Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

xabba"u
"kixo falo idan biron kikeso" akwai wasu dana ajiye
ki dauki wanda kike so" bana so kuna irin
wadannan maganganun akan abinda bai taka kara
ya karya ba"
xabba"u tace-:
"to Hajiya"
sannan taci gaba da daddanna wayarta" Hajiya
binta kuwa ta fita ta barsu" fatima ta fito taje wajen
famfon alwala cikin damuwa" ta xauna kenan xata
fara yin alwala sai taji hawaye sun xubo mata......".
Koda yaushe idan xabba"u tayi mata irin wannan
yarfen" bata ji ba bata gani ba" takan dade tana
kusa domin kuwa xabba"u tana takurawa
rayuwarta"
.
======>++++()++++<========
.
TUN ranar da mujahid ya dauko fatima a motarsa
suka rakata gida shida Umma sai yaji ya saka
samun sukuni a xuciyarsa"
Haka kawai idan yana xaune sai ya rika jin tunanin
fatima yana kai da komo a xuciyarsa" tun yana
jurewa har ya kasa" a karshe ya tabbatar ya kamu
da son fatima kuma ya kosa ya sake ganinta"
.
.
Da yake mujahid yasan fatima ba wacce xai
tunkare ta ba ce kai tsaye" a dalilin girman shi da
take gani da kuma kunyarsa da take ji" don tana
daukar sa yayanta ne" sai mujahid ya rasa hanyar
da xai bi cikin sauki ya sanar da ita"
Baya son kanwarsa Umma tasan halin da yake ciki
a game da fatima kawarta" yafi so komae xaiyi ya
samu fatima suyi magana shi da ita" Amma kumad
mujahid yana xullumin ko tana da wani saurayi da
take so" watakila ma har an san da maganar a
gidansu" anyi wa wani alkawari"
.x
.
Don haka sai ya bar abin a ransa" to amma kullum
son fatima dad'a shiga xuciyarsa take ti" babu
abinda yafi komai burgesgi game da fatima irin
ladabinta da kuma kunyarta"
Da mujahid ya rasa kome ya kamata yayi sai ya
samo abokinsa Aminu wanda suke aiki tare a
banki" sun tafi cin abinci da rana kafin su dawo
bakin aiki" sai mujahid yace da Aminu-:
.
.
Mujahid yace da Aminu-:
AßOKINA" gaskiya akwai wani abu wanda yake
damuna" arai kwana da kwanaki" amma na rasa
yadda xan bullo wa ala.amarin" shine nake so ka
bani shawara"
Aminu ya dubi mujahid"
"wane abu ne yake damunka mujahid?"
mujahid ya numpasa yace-:
"ka gane ko" wata yarinya ce nake so amma na
rasa hanyar da xanbi in bullo mata ta fahimci ina
sonta"
Aminu yace-:
"kai amma ka bani kunya mujahid" a matsayinka
na mai ilmi kuma dan birni" amma kace ka rasa
yadda xakayi ka fartawa mace kana sonta" 'yar
gidan wanene ita kuwa?"
.
.
Mujahid yace dashi-:
"Baka fahimce ni bane Aminu" ka gane ko wato
yarinyar kawar kanwata ce tun suna yara" nasanta
da dadewa" tana xuwa gidanmu kafin inje bauchi
karatu" to bamu sake haduwa ba sai a satin da ya
wuce" naga yarinyar ta girma" tayi hankali" kawai
tun daga ranar naji na kamu da son yarinyar"
saboda tana da ladabi" gata kuma da girmama
mutane"
.
.
To matsalar ni tana dauka nane a matsayin
yayanta tana girmamani" inajin tsoron in sameta
da maganar soyayya" idan akwai wanda takeso
kaga anji kunya" duk girmana da take gani" ince
ina sonta ban samu amincewarta ba" ya kake ganin
xa.ayi wa wannan al"amari?"
.
.
Aminu yace dashi-:
"Eh, to kaima kana da gaskiya mujahid" gaskiya
akwai matsala ka kamu da son yarinyar da take jin
kunyar ka" cikin biyu ne dai xa.ayi daya" kodai ta
amince da soyayyarka alakar dake tsakaninku ta
karu" ko kuma taki amsar soyayyarka kaxo kana
jin kunyarta daga baya" karshenta kuma taxo ta
daina jin kunyarka"
.
.
Mujahid yace-:
"Nima abinda nake ji kenan" shiyasa nabar
maganar a xuciyata" ban yarda kowa ta sani ba"
sai kai dana fadi mawa yanxu"
Aminu yayi tunani yace-:
"to mujahid gaskiya ni a ganina in har kana so ka
gane ko tana da wani masoyin da take so dole
saika tuntubi kanwarka" ku yi maganar domin
kuwa kanwarka ce tasan sirrinta fiye da kowa"
Idan ma tana da wani masoyi tsayayye to ta sani"
Idan ma bata da kowa to ta sani kawai ka samu
kanwarka cikin hikima ka tambaye ta" ita xata fadi
maka komai a game da yarinyar"
muhajid yayiwa Abokinsa Aminu godiya" A ranar
da ya taso daga aiki" bai tsaya ko ina ba sai ya
nufo gida" da shigowarsa da yamma ya fara kwada
wa Umma kira yahi ta amsa a dakin mahaifiyarsu"
.
.
"yaya gani nan a dakin mama"
mujahid ya nufi dakin mahaifiyarsu cikin sauri" da
shigarsa dakin ya iske Umma akan keke tana
dinkin wata karamar riga" ita kadaice a dakin"
"yauwa" xakiyiwa mama barna ko?"
"Umma tayi dariya.
"Ai hannuna ya gama nuna tun yaushe take bani
dinki nake yi mata"
mujahid yace-:
"kin fara yin dinkin manya an sa an gani?"
Umma tace dashi-:
"sau nawa kuma, ko jiya kala biyu na dinka na
ankon wani biki da aka kawo wa mama"
mujahid yace-:
"Bari dai ki kara kwarewa idan xanyi aure ke xaki
dinka wa matata kayan da xata sa"
.
.
Umma ta dafa keken tace da shi.....-:
"ko yanxu ka sayo" idan na dinka ba saika ajiye
ba har xuwa lokacin" kaga ai ka fara rage aiki"
mujahid yace-:
"Haba don nine uban 'yan garaje" nida ko matar
ma ban samu naga irinta ba"
Ya shiga cikin dakin ya xauna akan kujera"
"Ina mama taje ne?"
Umma tace-:
"ta shiga nan makwabta wajen maman faisal"
yanxun nan xata dawo" tace ba dadewa xatayi ba"
Mujahid yace da Umma-:
"Nima na biyo ne in dauki wasu takardu dana
mance dasu a dakina" xanyi ampani dasu ne
gobe"
"Umma tace dashi cikin shagwaba"
"kaidai yaya mujahid tunda ka gama sabon
gidanka" da wayau da wayau sai kwashe kayanka
kake tayi kana komawa can"
.
.
Mujahid yayi dariya-:
"waya ce dake kayana nake kwashewa?" ai baxan
tare ba sai da amarya" tun da aka gama aiki nasa
masa kwado na rufe shi" kada ma ki fadi wannan
maganar a gaban mama tahi" ki sa tayi mun fada"
Umma tace-:
"Ai ita naji tana fadin haka" tace kwanaki tana
kallon ka kaxo da jaka ka kwashe wasu kaya kayi
sauri ka fita" ka dauka bata ganka ba" ko shigowa
cikin gida baka yi ba"
mujahid yace da ita-:
"to yanxu dai mubar wannan maganar" ya gyara
xama ya tambayeta"
"Wai yaya kawarki fatima kuna gaisawa kuwa?"
Umma tayi murmushi"
"Sosae ma kowa" gobe ma xata xo nan gidan" tun
rana xata xo wuni xatayi mana"
.
.
Mujahid yaji wani dadi a xuciyarsa" yayi sauri ya
boye farin cikin da yaji don kada Umma ta fahimci
wani abu" yace da ita-:
"fatima tana da ladabi" ina so inga kina mu.amala
da irin wadannan kawayen!"
Umma taji dadin mujahid ya yabi kawarta"
"yaya mujahid duk a cikin kawayena babu tamkar
fatima" Ina alfahari da fatima kasancewarta babbar
aminiyata" ka duba fa ka gani tun muna yara muke
tare ni da ita" amma ko sau daya ba.a taba jin
kanmu ba"
mujahid ta tambayeta-:
Idan daya tayi aure tabar daya fa" ya xakuyi
kenan?" ko auren ma a gida daya xakuyi shi don
kada ku rabu?"
.
.
Umma tayi dariya sosae tace a karshe"
"Idan wata tayi aure sai mu dauki kaddara" ya
xamuyi tunda lokacin rabuwa ne yaxo" Amma dai
ina sai ran Allah ya yarda baxamu yi nisa da juna
ba"
"Amma ai ita an fara xancen aurenta a gidansu"
naji kwanaki kina cewa ita ma aure xa.ayi mata"
.
.
Sa.ar da xamu.........TUN A DUNIYA"
.
.
.
РÁĞE
04
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE"
.
.
"AMMA ai ita an fara xancen aurenta a gidansu"
naji kwanaki kina cewa ita ma aure xa.ayi mata"
sa,ar da xamu raka ta gida a mota"
Umma tace dashi-:
"yaya mujahid wasa nake yi mata" yar yanxu
fatima bata da wani saurayi tsayayye" ita a
ra.ayinta tafi so ta ci gaba da karatu" to amma
mahaifiyarta tafi so ta fito da miji ayi mata aure"
kuma ga alama auren xatayi" tun da dai da wahala
abarta taci gaba da karatun"
.
.
Mujahid ya sake jin dadi a xuciyarsa" yace da
Umma"
"to Allah ya xaba mata abinda yafi alheri agareta"
"Amin yaya mujahid"
Ummma tace cikin jin dadi domin kuwa tana
matukar farin cikin yadda yayanta mujahid yake
kulawa da rayuwarta da kuma duk wani al.amari
da ya shafe ta"
mujahid ya ciro kudi a aljihun rigarsa na gepe
sababbin 'yan dari biyu na dubu uku" ya mika wa
Umma ya ce-:
"ke baki iya tambayar kudi sai an baki ko?"
Umma ta amsa cikin farin ciki"
"Nagode yaya mujahid" Allah ya kara budi" Allah
ya tsareku daga sharrin makiya" nagode"
Ya ciro wasu ya kirga dubu biyar ya bata yace-:
"ki ba mama idan taxo" nixan tafi ne kada inje in
kashe su a banxa" don ba lallai bane sukai gobe
idan nabarsu a wajena" naga baba yana nan bari
xan bashu nasa idan na fita"
.
.
Mujahid ya tsashi ya fita" Umma tace dashi"-:
"to yaya sai yaushe kenan?"
mujahid yace da ita"
"yau a gidan xan kwana" ba inda xanje" gobe
kuma lahadi kin san dai bama aiki" nan xanxo ni
ma inyi muku wuni"
Umma tayi tsakke don jin dadi"
"Da gaske kana gida gobe yaya mujahid?"
"zanyi maki karya ne Umma?" ki xuba ido ki gani
mana"
.
.
Umma tace-:
"kace gobe akwai hadadden girki" indai kaxo xan
hada maka (delicious) din (lunch) na musamman"
Mujahid yace-:
"sai ki fara shirye shirye tun yau" dama kuma
kince fatima xata xo" kinga bakin naki suna da
yawa kenan"
Umma tace-:
"Allah ya kaemu goben lafiya"
mujahid ya tafi cike da farin cikin washe gari
fatima xata xo gidan" wacce ya ke so ya ganta
ruwa a jallo"
.
.
A ranar ne da hantsi Hajiya ßinta tacewa xabba'u
ta shirya suje su gaishe da mahaifinsu malam
Abubakar" duk bayan sati biyu xuwa uku Hajiya
binta takan je gidansu tayi wuni acan" wani lokaci
ma sai da yamma take dawowa"
Bayan rasuwar mahaifiyarsu" malam Abubakar ya
auri mata biyu wadanda yake tare dasu a halin
yanxu" tare da 'ya'yansu duk da yana da kananan
yara"
Abinda kowa ya sani shine" malam Abubakar yafi
son xabba'u aduk cikin 'ya'yan da yake da su"
.
.
Duk lokacin da xabba'u taje gida saiya tuno da
marigayiya (inna-uwale) wacce ta rasu a lokacin
haihuwar xabba"u"
shiyasa Hajiya binta take so ta rika xuwa masa da
ita saboda kullum idan taje ita kadai saiya rika
tambayarta ina xabba'u" ko kuma ya tambayeta
dalilin da yasa bataxo da ita ba"
Xabba'u tana ciki karashe kwalliyarta ne sai Hajiya
binta ta kwada mata kira a waje"
wai har yanxu baki gama shiryawa ba xabba"u?"
tace da ita a gurguje"
Gani nan xuwa Hajiya"
Fatima ta shigo dakin" wacce ita basu cika xuwa
da ita unguwa ba" indai ba wani sha.ani akeyi ba"
Xabba'u ta dauko gyalenta da jakarta" fatima tace
da ita"
sai kun dawo Anti xabba'u
xabba'u tace da ita"
"Ga kayana xan na shanya a waje" idan sun bushe
ki shigo dasu cikin daki ki ninke mani su"
.
.
Fatima tace-:"
"Ni ma anjima xan fita" munyi da Umma yau xanje
yi mata wuni gidansu"
xabba'u ta juyo ta dubeta"
"waike aikin kenan xuwa gidansu Umma?" ita
baxata rika xuwa nan gidan ba" sai kece kullum
kina kan hanyar gidansu" ke ga mai kawa"
Fatima tace da ita-:
"Ita ma tana xuwa (last week) ba a nan gidan ta
wuni ba?" ko kin mance ne?"
xabba"u ta tambayeta"
"to idan kika tafi wa kikeso yayi abincin?" kin san
dai bada wuri xamu dawo ba"
Fatima ta dan fara nuna damuwarta"
"Hajiya tace ai tare da Baffa da xainab xaku tafi"
kulle gidan xa.ayi"
.
.
Xabba'u tace-:
"A'a ke ki tsaya ki jira" ya xa.a bar gidan ba
kowa?"
fatima taji takaici ya bugi xuciyarta"
"To amma ai mun gama magana da Hajiya" tasan
xanje wajen Umma" tun jiya na fadi mata kuma
tabar ni"
Xabba"u tace da ita cikin gadara"
"to baxaki je din ba" ya xa.a bar gidan ba kowa?"
Hajiya binta wacce ta dauko nata gyalen ta yafa" ta
fito rike da hannun Baffa kanin fatima dan shekara
biyar ta leko dakinsu tace-:
"xomu je mana xabba"u wai nuku-nukun me kikeyi
ne haka tun daxun?"
xabba'u tace da Hajiya binta"
"wai Hajiya ya xa.ace an bar gidan nan ba kowa?"
datima ce tace wai itama xata je gidan su wannan
kawar tata Umma" wa xa.a bari a gidan?"
.
.
Hajiya binta tace-:
"Ni da cewa nayi asa kwado idan xata fita saita
rufe mu sai mu tafi da xainab da Baffa"
Xabba'u tace-:
"Haba Hajiya sai kace xuwa gidan su Ummulkhaeri
ya xama dole" kin san fa Alhaji yana fada a daina
rufe gidan ana dadewa" ana barin shi ba kowa" ta
bari mana wata rana ba sai taje ba" sai su tsaya
ita da xainab" mu sai mu tafi da Baffa"
.
.
Hajiya binta tace da fatima-:
"to in haka ne ki tsaya Fatima" kiyi abinci kuci ke
da xaenab"
.
.
FATIMA taji hawaye ya fara taruwa a cikin
idanunta" jikinta yayi sanyi" tace da mahaifiyarta"
"mama tun jiya fa na tambayeki kika barni" don
Allah kiyi hankuri ki barni in tafi" nayiwa Umma
alkawarin xanxo" kuma nasan xata jirani"
.
.
Hajiya binta tace a fusace-:
"to baxaki je din ba" wai ana wasa dake ne fatima"
Ance ku tsaye ke da xainab shine xaki ce xaki je
gidan su Umma?" to ki sa kafa ki bar gidan nan
yau!
Idan muka dawo naji ance ko kofar gida kin leka"
jikinki xai fada maki"
ta juya ta kalli xabba"u
"xomu tafi xabba"u goma ta wuce" bana so muje
mu taras da baba ya fiya"
.
.
Zabba"u ta dauko jakarta ta fito" ta juya ta dubi
fatima wacce ta fara xubar da hawaye" tace da ita
cikin iko da mallaka"
Kada ki mance da kayana a waya" idan sun bushe
ki ciro mani su" Idan kuma an dawo da wuta" ki
dauko (iron) a dakin mama ki goge mani
(underwears) dina"
Hajiya binta ta shige gaba rike da hannun baffa"
xabba"u tabi ta a baya" suka kama hanyar fita
daga gidan" xainab ta fito daga daki har xata biyo
su sai xabba"u tace da ita-:
.
.
Ke xainab" ki xauna a gida tare da fatima" ba dake
xamu je ba" fatima tana nan a daki" kije ku xauna
tare" sai mun dawo"
suka fice daga gidan" xainab 'yar shekara tara ce"
wacce tafi kama da fatima fiye da kowa a gidan" ta
tsaya cikin damuwa ita ma don kuwa taso su tafi
tare da ita kamar yadda Hajiya ta tsara" Amma
kuma xabba"u tayi musu cikas ita da fatima"
Duk cikin 'ya'yan Hajiya binta guda uku da suka
rage a raye" wato fatima" xainab" da kuma baffa"
babu wanda xabba"u take raga mawa a gidan" su
dukansu tana taka su yadda take so" saboda
kawai tana takama Hajiya ta bata dama a kansu"
.
.
Idan ta raya mata sai tasa waya ta xane xainab da
baffa ciki da bai" idan suka yi mata laepi" duk
gidan babu wanda xaice mata don me ta dake si"
ko kuma tasa su aiki" kuma dole suyi mata ko
suna so" ko basa so"
Bata dukan fatima domin kuwa tsararta ce" kuma
ido ba mudu bane amma yasan kima" sai dai duk
da haka tana yi mata garari ta numa mata ita
kanwar uwarta ce" tana yi mata wulakanci sosai a
gidan" tana takura mata"
.
.
Zainab ta nufi dakinsu fatima bayan ta gama yin
nata fushin" a dalilin rashin xuwa da ita da
xabba"u tasa akayi" ta samu fatima xaune ta kifa
kanta akan kujera tana sharbar kuka" xainab ta
matsa kusa da ita ta durkusa ta kira sunanta"
"Anti fatima meya faru?"
Fatima bata san lokacin da kanwarta xainab ta
shigo cikin dakin ba" tayi sauri ta daina kukan ta
share hawayenta" ta dago kanta suka dubi juna ita
da xainab"
"Ba komai xainab" tace da ita cikin karpin hali"
"su hajiya sun tafi ko?"
Xaenab wacce muryarta ke karkarwa uta ma tana
so tayi kuka tace-:
"Eh sun tafi"
.
.
Fatima tayi shiru tana tunanin abinda xabba"u ta yi
mata" bata da wani aiki sai dai taga ta hada ta da
hajiya tayi mata fada kullum"
Xainab ta fahimci abinda yasa fatima take kuka"
domin kuwa tsan irin xaman doya da manjan da
sukeyi ita da xabba'u
"Ta dade a xaune tana kallon fatima" suka xauna
su biyu cikin dakin" kowacce damuwa cike da
xuciyarta"
.
=====>+++++()+++++<=======
.
SU Hajiya binta sun isa gidan kenan a daidai
kokacin da mahaifinsu malam Abubakar yake shirin
fita wajen da yake sana.ar sayar da (spare parts)
din motoci 'yan kura"
Malam Abubakar tsoho ne dan kimanin shekaru
sittin wanda yanayin jikinsa baya bayyana yawan
shekarunsa don kuwa idan ba don furfurar dake a
fuskarsa ba" ba inda xa.a ga alamar yakae
shekarun da yake da su"
Malam Abubakar yana da fara.a kuma mutum ne
wanda yake da son mutane musamman 'ya'yansa
da jikokinsa"
Lokacin da Hajiya binta da xabba'u sukayi sallama
suka shigo gidansu" sai yara suka fara yi mata
sannu da xuwa suna tsalle saboda sun san duk
ranar da Hajiya binta taxo gidan akwai tsaraba"
tana xuwa masu da kayan tsotse-tsotse"
.
.
Matan malam Abubakar mama Hajara wacce ita ce
babba" sai kuma mama Balaraba wacce suke ce
mata Amaryata" suka fito da sukaji yara suna tsalle
suna yiwa su Hajiya sannu da xuwa"
mama Hajara tace-
"sannunku da xuwa"
"yauwa sannunku"
Hajiya binta tace tana dariya" ta kama hannun
yaran dake ta kamata suna kankameta" Amarya
tace-:
"sa,a tafi sammako" yanxun nan malam ya gama
shiryawa xai fita kasuwa"
Hajiya binta tace"
"shi yasa mukayi sauri" dama nace yanxun nan xai
tafi kasuwa" dana biyewa xabba'u da bamu same
shi ba" ita ta tsayar damu"
.
.
Xabba'u tace-:
"Ai wuni xamuyi" karshenta ya dawo ya same mu"
ko da yafi"
Hajiya tace-:
"Bari mu shiga mu gaisa kada mu tsayar dashi"
Xabba"u tabi yayarta Hajiya binta suka shiga dakin
mahaifinsu" sukayi sallama a lokaci guda" ya amsa
musu"
"ku shigo mana"
ya basu umarni" suka shiga cikin ladabi" suka
sameshi ya xu8a kayan da xai fita dasu kasuwa a
leda" ya xauna akan kujera"
Sannunku da xuwa" yanxu kuke tafe da safe
haka?"
.
.
Hajiya binta tace-:
"Dama munyi saurin fitowa ne don muxo mu
sameka" ashe yanxu ma kake shirin fita kasuwar"
suka xauna a kasa akan tabarmar dake malale a
tsakar dakinsu koda yaushe" malam Abubakar
yace dasu"
"
.
Yanxu ..........TUN A DUNIYA"
.
.
.
РÁĞE
05
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE"
.
.
SUKA xauna a kasa akan tabarmar dake malale a
tsakar dakinsu koda yaushe" Malam Abubakar
yace da su-:
"yanxu xan fita kasuwar ce ta dan fi kyau da safe"
amma da rana ta daga sai hira"
yayi dariya" ya dube su cikin farin ciki" yaji dadi
Hajiya binta taxo masa da xabba'u suka gaishe
shi"
"Baba ina kwana?"
ya amsa"
"Lafiya kalau"
"Ya Alhajin yana nan lafiya?"
HajIya Binta tace-:
Yana nan lafiya" yace in fada maka maganar da
kayi kwanaki ta wannan takardar rumpar da xa.ayi"
xaixo ya kawo maka ranar laraba"
Malam Abubakar yace-:
"Af, to, an rubuta kenan" dama maganar wata
runpa ta wani abokin kasuwancinmu ya saya a
hannunsa" shine ba.a bashi takardar ba" xa.a sake
sabinta wata"
.
.
Ya dawo da hankalinsa wajen xabba'u"
xabba'u ya htu" yanxu ana gida koh?"
tayi murmushi"
muna gida baba" ai hutun ya kusa karewa" saura
sati biyu mu koma karatu"
malam Abubakar ya tambaya"
"Ina fatima?" sunyi tasu jarabawar yanxu suna gida
ko?"
xabba'u tace-:
"Yanxu suna jiran sakamakon jarabawarsu ne" sai
nan gaba xai fito"
"To Allah ya taimaka"
"Amin baba""
Bayan sunyi hira na tsawon minti goma" sai Hajiya
binta tace da mahaifinsu"
"Bari mu kyaleka ka tafi kasuwa baba" mun tsayar
dakai" gashi dama ka makara"
malam Abubakar yace-:
"sai yaushe kenan?" sai an kwana biyu xaku sake
shigowa?"
.
.
Hajiya binta tace-:
"Eh, sai dai kuma ban sani ba ko akwai wata
maganar da kake so muyi baba" kana bukatar
ganina ne ba dadewa ba ko kiwa?"
yace
"to baxan ce a.a ba" idan kin samu lokaci ko nan
da sati biyu ne kika xo yayi" ba wata magana bace
musamman" kada ki damu kanki babu matsala"
.
.
Hajiya tace"
"to baba" xanxo in Allah ya yarda"
ta ciro kudi ta ajiye masa a gabansa" malam
Abubakar yace"
"to nagode" Allah ya saka da Alheri"
ya dubi xabba'u yace da ita" uana murmushi"
xabba'u ki rika mayar da hankali a karatu" kin ga
dai kokarin da 'yar uwarki take yi a kanki" ki rika
dagewa"
"to baba"
"Allah yayi maku albarka ku dukanku" na gode"
.
.
Hajiya binta da xabba'u suka tashi suka fito cikin
fara.a bayan mintuna biyu malam Abubakar ya fito
daga cikin dakin ya kulle kofar" yana rike da bakar
ledar da ya xuba wasu kayayyaki a ciki" matansa
biyu dake xaune a cikin baranda" tare da Hajiya
binta da xabba'u suka ce dashi"
"sai ka dawo..... Allah ya bada sa.a"
Malam Abubakar yace-:
Amin"
.
.
Har ya kai xaure saiya waigo ya kira Hajiya binta"
ta tashi cikin sauri ta sameshi" suka shiga xauren"
tasan akwai maganar da yake so ne suyi shi da ita
kawai"
Da taje ta same shi tace-:
"Gani baba"
malam Abubakar yace:
"Ba wata magana nake so muyi ba" dama akan
yarinyar nan ne xabba'u" nasan kina kokari a
kanta" Allah ya saka maki da Alheri" amma kinsan
yaro sai an hada da hankuri" ina so ko ina raye ko
bani da rae" kiyi mani alkawarin xakici gaba da
rike amana" domin yanxu kece uwarta" duk
duniyar nan bata da wata uwa kwatankwacinki"
kece farin cikinta" kece jin dadinta"
.
.
Banaso daidai da rana daya xabba'u tayi kuka
saboda wani bacin rai ko damuwa" in dai xaki iya
share mata hawaye" to kiyi min alkawarin xakiyi
iya kokarinki"
wannan ne kawai abu na karshe da nake rokon ki
kiyi mun a duniya" ko ina raye ko bana raye"
Hajiya binta tace da mahaifinta-:
.
.
Baba In Allah ya yarda xan cika maka wannan
alkawari" indai ina da karfin da xan taimakawa
xabba"u a rayuwarta" xanyi mata duk abinda take
so koda wannan shine abu na karshe daya rage
mani a rayuwata"
mahaifinta yace-:
"Na gode binta" Allah ya saka maki da Alheri"
"Amin baba"
sukayi sallama malam Abubakar ya tafi kasuwa"
Hajiya binta ta koma cikin gida" ta samu matan
mahaifinta a xaune suna hira da kanwarta xabba'u"
.
=======>++++()++++<========
TUN karfe tara na sape mujahid ya dauki wanka
mai xapi" ya xuba sabuwar shadda mai walkiya
kalar shudi da kuma hula tasha sitati" ya fesa
turaren da yafi so" kana ya dubi kansa a madubi
dake makale a bangon dakinsa" yayi murmushi
domin kusa shi kansa yasan cewar ko dai daura
aurensa akeyi" ya fito a haka yaci taro"
To amma farin cikin da yake ji a wannan ranar " ji
yakeyi kamar ranar daurin aurensa din ne ma
yaxo" tunda dai matar da yake sa rai xai aura" yau
a gidansu xata wuni" xasu yi hira shi da ita har ya
gaji"
mujahid yayi alkawarin ko bai fadawa fatima yana
sonta ba yau" ya xama dole ya nuna mata alamu
yadda xataje tayi tunani ta gane ita da kanta"
.
.
Yasa kaninsa ya wanke masa motarsa" tana kopar
gida sai sheki take yi" idan fatima taxo xai dauke
ta su fita cikin gari" ya yawata da ita" suyi hirarsu
a tsanake" baxaije da kanwarsa Umma ba" kada ta
dame su da surutu" ta hana su hira"
mujahid yayi alkawarin xai dauke ta suje
(shopping) ina ya kamata suje?" yana so ne yayi
mata halin girma" yadda ita kanta xata fahimci
yana sonta" kuma bada wasa ba"
Mujahid ya xauna a dakinsa yana duba agogo"
yana jiran Umma taxo ta fada masa cewar fatima
taxo" har kudi ya ba Umma yace ta shirya abinci
na musamman yau a gida" yama cikin farin cikin
son ganin fatima" ya kosa taxo"
.
.
YANA cikin farin cikin son ganin fatima" ya kosa
taxo"
Yayi mamaki da yaga karpe sha-daya ta wuce
fatima bata xo ba" mujahid ya kasa hankuri ya
tashi ya shiga cikin gida" ya samu Umma tana
kaiwa da komowa a waje" ya tambayeta-:
"Har yanxu kawar taki bata xo ba?"
Umma tace cikin damuwa"
"Har yanxu shiru bata xo ba" na kira wayarta a
kashe gashi kuma tun karpe goma tace mun xata
xo"
Abin ya ba Umma mamaki" wai me yasa mujahid
ya shiga damuwa sosae" duk bayan minti goma
saiya leko cikin gidan" tun yana tambayar Umma
har ya daina" sai dai ya shigo kamar yana son ya
dauki wani abu" sai kuma ya fita"
.
.
Abon yafi damun Umma don kuwa tasan indai ba
wani dalili ba" babu abinda xai hana fatima xuwa
kamar yadda tayi alkawari" sai dai ko idan wani
abune ya paru" wanda Umma bata sani ba""
Da karfe biyu yayi sai Umma ta xuba wa kowa
abincinsa wanda ta gama" ta kaiwa mujahid nasa
Abincin a dakinsa" ta same shi ya xauna yayi
tagumi akan katifarsa dake kasa" ransa ya baci fiye
da yadda Umma ta saba gani"
Da ta shiga ne takai masa abincin sai yace da ita"
"Umma dauke abincin nan ki mayar" baxan iya ci
ba"
Ta dubeshi cikin mamaki"
"saboda me yaya mujahid"
"Haka nan kawai na koshi"
.
.
Umma ta tsaya tana kallonshi cikin tsananin
mamaki" gabadaya ya wani canxa mata kamar ba
shi ba" duk wasan da suke yi da dariya kullun a
gidan" yanxu yayi kaura daga fuskarsa"
Umma ta tambayeshi"
"Ko dai baka da lafiya yaya mujahid"
ya bata amsa cikin pushi"
"Lafiyata kalau" me yasa kika tambaya?"
"saboda ba haka na saba ganinka ba" yaya
mujahid duk ka canxa kamar an bata maka rai"
mujadin bai san ya bata ransa ba" yadan yi
kokarin yiwa Umma murmushi" wanda ita kanta
tasan murmushin karpin hali ne!
.
.
Kada ki damu Umma" babu abinda yake damuna
kuma lafiya ta kalau" kawai dai na gahi ne ina
bukatar huwata yanxu" ki dauke abincin ki mayar
dashi cikin gida" idan na huta anjima xan kiraki"
Mujahid yayi tagumi ya dasa tunanin fatima a
xuciyarsa" baya so Umma ta gano rashin xuwan
fatima ne yake damun sa" to amma ga alama ta
fara ganewa"
ta dauki abincin" har xata fita sai tace dashi"
"xanje gidan su fatima in gani ko lafiya" bata xo
ba"
mujahid ya dago kai cikin sauri yace da ita"
"ya kamata kije Umma" (you ßetter go and see)
yarinyar nan tana da mutunci" bai kamata irin haka
ta faru kuma a xauna ba a je an ga ko meya
hanata xuwa ba"
.
.
Umma tayi murmushi" ba shakka yanxu kam ta
game abinda take ta wasi-wasi a kansa" Haba! Ai
dama ita tasan ba banxa tasa mujahid ya damu da
son yaga fatima ba tun jiya" ba shakka sonta yake
yi"
Umma ta fita cike da farin ciki" domin kuwa a
yadda ta shaku da fatima" xata so ace mujahid
yayanta shine ya aure ta" kenan xumunci ya karu
tsakaninsu"
Anyi sallar la.asar bada jimawa ba" da misalin
karpe hudu da kwata" sai Umma ta shirya ta nufi
gidansu fatima tabar mujahid a gida cikin bacin
rai" ko abinci bai ci ba" saboda rashin xuwan
fatima"
.
=======>++++()++++<========
.
FATIMA yana kan share tsakar gidansu" Umma tayi
sallama ta shigo" fatima ta amsa sannan ta dago
kanta cikin farin cikin ganin kawarta Umma" ta
jepar da tsintsiyar ta tarbe ta"
"Ya naga ba kowa a gidan sai ke kadae" Ina
hajiyar?"
Fatima ta kama hannun Umma a lokacin da tace-;
"Duk sun tafi gidan su malam tun sape" daga ni
sai xainab aka bari" yanxun nan ita ma ta fita na
aike ta sayo mun (enbelope) a shago"
Fatima taja Umma suka shiga daki"
"Naji dadin xuwanki Umma" dama na rasa wacce
xamuyi hira"
Umma ta ce-:
"Ni ma xuwa nayi in gani ko lafiya" kince xaki xo
shiru-shiru ana jiranki" kuma wayarki a kashe"
fatima da umma suka xauna akan faffadan gadon
dake dakin"
"kiyi hankuri Umma" nasan xaki damu" wayata ba
caji tun sape" nima naso in kiraki in fada maki
Hajiya sun tafi unguwa" mu kadai suka bari a gida
nida xainab"
.
.
Umma tace-:
"Gaskiya rashin xuwanki ya dagula al"amura yau
fatima" yaya mujahid yaso ku hadu yau" bai je ko
ina

Please Login or Register in order to submit comment