Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani dadi da wannan labarin yake dashi ba."
.
Nayi ajiyar xuciya na ce dashi.
.
"wannan matsalar ka ce kai da matarka alhaji. Bai kamata ka sanar da ni ba." wannan sirri ne da ya shafeka kai da ita.
.
Ya yi min murmushi sannan ya harare ni.
.
"kaima ya shafeka mansur."
.
Na ji Gabana ya fadi. Me ya shafe ni? Na shiga uku, anya kuwa bai fahimci Akwai wata alaqa tsakanina da matar shi ba?
.
"wannan magana ta shafeka mansur."
.
Ya sake tabbatar min yana kallona.
.
"don kuwa a jiya da daddare lkcn da nake dukan matata nayi mamaki da na hangeka a bakin tagar falo kana kuka. Me yasa to kake kuka don kawai kaga ina dukan mata ta, ko kana jin tausayinta ne mansur?"
.
.
** ** **
.
.
Wasu tsofaffin mata ne su shida a zaune kowacce ta tasa qatuwar qwarya a gabanta Suna ta amada ba ji ba gani. Ni Kuma ina tsaye a gabansu ina ta kallonsu, gashi dai ina son in taka rrawa, amma Kuma wata qatuwar malum-malum da na jibga a jikina ita ce take rinjayata, ko motsi bana iya yi. Wasu Suna zagaye da ni Suna kallona Suna yi min dariya, waigo ina son in taka rrawa amma Kuma na kasa motsawa.
.
Ina nan Kuma tare da tsofaffin dake kidan amadar, sai naji sun sake kaurewa da kidan kamar zasu fasa min dodon kunnena. Na ji sautin kidan ya kaure ga Kuma dararrakun da "yan kallo suke yi ya ta"azzara. A daidai lkcn ne na farka a gigice daga barcin da na ke yi. Na ganni kwance a dakin da aka sauke ni matsayin direban Hajiya zubaida. Sai a lkcn ne na fahimci mafarki nayi.
.
A daidai lkcn ne Kuma naji anan kwankwasa min qofar dakina da qarfi. Na yunqura daqyar na fara qoqarin tare mayafin dake nannade da ni kamar ankwa. Wannan shi ne ya ganar da ni cewa ashes sautin amadar da nake ji ba wasu mata ne ke kidan ba, qofar dakina ake bugawa. San Kuma da na saurara da kyau naji kukan tsuntsaye da tantabaru a cikin daren, sai na fahimci ko shakka babu sune suka zo min a matsayin dararrakun da mutane ke yi min a cikin mafarki. Sannan kuma qaton mayafin da ya taushenni shi ya shiga hana ni in iya motsawa in taka rawa a gaban tsofaffin matan dake buga min amada ba ji ba gani.
.
Na ji an ci gaba da buga min qofar
.
.
Lp=17Mugun albishir
Page 17
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Na ji an ci gaba da dukan qofar, nan da nan nayi sauri na ture mayafin dake lulli6e da ni na sauke daga kan gadon, na lalubi makunnin wutar lantarkin dakin dake jikin bango na kunna, haske ya gauraye dakin. Na duba agogon bango naga qarfe daya da minti bakwai na dare. Na ji tsoro ya sake kama ni.
Wane ne yake tashi na a cikin wannan uban daren?
Na tambayi kaina, a daidai lkcn ne na isa bakin qofar na sa hannu na dafa ta, aka sake bugawa da qarfi.
.
"wane ne?"
.
Na tambaya a tsorace. A daidai lkcn ne naji zazzaqar muryarta Zubaida ta keto daga cikin daren ta yada zango a kunnena.
.
"bude min mansur, ni ce...."
.
Shiru ban iya motsawa ba da na fahimci ko wace ce...."
Me ya kawo Zubaida dakina cikin wannan talatainin daren?
.
Ta sake bubbuga qofar cikin qosawa ta ce...."
.
"ya sauri ka bude min mansur, ni ce Zubaida."
.
Na bushe a jikin qofar ina xullumin budeta. Don kuwa na san in har mijin ta ya san cewar ta xo dakina a cikin wannan uban daren, to babu abin da zai hana shi ya harbeni a washe gari. Dama daxun ya gama gargadina cewar kada ya sake ganin nayi kuka don naga yana dukan matarsa.
.
To a qalla dai bai gano cewar masoyiya ta ba ce, sai dai Kuma a halin ynx idan ya ji maganarta a dakina abin da zai yi min ya wuce gargadi.
.
"mansur ka bude min qofar mana, ni ce Zubaida, Kada ka ji tsoro."
.
Zubaida ta sake rero min muryarta daga can waje, nayi sauri jikina yana tsima sbd razana na bude mata qofar a rikice. A daidai lkcn da qofar ta bude ne, hasken wutar lantarkin dake a cikin dakina ya sauka akan kyakkawar fuskarta, Kuma a lkcn ne ta saki wani tattausan murmushi a lkcn da muka hada ido ta ganni a tsorace kamar an koro zamo daga rami. Tana sanye da doguwar riga mai ruwan ciyawa, ta lullu6a wani qaramin gyale mai shara-shara a saman wadataccen gashin kanta, Wanda ke motsawa kadan a sakamakon wata qaramar iska da ake yi a waje.
.
Ganin cewar na bushe a tsaye ina kallon ta, sai ta sawo kai ta shigo kai tsaye bata daina murmushi ba, ta ce min..."
.
"ba ni wuri in shigo, ina ta faman bubbuga maka qofar kana ji na ko mansur?"
.
Na kauce na bata wuri ban ce da ita komai ba, na bi ta da kallo a lkcn da naga ta za6i wurin zama a gefen gadon da na tashi Babu dadewa. Nayi qarfin halin tambayaRta.
.
"Zubaida lfy kika zo dakina a cikin wannan daren? Kuma ba kika jin Tsoron kada ya jiyo muryarki kike daga murya kina surutu?"
.
Ta ce da ni ba tare da ta sake kallon razananniyar fuska ta ba."
.
"Babu damuwa mansur."
.
Ban gane manufarta ba." ganin cewar ban saki jiki da ita ba, sai ta dago kai ta sake kallona ta yi min murmushi ta ce...."
.
"don allah ka saki ranka mansur, ka cika tsoro, sai ka ce ba namiji ba." tun da na ce maka ba matsala. Ya yi barci, ba zai farka ba sai gobe da safe."
.
Nayi ajiyar xuciya sannan na dan ji sanyi a raina, don kuwa na gama tsorata da wannan mijin nata. Ina kyautata zaton yafi ni son Zubaida dari bisa dari. Ta sake cewa da ni.
.
"yau tun da wuri ya buge ni mansur, shi yasa yayi barci tun daxun, Kullum sai ya zane ni da bulala. Haka rayuwata take kasancewa, Babu yadda zan yi sai dai haquri."
.
Na ji tausayinta ya kamani a lkcn da naji tayi wannan maganar, musamman ma da naga tayi shiru tana tunani. na bi ta da kallo tsawon wani lkc, ban san abin da take tunani ba." ni Kuma ban tambayeta ba." xuwa can Kuma sai ta yi ajiyar xuciya ta ce da ni.
.
"zauna mansur, Akwai maganar da nake son muyi ni da kai, shi yasa Kaga na zo wurinka a daidai wannan lkc. Kada ka zargeni, ba wani abu yasa ka ga naxo dakinka ba."
.
Na samu wuri a gefen katifar dake kan gadon na zauna, nesa kadan daga inda Zubaida take zaune. To amma Kuma tazarar dake a tsakaninmu bata hana ni shaqar qamshin dake a jikinta ba, Wanda na rasa gane ko qamshin mene ne a tsakanin turare da man shafawa. To amma Kuma ko ma dai mene ne, ni dai ya burgeni. Don kuwa duk ya cika dakin kamar qamshin dakin amarya a qasarmu ta hausa. Na tuno zamanin da ta zo wurina ta zauna.
.
"....ga alama kaima irina ce...."
.
Zubaida ta katse min tunanin da na fara ta juyo ta dube ni da fararen idanunta, hannunta daya na dafe da gyalen da ta yafa akanta. Ta ce da ni.
.
"naxo wajen ka ne akan wata magana da naji mijina ya sanar da kai daxun da safe. Ina raku6e ina jin ku, ina jin duk abubuwan da ya fada maka mansur....na san cewar ynx fahimci kai duk ka amince da wannan sharrin da yayi min ko mansur? ta ci gaba da kallona don jin abin da zan ce...."
.
Nayi saurin girgiza kaina, da naga bata dauke idanunta akaina ba."
.
"ko kusa ban amince da wannan labarin ba Zubaida. Don kuwa tun muna makaranta na san cewar ke macece mai kyawawan halaye da mutunci. Ba zai ta6a zama gsky ba ace ke ce ke da irin wannan halin, tun daxun da ya bani labarin ni tunic na mance da maganar, in dai wannan shi ne abin dake damunki kika kwantar da hankalinki, har abada Babu wani mahaluqi da zai tunkare ni da irin wannan mmaganar a game da ke in amince."
.
Zubaida ta dan saki ranta a lkcn da na kai qarshe. Ban sanin ba ko don ta ji dadi na yabeta shi ya san ta mance ta saki dan figigin mayafin dake lulli6e da kanta. Ta yi sauri ta sake jawo shi ta dora a saman gashinta, Wanda yake ta sheqi a cikin hasken dake dakin aduk lkcn da ta motsa.
.
"na gode sosai mansur."
.
Ta ce da ni.
.
"naji dadi da ban same ka a cikin mutanen da suke dora min zargi akan abin da ban aikata ba." Sau da yawa ina mamakin halin wannan mijin nawa mansur....ba ya kyautata min, baya gani na da mutunci, shi a tunanin sa waigo Kullum kashe shi nake so in yi. To akan me zan kashe mijina ina da hankali mansur?
.
.
Lp=18mugun albishir
Page 18
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
To akan me zan kashe mijina ina da hannkali mansur? Wannan hadarin da ya baka labari, ba laifina ba ne tsautsayi ne....! Amma Kuma ya qi ya gane . Akan haka ne yake min irin wannan cin mutuncin, Kullum sai ya buge ni kafin in kwanta barci. Wai shi ba zai barni in zauna haka ba, tunda dai na jawo mishi ya zama gurgu babu abin da zai iya yi, a Maimakon haka yake yi min bulala hamsin a kowacce rana kafin in yi barci, sbd tsabar zalunci."
.
Zubaida ta saurara tana qoqarin mayar da numfashi, don kuwa Akwai alamar bata son tuno da al"amarin. Na gane haka ne da naga tana fadin maganar cikin fushi da Kuma sauri. Nayi sauri na kwantar mata da xuciyarta na ce da ita.
.
"ku yi haquri Zubaida matsalar zaman aure kenan sai haquri. Kin san wasu maxan haka suke yiwa matansu irin wannan wulaqancin da Kuma cin zarafin. Gsky bai kyauta ba, amma Kuma idan baki da alhakinshi wata rana zaki ga sakayya, in allah ya so zaki rabu dashi ki samu wani dan arziqi da sanin ya kamata ki aura."
.
Na fada mata haka ne don tun ynx in gyara tawa gwamnatin. Ina son in nuna mata kuskurenta ne da ta auri wannan Tsohon mai kudin ta bar yaro dan zamani irina. (amma Kuma talauci kamar 6eran maSallaci).
.
A cikin sa"a Kuma sai Zubaida tayi tsaki ta ce da ni cikin damuwa.
.
"na gama tsorata da halin maza mansur.ni ynx Babu wani abu da namiji zai fada min in yardda dashi. Don kuwa na sha wahalar aure ba Sau daya ko sau biyu ba." duk maza haka kuke mansur, halinku daya."
.
Na ji tsoro ya kama ni na ce da ita
.
"ba haka ba ne Zubaida. Wlh ba halinmu daya ba." Akwai masu hankali. Ke dai kawai ba ki yi dace bane. Amma ki qara jarraba ko da mutum daya ne ki gani a nan gaba."
.
Na qura mata ido ina qoqarin karantar abin dake kan fuskarta.
To amma Kuma da naga ta fara sakin ranta, sai naji dadi a raina. Don kuwa ina so ne in riqa kushe mijinta don ta yi qoqari su rabu, daga baya Kuma ni in zagaya in aureta.
.
Ta sake yin ajiyar xuciya, sannan ta yi tagumi tana kallon dardumar dake a malale a tsakar dakin, sannan ta ci gaba da cewa.
.
"wannan hadarin da ya faru kamar inda ya sanar da kai, ba a fi wata uku ba dayin aurenmu, sai naga cewar ya kamata mu je wani garin kakannina don na gaishesu Kuma su ga mijina. A ranar da zamu yi tafiyar tun da sassafe muka shirya muka shiga mota muka tafi. Ganin cewar ni na san garin, sai na amshi tuqin motar shi kuma mijina ya zauna a daya 6angered. Muna tafiya muna hira, har barci ya kwashe shi, na ci gaba da tuqin ni kadai ban tashe shi ba."
.
Zubaida ta jawo numfashi cikin damuwa sannan ta ci gaba
.
"ina cikin tuqa motar sai na ji fitsari ya kama ni mansur, nan da nan sai na rage gudu, nayi fakin na tsayar da motar a gefen wani qaton rami mai kama da rafi a gefen titi, sannan tsabar matsuwar da nayi sai na mance na fito ban bar motar a giya ba, Kuma ban sanya birkin yin fakin ba." gashi Kuma a saman tsauni ne, ban sani ba a lkcn da na juya baya na tsuguna ina fitsari ashe motar ta fara gangarowa tana komawa baya,sannan Kuma ba wani waigi da zai tare ta a gefen titin."
.
Muryar Zubaida ta fara rawa, sannan Kuma ta fara shassheqar kuka. Na qura mata ido ko qiftawa bana yi, a lkcn ne ta ci gaba da bani labarin.
.
"ban ankara ba mansur, sai na hangi motar ta tunkari qaton ramin dake a bakin titin, ta fada ciki. Ina kallon lkcn da motar tayi qundunbala Sau biyu ta fada qasa ta hadu da duwatsu ta tarwatse. Ba zan ta6a mancewa da irin mugun sautin da na ji ba a lkcn da motar ta tarwatse a cikin ramin. Mijina yana ciki yana barci. Na taso a tsorace ina kururuwa ni kadai a cikin naji mansur, Bayan motoci sun tsaya mutane sun taru, sai aka ciro motar aka bude aka fito da mijina jina-jina bai san inda yake ba, amma Kuma mun yi sa'a, bai mutu ba." da aka kai shi asibiti ne suka yanke masa qafafuwa don kuwa sun yirugu-rugu. Bayan ya yi watanni yana jinya sai muka dawo gida. Tun daga wannan lkcn bamu sake zaman lfy ba a gidan nan. Kullum sai ya ci min zarafi ya zazzage ni, Kullum sai ya dauki bulala ya dake ni akan abin da ba laifina ba ne....! A haka muke zaune tsawon shekaru biyu da suka wuce..."
.
Ta fashe da kukan baqin ciki, Wanda wannan shi ne ya tilasta mata dakatar da labarin da take bani. Ta sunkuyar da kai tayi tagumi, daga inda nake zaune ina iya hango hawayen dake cinye gudu a kumatunta. Na ji tausayinta ya kama ni fiye da Kowanne lkc a rayuwata. Sautin kukan ta ya ci gaba da fita Sannu a hankali a cikin daren ina zaune ina saurarenta. Takaici da baqin ciki ya sake kama ni, don kuwa na san cewa Zubaida masoyiya ta tana cikin wani qangin rayuwa, Wanda in har da gasske ina sonta to ynx ne lkcn da zan nuna mata irin wannan soyayya dake a xuciyata
.
Ya zama dole in raba ta da wannan azzalumin mijina nata Wanda yake yake azabtar da ita dare da rana. Nayi ajiyar xuciya sannan na ce da ita
.
"Kada kina damu Zubaida kina yi haquri, komai na duniya yana da iyaka. Kamata ya yi kina kai shi qara a raba kina dashi, Kada ya halaka kina da irin wannan zaluncin da yake yi ciki Kullum."
.
Tsawon wani lkc Zubaida bata ce min komai ba, ta ci gaba da kusa kukanta kamar ba ta ji ni ba, xuwa can Kuma sai ta bani amsar maganata, ta ce da ni cikin kuka.
.
"Akwai lokuta da damar da nake yin shawarar in gudu in bar shi, sai dai Kuma idan nayi la'akari da halin da yake ciki sai in ga cewar bai kamata in gudu in gudu in Bashir ba." don kuwa ko ba komai ni ce silar matsalar da ta same shi har ya naqasa ya zama gurgu."
.
Na ce da ita cikin lallaShi
.
"kina daina damuwa Zubaida. Abin da ya faru ba laifinki ba ne....!
.
.
Lp=19mugun albishir
Page 19
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ba laifinki ba ne.tsautsayi ne, Wanda zai iya faruwa da kowa a duniya, ko kina a cikin motar, idan allah ya qaddara wannan abu zai faru dole sai ya faru."
.
Zubaida ta share hawayen dake a idanunta, a wannan lkcn gyalen da yake rufe da gashin kanta ya sa6ule ya gangaro kan kafadunta, amma Kuma bata damu ba, a lkcn da take share hawayen ne gashin kanta ya fara qyalqyali a cikin hasken dakin. Ta ce da ni.
.
"na san tsautsayi ne, to amma Kuma shi har abada ba zai gane hakan ba." duk lkcn da ya hadu da mutane sai ya basu wannan labarin da ya baka. Ba komai zan ci gaba da zama dashi, har xuwa lkcn da mutuwa zata raba mu. Ba zan iya guduwa in bar shi a cikin wannan halin ba." don kuwa ni ce nake daukar duk dawainiyarsa tunda baya iya tashi ya yi wani abu da kanshi, komai sai dai in yi mashi."
.
Na ji kishi mai tsanani da takaici ya sake kama xuciyata. Don kuwa duk wannan baqar wahala da Zubaida take sha a wurin mijinta, ba ta so ya rabu da ita. Tana son zama dashi a haka. Naji duniyar tayi min qunci, don kuwa na fahimci babbar matsalar da zata yi min cikas wajen mallakar Zubaida ta zama matata, bai wuce wannan shashashan gurgun mijin nata ba dake zaune a falo a kan keken guragu. Nayi qarfin halin tambayarta.
.
"to amma ke kina jin ya dace ki yi ta zama da mijin da baya sonki har qarshen rayuwa Zubaida?" ya kamata ki yi tunani sosai, ya kamata ki yi qoqari ki rabu dashi don ki samu wani mijin Wanda yake sonki Ku yi aurenku na soyayya ba irin wannan ba."
.
Zubaida tayi shiru tana kallon bangon dakin tana tunani, bayan wani lkc sai ta ce da ni.
.
"wannan shawara ce mai kyau mansur. Idan har mijina ya mutu ba zan sake auren wani mai kudi ba." na gwammace in samu wani Saurayi sabon jinni in aura, yaro matashi dan zamani Wanda zamu yi soyayya, ni ynx ba kudi suka fi damuna ba a rayuwata na fi so in samu nutsuwa da kwanciyar hankali tare da masoyina."
.
Na ji farin ciki da xumudi sun kamani, don kuwa Zubaida ta ta6o layina. Ta ta6o min 6angaren da ya fi qaiqayi a xuciyata. Idan har ta amince zata auri Saurayi dan gaye, dan zamani, to babu abin da zai hana in aureta. Wannan wata dama ce a garre ni. To amma Kuma ta ce wai sai mijin ta ya mutu, sannan zata sake yin wani auren, sai yaushe wannan mijin nata zai mutu?
.
Nayi saurin dakatar da tunanina, na tambayata.
.
"Zubaida kin san lkcn da zai mutu ne da zaki fadi haka? Me yiwuwa ya qara lkc mai tsawo ba ki sani ba..."
.
Ta yi murmushi a karo na farko tun sanda ta kammala bani labarin hadarinsu da mijinta. Sannan ta juyo ta dubeni muka hada ido. Duk dna uban kukan da ta ci idanunta Suna nan tarwai farare.
.
"Kada ka yi mamaki don na fadi haka mansur, mijina ya kusa mutuwa, don likitoci sun aunashi, Kuma sun fadi mani iyakar adadin kwanakin da zai iya qarawa a duniya."
.
Zubaida ta miqe sannan ta jawo gyalenta ta dora a saman lallausan gashin kanta, ta ce da ni.
.
"zan koma daki in kwanta mansur, na gode sosai da 6ata lkcn ka da kayi ka saurare ni, Kuma na gode da shawarwarin da ka bani, sai da safe."
.
Zubaida ta nufi qofar dakin cikin taqama, na miqe cikin sauri na bi bayanta na ce da ita.
.
"Zubaida baki fada min lkcn da likitoci suka ce zai qara a duniya ba." ki fada min don allah, kwanaki nawa likitoci suka ce zai qara a duniya?"
.
Zubaida ta dafa qofar dakin da hannunta sannan ta juyo da fuskarta ta dubeni, ina kidime cikin qosawa, ta yi min murmushin soyayya sannan ta ce da ni.
.
"Kada ka damu mansur, ba wani lkc mai tsawo suka ce zai qara ba, sun yi min albishir mai kyau. Sun ce mijina ba zai wuce shekara talatin ba a duniya
.
Zubaida ta fice ta barni a tsaye kamar an dasa ni, naji sautin tafiyarta a cikin sauri a lkcn da ta nufi dakinta.. Har xuwa lkcn da na daina jiyo tafiyarta qwaqwalwata a rikice take, kamar Wanda aka yi wa albishir da xuwanka barzahu.
.
.
** ** **
.
.
Akwai wani zamani da ya wuce kafin in fara ganin kyakkyawa Zubaida, an sha fada min cewar soyayya ta kan san mutum ya fita hayyacinsa, idan Kuma abin yayi nisa wasu an ce har haukacewa suke yi. An sha fada min cewar Sauran da yawa akwai mutanen dake fadawa tarkon soyayya har su aikata abin da ba a yi tsammanin mutum mai hankali zai aikata irin shi na.
.
A zamanin da naji zantukan ban amince da su ba." ni a tunanina haukar soyayya ba gsky bane. Ban ta6a yarda cewar mutum zai iya fita a hayyacinsa ba don kawai son wata mace.
.
To amma Kuma a halin ynx da son wannan kyakkyawar mace Zubaida ya kama ni, bani da wani aiki dare da rana sai tunaninta, sai na fara tunanin haqiqa nayi kuskure a shekarun baya, sannan Kuma na yi wa soyayya mummunar fahimta, a halin ynx kam na san yadda soyayya take burkita tunanin ma'abocin yin ta, kamar yadda ta burkita nawa tunanin, gashi ynx idanuna sun makance Zubaida kawai nake son in gani a duniya.
.
Duk wannan tunanin nayi shi ne a lkcn da nake tsaye a cikin dakina ina tunanin maganar da Zubaida ta sanar da ni, sannan Kuma ta fice ta barni a cikin xullumi da wasi-wasi . Wannan maganar da ta sanar da ni ba wani albishir ba ne mai dadi. Sai dai in kira maganar da Suna
[Mugun Albishir]
.
Haqiqa wannan mugun albishir ne, don kuwa idan har a cewarta ba zata iya rabuwa da mijinta ba sai lkcn da ya mutu shi Kuma ba zai mutu ba sai ya qara shekaru talatin a duniya, shakka Babu rayuwata tana cikin hadari . Ba zan iya tsayawa ina kallonshi har nan da shekara talatin ba ina kallonshi
.
"ba wani lkc mai tsawo likitoci suka ce zai qara ba, sun ce ba zai wuce nan da shekara talatin a duniya ba...."
.
Na sake tuno maganar Zubaida. Ban san lkcn da hawayen baqin ciki ya fara sartu akan fuskata ba."
.
.
Lp=20mugun albishir
Page 20
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ban san lkcn da hawayen baqin ciki ya fara sartu akan fuskata ba. Na yi ajiyar xuciya sannan na motsa jikina dake a bushe tun tafiyar Zubaida. Na koma na nufi gado. Da zaunawata sai na kwanta cikin damuwa na qurawa sararin samaniyar dakin idanu, ina tunanin hanyar da ya kamata in dauka don mallakar Zubaida. To amma Kuma tsawon lkc ban gano wata sahihiyar hanya mafi sauqi da zan bi in auri Zubaida ba." sai shekaru talatin masu xuwa.
.
Shin mene ne jin dadin rayuwa idan har xuciyata bata cikin sukunni? na san cewa idan har ban auri wannan masoyiya tawa ba, har abada ba zan sake samun sukunni a xuciyata ba." gashi Kuma ba ni da wata hanya da zan bi in aureta. A halin ynx matar wani ce, Kuma ba zai iya sakinta ba har abada, ita ma ba zata iya bijire masa ba su rabu, sannan Kuma ana tsammanin ba zai mutu ba sai nan da shekaru talatin masu xuwa. Kuma zai iya kasancewar in zauna in jira shi har xuwa lkcn, daga baya Kuma ya xo bai mutu ba, wa ya sani ma ko wataqila ya qara shekara saba'in a duniya? Ko Kuma ya mutun, ta auri wani daban ba ni ba? Sai tsoro ya sake kamani sannan Kuma takaici mai tsanani ya sake mamaye xuciyata.
.
Dole ne in sake dabara!
.
Na tabbatar wa kaina. Ya zama dole in bi duk hanyar da zan bi don in samu nasara idan har ina son in auri wannan tauraruwar mace mai qyalqyali kamar daimon.
.
A lkcn ne mugun tunanin da ya zamo musabbabin ruguza tarihin rayuwata ya fado min a xuciyata. Wannan shi ne karo na farko da na fara tunanin kashe mutum.
' tabbas ya zamo mani dole in kashe Alh.Bashir!'
.
Na yi mamaki da na ji cikin qanqanin lkc xuciyata ta gamsu da wannan tunani mara kyau. Don kuwa a rayuwar da nayi a can baya ni mutum ne mai tausayi da Kuma tsoro. Ko kiyashi bana iya kashewa, to amma sai gashi ynx zamani ya xo, sbd wata mace guda daya har na fara tunanin kashe mutum ba ma kiyashi ko dan tsako ba." xuciyata ta ci gaba da ingiza ni tana yi min kururuwar shaidan
.
'yi sauri ka je ka kashe shi mansur! Idan har

1 Comments On MUGUN ALBISHIR
avatar
abdallah

1 year ago

Reply

Inason saya t coins

Please Login or Register in order to submit comment