Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qaurin Suna a wurin mutane.
.
Da na tuno alqawarin da na yi mata cewar ba zan ta6a bari a dora mata laifi ba, sai na ce da Lauyan dake a 6angarenmu ina da magana. Mutanen dake a kotu suka dube ni, alqalin da lauyoyi kowa ya dawo da hankalinshi wuri na. Na ce.
.
"ba Zubaida ta aikata wannan laifi ba, , ni na aikata laifin kashe mijinta. Ni na sayo guba na xuba mishi a cikin lemo ya sha. Amma ita Zubaida da ta sayo tata gubar qwari ta xubawa a cikin fulawoyi."
.
Mutane da dama sun yi mamakin abin da na fadi. Don kuwa ba a ta6a ganin wanda ya dorawa kanshi laifin kisan kai ba don kawai ya kare wata mace. To amma Kuma mecece soyayyar? Idan har da gaske kana son wata mace kamar yadda nake son Zubaida to dole ne mutum ya sadaukar da rayuwarsa. Dominn kuwa mace kamar Zubaida ta cancanci komai daga wurin masoyinta.
.
A qarshe alqalin kotun ya nuna damuwarshi akan yadda wannan shari'a ta zo a rikice. Don kuwa shaida qwaqqwara da hujjoji sun nuna cewar Zubaida ce ta kashe shi. Gashi Kuma na fansheta na ce ni na kashe shi, amma Kuma ni ba a ga wata hujja da za a bi ace ni na kashe shi ba." don haka sai alqali ya yanke min hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari sbd babu qwaqqwara hujjar ni na kashe Alh.Bashir Kuma a yadda kowa ya fahimci shari'ar shi kanshi alqalin ya san Zubaida ce ta kashe shi, a 6angarena Kuma ina ganin tunic nayi alqawarin karemu masoyiya ta, bayan haka Kuma ni ma ai na murde wa gawar wuya a cikin dare.
.
A haka 'yansanda suka yi awon gaba dani. Muka hada ido ni da Zubaida masoyiya ta tana kukan baqin ciki. Nayi mata murmushin Kada ta damu, zan fito komai dadewa, ina fatan zata riqe min alqawarin ta jira .ni. Zubaida ta yi min murmushin Kada in damu. Zan jiraka masoyina, komai dadewa ina nan ina jiranka. Na gode sosai da soyayyar da ka nuna min, ka fansar da rayuwarka a kaina.
.
'yansanda suka buga min ankwa a hannuna da qafafuwana, suka iya qeyata suka raba ni da masoyiya ta Zubaida da muke kallon juna, suka yi waje da ni suka bude mota suka ingiza ni ciki. Motar ta fara tafiya da ni xuwa wata duniya ta mutanen da basu da 'yanci a rayuwarsu. Har tayi nisa xuciyata cike take da farin ciki. Don kuwait a qalla ban tozarta masoyiya ta Zubaida ba." shekaru goma Kuma basu kai shekaru talatin yawa ba, na san cewa Zubaida tana so na Kuma zata jira ni in gama zaman gidan yarin in fito muyi aure.
.
Motar ta wuce da ni saitin wata makaranta inda wasu yara qanana ke wasan qwallo cikin farin ciki, Suna sanye da kayan makaranta iri daya. Yaran suka dagowa motar hannu kamar sun san ina ciki ina kallon ta ggilashi. Duk da yake basu ganni ba, sai da na daga masu hannu nima na ce dasu a xuciyata
.
"allah ya kare Ku da sharrin soyayya idan girma yara."
.
.
***************************
.
Bayan shekara goma.
.
Wata azababbiyar bulala dake kama da Fatan giwa ta ratsa gadon bayana. Na farka a gigice babu shiri, a lkc ne na ganshi a tsaye a kaina riqe da doguwar bulalarshi kamar Kullum.
.
Na dube shi a fusace bayan na wartsake daga barcin, yana tsaye yana murmushin mugunta da yamutsattsiyar fuskar mai kama da fasasshen tumaturi.
.
Da azzalumin gandiroban ya ga na tashi sai ya mayar da hankalinshi akan sauran abokan kwanana da muke cunkushe a daki daya mu shida kamar kifayen gwangwani.
.
Lp=25Mugun albishir
Page 25
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
,
Da azzalumin gandiroban yaga na tashi sai ya mayar da hankalinshi akan sauran abokan kwanana na da muke cunkushe a daki daya mu shida kamar kifayen gwangwani. Haka gandiroban ya bi su daya bayan daya yana tsala masu bulalar Suna farkawa a furgice, don kuwa idan ya fara dukan mutum in har ba farkawa yayi ya tashi ba, to ko bulala dari zai yi masa ba zai gaji ba, duka ne dashi tamkar Zazza6i.
.
Bayan mu duka mun farka daga barci, sai azzalumin gandiroban ya dube mu a lkc daya, sannan ya ce.
.
"na san cewar ynx kun gama wartsakewa."
.
Muka gyada kawunanmu cikin fushi kamar qadangaru. Don kuwa duk da yake xuciyarmu ta bushe sbd wahalar gidan, to hakan bai hanamu tsoron wannan gandiroban ba, Wanda a shekara goman da nayi a gidan yarinn, tun xuwa na shi yake bin dakunan fursinoni yana tashin su daga barci idan safiya tayi.
.
Wannan gandiroban da yake tashinmu daga barci ya fi duk Sauran ma'aikatan gidan yarin baqin jini a wurin mu. Don kuwa duk lkcn da muka kwanta barci bamu son wani abu ya tashe mu, sbd wuni muke yi muna shan wahala tun safe har dare. A haka muke kwantawa barci a gajiye da tsamin jiki, muna cikin barci Kuma babu zato babu tsammani sai mu ji saukar duka, da zarar mun ji haka mun san cewar gari ya waye kenan.
.
Gandiroban ya nannade doguwar bulalar ya sa6ata a kafadar shi kayan qato guda, ya ce da mu.
.
"ya kamata wanda zai yi sallah ya je ya yi, wanda Kuma ba zai yi ba ya je ya dauraye fuskar shi, yau tun da wuri zamu fita aikin fasa dutse."
.
Ya fice ya bamu wuri, mun yi shiru muna tunani, muna jin shi ya shiga wani daki Wanda yake kusa da mu. Muka ji qarar saukar bulalar shi a kan wasu irinmu da tsautsayi ya fado mawa suka xo gidan yarin, ko da yake wasu ba za a ce tsautsayi ya kawo su ba, wasu ganganci ya kawo su, da Kuma hadama da neman duniya.
.
Sauran abokan kwanana su biyar da muke kwana tare a cunkushe shekara da shekaru, sun bani labarin abubuwan da suka yi aka kawo su gidan yarin. Bangis da Gambo riqaqqun 'yan fashi ne da suka dade Suna daukar rayukan bil'adama. Sada dan damfara ne, Dumfama Kuma safarar miyagun qwayoyi yake yi. Jabiru shi ne mai dan dama-dama a cikin su, satar mitar wutar lantarki ya ce yana yi a gidajen mutane kafin dubun shi ya cika.
.
Ni kadai ne azal ta fado mawa, a lkcn da na basu lbrn cewar ni wata masoyiya tawa na fanshi laifinta don Kada a yanke mata hukuncin kisa, gabaki daya shu'man mutane biyar din da na taras a dakin sai da kowa ya yi min mari goma-goma. Bangis ne ya riqe ni da tsiya suka yi layi Suna wanke min fuska da busassun hannayensu dake kama da bayan Kada. Bayan sun gama kumbura min fuska sai Bangis ya ce da ni.
.
"ka san abin da ya san muka hora ka?"
.
Na girgiza kaina cikin tsoro, don kuwa a lkcn ni baqo ne ban saba dasu ba." Bangis ya ce.
.
"ka 6ata mana rai mansur,don kuwa mu biyar din nan da ka gani, mu duka jarumai ne....! kowa akwai gagarumin laifin da yayi aka kawo shi nan... Amma kai ka rasa abin da zaka yi na arziqi sai soyayya? Akan mace za ka zo gidan yarin?"
.
Na ce dasu.
.
"ina matuqar sonta ne shi yasa. Bana son wani abu ya same ta...." shi ya same na gwammace ni a yi min hukuncin da za a yi mata.."
.
Ragowar'yan fursunan suka kashe da dariya. Dumfama ya ce da ni.
.
"lallai kam baka da hankali mansur. Baka san halin mata ba." domin kuwa duk da wannan halaccin da ka yi, to zai yi wahala ta riqe maka alqawarin. Can zata je ta sami wani ta aura ta mance da kai, kana nan kana shanta wahala. Ka yi kuskure mansur."
.
Jabiru ya ce da ni.
.
"Sau daya na ta6a yin soyayya a duniya mansur....na wata bebi ce dake a layinmu, wacce muka yi alqawarin aure ni da ita. Na sha wahala ina nemo abin da zan aureta, har garinmu na bari. Amma lkcn da na dawo Bayan na samo abin da zan aureta, sai na sami labarin ta kaI wata biyu a dakin mijinta. Tun daga lkcn na daina soyayya a rayuwata."

.
Fursunonin sun bani labarai da dama na surqulle Wanda ya sa suka kauracewa soyayya, to amma Kuma ni duk wannan baiwa tsorata ni ba." ina nan da soyayyarki Zubaida a raina, Kuma ina fatan duk lkcn da na fito daga gidan yari zata zama mata ta...."
.
Sai dai kuma na fara shan jinin jikina. Don kuwa tun da na zo gidan yarin ko Sau daya Zubaida bata kawo min ziyara ba, sannan Kuma bata aiko min da wani saqo ba, Wanda zai sa in kwantar da hankalina, in san cewar tana nan tana jira na. Kwanci tashi gashi har an yi shekara goma.
.
Baqin cikin rashin ganin Zubaida masoyiyata, da Kuma tsananinn wahala da muke sha a gidan yarin, ya sa duk na kode na lalace. Nayi baqi wuluk, sannan Kuma gasusuwa sun firfito min a fuska duguzum, na zama abin tsoro a wurin yara qanana da ace zan fito duniyarsu su ganni.
.
Sau da yawa na kan rabat dare ina kukan baqin ciki idan na tuna cewar duk sbd soyayyar Zubaida na tsinci kaina a wannan wuri. Amma Kuma gashi ko sau daya ba ta zo ta ganni ba."
.
.
Lp=26
Mugun albishir
Page 26
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Sau da yawa na kan raba dare ina kukan baqin cikI idan na tuna cewar duk sbd soyayyar da nake yiwa Zubaida na tsinci kaina a wannan wuri. Amma Kuma gashi ko sau daya ba ta xo ta ganni ba." to amma babu mamaki Kuma wani abu ne ya faru da ita a lkcn da zan zo gidan yarin. Ban san ynx a wane halin take ba."
.
Don haka nan take sai naji tausayin Zubaida ya kama ni. Ina xullumin ko wani abu ne ya same ta, gashi Kuma bani a tare da ita ballantana in sake taimakonta. Kullum sai na tuno bankwanan da muka yi a lkcn da aka yanke min hukuncin a kotu. A lkcn da take kallona fuskarta sharkaf da hawaye.
.
Kafin mu tashi mu fita daga dan tsukukin dakin mai kama da akurkin tantabaru ni da Sauran abokaina biyar sai aka turo qofar dakin ta bude. Wani gandiroban ya shigo, to amma shi ba da bulalar ya shigo ba, ya shigo ne da wata doguwar takarda a hannunshi, da shigowarshi ya ce da mu.
.
"wane ne mansur a cikin Ku?"
.
Na ce dashi.
.
"ni ne....!
.
Gandiroban ya dube ni cikin farin ciki ya ce.
.
"to mansur sai ka yi bankwana da abokanka. Yau ne ranar da za a sallameka daga wannan gida. Yau ka cika shekara goma. Yi sauri ka zo mu je ofishin kwantirola."
.
Na ji farin ciki ya ishi xuciyata. Na dubi abokan kwanana su Bangis da Gambo, na ji tausayinsu ya kama ni, don kuwa su hukuncin daurin rai da rai aka yanke musu. Bangis ya ce da ni.
.
"mansur shi kenan Kuma zaka tafi ka barmu, Fatan nan gaba zaka kiyaye wajen yin soyayya
.
Sauran fursunan suka fashe da dariya.
.
Dumfama ya ce.
.
"muna Fatan wata rana zaka zo mana da Zubaida don mu ganta."
.
Nayi masu alqawarin zan zo da ita idan na aureta. Sannan na bi gandiroban muka fice muka bar dakin. Na ji iskar safiya mai sanyaya xuciya ta bugi fuskata sannan Kuma annashuwa da murna suka mamaye min xuciyata. Don kuwa rayuwata ta dawo sabuwa. Lkc ya yi da zan fita in ga Zubaida, na ce a xuciya ta...." gani nan xuwa, ina Fatan baki mance da ni ba." ni ne mansur Tsohon masoyinki, tun na shekaru goma da suka wuce."
.
.
**
.
.
Lkcn da aka sallame ni na fito daga gidan yari, ban zame ko ina ba sai unguwarsu da nake tsammanin zan ganta. Gidan Alh.Bashir yana nan kamar yadda na bar shi tun shekara goma da suka wuce. Sa6anin wancan lkcn, ynx ba dan tsoho Falalu mai kwari da baka ke gadin qofar gidan ba, a wannan karon wani baqin soja ne a zaune rungume da doguwar bindigarshhi Wanda nake kyautata tsammanin rabonshi da ya yi fara'a, Babu mamaki wataqila tun yana yaro qarami, lkcn da ake Bashir kudin tara.
.
Na qarisa inda yake nayi mashi sallama, kafin ya amsa sai da ya kalle ni sama da qasa, da ganina ko mutum bai tambaya ba ya san ceewar daga gidan yari na fito. Don kuwa Bayan kodaddun kayana masu kama da ragowar kura, duk jikina tabon duka ne kamar dokin suga. Da yaga na tsaya a gabnshi ina nemo abin da yafi dacewa in tambaye shi. Sai shi ya dakatar min tsawa.
.
"wa ka zo nema?"
.
Na ce dashi
.
"na zo neman Zubaida ne.l"
.
Sojan ya ce da ni.
.
"Babu wata Zubaida a gidan. Ya ce da ni gidan na wani kanal din soja ne."
.
nayi mashi gdy, sannan na fice cikin rashin sanin inda zan je on ga Zubaida. A halin ynx na fahimci cewar sayar da gidan aka yi Bayan rasuwar mijinta.
.
Don haka kai tsaye sai na wuce gidan Kawuna Wanda ya fara yi min hanyar xuwana gidan marigayi mijin Zubaida.
.
.
Lp=27Mugun albishir
Page 27
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Don haka sai na wuce kai tsaye gidan Kawuna Wanda ya fara yi min hanyar xuwana gidan marigayi mijin Zubaida a matsayin direba. Daga shi har iyayena da Sauran 'yan uwana, na san cewar ynx tuni sun haqura da ni. Don kuwa har na je gidan yari nayi shekaru goma babu wanda ya waiwaye ni. Su a 6angarensu Suna tsammanin ni ke da laifi, tunda dai ni na kashe wa Zubaida miji.
.
Da na je gidan Kawuna nan din ma ban yi katarin samun shi ba, don kuwa gidan a kulle yake da kwado. Da na tambaya ne ake ce min ya tashi ya bar kaduna tun shekaru biyu da suka wuce babu kowa a gidan.
.
Na rasa inda zan sa kaina in ji dadi, don kuwa a halin ynx ban san kowa ba." nima Kuma Babu wanda ya sanni. Zubaida ce kadai zata ganni ta tuna ni, gashi Kuma ita ma na neme ta sama ko qasa na rasa inda ta shiga a duniya. Shin anya kuwa Zubaida tana a raye? Wannan ita ce tambayar da na riqa nanatawa a xuciyata har nayi kwana daya ina neman ta, amma Kuma ko labarin ta ban samu ba."
.
Wasa-wasa har aka yi mako guda ina ta cigiyar inda masoyiyata Zubaida ta ke. Haka nake wuni tun safe har dare ina shige da fice a cikin garin. Duk wani wuri da na san cewar ta ta6a bani labarin ta je, sai da na je nayi tambaya a wurin, amma Kuma ban samu sa'a, wani ya ce min ya san inda take ba."
.
Aka yi wata daya Babu labarin Zubaida Babu labarin Wanda ya san inda take. Da naga cewar an yi wata uku ban ganta ba, sai na cire rai da Kuma tsammanin ganinta. Don kuwa nayi duk wani qoqari da ya kamata ace masoyi ya yi wajen neman masoyiya amma Kuma ban gano Zubaida ba."
.
Ganin yadda rayuwata ta zama a dalilin son wata mace daya a duniya, ina ta faman wahala akanta gashi har girma ya zo min ban sani ba." na kusa shekara arba'in amma Kuma ban samu nasarar mallakar wacce nake so ba, Kuma ban san inda take ba, wataqila tana raye a can wani garin, Babu mamaki Kuma ta dade da rasuwa.
.
Ba a jima ba da naga cewar ba ni da wata qwaqqwarar sana'a, tun fitowata daga gidan yari, sai na nemi aikin leburanci a wani reshen hukumar ruwa. Aikin mu shi ne xuwa haqa ramukan fanfuna da Kuma sauran aikace-aikace na leburanci. Wanda mutum zai yi ya samu abin da zai ci kada ya mutum da yuNwa.
.
Wata rana muna zaune ni da Sauran leburori 'yan uwana a hukumar. Sai wani mutum ya silalo motarshi mai qyalqyali da ganinta an san an mori inuwar sili, mutumin ya fito wani dan gajere mai fadin fuska yana sanye da kayan alfarma wadanda suka taimaka wajen rage masa muni. Ya shiga xuwa ofishin shugaban hukumar. Xuwa can suka fito tare, suka xo inda muke a Zazzaune muna jiran aiki. Shugaban hukumar ya ce.
.
"mansur zata ka je gidan wannan mutumin, sunan shi Alh. Rufa'i. zaka haqa mashi sabon rami, yana so ne a canza mashi hanyar ruwa. Ya ce ya baiwa iyalinshi sallahun cewar zata a je, don haka an san da xuwanka."
.
Alh. Rufa'i ya miqo min wani qaramin kati mai dauke da adireshin gidan nashi da Kuma lambar wayarsa. Na amshi katin, sannan na dauki kayan aiki shebur da Kuma diga. Na hau dan acha6a nayi masa kwatancen adireshin gidan ya dauke ni a cikin mintI bakwai muka isa unguwar, sannan muka je har qofar gidan.
.
in ban da na tabbatar cewar shi ne gidan da yaxo daidai da adireshin dake a jikin katin ba, da babu abin da zai sa in amince in shiga gidan. Don kuwa a tsarin ginin da aka yiwa gidan da wasu irin furanni dogaye da aka qawata gidan dasu, ya sa ni tsammanin ko shugaban qasa yake zaune a ciki ya ca6a.m.
.
Na sallami dan acha6a ya tafi, na isa bakin tangamemiyar qofar gidan riqe da kayan ginin a hannu na, sai ka ce mai xuwa ginin kabari, duk kayana, sun yayyage. A qalla dai na ci sa'a Akwai masu gadi a qofar gidan, don ina jinjinawa Tsoron in shiga Babu izini mutanen gidan su yi min ihun mahaukaci.
.
Na qarisa wajen masu gadin su uku ne sanye da kayan buzaye, kowannensu yana riqe da zabgegiyar bulala sannan Kuma sun bar gashin baki a fuskokinsu zaro-zaro.
.
Nayi masu sallama sannan na nuna masu katin shaidar aikina na leburanci, suka gani. Nayi masu bayanin abin da na zo yi da Kuma katin adireshin da mai gidan ya bani. Daya daga cikin buzayen wani sangamemen qato mai qirar 'yan kokuwa ya ce da ni.
.
"baring in shiga in sanarwar hajiya, bata son a shiga a dame ta in tana barci. Bamu son ka shiga ka bata tsoro, bata san da xuwanka ba, Kada ka jawo mana laifi a banza."
.
Sauran qartin suka yi dariya daya a cikin su ya ce.
.
"gskyrka mamuda, ya fi kyau ka jefi-jefi ka fara sanar da ita. Don kuwa idan rana ya 6aci sai ta rufe mutum da zagi kamar ita ta haife shi."
.
Qaton farko da ya fara magana Wanda shi ne suke cewa mamuda ya tashi ya shiga cikin gidan....xuwa can Bayan wani lkc sai ya fito ya dube ni.ya ce.
.
"ta ce a shigo da kai ta san maganar."
.
Na bi shi a baya muka shiga cikin gidan....tare. 6ata lkc ne na zauna bayyana aljannar duniyar dake maqare a cikin gidan. Don kuwa duk inda mutum ya kai dubana a farfajiyar gidan dawisu ne manyan da qanana fululu suke yawo, sannan Kuma a wani sashi bene ne hawa uku an qawatashi da gilasai da Kuma matattakalar zamani. Na ci gaba da zare idanuwa ina kallon abin mamaki a lkc guda Kuma ina biyu da qaton Wanda ke tafiya daqyar sbd qarfi kamar toron agwagwa.
.
Mun xo bakin wata qofa daidai inda wata siriyar hanya ta ratsa cikin wasu shuke-shuke, sai qaton da ya rakoni ya juyo y ce da ni.ya
.
"ka tsaya nan ka jira zata fito."
.
Sannan ya komai can wajen abokan aikinshi, ina nan tsaye dauke da diga ina mamakin a inda mutane suke samun irin wannan dukiya mai yawa a wannan duniya. Xuwa can sai naji an bude qofar, sannan an yi motsi a kusa da ni.ya na dawo da hankali na inda na ji motsin. Tana a tsaye a jikin qofar gilashi sanye da qananan kayan na dogon wando da kuma guntuwar riga. Ta xubo dogayen gashin kanta sun watsu a kafadarta kamar yadda ta saba yi a shekarun baya.
.
Ban san lkcn da na xube kayan haqan ramin ba na baje a qasa. Ko a wanne zamani, Kuma ko a ina na ganta to dole ne sai na gane ta. na dubi fuskarta mai cike da annuri duk da irin tsawon shekaru goman da nayi ban ganta ba, ni dai ban ga wani canji ba." tana nan radau da kyanta sai kace wacce ake canzawa fata. Sai sheqi take yi.
.
Na tuno muryarta dake a 6oye a dodon kunnena tun zamanin da muna makaranta. Tun muna yara.
.
"...yaya sunan ka...?"
.
Haqiqa nazo a sa'a. Na gano masoyiyata Zubaida.
.
.
.
** ** **
.
.
.
Zubaida!!!"
.
Na ambaci sunan a tsorace ina kallonta cikin tsananin kidimewa kamar naga aljana ko fatalwa. Na qara taku daya na matsa daf da inda take tsaye tana kallona sheqeqe kamar wacce take kallon mahaukaci. Ganin na matsa kusa da ita cike da farin cikin ganinta, sai ta ja da baya a tsorace.
.
"a ina ka ta6a gani na ka san ni malam."
.
Ta tambayeni cikin mamaki.
.
"Kuma wa ya fading maka Suna na?"
.
Na ce da ita a kidime.
.
"ni ne mansur.... Na fito daga fursuna tun wata uku da suka wuce. Ina ta nemanki, Zubaida me kike yi a nan gidan?"
.
Zubaida ta dan yi jim tana kallona, ga alama tana tunno inda ta sanni ne....! Xuwa can ta ce da ni.ya
.
"don allah ka sake tuno min inda na sanka, a ina muka hadu?"
.
Na ji xuciyata ta harba kamar talge . Na ji mamaki da damuwa sun taru a xuciyata. Wai ace Zubaida bata gane ni ba, Bayan Kuma ni ne masoyinta dake riqe da qaunarta fiye da shekaru goma shafi'u shida, tun ina saurayi dan makaranta.
.
"zaune kina nufin ki ce kin mance da ni'?
Ni nefa mansur masoyinki. Ni ne Wanda na ceto rayuwarki a kotu a lkcn da na bayyanawa kotu ce ni ne na kashe mijinki Alh.Bashir ba ke ce ba."
.
Zubaida ta dan yi murmushi kadan kafin ta ce.
.
"oh...(i could remember), sai ynx na gane ka. Ashe dama kana a raye mansur? NI na dauka cewar tuni ka dade da mutuwa kaima. "
.
Na ji Gabana ya fading ras, don kuwa a yadda Zubaida take kollona tana fada min maganganun Babu wata alamar soyayya, kamar ma ba ta ta6a ganina ba sai ynxn. Ta ce da ni cikin damuwa.
.
"me ya Kawoka gida na, Kuma wa ka zo nema?"
.
Na ce da ita cikin damuwa.
.
"baiwa kamata ace kin yi min irin wannan tambayar ba Zubaida. Da ace kin san yadda na qarar da gaba daya rayuwata kan soyayyarki, da ba ki yi saurin mancewa da ni ba."
.
Zubaida ta ce da nia fusace.
.
"baka da hankali."Kai ynxn har kana tsammanin akwai wanii lkc da zan ji ina son wani mutum irinka a duniya mansur?
.
.
Lp=28Mugun albishir
Page 29
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ba ka da hankali."
.
Ta ce da ni.ya
.
"kai ynx kana tsammanin akwai wanii lkc da zan ji ina son wani mutum irinka a duniya mansur? Kada in sake jin ka fadi irin wannan maganar a nan gidan, don kuwa ni matar aure ce, Kuma nan gidan mijina ne."
.
Zubaida tayi ajiyar xuciya, sannan ta ci gaba da cewa.
.
"bari in fadi maka wani abu wanda baka sani ba." tun lkcn da ka fara gani na a makaranta ni matar aure ce. Ban ta6a zama babu aure biyu ko uku akaina ba." na ta6a zama da maza hudu a lkc daya, Kuma babu wanda ya sani a cikin su, ba qananan milyoyin kudi na ke samu ba a dalilin wannan aurace-aurace da nake yi mansur. Ni ce nake kashe mazajena in kwashe dukiyarsu. Idan na qarar da wadannan mazajen sai in qara auren wasu. Abin ya zame min kamar sana'a."
.
Na ji tsoro da fargaba sun kama ni, na xubawa Zubaida ido ina mamaki jin cewar wai ita ce da bakinta take iya fadin wadannan kalamai. To amma Kuma dama marigayin mijinta ya bani wannan labarin a wani zamani da ya wuce.
.
Ta ci gaba.
.
"duk lkcn da naga wani miloniya, Kuma naji ina son ya aure ni in zama matarshi bana shan wahala mansur. Don kuwa ni kyakkyawa ce. Ba Kowanne namiji zai ganni ya ce baya sona ba!"
.
Zubaida ta fadada murmushinta tana kallon wani dawisu dake gudu a harabar gidan cike da jin dadin abin da take fadi. Har xuwa lkcn da dawisun ya 6ace a cikin 'yan uwanshi, bata dauke idanunta daga kansu ba." ni Kuma ban daina kallon ta ba." ta ce da ni tana tunani.
.
"na dade ina son in kashe Alh.Bashir don kuwa duk a

1 Comments On MUGUN ALBISHIR
avatar
abdallah

1 year ago

Reply

Inason saya t coins

Please Login or Register in order to submit comment