Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba" tun daxu yana gida saboda ke"
fatima ta dubi Umma cikin rashin fatimta"
Saboda nifa kika ce?Yaya mujahid ne xai xauna a
gida saboda ni Umma?"
Umma tace da ita"
"wallahi fatima ba wasa nake yi maki ba" tun jiya
dana fada masa xaki xo naga alamar yana so ku
hadu" yau tun sape yana gida baije ko"ina ba"
kuma saboda kawai yaji nace xaki xo ne" don har
tambayata yayi baki xo ba" shine nace dashi
xanxo gidanku in gani ko lafiya baki samu xuwa
ba"
.
.
Fatima ta bata ranta tace-:
"xabba'u ta jawo mani wannan matsalar Umma"
tun jiya fa na tambayi Hajiya ta barni" amma
yarinyar nan tayi min bukulu tace da Hajiya wai bai
kamata abar gidan ba kowa ba" sai Hajiya tace in
xauna har su dawo tunda haka ne" bansan meyasa
xabba'u take yi mun erin wannan rashin adalcin
ba"
Umma ta dafa fatima cikin tausayawa"
"kiyi hankuri fatima" nasan rin xaman da kikeyi da
xabba'u" to amma tunda 'yar uwarki ce ta jini babu
yadda xakiyi" kada ki mance ita da Hajiya uwa
daya uba daya suke"
.
.
Fatima tace da Umma cikin fushi"
To amma don tana matsayin kanwar Hajiya sai ta
rika min.........
TUN A DUNIYA"
.
.
.
РÁĞE
06
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE"
.
.
FATIMA tace da Umma cikin pushi-
"to amma don tana matsayin kanwar Hajiya sai ta
rika yimun haka?" na girme tafa" kanwata ce"
amma idan kika ga irin abubuwan da take yimun a
gidan nan ko kare baxae ci ba" saboda kawai tana
takamar Hajiya ta bata dama" tace min in rika
girmama ta saboda kanwarta ce"
Fatima tayi kwafa cikin damuwa" Umma taci gaba
da lallashinta"
"kiyi hankuri fatima" watarana sai labari" xamanku
da ita da wani lokaci ne" kema kinsan haka"
.
.
Fatima tace-:
"Gata da bala"in son maxa" kullum sai an kira ta
waje hira" A dalilin haka yasa Hajiya tace wa baba
ya aurar damu bana a huta" Ina so inci gaba da
karatu amma ta jawo mun"
Umma ta girgixa kai cikin tausayawa" tasann cewa
babu shakka fatima tana cikin damuwa a dalilin
xamanta da xabba'u wacce tafi ta matsayi a
gidansu"
Suna cikin hirrar ne sai xainab tayi sallama ta
shigo dakina ta mikowa fatima (envelope) din"
"Anti ga ambulan din"
Fatima ta amsa" Umma tace da xainab"
"zainab kenan" yau baki je islamiya bane?"
xainab tace-"
"Ai munyi huru" sai makon gobe xamu koma"
.
.
Fatima tace-:
"su ma sunyi hutu" wannan karon duk hutun
makarantu yayi (clashing)" da boko da islamiya"
tace da xainab wacce ke tsaye tana tu musu
murmushi"
Don Allah xainab jeki karashe sharar can" idan kin
gama" ki shiga kicin ki ga idan ruwan nan ya
tapasa" kixo ki fada min"
"to anti"
xainab ta fita tabar fatima da Umma" a lokacin ne
fatima tace da umma-:
"wai ke daxu naji kina fatin wata magana" mu
dawo baya" nifa ban gane abinda kike so ki fadi
mani ba a game da yaya mujahid" ni wacece da
xai tsaya a gida saboda yaji ance xanxo?" abin ya
daure min kai gaskiya........
.
.
Umma tayi murmushi" xuwa can ta nisa tace-:
"Fatima kin san ance ranar wanka ba.a boye cibi"
zan fada maki wata magana wacce abin mamaki
ce" amma ta wani bangare ba abin mamaki ba ce
fatima"
Duk duniyar nan bani da wata aminiya
kwatankwacinki" kamar yadda na tabbatar kema
baki da aminya kwatankwacina" don jaka ina so
xan fada maki wannan maganar" amma idan
kinsan akwai matsala" ina rokon ki don Allah ki fito
ki fada min gaskiya" kada ki boye mun abinda ke
xuciyarki" Ina so mu fara yin wannan maganar mu
biyu" mu kashe mu rufe ba wanda ya sani"
.
.
Fatima ta tambayeta-:
wacce magana ce Umma?" ni fa ban san inda kika
dosa ba" ina sauraron ki ne kawai"
Umma tace-:
"maganar gaskiya fatima baxan boye maki ba"
yaya mujahid sonki yake yi"
Fatima ta dafe kirji a tsorace"
"sO?"
ta tambayi Umma" " kai umma ba gaskiya bane"
me yaya mujahid xaiyi dani?" ai yafi ni aji" ya
xa.ayi yace yana sona?"
Umma ta tattara hankalinta waje guda tace da
fatima"
"Kada kiyi shakkar abinda na fada maki" ina da
hujjoji masu yawa dana dogara dasu kafin in yanke
wannan hukunci"
yaya mujahid yana sonki" ina tsammanin tun ranar
da kuka hadu kwanaki da kika xo gidanmu" ranar
da muka kawo ki gida a mota" yaki fitowa ya fada
maki ne saboda kunyar dake tsakaninku" yana jin
kunyarki sosae" kamar yadda kike jin kunyarsa"
.
.
Fatima tace-:
"shine ke kuma baki da kunya" kika ce bari ke ki
fasa kwai kowa ma yaji"
Umma ta danyi dariya"
"wanna ba maganar wasa bace fatima" tsayawa
xakiyi mu fahimci juna" kin gadai akwai xumunci a
tsakaninmu" wanda bai tsaya kanmu ba" ya shapi
har iyayenmu" ina so ki dada mani gaskiya" kina
jin kina son yaya mujahid" ko kuwa akwai
matsala?"
Ni idan kika fada min" kinga nasan yadda xanyi in
bashi hankuri cikin hikima" in hana shi yaxo
wajenki idan akwai matsala" don kada faruwar
hakan ta jawo mana rudani a tsakanin gidanmu da
gidanku" yanxu babu wanda yasan maganar nan
daga ni sai ke menene ra.ayinki?"
.
.
Fatima ta rike kai cikin kadauwa tace-:
"Umma kinxo da babbar magana" nipa dauka nayi
kamar wasa kike yi" yaya mujahid bashi ya fada
miki da bakinsa cewar yana sona ba" bai kamata
muyi wani abu ba" sai dai mu bari mana sai yaxo
da kansa yace yana sonta tukunna"
"Umma ta dan bata ranta"
"haba fatima" nifa ba yarinya bace" A matsayina
na mace baxan iya gane me namiji yake nufi ba
idan yana son wani abu?"
yaya mujahid bai fito ya sanar da ni baki-da-baki
yana sonki ba" amma na tabbatar da hajan koki
yarda ko kada ki yarda"
.
.
Fatima tayi ajiyar xuciya tace-:
"to amma ba abinda xance sai dai in godewa Allah
idan har hakan ta tabbata" domin kuwa idan har
abinda kika padi gaskiya ne" ni a ganina wannan
abin farin ciki ne a garemu ni da ke"
A sakamakon amintar dake tsakanina dake tun
muna yara" kuma abin farin ciki ne ga iyayenmu"
musamman saboda xumuncin da suke yi" kinga
amintarmu baki daya xata kara habaka kenan" In
dai Allah yasa hakan ta kasance"
Umma tayi murmushin jin dadi tace-:
"Naji dadin wannan bayani naki fatima" kuma dole
inyi maki godiya a sakamakon amincewa da kikayi
kina son dan'uwana kamar yadda na tabbatar
shima yana sonki" na gode" Allah ya karo mana
kaunar juna a amintaka har abada"
.
.
Ta dafa fatima cikin farin ciki" wacce kunya ya
hanta ta sake cewa wani abu"
.
.
SUNA nan xaune a cikin dakin sukaji sallamar
Hajiya da xabba'u sun shigo gidan"
Fatima tace-:
"Kinji su Hajiyar nan ma sun dawo"
Fatima ta tashi domin taje ta yiwa Hajiya sannu da
xuwa" a lokacin ne xabba'u ta shigo cikin dakin a
gajiye"
"sannunku da xuwa"
fatima tace da ita" sannan ta fita xuwa dakin
mahaifiyarta" xabba'u ta dubi Umma da ke xaune a
kan gadonsu"
Umma tayi mata sannu da xuwa" sannan ta tashi
domin ta bata wuri"
"Ya xaki tashi Umma?" kiyi xamanki mana"
Umma tace da ita-:
"Dama gida xan tafi yanxun nan" na dade anan
gashi har yamma tayi"
xabba'u tace-:
"to baxaki jira kawar taki ta dawo kuyi sallama ba?"
Umma tace-:
"Xanje dakin Hajiya ne in same ta" sai anjima
xabba'u
tace a lokacin da ta cire jakarta" ta ajiye akan
gadon"
to sai anjima Umma" ki gaida gida"
Umma ta fita xuwa dakin Hajiya" domin ta gaishe
ta" bata san dalilin da yasa take jin nauyin xama
tare da xabba'u ba idan taxo gidan" babu mamaki
ko tana jin tsoron tane" a dalilin cin mutuncin da
take yiwa kawarta fatima"
.
=====>+++++()+++++++<======
.
Da Umma ta koma gida bata tsaya bata lokaci ba
ta samu mujahid a xaune yana karanta jarida"
amma kuma akwai alamar ransa a bace yake" tayi
masa sallama ta xauna kusa dashi"
Mujahid ya tattara jaridar ya rufe ta ya jepa ta kan
tarin littatafansa" ya dawo da hankalinsa kan
kanwarsa Umma wacce ya tabbatar tunda ta samu
wur ta xauna" to akwai maganar da ke tafe da ita"
.
.
Har kin dawo kenan daga gidansu fatima?"
Umma tace dashi-:
"Na dawo yaya" tace in gaishe ka" Ashe Hajiya ce
suka tafi Unguwa" shiyasa ta tsaya a gida" taji
haushin rashin xuwanta ita ma"
Mujahid yayi ajiyar xuciya yace-:
"Ok" yaci gaba da sauraron Umma" bayan tayi
shiru na wani lokaci sai ta dago kanta tace dashi-:
"Dama ina so ne muyi wata magana yaya" amma
ina fatan baxata bata maka rai ba"
Mujahid yace da ita"
"Ina jinki Umma" ya akayi ne?"
.
.
Umma ta sake yin shiru kamar tana jin tsoron
abinda xata fada masa" xuwa can sai ta ce-:
"yaya akwai wani abu da yake faruwa wanda ka
boye mun" amma kuma daga baya na fahimci ko
menene" duk da yake a matsayina na babban
kanwarka bai kamata ka biye mun ba" banga
laifinka ba idan nayi la.akari da dalilin da yasa ka
boye mun" ka hana kowa yasan halin da kake ciki"
Umma ta saurara" mujahid yayi shiru yana
saurarenta cike da mamakin abinda take fada masa
yanxu" Umma taci gaba da cewa-:
.
.
"yaya mujahid" nasan cewa kana son fatima
kawata" kuma ka boye al"amarin baka fada mata
ba" nima kuma baka fada min ba" ba don komai
ba sai don kada ka samu matsala a wajenta kaxo
kaji kunya" bayan kuma tana ganin girmanka"
wannan ne yasa ka boye sonta a xuciyarka" yana
damunka kullum" ka rasa hanyar da xaka bi ka
sanar da ita ta fahimce ka kuma ta baka goyon
baya"
mujahid yaji lokaci guda jikinsa yayi sanyi" bai
taba tsammanin wannan maganar daga bakin
kanwarsa Umma ba" yaji kunya ya kamashi" don
kuwa dun abinda ta fada gaskiya ne"
.
.
Taci gaba da cewa-:
"A dalilin haka ne yasa ni a madadinka naje na
samu fatima na fada mata abinda ka kasa fada
mata" kuma ta bayar da goyon baya dari bisa dari"
ta amince da soyayyarka" tana sonka fiye da
yadda kake sonta"
Nayi wannan karambanin ne domin in cireka daga
wannan damuwar da kake ciki a matsayinka na
dan'uwana"
Ina fatan ban bata maka rai ba" idan kuma hakan
da nayi ya xama laifi" to ina rokon ka gaparceni"
.
.
Mujahid ya rasa me xaiyi saboda jin dadi"
Abubuwa da yawa sun taru a xuciyarsa a lokaci
daya"
-:yana mamakin yadda Umma tayi wannan
kokarin"
-:kum ya akayi ta gano halin da yake ciki?"
-;sannan kuma yana cike da farin cikin jin cewar
fatima ta amince tana sonshi ita ma"
Fatima tana son shi?" mujahid yaji sanyi a
xuciyarsa" yayi murmushi yace da Umma dake
xaune tana jiransa yayi magana"
.
.
Umma gaskiya ne da ake cewa naka sai naka"
idan bake ba kike 'yar uwata duk duniyar nan babu
wanda xai iya cire ni daga wannan kangin da na
shi" Na gode Umma" Allah shi saka maki da
Alheri"
Umma tayi dariya"
"Ni ma nagode" dakaji dadin abinda nayi maka"
Mujahid yace da ita cikin xumudi"
"yanxu ina son ki fada min abinda kikeso a duniyar
in mallaka maki shi Umma" dole in baki tukuicin
wannan gagarumar kyauta da kika nemo min"
dame xanyi maki tukuici Umma?"
.
.
Tayi dariya sosae a wannan karon"
"ko ma dake kayi mani ina so yaya" kome Allah ya
ciyar dani nagode"
Mujahid yace da ita"
"ki shirya gobe xamu je ki xabi babbar sarka
wacce ranki yake so a (county mall)"
Umma tayi tafi cikin murna"
"thank you my ßrother........
Allah yabar mu tare"
.
======>+++++()+++++<=======
.
ßayan kwana biyu mujahid ya fara xuwa gidan su
fatima" kafin ayi haka dama ya amshi lambar
wayarta a wajen umma" ya kirata ya shaida mata
cewa xaixo gidansu" fatima tace dashi to sai yaxo
cikin kunya da kuma farin ciki"
mujahid yje da karpe takwas na dare ya kirata"
tace tana xuwa" ya fito daga cikin motarsa ya
jingina a jikinta"
.
.
Fatima ta fito bayan minti biyar tana sanye da leshi
da kuma farin gyale" tana kamshin.............TUN A DUNIYA"
.
.
.
РÁĞE
07
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE"
.
.
MUJAHID Yaje karpe takwas na dare ya kira ta"
tace tana xuwa! Ya fito daga cikin motarsa ya
jinjina a jikinta" fatima ta fito bayan minti biyar
tana sanye da leshi da kuma farin gyale" tana
kamshin maya-mayan da ta shapa"
tayi sallama sannan tace dashi" yaxo su matsa
jikin kofar gidansu" saboda inda ya tsaya yayi kan
hanya da yawa! Mujahid yaji dadin fatima da take
da kamun kae" yabi ta suka matsa daf da komar
gidansu"
.
.
Fatima tayi masa sannu da xuwa sannan ta gaishe
shi cikin ladabi"
"ya baka xomin da babbar aminiyata ba?"
mujahid yayi dariya"
"Haka! Ko ke kika ga nayi haka ai kya min fada
kice a korata gida"
"saboda me?"
yace da ita"
"saboda yanxu hirar da xamuyi mu kadai ta shapa
daga ni sai ke" babu muhallin umma a ciki"
Fatima tace dashi-:
"Ni kuma a ganina babu wani abu da xanyi a
rayuwata ince babu muhallin Umma a ciki" ko
menene"
.
.
mujahid yace da ita-:
"baki xo kan abubuwan da dole xaki tsallake ta
daga cikinsu ba ne! Amma yanxu gashi kin para
xuwa kansu" komai shakuwarki da kawarki ai
baxata kai masoyinki ba fatima"
"Masoyi shine-: wanda baki da tamkarsa a duniya"
shine wanda xai san sirrinka fiye da kowa" shine
wanda xaki fadawa maganar da duk duniya babu
wani mahaluki da xaki iya fada wa" don haka
masoyi yafi kawa muhimmanci"
fatima tayi murmushi tace-:
"Ni kuma sai nake ganin kamar kawa tafi masoyi
muhimmanci" saboda kaga masoyi xai canxa ka"
xai iya ganin wata yace yana sonta" xai iya
yaudarar budurwarsa" amma kaga ita kawa indai ta
amana ce" baxata yiwa kawarta haka ba" shiyasa
gasjiya ni ina daukar kawa da muhimmanci a
rayuwata"
kaga ko bata mun rai saurayi yayi" dole kawar nan
dai xan nema in fada mata halin da ake ciki ta
tayani bakin ciki" tabani shawarar abinda ya
kamata in yi"
.
.
Suka dade suna tattake wuri suna jayayya cikin
wasa da dariya kamar sun dade tare" sun saba da
juna cikin kankanin lokaci"
mujahid ya sanar da ita irin son da yake yi mata
ya daukar mata alkawari komai wuya" komai dadi
baxai taba karya mata alkawarin da ya daukar mata
ba"
fatoma tayi masa godiya ta tabbatar masa da nata
cikin farin cikin kasancewarsa masoyinta"
tace dashi-:
"kaine mutum na farko dana fara tsayawa dashi a
rayuwata a matsayin masoyin da nake so da gaske
har cikin xuciyata" ina matukar farin cikin da Allah
ya nuna mani wannan ranar" kuma ina fatan kaine
mijina"
.
.
Suka dade suna hira har xuwa lokacin da fatima ta
fara gajiya saboda bata saba ba" da mujahid ya
fahimci haka sai yace da ita xai tafi" tace ya gaishe
mata da Umma da kuma mama idan yaje"
"suka rabu suna farin ciki da hirar da suka yi" a
karo na farko" a ranar fatima batayi barci ba sai da
ta tabbatar ta hankura da cigaba da karatun da
take so" taji tana son aure fiye da kowacce mace a
duniya" tana matukar son mujahid!"
.
=======>++++()++++<========
.
SAI da safe da fatima taje dakin Hajiya ta gaishe ta
sannan ta tambaye ta"
"Naji an kiraki jiya a waje" wanene?"
fatima ta sunkuyad da kanta kasa cikin kunta ta
ce-:
"yaya mujahid ne....... Yayan Umma
Hajiya binta tace-:
"mujahid kuma?"
Bata yi tsammanin haka al"amarin xai kasance ba
domun kuwa bayan mutuncin dake tsakaninsu da
gidansu mujahid" yanxu kuma ga auratayya xata
sake shiga tsakaninsu" Hajuya bata boye farin
cikinta ba" tace da fatima-:
.
.
"to Alla ya tabbatar mana da alheri" ke kuma indai
kinsan kin amsa masa kina sonshi" to ki tsaya a
kaifi daya" tunda kinga ba wajen da xa.ayi wasa ko
karanta bane" mutanen nan suna da kirki kuma
suna ganin mutuncinmu" na tabbatar shima
mahaifinki xaiyi farin ciki idan yaji haka"
fatima taji dadin yadda ta samu goyon bayan
Hajiya kai tsaye"
.
.
A bangaren gidansy mujahid kuma Umma ta fara
sanar da mama Rakiya halin da ake ciki" sa.ar da
take taimaka mata suna yanka wasu dinkuna da
aka kawo"
Umma tace-:
"mama inyi gulma?"
mama Rakiya tace"
"wace irin gulma kuma?" ke fa baki rabuwa da
soki-burutsu"
Umma tace-:
"Gulmar yaya mujahid"
"me mujahid din yayi da xakiyi gulmarsa?"
Umma tayi murmushi tace-:
"A.a ba laifi yayi ba" abin farin ciki ne mama"
mama Rakiya taci gaba da aikin yanka atamfar da
take yi" ta tambayi Umma ba tare da ta dago kai
ba"
"menene abin farin ciki da yayi?"
Umma ta ce-:
"yana son fatima kuma har yaje gidansu" kuma ita
ma tana sonshi"
mama Rakiya ta dago kanta cikin sauri"
"wacce fatimar?"
"fatima dai kawata da kika sani"
mama rakiya tace-:"
"ke Umma!! Bafa nason karya" kin tabbatar da
haka kodai labari kikaji?"
.
.
Umma tace-:
"wallahi mama ba karua na fadi maki ba"
mama Rakiya tace-;
"Umma ko indai haka ne mujahid yayi tunani mai
kyau" domin kuwa a yadda muka shaku da fatima
da iyayenta idan har wannan al"amari ya tabbata
na tabbata kowa xaiji dadi"
.
.
A ranar mama Rakiya ta samu malam Abdullahi
mahaifin mujahid da maganar" shima da yaji sai
yace-:
"alhamdulillahi" wannan abin alheri ne" domin
kuwa fatima yarinya ce mai ladabi da biyayya tana
girmama mu tamkar mune muka haifeta"
.
.
IDAN mujahid ya auri wannan yarinya" babu
shakka ya samu mata tagari"
mama Rakiya tace-:
"Dama jira nake ka dawo in tambayeka" tunda dai
muda iyayen yarinyar nan mun xamo daya" me xai
hana baxan je in samu hajiya binta ba muyi
magana" domin su tabbatar muna sin a hada
wannan aure na mujahid da fatima"
malam Abdullahi yace-:
"kada ayi gaggawa Rakiya tunda ba dadewa yaran
sukayi da daidaita kansu ba" a bari sai xuwa nan
gaba idan an tabbatar babu matsala" sun gama
fahimtar juna" sai mu shiga cikin maganar musan
abinda ya kamata muyi"
mama Rakiya tace-:
"to duk yadda kace haka xa.ayi malam" sai kuma
mu hada da Addu"a Allah yasa wannan al"amaru
ya xama mai ampani da albarka agare mu!"
"Amin Rakiya"
.
=====>+++++()+++++<=======
.
SHIMA Alhaji mahaifin fatima da Haiya binta ta
sanar dashi mujahid dan wajen mama rakiya yana
xuwa wajen fatima" ya nuna amincewarsa badon
komai ba sai don mutuncin da iyayensu suke
dashi da kuma irin tarbiyar da suka ba 'ya'yansu"
Alhaji sunusi yace da Hajiya binta-:
"yanxu kenan maganar ci gaba da karatunta yasha
ruwa kenan?"
.
.
Hajiya tace-:
"Ni dama ban goyi bayan ta wani ci gaba da karatu
ba" tunda dai ta gama karatunta na sakandire
lafiya" kawai ta fitar mana da miji ayi mata aure"
da ita da xabba'u duka aure ya kamata muyi
musu" bana son su fara tara mana samari a waje
kullum" wasu na xuwa wasu na tafiya"
Alhaji sunusi ya tambayeta"
"ita xabba'un tana da wani tsayayye ne a halin
yanxu ko kuwa?"
Hajiya tace"
"xan tambayeta itama" xance ta fitar da saurayi
kwakkwara guda daya muji ko wanene" in Allah ya
yarda xan tambayeta" muyi magana"
.
=====>++++++()++++++<======
SOYAYYAR mujahid da fatima sai karuwa take yi
kullum" duk bayan kwana glhdu ai yaxo gidansu
sunyi hira da daddare"
fatima ta dauke kafa ta daina xuwa gidansu Umma
saboda tana jin kunyar mama Rakiya"
Umma tana yi mata tsiya sosai a waya"
"wato yanxu yaya mujahid ya kwace mana ke ko
fatima" kin dauke kafa da xuwa gidanmu baki
daya"
fatima takance da ita"
"A,a ba haka bane Umma" kinsan ina jin kunyar
mama" wallahi ina son xuwa amma ina jin kunyar
mama ta ganni" ai sai ace mujahid na biyo ba ke
ba" kin gani?"
.
.
Umma tace-:
"ba wanda xaice haka saboda tun kafin ku fara
soyayya da mujahid shekarunmu nawa tare!" kowa
yasan amintar dake tsakanina dake" kuma a
bangaren mama ba haka take ba" ita ma tana
sonki xo kuyi magana keda ita" kada ki mance
dani dake fa duk daya ne a wajen mama" kamar
'yarta haka take daukar ki"
Fatima tace-
"to xan rika xuwa" kada ki damu aminyata"
Duk abinda akeyi" ita dai xabba'u tana jin ana
fadin mujahid musamman idan yaxo wajen fatima
ta fita suna hira" amma bata taba ganinsa ba"
wanta rana ne da 'yan mutuncin suke kusa suna
daki su biyu da daddare ita da fatima bayan ta
gama hira da mujahid ya tafi ta shigo gida" sai
xabba'u ta tambaye ta"
.
.
wai shi wannan mujahid da naji kuna ta magana a
ina yake?"
Fatima tayi murmushi tace da ita-:
"yayan Umma ne fa.... Umma kawata"
xabba'u tace da ita-:
"Naga alamar kina sonsa da yawa" a ina yake
aiki?"
fatima tace-:
"Aikin banki yake yi" amma bai dade da farawa ba"
xabba'u tace cikin kaduwa"
"banki?" kice yana da kudi dai sosai"
Fatima tace-:
"to ba laifi" yana da rufin asiri daidai gwargwado"
xabba"u tace da ita-:
"shi yasa hat yanxu bani da wani saurayi dana
yiwa alkawarin xan aureshi" saina samu babban
yaro (Ontop) wanda xai kula dani sosae" ya rika
yimun komai nake so a rayuwata"
.
.
Fatima tace da ita-:
"Amma anti xabba"u ai rufin asiri na Allah ne" xaki
iya samun wanda bashi dashi" amma daga baya
idan kunyi auren" sai kiga Allah ya buda mashi"
kuma kina iya auren wanda yake da shi din" daga
baya yaxo ya rasa abin" duk ba yadda Allah baya
yin ikonsa" don haka idan kina son mutum kawai
ki soshi tsakaninki da Allah badon wani abu da
yake dashi ba"
.
.
Xabba'u tace"
"Ai namiji ba.ayi masa wannan tabbacin fatima"
kina iya yin shahadar kin aure shi a talakansa
bashi da komai kuci wuya tare" amma daya samu
kudi maimakon ya maida hankalinsa a kanki" ya
kyautata maki" sai ya fara hangen wata budurwa
kyakkyawa wacce xai aura ya kawo maki" bata sha
wahalar komai ba amma sai yaxo ya fifita ta a
kanki"
shiyasa ni ban yarda da irin wannan kasassabar
ba" nafiso in gani a kasa" Idan ma wani abu ya
faru daga baya" nasan da kudinsa na same shi"
bansha wahala ba balantana kuma raina ya baci"
.
.
Fatima tace-:
"to Allah ya xaba mana maxa nagari" wadanda
xasu rike mu amana" su kula damu" ba wadanda
xasuci amanar mu ba" bayan mun gama shan
wahala tare dasu"
Da wannan suka rufe hirar tasu sukayi barci kamar
abin arxiki" Da safe bayan sun tashi abu na farko
da xabba'u ta fara yi shine sirfa wa fatima xagi
saboda kawai bata gyara shimfidar gadonsu ba"
bayan ta tashi" saida Hajiya taxo ta shiga
tsakaninsu"
.
======>+++++()+++++<=======
A wata dawowa da mujahid yayi ne daga tafiya"
bayan yayi sati daya baya gida" sai yayi wa fatima
waya ya sanar da ita ya dawo"
.
.
Kuma xaixo wajenta a ranar"
me kike so.......TUN A DUNIYA"
.
.
.
РÁĞE
08
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE"
.
.
A Wata dawowa da mujahid yayi ne daga wata
tafiya" bayan yayi sati daya baya gida" sai yayi wa
fatima waya ya sanar da ita ya dawo" kuma xaixo
wajenta a ranar" ya tambayeta"
"me kike so in xo maki dashi-:
ta ce-:
"kaxo mun da hotonka mujahid saboda shi kadai
ne abinda na rasa a dakina"
yaxo mata da babban hotonsa na bango ya bata ta
amsa cikin farin ciki da godiya" yana sanye da
karamar riga" ya jinjina da wata filawa a
makarantarsu yana murmushi" acan baya gine-
ginen ajujuwa ne da kuma dalibai dake giptawa"
.
.
Fatima ta tambayeshi?"
"A makaranta ka dauki wannan hoton ko mujahid?"
ya ce da ita-:
"shekararsa biyu kenan" tun lokacin da nake (300
level) a jami.a baki ganni ba a rame kamar ana
diba na ana miya dani"
fatima tayi dariya"
"to yanxu din fa?"
"Haba kema ai kinsan na canxa nesa ba kusa ba"
ya xaki hadani da lokacin da nake makaranta?"
fatima tace-:
"muma dai ya kamata muje jami.ar nan muji
aninda ake bamu labari"
.
.
Mujahid yace da ita cikin gatse-:
"ke kuwa xakije babbar jami.a" kinsan jami.ar da
ya kamata ki je?"
"sai ka fada"
"A.ß.U. Ya kamata kije"
fatima ta dubeshi cikin shagwaba"
"Aini na gane abinda kake nufi wato" Aure ßautar
Ubangiji ko?" to ba A.ß.U din xanje ba"
ß.U.K xanje ita ma kuma fa?"
"Oh! ß.U.K xaki je" wato ß-bana U-Umma k-
kawata" xasu samu karuwa a gidansu"
Fatima ta tuntsire da dariya kamar xatayi kuka!
"Kai dai wallahi mujahid ba.a kure ka a magana
komai mutum ya fada kasan abinda xaka ce dashi
ka kare kanka"
.
.
Suka rabu cikin farin ciki" fatima ta shaku da
mujahid" ji take kamar ma anyi aurensu" tana
daukarsa kamar mijinta ne! Ba saurayinta ba" tayi
nisa a cikin kogin son mujahid" kuma ta tabbatar
raba ta dashi yanxu aiki ne ja! Da wahala ta sake
jin tana son wani saurayi a duniya tamkar
mujahid"
Ta shiga da hotonsa a cikin dakinsu ta jinjine shi
akan karamin teburinsu da suke kwalliya ita da
xabba'u wanda yake hade da madubi" sannan ta
hau gado ta kwanta" a lokacin xabba'u tayi nisa da
barcinta har tana munshari"
.
=====>++++()+++++<========
.
ßAYAN sun tashi sunyi sallah da asubahi sai
fatima ta koma ta kwanta taci gaba da bacci"
xabba'u ta kwanta kenan sai ta kyalla ido kan
madubin mujahid dake ajiye akan teburin yana
fuskantar ta"
xabba'u ta samu kanta tana kallon kyakkyawar
saurayin dake cikin hoton yana yi mata murmushi"
Tahi xuciyarta ta buga da karpi" ta kurawa hoon
idanu ko kiftawa bata yi" wannan saurayin kuma
wanene?" ta tambayi kanta cikin mamaki" tunda
take a duniya bata taba ganin wani saurayi ko a
sarari" ko a hoto da taji a kallo daya ya bugi
xuciyarta irin wannan saurayin ba"
.
.
Ta bude baki ta taso sanye da kayan bcci" ta
sauko daga kan gadon ta nufi inda hoton yake" ta
durkusa a gaban hoton tasa hannuwanta biyu ta
dauke shi ta kura masa idanu tsawon lokaci"
Tana kallon hoton" tsananin so da kuma radadin
begen shi suna dada shiga xuciyarta"
.
.
Waya shigo da wannan hoton dakinsu?" ta dai
farka ne kamar daga sama" kawai ta dora idanunta
kan hoton saurayin da ta tabbata xuciyarta ta kamu
da ciwon sonshi a kallo daya"
Xabba'u ta mayar da hoton ta ajiyeshu a inda
taganshi" ta koma baya ta xauna dirshan a kasa"
taci gaba da kallonshi"
Ba sai ta tsaya wahalar da kwankwalwarta ba kafin
ta fahimci ko shakka babu fatima ce kawai xata
shigo da wannan hoton cikin dakinsu"
Da ma wannan shine mujahid din da take ji fatima
tana maganar shi kullum?" shine wanda yake aikin
banki?" gashi kyakkyawa mai fara.a gashi kuma
yana da kudi"
"xabba'u ta juya baya ta kalli fatima dake kwance a
gado tana bacci" sannan ta dawo da hankalinta
kan hoton mujahid" taji a ranta duk duniya ba wani
namiji da ya cancanta ya xama mijinta sai wannan
saurayi wanda fatima take so"
.
.
Xabba'u taji tafi fatima son mujahid" duk da yake
yanxu kuwa ta fara ganinshi a hoto" tunda yake
xuwa wajen fatima bata taba fita waje ta ganshi
ba" sai yau da fatima ta shigo da hotonshi cikin
dakinsu"
Xabba'u tace a xuciyarta" wannan saurayin nina fi
dacewa dashi ba fatima ba" kuma niya cancanta ya
aura ba ita ba"
Xabba'u ta sake matsawa ta dauko hoton ta
kankameshi a kirjinta" tana lumshe idanu ta fara
tunani" gaya nan harma sunyi aure sun xama ango
da amarya"
Xabba'u ta ce a sanyaye-:
"Ina sonka mujahid" kuma duk duniya babu mai
rabani da kai" ko da kuwa xan rasa raina ne"
Kuma har cikin xuciyarta haka abin yake"
.
=======>++++(1++++<======
A ranar da xabba'u taga hoton mujahid wuni tayi a
kwance kamar bata da lapia" tana sake-saken
hanyar da xata bi ta kwace shi daga wajen fatima"
ta raba soyayyarsu ya dawo wajenta"
Idan fatima bata dakin" idan ta fita waje" sai
xabba'u ta taso daga kan gado ta xauna ta kurawa
hoton mujahid idanu" Idan kuma taji tafiyar fatima
xata shigo dakin" sai tayi sauri ta koma ta kwanta"
don kada fatima ta gane abinda take sakawa a
xuciyarta"
.
.
GANIN ta wuni a daki ko fitowa waje bata son tayi
sai fatima ta fara kokwanto duk yadda akayi akwai
wani abu da yake damun xabba"u" ta sameta a
daki ta xauna kusa da

Please Login or Register in order to submit comment