Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alhaji sunusin yayi sa.a ma bashi
yaxo nan ba" yau da naji dalilin da xai sa ya kama
mun 'ya da duka" saboda yana takamar tana
xaune a gidansa" kome tayi ba.a xuwa a fada
mun?"
.
.
Hajiya ßinta" ta fara xubar da hawaye" domin kuwa
xabba'u ta jawo mata mahaifinta yana fushi da ita"
tayi iya kokarinta ta bashi hankuri ya fahimce ta
amma abun yaci tura" malam Abubakar ya dauki
so ya dorawa xabba'u" baya ganin laifinta"
Hajiya ßinta" ta tashi tana kuka taje dakin mama
ßalarava wato amarya" ta sami xabba'u a xaune
tana shan koko da karamin ludayi cikin kasaita
kamar wata karamar yarinya" Hajiya binta tace da
ita-:
.
.
"Nazo inyi maki godiya bisa sakayyar da kikia
yimun" na gode xabba'u"
ßa gori xanyi maki ba" amma nayi maki abinda a
wannan xamanin ba kowacce 'yar uwa xata yiwa
'yar uwa ba"
ko 'yar da na haifa fatima banyi mata abinda nayi
maki ba" ke kin sani" sai dai ki take sanin" saboda
tsabar son rai da butulci" tun kina jaririya na
shayar dake nonona" har kika rayu kika samu
kanki a halin da kike yanxu"
Amma yau an wayi gari wai nice xaki xo ki hada
da baba ko xabba'u?"
nice yau na xama abokiyar gabarki?" bayan ke kina
sane kece baki da gaskiya" kece kika yiwa fatima
sharri kika rabata da masoyinta" suna xamansu
lafiya"Amma duk wannan bai isheki ba" shine kika
kwaso kayanki kika dawo gida" kika cewa baba
mun kore ki"
.
.
Baki yimun adalci ba xabba'u kuma kin xalunce ni"
bani na haifeki ba" ke kanwata ce" Amma na
tabbata idan nayi maki baki wallahi sai ya kamaki
da sauri" to baxan yi maki baki ko wata muguwar
addu.a ba" xanyi maki fatan alheri"
Allah yasa kuma ki gane kuskurenku" kuma indai
akan mujahid ne kikayi wannan makircin" to fatima
ta rabu da mujahid har abada" kije an bar maki
shi" saboda a xauna lafiyaa" Allah ya baku sa.a"
.
.
Hajiya binta ta koma gida cikin tsananin bakin ciki"
da xuwanta xaxxabi ya bugeta ta kwanta a gado"
tana rawar sanyi" fatima tayiwa babanta waya tana
kuka" wanda ya tafi kasuwa" tace ya dawo gida
hajiya bata da lafiya" jikinta yayi xapi"
kafin Alhaji sunusi ya dawo sau biyu tana suma"
da xuwansa suka dauketa a rude suka kaita cikin
mota" suka garxaya da ita asibiti"
Likita da ya aunata yace ciwon xuciyane yayi mata
mummanan kamu" sai dai a dage da addu.a"
amma komai xasu yi mata" rayuwarta na cikin
tsaka mai wuya"
.
======>+++++¤+++++<=======
.
Da Umma taji abinda yake faruwa da sukayi waya
da fatima" bata tsaya jiran komae ba sai ta nufi
asibitin murtala" inda aka kwantar da hajiya binta"
ta samu fatima a waje tare da xainav sunyi jugum-
jugum" likita yace su fito waje" ana duba marasa
lafiya"
.
.
Umma da fatima suka kama hannun juna suka.....¤TUN A DUNIYA¤
.
.
.
ραgє
17
ωιтн
Aßßαη ßαѕмαян
Dαη
мυтαη уσßє
ωнтѕαρρ ριη +2348082035050
.
.
Umma da Fatima suka kama hannun juna suka
kebe gepe guda" kusa da wasu shuke-shuke dake
cikin asibitin" suka xauna kowacce tana xubar da
hawaye domin kuwa sun dade basu ga juna ba" a
sakamakon sabanin da ya shiga tsakanin fatima da
mujaid"
Fatima ta fadawa Umma yadda al'amarin ya faru"
tun lokacin da wani kato yaxo ya same su suna
hira ita da mujahid yayi mata sharri" yace wai ya
bata kudi xaiyi lalata da ita" amma taki xuwa
dakinsa"
ta kuma fadawa Umma yadda mujahid ya kasa
fahimtar sharri katon yayi mata" ya caba mata nasa
maganganun ya shiga motarsa ya tafi cikin fushi"
wanda wannan shine rabuwarta da mujahid ta
karshe"
.
.
Fatima tace da Umma-:
"kin san ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yake
yi" ashe da yake ita bakar annamimiyar xabba'u
tasan ita ta kulla abin" ita da wannan shedaniyar
kawar tata Asma'u sai suka samu mujahid suka ce
wai ya turo iyayensa suce sun xone a nema masa
ixinin yanxu ita yake so" bani ba"
kinji dalilin xuwan mama gidan nan" kinsan taxo
sunyi magana da Hajiya" kuma a dalilin haka ne
aka gane cewar xabba'u ce ta kulla mana wannan
makircin domin ta rabamu ni da mujahid"
Umma ta dafe kanta cikin jimami" tace-:
"Haba!" ni dama nasan akwai wani abu a boye"
amma nayi mamaki da mujahid ya kasa gane ita
ce ta kulla wannan sharrin" meyasa mujahid yayi
haka" har yasa mama cikin maganar" ta goyi
bayansa ya nemi xabba'u?"
.
.
Fatima tace-:
"kada ki ga laifin mujahid Umma" ki rabu da
makirci" ba wanda ya gagari irin wannan bala'in ya
fado masa" kedai kawai kiyi addu.ar Allah ya cire
mutum daga sharrin makiri akoda yaushe"
Ni a yadda na fahimci al'amarin tun lokacin da ta
kudiri aniyar xata rabani dashi" bata fito ta nuna
tana sonshi ba" sai da ta tabbatar ta shirya
makircin da xata rabamu" ta yadda shi mujahid
baxae taba xargin tana da hannu a cikin sharrin da
suka yimun ba" sai da ta tabbatar ta rabamu
sannan taje tasan shige da ficen da tayi" ta koma
suka fara soyayya"
Umma ta share hawayenta tace-:
"Amma kuwa duk inda ake neman makira'
macuciya" wacca batasan abunda take yi ba"
batasan abinda ya kamata ba a rayuwa" to idan
aka samu xabba'u an gama" duk wannan halarcin
da Hajiya take yi mata" amma ta rasa wanda xata
yiwa sharri sai ke?"
Fatima ta girgixa kai cikin takaici"
"Bari in fada maki Umma" ni na tabbatar yadda
Hajiya take son Xabba'u bata sona haka"
Akwai abubuwa da yawa da xaki ga Hajiya tayi
mata ita kadai" ba tare da tayi mun ba" kuma bana
damuwa saboda nasan kanwarta ce" yau ga
sakamakon da tayi mana" ta jepa mu cikin bala'i
mu dukkanmu"
.
.
Umma tace-:
"Ba komai" idan ita ta rike makirci da xamba" mu
kuma mu rike addu'a dare da rana" In Allah ya
yarda sai munyi galaba akanta" bada dadewa ba"
Allah saiya tona asirinta" kuma sai tayi nadama"
Fatima tace-:
"Ni yanxu rashin lafiyar Hajiya kawai yafi damuna"
Ga jikinta yayi xapi kuma nsan a dalilin wannan
bakin ckin abunda xabba'u tayi a gidan" shine ya
haifawa Hajiya da wannan ciwon"
Umma tayi ajiyar xuciya-:
"ki dauki wannan abun a matsayin kaddara fatima"
babu ta inda Allah baya jarrabar bawansa" Hajiya
xata samu lafiya in Allah ya yarda" Idan naje gida
xan samu mama" xan fada mata duk abinda ake
ciki domin ta fadawa baba su shiga tsakanin
mujahid da xabba'u saboda soyayyarsu ba alheri
bace" kuma xabba'u ba mace tagari bace" anno
bace a gida"
Sun dade a xaune suna maganar akan wannan
masifa data xo musu" bayan likita ya gama aiki ya
fito" sai fatima ta jagoranci Umma suka je dakin da
Hajiya take kwance" ta farka daga dogon baccin da
tayi" amma da kyar take iya bude idanunta a
sakamakon wahalar da ta sha"
.
.
"sannun Hajiya, yaya jiki?"
Umma tace da ita" bayan ta matsa jikin gadon
tana kallonta" Hajiya binta ta bude baki da kyar!
"Naji sauki"
ta dubi Umma da fatima 'yarta" wadanda suma
suka kura mata idanu suna jimamin halin da take
ciki" ta sake kokartawa tace dasu':
"Don Allah kada ku tayar da hankalinku a kaina"
xan tashi In Allah ya yarda" kuma game da xabba'u
kada kuce xaku dauki wani mataki akan abun da
tayi mana" ku dauki komai ba komai ba" ku rabu
da ita" bana son inji wani ya sake cewa komai
akanta""
Umma tace da Hajiya"
"Kada ki damu Hajiya" duk abinda kikace mana
xamu bi umarninki" kuma baxamu ce mata komae
ba" mun barta da Allah kome tayi"
Hajiya binta tayi ajiyar xuciya-:
"Allah yayi maku albarka" Na gode"
Bacci ya kwashe ta bada dadewa ba" fatima ta
raka kawarta Umma har bakin (gate) din asibitin
inda xata hau mota" ta koma gida" suna tafiya
suna hira bayan sun rabu ne sai fatima ta koma
domin ta amshi xainav xaman jinyar"
.
====>+++++¤+++++++<=======
.
"Xabba'u ta kira Asma'u ta fada mata abinda yake
faruwa da kuma rikicin da akayi"
"yanxu haka ina gidanmu inda babanmu yake
Asma'u na baro gidansu Hajiya jiya da daddare"
Asma'u tace da ita-:
"to sai me don kin baro musu gidansu?"
kawai suna yi maki bakin ciki ne don sun fahimci
yanxu ke mujahid yake so ba fatima ba"
.
.
Xabba'u tace-:
"Na sani, nasan komAi Asma'u" ai shi yasa dama
na baro musu gidan"
Asma'u ta sake ce mata-:
"A kan mujahid ba gudu ba ja da baya xabba'u
kuma ko suna so ko basa so" sai kin aureshi"
saidai su mutu" ai ni ban yi xaton Hajiya xata yi
maki haka ba" wato ita ma ta nuna 'yarta take so
kenan!"
Xabba'u tace-:
"Eh mana" ai taxo daxu da sape ta samu baba ta
fada masa karya da gaskiya" tayi xaton xai barta ni
ya xaxxageni" ina jinsu" tana gama fada masa ya
kuma fada ta da fada da xagi" ya koreta fata-fata"
.
.
Asma'u tayi dariya-:
"to kin gani" yanxu bamu da wata matsala wajen
su baba" tunda shi dama a bangarenki yake"
xabba'u tace-:
"A haba" baba ya xa.ayi ya goyi bayanta dama"
sa.a ma tayu bataxo jiya ba lokacin da naxo
gidan" da a lokacin ta biyo ni" ba abinda xai hana
ya dauko sanda ya biyota" saboda akan dukan da
Alhaji yayi mun" baba ya fusata sosae"
Asma'u ta tambaye ta-:
"kin kira mujahid kin fada masa abinda yake
faruwa ne?"
tace--;
"A,a bamuyi waya dashi ba yau"
Asma'u tace-:
"to kada ki kirashi" ki barni xanyi (handling) din
maganar" ina so ne yaxo har gidan ya sameki"
domin kowa ya tabbatar ya damuke dake"
xabba'u tace cikin farin ciki"
"Na gode kawata (thank you so much)"
suka rabu suna murnar nasarar da suka samu"
.
=====>++++¤+++++<========
.
Mujahid yana wajen aiki" Asma'u ta kirashi" da ya
dauki wayar ne" tun kapin su gaisa ta ce dashi"
"mujahid kaga abinda xabba'u take jin tsoro"
wanda yasa taki amsar soyayyarka" sai da na
matsa mata" kaga dai ya paru"
"meya faru Asma'u?"
mujahid ya tambayeta a tsorace" Asma'u tace-:
"kwai daga mamanka taxo ta samu Hajiya binta
akan maganar soyayyarka da xabba'u kawao da
tafiyarta Hajiya da Alhaji sunusi mahaifin fatima
suka rupar wa xabba'u da bugu kamar xasu
kasheta" dakyar ta kwaci kanta ta gudu"
yanxu sun koreta" korar wulakanci saboda tana
sonka" tana can gidansu wajen mahaifinta"
mujahid yaji xuciyata ta kawo masa wuya"
"xabba'un ce suka yiwa haka?" wanne mataki aka
dauka?"
Asma'u tace-
"to wanne mataki xa.a dauka mujahid?" ba suna
takamar su suka riketa ba" tun tana karama" kuma
suna takamar su masu kudi ne" shiyasa suka yi
mata wannan wulakancin" dama hankuri take yi a
gidan" yanxu dai tayi kai" ta koma gidansu" axan
ma ta kwana"
.
.
Mujahid yace a fusace-:
"Amma don xalunci don su suka riketa sai suyi
mata haka?" idan suna tunkaho da dawainiyar da
sukayi mata ne" su fada ko nawa a biyaso mana"
Gaskiya nixanje gidan su xabba'un in samu
mahaifinta muyi magana" a dauki mataki akan
bugun da Alhaji sunusi yay mata" kawai don yana
auren yayarta kuma sai ya dake ta" haka akeyi?"
Asma'u tace-:
"A,a hankuri xa.ayi mujahid" ita ma xabba'un ta
dangana ta rabu dasu" ta san saboda kace baka
son fatima" ita kake so shiyasa sukayi mata haka"
mujahid yace a fusace-:
"Na ki inso fatiman" indai akan nace banason
fatima ne xasu huce akan xabba'u to kome xasu yi
sai dai suyi"
.
.
Asma'u tace-
"zaka xi gidan su xabba"un ne idan ka taso daga
aiki ko kuwa?"
mujahid yace-'
"Of course" xan xo" yanxun nan ma da mun gama
wayar nan xan kirata inji yadda ta kara ji da jikin
nata" Allah yasa dai basu ji mata rauni ba"
Asma'u" tace-:
"No, munyi waya bataji rauni ba" yanxu ta samu
sauki" amma dai duk da haka ka bulla ku gaisa"
"Ai wannan dole ne" an jiman nan kuwa" a ina
gidansu yake?"
Asma'u tace-:
"yana yakasai ne ko kuma in ba matsala kawai ka
biyo ta gidanmu ka dauke ni" sai muje in raka ka
can gidan" naga xaifi sauki"
"shinkenan ma kuwa" xanxo da yamma in dauki
Asma'u"
mujahid ya fada tarkon xabba'u da Asma'u
.
=====>++++¤++++++<=======
.
Lokaci kusan daya Umma ta dawo daga asibitin
murtaka duba Hajiya binta da kuma mujahid wanda
ya dawo daga wajen aiki"
Umma tana xuwa" da yake ta riga mujahid
shigowa" ta samu mama Rakiya suka xauna ta fara
warware mata xare da abawar yadda abun ya paru"
Umma tace da mahaifiyarta"-:
"xabba'un nan makirace Umma" idan kikaji irin
makircin da tayiwa Hajiya wallahi kare ba baxai ci
ba" ki raba yaya mujahid da ita" idan kuka barshi
ya aure ta" yadda ta fasa gidan su fatima" haka
muma xata xo ta fasa mana wannan gidan"
Xabba'u uta tayi kutun-kutun din da ta raba fatima
da mujahid" duk abun da mujahid xaixo ya fada
maki a game da fatima duk sharrin xabba'un ne"
ni abunda nake so" ko da yaya mujahid baxai
koma wajen fatima ba" to gaskiya a rabashi da
xabba'u domin kuwa ba alheri bace gareshi"
,
,
mama Rakiya tace-;
"to nipa na rasa gane kan wannan lamari" idan
mujahid yaxo sai yace kaxa" ke kuma idan kika xo
sai ki rushe kice kaxa" ya kuke so inyi ne a gidan
nan Umma?" ke da dan uwanki kunki ku hada
kanku ku fahimci juna"
shi yana cewa karya kikeyi" ke kuma kina cewa
karya yake yi" ta yaya xan fahimci wanene yake da
gaskiya a cikinku?"
ke kina son kawarki fatima" shi kuma yana son
budurwarsa xabba'u"
.
.
Kince xabba'u ba alheri bace" to yaya xamu gane
wanene yafi gaskiya a cikinku Umma?"
.
.
Umma tace wa mama Rakiya-;¤TUNA DUNIYA¤
.
.
.
ραgє
18
ωιтн
Aßßαη ßαѕмαян
Dαη
мυтαη уσßє
ωнтѕαρρ ριη +2348082035050
.
.
Umma tacewa mama Rakiya-:
"ni nafi so kiyi bincike mama" kiyi binciken yadda
wannan matsalar take" yanxu haka Hajiya tana
asibiti" kuma inda badon abinda xabba'u tayi mata
ba" me xai bata mata rai haka?" ciwon xuciya fa
take yi mama?" idan mujahid ya auri xabba'u
mama" watarana haka xa.a kwashe mu akai mu
asibiti" bakin cikin ya kamamu"
Umma tana cikin fadin wannan maganar mujahid
ya shigo gidan cikin damuwa" yaji abinda yake
fada" don haka ko sallama baiyi ba" ya fara yiwa
Umma fada"
.
.
Ke Umma me kike fada?" kin sam abinda kike
cewa kuwa?" xabba'un ce kika xo kina hantararta a
wajen mama?" ni xakiyiwa munafunci?" dama baki
da kunya" saboda kinga ina sakar maki fuska ko?"
mama Rakiya tace dashi-:
"ya isa hakan nan" bana son in sake jin maganar"
kowa ya tafi ya bani wuri"
Mujahid yace da mama Rakiya-:
"In banda wannan yarinyar bata da mutunci mama"
bata san abinda yake faruwa ba" maganar da akeyi
yanxu xabba'un tana can kwance bata da lapia" su
Hakiya sunyi mata dukan tsiya" ita da Alhaji
sunusi" kawai saboda xalunci sun koreta tabar
gidan" ta koma gidan mahaifinta a yakasai"
menene wannan idan ba hauka ba" kawai sun
samu 'yar mutane da baugu sun tarar mata"
.
.
Umma ta daga kai tace dashi-:
"yaya mujahid ba haka bane" duk wanda ya fada
maka wannan maganar karya yake yi"
Hajiya batayiwa xabba'u komae ba" kuma ba
wanda ya kori xabba'u don kanta ta kwshe kayanta
ta gudu ta koma yakasai" Hajiyar ce ma taje daxu
da sassafr domin ta dawo da ita" shine aka samu
(misunderstanding) acan gidan" har abin ya bata
wa Hajiya rai" yanxu haka tana can a asbiti" nima
daga asibitin nake"
mujahid" ya dakatar da eta-:
"Rufe mun baki da karyar banxa" baki san yadda
maganar take ba kixo har kina wani hakikancewa"
wannan shine (last time) dinda xan baki" idan na
sake jin kinxo kin fada wa mama wani aibu akan
xabba'u saina karairayaki" a gidan nan" xaki tashi
ki bani wuri ko sainayi (ball) dake?"
.
.
Umma ta xumburi baki" ta tashi ta tafi dakinta cikin
pushi"
mujahid ya dawo da hankalinsa wajen mama
Rakiya" wacce tabisu da idanu tana kallon su suna
jayayyarsu yace da ita-:
"kiyi hankuri mama" duk wannan maganar da
Umma take fada maki karya take yi" kawai ta hada
kaine da fatima saboda taxo ta rika fada maki
karya da kaxapi" don ki tsani xabba'u" amma
komai ta fada ba gaskiya ba ne"
Xabba'u yarinya ce mai ladabi" ko kadan baxaki
hadata da wannan shashashar fatimar ba" wacca
bata san mutuncin kanta ba" ki toshe kunnenki
daga duk wata magana da wadannan yaran suke
fada" ba gaskiya bane mama!"
Mama Rakiya tace-:
"Ita ma na fada mata" ni yanxu baxan iya gane mai
gaskiya ba a tsakaninka da Umma" ku dukkanku
'ya'yana ne" amma kowa da abinda yake xuwa
yana fada" Ni abinda na barwa xuciyata shine"
koma a ina gaskiyar wannan al'amari take xata
baiyana komai dadewa" idan xabba'u ce tagari"
lokaci xai nuna" idan kuma fatima ce tagari" babu
abunda lokaci xai boye" idan mukayi hankuri" illa
iyaka"
mujahid yace-:
"Ai tuni ma lokaci ya gama nunawa mama" xabba'u
ce tagari" kuma xan tabbatar maki da haka"
Mama Rakiya tace dashi"
"to Allah ya bamu sa.a"
.
=====>++++¤+++++++<=======
.
Kwana biyar Hajiya binta tayi a asibiti" ta samu
sauki sosae" Alhaji sunusi ne ya matsa aka
sallamesu" suka dawo gida" A kwanakin da tayi a
asibitin" kowa yaje gaisheta har mahaifinta da yake
pushi da ita" shima saida yaje ya duba ta" amma
xabba'u ko sau daya bata je ba"
Da suka xo gida ne Alhaji sunusi ya tara su a falo
su dukansu" Hajiya binta da 'ya'yanta watau fatima
da kannenta biyu yace dasu-:
"Ina so mu dukkanmu mu dauki wannan masifa
data same mu a matsayin kaddara" bana son
wannan yasa my kullaci wani mutum a xuciyarmu"
musamman ita wannan yarinyar xabba'u mu
daketa har yanxu a matsayin 'yar uwarmu" ko in
cema 'yar cikin nan gidan" domin kuwa har abada
kome xabba'u ta xama a duniyar nan" to bata dafa
ina yakai nan"
Ba lokaci ba bane yanxu da xata gane haka" amma
da sannu xata gane yau da kullim"
.
.
Ke kuma Hajiya ki kwantar da hankalinki ki daina
damun kanki" ki cire duk wata damuwa daga
xuciyarki" nasan abunda yake damunki" bai wuce
takaicin fushin da baba yake yi da ke ba akan
sabanin da ya shiga tsakaninmu da xabba'u"
Ki daina damuwa duk wannan ba wani abu bane"
Alheri da kika yi masa don neman albarka" kici
gaba da yi" Allah yasan abinda yake xuciyarki
kuma xai taimakeki" komai xaixo ya wuce in Allah
ya yarda"
Tun daga ranar suka kwantar da hankalinsu a
gidan" sukaci gaba da harkokin su kamar komai
bai taba faruwa ba"
.
=====>++++¤+++++<========
.
A bangaren xabba'u kuma suna can suna shan
soyayyarsu ita da dan lelen saurayinta mujahid"
kusan kullum sai yaje gidansu" kuma da yake
xabba'u 'yar sin lalacewa ce" koda yaushe sai ya
dauke ta a mota sun tafi yawo" xabba'u tana
sha.awar suje (shopping) mujahid yana kashe mata
kudi sosae" yana yi mata duk abinda take so"
.
.
A wani mako ne da ya xagayo" wani abokin mujadi
da suke aikin banki tare sai yayi aure" yaba
mujahid ankon da 'yan matan amarya da danginta
xasuyi" wane leshi ne fari na dubu biyar"
salim yace wa mujahid yakaiwa xabba'u ta dinka
taxo bikin tare da ita" ya basu (gate pass) guda
biyu" inda xa.a yi fati a ranar asabar da daddare"
mujahid ya amso leshin" bai fadawa xabba'u ba sai
ana saura gobe yace ta shirya xai bada leshin
ankon a dinka mata" xaixo mata dashi gida" sai
dai kawai tayi wanka tasa su tafi biki"
.
.
Mujahid yakaiwa Umma kanwarsa leshin ankon
ranar juma.a yace-:
"Ina son ki dinka leshin nan na anko ne" kiyi masa
dinki mai kyau" gobe muna da bikin wani abokina
ne"
Umma ta amshi leshin" ta ciro shi a leda" ta
tambayeshi"
"Na wanene yaya mujahid"
ya bata rai yace-:
"Na xabba'u ne"
Umma ta yatsine fuska cikin fushi" ta kalli leshin a
wulakance" mujahid ya harare ta yace-:
"saura kiyimun shirme" gobe da safe nake sonsji"
xan tafi dashi ne" daga wajen aiki xan wuce in kai
mata"
.
.
Umma ta figi ledar leshin xata kai dakinta"
"ko bakiji abinda nace bane" Umma?"
mujahid ya daka mata tsawa" tace a fusace
"na ji"
Har yamma tayi umma bata ciro leshin ta yanka
ba" mujahid yaje har dakinta ya sameta ya gargade
ta"
Umma" ya naga baki je kin fara dinka leshin ba?"
wai me kike nufi ne?"
Umma tace-:
"xan dinka"
mujadin yace da ita-:
"kinga akan dinkin nan ranki xai baci" Umma" kina
ji na?" xan saba maki a gidan nan idan aka wayi
gari naga baki dinka mata ankon nan ba"
Ya koma daki a fusace" Umma ta dauki leshin taje
dakin mahaifiyarta" ta ciro leshin ta yanka" ta hau
keke ta fara dinkawa" Da mujahid ya sake dawowa
yaga tana kan aikin dinka leshin ne sai yaji sanyi a
ransa" ya tafi ya bata wuri"
.
.
Da yake Umma ba kanwar lasa bace" ashe ta gama
shirya musu tsiya shi da xabba'u" tayi rigar wata
irin falkekiya kamar buhun masara" Hannunwan
rigar 'yan sirara mitsi-mitsi" dakyar hannu xai iya
shiga" ta matsw wuyan rigar kamar rigar maxa"
sannan taxo yin siket din shima sai tayi sama yayi
yawa" kasa kuma sai ya tsuke kamar kayan hawa
bori"
.
.
Ta gama dinkin ta ninke kayan tana girgixa kai
cikin mugunta" ta saka masa a leda tsap" ta gyara
su kamar abun arxiki" sai da sape da xaije aiki
mujahid yaxo ya tambayeta"
"Ina kayan suke?"
Umma ta dauko su a leda a ninke" ta bashi ya
amsa"
Ya tambayeta a fusace-:
"Nawa ne kudinki?"
Umma tace-:
"Ai kyauta nayi maka" kabar kudin" ka kaiwa
xabba'u taci biki lapia"
Mujahid yadan sake ransa don kuwa yaga alamun
watakila Umma ta dawo ita ma ta goyi bayansa
akan soyayyarsa da xabba'u dama itace kawai
matsalarsa" kowa yabi a gidan" amma ita tana nan
tana adawa" tana bangaren kawarta fatima"
.
.
Mujahid yaje aiki yabar kayan a cikin mota" saida
yamma" sanda kowa yake tashi domin suje suyi
shirin xuwa fatin abokinsu" sai ya kira xabba:u a
waya shina yace mata-:
"xanxo maki da naki ankon yanxun nan" ki dauki
kwalliya da naxo saiki sa mu wuce" na bayar da
kayan an dinka maki"
xabba'u tace-:
"to (my sweetee) xanyi wanka in shirya kafin kaxo"
"i love you xubee"
"i love you too"
.
====>+++++¤++++++<=======
.
Mujahid ya isa gidan su xabba'u bayan minti
talatin dayin wayarsu" ya fito daga cikin mota
kenan ta fito daga gida" da yake da xuwansa ya
matsa hon" a haka yake kiranta idan yaxo koda
yaushe"
xabba'u ta dafa kopar gidansu tana dariya" da
ganinta tayi wanka da kwalliya" shi kawai dama
take jira" mujahid ya dauko kayan da ya xo mata
dasu" na ankon" ya isa inda take tsaye"
"you are welcome my love"
tace dashi tana kashe masa idanu" mujahid yace
da ita"
"kinga lokaci ya kure xabba'u wasu tun daxu har
sun tafi" Amshi kayan nan kisa" ki fito mu tafi"
xabba'u ta mashi kayan cikin farin ciki" tace
"xan fito yanxu nan" minti biyar ya isa"
.
.
Mujahid ya koma ya jinjina da motarsa yana kada
makullin motar dake hannunsa" ba a kai minti biyu
ba xabba'u ta fito tana kukan shagwaba" sanye da
kayan" ta tsaya a bakin kofa ranta a bace" tace da
mujahid"
"Haba mu love" ya xakayi mun haka?" Don Allah
duba pa dinkin da ka kawo mun"
taci gaba da kuka shagwaba" da pushi" mujahid ya
matsa xuwa inda take a kidime" yaga tasa katuwar
riga kamar malum-malum" ga hannayenta ma
dogaye ne har sun kusa shanye hannayenta"
wuyan rigar ya shaketa tamau da kyar take iya
magana" siket din kuma bashi da maraba da
wandon leda" bai taba ganin kayan ban tsoro irin
wannan ba"
ya tambayi xabba'u
"wadannan ne kayan da naxo maki dasu yanxun
nan?"
xabba'u ta harareshi-:
"to da wadanne?" kace xamuje fati" amma ya
xakaxo mun da irin wannan dinkin?"
(i,em very embarassed)
ta sake fashewa da kuka"
.
.
Mujahid ya lallasheta"
"kiyi hankuri" ya isa hakan nan xabba'u" kiyi
hankuri ban san haka tayi maki wannan dinkin ba"
yaji kunya ta kamashi sosae ya rasa inda xaisa
kansa" gabadaya maganar xuwa biki ta rushe
kenan kwata kwata"
"
jeki ciro kayan ki dawo mun dasu" kiyi hankuri
xabba'u" ban san haka dinkin yake ba"
.
.
Xabba'u ta koma cikin............¤TUNA DUNIYA¤
.
.
.
ραgє
19
ωιтн
Aßßαη ßαѕмαян
Dαη
мυтαη уσßє
ωнтѕαρρ ριη +2348082035050
.
.
Xabba'u ta koma cikin gida tana kunkumi da
shagwaba" bayan minti biyu ta dawowa mujahid
kayan a cikin leda" ta cillo masa" ya amsa" tun
kapin ya sake baya hankuri ta sake komawa cikin
gida tana pushi"
mujahid ya cije baki" xuciyarsa tana kunar abinda
Umma kanwarsa tayi masa"
ya mayar da kayan cikin mota" ya tuka ya nufi
gida cikin pushi"
Da xuwansa ya fito tare da kayan a hannunsa" ya
shiga cikin gidansu kamar xai tashi sama saboda
sauri"
.
.
Umma" kina ina?" Umma....?"
tunda Umma taji kiran mujahdi yayanta" sai tayi
sauri ta ruga dakin mahaifiyarsu mama Rakiya"
saboda tasan tsiyar da ta aikata" mujahid yabita
dakin mama" da xuwa ya same ta ta boye a
bayanta"
"wai me kuke yi haka ne a gidan nan?" kun san
bana son wannan haukar da kuke yi mani kullum"
menene kuma?"
mama rakiya ta tambayi mujahid wanda ya shigo a
fusace da ankon da Umma ta dinkawa xabba'u da
ya rasa abinda xaiyiwa Umma ya huce" saiya
numpasa yace da mama-:
.
.
"ßa wani abu bane ya faru" mama dama xamuje
wani biki ne ni da xabba'u na abokina salim" bana
fada maki yayi aure ba?"
Acan garinsu aka daura auren" amma anan xa.ayi
bikin"
mama rakiya tace-:
"to! Naji, anyi haka" ka kuwa fada min"
mujahid yace-:
"yauwa to mama kinga yadda muke tare dshi" ai
yakamata daga bangarena a samu wani yaje bayan
ni tunda dai shima an xama daya dashi"
mama Rakiya tace-
"A kwarai ma kuwa" to dama meye ampanin
xaman taren?" ai irin wannan ne idan biki ya tashi
ajewa mutum a tayashi farin ciki"
mujahid yace-:
"yauwa mama" to kinga xabba'u bata da lafiya"
baxata samu xuwa ba" kuma ga ankonta da umma
ta dinka mata" tunda haka ne Umma sai tasa
ankon" muje tare ta raka ni bikin" mudan tayashi
farin ciki" tunda dai ba.a rasa wacce xata raka ni
bane" ga kanwata 'yar uwata ko kuwa?"
.
.
Mama rakiya tace-:
"eh wannan yayi" xuwanka da 'yar uwarka ai yafi
tunda tayashi murna xakuyi" ke Umma tashi kisa
ankon kuje ki rakashi mana" kuce ina murna" Allah
ya bada xaman lafia"
Umma tasa hannu a kanta"
"mama nima pa kaina yana mun ciwo" tun daxu"
baki ga ina kwance ba...?"
mama rakiya tayi mata xagir-xagir
"Bana son rashin mutunci Umma" don kinga ina
hanashi ya rika dukanki" shiyasa kike raina shi ko"
idan na sake buda idanuna banga kin tashi kin
shiga wanka da sauri kin fito yanxu kun tafi ba"
saina bata maki rai"
Umma ta tashi tana kumbure-kumbure" ta wuce
mujahid ta fita daga dakin" yace da ita"
"kiyi sauri kiyi wanka" ga ankon kixo kisa mu tafi"
dama ke kika dinka kayanki"
Umma tace-;
"Ni ina da kayan da xansa" ba wani ankon da
xansa" ka rike kayanka"
mujahid yace da ita-:
"kinyi karya kuma anan" komai tsiyarki sai kinsa"
.
.
Umma ta debo ruwa ta shiga wanka" mujahid ya
jirata a dakin mama rakiya" suka xauna hira" har
Umma ta fito daga wanka xata wuce dakinta kenan
sai mujahid yace da ita"
"Xo mana ga kayan da xaki sa na ankon" sauri
nake yi pa" kada ki bata mun lokaci"
Umma taja ta tsaya cikin xullumi" mama rakiya ta
daga murya tace da ita"
"yau dai sina taba lafiyar jikinki xakiji dadi umma"
yayan naki kike yiwa wannan iya shegen?" ke yayi
ta xaman jira pa" baxaki xo ki amshi kayan kuje
kisa ku tafi ba?"
Umma tace da mahaifiyarsu"
"mama ni bana sa anko idan ana biki" nace yabar
shi insa kayana mana" duba daya bane?"
.
.
Mujahid yace da mama rakiya-:
"Don me to nasa ta dinka kayan mama?" badon
asa in gani nasa a dinka

Please Login or Register in order to submit comment