..........๐Ÿ˜‚



LUV U ALL๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜



๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿป
๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘


{9/5/2018} 8:27 pm



๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿป


*Inasonki my swt my lovely my blood my mom sonki ajinina yake allah yabiyaki da jannarti firdausi*๐Ÿ˜๐Ÿ‘„



PAGE3โƒฃ1โƒฃ

Agigice likitocin dasuketa zirga2 suka karaso suka kamashi tareda dr ibnu mu'azzam suka shiga dashi emergency room


Agigice ya Isa Ofishin dr khaleed ya labarta mishi atare suka fito suka shiga emergency din


cikin hanzari suka dukufa akanshi dakyar suka samu numfashinshi yadawo suka bashi wani special room tmkr agida suka saka mishi drib yasamu barci sosai

komawa office Din dr khaleed sukayi suna maida numfashi

Suka ciro ruwan gora me sanyi suna korawa

dr khaleed ne yace yakamata mukirawo yan uwansu dukda munada isassun wadanda zasu kula dashi kasan tsarin asibitinnan bamason yan jinya domin munada likitoci

Dr ibnu mu'azzam yace gaskiane to amma yaxa muyi da gawar baiwar allan nan

Dr khaleed yace ai dole se mun jira yallabai ya farfado

Dr ibnu mu'azzam yadanyi jim nan da nan hawaye yafara sintiti akuncinci kuka yakeyi dukda bayaro bane

Dr khaleed nabashi hkr shima yana hawaye

Dr ibnu mu'azzam yace cikin kuka "allah yajikan baiwar allannan wlhy tanada taimako gason mutane

Dr khaleed yadaura dacewa "aiduk garinnan babu wanda besan *Hajiya hussaina*ba komu kanmu itace tagina wannan asibitin bayannan asibitocin data gina sunfi dari kuma kullum tana ziyarar gidan marayu tana bada taimako......yana kaiwa nan yafashi da kuka๐Ÿ˜ญ

Dr ibnu mu'azzam yabude baki zeyi mgn aka kwankwasa kofar office din

dasauri suka goge hawayansu tare dayima me kwankwasa kofar iso


Yar madaidaiciar balarabiace wadda shekarunta bazasu dara 28 years ba tana sanye da kayan nose aguje ta afko office din tana maida numfashi alamar tayi gudu sosai cikin in ina tace " dr wannan matar bata mutuba wlhy hannunta namotse (cikin harshen lrbci take mgn)

Atare suka zaro idanu nan da nan suka dugun zuma inda take suka fara bata taimako tareda sa mata abin jawo numfashi Nan tasamu take numfashi amma batasan inda kanta yakeba suka kaita dakin hutu tareda bada izinin abasu kulawa ta musamman

atare suka dawo office kowannensu zuciyoyinsu fari kal tareda addu'ar allah yatashi kafadarsu



Acan gidansu kuwa dukkan masu aikin hnklinsu atashe yake musammanma yar datti juwar

Zuwa tayi tazauna adakin uwar gijiyar tata tanata zubda hawaye tareda addu'ar allah yadawo musu da Ummun HUM@IR@H lpy

Tana cikin wannan halinne wayar uwar gijiyar tata datake kan gado tadau ruri

Cikin hanzari ta isa tadauki wayar domin azatonta *Alhaji*ne yakira

tadanna wurin amsawa takara akunne

Cikin harshen larabci taji ance Yar uwata ykk I miss u my sis keda kika saba kirana tin safe amma gashi har rana tayi najiki shir......

Tin kafin takai karshe tagane me mgn *hajia hassana*ce

Cikin ladabi tace "ranki yadade ba ita bace

da alamar mamaki tace ina take ita

Rushewa da kuka tsohuwar tayi harda shashsheka

Nanfa hnklin mom yatashi cikin tashin hnkli tace "kigayamin menene yasamu yar uwata?

Tsohuwar takasa mgn domin kukan yaci karfinta

Itama mom hawayen tafarayi tana cewa tamutu koh? Dama munyi wayada ita jia tacemin batada lafia ni nasan tamutu.......๐Ÿ˜ญkuka yaci karfinta takatse wayar

Kai tsaye me gidannata takira take sanar dashi shima agigice yakatse wayr ya danna lambonin *alhaji Muhammad* shima shiru be daukaba

Nan shima *alhaji imran*yarude yashiga dimauta

Lmbar mom yakira yasamu yadan kwantar matada hnkli

Cikin kuka tace mishi ita zatabi jirgi taje taganta

Ganin duk hnklinta yatashi dan dole yabarta shima bayan ta isa da kwana daya ze iso sukayi sallama

Nan takira *Annur* tana kuka

Cikin tashin hnkli yakatse wayar dama yana cikin gida yanufo bangarenta

Da sallamarshi yashigo bedroom dinta hnklinshi atashe baba talatu yagani tanata rarrashinta agefe guda kuma wasu masu aikin suna saka mata kayanta a akwatinta

Da ganin yadda take kuka yasan cewa ba lafia

Karasowa yayi yarungumeta tareda korar kowa daga dakin

Rarrashinta yashigayi tareda kawo mata ruwan faro me sanyi amma taki sha

Shima jiyakeyi tmkr yayi kukan

Cikin dauria irinna mazan fama yace cikin harshen turanci pls mom menene yafaru? kinsan banason ganin hawayenki pls kisanar dani menene pls my best...............



LUV U ALL๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜



๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿป
๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘



{2/6/2018} 11:12 p.m




๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿป



*Bazan mance dakuba masoyana bazaku lissafuba maza da mata duk ina tabbatr muku kunanan kunyi male2 azuciata*โค๐Ÿ‘„

*Happy ramadan*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


PAGE3โƒฃ2โƒฃ

Ahankali ta labarta mishi abinda yasamu mom dintashi ta saudia

Hankalinshi atashe yakoma bangarenshi shima yashirya tareda kiran direban pilot dinshi cikin dan kankanin lokaci ya iso

Suka kama hanyar zuwa saudia



** **
Koda suka isa direct asibitin suka nufa alokacin alhaji muhammad ya farka yana zaune agefen gadonnata

koda suka shigo cikin asibitin suka hadu da doctor *Khaleed* yakaisu har dakin da aka kwantr da ita

kmr daga sama suka shigo cikin dakin kowa hnklinshi atashe

Cikin sauri mom ta isa gadonnata tana hawaye

Annur kuwa suka gaida da alhaji muhammad cikin girmamawa tareda tmbyr me jikin

Alhaji muhammad ya amsa da *alhmdllh

Dakyar aka samu mommy tazauna amma hnklinta baya jikinta




**** ***
tafe suke acikin tsaleliyar motr *Fa'iza* ce takeyin tuki domin ita kwanace inde afannin tukine

hajia samira tana kusa da seat din *Fa'izan* hajiarce ke nunnuna mata hanyar daza tabi

Ahaka har suka isa wani kasurgumin jeji dake cikin garin sakkwato

Nan *Fa'izar* tafara razana tareda fadin *Mommy acikin jejinnan akwai mutun?

Hajia samira tayi murmushi tareda fadin *sosaima kuwa yar albarka

Itadai taba baki tayi azuciarta tana fadin dabadan bukatata bace wlhy banga wanda ya isa yasani nayi tuki tin daga garin kano har zuwa garin sakkwatoba

dakyar suka karasa suka faka motr suka fara cin wata uwar tafiyar

Itadai fa'iza tama fara gajia da wannan tafiar kmr zasuje bangon dunia ga uban duhu jejin dukda ranace.......

wani macijine yazo yagibta ta kafarta yawuce cikin sauri nan ta rabka wani uban tsalle ta makalkale ajikin mommy tana kuka

Mommy tanata rarrashinta domin ita ko firgita batayiba domin inda sabo tasaba

Da kyar tasamu ta lallabata suka cigaba da tafiar

Ahankali suka iso wani kogo me dan banzan duhun tsiya

Itadai *Fa'iza* jikinta har rawa yakeyi

Mommyce taji tafara ma bokan kirari *Kaga boka dan tatsitsi, kaga mara imani, kaga me aiki da cikawa, kaga me biyamin bukatuna, kaga me aiki da bakaken aljanu, kaga me dunia wanda yamaida dunia kmr gidanshi kaga gatana .......


WaTa irin dariya yayi cikin katuwar muryarshi wanda seda duk jejin ya amsa dariar tashi

Itadai *Fa'iza* waige2 tashigayi jikinta na mugun rawa domin dariar kawai takeji amma bataga kowaba

nan yashiga wani yare irinnasu na bokaye

Daganan mom taci gaba da fadin *gaisuwa nakeyi me amsa bukatuna (subhanallahi)

Wata dariyar yakarayi Kana yadaura dacewa

Mekukeso ayi mishi?

Murmushi mommy tayi tareda cewa ranka shi dade ai bakaji meke tafe damuba?

wani irin tsawa ya daka mata wanda seda hanjin cikinsu ya kada

Yadaura dacewa *Tin kafin kixo Dan suburbusu ya sanar dani komi dan hk ki iya bakinki

Cikin rawar murya tace *Shugaban aljanu ya huci zuciarka

nan ya kara kyalkyalewa da daria

Yaci gaba dacewa *so kikeyi asashi yazo ya kwanta yana kuka akan kibashi auren yarki?

Wani irin kayataccen murmushi mommy tayi sannan tadaura dacewa *Eh burina yasota fiyeda iyayenshi ya aureta ta haifa mishi yara daga baya akasheshi yabar dunia yabarmu muci dukiyarshi nida yata da jikokina

Wata dariar muguntr yakarayi kana ya daura da cewa *Angama kisa aranki harya auri yarki yagama shidin me

Mommy tashiga kwararo godia

Yadaura dacewa tin ynzu aiki zai fara

Se wata iska tazo me karfi segashi zaune akan wani dutse

Ganinshi seda numfashin *Fa'iza* yadauke domin mummunane na karshe bakinshi tmkr bakin zunubi gashi da jajayen hakora da jajayen idanu tmkr gauta ga gajarta tmkr guntun kashi ๐Ÿ˜‚

Yayi wadansu yan surutai tareda daga hannu sama nan se wata katuwar kwarya tafado ahannun nashi yashiga yan tsubbace tsubbacenshi

Cikin yan mintoce sega hoton *Annur* yafito acikin kwaryar

kwalalo idanuwa sukayi suna kallonshi zaune akasar saudia

Wata irin daria yakarayi tareda basu labarin halin dayake ciki harda labarin yanason *Inteesar* ya tabbatr musu da bakaramin so yake mataba ji yakeyi tmkr zai iya rasa ranshi akanta kuma akwai wani *BOYEYYEN AL'AMARI* atattare da ita shi kanshi yakasa ganin shi

Nanfa zuciar *Fa'iza* tmkr zata tarwatse dun kishi idanuwanta suka fara zubda hawaye tana hawayen tace *Plss ka taimaka boka wlhy zan iya mutuwa akanshi plss ka kasheta kawai yarinyar

wani irin uban ashar ya antayawa *Fa'izar* tareda cewa *baki da hnkli so kikeyi narasa raina wannan yarinyar tafi karfin ubana bama niba kawai ki lallaba kedai kisamu kishiga daga ciki amma yarinyarnan tafi karfinmu. yakara kyalkyalewa da wata dariar

Mommyce tace *Ranka ya dade ita yarinyar yanxu babu yadda za ayi da ita?

Yace bazan iya mata komiba domin ko fuskarta bazan iya kalloba tariga tajiku da tsoron allah tanada kusanci da mahaliccinta

Kowannensu zuciyoyi ba dadi

Bokan yadaura dacewa *Shima kanshi yaron semun fara sanya mishi wasa da ibada kana zamuyi nasara akanshi kuma ahalin yanzu yana kasa me tsarki seya dawo zamu fara aikinmu akanshi

Nanfa suka kwanta suna godia tareda aje mishi uban bandir bandir na kudade

Yabawa *Fa'iza* layoyi tareda umartarta dataje gidansa ta birne layar akofar get dinsu dayar kuma akofar shiga falonshi ya gargadeta kada tabari kowa yagani

Sukayi godia kana sukabar gurin zuciyoyinsu tar domin itadai *Fa'iza* harta fara mafarkin gata gashi akan gado suna zuba soyayyarsu abinsu ๐Ÿ˜‚


*** ***
mom tana zaune akan dadduma tana lazimi annur da alhaji suna masallaci

farkawa tayi bakinta na furtar sunayen allah

Cikin hanzari mommy ta iso gaban gadonnata tana mata addu'ar

Idanuwanta suka sauka akan mom budar bakinta tace Cikin harshen larabci *Ukti* kinganta koh? Ai kin taba ganinta koh? Wlhy tana raye ni ina ganinta yanzuma nayi mafarkinta tanatamin murmushi ๐Ÿ˜ญ

Hawayene yazubowa mommy ta goge tareda fadin *naganta ukti insha allah takusa isowa gareki

Murmushi tayi tareda cewa allah ya amsa

Suka amsa da amin

Mommy tadauki wayarta takira ammi dattijuwar tadauka mommy tabada umarnin ta dafawa mara lafiar abinci zatasa annur yazo ya amsa

Ta amsa da angama ranki ya dade

kana suka ajiye wayar

Dai2 lokacin suka shigo cikin sauri annur yakarasa gadonnata yana mata sannu

Farin cikine tsantsa ya bayyana afuskarta cikin murna tace *Annurul khalbi I miss u wato dabadan zan mutuba dabaza kazo kaganniba koh?

Murmushi yayi yace *Wlhy ummih inada niyar zanje amerika daganan zan biyo tanan in ganki ummihnah yafadi hkn tare da manna mata kiss agoshinta

Shafa miki sumar kanshi tayi taredayin murmushi

Alhaji Muhammad yakaraso tareda murmushi afuskarshi yace *ni amma mannce dani koh? Saboda kinga danki

Murmushi tayi tareda mika mishi hannu yarike yayi mata kiss akan hannunnata

Mommy tasa annur yaje gida ya amso mata abinci

Cikin dan kankanin lokaci ya isa gidan dama ammih tashirya komi ready suka gaisa sosai da annur din tareda tmbyrshi saukar yaushe ya lbrta mata komi

Tajinjina kai tareda tmbyr me jikin *yace da sauki

Tarokeshi akan su tafi tare

Atare suka iso asibitin sunata hira. annur shi mutumne me girmama mutane


Ammih tagaida mommy sama2 mommy ta amsa domin ita bata da son mutane ballan tanama talaka

Ummih taci abinci alhaji yarinka bata abaki taci takoshi tasha mgni

Ganin annur yasa jikinnata taji dadinshi

duk inda annur din yayi seta bishi da ido harde takasa daurewa tace *Annurul hayat wai meke damunkane my kaga yadda dukka rame kodai kayi ciwone?

Mommy tayi charab tace *kinde ganshinan wlhy nida daddynshi munyi tmbyr duniarnan amma amsar dayace ba komi

ummih tace *anya kodai baku iya lallabamin shi bane ni zan tmbyeshi nasan zai fadamin

Nande suka cigaba da hira da daddare mommy tace ita zata kwana da ita a asibitin annur yace tabarshi ya kwana daddyma yace suje su huta shizai kwana

Nan sukayita jani in jaka akarshedai mommyce tace seta kwana duk suyi hkr

se wajen sha dayan dare suka taho shida Alhaji muhammad da ammih annur ke tuka motr

suka iso gidan Yayiwa daddy seda safe yasa ammih takawo mishi irin abincinsu na larabawa

Shi ya isa bangarenshi agyare tsaf kullum se ummih tasa an gyara mishi bangaren nashi

Katon falone wanda yaji adon white and blue hatta kujerun falon white and blue ne da gun daining area din yasha adon fulawer me fitar da gamsassshen kamshi Ga wani katon flasma ya mamaye bangon dakin falon ya kayatu an narka dukiya kmr banza

Kai tsaye upstair yanufa ya haye sama nanma wani falonne me dauke da adon purpule and milki komi yaji nanma tsaftsaf

yana dauke da three bedrom

Daya daga cikin bedrom din yanufa asaman dakin an rubuta sunanshi da danyen zinari da manyan baki *ANNUR* sunan se kyalkyali yakeyi

Murmushi yayi yabude dakin yashiga

Makeken gadone me matukar haduwa ajikin gadon an rubuta *Annurul khalbi* yanada katuwar durowa da mirrow an jera duk wani abunda zai bukata akan mirrow din murmushi kawai yasaki

Yafada bandakin dake manne adakin yayi wanka tareda dauro alwala yasaka kayan barci wadrop din cike take da kayanshi na alfarma

yashimfida dadduma yayi nafila raka a hudu

Ammih tasa an jere mishi daining dinshi nasama da kala kalan abinci

Tazo ta sanar dashi

Godia yayi mata kana cikin kasaita yafito ya isa daining din yadanci abincin kadan yadan kora kunun aya me sanyi

Yana gamawa yasa aka fita da kayan yakoma dakinshi yakwanta amakeken gadonnashi wanda yaji katifa me tsananin laushi

Nanfa lissafinshi yakwance cikin kankanin lokaci yaji abubuwa namishi yawo amararshi

Nan ya tabbatr da kunun ayar daya shane domin dama kunun aya na tada mishi sha awa๐Ÿ™ˆ

Babu wadda tunaninta ya ziyarci zuciarshi se ita surarta tafara mishi yawo acikin zuciarshi yadda hips dinta ke kadawa in tana tafi.........๐Ÿ™ˆ



LUV U ALL๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜


๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿป
๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘
BOYEYYEN AL'AMARI
๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘



{10/6/2018} 11:06 p.m



๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿป



*Wannan page din na masoya fati washa ne kyautarshi nabaku kuyi yadda kukeso dashi*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ‘„



PAGE3โƒฃ3โƒฃ

Ahaka yayita juyi akan gadon yana faman rike mararshi๐Ÿ˜ช

Adaren dai kwanan wahala yayi se kusan asuba yasamu barci yayi awan gaba dashi

Barci yakeyi me cike da mafarkinta.......๐Ÿ™ˆ

(mmn mama tace karna bayyana๐Ÿค)


*** ***
tsakar gidan yafito hannunshi rike da yar leda me dauke da kayanshi kala biyu da zabgegen charbinshi adayan hannun nashi

Kwala mata kira yshiga yi * Me nasara! Me nasara!! Wai kina inane?

Daka can cikin dakin iya tafito tana rike da tsintsiya ta iso ta tsugunna agabanshi tareda cewa *Abbah gani

Yace *me kikeyine naketa kwala miki kira

Cikin ladabi tace *ina aikine abbah nah

Yace *Toh allah yayi albarka

cikin jin dadi tace *amin

Yadaura dacewa *Dama nakirakine in fada miki yau zanyi tafiya zanje can Lagos gurin yiwa me girma govenar saukar alqur'ani me girma asabon gidanshi daya gina acan

Cikin wani yanayi tace *Abbah kai kadai zaka tafi?

Yace *Aah nida su malam sabone ammasu sun rigani tafiya ai tin jiya su suka wuce

hawayene yafara bin kuncinta domin dai tasan watan tonan asirinta yayi dama ganin malamne yasa suke raga mata.....

Kukan data keyine yasa hnklinshi yatashi nan ya tsugunnah yafara rarrashinta tareda mata alqawarin bazai jimaba sati daya zaiyi insha allahu

Nan tadanji hnklinta ya kwanta tayi mishi fatan dawowa lafiya

Dama iya suna labe itada hafsat sunajin abinda akeyi itadai hafsat harda murna takeyi domin zataci karanta ba babbaka๐Ÿ’ƒ๐Ÿป

Malam ne yafara kwalawa iya kira *Hajara kina inane?

Da sauri tafito tana gyara daurin kodadden zaninta takaraso tareda cewa na am malam

Yace *Toni nafito yarinyarnan amanarta na damka miki dan girman allah karki cuceta

Wangale hakora tayi dasukayi ja saboda cin goro Tareda fadin *Ahaba malam ai anzama daya ade dawo lafia bakomi ai


Dukda yasan bada zucia daya tafadiba yace *To allah yasa

Tace amin tareda sosa kanta me cike da datti inza abin cika baza arasa kwarkwataba๐Ÿคฃ

Yaciro naira dubu hudu yamikawa iya

ai kmr jira takeyi ta fisge tanata juya kudin ahannunta tana yatsina fuska tace *Malam bamufa da abinci agidannan saura kadan yarage wannan kudin mezai min?๐Ÿ˜

Yace *Haba hajara wlhy banda kudi wannanma kinsan da yaya nasameshi?

Yatsina fuska tayi tanata gungunai wai ita wannan kudinne zai mata sati daya inba wulakanciba๐Ÿ˜

Yakara ciro dubu biyu yamikawa *Inteesar* *Amshi me nasara kinji kiyi maneji banida kudi

Tace *aah abbah kabarshi inada canjina insha allahu zasu isheni harka dawo

Yaji dadin irin halin diyar tashi *Yace ungo karkimin gardama knji koh ? Kika sani ko bazan dawoba

Dagowa tayi arazane taredacewa *Insha allahu zaka dawo lpy

Yace allah yasa tareda mika mata kudin

Badan tasoba ta amsa tayi mishi godia

Sukayi sallama inteesar na biye dashi tadaukar mishi ledar kayanshi

haryakai kofar gida yajuyo tareda cewa *Hajara kada kibar hafsatu ta tafi yawo dan allah

Ta yatsina fuska tareda cewa toh naji๐Ÿ˜—

har kofar gida *Inteesar* tarakoshi ya kara mata natsiha sannan yatari napep ya umarceshi yakaishi tashar inda zai hau motr Lagos

Har napep din yakule tana daga mishi hannu sannan tadawo cikin gidan

Aifa yana fita hafsat tafito tanata tikarrawa tana kwaso shoki๐Ÿคฃmurna kmr zata kasheta

Tashigo gidan zuciarta cike da kunci

Aiko iya kmr jiranta takeyi tashigo ta danko mata gashi ta watsa mata mari๐Ÿ˜ณtareda kunduma mata uban ashar *Ke dan kan ubanki kawo kudinnan da malam yabaki yar matsiyata kawai yar ........

Se kuma tayi shiru๐Ÿคญ

Kuka nashigayi tareda ciro kudin na miki mata

Aiko tajawoni ta zaunar dani ta datsamin rankwashi ji kake kwasss........

Aiko nan nasaki wata razananniyar kara domin Bakaramin jin raฤ‘adin rankwashin nayiba.....

aiko takara daja min sumar kaina

Nanma wata azabar naji seda wani wahalallan hawaye yazubomin ban shiryaba ๐Ÿ˜ช

Tadaura dacewa *Daga yau wlhy bazaki kara zuwa makarantaba kuma talla dole kije min ita kina jina kuma aikin gidannan duk yazama naki dukkanshi wlhy tin asuba nakeso kirinka tashi kuma danwake ke zaki rinka yinshi kina sai damin kina jina koh?

takama kunnena tamurde nafasa ihu ta gwabemin baki sega jini yana juba ๐Ÿ˜ข

Ai awahale nace naji ๐Ÿ˜ญ

Itako hafsat tazo itama ta dunguremin kai tareda cewa *iya nima zan rinka mata gullisuwa tarinka zuwarmin tallah nima ๐Ÿคฃ

Aiko iya tayi carab tace *Wlhy yazame mata dole yar lelena ai komi kikeso dole tayi miki shi keda gidan ubanki........๐Ÿค”


** **
tin ana sauran kwana biyu zasu sauka akasar Nigeria dama hajia samira takira hajiya hassana asiyasance ta tambayeta randa zasu dawo tasanar da ita randa zasu dawo din

Aiko tin ana sauran 2 days su dawo hajia samira ta tasa diyar tata agaba sukaje sukayi birne birne agidan suka cika me gadin gidan da kudade

suka gama suka ja motarsu suka dawo garin kano



*** ***
Kwananta biyu a asibitin aka salla mota domin taji sauki sosai

Shiko gogan duk akwanaki biyun yakara ramewa seya kara haske sosai idanuwanshi suka kara fitowa ( hmm naso ku ganshi boyeyyen al'amari fans๐Ÿ˜œ)


Akwana biyun koda yaushi Alhaji imran cikin waya suke da iyalanshi tareda tambayarsu randa zasu dawo domin shima nan da 2 days yakesa ran zai shigo nigeria

Suka yanke shawarar suma nan da 2 days din zasu dawo

yaude kmr kullum sunata yin dinner akayataccen daining area abangaren ummih kowa ranshi fess cikin farin ciki suke ummih tawarware sosai har wata kiba takara yi ta murmure tayi bulbul


kawai juya cokalin yakeyi amma yakasayin koda loma dayane gashi ummih ta tasashi agaba

Ya afka duniyar tunaninshi surar tace taketa mishi gizo shidai ji yake kmr adauko mishi ita akawo mishi ita amatsayin matarshi......๐Ÿค”

Ummih ce ta taso daga mazauninta ta iso kan nashi kujetar ta amshi cokalin

Firgigit yadawo daga duniyar tunanin daya afka

Ummih tace cikin harshin larabci *Wai Menene yake damunka nurul aini?

murmushin karfin hali yayi tareda cewa *Ummih bakomi......

Mom tayi carab tace *Aina gaya miki kibar yaronnnan kawai tinda an tambayeshi an tambayeshi shiru toki gyaleshi kawai

Ummih tace *To ina ruwanki nida ฤ‘ana ne karki saka mana baki kija bakinki kiyi shiru๐Ÿค

Tissue tasa tagoge bakinta sannan ta tattara wayoyinta tareda cewa toni naji nafita masu yaya ni kinmaga tafiyata bari naje nayi barci

Ummih race *Gaskia kwara ki tafi domin naga kina samana ido ๐Ÿ‘€

Mom ta haye sama abinta

Ummih tashiga bashi abincin abaki seda yaci yakoshi

Tadauko kunun aya zata bashi

Ya girgiza mata kai domin yasan azabar dayasha๐Ÿคฃ(nidai nace maza sunji jiki๐Ÿคญ)

yadauki ruwa yasha

Ummih tajawo hannunshi suka koma kan kujera me zaman mutum uku

ummih ta rungumoshi jikinta tareda cewa *Son menene yasameka dukka rame plx tell me kaji ?

Kakalo murmushi yayi tareda cewa *Ummih nah bakomi

Hada rai ummih tayi tareda cewa *Son kanaso nayi fushi da kai ? Kodaini bankai ka gayamin damuwarka bane?


Cikin sauri yace *No mom amma.........


In bazaka fadaminba nima zan fita harkarka.....

Seda ummih tayi da gaske tayita lallabashi

yakwashe komi yagaya mata

Tinda yafara bata labarin zuciyarta keta mummunan bugawa

Ummih tace cikin kwantar da murya *Son kasan mom dinka bazata yarda ka auri yarinyarnnanba kaga son kawai ka hakura da ita kanemi wata .......

Ai ji yayi tmkr ta datsa

2 Comments On BOYEYYEN AL'AMARI
avatar
nafeesat-yusuf

1 year ago

Reply

Continuenation pls

avatar
shuraihu

1 year ago

Reply

Replying to nafeesat-yusuf

We will complete it soon Insha Allah

Please Login or Register in order to submit comment