Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hu'du tazo sai Salman ya kirani yace nazo wani muhimmin abu ya faru nazo a lokacin kika tanbayeni nace miki nazo ne mu tafi tare da mimie, to a ranar Salman ya cemin muje ogarsa ce keson yin magana muhimmiya da mu nace to mu kaje


Koda muka isa muka gaisa sai ta kalleni tace tana 'dan qwalla tace taimako take so muyi mata ganin ta da'de da Salman ta yaba sosai da hankali da nutsuwarsa tace akwai yaron yayarta da ke aiki à qasar waje to yanada hannun jari a wani kamfani amma kamfanin na gado ne wanda wai mahaifiyarsa ce ta rubuta ta bada wasiyya cewa kada a bashi nasa 'bangaren sai yayi iyali to shi kuma bayason ma yin aiki a kamfanin ita hajiya da yaron sunada qasar da suke so ya koma to kuma dole ya tattara kan kadarorinsa kafin ya koma can, goggo ta 'danyi shiru kafin taci gaba don haka take so Salman ya taimaka mata da ke tasan mimie tace ya amince a 'daura auren mimie da yaron domin su kai a gani a can qasar idanun mama ne suka fito goggo jummai ta furta innalillahi nan duk a ka juya goggo tayi shiru idanunta suka qara fitowa waje duk ciki suka qara shiga gaba 'dayansu mimie na sunkuye hannun mama tana hawaye Safwan ya kalli goggo yace "goggo muna jinki... Hawaye ta fara sosai taci gaba


Tace tanaso mu bata aron mimie ko na wata uku ne ko hu'du zata kaita kowa ya ganta sannan su 'dan zauna tare à kan duk a yadda cewa eh yaron yanada iyali sosai mu ka tsorata da abin inda hajiya ta kalli Salman tace don Allah ka taimakamin wlh yaron shi ka'dai yayata ta haifa banason komai nasa ya salwanta akwai abinda na ke son tsamoshi daga ciki wanda na rayu a kan wannan burin tun bayan rasuwar iyayensa to kuma burina bazai cika ba sai bayan na tattara masa dukiyarsa ya koma qasar da nake so ya koma nan ta shiga kuka sosai hankalinmu ya tashi tausayinta ya kama mu duk jikinmu yayi sanyi a matssyina na uwa nasan abinda ta keji na kalli Salman nace babu komai IA mun amince, Salati goggo hanne ta fara Safwan yace pls goggo tayi shiru tana qwalla.... Goggo taci gaba to nan ta fa'da mana cewa tare da mimie zasu tafi ma bayan 'daurin auren sannan shi ba tare da su zai zauna ba ma'ana babu alaqar da zata shiga tsakaninsa da mimie hakan ya qara kwantar mana da hankali musamman munsan halin mimie itama ba shashasha bace muka amince inda a washegarin ranar Salman ya shirya 'daurin auren a sheikh jafar can U/doxa kusa da gidansu abokinsa Faisal inda shi da kansa ya kar'bi auren mimie da yaron sosai hajiya da mijinta su kayi taro gun 'daurin auren qwalla Safwan ya share goggo taci gaba, inda a kayi video sosai wanda zasu kai qasar kwana biyu bayan haka ya ranar da muka sallameki a kan zamu wuce bauchi abuja muka je muka raka hajiya da Mimie ta share qwalla tace kuma lokaci zuwa lokaci hajiya na turo mana video mimie sannan muna waya da ita kuma ashe can ma ta saka Mimie makarantar koyon aikin kar'bar haihuwa domin ragewa mimie tunani da zaman gida watan hajiya 'daya da rabi ta dawo ta bar mimie amma ta barsu ne tare da wata tsohuwar goggonsu domin tsare mimie da kuma tabbatar da babu abinda ya faru da ita har wa'adin abinda ya kaita ya cika to dama a kan sai nan da sati 4 zata dawo ma baba da ya ce ta dawo ne yasa mu kayiwa hajiya bayani taje ta 'dauko mimie wannan shine abinda na sani salati duk suka fara magana yi inda Dada ta matsa can kusa da mimie ta riqota suka zo suka zauna ta kalli mimie tace mimie haka ne.? Mimie na hawaye ta girgiza kai Dada tace to ta yaya kika samu ciki idan har bama gida 'daya kuke ba da shi.? Hawaye ta keyi sosai ta sunkwi da kai kallon su dada tayi tace pls duk kuje ku barni nayi magana da ita duk suka fita kowa jikinsa a sanyaye a ka bar mimie da mama da Dada ta kalli mimie tace mimie nasan kinada hankali da nutsuwa inaso ki bani labarin abinda ya rafu bayan isarki qasar..

Shiru kusan 13mnts mimie ta fara magana magana a hankali.. lokacin da muka isa da hajiya daga shi ni sai ita sai wata tsohuwa anyi walima sosai a gidan na zuwana saidai shi ba gidan ya ke ba 1wk da zuwana hajiya ta sakani school wanda motar school 'din ke kaini ya kuma dawo da ni babu wata alaqa tsakanina da shi saidai in zasuyi baqi sai ranar yazo mu har baqin su tafi kafin ya tafi shima haka har hajiya ta dawo Nigeria sai tayi shiru tana hawaye dada ta riqo hannunta tace mimie karki manta da ke da fauza duk 'daya ne a gurina ki fa'damin ta share hawaye tace sai bayan zuwan hajiya idan zeyi baqi yazo to ko sun tafi sai shi baya tafiya ya kwana amma can 'dakinsa wata rana yayi baqi bayan na gaishesu na 'dan zauna naga dare yayi nisa basuda alamar tafiya na barsu naje na kwanta bansan lokacin da suka tafi ba saidai na ta farka sakamakon qishirwa da ya dameni na fito kiching ina 'daukar ruwa sai naji ya riqo ni na fisge jikina da qarfi har ruwan ya zube na zame zan fa'di ya rikoni a jikinsa ya 'daukeni zuwa 'dakinsa ya kullo nayi ta qoqarin kwatar kaina na kasa har yayi abinda zaiyi da ni ta fara hawaye mama na hawayen sai tayi shiru... Dada tace to maiyasa baki fa'dawa hajiya abinda ya faru ba a lokacin.? Shiru mimie tayi dada ta sake cewa to tun daga lokacin babu abinda ya qara faruwa.? Mimie tayi shiru dada tace mimie kince bayan tafiyar Hajiya et kenan yanzu watanni kusan uku kenan ke kuma cikin ki 2wks ne kawai bayan wannan ranar yaci gaba da saduwa da ke ne.? Hawaye ta sauke sosai kafin ta girgiza kai.. dada ta qura mata idanu kafin ta furta kuma kullum yazo da arfi ya ke saduwa da ke..? Shiru babu ansa dada tace mimie kimin magana domin dole mu kar'ban miki hakkinki idan har wannan matar da 'danta sunci zarafinki zamu shigar da su qara kotu ce zata raba mu da su da sauri mimie ta 'dago kanta tana girgiza kai Dada tayi ajiyar zuciya ta gane amma ta furta ban gane ba kenan da yardarki kuka ci gaba da saduwa.? Kuka ta 'dan saki tana kuka girgiza kai.. dada ta kalli mama da ke hawaye sosai itama kafin ta furta to yanzu ya sake ki kine kika dawo har a ka 'daura aurenku da Safwan..? Goggo ce ta shigo ta furta eh ya saketa dada ta kalleta cike da takaici tace a yaushe ya ssketa idan har tanada et cikinsa na wata sati biyu.? Yawu goggo ta ha'diya dada ta furta goggo kunyi son zuciya kun cutar da mutane dayawa naji ya saketa kuka dawo da ita a to yaushe tayi idda har kuka bari a ka 'daura mata aure.? Hawaye goggo tayi mama ma shi take yi dada ta miqe tana kashe wayarta ashe na'dar duk maganarsu tayi ta juya ta fita ranta a mugunw jagule ta samesu kamar masu jiran gawa tace ku muje wannan tashin hankali yafi na 'dazu duk suka 'dunguma mimie kuwa kuka take sosai ta kuma ta rungume qafar mama tana furta "mama don Allah ki yafemin mama kuka ta keyi sosai mimie na ci gaba da roqonta har goggo kamar an shukata su kaji mama na wani irin tari suka koma kanta da sauri suna shiga kuka tana kallon mimie ta furta "na yafe miki Allah yayi miki za'bin alkairi kiyita neman mafita gurin Allah mimie ta share hawaye tace mama na tuba na tuba mama ta riqo hannnun goggo tace asma'u na yafe miki amma ki gyara halinki uwa ta gari ba haka take ba nan ta fara tari da arfi duk suka gigice goggo ta fita kiran dr mimie tace mama bari na kawo miki ruwa ta fita itama kamar zata fa'di word ' dinta taje ta 'dauko faro saidai tana shiga taji goggo na zunduma qara mimie ta yar da bottle 'din hannunta ta qarasa taga nurse na rufewa mama fuska ta saki qara itama ta fa'di sumammiya hankalin goggo ya qara tashi wai ina Salman take furtawa a ranta haka nurse suka tafi da Mimie a ka kirawo Safwan da yanzu suke isa kinkinau ya 'daga a ka sanar da shi mama ta rasu wani irin firgita yayi ya yi parking ya fara fa'dawa sauran hankalin kowa a tashe a ka fara salati wasu suka saki kuka musamman dada da Layla nan suka qarasa shiga gidan suka sanar da baba da shima hankalinsa yayi matuqar tashi inda ya shirya zasu anso gawar Mama


Tunda mummy ta bar asibitin bata ma koma gida ba wajen wata qawarta taje tayi wanka ta bar kayanta ta nemi fly na dare zuwa Nigeria cikin sa'a ta samu inda ta yanke hukuncin direct gidansu Mimie zata wuce kome zai faru dole mimie ta biyota tunda har yanzu "Hayat" mijinta ne


A dole a ka sallami mimie duk su kayi kinkinau can a kayiwa mama sutura a ka a ka kaita gidanta Mae gaskiya mimie tayi kuka kamar ranta zai fita ga Salman a nata kiransa layinsa babu duk girman kaduna an nemeshi babu abokansa kaf anbisu babu labari haka a ka hakura a na jiran jin ta inda zai 'bullo kowa yaga mimie zai tausaya mata ga laulayin yanzu ya ya sakata gaba sannan dada sun hana kowa ya sanarwa baba abinda ya faru ranar rasuwar har sai anyi bakwan mama


Koda mummy ta shigo kaduna direct ta wuce t/wada majors du kace basunan amma taje kinkinau a ka mata kwatance nan a ka fa'da mata mamarsu ce ta rasu ta jajanta kafin ta nufi kinkinau domin mijinta yana germany dama shi ba zama ya keyi ba


Koda mummy ta osseuse kinkinau gidan na cike don haka ta ga wani tace masa tazo ganin baba ne yace mata to yaje ya fa'dawa baba baba yace a kaita falonsa a ka kaita ya 'dan jima kafin ya qarasa bayan sun sun gaisa ta fara magana nazo ne akan maganar "Farida" baba ya kalleta yace daga ina tace ni surukarta ce 'da na take aure" irjin baba ya buga bai gane ba yace wace Farida ko kinyi ,batan hanya tace "mimie" kallonta baba ya shiga yi kamar mahaukaciya sai ga dada na shigowa nan ta kuma ji tayi maganar mummy don haka ta zauna kusa da baba ta kunna wayarta baba na sauraro tun daga maganar goggo har na mimie wani irin mugun b'aci ran baba yayi yace wa dada ta kira masa goggo koda goggo ta iso ta fara kuka baba "yace haka ne duk abinda na ji da kuma wanda wannan matar ta fa'da? Share hawaye goggo tayi tace haka ne amma ya sake ta takardar na hannun Salman hajiya tayi karaf tace 'ya saketa da safe sannan a daren ranar ya sadu da ita wanda kowa yasan duk namijin da ya saki matarsa ya kuma dawo ya sadu da ita ya mayar da auren kenan baba ya kama kansa goggo tace ya saketa Hajiya kuma da hannunki kika bamu takardar baba da Dada cikin 'bacin rai suka kalli goggo suka ce kije ki kawo mana takardar sai a ci gaba da maganar ta miqe ta fito hijabi ta 'dauka ta nufi t/wada rannan Salman yace mata takardar na saman wadrobe 'dinsa....
💖AQIDARMU💖

Na

boyayyiyar marubuciya


🅿️17/18




Tunda ta fita baba yayi shiru wanj irin baqin ciki ya ke ciki mara iyaka mai kenan ya faru ya 'daura aure kan aure.? Ba ma haka ba Salman da goggo sun wulakantashi sunci zarafinsa shin ma yanzu wane mataki zai 'dauka to ma waye wanda suka aurawa mimie 'dagowa yayi cikin yanayin rashin walwala ya kalli Hajiya ya fara magana " yanzu idan irin abinda ya faru da mimie ya faru da da 'diyarki ya zakiji.? Ta yaya zaki yanke hukunci irin haka ba tare da tunani ba a matsayinki na musulma.?




Hawaye ta saki tace nasan nayi kuskure Ta fara basu labarin "Hayat" maraya ne wanda dukiyarsa ke hannun danginsa kuma shi ka,dai yayanta ta bari banason rasashi yanada burin aiki qarqashin kansa Hakan kuma bazai yuwu masa ba sai yanada aure a tsarin danginsa hakan yasa na shirya yi masa aure domin cika masa burinsa na kar'bar gadonsa ta dai fa'da musu yadda ta fa'dawa su goggo da Salman domin ta tabbata yadda mimie ke son Hayat ba zata ta'ba furta musu asalin Hayat da "AQIDARSA" ba baba yayi shiru sam ya rasa Madigan on domin kuwa abinda ya sani tabbas shine ba'a aure kan aure wannan al'amari ya zama babba domin dole sai an yawaita bincike dalla2 domin yanke hukunci na musulunci da haka ya kalli Dada yace kuje ki bata masauki kafin asma'u ta dawo toh Dada tace suka miqe saidai ya qara kiran Dada yace ki tabbatar basu ha'du da mimie ba har asma'u ta dawo "toh" tace suka wuce mummy na ayyana komenene za tayi a wannan karon sai ta maidawa Hayat farin cikin sa


Goggo ta duba 'dakin Salman tass babu 'daddaya tayi da 'dakin saidai babu ta zauna tayi jigum ga zazza' bi itama tanaji sosai a haka ta miqe zata koma kinkinau jin jikinta ya qara 'dan rikice mata ta bu'de 'dakin mama ta shiga ta kwanta saidai baccin ya gagara tanata tariyo rayuwarsu da mama tun suna yara da kuma inta zo suna 'dakin nan ta fara gyara 'dakin can saman Shoglass 'din Mimi da ke 'dakin goggo ta ga takarda ta 'dauka ta fara kokarin bu'dewa tana bu'dewa kuwa ta ga ni cikin hanzari ta mayar da hijabinta ta kullo gidan ta nufi kinkinau


Mummy tayi sallah a ka kawo mata abinci bata ma ci ba bataso kowa yasan tana kaduna sabida da sun gama zasu koma da mimi


Sai bayan Ishaa wajajen 9:pm y'en gaisuwa sun tsagaita baba ya tarasu kaf a falonsa harda mimi kanta na qasa domin bata magana ko ta second da kowa baba ya gabatar musu da mummy inda duk abin kowa ke ganinsa kamar almara inda baba yace inaso duk mu kwantar da hankalin mu zamu bi yadda ya kamata in ta kama har gaban alqali zamu je domin a warware komai cikin adalci da tsarin musulunci yanzu muna jiran asm.... Goggo tayi sallama duk suka bita da kallo ta qarasa ta rusuna gaban baba ta miqa masa takardar ya kar'ba ya miqawa Dada yace ta karanta da arfi kowa ya ji ta fara...


Salaam.. 9:34 am 23/05

Ni Hayat Muthallib Ahnan na saki matata Farida Muhammad saki 'daya.


Baba ya kalli mummy yace kinji , mummy tace wlh ya mayar da ita a ranar a tanbayeta... Duk juyawa su kayi suna kallon mimi da kanta har lokacin ke qasa tanata hawaye a kayi a kayi tayi magana ta qi a qarshe ma kuka ta saki sosai baba yace Dada ki riqeta kuje Dada ta riqeta bayan fitsrsu baba ya kalli mummy yace hajiya kiyi hakuri wannan maganar mu barta nan to ma shi 'dan naki yazo da kansa ayi komai da shi domin wannan al'amarin ba qarami bane yanzu dole sai mun kaishi ma ga manyan malamai su tayamu dubawa domin sannan dole sai 'danki na gurin shi yasan abinda ya faru yazo ya warware mana komai" kuka mummy ta saki ta fara roqon baba tana fa'da masa halin rayuwa da mutuwar da hayat ke ciki baba yayi shiru sai ga Dada da ta shigo ta da'de tsaye mummy na kuka tana wa baba magiya ta qarasa tace malam mimi jikinta ya qara zafi ko na maidata asibiti "yace ki bari zan kirawo likita kije ki zauna da ita kuma kada kibari kowa ya shiga inda take "to tace ta koma duk al'amarin ya fara yi musu yawa daga wannan sai wancan


A haka mummy ta koma masaukinta cike da ru'dani da neman mafita har dare ta kasa bacci sai tunani


Wajajen 1:45 na dare ne Dada najin motsin kukan mimi abin ya mata yawa ga rashin mama ga na yah Salman ga nata matsala kuka ta keyi a hankali mai ban tausayi Dada ta tashi tazo har gefenta ta 'dagota ta zauna ta fara magana "mimi wai bakisan qaddara bane.? Wanne daga cikin qaddararki ke damunki? Mahaifiyarki da wanda ya fiki sonta ya ansa.? Girgiza kai tayi mimi tayi, dada ta kalleta tace mimi inaso ki fa'damin komai a kan abinda matarnan da goggo ke musu à kai kingà mahaifiyarsa tace yayi hatsari yana can rai a hannun Allah 'dagowa mimi tayi tana kallon dada cikin tashin hankalii dada tace wai a ranar da kuka taso yayi hatsarin kuka mimi ta saki tana kama kanta dada ta 'dan qura mata idanu kafin taci gaba kinga babu yadda zamu ganshi bare a ji nasa 'bangaren zahiri à gabanki na karanta takardar sakinki safiyar talata shin da gaske ne kunyi kwanciyar aure a ranar talata da daddare? Sosai mimi ke kuka dada ta riqeta tana kallonta tace mimi ki rage kukan nan kada ciwo ya shige ki" kunyi saduwar aure a ranar da daddare"? Cikin kuka mimi ta girgiza kai shiru dadan tayi tana nazarinta kafin ta 'dago fuskarta tana kallon idanunta furta "Mimi kina sonsa ko"? Kuka ta qara sosai dada tayi Shiru duk jikinta ya mutu tabbas kwai ru'dani sosai cikin lamarin a hankali jawo mimi jikinta tana shafa bayan ta saidai itama yanzu sai taji mimin na bata tausayi domin kuwa tasan baba bazai ta'ba barinta da wani ba bayan Safwan musamman yadda auren na ta da Hayat ya kasance..



Sosai ta ke kuka tanajin yadda take matuqar buqatarsa daidai wannan yanayi da komai ya rikice mata ta dawo bata da kowa mama ta tafi yah Salman ya tafi ta saki wani kuka mai ban tausayi tana qara kwantar da kanta jikin dada shafa bayanta dada ke yi sosai tana rarrashinta har ta 'dan tsagaita da kukan kafin dada ta 'dagota tana kallonta ta furta "amma inaso na tanbaye ki wani abu guda 'daya don Allah mimi ki fa'damin gaskiya kinji.? Girgiza kai mimi tayi dada tace "à wane lokaci kika gane cewa kina son sa.? Shiru mimi tayi dada tace zan taimaka miki ne in kika fa'damin komai.. cikin sarqaqiyar murya tace tun ranar da na fara ganinsa naji zuciyata ta buga .. dada tace to ya mu'amalarku ta fara.? Shiru tayi kafin ta fara magana


A duk lokacin da zaiyi baqi in suka zo ya kance na zauna ne kusa da shi kamar dai da gaske muna rayuwa tare sa'in a gabansu ma har ya kan riqe hannuna ko janyoni jikinsa da dai sauransu... Dada tayi ajiyar zuciya tace to in yanayin hakan ke ya kike ji.? Tayi shiru kafin tace abinda na kanji ne yasa yawanci in yayi baqin na ke tafiya na barsu.... Dada tace ki fa'damin gaskiya da gaske ne da arfi ya fara anfani da ke.? Shiru tayi kafin tace bawai don bana so bane a lokacin sai kawai don ina kiyayewa kaina soyayyarsa da naji ta fara nisa a zuciyata a lokacin.. Dada ta qura mata idanu tace kenan bai tun farkon saduwarku baiyi miki dole ba.? Girgiza kai tayi..! Kallon qofa dada tayi tace mimi yanzu in nace ki za'ba tsakaninsa da Safwan fa.? Shiru tayi dada ma tayi shirun tana kallonta jin shirun yayi yawa dada tace ina sauraronki.. ita mimi tana tunanin ranar da zasu gane waye "Hayat" da kuma asalinsa ranar ne tashin hankali zai faru ta tabbata saidai "ina sonshi fiye da kaina" tana lumshe idanu da hawaye bata sani ba a fili ta furta kalmar "Inajin sonsa fiye da kaina" dada ta ta kashe recorda 'dinta ta dafa mimi tana qara lallashinta ta ce ta kwanta Dada tayi shiru tana ayyana yadda baba ke da taurin kai " tabbas babu wani auren Safwan ko gaban wa zaaje mimi matar "Hayat" ce wannan record 'din kawai ya isa alkali ya bar mimi da mijinta wanda ta ke so da haka itama ta fara bacci



A babban office 'din kamfaninsu Najwa da Abu'noor da Abu'Nahal sai Abu'Ahlam..


Najwa ta kalli yayyunta ta aje qaton laptop 'dinta na Apple a tsakaninsu ta kunna musu video suna kallo... Hayat ya kalli Mutumin yace Mummy tace kaima 'dan Nigeria ne.? Eh mutumin yace yaci gaba sannan shekarata 29 a Ireland kamar yadda ta fa'da maka kuma kamfanin dama ni da abokina ne 'dan Spain ne to babansa ya rasu ya koma qasarsu so kuma as'idar ko yazama na saidawa 'dan qasa ko gomnati ta saya shine mummynka tace zaku saya amma sai kagama shawara ko.? Ajiyar zuciya Hayat yayi yace eh zanyi tunani sosai dukda komai ta yanke ina kai nima dis is abt in dawo nan da rayuwata gaba 'daya so dole na qara tunani kit video ya tsaya .. Abu'noor ya saki huci mai zafi yace tabbas Yasmin rabamu ta ke son yi à fakaice da Hayat sannan shi kansa bata barshi ya gane ba, Abu'ahlam yace sosai kuwa ace duk kamfanoninmu a qasar nan har Hayat ne zaije qasar wasu sayan kamfani sannan ya koma can da zama shiru su kayi suka ji najma ta furta abinda baku sani ba Yasmin ta sayi gida a Ireland 'din duk suka tsurawa Najwa Idanu tace Lima de har yau bata ta'ba zuwa vidange de ba sannan da sunan Hayat ta sayi gidan zaro idanu su kayi duka najwa taci gaba so nagama duk bincike na shiri ta keyi na rabamu da Hayat ta cireshi daga qasarnan wanda kuma hakan na nufin dole mu Tadjikistan de mu fara yaqarta et muma ajiyar zuciya su kayi duk abu Abu'ahlam yace ta yaya.? Tayi ajiyar zuciya su tace inada qawata 'yer Nigeria zan shiga Nigeria yau zan binciko wacece Hayat ke aure kuma 'yer uban waye domin wannan shine ta inda zamu fara yaqi da ita idan har 'yer qananan mutane ce to tabbas Yasmin ta auro masa ita ne domin su ha'da kai su yaqe mu kaga mu sai mu fara yaqar su duk 'yen uwan su kayi na'am da maganar najwa inda tace ita zata bi jirgin dare domin qawarta 'abuja take mummy kuma yasmin kuma a kaduna take na kwashe duk informations 'dinta a Facebook so qawata zata taimakamin da haka su kayi sallama suka watse



Haka mimi ke bacci tsakanin mafarkin Mama da mafarkin hasken ruhinta "Hayat" kewarsa da kaunarsa da tausayin sa ta ke ji mara iyaka a hankali ta miqe taje tayi alwala sam batajin da'din jikinta ga yunwa ta fara jero nafilfili har a ka tada sauna tayiwa iyayenta addu'a sosai sannan tayi wa "Hayat" tana kuka da yi masa fatan warkewa da kuma shiriya ya bar "AQIDARSU" ta gado ya gane gaskiya "sujadda tayi tana kuka tana gayawa Allah ya tausaya mata ya kuma tausayawa abunda ke cikinta ya shirya mata "mijinta" ya dawo "AQIDAR" gaskiya a yanzu batada babban damuwa irin "AQIDAR" sa wannan wani sirri ne da zata yi komai domin ta tabbatar babu wani da ya sani cikin danginta hatta goggo da Yah Salman Dada ta tashi ganin mimi kan dadduma ta wuce itama toilet


Najwa ta sauka Abuja ta kira qawarta Zinat matar wani tsohon ambassador ne Zinat tace zan driver zaizo ya 'dauko ki nima ina kaduna gun naje ta'aziya so zaikai ki airport ki biyo jinrgin kaduna zansa a zo a 'dauke ki ok Najwa tace


Tsohon Ambassador Musharraf 'dalibi ne ga baba tabs kar'ban darasi duk sati sau biyu domin gidansa na Gobarau road U/rimi kaduna su ke wk end da iyalansa hakan yasa su ke zumunci


Koda a driver na kaduna ya 'dauko Najwa a airport ya wuce da ita

1 Comments On AQIDARMU
avatar
maryam-shaleele

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment