Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin kangin
da Allah ya fitar dani"
.
.
Ba abinda xance maka sai dai inyi maka fatan
samun wata macen" amma badai ni ba" nagode da
soyayyar da ka nuna mani a baya" Anyi mun miji"
.
Ina patan wannan itace haduwarmu ta karshe
wacce xanji furucin soyayya daga gareka" sai dai
furucin xumunci da kuma furucin alakar dake
tsakanina daku" A matsayina na kawar kanwarka
Umma" na gode" sai watarana"
Fatima ta tafi tana share hawaye" ta sgige gida
tabar mujahid a durkushe yana xubar da nasa
hawayen"
.
======>+++++ß+++++<=======
.
Duk abinda akeyi xabba'u da Asma'u basu san
dalladi yaje ya wargaxa musu shiri ba" xabba'u taji
shiru mujahid ya daina kiranta" Har aka kwana
biyu baixo gidansu ba" kuma ko (messege) bai
turo mata ba" idan ma tafiya yayi" Data fahimci ba
lafiya ba" saita kira Asma'u"
Kwana biyu mujahid bai kirani ba" baixo gidanmu
ba" kuma ina so in kirashi inji ko lapiya" amma
kince in daina kiransa" sai dai shi ya kirani"
Asma'u tace da xabba'u-:
"ki bari ni xan kirashi inji" Amma ke ya xaki kira
saurayinki?" sai ya raina ki" yace kin damu dashi"
.
.
Asma'u ta kira mujahid yaki daga wayar har ta
katse " ta sake kira" yaki dauka" ta kirashi a jere
yakai sau biyar" amma bai dauka ba" Don haka sai
ta kira xabba'u tace da ita-:
"mutumin nan da gaske yakeyi xabba'u aji yake ji"
ya kamata muje mu sameshi tare dake" mu sauke
masa lodi" ya dawo normal"
xabba'u ta tambayi Asma'u"
"yaushe xamuje?" kuma a ina xamu same shi?"
Asma'u ta ce-:
" wajen aikinsa mana" banki" ya isa mu bishi gida
ne?" ki bari sai da yamma idan sun tashi sai mu
daidaici lokacin da yake fitowa" mu sameshi a
waje"
.
.
Da yamma misalin karpe biyar lokacin da mujahid
yake tafiya gida" xabba'u wacce tabi Asma'u gida
suka hau tasi ta kawosu bankin" Da suka hango
motar mujahid a waje sai suka samu wuri suka
tsaya" suka ki shiga ciki" suna nan sai suka hangi
fitowarsa yana sauri xaije inda motarsa take"
Asma'u da xabba'u suka je suka same shi" sai dai
daga kai yayi ya gansu a gabansa ransu a bace"
ko sallama basuyi masa ba" Asma'u ta bata fuska
tace dashi-:
.
.
"Dama wucewa xamuyi" hanya ta biyo damu shine
muka hangeka" nace muxo mu gaisa" Da kyar da
shawo kan mutuniyar ta shigo" tunda ka yada ita
kwana biyu"
mujahid ya cire hannu iya karpinsa ya tsinke
Asma'u da mari saida ta fadi kasa" ta fasa kuka
wanda hakan ya jawo hankalin mutanen da ke kusa
da wajen" suka waigo don ganin ko menene ke
faruwa" Xabba'u taja da baya a tsorace" tayiwa
kanta kiyamul-laili" don kada a hada da ita"
.
.
Mujahid ya nuna Asma'u da yatsa yace da ita"-:
muguwa bakar munafuka" kedai annoba shegiya"
Allah yayi mana tsari dake da masu hali irin naki a
duniya" axxaluma annamimiya" duk makircin da
kuka yimun kika rani da masoyiyata tagari fatima
bai isheki ba shine kike sake biyo ni har nan" xaki
sake cuta ta ko?" to asirinki ya tonu" na gane
komae" duk abinda kuka kulla ya dawo kunnena"
ya koma kan xabba'u wacce tayi turus kamar
xatayi kuka" yace da ita-:
"ke kuma shashasha mara hankali! Ashe kece kike
biye da wannan muguwar kawar taki" ta ixa ki kika
yiwa 'yar uwarki sharri da kaxapi" mutanen da
suka rike ki amana tun kina jaririya" sune cinki da
shanki" sune suturarki da ilminki" sune komae
naki na rayuwa"
Amma kika biyewa wannan shaidaniyar ta rabaki
dasu" bari in fada maki" daga yau bani ba ke"
kada ki kara kusantar inda nake" bana son ki"
kuma a tsane ki" Ina kuma jawo hankalinki daki yi
gaggawar komawa wajen 'yar uwarki ki nemi
afuwarta" Idan kika sake Hajiya ta mutu baki roketa
ta yape maki ba" duk duniyar nan sai kin rasa
wajen tsayawa" sakarya! Sokuwa! Mara wayau!"
.
.
Mujahid ya shiga motarsa ya tayar" suka kauce
suka bashi hanya a guje da suka ga yayi ribas
yayo kansu da motar" kafin ya tafi ne ya leko da
kansa yana hararar su yace-:
Da kun tsaya mana" in take ku in rage mugun iri"
ko duniya ta samu sauki idan baku"
ya 2ka ya tafi ya basu wuri yahau titi"
.
.
Asma'u ta cira kai a fusace tana kuka tace da
xabba'u-:
meye ampaninki kina kallon shi yana yi mana
wulakanci" amma kin kasa cewa komai" baki da
katabus!"
Xabba'u wacce xuciya ta kusa kasheta" tace da
Asma'u
"Rufe mani baki" duk wa ya jawo mani wulakanci
idan bake ba" Ina xaune a cikin 'yan uwa lafiya" da
baki ixani ba da nace ina sonshi" da yanxu ina
nan lapia tare dasu" ke kika jawo mun kome ya
paru"
.
.
Xabba'u ta fara kuka tace da Asma'u-:
"kin cuci rayuwata" kuma kin jawomun abun kunya
a titi" baxan taba yape maki ba"
Daga yau bani ba ke" xan koma wajen 'yar uwata
in roketa ta yape mani" mu sasanta duk abinda
mujahid ya pada gaskiya ne" kece kawa uwar gami
munafuka" muguwar kawa"
.
.
Xabba'u ta tafi ta bar Asma'u tana kuka" mutanen
dake wajen suka taru suna kallonsu ita da kawarta
suna fada" xabba'u ta wuce su" bata daga kai ta
kallesu ba"
.
====>++++++ß+++++++<======
.
Da xabba'u taje gida tana kuka" ta samu
mahaifinta ta fada masa duk yadda gaskiyar
al"amarin yake" tace dashi muguwar kawarta
Asma'u tayi mata ingixa mai kantu ruwa" ta fada
masa duk makircin da suka yiwa fatima da sharrin
da tayiwa Hajiya da Alhaji tace sun koreta"
.
.
Da mahaifinta malam Aßußakar yaji haka sai ya
kira matansa biyu yace da xabba'u ta maimaita
abinda ta fada masa" ta sake maimaitawa tana
kuka" mama Hajara tace-:
"shiyasa tun farko nace abi maganar nan cikin
nutsuwa" kada ayi saurin yanke hukunci malam"
kaga yanxu gaskiya ta nuna" an xalunci Hajiya
binta"
.
.
Malam Abubakar yayi nadama"
"to nima dole in dorawa kaina laifi a nan" domin
kuwa na dauki so na dara akan xabba'u bana so a
fadi laifinta" na shagwaba ta" tun farko da ban
nuna mata haka ba" duk wannan al"amari da bai
faru haka ba"
A ranar ya aika yace yana son Hajiya binta taxo
cikin sauri" Da xuwanta ta sameshi yana hawaye"
xabba'u kuma tana kuka a gidan" malam Abubakar
yace da ita-;
"Ni na haifeki binta" amma nayi maki laifi" ki yape
mani"
Hajiya tace-:
"Na yape maka baba" kuma na godewa Allah daka
gane gaskiyar wannan al"amari"
Ya fada mata duk abunda xabba'u ta fada ya kira
xabba'u yace-:
"Ga 'yar uwarki nan ki roketa gapara" ta yape
maki"
xabba'u ta durkusa gaban hajiya binta tana kuka"
.
.
"ki yape mani hajiya" nayi maki butulci" ki
gaparceni" sharrin shaidan ne da kuma muguwar
kawata Asma'u wacce ta ixani nayi duk wadannan
abubuwa gareki"
Hajiya binta ta kama Hannunta"
"Na yape maki xabba'u na yape maki duniya da
lahira"
malam Abubakar yayi musu nasiha mai tsawo"
sannan yace da Hajiya idan taje gida tace da Alhaji
shima yaxo yana son ganinsa" domin ya bashi
hankuri akan laifin da xabba'u tayi musu"
.
.
Hajiya binta tace da xabba'u
"Dauko kayanki mu koma gida"
xabba'u tace-:
"A,a Hajiya" baxan iya komawa ba" bayan
abubuwan da nayi muku" musamman fatima"
tayaya xan iya kallon fatima a halin yanxu?"
Hajiya binta tace-:
"Ba komai" duk wannan ta wuce" fatima ma ta
samu miji yanxu lokaci kawai ake jira"
Xabba'u taki yarda ta koma" don tana jin kunya"
Hajiya binta ta rabu da ita" ta tafi gida" data koma
ne ta sanar da Alhaji sunusi abunda ya faru duka"
tace baba yana son ganinsa" ita kuma xabba'u
tana jin kunya taki yarda ta dawo"
.
.
Alhaji sunusi yayi dariya yace"-:
"Allah sarki! Tunda ta gane kuskurenta ai komai ya
wuce" muma 'yan adam muna yiwa Allah laepi ya
yape mana" ta yaya baxamu yape wa mutane 'yan
uwanmu ba?"
Da yaje gidansu Hajiya binta ne ya samu malam
Abubakar sukayi maganar" ya bashi hankuri" sai
Alhaji sunusi yace da mama Hajara ta dauko
Akwatin xabba'y ta taso ta su tafi"
mama Hajara ta taso xabba'u da kayanta"
Alhaji sunusi ya amshi akwatin ya tasata suka fita"
suka shiga mota" ya dawo da ita gida wajen 'yar
uwarta" Hajiya binta" suka ci gaba da xamansu
kamar yadda suke a da tun parko"
xabba'u ta dawo tana girmama fatima domin kuwa
tasan tayi mata laifin da baxata taba mancewa
dashi ba a rayuwarta"
.
====>+++++ß++++++<========
.
Wata daya da fara haduwar fatima da dakta Usman
aka tsayar da lokacin aurensu wata biyu masu
xuwa" mama Rakiya da Umma har gida suka xo
suka yiwa Hajiya binta murna" da lokacin auren
yaxo" kowa yasan fatima ta auri babban mutum"
Bayan akwati goma sha biyu daya ciko mata su da
kayan lepe masu tsada" ya kashe kudi masu yawa
wajen shagulgula" Umma da xabba'u suna cikin
manyan kawaye na gaba"
sati daya fatima tayi da angonta a kaduna" daga
nan sukayi bankwana da 'yan uwa ya dauketa suka
keta haxo xuwa kasar malesiya" Inda fatima taci
gaba da karatunta acan"
:
.
Duk bayan kwana biyu sai fatima tayo waya a
gida" tana dadewa suna hira da babbar kawarta
Umma" daga baya da aka canxawa mujahid wajen
aiki ya koma ibadan da xama".
.
.
Umma ta samu wani saurayi wanda suka taba yin
soyayya da dadewa kafin ya tafi aikin soja" da ya
dawo ne ya sake xuwa wajenta soyayya ta dawo
sabuwa" aka tsayar da lokacin aure wata uku masu
xuwa"
.
.
Samßarka! Ita ma xabba'u ta samu nata wani
ma'aikaci ne a hukumar wutar lantarki" ta dai
samu yadda take so domin kuwa shima akwai
'ya'yan banki"
fatima tayo waya daga malesiya tace taci gaba da
karatunta" kuma tana xaune da mijinta dakta
Usman lafiya"
.
.
Da lokacin bikinsu xabba'u da Umma ya karato ne"
suka dawo gida ita da mijinta" yayi kwana Uku ya
koma" ya barta idan aka gama bikin sai yaxo ya
dauke ta" su koma"
.
.
Saida fatima ta dawo ne aka ga kyanta ya wuce na
amarci" sannan kuma sau biyu tana kyarawa
Hajiya amai a tsakar gida" ba wanda ya tambayeta
abinda ke damunta" domin kuwa ance inkaji
gangami to da LAßARI........"
.
.
KARSHE......
DAGA
mai debe muku kewa"
SHAFI'U DAUDA GIWA"
MAI
GIDAN LITTAFI"
.
.
NI
Sadeeq shehu shariff
Aßßαη ßαѕмαян
Dαη
мυтαη уσßє
Dana kawo muku kofin labarin nake cewa ku huta
lapia"
.
.
INA KUMA
godiya ga dukkan daukacin jama,ar da ke cikin wadannan xauruka
"TASKAR GIDAN LITTAFI"
. TSANGAYAR MARUBUTA
. DUNIYAR MARUBUTA
SOYAYYA RAYUWA CE
. GIDAN LITTAFI PUBLISHER'S
.
Musamman wadanda sukayi bitar
karatun wanga
labari" dana suburbudo" Ina maiyi musu godiya
game da patan alkhaeri"
.
.
SAI KUN
sake jina a wani sabon labarin"
.
.
GAISHUWA TA MASAMMAN
GA
MADUGUN TASKAR GIDAN LITTAFI"
.
# ILIYAS_ISHAK_GUNDUTSE
AßßAN IHSAN"
.
.
DAGA NAKU
AßßAN ßASMARH
DAN
MUTAN YOßE"
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment