Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ni, in har tana gidan to ban isa in ce bani nan ba." to amma Kuma a zahiri irin wannan ziyara da Maman bose mai shago ta kawo man Babu alheri a cikinta, ba rahama ba ce, don kuwa na dade ina yi mata qarairayi ina amsar bashin kayanta dake a shagon layinmu. Babu shakka yau ta gaji ne shi yasa ta biyo sawu na.
.
.
Ina jiran tarin comment dinku kafin in watso
page -6
mugun albishir
Page 6
.
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba.
.
.
Wata qila yau ta gaji ne shi ya sa ta biyo sawuna har gida don ta tsare ni in biyata kudinta, gashi Kuma tsawon wunin yau ko qwandala ban gani ba ballantana in mallaketa a Aljihuna. Don haka ya rage nawa in san yadda zan da wannan mafadaciyar bayerabiyar dake a qofar gida tana jira na. Na ci sa'a ma da ba ta shigo har cikin gidan namu ba." don kuwa bana son kakata juma ta san halin da ake ciki.
.
Na tashi gabana yana haduwa na tsallake rikodar da nake gyarawa, na fita waje ina wasi-wasi ni kadai. Na wuce juma tana alwala tana surutai ita kadai.
.
"in ba lalata ba." a kira ka amma ka ce wai a ce baka nan. Baka san alherin da yasa aka xo neman ka ba, iirin wannan ke sa mutum ya 6arar da qoqon furar arziqinsa da kan shi bai sani ba."
.
Ni dai ban ce mata komai ba, don kuwa abin dake damuna a raina ya ishe ni. Wani lkcn na kan biye mata mu wuni muna jayayya ni da ita. To amma ban da irin wannan lkcn da Maman bose ta xo ta ritsa ni.
.
Da fita ta qofar gidan na same ta a tsaye tana ta kumbura tana sacewa, kamar anan qara mata iska da fanfon mota, kumatunta sun kumbura kamar kwallon kafa . 'yar gajera ce dunqulalliya wacce ba Kowanne qato zai iya kayar da ita ba idan za ayi kokuwa. Na tsaya baya na jingina da qofar zaurenmu, sannan na lalubi wani murmushi na musamman Wanda yawanci bana yin irin sa sai rana ta 6aci in an zo an tsare ni in biya bashi, ni Kuma bani dasu. To amma Kuma a wannan karon murushin nawa bai yi rana ba, don kuwa matar bata saki ranta ba." Maimakon haka ma sai ta sake hade fuska kadan ake iya ganin idanunta dake 6oye a cikin loko. Na ce da ita.
.
"Maman bose manyan gari ...ashe ana ganin Ku haka..."
.
Ta daka mani tsawa a fusace ta dakatar da ni ba tare da na shirya ba."
.
"kada ka raina min hankali mansur ni ba wannan ya kawo ni ba..na zo ne ka biya ni kudina, na gaji da qarairayi da kake man. Kwanaki da na ganka ka ce min shekaran jiya zaka bani. Shiru-shiru baka zo ba, jiya Kuma ina hangenka ka zagaye baka biyo ta qofar shago na ba don Kada in tamvayeka. To ynx na biyo ka gida Tunda baka da niyyar biyana, ko an ce maka ni a banza nake debo kayan a kasuwa?
.
.
Ku yi haquri da iya wannan.
Sai mun hadu a
page 7Mugun albishir
Page 7
.
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.

Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI"bata amince da daukar shafin ba.
.
Ko an ce maka a banza nima nake debo kayan a kasuwa?"
.
Nayi ajiyar xuciya da naji ta kai qarshe. Na san cewa Babu ta inda zan layancewa wannan mata. don kuwa ta ji hausa radau, kamar jakar Kano. Duk ta inda na biyo mata tana kallona. Na ce da ita cikin lallashi
.
"ina sane da kudinki Maman bose, ba cewa nayi zan cinye ba, ina sane dasu. Garin ne ya dan yi mana zafi, wallahi Jira nake yi komai ya warware zan xo in yi maki balas, ai ina sane, ba dari hadu da tamanin bane? Ina sane Wlh ban mance dasu ba."
.
Ta sake murtuke fuska, ta haye sama.
.
"baka yi niyyar biyana ba, da ace kana da niyyar biyana ai ba zaka riqa zagaye wa ba idan ka hange ni a shago. Ka biya ni kudina kawai yau Tunda na gaji na biyoka har gida, ka biya ni ko in tara maka mutane ehe!"
.
Na waiga kusa da mu, naga wasu almajirai riqe da robobi sun tsaya kallo, da suka ga yadda bayerabiyar take daga muryarta tana kwaratsi. Daga can nesa Kuma a kusa da shagon wani iyamuri wai shi obi wasu mutane ne a zazzaune sun quro mana idanu, shi Kuma iyamurin yana dariyar mugunta daga nesa, don kuwa shima na cinye masa wasu ragowar dari da ashirin. A dalilin haka muka 6ata baram-baram don kuwa cewa nayi idan ya sake tambayata sai na kwantar dashi, ku ji Fa sbd tsabar zalunci, sai dai Kuma gashi tun ba aje ko ina ba wata mace wacce ta fi ni hadama ta ritsa ni ina zaman-zama na. Ta sake daka min tsawa.
"zan tara maka mutane mansur, Wlh ka biya ni kudina ko in tara maka mutane."
.
Na ce da ita cikin damuwa.
.
"mutane Kuma Sau nawa zaki tara min su Maman bose? Ai in dai mutane ne ko ynx ma kin tara min su."
.
Maman bose ta waiga taga mutanen dake kallon mu daga nesa, su Kuma almajiran dake kusa suka watse da gudu a tsorac, da suka ga ta wurgo masu wata harara. Ta dawo kaina ta sake cewa.
.
"mansur ka bani kudina in ba so kake yi mu kwashi bala'i da kai a wurin nan ba, ba Fa tsoronka nake ji ba."
.
Na jawo baya a tsorace da naga ta matso tana huci,ganin cewar tayi min barazana da mutane ban damu ba, shi yasa zata biyo min ta hanyar dambe da kokuwa. Ynx kam ta biyo min ta hanyar da zan biya ta, da ace ina dasu. To sai dai Kuma har ga allah bani da ko kwabo a aljihuna. Sannan Kuma idan na bari ta ci min kwala to sai ta yi min kayi dari a banza ban rama ko daya ba, don kuwa ruwa ba tsaran Wanda bane.
.
Na rasa inda zan sa kain, sbd masifa. Na ji hawayen baqin ciki Suna neman taruwa a idanuna, don kuwa tun lkcn da na gama makaranta shekara uku kenan ina fafutikar neman aiki ban samu ba." da na gaji shi ne na dawo na zauna a gida, na shiga sawun masu zaman tsammanin warabbuka, wai malam ya qirga noma don zakka. Shekara uku ba wasa ba ce, na sha wahala a baya, ko Kuma in ce ina kan shanta, don kuwa yau gani a gaban azababbiyar matar da ko mutuwa zan yi ba zata yafe min bashin da take bi na ba." ta sake cewa min..."
.
"idan lissafi zamu yi allah ne kadai ya san adadin kudin da nake bin ka mansur. Sauran biyu kana amsar taba (rothmans), ni na mance dasu ma sai ynx na tuno. Kuma kwanaki ma ka sha a bakin shagona ko ka mance ne....?
.
Gabana ya fadi, nayi saurin dakatar da ita.
.
"ina sane, haka mama bose, meyer Kuma na wani tone-tone?"
.
Nayi saurin katseta ne sbd a 6oye nake sha tabar, bana son kowa ya sani, ita ma don ya zama dole ta sani ne Tunda dai tana siyarwa. Nayi saurin kasa kunne ko zan ji tafiyar kakata juma, bata damu ba don ta ji anan rigima da ni akan kudi domin kuwa ta saba. To amma Kuma da zata ji maganar taba na san cewar sai ta fito ta ji ko waye yake sha. Idan kuwa ta fahimci cewar ni ne nake sha, to na shiga dari ba ma uku ba." don kuwa duk danginmu, na kusa da na nesa har ma Wanda ba a qasar yake zaune ba sai ta kai masa lbr.
.
Da mafadaciyar matar ta fahimci bana son ayi magana taba sai ta fahimci mahalarta. Sbd tsabar rashin mutunci sai ta sake daga murya.
.
"an fada, kana shanta tabar ko baka shafi'u ne iye! Sai ka biya ni kudin taba ta da ka xo ka amsa ka kunna ka sha..."
.
Na ji kamar in sa itace in buge ta sbd tsabar takaici, na leqa waje sosai inda mutanen unguwarmu ke zazzaune, na hango iyamuri yana dariya da qaton ciki.
.
Muna nan tsaye cirko-cirko ni da matar tana huci,ganin a Gabana kamar zata cinye ni danye. Kamar aikin budar idanu sai naga wata danqareriyar mota tana malalowa kusa da mu kamar ba zata qare ba, kafin mu tsayar da hankalinmu kan matar tuni har ta tsaya tana fitar da sauti kadan-kadan kamar iska. Bayan an kashe motar sai.......
.
Lp= 7mugun albishir
Page 8
.
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba.
.
.

Bayan an kashe motar an bude qofar sai kawuna alh. Badamasi dake a kaduna ya fito yana murmushi. Muka hada idanu, naji farin ciki ya kama ni don kuwa allah ya kawo min kudi a lkcn da nake neman su ruwa a jallo. Yana sanye da fararen kaya shadda riga da malum-malum. Dan matashin dattijo, mai kimanin shekaru hamsin a duniya, Wanda ko kusa a tarihin rayuwarsa bai shafi'u wata wahala ba." shi ya sa siffarsa babu alamun gajiya ko tsufa.
.
Da fitowarsa na tar6e shi cikin farin ciki
.
"sannu da xuwa alhaji."
.
Ya kama hannuna ya riqe yana dari.
.
"mansur manyan samari."
.
Muka kama hanyar zamu shiga cikin gida, Maman bose dake tsaye tana kumbure-kumbure ta ce a fusace.
.
"baka bani kudina ba, za Kuma ka shiga ciki."
.
Na juyo a fusace na harareta.
.
"amma ai sai ki bari sai naxo shagon, ko baki gani mun yi baqo ynx?"
.
Ta ce da ni.
.
"ni gsky ban yarda ba sai ka biya ni kudina."
.
Kawuna ya kallon, sannan ya kalli matar cikin damuwa.
.
"me yake faruwa ne?"
.
Ya tambayata.
.
"wane kudi zai baki?"
.
Maman bose tace dashi.
.
"bashi nake bin shi wata daya kenan ya hana ni. Shagona ya xo ya amshi tab..."
.
Jin zata tona min asiri yasa na hanzarta daka mata tsawa, na ce.
.
An tambayeki abin da naxo na amsa ne mara mutunci? Ki fadi kudinki mana a biya ki."
.
Kawuna ya ce da ita.
.
"ynx dai ke kudinki nawa ne malama?"
.
Maman bose ta ce dashi cikin ladabi.
.
Dari hudu ne da tamanin alhaj."
.
Kawuna ya zaro dari biyar a dunqule ya miqa mata. Tayi sauri ta miqo busassun yatsunta ta warce kudin. Ta ce dashi."
.
"na gode alhaji, gashi Kuma bani da canji, zan baka naira ashiri."
.
Alh. Badamasi ya ce da ita.
.
"jeki kawai abin ki, an bar maki."
.
Ta yi murmushi. Na sake hararta na ce.
.
"ba ki ci bulus ba, zan xo in amshi cannjina ke ma kin sani."
.
Kawuna ya janye ni muka shiga cikin gida, bamu zame ko ina ba sai dakin kakata, Kada ka tambayeni inda iyayena suke, don kuwa mahaifina qaramin ma"aikacin hukumar aikin gona ne a qaramar hukuma..yana can zaune a gidan ma"aikata tare da mahaifiyata da Kuma Sauran qanne na uku. Da yake kakata juma ta saba da ni, bata son rabuwa da ni, shi yasa bata amince in zauna a gidan mahaifina ba na ma"aikata. Duk kuwa da irin fafatawar da muke yi da ita, Fadan safe daban, na rana daban, haka na maraice, to amma ai duk laifinta ne, tunda dai ita ba zata iya gani ta yi shiru ba, sai dai Kuma da ace ta san ina shan tabar a 6oye aniya kuwa zata amince ta zauna tare da ni?
.
.
.
**
.
.
Minti goma bayan haka muna zaune a dakin kakata tare da Kawuna da ya kawo min ziyara yana yi min fada cikin fushi.
.
"ina amfanin irin wannan rayuwata takalmi mansur? Ace kai kenan Kullum naxo gidan nan sai na sameka a cikin masala. Ba ka da wata qwaqqwarar sana"a sai rigima da mutane akan kudi, kana jin wanna ita ce rayuwa mai kyau?"
.
Na sunkuyar da kai ban ce komai ba."
.
Kakata ta ce.
.
"Tunda ynx kaxo ka fada mashi, wata qila kai yaji maganarka. Amma ni da yake ya raina ni yaushe zai ji Fadan? Nayi juyin duniya da yaron nan ya samu sana'a, tunda dai aikin gwamnatin ya qirga samuwa, ya qi sbd girman kai. Wai shi tunda dai yayi karatun book bai ga dalilin da zai sa ya yi aikin qarfin ba." wai sai dai ya ci a huce."
.
Kawuna ya yi tsaki, ya ce.
.
"to ina maganarka hutu a qasar nan? Ai babu hutu mansur, haka nan zaka dake ka nemi na kanka ka hucewa kanka takaici da wulaqancin mutane."
.
Ya dan saurrara sannan ya ce da ni.
.
"Tunda abin ya xo a haka, ina ganin abin da zamu yi shi ne....! Ka shirya mu tafi kaduna tare.sai in samar maka aiki a can.
.
.
Lp=9Mugun albishir
page 9
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
(Madugun taska)
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba.
.
.
Ka shirya mu tafi kaduna tare, sai in samar maka aikin yi a can. Dama Akwai wani abokina da yake neman doreba, Kuma ni ya baiwa alhakin in nemo mashi yaro nutattse, don kuwa mutumin gurgu ne bashi da qafafuwa."
.
Na dago kai cikin damuwa na dubi Kawuna
.
"amma Kawuna sbd allah idan ma tuqin zan yi sai in rasa wanda zan riqa tuqawa sai musaki mara qafafu?"
.
Kawuna ya fashe da dariya, sannan ya ce da ni.
.
"ka cika gajen haquri mansur, in banda abin ka ai sai ka tsaya kuna in yi maka bayani. Kada ka raina wannan gurgun, duk da kasancewar sa musaki ina son ka san cewar duk fadin birnin kaduna babu hamshaqin mai kudi kamar sa. Idan har ka amince zaka bi ni ka riqa yi mishi tuqin to ka gama hayewa mansur....don kuwa a qalla duk wata zai riqa biyanka ladan duba talatin."
.
"dubu talatin?"
.
Na tambayi Kawuna cikin xumudi.
.
Ya ce da ni yana fara''a,
.
"qwarai kuwa. Bayan haka shi zai baka muhalli, shi zai dauki nauyin abincinka safe da rana ko da yaushe."
.
Nayi shiru ina tunani don kuwa arziqi ya soma qwanqwasa min qofa. Nayi saurin lissafa dubu talatin Sau goma sha biyu, naga cewar kudin sun kai har naira dubu dari uku da sittin. a shekara daya fa kenan kawai. To idan Kuma na kai shekara goma milyan nawa kenan?
.
Naji xufa ta fara kwararo min, Kawuna yana kallona yana murmushi.
.
Haqiqa arziqi ya samu!"
.
Abu na farko da na fara rayawa a xuciyata shi ne, aure Zubaida. abu na biyu Kuma shi ne yadda zan yada zango a qofar shagon Maman bose cikin isa da qasaita a duk lkcn da nazo garin. In fito daga cikin mota ta mai shegen tsaya in more. Kawuna ya ci gaba da cewa.
.
"ya kamata tun ynx ka fara tunanin abin da zaka yi da kudin da zaka samu mansur....bana son almubazzaranci, ya kamata ka yi aure nan ba da jimawa ba." don kuwa in kana da aure zaka fi zama mutum nutattse mai kamala a idon mutane."
.
Aure! naji Kawuna ya sake budo min wani babi mai cike da damuwa a xuciyata. Kullum in aka yi min tadin aure sai na tuno da abar begena Zubaida. har ynx ina son Ku san cewar tun lkcn da nayi bankwana da Zubaida a ranar mu ta qarshe a makaranta har ynxn qaunarta tana nan daram a xuciyata. Kamar aikin sihiri, Kuma tun daga lkcn ban sake jin labarin inda take ba a duniya. Ban san a inda tayi aure ba, to amma Kuma xuciyata ta kasa jurewa in haqura da son ta, har ynx ban sake jin ina son wata mace ba a duniya. Bani da tamkar Zubaida. Kuma ba zan sake samun tamkarta a duniya ba." don kuwa ita kadai ce mace da xuciyata take so da qauna. Kuma Kullum idan na kwanta barci sai na ganta a mafarki. Wani lkcn in ganta a cikin damuwa, wani lkcn Kuma in ganta cike da annashuwa. Amma Kuma duk sanda nayi mafarkinta bata tsyawa muyi hira, sai dai in qura mata ido tana tsaye.
.
A haka nake ta bin rayuwar wannan masoyiya tawa, na san cewar ita tana can tuntuni ta mance da ni a rayuwata. Amma Kuma ni gashi ta barni ina ta fama da ciwon sonta shekara da shekaru.
"sai yaushe wannan ciwon mai tsanani zai rabu da xuciyata, don in samu sukuni a rayuwata?"
.
Nayi murmushin qarfin hali na cewa Kawuna.
.
"alhaji ai ni tuni na haqura da aure a duniya."
.
"sbd me mansur...a qanne dalili?"
.
Na kalle shi, sannan na waiga gefen da kakata juma take na ce dasu cikin damuwa.
.
"tun lkcn da na rasa wata masoyiya tawa a makaranta mai Suna Zubaida. Tun lkcn na haqura da batun aure a rayuwata. Don kuwa ita kadai ce macen da nake so
Gashi kuma ta tafi ta barni."
.
.
**
.
Tun lkcn da na sauka daga tasin da ta daukoni daga gidan Kawuna na fara hango katafaren gidan Alh. Bashir Gurgu. farin sol dashi daga nesa kamar an daukoshi daga birnin sin. Na tsaya akan titi ina kallon gidan xuciyata cike da mamaki, don kuwa duk tagogin gidan da Kuma qofofin duk na gwalagwalaine. Sannan Kuma ga shuke-shuke nan burjik sun zagaye gidan cike da furanni jajaye da farare masu ban sha'awa.
.
Bayan na gama kallon ne sai na kama hanya na tunkari faffadar qofar shiga gidan. Daga nesa ina iya hango wani tsohon mai gadi a zaune riqe da bulala a bakin qofar. Kwana biyu kenan da xuwanka kaduna tare da kaduna tare da Kawuna. A cikin kwanaki biyun suka gama shirya komai da alhaji bashir gurgu, ynx xuwana kawai ake jira in xo in fara aiki, Kuma gashinazo.
.
Kafin in qarsa inda mai gadin yake sai da na sake tsayawa na dubi kayan dake jikina, kafin in baro gidan Kawuna na daukar cewar kayan da na sako na qure adaka zasu fitarku da ni kunya. To amma Kuma a halin ynx da naxo naga yanayin gidan, sai Kuma naji kwalliyar da nayi ba ta gamsar da ni ba." na dubi takalmina mai kan ,.kura, Wanda shi kadai ne abin arziqi a kayan jikina. Bana shekara takalmin shiga kenan a wajena, a wurin wani tsohon dan sanda mai ritaya na sayen shi. Kada ka so jin Sauran kayan dake jikina, don kuwa kodadden wando ne shudi Wanda ya sha faci manya-manya kamar tamfol din fyadin masara. Sai Kuma baqar riga mai kwala da Kuma shudiyar hula hana-sallah da na ta6a ciyota a wajen caca.
.
Na sake duban katafaren gidan naji tsoro da Kuma rashin qarin guiwa sun kamani. Don haka ina xullumin wataqila idan Alh. Bashir yaga shigar da nayi ya ji ban kwanta mashi a raina ba." wataqila ma ya ce ya fasa daukata aiki a gidansa. To amma kuma me zai sa in damu kaina? Shi Fa gurgu ne, ni Kuma ina da qafafuwana.
.
Don haka sai na tunkari gidan kai tsaye, na samu tsohon dake gadi a zaune kan bench, tun kafin in yi masa sallama ya dago kai ya duba ni sannan yayi min murmushi, kamar damar can ya ta6a ganina, sai dai Akwai alama ya san da xuwana.
.
Bayan nayi masa sallama ya amsa, tun kafin in yi masa Bayani ko ni wane ne, sai ya tambayeni.
.
"kai ne mansur da aka ce zaka xo?"
.
Nayi saurin gyada masa kaina.
.
"eh, ni ne."
.
Tsohon ya riqe ya tarbeni cikkin girmamawa.
.
.
Lp=10Mugun albishir
page 10
.
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
(Madugun taska)
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
.
Tsohon ya tarbeni cikin girmamawa. Akwai alamar fadanci a tattare da shi, sannan Kuma idan mutum yayi la'akari da busassun idanunsa da ya ragadawa kwalli da Kuma yadda Ya karkace hularsa gefe daya, nan da nan mutum zai gane cewar a wani zamani can da ya gabata sanda yana Saurayi da wahala idan ba taqadarin yaro akayi ba."
.
Tsohon ya sake ce min..."
.
"sannu da xuwa mansur...ai tun daxu Alh ke tsammanin xuwanka. Ya ce da ni in ka xo in jagoranceka mu shiga tare. Zo mu je mansur."
.
Na bi Tsohon a baya muka shiga cikin gidan, ina zazzare idanu kama 6atacciyar tunkiya. A farfajiyar gidan, danqara-danqaran motoci ne guda biyar Suna ta qyalqyali kowacce launinta gaban. Tsohon ya bude wata qofa. Muka shiga wani dogon daki mai cike da gwala-gwalai. Sai qamshin ke tashi a ciki. An malale darduma mai taushi kamar zata hadiye qafar mutum idan yana tafiya kanta. Na ja na tsaya a wuri guda ina kallon ikon allah. Tsohon ya juyo cikin mamaki ya ce da ni.
.
"zo mu je mana mansur."
.
Na ce dashi.
.
"ina Kuma zamu je banda nan baba?"
.
Tsohon ya bushe da dariya sannan ya ce da ni.
.
"ai bamu kai falon alhaji ba." nan ai zaure ne kawai mansur....kai dai biyo ni kawai mu tafi."
.
Tsohon ya sake ja na muka fita daga tsararren dakin, muka fada wani tanqasheshen falo mai dauke da wani qaton gilashi a bango yana bayyanar da hotunan namun daji iri-iri, da Kuma kyawawan furanni, sai ka ce fuskar majigi. Shima wannan gwala-gwalai ne a jiki kamar kayan wasa. Na rabu6e a jikin bangon falon ina jiran Tsohon ya bani izini, don kuwa tsammanin da nake yi duk inda na tsaya a cikin falon laifi ne....!
.
Tsohon ya dube ni cikin murmushi
.
"naga ka sake tsayawa mansur. Me ya faru Kuma?"
.
Na ce dashi.
.
"ai na dauka nan ne falon alhaji din da kake magana."
.
Tsohon ya sake yin dariya ya ce da ni.
.
"haba mansur, me alhaji zai yi da wannan falon, kai dai baka rabo da abin dariya Wlh. Wannan ai dakin saukar baqin ne, masu neman ganawa da alhaji kafin ya buqaci ganin su." Kada ka damu mansur, zamu je kaga falon alhaji."
.
Tsohon ya sake shigewa gaba, na bishi a baya muka fice daga wannan falon ya sake tura wata qofar zinare dake kalle, duk jikin qofar qyalqyali yake yi. Nayi tsammanin zan hango ko me ke a cikin dakin ta gilashin qofar, Maimakon haka sai na hango hoton razananniyar fuskata a jikin gilashin qofar. Nan da nan sai na fara addu'arziqi allah ya sa babu qananun yara a gidan. Don Kada in tsorata su su da abin da na gani a jikin qofar a matsayin fuskata. Tura qofar keda Wuya sai ta bude ba tare da wani sauti ba, a lkcn ne to naga wani abin mamaki, Kuma na gamsu haqiqaTsohon nan bai yi qarya ba, Sauran dakunan da muka je a baya, idan aka saka su a cikin tsararren falon Alh.Bashir Gurgu to duk sai sun 6ace ma an rasa inda suke. Tsohon ya shige gaba na bishi a baya. na saka qafata a cikin tsararren falon mai dauke da lallausan kilishi. Na fara kalmar shahada a 6oye a xuciyata, don kuwa nayi tsammanin xuqeni kilishin zai yi.
.
A zagaye da falon kujeru ne na alfarma shiga-shiga sun yi kuri sun saka wani faffadan teburi a tsakiya, yana ta sheqi da daukar idanu. Tunda nake a duniya ban ta6a ganin kwatan-kwacin kayan alatun da na gani a wannan falon ba." gabaki daya gidan cunkushe yake da kayan alatu. Sai da naga tsohon ya xube a qasa cikin girmama, sannan na lura da abin dake zaune dan surutu akan kujeru kamar kashin tsoro. Wani motsattsen mutum ne dan tsurut a zaune' qafafuwan wandon shi biyu suna ta reto babu komai a cikin. Idanuwanshi jawur kamar garwashin wata. Dogon hancinshi da Kuma tsukakken baking shi hade da motsattsiyar fuskarshi su ne suka maishe shi xuwa siffar aku kuTuru sannan suka maida shi mai siffar 'yan bori
.
"rana ya dade ga mansur din da ka ce in ya xo a shigo dashi."
.
Tsohon ya fada a sanyaye sannan ya tashi cikin girmamawa ya fice daga falon kamar walqiya.
Mutumin da na kasa tantance aljani ne ko bil adama , ya dube ni sannan yayi murmushi. Ina tsaye akan shi qerere ina dubanshi. Wani in ya zo ya same shi zaune a falon, yana iya daka mashi tsawa ya ce zai kore shi. Don kuwa sam muhallin baiwa yi kama dashi ba sam. Zai yi kimanin shekaru hamsin, kanshi cike yake da furfura, kamar an yi 6arin garin masara.
.
"ga wuri nan mansur, zauna mana."
.
.
Lp"11
mugun albishir
Page 11
.
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni.
Abu ihsan bn ishak
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"ga wuri nan mansur, zauna mana."
.
Ya ce da ni, sannan ya nuna min kujera da hannunshi. Nayi ajiyar xuciya sannan na za6i kujera daya na zauna. Duk da yake Akwai na"urar sanyaya daki a falon, hakan bai hana ni jin xufa na keto mani ba, don kuwa na tabbatar wannan firirinn da na iske a ynx shi ne attajirin da ya dauke ni aiki, Kuma shi ne ke da wannan tarin dukiya kamar qasa.
.
Ganin na qurawa qafafuwan wandonshi idanu, sai mutumin ya dubi

1 Comments On MUGUN ALBISHIR
avatar
abdallah

1 year ago

Reply

Inason saya t coins

Please Login or Register in order to submit comment