Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

datsattsun qafafuwanshi sannan ya dubenni ya ce da ni.
.
"kada kayi mamaki mansur, na san cewar kawunka ba zai rasa baka labarina ba, bani da qafafuwa, ni gurgu ne, yadda ka ganni zaune a haka nake kwana nake tashi babu inda nake xuwa."
.
Na girgiza kaina cikin damuwa. Don kuwa ban san abin da zan iya cewa ba, ya sake cewa da ni.
.
"to amma duk da wannan naqasar da nayi mansur, ina da milyoyin kudi masu yawa. Sannan Kuma duk abin da nake neman a duniya na samu."
.
Ya yi murmushi, shi kanshi ga alama abin da ya fada yayi mashi dadi. Nayi shiru ban ce dashi komai ba, xuwa can Kuma sai na ji yayi ajiyar xuciya, ya dawo maganar da ta kawoni gidanshi.
.
"mansur kamar yadda ka sani, ka xo gidan nan ne a matsayin direba to amma Kuma ba ni zaka riqa tuqawa ba, ni Babu inda nake xuwa, matata zaka riqa tuqawa a mota, duk inda zata je kai nake so ka riqa tuqata kana kai ta."
.
Ya tsayar da idanunshi akaina sannan ya rage fara"a.
.
"ka san abin da yasa nake son ka zama direban matata mansur?"
.
Na ce dashi.
.
"A 'a."
.
Alh Bashir ya ce da ni cikin damuwa,
.
"ban yarda da ita bane mansur, ina zarginta, don kuwa ta kan dauki mota ta fita ban san inda take xuwa ba." Babu mamaki don taga na zama gurgu na naqasa shi yasa take xuwa wajen wasu mazan a can wani wajen. Shi yasa na yanked shawarar in nemo mata direba.
.
Ya sake yi min murmushi, ina zaune ina kallon shi.
.
"ina matuqar son wannan mata tawa mansur."
.
Ya ce da ni.
.
A duniya kaf ban ta6a ganin abin da nake so ba irin ta, shi yasa nake masifar sonta, ko kallon ta naga wani namijin yayi, sai in ji duk na damu. Zan iya sa bindiga in harbe mutum idan na fahimci yana son wannan mata tawa. Shi yasa aka nemo min kai mansur, don kuwa na samu labarin kai yaro ne mai amana. Kuma nutsttsen mutum, na san cewar zaka riqe min amanar matata. Na barta a hannunka amana mansur, Kada ka bari mutane su riqa kallonta. Ko kallon ta ba na so a riqa yi. Ina fatan zaka riqe min amanar ta mansur?"
.
Nayi ajiyar xuciya sannan na ce da shi.
.
"ba komai Alh. In allah ya yarda zan riqe maka amanarta kamar yadda kake so."
.
Alh.Bashir yayi murmushin jin dadi. To amma ina matar tashi take? Na qosa in ganta.
.
Muna nan zaune sai muka ji sautin shigowar mota cikin gidan, a can harabar gidan. Aka ba motar wuta xuwa can kuma aka kashe motar, sai muka ji an rufe ta da qarfi garam! Alh.Bashir ya ce da ni cikin damuwa, bayan ya dube ni.
.
"matata ce ta dawo mansur, haka take Kullum bata tuqa mota a hankali, duk ta lalatamotocin gidan nan."
.
Muna nan zaune sai muka ji sautin tafiyarta zata shigo falon. Qwas-qwas! Naji gabana ya fadi, don kuwa akwai wani zamani da ya wuce na ta6a jin irin sautin tafiyar.
.
Ta turo qofar falon ta shigo a fusace Babu ko sallama, na waiga cikin kidimewa na dubeta. Jikin jikina ya tsaya cak!! Sannan hantar cikina ta kada. Numfashina ya tsaya na wucin gadi sbd tsananinn kaduwar da nayi a dalilin ganiNta
.
Tana nan da xunxurutun kyanta kamar yadda na santa tun a shekarun baya da suka wuce fuskarta mai cike da annuri tana nan wasai, ta qara annuri da kwarjini. Na tuno ranar farko da muka fara haduwa a makaranta.
.
"yaya sun ka.."
Na tuno daddadar muryarta mai kama da dorewa.
.
Kafin in dawo hayyacina ne Alh. Bashir ya yi min dariya sannan ya ce da ni.
.
"ita ce matata da nake baka labarin ta mansur, Kuma gaisa mana. 'yar garinku ce, a dariya na aurota, sunan ta Zubaida!!
.
.
Lp=12mugun albishir
Page 12
.
.
Daga alqalamiN
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
.
"yar garinku ce, a zariya na auro. Sunan ta Zubaida!!"
.
.
.
** ** **
.
.
Ganin kamar a fusace take sai Alh.Bashir ya ce mata.
.
"Kada kina damu Zubaida wannan yaro ne mai ladabi. Don baki san shi ba ne, amma Kuma kema zaki gani da idon ki, shi ne sabon direban da na samo miki. Duk inda zaki je kina iya fadi mashi, nafi son ya riqa tuqa ki, bana son kina fita ke kadai."
.
Zubaida ta yatsina fuskarta sannan ta wuce ba ta yi magana ba, ta bude wata qofa dake a cikin falon ta shiga ciki.
.
Alh.Bashir ya ce da ni.
.
"Kada ka damu mansur, haka take da saurin fushi, amma zata huce ne daga baya. Kayi haquri da halinta ni ma haka nake haquri."
.
Nayi ajiyar xuciya, sannan na share xufar dake a fuskata, don kuwa ji nake yi kamar fatalwa na gani ko aljana. Naji soyayyar Zubaida ta sake taso min a xuciyata. Na sake tuno ranar qarshe da zamu rabu a makaranta.
.
"yau Kuma ranar rabuwarmu ta zo mansur, mu yafewa juna, sai wata rana..."
.
Da Alh.Bashir ya ga ta dade a cikin daki bata fito ba, sai ya qwala mata kira da qarfi. Zubaida bata amsa ba, ta fito cikin damuwa,,ta sauya kayan dake jikinta, ta sako wata doguwar riga fara da Kuma dogon siket mai qyalqyali kamar jikin macijiya. Ta xubo da gashin jikin ta kan kafadunta kamar balarabiya. Hakan shi ya sake tuno min da ranar da ta xo wurina ta zauna tana yi min murmushin farin ciki. Da xuwanta ya ce da ita.
.
"ki tafi dashi ki kai shi dakin da zai riqa kwana, ki yi sauri ki dawo ina son ganin ki."
.
Zubaida ta wuce gaba, na yi sauri na tashi guiwa ta Babu qwari na bi bayanta tana tafiyar a cikin taqama, muka fita daga falon, naga ta bude wata qofar, muka nufi dakin da za a saukeni. Da shigarmu dakin naga ta juyo ta dube. Muka qurawa juna idanu a lkc guda. Ta ambaci sunana da zazzaqar muryarta.
.
"mansur!"
.
"na'am, Zubaida?"
.
Ta sake ce min..."
.
"baka samu aiki ba ne tun lkcn da muka gama makaranta me kake yi?"
,
Nayi ajiyar xuciya, don kuwa ban san abin da ya dake in ce da ita ba." to amma Kuma ai gashi ynx na samu, Kuma na samu masoyiyata da nake ta faman neman ruwa a jallo. Muna nan a tsaye ni da ita.mun yi cirko-cirko a cikin dakin muna kallon juna, sai muka ji mijinta ya fara daka tsawa a fusace. Da yake daga cikin dakin idan mutum ya tsaya a jikin taga zai iya hango komai na cikin falon alhaji ta hanyar wagegiyar tagar falon. Alh.Bashir ya sake daka mata tsawa.
.
"Zubaida me kake yi ne a dakin? Ba cewa nayi ki kai shi ki yi sauri ki dawo ba? Uban me kuke yi ne a dakin?"
.
Zubaida tayi sauri ta fice a tsorace. Nayi mamakin ganin yadda take jinjinawa Tsoron shi sai ka ce ba gurgu ba." to amma Kuma da nay la'akari da tarin mmilyoyin kudin da ke shaqare a gidan da kayan alatu burjik a ko ina, bai kamata in yi mamaki ba don ta ji Tsoron shi.
.

Lp=13Mugun albishir
Page 13
.
Daga alqalamin
shafi'u dauda Giwa
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
(Madugun taska)
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Bai kamata in yi mamaki ba don ta ji Tsoron shi.
.
Tun lkcn ban sake jin motsin Zubaida a gidan ba." da lkcn cin abincin dare ya yi Alh.Bashir da kanshi ya qwalla min kira. Na same shi a falon ta jera mashi abinci, ta shiga dakinta ta kulle. Ya umarce ni mu ci abinci tare. Ga alama Alh.Bashir yana matuqar sona. Na sa hannu na muka ci lafiyayyar sakwara da naman shanu zuqa-zuqa a daddadan miyan taushen. To amma har lkcn da muke cin abincin hankali na yana kan dakin Zubaida. Na qosa ta fito don in sake ganinta, zan so ace na sake ganin masoyiyata ba don mijinta dake zaune a falo dare da rana ba."
.
"..bana son a riqa kallon ta...ina matuqar son matata...
.
na tuno gargadin shi.
.
.
**
.
.
Wannan shi ne dan taqaitaccen abin da ya faru a rana ta ta farko a gidan Uban gidana da ya dauke ni aikin tuqa matarsa, ni Kuma tsohuwar masoyiyata Zubaida. Don haka da dare yayi sai naji na kasa barci, xuciyata ta cika da baqin kishi mai tsanani , da Kuma damuwa, da na tuna cewar Zubaida masoyiyata tana cikin daki tare daki tare da wannan lanqwasasshen mutum. To amma Kuma ni menace nawa a ciki? Shin ba mijinta ba ne?" na san cewar tunanin dake a xuciyata ba qaramin wauta ba ne da Kuma shirme. Don kuwa in ba tsabar sakarci ba me zai sa in riqa jin haushin mutumin dake tare da matarshi?
.
To amma Kuma ya kamata ni ma fa a tausaya min, don kuwa na riga shi fara son ta. Tun muna makaranta nake nuna mata soyayya. To sai dai Kuma soyayya ta banza ce, tunda dai ni ba ni da motoci da gidan alfarma. Ita Kuma Zubaida kyakkyawa ba matar riqaqqen talaka ba ce irina. Ina ma laifi da na samu aka daukeni aikin direbanta?
.
Ganin cewar barci ya qauracewa idanuna, sai na fito waje cikin tsakiyar dare na zauna ni kadai nayi shiru.
.
Dole ne in qwace Zubaida daga hannun wannan shashashan gurgun mijin nata.
.
Dole ne ya sake ta ya bar min ita in aura, ko yana so ko baya so.
.
Tsawon lkc ina nan zaune kamar a cikin mafarki, sai naji ihun Zubaida a cikin daren ta qwala kuka iya qarfinta. Na tashi xumbur a cikin sauri jikina yana tsima, na nufi inda wagegiyar tagar falon take na leqa. A lkcn ne naga abin takaicin da har abada ba zan ta6a mancewa da shi ba."
.
Alh.Bashir ne riqe da bulala yake dukan Zubaida. Tana durqushe cikin ladabi akan dardumar falon tana kuka, shi Kuma a zaune dan tsurut akan kujera yana ta tsala mata bulala tana kai hannu tana karewa, tana kuka. Ya zaro mata idanu a fusace ya ce..."
.
"don ubanki ko mutuwa zaki yi sai na cikashe bulala hamsin din da nayi niyyar yi maki, ina lissfawa ynx talatin da uku nayi."
.
Ya ci gaba da tsala mata bulala tana noqewa. Ta ja da baya tana sosawa cikin tsananin azaba. Ya ce da ita.
.
"ki matso in qarishe Sauran bulala shida, arba'in da hudu nayi, ina lissafe."
.
Naji tsananin takaici ya soki zuciyata.
.
"shiga ciki ka kashe shi mansur..!
.
Wata xuciyar ta fara yi min kururuwa. Amma ina kallo Alh.Bashir ya qarishe bulalarsa a jikin masoyiyata Zubaida, Babu wanda zai ceceta. Da ya kammala kanta sai ya wurga mata bulalar yayi murmushin mugunta, ya ce da ita.
.
"dauki bulalar gata nan ki 6oye min ita, sai Kuma gobe idan lkcn duka ya yi. Tashi ki bani wuri 'yar iska munufukar banza."
.
Zubaida ta tashi tana sauri da bulalar a hannunta, a haka har ta shige dakinta ta turo qofa ta kulle. Na ji kishi da damuwa sun cika xuciyata. Na san cewar bani da hujjar da zan shiga cikin falon in ce da mijinta wani abu. Don kuwa ko me yayi mata matarsa ce..." ko kasheta yayi ba ruwana. Maimakon haka sai na tsaya jikin tagar Tsawon lkc ina xubar da hawaye. Ina tausayawa masoyiyata Zubaida.
.
.
**
.
Washe gari da sassafe na nufi falon Alh.Bashir cikin damuwa. Na same shi a zaune kamar yadda nake tsammanin zan same shi. Na durqusa cikin ladabi na gaisheshi ina kumbure-kumbure,don kuwa da baqin ciki na kwana a raina. Ya amsa yana murmushi, sannan ya ce da ni, da yaga alamar zan tashi in tafi.
.
"dawo ka zauna mansur, ina son muyi wata 'yar magana ni da kai, zo ka zauna."
.
Na juyo na dube shi cikin mamaki da Kuma fargaba, don kuwa bana son ya fahimci Akwai wata sanayya a tsakanin da matarsa Zubaida. Na dawo na zauna akan daya daga cikin kujerun falon ina fuskantarshi. Ya kanannade kamar alkaki. Ya tattara hankalisa akaina, sannan ya ce da ni.
.
"mansur tun lkcn da kaxo gidan nan daga jiya xuwa yau, na san cewar dole ne ka riqa ganin wasu abubuwa Suna faruwa a tsakanina da matata Zubaida, wadanda zasu daure maka kai sosai. Shi ya san nake son muyi hira in baka wani labari, don ka san ko wacece Zubaida. Sannan Kuma ka san ko ni wanene."
.
Na bi shi da kallo Gabana yana faduwa, don kuwa nima na fara jinjinawa tsoron wannan lanqwasasshen Tsohon mai baqin ran tsiya. To amma Kuma ni ba bulalarsa nake jin tsoro ba, ni bindiga nake tsoro, don kuwa na san cewa a 6oye a jikinshi ba a rasa shi da bindiga. Tabbas ba haka nan yake zaune a falon ba.
.
"mansur."
.
Ya sake kirana, na amsa. Ya ce da ni.
.
"ka ta6a yin aure a garinku ku?"
.
Na girgiza kai cikin mamakin wannan tambaya.
.
"A 'a, bani da mata alhaji, daga ni sai halin."
.
Alh.Bashir ya yi murmushi ya shafi busassun yatsunshi.
.
"kayi sa"A mansur da baka da mata, don kuwa ynx ne zan baka shawarar irin macen da ya kamata ka aura duk lkcn da ka tashi yin aure."
.
Ya sake gyara zaman qafafunshi, qafafun wandon suka motsa suka hadu da juna, Babu komai a cikin su."
.
"Sau da yawa mu maza muna da wani irin halin mansur,"
.
Ya ci gaba da cewa.
.
"wannan halin kuwa shine, duk lkcn da zamu yi aure muna son mu auri mata kyawawa a duniya wadanda duk inda a shiga zamu a riqa kallonsu anan yawa."
.
"haka ne alhaji."
.
na ce dashi. Don kuwa lalla6a shi nake yi don mu rabu lfy, bananas son ya ga kamar na raina shi.
.
Ya yi min murmushi, sannan ya ci gaba.
.
"nima ina da irin wannan halin mansur....na ina son in ga na auri mace mace mai kyau a duniya nan...ka
.
.
Lp=14Mugun albishir
Page 14
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
Tare da ni
.
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
.
Ni ma ina da irin wannan halin mansur, ina son in auri mace mai kyau a duniyar nan. Kai bari dai in taqaice maka labari, tun ina yaro kamar ka har tsufana, ni ban ta6a son wata mace ba sai kyakkyawa. Ban damu da kowanne irin halin mace take dashi ba, in dai kyakkyawa ce to ni kam ta gama biyana komai mansur."
.
Ya sake dubana har cikin idanuna, ya ci gaba.
.
"wannan shi ne abin da ya sa na kamu da son wannan mata tawa Zubaida. Lkcn da na fara ganin ta ban tsaya wahalar binciken halinta ba, haka kawai sai naji duk duniyar nan babu wacce nake so in mallaka kamarta. Ina son Zubaida sosai fiye da yadda zan fasalta maka. Ina sha'awar in ganni tare da ita a cikin mota ta ta haske ko'ina da kyakkyawar surarta. Ni Kuma ina tuqata muna yawon a cikin jin dadi da kwanciyar hankali."
.
Alh.Bashir yayi ajiyar xuciya.
.
"Zubaida kyakkyawa ce, sai dai Kuma halinta bai zamo kyakkyawa ba mansur. Zaka yi mamaki sosai idan na ce da kai Zubaida ce ta mayar da ni gurgu. Shekara uku da suka wuce lfy ta lau, ina da qafafuwa na kamar kowa, ina so ka sani, ba qafafuwa kadai ta so ta raba ni dasu ba, raina ta so ta raba ni dashi mansur. So ta yi ta kashe ni gaba daya!"
.
Kisa? Na tambayi kaina a tsorace. Kamar ya san abin da nake tunani sai yayi farat ya ce da ni.
.
"ba lallai ba ne ka amince da labarin da nake baka mansur. Don kuwa nima a wasu lokuta da suka wuce, sanda na fara son Zubaida da aka zo min da labarinta qin amincewa nayi, sbd na mace akan qaunarta. Sai daga baya da abin ya faru gare ni sannan na gano cewar gsky ake fada. Mansur ni ne mijin Zubaida na tara, Kuma duk cikin mazan da ta aura Babu talaka, duk mutane ne masu bilyoyin kudi irina. To amma Kuma ba wannan ne abin mamaki ba, ina son ka sani cewar mazaje takwas na baya da Zubaida ta aura tuni sun riga mu gidan gaskiya. Sun mutu!"
.
Na sake duban motsattsen mutumin a tsorce. Ya zaro min idanu ya ce.
.
"qwarai kuwa mansur, sun rasu baki daya. Don kuwa duk lkcn da Zubaida ta auri namiji ba ya wuce wata hudu a duniya, wasu Kuma su kan yi tsawon rai su kai har wata shiga ko bakwa, ba ciwon kai ba na qafa sai a wayi gari a ga mutum ya mutu . To amma Kuma ni duk na fi su tsawon kwana. Don kuwa ni shekararmu uku kenan ni da ita har ynxn ban mutu ba, qafafuwa na kawai na rasa."
.
Ya yi murmushi kamar abin da ya fada ya burgeshi. To amma Kuma ni ban yi murmushi ba
.
Ku yi haquri da iya wannan. Sai gobe in Allah ya kaimu a
.
Page 15mugun albishir
Page 15
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
.
To amma ni kuma ban yi murmushi ba, don kuwa tsoro ne cike da xuciyata. Dole ne in ji tsoron wannan labarin da na samu, don kuwa ni ina son in aureta . Gashi kuuma tun ba a je ko ina ba na samu wannan labarin wai mazan da take aura mutuwa suke yi.
.
Na sa hannu na share xufar dake a goshina. Alh.Bashir ya ci gaba da bani labarin
.
"wani lkcn mu maza muna da matsala mansur.ba mu san halin mata ba amma Kuma su sun san halin mu. Mu maza har Kullum mukan dauki kanmu ne a matsayin mutane wayayyu, don haka ba mu da tsayawa mu yi bincike ba akan mace idan zamu aureta.
.
Lkcn da na auri Zubaida na rainata mansur, don kuwa ni din nan da kake gani Dakta ne, ita Kuma yarinya ce qarama, ba wani karatun kirki tayi na azo a gani ba, don kuwa ko digiri ba ta yi ba." to amma Kuma sbd tsananinn wayau da makirci, duk da tarin ilimin nawa, wannan bai hana Zubaida ta shirga min maqarqashiya ba."
.
Ya yi saurin sauya akalar hirar
.
"bari in baka labarin abin da ya faru a tsakanina da matata Zubaida a lkcn da take so ta kashe ni.
.
"Alh. Ya kawar da idanunshi daga kaina ya qurawa wani qwan lantarki na gwal ido, sannan ya ce da ni.
.
"bana kusan shekara uku kenan da yin aurenmu ni da ita. Na fara haduwa da ita ne a wajen wani biki a zariya, duk cikin daruruwan 'yanmatan dake a otel din da aka yi shagalin bikin Babu wacce ta kai Zubaida kyau. Nan da nan na tuntu6eta muka fara hira. Abu kamar wasa tun a ranar farko ta yi min alqawarin zata aure ni, sbd ta san cewar ni ba qaramin attajiri bane. To amma Kuma kafin Zubaida ta yi alqawarin zata aure ni, sai da gindaya min sharudanta, cewar bata zama da kishiya, a lkcn ina da matata mai Suna fiddausi, dawowa ta gida keda wuya na sake ta, muka rabu. Bayan mun rabu sai na kwashe yaranmu biyu na kaisu legas wajen wata qanwata dake zaune a can. Don kuwa Zubaida ta ce min bata son hayaniyar yara a gidanta. Ni Kuma bana son in yi abin da zai 6ata mata rai a rayuwata. Ba a jima ba na aurota mansur, muka zauna kamar da gaske."
.
Ya ci gaba da kallon bango kafin ya ci gaba.
.
"bayan an yi wata uku da yin aurenmu, wata rana kwatsam sai Zubaida ta ce min wai zamu yi wata tafiya. Zamu je wani qauye can gariin kakanninta zamu gaishe su." muka shirya tun da sassafe muka shiga mota. A lkcn ne Zubaida ta ce min ita zata tuqa motar wai a cewarta bata so taga ina shan wahala. Ban yi mata musu ba mansur, na bata kan motar, ni Kuma na zauna a gefenta tana tuqa motar ina kallonta, muna hira a haka har barci ya kwashe ni ban sanI ba, don kuwa tafiya ce mai nisa, kuma gashi hanyar qauye ce akwai muka da kwazazzabai."
.
Alh.Bashir ya yi shiru na dan wani lkc sannan ya ci gaba.
.
"ina a cikin motar ina barci ban sanin ba mansur, sai Zubaida ta tsayar da motar akan wani tsauni mai bisa, Kuma a gefen tsaunin Akwai wasu manyan ramuka masu girma. Shi ne sai ta fito ta barni a a ciki. Motar ta fara gangarowa baya ita kadai, ba a jima ba ta saki hanya ta fada a cikin qaton ramin dake a gefen tsaunin.
.
Motar ta tarwatse a cikin ramin, ni dai ban farka ba sai akan gadon asibiti an yanked min qafafuwa. Ita Kuma Zubaida tana can a hannun 'yan sanda Suna tuhumarta a yadda aka yi ta bar wannan hadarin ya faru bata a cikin motar."
.
Lanqwasasshen mutumin ya dan saki ransa kadan ya dube ni.
.
"ka san abin da Zubaida ta fadiwa 'yan sanda da suka tambayeta mansur?"
.
Na girgiza kai a tsorace, xufa na wanke min fuska."
.
"cewa ta yi wai tana cikin tuqa motar ne sai ta ji fitsari ya kamata, shi ne a cewarta wai sbd tsabar matsuwa ta tsayar da motar ta fito bata kashe ta ba, Kuma bata sa waigi ba har motar ta fara gangarowa da baya. Ita Kuma wai sai sautin fadowarta kawai ta ji cikin rami. "yan sanda basu amince da wannan labarin da ta bayar ba, don kuw duk wanda ya ji wannan labarin ya san na qanzon kurege ne, ta shirya wata hanya ne kawai da zata kashe ni ta kaucewa zargi. To amma Kuma da yake ina matuqar qaunarta ni da kaina na dauki lauyoyi na tura su na ce su kareta, Bayan an gama shari"a an yafe mata, sai na dawo da mata ta Zubaida muka ci gaba da zama a matsayin mata da miji."
.
Na ji xuciyata tana harbawa fas! Fas! Don kuwa na gama tsorace. Da qyar nake shaqar numfashi.
.
"anya kuwa masoyiyata Zubaida ita ce take da irin wannan mummunan hali? Me yasa to take son ta kashe mijinta?
.
Kamar Alh.Bashir ya san tunanin da nake yi sai ya ci gaba.
.
"ba wani dalili ya sa Zubaida take son ta kashe ni ba mansur, sai don kawai tana so ta mallaki dukiyata ita kadai. Don kuwa ta san sirrin komai na dukiyata. Daga baya na sa an yi min bincike sosai akanta. Duk mazajen da ta aura a baya ita ce ta kashe su." tun tana yarinya matashiya take aure tana kashe mazajen ta. Wani abin takaici a game da munanan halayenta shi ne, Zubaida ta kan yi aure biyu ko uku a lkc daya. Don kuwa mazajen da take aure yawancinsu ba a zaune suke ba 'yan kasuwa ne dake yin kasuwanci tsakanin qasashen qetare. Sannan da na yi bincike akanta ya nuna cewar iyayenta na bogI ne ba na gsky ba ne....! Wasu "yan damfara ne kawai ta samu suke zama matsayinn iyayenta idan zata yi aure, wurin su ake xuwa a daura mata aure.
.
.
Lp=16
Mugun albishir
page 16
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Idan zata yi aure wurin su ake zuwa su daura mata aure."
.
Wannan labarin dole ne ya tayar min da hankali, don kuwa idan har wadannan halaye sune halayen masoyiya ta Zubaida to tabbas rayuwata tana cikin masifa. Don kuwa ni dai ina sonta ko da kuwa ni ma kashe ni zata yi a ranar da na aureta ba zan iya daina sonta ba."
.
Alh.Bashir ya ci gaba da cewa.
.
"mutanen duniya sai dai a barsu wajen neman abin duniya mansur. duk da wannan abu da ya faru wannan "yar talika bata daina qoqarin ganin ta kashe ni ba." Kullum ina lura da ita, so take yi ta kashe ni, Kuma na san cewar yau da gobe bata bar komai ba." wata rana zata kashe ni. Zata yi masara."
.
Ya sake fadada murmushi ya ce da ni
.
"shi ya sa ni Kuma na fahimci kudina take so, sbd haka ne nake yi mata dukan kudina Kullum. Don kuwa Tunda ta mayar da ni gurgu, babu wani abu da zan yi a rayuwata in ji dadi, shi yasa nayi alqawarin daga nan har xuwa ranar da zata kashe ni Kullum sai na yi mata bulala hamsin mansur....na kasancewar kome zan yi mata ba zata bar gidan nan ba sai ta cimma burinta. Ina matuqar jin dadin zamana da wannan mata tawa mansur. Kada ka ta6a zaton don so da qauna take zaune da ni alhalin ina gana mata wannan azabar, ni na san Akwai abin da take son ta mallaka a wurina."
.
Ya yi dariya...Akwai alamar shi kanshi yana matuqar jin dadin wannan labarin da yake bani. To amma Kuma ni dai ban ji

1 Comments On MUGUN ALBISHIR
avatar
abdallah

1 year ago

Reply

Inason saya t coins

Please Login or Register in order to submit comment