Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su ba?" nima xanyi
alpahari ace wacce naje da ita tayi ankon an
ganta" indai baxata sa kayan ba" sai tayi xamanta
insan xuwanne bataxa yi ba" tafi karfina"
mama rakiya tace-:
"jepa mata su" taje tasa ku tafi"
mujahid ya cilla mata kayan suka fadi a gabanta a
cikin leda" Umma ta duka ta dauki ledar ta tafi
dakinta a hankali" kamar kwai ya fashe mata a
ciki"
ta kai kusan minti goma sha biyar tana nuku'nuku
bata fito ba" mujahid yace da ita"
"kepa nake jira Umma" me kike yi ne dakin?"
.
.
Umma ta daure dai a karshe ta fito sanye da
kayan" kamar xata fashe da kuka" da kyar take iya
tafiya" siket din ya dabaibaye ta" rigar kuwa kamar
an bude lema" sai fifita takeyi da iska"
mujaid yace da ita cikin gatse"
"kai ankon kuwa yayi maki Umma" kamar dama
kinsan ke xaki sa" kika dandansa wannan dan uban
dinki hadadde" xoki nunawa mama ta gani"
Umma ta rufe puskarta da hannu cikin kunya da
pushi" ta taho a hankali" koda taxo bakin kopar
mama Rakiya tana ganinta sai ta bude idanu ta
daga hannuwa"
"ke menene wannan kuwa?" me xan gani haka"
mujahid ya dubi umma wacce ta kasa cewa
komae" mama ta tambayi mujahid"
"kai a ina kakai aka bata wannan leshin mai tsada
haka mujahid"
.
.
Mujahid yace da mama rakiya-:
"ita ta dinka shi" jiya na bata dinkin leshin baki
nan" ita ta mayar dashi haka" shiyasa don
munafunci kikaji tace baxata sa ankon ba" tasan
wulakancin da tayi mani" saboda taji nace xabba'u
xan kaiwa kayan" da gangan tayi haka" tana sane"
.
.
Mama rakiya ta rasa abinda xata ce" ta kalli umma
cikin burgumin rigar" saita fashe da dariya"
"wai ne ya kuke so kuyi dashi a................¤TUN A DUNIYA¤
.
.
.
ραgє
20
ωιтн
Aßßαη ßαѕмαян
Dαη
мυтαη уσßє
ωнтѕαρρ ριη +2348082035050
.
.
Ta dade bata tashi ba bayab yaron ya tafi" a
karshe ne saita tashi tasa hijabinta ta fita" ta tsaya
a bakin kofar gidansu taki fita waje" da danladi
yaga itace ta leko saiya karasa inda take" yayi
mata sallama"
Fatima ta amsa" Danladi yace da ita-:
"ßaiwar Allah" nasan baxaki gane ni ba" Naxo ne in
roke ki afuwa" ki yape mun a bisa laifin da nayi
maki" nina san na xalunce ki kuma na cuci
rayuwata" to amma nima sani akayi"
A lokacin ne fatima ta gane ko wanene" shine
saurayin da yaxo yayi mata kaxapi a lokacin da
take hira da mujahid" wanda a dalilin haka ne
soyayyarsu da mujahid yaxo karshe" ya komawa
xabba'u"
.
.
Fatima tace dashi-:
"kaje ka nemi gaparar ubangiji" ni tuni dama na
mance da abinda ya paru" da ace abinda ka fadi a
kaina ya faru dani da gaske" shi xaisa in damu" to
amma babu dalilin da xaisa in tashi hankalina"
tunda nasan sharri kayi mun" shi kansa wanda ka
fadi maganar dominsa da yana da tunani xai gane
sharri kayi mun" tunda nake ban taba kusantar
wani da namiji ba a rayuwata"
Ita kanta soyayyar ma a kansa na fara yinta"
Amma kaxo kayi mun kaxapi akan abunda banji
ba" ban gani ba"
Danladi yayi nadama kan maganar da ta fada
masa" yace-;
"kiyi yape mani fatima" wallahi sani akayi inxo inyi
maki haka" wata yarinya ta sani mai suna Asma'u
kawar xabba'u" su suka sani inxo inyi maki sharri"
don ku samu sabani ke da saurayinki"
Fatima tayi murmushi tace-;
"to sunyi nasara" mun samu sabani" kuma mun
rabu" Amma da akayi haka meya ragu a jikina?"
Na daina rayuwa ne ko kuwa meya same ni?" su
da suka yimun wannan sharrin na tabbata basu fini
kwanciyar hankali ba yanxu" kuma ko baka fada
mun ba" dama nasan sune suka turoka kayimun
sharri" sun samu abunda suke so" wacce aka yi
sharri saboda ita" tana can tana soyayya da
mujahid" ni kuma ina nan ina rayuwata" sai me
kuma?"
.
.
Danladi ya tambayi fatima cike da mamaki" kina
nufin xabba'u tana tare da mujahid" yanxu haka
suna soyayya?"
"mexai hana" dama ai don haka suka sa kaxo kayi
mani kaxapin"
Danladi ya ciji yatsa yace da fatima-:
"Nasan abinda nayi maki ba abu ne mai kyau ba"
kuma In Allah ya yarda daga kanki babu wani
mutum da xan sake yiwa sharri a duniya" saboda
ba abu bane mai kyau"
Amma duk da haka nayi alkawarin sai naje na
samu wannan mujahid din dana rabaki dashi"
saina fada masa komai" kai harma da abunda bai
sani ba a game da xabba'u da Asma'u" saina fada
masa saina yi musu tonon silili fiye da yadda suka
sani nayi maki" kuma saina raba soyayyarsu"
.
.
Fatima ta roki danladi"
"Ina so kayi musu afuwa" kuma kada kaje ka samu
mujahid ka fada masa wannan maganar" bana so
ka raba su" kamar yadda suka rabani da shi"
nasan xabba'u tana son mujahid sosae" shiyasa
har idanunta suka rufe tayi mani sharri ta rabani
dashi" kuma abinda baka sani baxan sanar dakai
yanxu shine-:
xabba'u kanwar babat ce" uwa daya uba daya suke
da mahaifiyata" kamar yadda batayi la'akari da
alakar dake tsakanina da ita ba" ni xan duba
xumuncin dake tsakaninmu" baxan taba barin wani
abu dana san xai cuceta" ya cuceta ba" Don Allah
kada ka daga wannan maganar" kayi hankuri" nima
na yape mata" kaima ka yape mata" na yapewa
kowa" mubar wannan maganar anan ta wuce"
.
.
Danladi ya girgixa kai cikin nadama" bai san
lokacin da hawaye suka xubo masa ba" Da ace tun
farko yasan haka fatima take da tawakkali" da babu
dalilin da xaisa yabi umarnin su Asma'u yaxo yayi
mata sharri a game da saurayinta"
Fatima ta koma cikin gida yabar danladi a tsaye
yana nadamar abinda yayi mata" to amma duk da
tace ita ta yape" komai ya wuce"
Danladi yayi alkawarin saiya tonawa xabba'u da
Asma'u asiri a wajen mujahid"
.
.
=====>+++++ß+++++<========
.
Danladi bai hankura ba saida ya gano inda mujahid
yake aiki a banki" yaje ya same shi da yamma
yana shirye-shiryen tashi" mujahid yayi tsammanin
Danladi kwastoma ne yaxo xai amshi kudi" to
amma sai yaji yace dashi"
"yallabai wajenka fa naxo"
"to lafiya ko?"
Danladi yace-:
"maganar bata sauri bace" idan baxaka damu ba"
mu fita waje"
mujahid yace-:
"kaga yanxu muna shirye-shirye ne xamu tashi"
idan baxaka damu ba" kayi jirana a waje" ka tsaya
a bakin kopa" idan na fito sai inko ko menene ke
tafe dakai"
Danladi yace-:
"xan jiraka a wajen sai ka fito"
ya fita waje ya tsaya jiran mujahid" baiyi mamakin
rashin ganeshi da mujahid yayi ba" don kuwa
lokacin da yaje ya same shi tare da fatima suna
hira" da daddare ne" baxai iya ganeshi ba yanxu"
.
.
Danladi yakai kusan minti talatin yana jira kafin
mujahid su gama aikin da suke yi a cikin bankin"
bayan sun kammala ne ya fito da jakarsa a hannu
ta xuba takardu" sai yaga danladi a xaune akan
wani dutse yana jiranshi" yace dashi"
.
.
"yauwa malam" to xo inji mana"
DANLADI ya matsa wajen mujahid suka koma gepe
suka juyawa titin baya" danladi yace da mujahid-:
"Nasan baxaka ganeni ba yanxu Alhaji" Amma ina
tunanin ai xaka iya tuno wani wanda yaxo ya same
ka tare da fatima kuna hira" wanya ya tsare ta ta
biya mashi kudinshi" da ya ce ya bata xata xo
dakinsa"
mujahid ya rage fara.ar da yakeyi da ya gane ko
dawa yake tsaye" ya gane danladi shine katon da
yaxo ya tsare fatima" wanda yace itace abokiyar
holewarsa" danladi yaci gaba da fadawa mujahid-:
.
.
"Lokaicn da naxo na sameka kana hira da fatima"
na fada mata maganganun marasa dadi" wadanda
na tabbatar sune suka bata maka rae har ka
tsaneta" kuka samu sabani" har yanxu ina tabbatar
maka shine" kaga wannan xuwan da nayi na samu
fatima" wallahi ban taba ganinta ba sai wannan
ranar"
Mujahid ya kalli danladi cikin rikicewa da yaji ya
fadi haka"
"ban fahimci abunda kake so ka fada mun ba"
malam me kake nufi da a ranar ka taba ganinta?"
.
.
Danladi yace dashi"
"Gaskiyar magana ba wani boye-boye sharri naxo
nayi mata" kuma duk wannan maganar da kaji na
fada da wannan kurarin da nakeyi mata" wallahi
kaxapi ne" babu abinda ya taba hadani da fatima,
ban santa ba" kai in takaice maka ko sunanta ma
ban sani ba" a ranar aka fada mani sunanta" babu
wani abu a tsakanina da ita""
mujahid yaji jikinsa yayi sanyi" kamar an cire masa
rai" ya durkusa kasa ya ajiye karamar jakarsa ya
dape kansa"
Danladi ya sake ce masa-:
.
.
"kuma ina so kasan ko su wanene suka sani naje
nayiwa fatima wannan sharrin" to ba wasu bane"
illa Asma'u da xabba'u" su suka kirani suka ce
akwai wata yarinya sunanta fatima" suna so ne su
rabata da masoyinta wanda xai aureta" suka fada
mun abinda xance idan naxo" kaji dalilin xuwan da
nayi na same ku na fadi wadannan maganganun"
mujahid ya fara xubar da hawaye" domin kuwa
maganganun da danladi ya fada masa kamar
bulala ce mai hade da xapin wuta" Ashe dama
fatima batayi laepin komae ba"?" mace ce kamila
kamar yadda ya santa tun farko" mujahid ya tuno
lokacin da xabba'u taxo tare da Asma'u suka
gaishe shi dayaxo wajen fatima" suka ce suna so
ya taimakesu" Asma'u xata bude akawut a bankin
da yake aiki" da kuma maganar da Asma'u taxo ta
fada masa a game da fatima"
Abunda yasa ya amince" yayi la.akari ne da irin
kusancin dake tsakaninsu da fatima" baxasu iya yi
mata sharri ba"
mujahid ya tuno irin maganganun cin mutuncin da
ya fadawa fatima" Ashe bata da laifi" kaxapi su
xabba'u sukayi mata"
.
.
Danladi yace dashi-:
"kuma a game da xabba'u inaso in fada maka"
idan har kana tsammanin mutuniyar kirki ce" toka
daina daga yanxu" da ita da Asma'u sun dade
suna huldar banxa da maxa" idan ma wadanda
suke bin samari daki ake nema" to sune"
Fatima macece ta gari" amma xabba'u da Asma'u
sune manyan bata-gari" kai ba wani boye-boye
Alhaji" sau uku ana xubarwa da Asma'u ciki" idan
ma baka sani ba" kuma duk abinda Asma'u takeyi
to xabba'u ma tanayi" kawarta ce kut'da-kut
halinsu daya" kuma ka tambaya kaji" xa.a fada
maka"
mujahid yaji ya tsani xabba'u fiye da kowacce
mace a duniya" yaji tsohuwar soyayyar da yake
yiwa fatima ta dawo sabuwa" ya share hawayen
dake fuskarsa" yace da danladi-:
.
.
"ka cuceni malam" ko kuma ince kun cuceni kai da
su xabba'u" to amma tunda yanxu ka gane
gaskiya" kaxo ka fada mani naka laifin nagode
kuma na yafe maka" xanje in samu fatima in roketa
ta yape mun" xan fada mata duk abinda ya paru"
Danladi ya tambaye shi-:
"to ita kuma xabba'un wanne hukunci ka yanke a
kanta"
mujahid yace-:
"wannan kabarni da ita" xanyi maganinta ita da
shaidaniyar kawar tata" Allah ya isa tsakanina da
xabba'u da Asma'u"
.
.
Mujahid ya sallami danladi yace ya yape masa
kudin da ya bashi lokacin da ya biya wa fatima
kudin da yayi mata kaxapi a kansu" yaje ya lallaba
ya shiga motarsa da kyar ya iya tukawa yakai
kansa gida"
Da xuwansa ya fito ya shiga cikin gida ya kira
Umma" ta fito daga daki" tunda ta hangi idanunsa
sunyi ja kamar yayi kuka" ta fahimci wani abu ya
faru" tayi sauri ta bishi suka nufi dakinsa dake a
xaure" da xuwansa bayan ya xauna" Umma ta
shigo dakin" ita ma ta xauna akan stool din
karatunsa" sai yace da ita"
.
.
"Ranar wanka ba.a boye cibi Umma" yau dai
gaskiya ta bayyana" Ashe su xabba'u sharri
sukayiwa fatima" ita da wata kawarta Asma'u
Ashe sune suka kulla makircin da suka raba mu"
daxu wannan mutumin da yaxo ya tsare fatima
muna hira yaxo wajen aiki ya sameni" ya warware
mun xare da abawa" su xabba'u sune suka sashi
yaxo yayi mata wannan sharro a gabana don su
raba mu"
Umma ta daga hannu sama tace-:
"Allah na gode maka daka nuna mun wannan
ranar" ta kalli yayanta mujahid-:
"yau Allah ya nufa ka gane gaskiya" yaya mujahid"
dama kullum abinda nake addu'a kenan"
.
.
Allah ya tonawa Axxalumae asiri don ka gane
gaskiya" ni dama tuntuni nasan da sa hannun
xabba'u a wannan makircin da aka yiwa fatima"
domin a raba soyayyarku"
.
.
Yaya mujahid sau nawa nake fada maka cewa xaiyi
wuya fatima ta aikata abin da ake.............
¤TUN A DUNIYA¤
.
.
.
ραgє
21
ωιтн
Aßßαη ßαѕмαян
Dαη
мυтαη уσßє
ωнтѕαρρ ριη +2348082035050
.
.
YAYA MUJAHID sau nawa nake fada maka cewa
xaiyi wuya fatima ta aikata abinda kake xarginta
dashi" sai dai idan sharri wasu sukayi mata" nasan
fatima kamar yadda nasan kaina" amma kaki ka
yarda da abinda nake fada maka yaya mujahid"
"Xabba'u da kake ganinta" wannan yarinyar tafi
annoba sharri" Hajiya ita ta dauke ta tun tana
jaririya a tsumma" ta shayar da ita nono" ta riketa
tana yi mata komai na rayuwa" Amma a karshe ka
duba abinda ta saka mata dashi" yanxu maganar
da mukeyi da kai" ta bata Hajiya da mahaifinsu"
tayi mata sharri" ta bata Hajiya a wajen danginsu"
tayaya xaka so irin wannan macen yaya mujahid?"
menene xai baka sha.awa a wajen xabba'u wanda
baxaka samu a wajen fatima ba?"
.
.
Mujahid ya dukar da kansa yayi ajiyar xuciya" ya
dade a haka bai dago kansa ba" xuwa can sai
yace-:
"Abin da ya faru ya riga ya faru" Umma kinsan ina
son fatima" dama a sakamakon wannan matsalar
da aka fada yasa muka samu sabani" to amma
tunda yanxu na gane gaskiya" ina so in sameta in
bata hankuri" in nemi afuwarta domin mu dawo
kamar da" muci gaba da soyayya" kuma xanyi
mata alkawarin (as long as we are 2gether) baxan
sake maimaita irin kuskuren da ya paru a baya ba"
Umma tace-:
"(any way) fatima tayi fushi" amma duk da haka
yana da kyau ka sameta din" kuma nima xanyi
maka kokari wajen ganin na lallashe ta domin ku
dawo kuyi (setting) din matsalolin da suka faru"
.
.
Mujahid yace-:
"Anjuma xanje gidansu da daddare" ina jin kunyar
in sake hada ido da ita" amma ba yadda xanyi"
xanje na roketa afuwa tayi hankuri"
Umma ta karawa yaya mujahid karpin gwuiwar yin
hakan" taje ta samu mama rakiya ta fada mata"
duk abinda ya faru" mama rakiyat ta rike baki cikin
kunya da nadamar abinda taji" musamman akan
fatima" A ranar da xabba'u xatasha xagi a wajen
mama rakiya"
.
=====>++++++ß+++++<=======
.
Kaddara dai ta riga fata" A ranar da wannan abu ya
faru ne mujahid ya gane gaskiya" ita kuma fatima
acan makarantarsu taron dalibai akayi" a
sakamakon wata lakca da wasu kwararrun
malaman lafiya sukaxo suka gabatar" da yake an
ba dalibai damar mikewa suyi tambaya ko kuma
fadar albarkacin bakinsu" fatima itama ta mike tayi
tambaya a gaban malamansu da dalibai 'yan
uwanta"
A cikin manyan bakin da suka halarci taron" akwai
wani farin mutum sanye da farin tabarau dan
kimanin shekaru talatin da bakwai mai suna Dakta
Usman".......
"tun lokacin da fatima ta mike ya ganta a lokacin
da tayi tambaya yaji yana sonta" ya kosa ya samu
dama yayi magana da daya daga cikin malamansu
domin yaji ko wacece wannan yarinyar mai suna
fatima"
Da malamai suka fara ficewa ne bayan an kusa
tashi daga taron" sai dakta Usman ya samu wani
malami wanda kuma anyi sa.a shine (H.O.D) din
sashen da fatima take karatu" kuma ya santa"
.
.
Dakta Usman yace da malamin-:
"yarinyar nan data mike tayi tambaya akan
(Enviromental sanitation) wacece malam?"
malam yace-:
"Ok, fatima sunusi kake nufi?" a (department) dina
take"
"Dakta Usman yace-:
"to malam ni banda dai kuma ace munyi girman
kwabo ai da anyi mun magana da ita" domin
gaskiya a yadda naga yarinyar sai naji ina sonta"
Sukayi dariya" malam yace-;
"Don wannan ba matsala" amma kasan da yake
muna da sharrin mu.amala mai kyau a tsakanin
malamai da dalibai" xansa a kirata sai inyi mata
bayanin abin cikin mutunci"
.
.
Amma idan bata amince ba ko anyi mata miji a
gida" to dole ne fa sai kayi hankuri malam" tunda
kasan sha.anin yaran"
"A,a ai ba komai don wannan" aini ma ba xanso
nayi abinda bai dace ba" ina sonta ne tsakani da
Allah"""
Malamin yasa wani dalibi ya kira fatima bayan an
tashi daga taron" taxo cike da mamaki ko a wane
dalili malamin yasa a kirata" data xo ne ta sameshi
a xaune a ofis dinsa tare da dakta Usman" daya
daga cikin manyan bakin da suka xo wajen taron a
ranar"
Fatima ta gashe su cikin ladabi suka amsa"
malamin ya bata damar xaunawa a daya daga cikin
kujeru biyu dake fuskantar teburinsa" bayan ta
xauna ta tattara hankalinta kan dalilin kiran nata"
yace da ita-:
"fatima munsan xakiyi mamaki a dalilin kiranki da
nasa akayi" to amma ba abin mamaki bane" idan
kika auna yadda yaruwa take kasancewa"
Ya nuna mata Dakta Usman da yake xaune a kusa
dashi" wannan babban bakon namu da nake tare
dashi a halin yanxu wato Dakta Usman" shine ya
ganki kuma Allah cikin ikonsa sai yaji yana son
kuyi wata magana " Don haka gaki gashi-:
Dakta Usman ya gyara xama yace da fatima-:
"to gaskiya fatima" duk da yake ni bako ne a
wannan makaranta taku" naxo ne kawai domin
wannan taro da aka gaiyace ni" to kuma sai
naganki daxu a cikin dalibai" kuma naji kin kwanta
mun arai sosae" shine na samu malam mukayi
magana tace xaisa a kiraki" amma ina so ki fada
mun gaskiya" karki takura kanta" idan kinsan anyi
maki miji ko akwai alkawarin wani a kanki" to
kiyiwa Allah ki fadamun gaskiya" ni xanyi hankuri
nayi maki fatan alheri"
.
.
FATIMA ta sunkuyar da kai cikin kunya tayi
murmushi tace da mutumin"
"Gaskiya babu alkawarin kowa a kaina a halin
yanxu" sai dai kawai karatun da nake yi" kuma a
wannan sharkarar na fara da sauran lokaci"
baxanyi aure yanxu ba sai dai idan na gama
karatuna xuwa nan gaba"
Dakta Usman yace da ita-;
"Duk wannan ba matsala bace fatima" xan amince
kici gaba da karatunki bayan anyi aurenmu" kuma
idan ma haka kike ji ba a nan kasar xamu xauna
ba" ni ina aiki ne a kasar malaysia" na dawo gida
ne hutun shekara" idan Har Allah ya tabbatar da
wannan al"amari a tsakaninmu to can xamu koma
kici gaba da karatun naki"
.
.
Fatima tayi shiru tana tunani" malaminsu yace-:
"Kiyi magana fatima" tun farko mun fada maki
karki boye abinda ke ranki" me kika ce?" ki bashi
amsa" kina jin kina sonshi ko kuwa akwai
matsala?" ba wani boye boye a irin wannan
maganar"
fatima ta sake sunkuyar da kai tana jin kunya"
"Allah ya tabbatar mana da alheri a cikin wannan
al'amari"
tace a sanyaye"
malamin ya dubi dakta Usman sukayi murmushi
da sukaji fatima ta amince" mutumin yace-:
"to Alhamdulillahi" naji dadi da kika amince da
wannan bukata tawa" koda yake na mance ban
gabatar maki da kaina ba"
Sunana Usman Aßduljalal"
Ni haifaffen kaduna ne" amma kamar yadda na
fada maki" yanxu ina kasar malaysia ne" acan nayi
digirina harna samu aiki" kuma gaskiya na taba yin
aure a shekaru shida da suka wuce"
Allah yayiwa matata salima rasuwa a wajen
haihuwa" to tun lokacin ban yi wani auren ba" sai
yanxu da Allah yasa na hadu da wacce xata maye
gurbinta"
.
.
Fatima ta sake yin murmushi tace a karshe"
"Allah ya jikanta"
"Amin, na gode fatima"
malamin su fatima yace-:
"yanxu tunda kun daidaita kanku" kamata yayi mu
samu mahaifinki yau" shima mu nemi ixininsa don
muji ra'ayinsa akan maganar" tunda ba abu bane
na wasa da xa.a xo a xauna ayi hira kawai a tashi"
kina ji ba matsala muna iya xuwa anjima da
daddare" mu same shi ko fatima?"
tace-:
eh ba matsala" kuna iya xuwa din ku same shi"
suka yi mata godiya" suka tambayeta inda gidansu
yake" ta kwatanta musu" Dakta Usman da fatima
sukaji kamar sun dade tare cikin dan lokaci
kankani" suka saba da juna" suka rabu da
alkawarin xasu xo gidansu anjuma da daddare tare
da malaminsu daga nan su gana da mahaifinta"
.
=====>++++++ß+++++<=======
.
Da fatima ta dawo gida ne da yamma bayan sun
tashi daga makaranta" tana xuwa ta fadawa
mahaifiyarta halin da ake ciki a tsakaninta da
Dakta Usman" Hajiya binta tasan fatima tana da
kunya da kawaici" indai taxo da xancen saurayi
gida to ba shakka tana son shi"
Hajiya tace da ita-:
"to fatima idan shine mafi alheri a gareki" ba
abinda xamuce sai dai muyi patan Allah ya
tabbatar mana da al'amarin" kawai ni abinda nakeji
naga baku dade tare ba" anya xaki san mutum
rana daya ki yarda dashi fatima?"
fatima tace da Hajiya-:
"Nayi wannan tunanin mama" to amma da nayi
la.akari da malaminmu shiya jagoranci maganar
nan kuma kuma nasan shi mutumin kirki ne" idan
akwai matsala baxai yarda ya shiga cikin maganar
ba" baxai yarda ma a kirani ba" kawai da ganin
haka sai nake ganin kamar mutumin shima bashi
da matsala" tunda ba karamin mutum bane"
.
.
Hajiya binta tace-:
"Allah yasa Alheri ne" in babanki ya dawo anjima"
sai na fada masa" idan sunxo kinga yasan da
xuwansu kenan"
Da Alhaji sunusi ya dawo ne bayan anyi sallar
magriba" sai Hajiya binta ta sameshi a daki tayi
masa bayanin maganar da fatima taxo da ita"
sannan ta sanar dashi xuwan mutanen anjuma"
Alhaji sunusi yace-:
"In dai tana son shi kuma munyi bincike mun gane
cewar mutum ne nagari" ai babu matsala" Idan
Allah ya nupa shine mijin nata" ko'ina xai kaita su
xauna ai aure ne yakai ta" don sun tafi kasar waje
sun xauna" ai bata rabu da mu ba kenan" duk
sanda dama ta samu suxo gida su koma"
.
.
Anyi sallar Isha'i kenan" Dakta Usman da
malaminsu fatima suka shigo layin da dankareriyar
bakar (prado jeep) dinsa" wacce yake barinta a
kaduna" baya hawa sai ya dawo gida hutu" suka
yada motar a kopar gidan" suka fito suka sa akayi
musu sallama da Alhaji sunusi"
Ya fito ya tarbe su cikin mutunci" da suka gabatar
da kansu yaji kosu wanene" sai yayi musu barka
da xuwa" yace su jirashi ya bude falo" da shigarsu
bayan sun xauna a kasa sai ya basu hannu ska
gaisa" ya saurara don yaji maganar da ke tafe
dasu" duk da yake dai dama an fada masa a cikin
gida"
.
.
Malamin su fatima shine ya gabatar da kansa da
kuma Dakta Usman" sannan ya fada masa dalilin
xuwansu" watau neman ixni da amincewa akan
neman auren fatima da Dakta Usman yake yi"
Bayan Alhaji sunusi ya gama sauraren su ne sai
yace-:
"to wannan maganace mai matukar muhimmanci"
kuma da yake kun biyo hanyar da ta dace ku biyo"
naji dadi" nidai abinda xance shine" nidai a
bangarena na amince na kuma baku dama" yanxu
ya rage tsakaninku da yarinyar" ku sake daidaita
tsakaninku" sai muga kuma abinda Allah xaiyi"
.
.
Sukayi masa godiya cikin girmamawa" ya tashi ya
shiga cikin gid.........¤TUN A DUNIYA¤
.
.
.
ραgє
22
ωιтн
Aßßαη ßαѕмαян
Dαη
мυтαη уσßє
ωнтѕαρρ ριη +2348082035050
.
.
•KAMMALAWA∆°°°°√™
(THE END)
.
Sukayi masa godiya cikin girmamawa ya tashi ya
shiga cikin gida" yasa Hajiya ta tura fatima domin
su sake xantawa" fatima ta shigo ta samesu ta
gashesu" sannan ta xauna a gepe guda" suka
sanar da ita amincewar da mahaifinta yayi" fatima
ta nuna musu jin dadinta"
Suna cikin maganar ne mujahid yaxo da motarsa"
ya samu katuwar jeep din a kopar gidansu" yayi
tsammanin mahaifintane yayi manyan baki" ya
matsa da tasa motar gaba kadan sannan ya fior"
yaga falo a bude don haka sai ya saurara tukunna
ya tsaya a kopar gidan"
.
.
Ba.a jima ba yaga fatima ta fito tare da mutanen
sunsha suturu na alparma" ta raka su wajen jeep
din tayi musu sallama" cikin parin ciki"
mujahid yaji tsoro ya kamashi domin kuwa a
yadda yaga fatima tare da wadannan hamshakan
mutanen ya fahimci wajenta suka xo" kuma
saboda matsayinsu ma har falo aka basu" a ciki
sukayi xance da ita"
ya jira suka shiga motar" Dakta Usman ya tuka
sukayi ribas" sukayi kwana suka tafi" duk sannan
fatima tana tsaye a kopar gidan tana kallon su"
bata shiga gida ba"
mujahid ya matsa inda take ya kira sunanta"
"Fatima"
ta juyo ta dubeshi" tayi mamaki da taga mujahid
ne yau a kopar gidansu" tace dashi ba tare da
wata damuwa ba"
.
.
"Ah, yaya mujahid" yaushe kaxo?"
yace da ita cikin kunya"
"na dan jima anan" naga kinyi baki ne shine na
jira suka tafi"
ta gaeshe shi cikin ladabi"
"ya umma dasu mama?"
yace-:
"suna nan lafiya" Umma tace in gaesheki"
"Ina amsawa" bamuyi waya ba tun shekaranjiya"
fatima ta tambayeshi"
"lafiya naganka anan kopar gidanmu mujahid" baka
san xabba'u ta koma gidansu ba ne?"
mujahid yayi ajiyar xuciya" yace da fatima"
"Don Allah ki daina yimun xancen wannan
manafukar" Idan naji an fadi sunanta a gabana" sai
inji kamar ana dukana" wannan yarinyar makira
ce... Axxxaluma....."
"Haba yaya mujahid" wannan wanne irin cin
mutunci ne?" ya xaka xo har gida ka rika xagin
'yar uwata?" baka san yadda nake da ita bane?"
kanwar mahaifiyata ce fa?"
mujahid tace-:
"Na sani" to amma abinda baki sani ba fatima"
itace tayi makirci ta rabamu ni dake" Ashe wannan
mutumin da yaxo yayi maki sharri" ita ta sashi"
tare da wannan muguwar kawar tata" sune suka
shirya wannan makircin"
.
.
Fatima tace-:
"Na dade da sanin haka" ai kaine baka sani ba sai
yanxu" yaya mujahid"
mujahid ya fara yi mata magiya"
"kiyi hankuri fatima" nasan ranki ya baci a
sakamakon irin maganganun da na fada maki" Don
Allah ki yape mun" Naxone domin in nemi
afuwarki" yanxu na gane duk duniyar nan babu
wata mace wacce ta cancanta dani irinki" kinsan
ina sonki fatima in banda wannan makircin da
xabbba'u ta shirya a tsakanina dake" da har
yanxun muna tare" kiyi hankuri ki yape mani" mu
daidaita kamar da" Ina sonki fatima"
.
.
Fatima tayi murmushi-:
"yaya mujahid kenan" tace sannan tayi ajiyar
xuciya"
"to da parko dai kamar yadda ka roki inyi maka
afuwa" nayi maka dama tuntuni" ban kullace ka a
raena ba" kuma banyi fushi kamar yadda kake xato
ba" babu dalilin da xai sa in damu akan abinda na
tabbatar ba halina bane" kaine mutum na farko
dana fara tsayawa dashi da sunan soyayya" duk
wanda xaiyi mun adalci idan ka tambayeshi" nasan
xai pada maka haka"
Lokacin da wannan mutumin yaxo yayi mun kaxapi
a gabanka" kai kanka ya cancanta ka gane sharri
yayi mani" to amma nasan komai dadewa gaskiya
taxa bayyana" gata kuma yau ta bayyana" tunda
gashi kaxo da bakinka ka fada mun" ka gane
sharri akayi mani" ba halina bane abinda kake
xargina dashi"
.
.
Mujahid yace da ita a karaye-:
"to fatima yanxu yaya soyayyarmu...? Kinsan ina
sonki" kuma ina burin ki xamo matata a duniya"
fatima tace dashi kai tsaye"
"Bakin alkalami ya riga ya bushe mujahid" domin
kuwa ka ganewa idanunka da kaxo wannan
mutumin da yaxo tare da malaminmu shixan aura"
don kuwa sun riga sun nemi ixni a wajen
mahaifina" kuma ya basu dama" ya amsa
maganarsu"
mujahid yaji kamar an kwada masa dutse akai" yaji
kamar ya juwa xata kayar dashi kasa" bai san
lokacin da ya durkusa a gabanta yanayi mata
magiya ba"
fatima ki ceci rayuwata" ki duba halin da xan shiga
idan na rasaki a halin yanxu" kiyi hankuri ki amshi
soyayyata" nayi maki alkawarin baxan sake
maimaita abunda nayi maki ba" Idan baki amsheni
ba yanxu" rayuwata xata shiga cikin garari fatima"
ki tausaya mani"
fatima taji hawaye ya xubo mata tace dashi-:
.
.
"tun ran gini tun ran xane mujahid" na baka dama
a lokacin da ban taba ba wani namiji ba" nasoka
irin sonda ban taba yiwa wani namiji irinsa ba"
nayi kuka a dalilin sonka" a lokacin da ban taba
yin kuka saboda wani namiji ba"
Na kasa bacci a dalilinka nayi wahala akan
soyayyarka" a lokacin daka juyamun baya" don
haka babu yadda xanyi in sake dafawa

Please Login or Register in order to submit comment