Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka barshi a raye to har abada ba zai ta6a rabuwa da Zubaida ba." Kuma ba zai mutu ba sai ya qara shekara talatin a duniya, ka yi sauri ka je ka kashe shi don ka mallaki kyakkyawar masoyiyarka wacce ka ke so shekara da shekaru.
.
Tunane-tunane barkatai mara san kyau suka cika min qwaqwalwa. Na tuno zazzaqar muryarta da Kuma kyakkyawar surar jikinta.
Xuciyata ta wassafa min lkcn da za a ce gashi an daura aurenmu ta zama mata ta.
.
"idan har mijina ya mutu ba zan sake aurenmu wani mai kudi ba." na gwammace in sami wani saurayi sabon jini Kuma yaro dan zamani wanda zamu yi soyayya
.
Wannan shi ne albishir din da Zubaida ta yi min, Kuma na sannan cewar da ni take. Bata so ne ta fito fili ta sanar da ni, sbd tana jin kunyata. To amma Kuma Babu komai na gane hakan da kaina. In dai saurayi take so dan zamani, idan ba kudi da motoci take so ba....to ta samu abin da take so. Ynx kam ya rage nawa in yi sauri in je in kashe mijinta. Don wannan albishir da tayi min ya zama gsky.
.
Na tashi xumbur, kamar Wanda aka cakawa allura na sauko daga kan gadona, na bude qofar dakin na fice waje a fusace, xuciyata na tafarfasa na nufi falon da Alh.Bashir gurgu yake babu alamar tsoro ko fargaba a tare da ni, don kuwa na qosa in ga ya mutu.
.
.
Lp=21
Mugun albishir
Page 21
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Na nufi falon Alh.Bashir gurgu Babu alamar tsoro ko fargaba a tare da ni, don kuwa na qosa in ga ya mutu. Babu motsi ko sautin wani abu da ake iya ji a cikin gidan face kukan tsuntsaye da ke wasanninsu akan bishiyoyin dake a can wajen gidan da Kuma wadanda ke shigowa Suna guje-guje akan qananan shuke-shuke.
.
Na san cewar tuni Zubaida ta kwanta ta yi barci, da wahala ta ji motsina a lkcn da na shiga falon. Na rage saurin da nake yi na fara tafiya Sannu a hankali ina sanda a cikin daren, kamar 6arawon tantabaru. Na tura qofar gilashin falon a hankali ta bude ba tare da tayi wani motsi Wanda zai iya farkar dashi daga barci ba, na shiga cikin falon, duk an kashe qwayayen babu wani haske, hakan bai hana ni ganin inda alhaji ke kwance ba akan doguwar kujerar dake a falon inda yake kwana ya wuni a zaune.
.
Na san cewar barci yake yi, to amma Kuma duk da haka idan nayi motsi qwaqqwara me yiwuwa ya tashi a firgice, Kuma idan har na sake ya farka ya ritsa ni, a cikin dare irin wannan a falon shi, to kashina ya bushe, domin ina zargin ba za a ta6a rasa shi da bindiga a 6oye ba." Kuma kai tsaye zai harbeni, don kuwa ya san cewar in dai har ina da gsky to Babu abin da zai san in shigo falon ina sanda da qarfe kusan biyu na dare.
.
Da nayi wannan tunanin sai nayi sauri na qarisa inda yake kwance ya miqe ya bi tsawon kujerun kamar matacce, ko numfashi baya yi, to amma Kuma ni dai na san cewar barci yake yi.
.
Ban tsaya jiran komai ba sai nayi tsalle na cafi wuyansa da kanshi, cikin sauri na murde wuyansa ya karye, naji sautin karyewar qashi kamar an 6allah sillan kara. Nayi mamaki sosai da naga bai motsa ba, Kuma bai farka ba yana a kwance kamar mushen zakara. To amma Kuma wannan bai karya min guiwa ba, ya riga ya mutu. Da wahala a karya wuyan mutum Kuma ya qara shekara talatin a duniya
.
Na yi sauri na ja da baya na fara shirin ficewa daga falon, xufa na kwararo min ta ko ina a jikina. Don kuwa nayi abin da ban ta6a yi ba a duniya. Sannan Kuma abin da ban ta6a tsammanin aikatawa ba."
.
Na kashe mutum!!
.
Nayi saurin bude qofar na fice xuciyata tana rufdugu kamar ana daka lura a cikin ta. Na koma dakina na shiga na rufe qofa na zauna a bakin gadona ina mayar da numfashi. duka-duka abin ya faru ne a cikin dan lkc qanqani, xuwan Zubaida dakina da Kuma ficewarta, sai Kuma xuwana falon, kashe mijinta da Kuma dawowata. Abin kamar aikin bude idanu. Ko shakka babu abin da ya faru ya faru.
Na kashe mijin Zubaida Alh.Bashir mutumin da ya daukeni aiki. Kuma yayi alqawarin zai kyautata min a rayuwata in har na riqe mashi amanar matarsa. Haqiqa ban yi amana ba, Kuma ban riqe alqawarin ba." wannan wani abu ne Wanda zai zauna min a xuciyata ya yi ta bi na a duniya yana damuna shekara da shekaru masu xuwa.
.
Da naji zafi ya dame ni sai na kashe wutar dakina na zauna a cikin duhu, nayi tagumi. Ni kaina na san cewar nayi abin da baiwa dace ba." nan da nan naji tsoro ya kamani, da na tuna cewar a halin ynx muna tare da gawa a cikin gidan. Duhun da nake ciki da Kuma talatainin daren da ake ciki su suka sake taruwa suka iza wutar fargabar da nake ciki.
.
Na san cewar Babu wani maganar barci, don haka sai na ci gaba da zama ni kadai a cikin daren ina wasi-wasin halin da abin da na aikata,sannan Kuma a lkc guda ina addu'ar allah ya mallaka min wannan masoyiya tawa da nake ta so shekara da shekaru wato Zubaida. Gara in roqi allah, don Kada in yi wannan mugun aikin a banza.
.
.
** **
.
.
Wani zakara mai zaqin murya ya kwantsama cara iya qarfin sa ta karade kusan ko ina a unguwar. A daidai lkcn ne Kuma na jiyo daddadar muryar Zubaida ta kwantsama tata carar ta 6urari ita ma iyakar qarfInta
.
"wayyo allah na shiga uku na lalace....alhaji...?"
.
Na ji gabana ya fadi ina zaune nayi tagumi, na san cewar asuba ta yi. Zubaida ta fito zata yi alwala kenan Kuma ta tsinci gawar mijinta a falon yayi kwanan Keso.
.
Na san cewar idan har ban tashi na je na ga abin da ya faru ba, me yiwuwa ta zargeni, sai nayi sauri na tashi na bude qofar dakina a cikin sauri na nufi falon, daidai lkcn ne na ci karo da mai gadi ya shigo cikin gidan a guje riqe da kwari da baka a hannunsa, kamar Wanda zai je farautar ragon maza. Muka fada cikin falon a lkc guda ni da shi. A lkc ne muka samu Zubaida ta durquusa a gaban gawar mijinta tana kuka kamar ranta zai fita.
.
"hajiya lfy? Me ya faru?"
.
Dan Tsohon dake gadi ya fara tambayarta a tsorace. Zubaida ta ce dashi tana 6urari.
.
"alhaji ne ya rasu, yi sauri ka yiwa 'yansanda waya su zo falalu."
.
Dan tsohon ya saki kwari da bakar hannunsa yana kyarma, yana qoqarin motsa baki . Wataqila Kuma yana qoqarin tuno wata addu'a ce da ya dade da mancewa, Zubaida ta sake ce mashi a fusace.
.
"ka yiwa 'yansanda waya su zo ko baka ji ba ne?"
.
Dan tsohon ya dan murmure yana inda-inda, yayi sauri ya fice daga falon yana mis-mis da baki. Nayi ajiyar xuciya sannan na durquusa kusa da Zubaida, ina kallon gawar Alh.Bashir yana kwance kamar yadda na barshi jiya da dare. Na ce da Zubaida
.
"ya kamata kina daina kukan haka nan, don kuwa kowanne mai rai mamaci ne, ki daina kukan, addu'a ya kamata ki yi masa.'
.
Zubaida ta sassauta kukan da take yi, sannan ta kawar da kai cikin damuwa, tana sanya da doguwar rigarta ta daren jiya, amma Kuma a wannan karon ba gyale ta yaro ba, dankwalin rigar ta daura Wanda aka qawata shi da adon wasu dinkakkun furanni a saman goshinta. Ban san me yasa take jin kunyar hada idanu da ni ba." Babu mamaki Kuma me yiwuwa tana zargin ni na zo na kashe shi cikin daren. To koma dai me zata yi tunani aikin gama ya riga ya gama.
Shekaru talatin sun zo qarshe.
.
Ta ce min ba zai mutu ba sai ya qara shekara talatin a duniya, shi ya sa ni Kuma na dan rage yawansu suka qare a cikin dare daya. Don kuwa na qosa in aureta, na qosa ta zama mata ta.
.
Tsawon lkc muna a durqushe ni da Zubaida mun tana gawar gabanmu, ita Kuma tana shassheqar kuka. Xuwa can sai muka jiyo sautin jiniyar motar 'yansanda ta shigo cikin gidan. Nayi mamaki da naga har ynx Zubaida bata daina kuka ba, sai ka ce tana baqin ciki da mutuwarshi, sai ka ce ba shi ne yake jera mata bulala hamsin ba Kullum a gadon bayanta kafin ta kwanta barci.
.
'Yansanda hudu suka shigo cikin falon sanya da baqaqen kaya, Babu alamar wata damuwa a fuskokinsu. Muka jiya muka dube su. A lkc ne na miqe tsaye na basu wuri, suka kalle ni a lkc guda sannan suka mayar da hankalinsu akan gawar Alh.B. Wani a cikinsu ya tambaya.
.
"muna Fatan dai Babu Wanda ya ta6a gawar a cikin Ku?"
.
.
Lp=22mugun albishir
Page 22
.
daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"muna Fatan dai babu Wanda ya ta6a gawar a cikin Ku?"
.
Zubaida ta girgiza kai tana shassheqar kuk, ni ne samu damar yi musu magana.
.
"Babu wanda ya ta6a gawar shi, a haka muka same
.
Wanda ya yi tambaya da farko ya sake cewa.
.
"shi kenan, kuna iya tafiya, amma kada Kuma yi nisa domin bayan mun gama binciken akwai tambayoyi da zamu yi maku."
.
Nayi sauri na fice daga falon, don kuwa xufa nake yi, duk iskar safiyar da ake busawa. Na san cewar idan har 'yan sanda suka yi la'akari da yadda na rude, me yiwuwa asirina ya tonu su gane ni na kashe mijin Zubaida . Na fita waje naga tuni gari ya waye. Na hango Falalu mai gadi raku6e a jikin falwayar da ta shigo katafaren gidan inda mai gadi yake zama.
.
Da gani na ya yi sauri ya tarbeni ni kamar Akwai wata magana da yake so ya sanar da ni. Muka hadu ni dashi har ynxn baiwa daina karma ba, Kuma Akwai alamar hawaye a cikin busassun idanunshi.
.
"Mansur."
.
Ya kira suna na. Ban yi tsammanin ya riqe suna na haka ba, don kuwa kwana na biyu kawai a gidan, Kuma tun xuwa na ban fito mun yi hira ba."
Me zai sa in fito, tunda dai muna tare a ciki ni da masoyiya ta?
.
na amsa kiran da ya yi min, na ce dashi.
.
"Baba sai haquri ka daina kuka, shi dama rai baqon duniya ne, idan lkc ya yi sai tafiya.
.
Tsohon ya share hawaye ya ce da ni.
.
"wannan gsky ne mansur, to amma dole ne in yi jima da wannan rasuwa ta alhaji. A ce abu cikin dare daya ba ko ciwon kai ba na qafa.."
.
Ya sake rikicewa yana qoqarin gyara tsayuwa, don kuwa duk ya birkice, kamar Wanda aka dora shi akan bishiyar macizai. Na ce dashi.
.
"idan kwana ya qare ko babu ciwo sai an je baba. Sai dai a yi mashi addu'a"
.
Akwai alamar zargi a xuciyar Tsohon, na gane haka ne da naga ya yi saurin waigawa duk wani 6angare na gidan. Da ya tabbatar Babu Wanda yake saurarenmu sai ya yi qasa-qasa da muryarshi ya ce da ni.
.
"Mansur ina zargin hajiya. Da wahala idan ba ita ce ta kashe alhaji ba, don kuwa dama ana zarginta ta ta6a yunqurin kashe a lkcn baya. Domin kuwa ta ta6a jefa shi cikin rami a mota, a dalilin haka ne ma ya zama gurgu. Dama can tana son ta kashe shi."
.
Daqyar na kawar da fushin dake xuciyata, don kuwa Tsohon ya gama qule ni. Bai san irin son da nake yi wa Zubaida ba, shi ya sa yake gulmarta a gaba na, amma don Kada ya yi zargin wani abu sai na ce dashi.
.
"Babu mamaki Kuma ba ita din ba ce, don kuwa idan kwana ya qare ko ba a kashe mutum ba, shi da kan shi ma zai iya faduwa ko Babu ciwon kai ba na qafa."
.
Da dan Tsohon ya ji na kare Zubaida sai ya yi gum da bakin sa, yayi shiru yana girgiza kai, muka yi tsaye mu biyu kowa yana tunanin da ya dame shi. Na san shi tunanin mutuwar mai gidan sa yake yi, ni Kuma lissafin kwanakin da Zubaida zata yi kafin ta gama takaba nake yi.
.
Bayan wani lkc sai na hangi Zubaida ta fito daga cikin gidan ranta a 6ace, ga alama ni take nema. Don kuwa da fitowarta ta tsaya tana dube-dube, da ta hango ni tare da mai gadin a tsaye bakin qofa sai ta yafito nI da hannunta. Na bar dan Tsohon na nufi inda take cikin sauri. Da xuwa na ji ta ce da ni a sanyaye.
.
"ka shiga ciki. 'yansanda ne suke son ganin ka, ni na gama amsa nawa tambayoyin."
.
Na dubi Zubaida sosai, tana nan a cikin damuwa, Kuma da alama kamar tana fushi da ni, sai ka ce nayi mata laifi . Sai ka ce ba mijinta kawai na murde wa wuya ya mutu ba."
.
Na shiga cikin gidan kai tsaye na cire duk wata alama da zata san 'yan sanda su gane bani da gsky a fuskata. Na saki 'yan sanda su hudu a falon suna jira na kamar kuraye sun samu tunkiya.
.
Sun yi min tambayoyin da ban san iyaka ba." har da tambayar yadda aka yi aka haifeni? To
Amma Kuma amsa daya na tsaya mawa. Ni baqo ne a gidan, ban san abin da ya faru ba." na kwanta barci da wuri, Kuma na farka da safe naji matar gidan tana 6uurari waigo mijinta ya mutu. Dole akan haka suka rabu da ni, tunda dai ko maqure ni zasu yi ba zan tonawa kaina asiri ba in ce ni na kashe shi. Na bar su a cikin falon suna gwaje-gwajen su na al'ada, a lkc da na fita waje ne naga wata doguwar farar motar asibiti ta daukar gawa ta shigo gidan. Ta yi fakin , wani likita ya fito dan sirri sanye da farar riga da Kuma farin tabarau, wasu qananan likitoci biyu Kuma suka biyo bayan shi suka fito da wata makarar asibiti ta qarfe.
.
.
a lkcn da na wuce cikin faffadar farfajiyar gidan ne na hango Zubaida a cikin mota daya daga cikin motoci biyar din dake qyalqyali a cikin hasken safiyar.
.
Zubaida ta tayar da motar, sannan ta tuqo ta cikin sauri, ta zo daidai inda nake tsaye ina kallonta. Ta dube ni sannan ta ce.
.
"shigo mu tafi."
,
Na tsaya sororo ina kallonta...
.
.
Lp=23Mugun albishir
Page 23
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
Madugun taska
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Na tsaya sororo ina kallon ta, ganin bata son ta yi min dogon sharhi sai na fasa tambayarta inda zamu je a daidai wannan lkcn da ake tsaka da bincike a gidan. Na zagaya 6angaren damar na bude motar na shiga baya na zauna, ita Kuma ta tuqa ta nufi qofar shiga da fita ta gidan, wacce ke a bude fayau! Shi kansa mai gadin ya rude, ya mance bai rufe ba."
.
Zubaida ta fice da mu, muka bar gidan. Ta hau kan titin layin gidan, muka doshi yamma. Bayan mun yi nisa mun daina hangen gidan, sai tayi fakin da motar a bakin titi, a wani waje da ke da qarancin mutane. Har xuwa lkcn ban ce da ita komai ba, ban tambayeta dalilin da yasa ta daukoni muka fito ba, har xuwa lkcn da ta kashe motar ta juyo ta dube ni. To amma Kuma na san cewar wata magana ne mai muhimmanci take son mu yi, wacce take buqatar sirri.
.
"mansur"
.
Zubaida ta ambaci Suna na a cikin damuwa da Kuma shiga6a.
.
"na qura mata ido ban amsa ba, na ci gaba da sauraren abin da take son ta fada min..."
.
"ina so ne muyi wata magana mansur."
.
Ta ce da ni.
.
"ina so ne ka fada min gsky bana son ka yi min qarya. Me ka sani a game da rasuwar mijina?"
.
Ta qarishe maganar a cikin kuka, hawaye ya xubo mata cikin sauri. Ta share hawayen sannan ta tsayar da ganinta a kaina.
.
"ka yi min magana mansur."
.
Ta sake cewa da nni cikin damuwa.
.
"me ka sani game da wannan mutuwar?"
.
Na yi ajiyar xuciya sannan na ce da ita.
.
"ni na kashe shi."
.
Tsawon lkc muna kallon juna Babu wanda ya sake cewa wani abu. Na sake tabbatar mata.
.
"tabbas ni na kashe mijinki Zubaida. Na san cewar ke kanki kina zargin hakan, Kuma ke ce kika roqe ni da kada in yi maki qarya. Shi yasa na fadi maki gsky."
.
Zubaida ta lumshe idanunta cikin damuwa, sannan ta dafa sitiyarin motar xuwa can ta bude idanunta ta qurawa gilashin motar idanu.
.
"me ya sa ka kashe min mijina mansur? A wane dalilin zaka kashe shi?"
.
Zubaida ta tambayeni lkcn da wasu sababbin wahayen ke gangarowa daga cikin idanunta.
.
Na ce da ita.
.
"sbd ina sonki Zubaida."
.
Ta juyo a tsorace ta kalle ni, muka hada ido.
.
"so?"
.
Ta tambayeni
.
Na share xufar dake a goshina. Sannan na ce da ita.
.
"ranar wanka ba a 6oyon cibi Zubaida, ina son ki san cewar na dade ina son ki a rayuwata. Tun ranar da na fara ganinki a makaranta, tun ranar na ji ina sonki a duniya. A haka na dauki shekaru uku ina faman da radadin soyayyarki a xuciyata amma Kuma na kasa sanar dake, don kuwa na san cewar kin fi qarfin matsayina Zubaida."
.
Har xuwa lkcn da muka gama karatu ban daina sonki ba Zubaida. Ban san inda zamu sake haduwa ba, a haka na sanyawa xuciyata tabbacin haduwarmu wata rana, don in ganki in samu sUkuni a xuciyata.
.
Lkcn da na zo nan garin neman aiki, sai Kuma sai na ci sa'a, mijinki yana neman direba, shi ya daukeni aiki, a lkcn ne na sake ganinki, sannan Kuma na ji soyayar da nake yi maki tun shekarun baya ta sake taso min ta dawo sabuwa. Sauran abubwan da suka faru kuma kin sani Zubaida. Don kuwa a dalilin lbrn da kika bani a daren jiya cewar mijinki ba zai mutu ba sai ya qara shekaru talatin a duniya sai na ji kishi da Kuma damuwa sun cika min xuciyata. Don kuwa ba zan iya tsayawa ina jiran shi ba, shi yasa na kashe shi, don ina so ki aure ne.kamar yadda kika yi min alqawarin idan ya mutu ba zaki sake auren tsoho ba, yaro zaki samu irina wanda zaki yi soyayya dashi ki more quruciyarki."
.
Zubaida ta sunkuyar da kanta a kan sitiyarin motar ta na xubar da hawaye a lkcn da ta ji na kai qarshe. Ta ce da ni.
.
"ka yi kuskure mansur,don kuwa wannan abu da aka aikata ni zaka dorawa laifi, kasancewar na fading maka mutane da damar Suna zargina waigo ina so in kashe shi, ynx idan aka yi bincike dole ne a nemo wani abu da za a rataya min, don a ce na kashe shi. Babu wanda zai dora maka zargin kisan kai mansur....na tunda kana so na da gaske. Me zai san ka jawo min laifin da ban aikata ba? Wannan ita ce soyayyar da kake yi min?"
.
Nayi ajiyar xuciya sannan na ce da ita.
.
"Kada ki damu Zubaida, Babu wanda zai dora maki zargi. Ni nayi alqawarin in har sun gane kashe shi aka yi, to zana fito in fadi masu gsky cewar ni na kashe shi. Ba ke ce kika kashe shi ba."
.
Zubaida ta dago kanta a sanyaye daga kan sitiyarin motar ta yi min kallon soyayya, to amma Kuma Akwai hawaye a idonta. Ta ce da ni cikin sassanyar murya.
.
"ban ta6a tsammanin kana sonar kamar haka ba mansur.. Allah ya bar mu tare ni da kai masoyina, Kuma in allah ya yarda ba zasu gano cewar kashe shi aka yi ba.da zarar na gama takaba zamu yi aurenmu na soyayya."
.
Tunda na zo duniya ban ta6a jinjinawa wata magana mai dadi da sanyaya xuciya kwatankwacin wannan ba." na ji farin ciki da kuma annashuwa sun cika min xuciyata. Ta6! Waigo ni ne yau Zubaida take kallo tana kirana masoyina. Abin da nake ta mafarki shekara da shekaru gashi ynx ya zama gsky.
.
A daidai lkcn da muke zaune a cikin motar ne muka ji 6urarin motar asibiti ta dauko gawa. Ita ce motar da ta dauko gawar marigayi mijin Zubaida. Motar tazo ta wuce mu kamar iska ta juyo mana baya a guje, muka bi ta da kallo ni da Zubaida masoyiya ta.
.
Don kuwa mun san Kowanne ne a cikin motar, muka kalli juna cikin kunyar abin da muka aikat, sannan muka yi saurin kawar da kanmu. Kafin motar gawar ta 6ace ne mu daina ganinta na tuno Alh.Bashir da kuma lbrn da ya bani da zaman soyayyarshi da zubaida, na tuno lkcn da ya kira ni muka ci abinci tare a falo. Yana matuqar so na!
.
Na tuno gargadin da ya sha yi min tun xuwana gidan.
.
..ka riqe min amanar matata Zubaida....."Don kuwa duk duniyar nan babu abin da nake so kamar ta...."
.
A karo na farko na dan ji tausayinsa ya yi zarya a xuciyata.
.
.
** ** **
.
.
Bamu samu sukuni ba har aka yi biyar da yin rasuwar, don kuwa 'yansanda tuni sun miqa maganar xuwa kotu.
Kullum sai mun samu baqin dake kawo mana ziyara, baqin kuwa ba wasu bane, 'yansanda ne da lauyoyi wadanda ke xuwa su tsare mu da tambayoyi. Don kuwa mutane da damar Suna ta bayar da jita-jitar wai wwannan mutuwar da mijin Zubaida yayi wai ba ta allah da annabi ba ce. Kashe shi aka yi. Ni da zubaida masoyiyata muna shanta tsinuwa a wajen mutanen duniya kamar 'yan kashin kasuwa. Don kuwa ni da ita aka dorawa zargin kashe Alh.Bashir gurgu.
.
Tun anan saura kwana biyu a fara shari'a. Zubaida ta dauki lauya Wanda zai karen mu a kotu. Da ranar shari'ar ta zo tun da sassafe jami'an tsaro suka zo suka yi awon gaba da mu har da mai gadi muka dunguma. Aka fara shari'a.
.
Abin ya zo a bazata, don kuwa 'yansanda sanda sun yi dogon bincike, mai tsanani
.
Kuma sun gano abubuwa da dama fiye ma da yadda muka yi tsamni .
.
Lauya kotu shi ya fara miqewa yayi jawabin share fage a shari'a ar. Kuma miqewarsa ke da wuya ya fara jawabinsa kai tsaye.
.
"wannan shari'ar ba zata daukemu xuwa wani dogon lkc ba, don kuwa tuni mun gano yadda wannan ala'amari ya gudana. Zubaida ce ta kashe mijinta, Kuma ta kashe shi ne ta hanyar ba shi guba a cikin lemon gwangwani . Jikina ya auna gawarmarigayin kumaa zamu tsayar dashi a gaban kotu don ya ba.da shaida a bisa binciken da ya yi. Sannan Kuma shi kansa Wanda ya siyarwa da Zubaida wannan guba zamu gabatar da shi a gaban kotu don ya ba.da shaida..."
.
Abin ya bani mamaki, Kuma ya yi matuqar jikina ni.
.
.
Lp=24mugun albishir
Page 24
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Abin ya yi matuqar bani mamaki Kuma ya rikita ni, don kuwa ni dai na san cewar ni na kashe shi. Ni na karya mashi wuya, to amma Kuma gashi lauyoyi sun yi bincike sun gano cewar wai guba ya sha ya mutu. Wata qila Kuma biri yayi kama da mutum, don kuwa ni dama a lkcn da na je na kashe shi, ban ga yayi motsi ba."
.
Lauyan kotu ya gabatar da likitan da ya xo ya auna gawar Alh.Bashir yayi gamsasshen bayani. Kowa ya gamsu tabbas gubar marigayin ya sha ya mutu. Daga baya Kuma Lauyan ya gabatar da wani mutum, mutumin ya ce sana'arsa ne sayar da magungunan qwari shekara da shekaru. Zubaida ta zo wurin shi ta sayi magani mai qarfin wanda tace zata xubawa wasu qwari dake gina mata rami a lambun gidan ta...." a ranar da ta sayi maganin a ranar ne Kuma mijinta Alh.Bashir ya rasu ta hanyar shan guba a cikin lemonn gwangwani
.
Lauyan dake karemu ya tashi yayi nashi surutun, to amma Kuma bai samu wasu hujjoji ba da zai dogara dasu. Don kuwa lauyoyin dake a 6angaren kotu sun fi shi hujjoji da za a yarda dasu.
.
Na dubi Zubaida dake a tsaye naga tana hawaye a gaban kotu, naji tausayinta ya kama ni, don kuwa ni na jawo mata wannan masifar, dama ta ce da ni dole ne a nemo wani abu da za a dora mata zargin a ce ita ta kashe shi, tunda dai tayi

1 Comments On MUGUN ALBISHIR
avatar
abdallah

1 year ago

Reply

Inason saya t coins

Please Login or Register in order to submit comment