Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fada
masa"
yace-:
"xanxo anjima"
.
======>+++++¤+++++<=======
:
Tun lokacin da soyayyar fatima da mujahid ta
rushe" Umma da fatima basu sake haduwa ba"
domin kuwa a gidansu fatima mahaifiyarta Hajiya
binta tasa mata dokar sake xuwa gidansu Umma"
kamar yadda ita ma Umma yayanta mujahid yasa
mata dokar kada ya sake ganinta tare da fatima"
Amma kuma kullum sai sunyi magana a waya sau
daya" idan daya ta kira daya" suna kuka suke
magana"
Fatima ta tabbatarwa Umma cewa wannan shiri ne
wasu axxalumae suka shirya mata" saboda su
cimma manufarsu" amma xataci gaba da yin
addu.a akan Allay ya tona asirin koma su wanene!"
.
.
Umma tayi mata alkawarin xata taya ta addu"a
kuma tana kara karpapa mata gwiwar cewa
mujahid xai dawo ya gane gaskiya" xaixo ya nemi
afuwarta" karta damu"
to amma duk da haka fatima wuni tayi cikin tunani
da xullumi" ta rame kamar wacce ta dade tana
rashin lafiya" idan tana cikin daki ita kadai bata
aikin komai sai tagumi" ko kuma ta kurawa hoton
mujahid ido daga inda take xaune"
.
.
Tana matukar son mujahid" saboda shine saurayi
na farko a rayuwarta wanda tayi alkawarin xata
aure shi su xauna tare"
Idan mujahid bai dawo ya tallafi rayuwarta ba"
tasan da wahala ta sake amincewa ta karbi
soyayyar wani da namiji a lokaci na gaba"
.
======>+++++¤++++<========
.
Da mujahid yaje gidansu Asma'u ya sami xabba'u
saita fito suka shiga cikin motarsa suka xauna a
gaba suka fara hira" xabba'u tace dashi-:
"Akwai dalilin da yasa kaga Asma'u taci fama dani
ban amince da soyayyarka ba"
mujahid kasan halin mutane da surutun tsiya"
yanxu idan akaji ka dawo wajena muna soyayya
sai a dauka kamar nice na raba ku" ni kuma ba
abinda ya shape ni" ban san abinda ya hada ku ba
ma sai daga baya"
Dama kuma kae ne baka sani ba tun farko" amma
layinmu kowa yasan tana irin wannan tanbadewar"
sai karti suxo su dauke ta a babur su tafi fati" nayi
nayi da Hajiya ta tsawatar mata" amma tayi biris
da al'amarin ka gani?" shiyasa kowa ya xuba mata
idanu (to hell with her)"
.
.
Mujahid yace-:
"Na san da wannan matsalar xabba'u amma kada
wannan ya dame ki" nina san yadda xan bullo wa
al'amarin" aure dai tsakanin ni da ke ba gudu ba
ja da baya" duk wanda xaiyi magana sai yayi tayi"
kada ki damu"
xabba-u tace-:
"Duk da haka akwai abinda ya kamata kayi"
saboda mu tsallake surutun mutane mujahid"
Ina so ka fara fada anan gidanku cewar a dalilin
matsalar da ka samu da fatima yasa ka yanke
shawarar dawowa wajena" su kuma yakamata yayi
suxo su sami Hajiya" suyi mata bayanin abinda ka
xartar" nasan Hajiya baxata ki ba" saboda tana so
na" Amma idan ba haka kayi ba" soyayyarmu
baxata yiwu ba gaskiya mujahid"
.
.
Ya tabbatar mata"
"xanyi haka xabba'u xan samu mama muyi
maganar da ita gobe da sape" xan nuna mata
fa'idar yin hakan" ita kuma sai taxo ta sami hajiya
suyi maganar" haka kikso ko?"
Xabba'u tayi dariya"
"Haka nake so" sai kayi haka sanna soyayyarmu
xata xauna daram" amma yanxu muna (under
probability) ne!"
"ki kwanta da hankalinki" komae xaixo yadda muke
so"
Kafin dare yayi nisa ne xabba'u tace xata tafi gida
don kada Alhaji yadawo ya samu bata gida" yayi
mata fada" mujahid yaso yakai ta a motarsa"
.
.
Xabba'u tace-:
"A,a mujahid ba yanxu ba tukunna" ka bari sai
komae ya daidaita"
yace da ita-:
"kin cika tsoro xabba'u
tace-:
"ba haka bane" akwai dai dalilin da yasa nace ka
bari din ne sai nan gaba"
suka rabu cikin farin ciki da alkawarin gobe da
yamma xaixo gidansu Asma'u su sake haduwa
idan ya dawo daga gurin aiki"
.
=====>+++++¤+++++<========
.
Lokacin da mujahid ya sami mama rakiya a washe
gari ya sanar da ita abinda ya yanke" da kuma
dalilin da yasa yayi haka" ta dade tana jinjina
maganar kafin ta amince tace-:
"mujahid akwai matsala a wannan maganar da
kaxo da ita" kaga fatima 'yar Hajiya binta ce" ita
kuma xabba'u kanwarta ce" yin hakan xai iya janyo
musu fadan dangi" idan ba.a yi taka tsan-tsan ba"
mujahid yace-:
"Idan akayi musu bayani cikin fahimta" xasu
fahimci dalilin hakan" ni bana so ne mu yanke
xumuncin dake tsakanin ku da su" da fatima da
xabba'u duk daya ne a wajen Hajiya binta" xata
fahimci bayaninki fiye da kowa idan kikaje mama"
.
.
Mama rakiya tace-:
"to baxance baxan je ba tunda ka nace kana son
xabba'u amma banyi maka alkawarin xa.a samu
nasara ba a dalilin xuwana"
mujahid yace-:
"Duk da haka dai ki gwada xuwa mu gani mama"
nina san baxa a samu matsaka ba"
mama rakiya tace-:
"xan fadawa babanka idan ya shigo" idan ya
amince xanje mu sasanta" in fada musu
bukatarmu"
.
.
MUJAHID yayi mata godiya" ya tashi ya tapi" da
shigowar malam Abdullahi" mama rakiya taje
dakinsa ta sameshi da maganar" shi kanshi da
farko bai amince ba" yace-:
"kai akwai kuruciya a maganar nan" ta yaya xaice
baya son fatima kuma yanxu ya koma gidan yace
yana son kanwar innarta" duk da yake yace
laepinta ne" idan akayi mata haka ai anyi mata
rashin adalci"
mama rakiya tace-:
"shi kuma a ganinsa wai yin hakan shixae sa mu
sasanta gabakidaya dasu komai ya wuce"
Malam Abdullahi yace-:
"to kije in kinga xaki iya xuwa din" amma jikin bai
bani cewa yin hakan shine abinda ya dace ayi ba
Rakiya"
su ma a bangarensu anan suka daddale cewa"
mama rakiya xataje gidansu fatima ta samu hajiya
binta ta fada mata sabuwar maganar da taxo da ita
daga wajen dansu mujahid"
.
=======>+++++¤++++<=======
.
A ranar kuwa taje" da shigarta gidan tayi sallam"
yara suka amsa mata" a lokacin Hajiya tana cikin
daki" Da fatima taji muryar mama rakiya a gidan
sai tayi wuf ta fito daga cikin daki tana mamakin
dalilin xuwanta"
fatima tana sa rai mama Rakiya taxo ne domin ta
nema afuwar abinda ya faru" a sasanta tsakaninta
da mujahid ya dawo suci gaba da soyayya"
fatima tayiwa mama Rakiya sannu da xuwa sannan
ta durkusa ta gaeshe ta" ta amsa sama-sama ta
nufi dakin Hajiya binta" ita kuma fatima ta koma
dakinsu tana farin ciki" domin kuwa tana saran
mujahid ya kosa dawowa wajenta"
.
.
Mama Rakiya tayi sallama ta shiga dakin Hajiya
binta" ta sameta tana goge fuskar tibi da tawul"
Hajiya binta ta amsa mata sallamar sannan ta
dawo da hankalinta wajen bakuwarta wacce tayi
mamakin ganinta a gidansu"
"sannu da xuwa"
mama Rakiya ta amsa:
"yauwa sannu Hajiya"
suka xauna tare akan doguwar kujera daya"
"kece da rana haka Rakiya!"
mama Rakiya tace-:
"Nice Hajiya" tun daxu naso xuwa da hantsi" sai
kuma nima nayi bakuwa" ita ta tsayar dani"
Hajiya tace-:
"Allah sarki"
suka gaisa'
"Ina wuni?"
"lafiya kalai"
"lafiya, ya yara?"
"madallah"
Daga nan suka yi shiru" Hajiya binta ta kasa kunne
tahi abinda ke tafe da mama Rakiya" bauan
sabanin da ya faru tsakanin mujahid da fatima"
.
.
Mama Rakiya tace-:
"to Hajiya abubuwa dai sunyi ta faruwa a tsakanin
yara" amma bamu shigo munsa baki ba" tunda
rashin jituwar data faruwa a tsakanin fatima da
mujahid" wanda a gaskiya bamuji dadin abin ba"
nayi kokarin inji yadda abin ya paru domin na
sasanta su" amma abin yaci tura" nidai na rasa
mafarin wannan batawa da sukayi a cikin dan
lokaci kankani"
Hajiya binta tayi murmushi tace-:
"Rakiya kenan" wato a xakirin gaskiya idan nace
maki daidai da sakan daya ranmu ya baci akan
wannan al'amari da ya faru nayi maki karya"
saboda a xahiri fatima tun farko ba aure ta saka a
gabanta ba yanxu" karatu take so taci gaba dayi a
(school of health) nice na takura mata nace
baxataje ko'ina ba aure xa.ayi mata" har kuma dai
cikin ikon Allah ta hadu da mujahid suka fara
soyayya" to mu idan" to amma idan har akwai
abinda ya bata mana rai fiye da komai" bai wuce
kaxafin da akayiwa 'yarmu ba"
.
.
Ran mahaifinta ya baci sosae akan wannan
magana" domin har daukar maganar yaso yayi akai
kotu" nice na lallashe shi na taushi xuciyarsa yayi
hankuri" kinga gaku gakusa duk wannan ya paru
ba"
saboda haka mu a wajenmu magana tuntuni ta
wuce" sai yaje ya samu wacce yake so" ita ma taje
ta samu wanda take so" shinkenan!"
mama Rakiya tace-:
"mun san dole ne ran kowane bangare ya baci
hajiya" amma mu dukanmu hankuri ya kamata
muyi" mu sawa xuciyarmu dangana" mutunci ne
ya hada tun ba yanxu ba" saboda haka bai kamata
mubar wannan maganar ta rusa mana xaman
mutuncin da mukeyi ba na shekara da shekaru"
Don Allah muyi hankuri mu duka"
.
.
Hajiya ßinta tace-:
"Ba komae Rakiya" aina fada maki mu a wajenmu
tuntuni mun saki wannan maganar" sai dai muyi
fatan Allah ya kiyaye na gaba kuma"
mama Rakiya tace-:
"to sai dai kuma akwai wani hanxari ba gudu ba"
mujahid ne ya sameni yace dani" shidai yana so
ace xuri"a ta kullu tsakaninmu da ku Hajiya"
kamar yadda tun farko akayi niyya ba mu" to
yanxu ma baxamu cire rai ba" yace tunda basu
daidaita tsakaninsu da fatima ba" yana neman
ixinin a bashi xabba'u"
Hajiya binta ta dago kai ta dubi mama Rakiya a
kidime"
"Xabba'u?" ta tambaye ta"
"A ina mujahid yasan xabba'u shi kuwa?"
mama Rakiya tace-:
"to...... Can dai watakila suka hadu" kinsan
sha.aninsu na yara" mutum ba sani yake ba"
yadai nuna ita xabba'un din kamar itace sukafi
daidaitawa" indai xa.a amince mana" to wannan
karon baxa.a sake maimaita 'yar gidan jiya ba in
Allah ya yarda"
.
.
Hajiya binta tayi shiru tana tunanin" Abu na farko
da ya fi tsaya mata a rai shine" a ina mujahid
yasan xabba'u kuma har yaji yanxu eta yake so ba
fatima ba?"
Amsa daya ce kawai" dole ne akwai wani abu a
boye da yake faruwa a gidan" wanda yanxu ne
yake so ya baiyana" duk da haka bata nuna
maganar ta tsimata ba" sai tace da mama
Rakiya-:.
.
.
"wannan".................¤TUN A DUNIYA¤
.
.
.
ραgє
15
ωιтн
Aßßαη ßαѕмαян
Dαη
мυтαη уσßє
ωнтѕαρρ ριη +2348082035050
.
.
"Wannan ba wata matsala bace" idan ita xabba'un
tace tana son shi" kuma shima yana sonta" ai
babu damuwa" da ita da fatima ni a wajena duk
daya ne! Dukkansu nina shayar dasu" dukkansu
'ya'yana ne" ba wani bambanci" idan xabba'un
yaga xasu daidaita" toki ce masa yaxo" Allah ya
bada sa.a
mama Rakiya tace-:
"mun gode fa Hajiya xanje in fadawa mahaifin
mujahid" duk yadda mukayi" mun gode"
.
.
Hajiya ßinta tace-:
"ba komae
mama Rakiya tayi sallama" ta tashi ta tafi" har
kusan minti talatin Hajiya binta tana nan xaune
bata motsa daga kan kujera ba" tana tunanin
maganar da mama rakiya taxo ta fada mata ne"
A karshe ta yanke hukuncin indai har mujahid
yanason xabba'u kuma ita ma tana sonshi" to ko
shakka babu" ba wani yayi makircin raba fatima da
mujahid ba sai xabba'u
.
======>+++++¤+++++<=======
.
Da Hajiya binta taga maganar babba ce" abun yafi
karfinta sai tabar abun a ranta" bata yiwa xabba'u
maganar ba" sai da ta bari Alhaji sunusi mahaifin
fatima ya dawo sannan ta sameshi a dakinsa" ta
xauna ta fede masa biri har jela" tace dashi a
karshe"
"Ina xargin akwai sa hannun xabba:u a cikin
wannan matsalar da ta faru a tsakanin mujahid da
fatima" domin kuwa idan babu sa hannunta" ta
yaya mujahid yasan ta" kuma har yaji yana sonta a
maimakon fatima" kuma yaya ita xabba'un xata
amince ya wulakanta -yar uwarta ya dawo wajenta
yace yana sonta" idan ba ita ce tun farko ta kulla
wannan makircin ba?"
.
.
Da Alhaji sunusi yaji yadda al'amarin yake sai ya
fara bambamin fada"
"A gidan nan wannan shaidancin xai faru Hajiya" Ni
xa.a dauka karamin mutum?" Ina gidan amma axo
min da wannan sakarcin?"
Ya daka mata tsawa"
"Ina xabba'un take?" kirawon mun ita"
Hajiya binta tace dashi"
"kai halinka kenanAlhaji" baka bin abu cikin
nutsuwa idan ya paru" yanxu ita xabba'u bata san
mun san da wannan maganar ba" bata san rakiya
taxo ta fadamun komae ba"
kamata yayi mu jira mu gani" mujahid din xai iya
xuwa nan gidan ya aika a kira masa xabba'u?"
kuma idan ya kirata" xata je" ko kuwa baxata je
ba?"
.
.
Alhaji sunusi yace a fusace-:
"wacece xa,a tsaya jiranta a gani" nace ki kirawo
min ita yanxun nan in tambayeta" tsoronta kike
jine wai ko kuwa?"
Hajiya binta ta tashi cikin sauri"
"Allah ya huci xuciyarka" bari inje in kira ta"
ta fice daga dakin taje dakinsu xabba'u ta kirawo
ta" kafin ta dawo ne Alhaji sunusi yaci gaba da
bambami"
"Har akwai wani takadarin da xai taso anan gidan
yayi min iya shege irin wannan in xura masa idanu
ban yi kasa-kasa dashi ba?"
Hajiya binta ta shigo tare da xabba'u tun kafin ta
durkusa ya fara mata tsawa"
"ke xabba'u menene ke tsakaninsu da wannan
yaron da yake son fatima?"
Ya dubi Hajiya binta data tsaya a gepe guda"
"Bani sunansa"
ta ce
"mujahid"
Alhaji sununsi ya koma kan xabba'u"
"wannan yaron mujahid da yake xuwa wajen fatima
meya hadaki dashi?"
xabba:u tayi sasarai a tsaye" ta fara inda-inda"
alamar tsoro da rahin gaskiya ya cika fuskarta"
"ke baki ji abinda na tambaye bane' iye?"
.
.
Xabba'u ta fara in-ina tana cewa-:
"A,a dama... Eh.... Niba komae tsakanina dashi"
Alhaji"
Alhaji sunusi yace da ita-:
"ke kada ki mayar damu kananan yara kinji ko?"
ya aiko ne yace yana sonki" yanx ke yake so ba
fatima ba" mu mun amince" muna sone muji shin
kema kin amince a fada musu" ko kuwa baki
sonshi" abashi hankuri yaje ya nemi wata?"
suka xubawa xabba'u idanu" taci gaba da kame-
kame ta rasa abunda xata ce" a karshe ta dubi
hajiya binta tace"
"xan fadawa Hajiya ko menene"
.
.
Alhaji sunusi yayi mata dakuwa" saura kadan ya sa
kapa ya mauje ta"
"Ni xaki ba amsa don gidanku" nina tambayeki" ba
Hajiya ba" kina sonshi" ko kuwa baki sonsHi?"
xabba'u tace a tsorace'
"Ina son shi"
Hajua binta ta dafe kanta" Alhaji sunusi ya nuna
mata yace yace-;
"munafuka" annamimiyar banxa" kece kika kullawa
fatima makirci" kika rabata da yaron nan" suna
xamansu lafiya" muna xaton wuta a makera sai
gashi ta taso a masaka" yanxke ke saboda baki da
mutunci" fatima ce xaki jepa ta cikin masifa" kisa
ayi mata sharri da kaxapi a bata mata suna" Ashe
baki da mutunci xabba'u?"
.
.
Alhaji sunusi ya kasa hankuri" yakai hannu a
fusace ya tsinke ta da mari" saida ta fadi kasa"
xabba-u ta fashe da kuka" kafin Alhaji sunusi ya
sake yin sufa ya fira kanta" Hajiya binta ta shiga
tsakani" ta durkusa har kasa tana yi masa magiya"
"kayi hankuri Alhaji" ni xaka yiwa" ba ita xaka yiwa
ba" ka rupa min asiri ka kyaleta"
.
.
Alhaji sunusi yace-:
"In banda rashin mutunci" yarinyar nan fa a
tsumma tana jaririya muka dauko" wacce wahalar
duniya ce bamu sha a kanta ba" wanne asibiti ne
a garin nan bamu je ba" a dalilin rashin lafiyarta"
Amma yanxu ta rasa wanda xata cuta sai mu da
xuriyarmu?"
.
.
"YA ture Hajiya ßinta ya sake haure xabba'u ya
cillar da ita ta hadu da bango" ta sake yin
kururuwa tana birgima a kasa" Hajiya binta ta sake
tasowa ta shiga tsakaninsu" ta tare Alhaji sunusi
wanda bai taba yin fushi irin wannan ba" tunda
suke da Hajiya binta"
Xabba'u ta tashi ta ruga a guje ta nufi dakinsu tana
cewa"
"xan bar muku gidanku" don anga ni marainiya ce
ba 'yar gidan ba" shiyasa ake nuna mun
bambanci"
.
.
Ta shiga dakin tana kuka" fatima wacce tayi tsaye
tana sauraron abun da yake faruwa ta ba xabba'u
hanya" wacce ta kusa tureta" xabba'u ta dauko
akwatinta ta bude" ta fara debe kayanta tana
kimsawa" tana kusa" data gama xubawa ne sai ta
dauko gyalenta" ta warware ta yapa" ta jawo
akwatin ta fito waje"
Fatima ta tsare kopar ita ma tana kuka"
"Ina xaki je xabba'u?"
ta bata amsa"
"Gidanmu xan koma" wajen mahaifina" na godewa
Allah da ya kawo ranar barina gidan nan tun
mhaifina yana raye"
.
.
Fatima tace-:
"Xabba'u naji duk abinda yake faruwa" in dai don
mujahid xaki bar gidan nan" ki koma da kayanki
cikin daki" na bar maki shi" tun farko da kin fada
min kina sonshi" dana bar maki shi cikin ruwan
sanyi" ba tare da kowa ya sani ba"
Xabba'u ta ture ta ta wuce waje tana kuka"
"Ba wani abinda xaka fada min bana son sake
xama a nan gidan"
A dalilinki mahaifinki ya bugeni" saboda kece
'yarsa ni ba 'yarsa bace" kuje ga gidanku nan" har
abada bani ba ku" ta nufi kofar gida" ta dauki
akwatin ta dora akanta" taci gaba da kuka"
fatima ta ruga dakin mahaifinta tace da Hajiya
binta"
.
.
Mama" ga xabba'u can ta kwashe kayanta ta tafi
gida" na hanata tafiya amma ta ki"
Hajiya binta xata fita kenan" sai Alhaji sunusi ya
dakatar da ita"
"Idan kika bita saina saba maki anan gidan" rabu
da ita" duk inda xataje tayi ta tafiya"
Hajiya binta ta fara kuka tace-:
"Alhaji kasan halin xabba'u yanxu idan taje ta cewa
baba mun koreta" ban san halin da xai shiga ba"
nayi masa alkawarin xan rike xabba'u xanyi mata
abinda take so daga nan har karshen rayuwarta"
.
.
Alhaji sunusi yace-
"to ba.a nan gidan ba" daga yau babu ni babu
waccan yarinyar" (MUN DAUKO WA KANMU
KADDARA DA MASIFA)"
Xabba'u ta tafi gidansu da akwatin kayanta" xata
fadawa babansu malam Aßußakar an korata daga
gidan" wata sabuwar rigimar xata taso kenan!
.
.
======>+++++¤+++++<=======
.
.
A bangaren danladi saurayin da Asma'u suka sa
yaje yayiwa fatima kaxapi a gaban mujahid kuwa
sau biyu yana xuwa wajen Atine amma babu labari
mai dadi"
xuwansa na farko da yayi" bayan ya kammala yiwa
Asma'un aikin da ta sashi" kuma bayan ta tabbatar
masa cewa tayi magana da Atine babu matsala" da
ya aika gidansu Atine cewa a fada mata ana
kiranta" sai ta ce da yaron"
"kaje kace wanene?"
Da yaron ya dawo ya fadawa danladi haka" sai
yace" kaje ka fada mata" Danladinta ne" tayi sauri
ina jiranta"
yaron ya koma cikin gidan" da ya fitocsai yace da
Danladi"
"wai tace kanta yana ciwo" ka tafi"
Danladi ya ciji yatsa" ya gaji da tsayuwarsa ya tafi"
.
.
Ya kira Asma'u a waya yace da ita" yaje wajen
atine amma taki fitowa" Asma'u ta bashi hankuri"
"Xan sake xuwa in sameta gobe" kayi hankuri
danladi" xan cika maka alkawarinka" ka koma
xuwa jibi xata fito"
Da jibin tayi ne sai danladi ya koma gidansu Atine"
ya aika yaro yace taxo inji danladi"
Da yaron ya fito ne sai yace dashi"
"wai dani da danladin sai taci ubanmu" idan ban
tafi na bata guri ba"
Danladi ya tambayi yarin cikin kunan rai"
"la tabbata haka ta fada maka" yaro bafa nason
karya"
yaron yace mana!"
.
.
Danladi ya girgixa kai cikin pushi" yake-:
"jeka yaro na gode"
ya ciro wayarsa ya kira Asma'u" data dauka sai
yace da ita cikin baraxana"
"kince in dawo" na sake xuwa yau ma ta
wulakantani" tunda abin naku wulakanci ne" nina
fiku rashin mutunci" kinsan baxaki iya shawo min
kanta ba" amma kika sani aiki naje nayi maki?"
Asma'u ta rude"
"kayi hankuri danladi" naje na sameta" kuma tace
dani ba matsala fa...."
Danladi yace-:
"Ba wani dadin baki da xaki yimun" kawai tunda
abun rashin mutunci ne xanje in bata aikin da nayi
maki" xanje gidansu fatima ince ke kika sani inxo
in mata sharri" kuma xanje in samu wannan
saurayin fatima shima xan fada masa gaskiya" ke
kika turo ni inyi wa fatima sharri"
.
.
Asma'u ta rude" ta fara yiwa Danladi magiya"
"Dan Allah kayi hankuri danladi" ka sake bani
kwana daya" xan shawo maka kan Atine" xata
fahimce ni yanxu idan na koma" kayi hankuri"
Danladi yace-:
"Na baki nan da gobe" idan na sake xuwa gidansu
Atine tayi mani wulakanci" duk abunda kikaji ya
biyo baya" to kece kika jawo"
Ya kashe wayar" a lokacin da Asma:u take yi masa
magiya yayi hankuri" tana kiran sunansa a tsorace"
"Danladi...... (please) Danladi"
.
=======>++++¤++++<========
.
"Xabba'u ta shiga gidansu tana kuka dauke da
akwatin kayanta" matan mahaifinta suka tarbe ta a
tsorace" suna tsammanin mutuwa akayi a gidansu
Hajiya" taxo ta fada musu"
.
.
To amma kuma da suka ganta da akwati a kanta
sai suka fara tsammanin wata.....¤TÛÑ Ä ÐÛÑIÝĤ
.
.
.
ραgє
16
ωιтн
Aßßαη ßαѕмαян
Dαη
мυтαη уσßє
ωнтѕαρρ ριη +2348082035050
.
.
TO amma kuma da suka ganta da akwati a kanta
sai suka fara tsammanin wata matsalar ce dai ta
faru" ba mutuwa akayi ba"
"lafiya' me ya faru?"
Abinda mama Hajara ta fara tambayarta kenan"
kafin xabba'u ta fadi yadda akayi" tuni har
mahaifinta ya fito daga cikin dakinsa rike da carbi
a hannunsa"
"xabba'u" ya kira sunanta"
"me ya faru haka kikaxo kina kuka?" wani ne ya
rasu ko kuwa?"
Xabba'u ta saurara da kukan da takeyi" ta ajiye
akwatinta a baranda inda dakunan matan
mahaifinta biye suke" ta share hawayenta" tace da
mahaifinta malam Aßußakar"
.
.
Alhaji ne ya koreni daga gidan" wai tunda ba
gidanmu bane" in kwashe kayana in bar masa
gidansa" shine kuma ya hauni da duka har yaji
mun rauni"
ta sake fashewa da kuka"
malam Aßußakar ya harxuka" nan take ya fara
kwaratsi a tsakar gidan"
Alhaji sununsin ne yayi maki wannan korar karen"
yace ki taho gida" tunda ba gidan ubanki bane?"
Xabba'u ta gyada kanta"
"eh, shine"
mama Hajara da mama ßalaraba suka fara salatu
suna tafa hannuwansu cikin jimami"
malam Aßußakar yace-:
"Ni Alhaji sunusi xai ciwa mutunci ko?" idan ma
wani laifi kika yi a gidan baxai xo ya sameni ya
fada mun ba" shine ya koreki ko?"
Malam Abubakar yaja dogon numpashi cikin pushi"
.
.
Mama ßalaraba ta tambayi xabba'u-:
"to ita Hajiya binta me tayi a kai?" tana kallonsa ya
koreki bata ci komai ba?"
xabba'u tace-:
"tana kallon sa"
malam Abubakar ya sake tasowa a fusace yace-:
"Ai dole ne suyi haka" ni wanene da baxasu ci
mutuncin 'yata ba" su koreta?" tunda sun ganni
talaka ne" shiyasa sukayi haka ai" to xan gwada
musu iyakarsu su dukansu daga shi Alhaji sunusin
har ita bintan" sai naci mutuncinsu"
.
.
A lokacin ne mama Hajara tasa baki a cikin
maganar tace-:
"A,a malam" a saurara tukunna" sai anyi bincike
bai kamata da mutuncinka ka shiga wannan
maganar ba yanxu" ka saurara tukunna muga
abinda xai biyo baya"
malam Abubakar ya dubi Hajara matarsa yace-:
"Amma dai ai xabba'u ba karamar yarinya bace
wacce xa.ace bata san abinda akayi mata ba" Idan
basu koreta ba" xata kwaso kayanta ne tace sun
koreta" ai ba cewa nayi dama batayi laipi ba" aje
tayi laifin" amma inda abin ya konamun rae" suxo
mana su fada mun suce baba kaji"- kaji" abinda
xabba'u tayi kayi mata fada" mu batahin
maganarmu" ai kunga xan kira ta inja mata kunne
ta daina" to basuyi haka ba" sunce tabar musu
gidansu" su gasu masu gida koh?" ita kuma
marainiya 'yar talaka"
mama ßalaraba ta tambayi xabba'u"
"to laifin me kikayi a gidan har Alhajin ya koreki"
yace ki dawo gida"
.
.
Xabba'u tace-:
"A kan wani saurayina ne mujahid" yace ni yake
so" shine su kuma suke so su hadashi da fatima"
yace kuma baya son fatima" ni yake so" akan haka
ne Alhajin ya kamani da bugu ya koreni"
Malam Abubakar ya girgixa kai cikin takaici"
"watau akan saurayi xai koreki koh?" shi Alhajin da
girmansa da mutuncinsa xai shiga cikin shirginku
na yara" meya hadashi da saka kai cikin wata
maganar saurayi" don yace yana sonki?" a takaice
dai yanxu ya nuna 'yarsa yake so" ke kuma tunda
ba 'yarsa bace shine ya kamaki da bugi?"
mama balaraba tace-:
"Gaskiya idan haka ne malam" Alhaji bai kyauta
ba" kuma baiyi ampani da girmansa ba wajen
yanke wannan hukuncin" aini na xata fatima da
xabba'u duk daya ne a gurinsa" ba wani
bambanci" Ashe abin ba haka yake ba"
.
.
Mama Hajara tace dasu-:
"Duk da haka dai ni bana so a dauki maganar da
xapi malam" don Allah a saurara tukunna a jira sai
hankali ya kwanta" sannan a bincika yadda
maganar take"
malam Abubakar ya dubi xabba'u wacce take share
hawaye"
"shikenan" dauki akwatin ki shiga daki" kuma ki
daena kuka hakan nan" tunda kin dawo gida"
Xabba'u ta dauki akwatin ta shiga dakin mama
ßalaraba" wacce tabita a baya domin sake
lallashinta" dama tasu tafi xuwa daya"
.
====>++++++¤+++++<=====
.
"Da sape ko karyawa Hajiya binta batayi ba ta
shirya ta nufi gidansu hankalinta a tashe" ko
wanka bata tsaya yi ba" ta sa silifas" ta isa
gidansu misalin karpe bakwai" a lokacin da su duk
su mama Hajara suna cikin dakunansu tare da
yara"
Hajiya binta tayi sallama" ta doshi dakin mahaifinta
wanda yake a bude" alamar yana ciki kenan" sa.ar
da take kokarin yin sallama ta shiga dakin ne"
mama ßalaraba" wacce ta fara jin muryarta" ta leko
da kanta tayi mata sannu da xuwa"
.
.
Hajiya binta ta shiga dakin mahaifinta ta same shi
a xaune yayi shiru yana tunani" taji gabanta ya fadi
domin kuwa da ganinsa haka tasan ransa a bace
yake" kuma cikin fushi ya kwana"
"Ya amsa sallamar da tayi a ciki" Hajiya binta ta
durkusa ta gashe shi"
"sannu baba' ina kwana?"
yace a fusace"
"lafiya"
tace dashi-:
"Baba dama naxo ne akan abinda ya faru jiya"
nasan xabba'u taxo da daddare dauke da
kayanta........."
tun kafin takai karshe ya dago kansa yace mata"
"eh ta xo" ko kuwa xataki xuwa ne" tunda kun
koro ta saboda 'yarku?" kuna takamar gida naku
ne" shiyasa kuka nuna mata bambanci a
tsakaninta da 'yarku da kuke so" to ita ma yanxu
ta dawo gidansu"
.
.
HAJIYA ßINTA tayi bakin ciki ya tokare mata
xuciyarta" tunda take mahaifinta bai taba yin fushi
da ita irin haka ba" kuma bata taba ganin fushinsa
a bayyane irin wannan lokaci ba" tace dashi a
tausashe-:
"ßaba wallahi komae yarinyar nan taxo ta fada
maka karya take yi" kai kasan cewar babu yadda
xa.ayi in bambanta fatima da xabba'u"
kuma idan ma har ina nuna bambanci" to nafi
kyautatawa xabba'u fiye da fatima" ita kanta
fatima" tun suna yara" na nuna mata matsayin
xabba'u kanwata ce" don haka fatima tana
giramama ta" kuma ko wani abu ya hada su"
fatima nake ba rashin gaskiya in goyi bayan
xabba'u ba tare da nayi bincike ba" don in rike
amanarta da kyau" kamar yadda nake yi tun tana
jaririya"
.
.
Mahaifinta yace-:
"Ai duk nasan haka" ba sai kin tuna min
dawainiyar da kika yi mata ba" Amma yanxu
abunda ya taso ai magana ce ta saurayi ita
xabba'un tace wani yaro take so" shima yana
sonta" shine ke kuma ke da mijin nakin masu 'ya
kuka ce lallai wannan yaro sai dai yaxo ya nemi
fatima" ba xabba'u ba" akan haka Alhaji sunusi
yahau ta da duka baji ba gani" jiyan nan data
dawo sai da na nemo wani likita nan da yake da
kyamis" ya auna ta ya duba lafiyarta" yana nan ya
rubuto magunguna an sayo" ko duk wannan ma
karyar take yi"
Hajiya ßinta tace da mahaifinta-:
"Haka ne baba" don duka hakika Alhaji ya bugeta"
amma ko shi din ma ba wani duka ne da yakai
yadda xata kwaso kayanta ta dawo gida ba" ba
wanda yace ta dawo" kawai sai dai mukaji fatima
tana cewa ga xabba'u can ta dauki akwatinta ta tafi
tana kuka"
.
.
Malam Abubakar yace-;
"to ai dawowar da tayi tayi daidai" tunda har xai
rika kamata yana duka" aini gara ta dawo gida"
tunda bana kasa riketa bane" dama saboda maraici
yasa tun tana jaririya na baki rikonta" tunda kuma
yanxu kun gaji da xamanta" 'y'yanku kuke so"
shinkenan kowa ya huta" ita ma sai ta xauna a
gida"
Hajiya binta ta roko mahaifinta cikin karaya kamar
xatayi kuka"
"Baba kayi hankuri" maganar nan ta wuce don
Allah" kasa ta dauki kayanta mu koma gida"
Malam Abubakar yace-:
"Xabba'u baxata koma ba" yau da ace da wannan
al'amari ya faru kunxo kun fada min na shiga
maganar" baku dauki mataki da hannunku ba" to
xan iya hakura" Amma tunda kuka yi gada-gadi"
kuka dauki irin wannan matakin" to baxata koma
ba" kuma shi

Please Login or Register in order to submit comment