Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin mazajen dana aura shi ya fi bani wahala fiye da kowa a cikin su." ya cika taurin ran tsiya, na bi hanyoyi da dama don in kashe shi, amma Kuma ban samu nasara ba." gsky ne, haqiqa ni ce na tura shi a rami da gangan, musamman na samu waje nayi fakin da motar don ta dawo baya ta fada cikin ramin yana barci bai sani ba." tun kafin mu fito na zuba mashi maganin barci a shayi. Nayi haka ne don in tuqa shi yadda nake so ba tare da ya farka ya fahimci abin da nake son aikatawa ba." to amma a wannan hanyar ma ban samu nasara ya mutu ba, sai dai kawai ya rasa qafa ya zama gurgu."
.
Zubaida ta dan yi siririyar dariya, sannan ta dawo ta hade ranta. Naji xufa na keto min ta ko ina. Ta dube ni cikin raini , sannan ta ce.
.
"ina ta neman hanyar da zan bi in kashe gurgun mijina kwatsam, sai ga ka mansur wai ka zo mijina zai daukeka aikin direba. Da ganin haka na san cewar na samu hanya da zan kashe mijina cikin sauqi Kuma in fitar da kaina daga zargi. Don kuwa na san cewar kana sona, kana qaunata tun muna makaranta. Ban ta6a fitowa na nuna maka na fahimci kana qaunata ba sbd baka kai matsayin da zan yi soyayya da kai a duniya ba mansur."
.
Don haka sai na yaudareka, nazo dakinka a cikin dare na baka labarin qarya don ka ji tausayina ka taimake ni. Kuma na baka tsoro na ce mijina ba zai mutu ba sai ya qara shekara talatin a duniya. Abin da baka sanin ba shi ne;
Tun kafin in zo in baka wannan labarin dama tuni na zubawa mijina guba ya sha a lemu. Sai da na tabbatar ya mutu san naxo na same ka a dakinka. Nayi maka haka ne don ka tashi ka je ka kashe shi ka riqa tsammanin kai ka kashe shi ba ni ba." ina ganin lkcn da ka shiga falon kana sanda a cikin dubu ka mirdewa gawarshi wuya. Sannan ka koma daki. Nayi haka ne sbd kodak anzo shari'a ba zaka bari a dora min laifi ba Tunda kana qaunata, Kuma kayi alqawarin zaka yi wa kotu bayanin kaina ne ka kashe shi."
.
Bayan mun je kotu an yanke maka hukuncin daurin shekara goma, ni Kuma sai na sake samun wani attajiri, Wanda yake son yaga ya ajiye kyakkyawar mace yarinya. Kafin wata hudu ya bi Alh.Bashir shiga na kashe shi. A cikin shekaru goman da kayi a furzun ba zan iya fadin adadin mazan da na aura ba kai tsaye, sai dai Kuma a halin ynx sun zama tarihi."
.
Xuciyata ta ci gaba da bugawa kamar zata fasa qirjina ta fito waje. Don kuwa Zubaida ta gama rikita ni. Na bi ta da kallo cike da takaicin ganin na qarar da rayuwata a qaunarta, amma Kuma ita ba ma ta ni take yi ba." sannan Kuma na dorawa kaina laifin da ba ni na aikatashi ba, don in karen rayuwarta da mutuncinta naji nayi shekaru goma a gidan yari, duk a dalilin wannan kyakkyawar mace dake tsaye a gabana tana yi min kallon mahaukaci sha-sha-sha!
.
.
Naji hawaye sun taru a cikin idanuna, sannan Kuma naji ni kaina na tsani kaina. Na ce da Zubaida ina kuka.
.
"Kada ki yi min haka Zubaida. Duk duniyar nan ban ta6a jin ina son wata mace ba sai ke kadai. Ki ji tausayina Zubaida Kada ki karya alqawari."
.
Hawayen baqin ciki suka fara kwaranya a idanuna, Zubaida ta dube ni a yatsine cikin izgilanci ta ce da ni.ya
.
"kayi kuskure mansur, Tunda nake ban ta6a jin ina sonka ba, Kada ka ta6a rayawa a xuciyarka na ta6a sonka a duniya, Kuma har abada ba zan ta6a sonka ba."
.
.
Lp=30Mugun albishir
Page 30
.
daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ka yi kuskure mansur, tunda nake ban ta6a jin ina sonka ba, Kada ka ta6a rayawa a xuciyarka na ta6a sonka a duniya, Kuma har abada ba .zan ta6a sonka ba."
.
Muka hada idanu da ita tsawon lkc, xuwa can Kuma sai naga kamar zata fashe da dariya, sai nace da ita.
.
"ni dama na san cewar wasa kike yi min, kin cika son wasa Zubaida. Bai kamata ace kina yi min irin wannan wasan ba, ni na san kina sona, kina dai fadar wadannan maganganun ne don ki bani tsoro....bana son irin wannan wasan, in abin ya xo da tsautsayi sai ki ga mutum ya kamu da hawan jini."
.
Zubaida ta murtuke fuskarta a fusace ta ce da ni.
.
"wa ya fadi maka cewar wasa nake maka? To bari in tabbatar maka cewar ba na sonka Kuma ba wasa nake yi maka ba mansur."
.
Tana gama fadin haka sai ta daga zazzaqar muryarta ta kwadawa qartin da na baro a waje kira.
.
"kuna ina?"
.
Na ji qartin sun amsa baki daya kamar kwaduna.
.
"gamu nan xuwa hajiya."
.
Na ji sun rugo aguje kamar an koro raquma har qasa ke amsawa. Suka shigo harabar gidan suka shawo kwana kowannensu da qaton ciki kamar masaki. Da xuwansu tun kafin su huta, sai Zubaida ta nuna ni da dan yatsa sannan ta ce a fusace.
.
"Ku lallasa min wannan baqon har sai kun ga baya numfashi."
.
Tun kafin ta rufe baki babban cikin su ya daukeni yayi qoli-qoli da ni kamar ya dauki 6awon kara, ya kwada ni da qasa, kaina ya hadu da dutse, naji xogi da radadi sun soke ni, na fara ihu ina yi masu magiya.
.
Qato daya ya sake rarumata ya yi sama da ni shima ya sake ni na fado tim! Suka hau ni da duka kamar Suna buga ganga. Tun ina iya yin ihu har na kasa motsawa. Abu na qarshe da naji kafin in suma shi ne tattausar muryar Zubaida tana dakawa qartin tsawa a fusace tana cewa.
.
"ku dauke shi ku je can ku jefar dashi a bakin titi ya qarisa a can!!"
.
.
**
.
.
Ban san adadin lkcn da na yi a some ba, na dai farka na samu kaina a kwana a cikin wasu ciyayi dake a cunkushe da bakin titi. Na dago kaina daqyar naji hucin wucewar motoci Suna wucewa ta Gabana a guje kamar kibiyoyi. Nayi qoqari na tashi daqyar. Idanuna sun yi min nauyi, daqyar nake iya ganin hasken sararin samaniya. Yamma tayi sosai Babu hasken rana, ga alama qarfe shida tayi na yamma. Wannan shi ya ganar da ni cewar na dauki fiye da awoyi biyar a cikin ciyayin ban san inda kaina yake ba." idan nayi la'akari da lkcn da masu gadin Zubaida suka lallasa ni a gidan ta, kafin su dauko ni su zo su watsar da ni a bakin titi kamar yadda ta basu umarni cikin fushi.
.
Na kama ciyayin da na tsinci kaina a ciki na fara yunqurin miqewa tsaye, hannu a hankali ina qara samun sauqi, don kuwa na fara ganin abubuwa dake kai komo a wurin da aka jefar da ni. Inda Babu kowa, ga alama Bayan gari ne....! Don kuwa Babu Wanda ya san ina kwance a wurin. Babu mutane sai jefi-jefi da gine-ginen qananuun masana'antu da aka rufe suka daina aiki a bakin titin. Wannan shi ya ganar da ni cewar babu mama a cikin mota suka xubo ni suka zo da ni suka watsar.
.
Na lalla6a na samu a hankali na fito daga cikin ciyayin kayana sun yi fata-fata, duk jikina a kumbure yake don kuwa na ci uban duka kamar kalangun noma. a haka na samu ina tafiya juwa na barazanar daukata ta kayar da ni a qasa, har dai na samu na kai kaina gida inda nake kwana a wani aljihun aure a gidan wani mutum da ya saba da ni Bayan na fito daga gidan yari.
.
Bayan na kwanta sai abubuwa masu yawa suka riqa dawo min cikin xuciyata
.
"ku lallasa min wannan baqon har sai kun ga baya numfashi..."
.
Na tuno muryar Zubaida sannan kuma na lkcn da take cewa qartin.
.
"Kuma dauke shi Kuma je can Kuma jefar dashi a bakin titi. Ya qarisa a can...."
.
Abin da ya faru ya riga ya faru! Ynx tunanin abin da ya wuce Bashi da amfani. Don kuwa tunanina bai wuce na Zubaida ba." gashi kuma ta butulce min ta yaudare ni ta cuci rayuwata. Kin zalunce ni Zubaida! Na ce a xuciyata ina kukan baqin ciki
.
To amma kuma nima na zalunci kaina, don kuwa tun farko da ace na haqura tun a lkcn da na fahimci Zubaida ta fi qarfina da duk wannan matsalar bata faru da ni ba." sannan kuma wannan lamarin da ya faru da ni, na san cewar alhakin marigayin mijinta ne Alh.Bashir gurgu. Don kuwa na ci amanarshi na goyawa Zubaida baya ta kashe shi. Alhakinshi ne ya fara kama ni, kuma zan ci gaba da fuskantarabubuwa da dama a gaba a dalilin wannan son xuciya da nayi na kasa mashi amanar da ya bani.
.
Ba zan ta6a mance lkcn da motar asibiti ta dauko gawarshi ta wuce ta gaban mu muna a cikin mota muna kallo ni da matarshi Zubaida ba." lkcn ban ta6a tsammanin zata yaudareni ba, haqiqa nayi kuskure. Kuma nayi abin da xuciyata take so na 6ata tarihin rayuwata
.
na san cewar ba zan ta6a daina son Zubaida ba a rayuwata. Har ynxn kuwa da ta san aka yi min wannan rubdugun dukan, ina nan ina sonta a cikin xuciyata. To amma Kuma ya zame min dole in haqura in qaurace mata. Don kuwa ruwan ba tsaran kwando bane. Babu matsala! Na ce a xuciyata. Ba ni kadai bane namiji na farko da ya ta6a samun matsalar soyayya. Akwai mutane da dama a duniya wadanda suka dade Suna neman soyayyar wasu matan, kuma basu samu goyon baya ba."
.
Zubaida bata qaunata! Don haka na haqura da ita!!
.
Na rufe babinta a cikin xuciyata. Amma Kuma duk da haka idan nayi sa'a, wata rana zata canza ra'ayinta ta xo wurina ta ce ta dawo tana sona. Zan amshi soyayyarta Kuma cikin gaggawa sannan Kuma zan yi farin ciki mai yawa a duniya. To amma kuma anya Zubaida zata so ni?
.
Bayan nayi kwana ina jinya kamar Wanda yayi hadarin mota, sai qarfina ya dawo na ci gaba da harkokina. A safiyar rana ta uku ne, ina zaune nayi tagumi ina sauraren qaramin rediyona ina jin labaran duniya, sai naji muryar matar dake gabatar da labaran tana cewa;
.
"A yammacin jiya ne jami'an tsaro suka cafke Hajiya Zubaida wacce aka kama dumu-dumu da laifin kashe mijinta alh.rufa'i, ta hanyar tuno shi daga bene mai hawa uku. Wata majiyar ta ce Zubaida ta auri mazaje barkatai sun mutu. Kuma anan zargin duk ita ce take kashe su." a halin ynx dai tana nan a babban ofishin 'yansanda na jiya. To allah ya kyauta, Kuma ya jiqan marigayi Alh. Rufa'i...."
.
Tun kafin in gama jin labarin nayi sauri na miqe tsaye Xumbur! A tsorace kamar Wanda aka tsirawwa allura. Wacce Zubaida Kuma 'yansanda suka cafke? Na tambayi kaina. Zubaida masoyiyata? ko shakka Babu ita ce, don kuwa sunann mijinta alh. Rufa'i! Shi ne mutumin da ya aikeni gidanshi aikin gida ramin fanfo har matarshi Zubaida ta sa aka lallasa ni.ya kwana uku fa kacal kenan da ganin mutumin, amma Kuma gashi ynx anan bayar da sanarwar mutuwarshi a rediyo.
.
lp=31
Mugun albishir
Page 31
.
(kammalawa}
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
kwana uku kacal fa kenan da ganin mutumin amma Kuma ynxn gashi anan bayar da sanarwar mutuwarshi a rediyo.
.
Duk da haka sai naji tausayin ta ya kamani, don kuwa ina yi mata so ne irin wanda ko me zata yi min a duniya ba zan ta6a ganin laifinta ba." bana so in amince da wannan zargi da naji an fadi a rediyo, Wanda aka dora shi a wuyan kyakkyawa Zubaida. Bana son in ji mutane Suna cewa ita ce ta kashe mazajenta. To amma Kuma dole ne in amince tunda dai ni da bakinta ta sanar min..."
.
Haqiqa masoyiya ta 'yansanda suka kama!!
Naji hankali na ya tashi sannan Kuma tsoro ya kama ni. Wa zai taimaka mata a wannan karon don kada a yanke mata hukuncin kisa? Nan da nan naji tuni na mance da dukan da ta sa aka yi min, naji ina muradin sake xuwa in taimake ta ko da kuwa wannan shi ne abu na qarshe da zan yi a rayuwata.
.
Na san cewar wasu zasu ga laifinta akan wannan aikin keto da zan sake yi wa masoyiyata. To amma Kuma me zai sa mutane su ga laifina don na ceto rayuwar wacce xuciyata ke bege dare da rana? Duk lkcn da dan adam ya fada tarkon soyayya, to shi kenan rayuwarsa ta fada cikin hadurra masu yawa, don kuwa babu mamaki don ma'aboci soyayya ya sadaukar da rayuwarsa ga macen da yake so. Ko da kuwa ace ita bata qaunarshi, kamar dai yadda nima na fada cikin tarkon son Zubaida Kuma nayi rashin sa'a, ita bata so na a rayuwarta.
.
Nan da nan cikin sauri na fice daga dakin, na bazama xuwa babban ofishin jami'an tsaro don in ga masoyiyata, Kuma na dauki alqawarin sai na ceto rayuwar ta kamar yadda na ta6a ceto rayuwarta a wani zamani can da ya wuce. Mai yiwuwar a sake yanke min hukuncin daurin shekaru goma, idan ban ci sa'a ba kuma a yanke min hukuncin daurin rai da rai, ko Kuma hukuncin kisa.
.
To a qalla dai ko ma dai me za a yi min, na san cewar ba a kashe min wannan kyakkyawar mace da nake so ba shekara da shekaru. Wani dadin gushi Kuma na san cewar ko bani a raye zata riqa tuna ni tana baiwa mutane labarin soyayyar da nayi mata a duniya, Kuma ta haka ne zata gane cewar ni ne masoyinta na gsky, Wanda ba zata sake samun kwatankwacina ba a rayuwarta.
.
.
**
.
.
Lkcn da na isabella ofishin 'yansanda na roqi ganin Zubaida na dan sha wahala kafin a amince a bani wannan damar. Daga baya ne aka hada ni da wasu kwalawa biyu suka raka ni xuwa wani daki inda aka kume ta da wani murgujejen kwado kamar Damisa. da yake Akwai dogayen qarafunna da suka tare qofar dakin, ta nan na hangota a zaune ta kifa kanta akan guiwoyin qafufunta tayi shiru ga alama kuka take yi.
.
'yansanda suka ce sun bani minti biyar agurguje, sannan Kuma suka dan matsa daga nesa suka bani wuri. A lkcn ne na kira sunanta a cikin tausayawa. Zubaida ta dago kanta a cikin kaduwa da mamaki a lkcn da tajikistan muryata. Idanunta sun kode sbd tsabar kukan da ta ci. sannan Kuma duk gashin kanta ya hargitse da gani ka san ta ci uban wahala a wajen tuhumar. Ta taso cikin sauri ta matso jikin qarafunan, sanye da doguwar riga baqar mai kwalliya a qirjinta. Ta tsaya a jikin qarafunan muka qurawa juna idanu. Ta fashe da kukan nadama ta ce.
.
"ba zan iya hada ido da kai ba mansur....na cuci rayuwarka na zalunceka a duniya ka yafe min..."
.
Na ce da ita cikin tausayawa
.
"....kada ki damu Zubaida na yafe maki duniya da lahira, ba koma..."
.
Zubaida ta sake dubana hawaye Suna tsere akan kyakkyawar fuskarta ta ce da ni.ya
.
"tun lkcn da jami'an tsaro suka kamani suka kawo ni wannan wurin, Babu wani mutum da ya xo ya kawo min ziyara yaga halin da nake ciki mansur....amma gashi kaine mutum na farko da yaxo ya kawo min ziyara, duk da butulcin da nayi maka baka mance da ni ba mansur?"
.
Ta sake fashewa da wani kukan. Na ce da ita.
.
"ba komai Zubaida, wannan ya wuce, ki daina wannan maganar, na san cewar abin da ya faru sharrin shaidan ne. Kuma ynx ma na sake xuwa ne don in ceto rayuwarki, ba zan ta6a bari wani abu ya sameki ba muddin ina numfashi a duniya. Na zo ne in sanar dake cewar zan fadawa 'yansanda cewar nine na turo mijinki Alh. Rufa'i daga saman bene ya mutu. In yaso ke ma ki basu wannan labarin, na amince ko me zasu yi miki ni suyi min a madadinki Zubaida."
.
Zubaida ta girgiza kai cikin rashin amincewa.
Ta zzaro hannunta ta dora su akan yatsun hannuna dake riqe da qarafunan. Wannan shine karo na farko a rayuwata da ta ta6a yi min haka. Ta ce da ni.
.
"ba zai yiwu ba mansur,don kuwa ka dade kana shanta wahala a dalilin qaunar da kake yi min.ko me ya faru da kai ni ce na jawo maka. Lkc ya yi da ya kamata nima in fuskanci na wa hukuncin, don kuwa na aikata laifuka masu yawa a duniyar nan. Ba zan sake bari laifina ya shafeka ba." ynxn kam na amince kai masoyina ne mansur,don ka san martabar soyayya, Kuma ka san haqqin masoyrka, amma Kuma baka yi dace da wacce kake so ba." ban dace da irin rayuwarka ba mansur....kai mutumin kirk ne, ni Kuma mai laifi ce. Ina fatan zaka samu wata masoyiyar wacce ta fi ni a duniya, don kuwa ni tawa tazo qarshe. A wannan satin za a yanked min hukuncin kisa!!!"
.
Naji takaici ya lulli6e min xuciyata, sannan Kuma hawaye suka fara xubo min..." Zubaida ta sake qanqame yatsun hannuna ta ce da ni.ya
.
"Kada ka damu mansur, mutuwata ita ce samun sauqi a gareka, idan ina raye zan ci gaba da jawo maka wahalhalu a rayuwarka, don kuwa kana matuqar sona, ba zaka iya bari wani abu ya faru da ni ba." kayi haquri kabarin su yanke min wannan hukuncin a halin ynxn na amince da soyayyarka, to amma kuma hakan Bashi da wani amfani. Bakin alqalamin ya riga ya bushe."l
.
Muka kalli juna muna kukan soyayya da baqin ciki. Zubaida ta yi min murmushi kamar Babu wani abu da yake damunta. Ta ce da ni a sanyaye.
.
"na da dade ina yi maka (MuGun ALBISHIR) mansur. To amma kuma yau a karon farko zan yi maka albishir mai kyau. Wannan shine sakayyar da zan yi maka a bisa wahalhalun da kasha da ni baya.
.
"wane irin albishir zaki yi min Zubaida?"
.
Ta rage muryarta kamar zata yi min rada sannan ta ce
.
"mansur ina dare yayi ka je Bayan gidan mijina da na turo shi daga saman bene, marigayin Alh. Rufa'i idan ka je zaka isle shuke-shuke a cikin lambun dake a bayan gidan. A cikin wadannan shuke-shuke zaka iske watgajeruwar bibiyar gwanda, ka tonal gindin bishiyar, zaka iske wani qaton akwatu na 6oye, kudi ne a ciki naira milyan hamsin ka dauka duk rabonka ne, damar na 6oye su ne don Kada azo bincike a gansu. Ka daukesu na bar maka su kyauta. Na gode Kuma da soyayyar da ka nuna min, Kada ka mance da ni masoyina, na gode, ina yi maka bankwan...."

Wasu hawayen suka sake zuba mata. To amma Kuma ni a halin ynx ba kudi suka fi damuna ba, baqin cikin rayuwar da ita shi yafi damuna. Kafin in sake cd ita wani abu ne naji hannayen 'yansanda da suka rakoni sun ta6a ni a baya. Na waiga a tsorace na gansu su biyu sun qariso. Lkc ya cika kenan. Suka janyeni da tsiya daga qarafunan da suka ga bani da alamar tafiya. Suka 6an6are hannuwanmu dake manner da juna ni da Zubaida.
.
Ta dago min hannu tana yo min bankwana, wannan shi ne hoton da ta ajiye min a cikin xuciyata. Wanda ba zan ta6a mancewa dashi ba." shi yasa tun a farkon wannan labari na fading maku na dade ina ganin 'yanmata a duniya ina mancewa dasu. To amma Kuma ba zan ta6a mancewa da masoyiyata Zubaida ba."
.
Na daga Zubaida hannu ina tafiya ina waigowa muna kallon juna har na fice daga gidan tuhumar. Na fara tafiya ni kadai a kan titi ina baqin cikin rabuwa da Zubaida. Sai na fara kokwanton anya kuwa ba sharrin ake yi mata ba? Na tuno yadda muryarta musamman a ranar da muka fara haduwa, tun lkcn da ta zo wurin ta zauna, tana yi min kallon soyayya.
.
"....ya sunanta...?
.
Anya kuwa Zubaida ce take kashe mazajenta? Ba zan ta6a amincewa ba." na ce a xuciyata. Sharrin ake yi mata.
Ta amma Kuma ita ma ai ta fading min da bakinta. Ba gsky bane. To dukan da ta sa aka yi min fa? Shima wannan ba laifinta bane, don kuwa tayi ne don ta karen martabar aurenta. Don Kada in sake binta gidan miji in murderers masara wuya.
.
Zubaida bata da wani laifi, tabbas sharrin ake yi mata. Wataqila Kuma ita ce ta aikata laifukan. To amma Kuma ni dai banana....." zarginta. Yaya kuwa zan dorawa wacce nake so a xuciyata laifin kisan kai? Bayan Kuma ita ce mace ta farko da na fara so a rayuwata? sannan Kuma zan ci gaba da son Zubaida har nan da qarshen rayuwata.
.
.
Alhamdulillah!!
Na sadaukar ga kafatanin ahalin "TASKAR GIDAN LITTAFI"
.
Jinjinawa ga mai mai gida shafi'u D Giwa
.
Kina na a xuciyata khadija musa shehu.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On MUGUN ALBISHIR
avatar
abdallah

1 year ago

Reply

Inason saya t coins

Please Login or Register in order to submit comment