Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

goggo ta qara riqo hannunta tana kallonta ta sake maimaita Mimie ki fa'damin kinji.? A hankali kamar nunfashinta na son 'daukewa tace "goggo in ya mutu nima mutuwar zanyi" goggo kamar daqiqiya tace "ban gane ba.? a mainaitawa ta qara yi tana hawaye ba qaqqautawa wani na bin wani, riqota goggon tayi da kyaw tace "waye shi mimie"? Kallon goggo tayi tace "HAYAT" goggo dai bata gane ba tace waye "Hayat"? Mimie ta saki hawaye sosai tace "Mijina" irjin goggo ta ne ya buga tace "mimie hala kin samu baki cikin hankalinki sunan mijinki "Safwan" kallon goggo mimie tayi ta kasa iya qara magana goggo tace 'dazu a ka 'daura muku aure wani zazzafan hawaye ne ya fara biyo kunatunta tana kallon goggo kafin goggo taga ta sulale mata a jiki sumammiya cikin forgiving and goggo ta fara jijjigata ina shiru salati goggo ta saki a ka kuwa jiyo a kazo ana buga qofar da kyar goggo ta bu'de cikin mugun tashin hankali ta ma kasa ta'ba mimie su goggo hanne da su jummai suka riqeta har mota Salman ma da shigowarsa kenan shi ya kwashesu a ka koma asibiti hankalinsa shima a tashe gashi talata zai bar Nigeria kuma lahadi da yamma zai bar kaduna zuwa abuja ya gama sauran hidimomin tafiyar sa haka yake jan mota da arfi cikin mintuna suka iso giwa hospital




Nan a ka qara bawa mimie gado wannan karon ba ta ita ba barin asibiti har sai angama dukkan bincike haka dr yace Nan a ka yanke bilingual goggo zata zauna da ita a asibiti


A kinkinau kowa hankalinsa a tashe baba yana masallaci a na jira ya shigo a sanar da shi Safwan kuwa yafi kowa gificewa saidai iyayensa ke danneshi da haka ya kwantar da hankali mamansa tace kada ya je asibitin ya bari sai zuwa gobe da safe da kyar ya hakura yaso yaje ya ganta yayi missing komai na ta


Sosai a kayi fama da numfashin Hayat kafin ya samu ya dawo normal normal dukda bai farfa'doba mummy kuka take sosai tana dana sanin auren shirya auren Hayat da Farida Noor ma yaji tausayin mummy dukda da suna jin haushinta shi da Iyayensu kallonta yayi ya furta mummy kiyi hakuri and addu'a zamu rika yi masa shiru tayi kawai shima ya wuce yana kiran iyayensu yana sanar da su


A giwa ma hankalin Salman na tashe ganin wai sai Monday lab zasu dawo amma an d'ora mimie kan drip ta samu bacci goggo da Salman duk sunyi tagumi kowannensu da abinda ya ke saqawa zuciyarsa


Mama da ke aiki a tsakar gida maqota 'yen Allah ya sanya alkairi na ta shigowa yanzu ne suka ragu tana 'dan gyara gidan ta jiyo wayar Salman na ta ringing ta kasa kunne tabbas wayarsa ce ya manta gida tun safe gashi yau sai Allab qila ma sai gobe zai shigo gidan domin yace tafiyarsa ranar lahadi ce a hankali ta tura qofar da nufin ta kashe masa wayar ta shiga cikin 'dakin wayar na kan takardar sakin mimie sabida Salman ya tura sauran a envelope sunkuyawa tayi a hankali ta 'dauki wayar zata kashe kira na shigowa ta zata 'daga a tajiyo a na sallama ta fara kallon kofar fita inda kawai ta sunkuya ta ninke takardar da sauri bata kalla ba ta tafi dashi da wayar ta fito ta fara gaisawa da baqin da suka shigo Allah ya sanya alkairi


Sai kusan 11:pm Salman ya bar giwa gida ya nufa direct duk zuciyarsa babu da'di har ya iso mama ta da'de da bacci shima 'dakinsa ya wuce baima wani dogon tunani ba ya nemi guri ya kwanta saidai ya kai 1:pm kafin yayi bacci


A Giwa hospital goggo na ta rarities maganarta da Mimie tanason ta fahimci wani abu ta kasa sai kalma biyu da ke dawo mata "In ya mutu nima mutuwar zanyi in" mijina" waye "Hayat" zabura goggo tayi ta Jawo wayar gefen ta jefa layin Salman na mtn a kashe ta fara duba qaramar tecno 'dinsa da ba kowa ya sanshi da layin ba cikin sa'a taji wayar na ringing Salmn da bai da'de da fara bacci ba wayar na ringing cikin magagi yaji kiran ya fara neman wayar can cikin wadrobe 'dinsa ya ganin wayar sai lokacin ma ya tuna da ba bar wayarsa itama ko kallon wayar baiyi ba ya ansa yasa kunnensa goggo tace ka tashi da kyaw muyi magana to yace yana gyara zamansa " tace ka karanta takardar sakin mimie.? Eh yace na fara na fita amma amma sakin yayi tace ko kasan sunansa.? Yace wa.? Tace shi wanda su kayi auren kudin.? Yace wlh ban sani ba nifa tun da mu ka abada na 'daura na fita zanc.. tace amma Salman ka iya sakarci ta yaya zaka 'daura auren qanwarka da kanka ka manta da sunan mij... Ya katseta na tuna goggo tace yawwa yace "Hayat" irjin goggo ya buga Salman ya qara da cewa kuma a Takarar sakin ma haka ya rubuta sunansa "Hayat" salati goggo ta fara tace Salman yace menene goggo.? Tace Salman asirinmu zai tonu.. cikin tashin hankali yace "a sabida me asirinmu zai tonu bayan gashi har an 'daura auren mimie da Safwan"? Tace Salman ciwon son "Hayat" mimie keyi cikin rashin fahimta yace kamar ban gane ba goggo nan ta bashi labarin yadda su kayi da mimie wato rabuwarsu ce ta saka mimie cikin Wannan ciwon, ajiyar zuciya Salman yayi ya aro jarumta a matsayinsa na namiji yace "goggo to ko tana sonsa ina zata ganshi yana can yana aikinsa Hajiya tacemin yafi 20yrs a can kuma kinsan halin masu ku'dinmu basu ta'ba yadda yaransu su auri yaran talakawa kuma ma ai magana ta qare ita matar Safwan ce yanzu haka dai yayi ta kwantarwa goggo hankali bayan shima ya 'dan shiga ru'dani inda a qarshe su kayi sallama da goggo yayi Shiru


Itama goggo Shiru tayi ta qurawa mimie da ke bacci idanu zuciyarta fal tanbayoyi


A kinkinau ma dai hankalin mutane dangi duk ya karkata kan mimie inda a lot suke ganin dama ba'a maida auren ba har sai ta warke baba kansa ciwon mimie ya fara 'daga masa hankali inda yace a gyara mata 'dakin su Fauza ita ka'dai zata zauna nan har ta warke sosai kafin ta tare


da safe Salman ya qi fa'dawa mama halin da mimie ke ciki baya son qara tayar mata da hankali ita tsammaninta goggo zata zauna ne gidan baba babba har a a gama da jama'a don haka ya mata sallama ya wuce asibiti a can ma goggo sama2 take ya lura ya basar domin baiso suna 'dago abinda ya wuce a gurinsa auren mimie da "Hayat ba wani abin baiwa muhimmanci bane "ikon Allah haka suka da'de da goggo suna fira zuwan Safwan ne ya sasu yin shiru har Safwan kallonta yake kamar ya ha'diye ta kasa fita ta batshi da mimie ya da'de kafin ya miqawa goggo jakar da yazo da ita sannan ya bata 10k yace in tana buqatar wani abu godiya ta masa ya miqe Salman ga bishi suka fita tare suna 'Dane tattaunawa har kowa ya shiga motarsa


Mummy tun lokacin da Hayat jikinsa ya tashi ta bi noor a gigice a she ta yar da wayarta kuma ko ta kan wayar bata qara bi har yanzu..


Sai yanzu Salman ya kunna wayarsa da y shiga mota inda yaga 52 mclls na Mummy mugun firgita yayi a kan mai ya faru ya shiga binta s/off ya shiga wpp rabonta tun last 4dys ya kira laraba tace masa ai Mummy tayi tafiya tun washegarin dawowarta sosai ya shiga fargaba da tulin tanbayoyi a ransa


Lahadi da 7:am Salman yayiwa mama sallama ya wuce tanata masa fatan alkairi domin yace mata bayason danginsu susan da tafiyar sai ya isa zai kira kowa yace ya isa Mama tayi masa Madigan Sosai da ke dama tasan da tafiyar yasha ce mata kwatsam tafiyar zata tashi sabida yanata shirinsa a hankali daga gida ma asibiti ya wuce saidai cikin rashin sa'a mimie ta farka tayi sallah a ka qara maida mata drip ta komai so yayi sallama da goggo a kan sai ya isa za suyi magana domin ma nan da 4mths zaizo hutu IA nan ya mata sallama ya wuce Isa kaita ya nufa ya ajiye mota su kayi sallama da su balaraba da Tara ya wuce 'daukan train zuwa abuja



A na cike falon baba ne Dada matarsa ta biyu tace Malam gobe mu ma bayan yara sun wuce boko za'a saukemu asibiti gaba 'daya sai mu duba jikin mimie tunda suka kwanta goggo hanne ce kawai ta Samuel zuwa sai su Fauza, ajiyar zuciya yayi yace haka ne Allah ya kaimu sai kuje har da su yapendon shanono sabida wai jibi zasu wuce 'to tace a kaci gaba da hira...


Cike suke can special sitting room da suke da shi a Asibitin mummy na can nesa da su wacce a kwana biyu kawai ta gigice duk ta fita kammaninta Abu'Noor yace "Yasmin wai har yanzu matar Hayat batada labarin halin da mijinta ke ciki.? Za tayi magana Abu"Ahlam yace Yasmin yau kwanan hayat uku a asibiti ke uwarsa har kinbar duk abinda ke gabanki kin dawo tayaya matarsa da ya kamata ace itace za tayi haka ace har yau batazo ba..? Za tayi magana still Najwa ta katseta kinga Yasmin wlh wannan yarinyar in tana juyaku ke da Hayat mu ba zamu 'dauka ba sannan yanzu ma hukuncin da muka yanke zamu fa'da miki yadda kika kawota har gidan mijinta to kema bamuson qara ganinki Asibitin nan har sai kuna tare in kuma sun rabu ki fa'da mana sai musan abinyi da wuri sabida mu munada ayyuka dayawa a rayuwarmu dole matarsa ce ya kamata ta kasance dashi a kowani lokaci har ya warke in kuwa sun rabu mu sani domin a yadda yake a kwancen nan zamu masa aure tsaf matar kuma da gudunta zata tare asibitin nan tafara jinyarsa

Yawu mummy ta ha'diya abu Nawwal yace gaskiyar kenan yanzu ki koma abinki ko ku dawo tare yadda kika aurota ko kuma kuma ki fa'da mana ainihin halin da aurensu ke ciki sosai mummy ta fara gumi tana binsu 'daya bayan 'daya da kallo


Tun 7:am a kazo a ka 'diba jinin Mimie da fitsari da komai inda a ka tafi gwaji mimie da farkawarta kenan bayan an gama 'diba goggo ta tilastata shan tea mai kauri wanda tun kan ta gama sha taji yadda gaba 'daya maha'dar jijiyoyin jikinta sun bata wani mummunan garga'di ji tayi komi na jikinta na yanutsewa ta runtse idanu saidai ta kasa magana ta riqe kanta idanunta a rufe su kaji shigowar gayya sosai goggo ta fara musu maraba haka duk a ka zauna a takure a ka fara Hayat da goggo da tanbayar mai jiki ko 5mnts ba suyi ba sai ga Safwan shima haka goggo tace su Fauza su sauka gefen mimie ya zauna kallonta ya ke tunda suka shigo har yanzu bata 'dago kanta ba sauran da goggo sunata fita shi SafwAn yanata kallonta inda ya juya ya kalli goggo yace Dr bai shigo ba har yanzu.? Ya shigo harma sun 'diba jininta da fitsari sunje bashi wai yanzu zasu gama sai a san abunyi a kan zazza'bin ok yace. Bari mu jirashi



Har a abuja Salman naci gaba da neman layin mummy still off dole ya hakura saidai sam zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa in ya tuna yawan kiran da tamasa ko da yayi aiki gidanta 5yrs bata ta'ba masa ko 5mclls ba koda yayi lattin kai yara school ko lattin 'daukosu tabbas abune mai matuqar muhimmanci zai sa tayi masa wannan kiran da haka dai ya share yaci gaba da hidimominsa domin gobe da rana zai tashi zuwa (kuala lampur


Suna zaune duk dr ya shigo ya kalli yada sunkai su 13 yace wannan in kuka da'de a nan zaku qarawa patient 'dina ciwo bayan ta na buqatar hutu sosai ajiyar zuciya Safwan yayi suka gaisa ya ce "ina yayanta"? Goggo jummai ta ce likita ai wannan yayanta ne kuma mijinta" ok yace yana murnushi ya miqawa Safwan hannu tare da furta "Congratulation" dûk suka qurawa dr ido musamman su fauza Safwan yace dr ban gane ba.? Dr yayi murmushi yana dafashi yace "matarka na da shigar ciki ..
💖AQIDARMU💖

Na

Boyayyiyar marubuciya



🅿️15/16



Cikin mugun tashin hankali dukkansu suka miqe dr ya kallesu da mamaki ya ma kasa qara magana yana jiran yaji su mai zasu ce


Goggo kuwa irjinta ya ne ke bugawa kamar zai fashe idanunta duk sun fito waje, Layla ta 'dan matsa gaban Dr ganin Safwan ya bushe galala haka ma sauran iyayensu da ke gurin tsabar tashin hankali ta kalli Dr tace wai dr wa kake nufi tanada ciki.? Kallon yarinyar yayi ya kalli sauran dattijawan gurin da duk idanunsu na kansa yace musu ko ba "Farida ba"? Basu ansaba yace nasan kinyi karatu ga result 'dinta ya miqa mata ya juya ya fita cikin mugun tashin hankali take karantawa ta gama ta juya tana kallon Safwan wanda har yanzu yana bushe kamar gunki duk iyayenma haka suke yayinda goggo kuwa ta fara hawaye sosai


Mimie kuwa itama tunda ya furta (ciki) ta ke sakin hawaye saidai ko ka'dan bata razana ba domin kuwa ji tayi ko me zai faru zata haifi abinta..


Shiru word 'din kusan 25mnts kafin goggo jummai ta kalli Dada tace "Safiya ku muje babu wanda yayi magana har su layla a hankali duk kamar an fiddosu cukin ruwan qanqara suka miqe Fauza ce ta riqo hannun Safwan suka fito babu wanda ke magana à motar gidan baba driver ya tayar yayinda motar Safwan layla ke tuqin suka bar giwa hospital cike da mugun tashin hankali har suka isa kinkinau


Kusan 10mnts da fitarsu har lokacin kan mimie na yadda ya ke goggo da ke ta hawaye ta 'dago tazo har kusa da ita tana kallonta ta 'dago fuskarta saidai yadda taga idanunta sun gama tsumewa da kumburewa ta ma kasa magana kusan 10mnts tana riqe da hannunta kafin ta furta "mimie sadu da ke"? Kuka sosai ta saki tana sunkwi da kanta cinyar goggo, goggo ta shiga shafa mata baya ta da'de kafin goggo ta sake 'dagota tace mimie garin yaya haka ta faru.? Hajiya tace mana ba ma gida 'daya zaku zauna ba.? Kuka mimie keyi kawai.. goggo tace don Allah mimie kiyimin magana musamu mafita kinga yanzu muna cikin tashin hankali " qarfi ya gwada miki"? shiru goggo ta 'dagota tace da qarfi yayi anfani da ke shiru still tana dai ta hawaye..


Duk falon baba suke yanacan da 'dalibai 'yen karatun safe bayan sun gama ya shigo mamaki yayi ganin Safwan yace ba kaje aiki ba.? Saidai yanzu ya kula da duk 'yen gurin yanayinsu kamar anyi rasuwa ya wuce ya zauna yace "ko jikin Farida ne.? Duk shiru an da'de kafin Layla ta fara bashi labarin abinda ya faru cikin mugun tashin hankali ya kalli matansa yace wai haka ne? Suka ce haka ne malam shiru yayi yace ku kirawomin Kaltume nan fauza ta kira Mama da dama ta fita zuwa kasuwa fauza ta gaisheta ta fa'da mata kiran baba tace gatanan yanzu


Maman Safwan kuwa sai hawaye take goggo jummai tace Salman da asma'u ne suka cucemu duk 'yen uwanta na zaria ita suka kaita har bauchi sannan ita asma'u kowa yasan sakacinta ga bata yiwa yara fa'da




Mami uwargidan baba tace wlh kuwa asma'u ta cuce mu nan Mimie da take budurwa samari babu irin wanda basu nemeta ba bata kula su sannan a kayi aurenta da Safwan kowa shaida ne budurwa cif ya same ta Safwan ya share qwalla tabbas wannan shegen karatun da "Goggo da Salman suka matsa ne ya jawowa mimie wannan qaddarar baba zaiyi magana mama ta shigo ganinsu kamar a na makoki jikinta yayi sanyi ta shiga ta zauna ta gaishesu duka tayi mamaki ganin babu wanda ya ansa cikinsu saidai ta share itama ta yi shiru


Baba ne yayi ajiyar zuciya ya fara magana " Kaltume 'yer uwarki tayi mana abinda zuri'armu ba zamu ta'ba mantawa da ita ba ta cucemu ta ha'ince mu yayu mama ta ha'diya idanunta suka fara kawo qwalla saidai tana jiran jin dalilin wannan mugun jafa'in da baba ke yiwa qanwarta baba yace zamu kar'bi qaddara amma daga yanzu babu zuri'armu babu taki 'dagowa mama tayi cikin mugun tashin hankali haka Safwan ma domin shi ya yanke hukuncin zai zauna da mimie zai kar'bi cikinta a matsayin qaddararsu

Baba yace nan asma'u tazo har falon nan tacemin gabanta mimie zata zauna zata kula da mimie kamar su Zulaiha tace qawarta na aiki jami'ar bauchi ita da Salmanu sun samawa mimie gurbi naki amincewa suka takura na bata shara'din riqe amanar mimie amma yau asirinta ya tonu bata riqe amana ba tunda ga mimie da (cikin shege) mummunan bugawa irjin mama yayi ta zabura ta qwalalo Idanu goggo hanne ta kar'ba wlh kaltume Allah ya isa tsakaninmu da Asma'u domin sakacinta ya lalata tarbiyar mimie innalillahi mama ke ta nanatawa


Baba yaci gaba kuma babu ni bab... Safwan ya furta don Allah baba kayi hakuri wlh inason mimie zan Kar'beta da kowani irin qaddararta , baba yace dama aurenku babu fashi saidai cikin dole ta haifeshi domin bazan 'dauki zunubin kisan rai ba kuka mama ta fashe da shi sosai tana riqe kanta wannan wani irin baqin rana ne haka cikin shege mimie.? Kuka take sosai har duk kuma hankali ya dawo kanta inda baba yaci gaba wannan magana ta cikin gida ce ko da wasa na jita waje wanda ya fiddata zai sha mamak... Suka ga mama ta sulale ta suma cikin zafin nama duk su kayi kanta a ka 'debo ruwa saidai inaaa bata motsi sam da mugun zafin nama a ka 'dauketa zuwa motar Safwan su goggon duk suka fito gaba 'dayansu a ka sake 'dunguma mota biyu suka nufi Giwa hospital suna zuwa a ka kar'beta a ka shiga da ita


Goggo ma da ganin mimie ta zama bebiya a dole ta kyaleta cikin mugun tashin hankali ta rasa mai za tayi tsoronta labarin cikin mimie ya iske mama ta fito da nufin taje ta nema layin Salman sai taga dandazonsu da hanzari ta qarasa gurin tana tanbayarsu abinda ke faruwa babu wanda ya kalleta saiga nurse tazo tace kune kuka kawo wancan matar.? Goggo jummai tace eh cikin sanyi murya tace "dr yace a kawo mata asma'u da Farida" goggo ta matsa tace nice wacece muje nurse tace ina farida.? Goggo ta nuna mata word tace ni bari nafara zuwa kije ki taho da ita, kallonsu kawai su Safwan ke yi, goggo duk tana gigice ta nufi word 'din mama da kuka goggo ta isa gaban gadon ta riqo hannun mama da ke numfashi da kyar idanunta fal hawaye ta furta " 'yer uwata ke ka'dai kika ragemin tayaya kika yimin haka"? Hawaye goggo ta share tace wlh yaya ba abinda kuke zarg... Mama ta katseta tun da naga sarqar qugun mimie hankalina ya daina kwanciya zuciya ta ta fa'damin akwai abinda zai faru mara da'di hakan ne yasa na bari a ka mayar da auren mimie da Safwan in ba haka ba na ta'ba fa'da miki na goyin bayan Salman ne lokacin mutuwar auren mimie da Salman sabida nagane mimie batason Safwan sai domin biyayya ta hakura da aurensa wanda a lokacin da ya fara matsa mata da kulle kuma ya hanata cigaban karatu alhalin duk yaran danginsu kowa na karatu na lura mimie ta fake da wannan matsalar ne kawai domin dama ba sonsa ta keyi ba cikin kuka mama taci gaba tunda kuka iso na lura da komai na mimie na hallitar mimie ya qara cika tayi haske mai sheqi ta zama kamar 'yer manyan mutane wanda sosai zuciyata ta shiga zargi hankalina ya kwanta ne bayan 'daurin aurenta' ta fashe da kuka tace asma ta yaya mimie ta yi ciki gidanki hannunki baki sani ba kuka goggo keyi sosai ta fara tari sai ga nurse sun shigo da mimie cikin mugun tashin hankali itama mimie ta qarasa tana riqo hannun mama tana kuka "mama na tari sosai nurse tace bari na kirawo Dr ta fita sai kuka mimie ma keyi tana qanqame hannun mama tana kuka mama ta 'dan kalleta tace mimie kinci amanata da ta marigayin mahaifinki ba'a ta'ba cikin shege zuri'arku ba sai kank...mimie ta 'dago tana kuka ta kalli mama tace "wlh mama ban ta'ba cin amanar tarbiyarku b... Mama ta katseta mimie hankakinki zai kwanta zaki zama ajalina domin da inganki kina naqudar shege gara mutuwa ta kuma wlh bazan ta'ba yaf... Mimie ta saki kuka sosai tana qanqame qafar mama ta furta wlh tallahi mama ba shege bane halal ne ki tanbayi gogg.... Mama ta tashi cikin wani tashin hankalin ta niyar miqewa ga jiri kamar zata fa'di mimie ta riqeta tana kuka goggonma miqewa tayi saidai mama ta fara tari sosai kwantar da ita goggo tayi mimie ta qara zama gefenta tana furta mamana don Allah ki yafemin wlh tallahi cikin aure ne mama ki tanbayi yaya Salman da goggo su suk... Goggo cikin tashin hankali ta matso itama ta riqo 'dayan hannun mama tana hawaye tace "yaya haka ne cikin mimie na aure ne" kallonta mama tayi tace "asma'u kinada hankali ta yaya mimie tayi aure har da ciki.? Sannnan ni ko kawunsu wanda shi ke 'daura musu aure bamu sani ba.? Ajiyar zuciya goggo tayi tana share hawaye tace don Allah yaya ki kwantar da hankalinki na baki labari tun daga farko...



Jin shirun yayi yawa suka tanbayi nurse abinda ke faruwa ta ce musu matar nacan tanata kuka suma wanda na kirasu suna yi da haka sai goggo hanne tace mu qarasa mu ga jikinta mu wuce


Suna tsayuwa qofar goggo ta fara magana suma suka tsaya babu wanda yasan da tsayuwarsu tsakanin goggo mama mimie tsabar tashin hankali goggo ta fara magana..


Bayan mutuwar auren mimie da Safwan da kwana 9 nazo Salmanu ya ke bani labarin yadda yake ta lalla 'ba mimie a kan tayi hakuri ta koma gidanta domin shi abinda yayiwa Safwan bawai don ya lalata aurensu ba ne sai don ya nunawa Safwan rayuwa batada tabbas in yau mune gobe ba mu bane ya kamata ya bar mimie taci gaba da karatunta tunda ma gashi lokacin watansu 8 da aure amma babu rabo yace wata qila ma rabon mai nisa ne ya barta suyi anfani da lokaci ta gama karatunta koda ba za tayi aiki ba tunda ga dayawan qanninsu ma na karatun kuma ma basuyi aure ba yace sam Safwan yaqi amincewa shi kuma bayason fa'da miki kada ki masa fa'da kice ina ruwansa yace ranar da Layla su kaje sallamar mimie Zasu koma makaranta mimie hankalinta ya tafi sosai kan karatu har ta kirashi yace mata shi yayi iya yinsa Safwan yaqi kuma in ya fa'dawa babansu babba bayan Safwan zaibi don haka ki hakura ko ki fara masa da kanki to a ranar ne tayi masa kanta wanda hakan ya jawo musu rigima har ta furta masa cewa itafa dama bata ta'ba sonsa ba saidai kauna ta zumunci wanda hakan ne ya fusata Safwan ya mareta har ta ce masa ita ba mari take so ba saki take so in ya isa shi kuma shai'dan ya zugashi inda ya bata saki a take ya dawo yana nadama tare da fa'dawa iyayensu wai Salman ne ke zugata to nima nayi2 da mimie tayi hakuri tunda Safwan na ta biyota ta koma taqi shi kuma babansu babba shima a lokacin sai yayi fushi da Safwan cewa yayi saki cikin gaggawa don haka bazai mayar masa da mimie ba sai ya qara hankali yasan cewa mata hakuri a keyi da su to da wannan damar ne Salman ya cemin mu nemawa mimie gurbi a gunmu tazo ta zauna sabida yanaso tayi nisa da gida ta mayar da hankali tayi karatu to shine har na fa'da miki a lokacin kikace Allah ya tabbatar da abinda yafi alkairi to munata shirin fara karatun mimie saura kwana

1 Comments On AQIDARMU
avatar
maryam-shaleele

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment