Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hajiya zenat ta gama shirin zuwa ta'aziya sosai su ka rungume juna Najwa tayi wanka ta ci abinci ta kintsa ta suka qara duba adress 'din mumny Zenat tace ai ba nisa daga gun ta'ziyar zamu wuce can yaso acan zan samu ko maqota mu kwashi informations 'din da muke buqata a kan surukar tata da haka Suka miqe suka fita Zenat ke driving har kinminau

Mimi na folon Baba da Dada sabida jikinta nan yafi shiru sannan sabida yanzu dayawa na jifanta da mugayen kamai da habaici a wai tayi auren sirri sabida kwa'dayi ko da safe da ta gaida su goggo hanne da jummai banza suka mata haka layla duk dada na kula agissant ta kaita falon baba ganin cikin gidan a cike ya ke


Mummy ma bata fito ba tukuna sabida dare ta kwana sallah sai asuba ta kwanta gajiya ganin batama da wayar kiran Banat taji jikin hayat amma yau komai dare zata bar gidan nan da mimi haka ta ke ta saqawa har ta koma baccin






**************


Koda su Zenat su ka iso

Direct su ka isa cikin gidan sun gaisa da kowa Zenat tayi ta'ziya inda Najwa ta tanbayi Zenat wannan gidan 'yen wace AQIDA ne.? Zenat tace "IZALA" Babban malamin sunna ne tsaki Najwa tayi har mutanen da ke gurin su ka kalleta tace shiasa naga ne da sauri da gida kika barni da zuwa wannan gidan "sosai a ke kallonta à falon taci gaba ke kinsan sarai ko gaisuwa ba nayi da wanda ba 'dan "AQIDARMU" ba rage murya Zenat tayi tace yi hakuri ai yanzu zamu tafi shi malamin zanwa gaisuwa mu wuce.. Zenat ta qara tsaki goggo hanne sai hararta ta keyi inda Dada ta shigo suka gaisa da Zenat tace yace kuje falo yana zuwa toh tace suka miqe


Mimi na falon tana kwance can nesa suka shigo suka zauna cikin bacci taji wani irin anshi da ya fara yamutsa mata hanji taji amai na taso mata 'dan 'dagowa tayi ta hango baqine don haka ta fara qoqarin miqewa ta bar falon kafin tayj amai gaban baqi tana miqewa baba na shigowa Zenat na juyowa Najwa fuska ba annuri ganin na'din kan baba na 'yen sunna tabbas wannan maqiyan "AQIDARMU" ne baba ya hango mimi da jiri ke shirin yar da ita ya furta subhallahi Hajiya yarinyata zata fa'di ku tare ta da ke sun fishi 'dan kusa da mimi Zenat tayi maza ta qarasa tana tare mimi inda ta cesse Najwa tazo su kai mimi cikin gidan a dole Najwa ta qarasa ta tayata saidai irjinta ne ya harba idanunta suka fito ganin mimi ta kalli Zenat ta qara kallon mimi...
💖AQIDARMU💖

Na


Boyayyiyar marubuciya


🅿️19/20




'Dago mimi Najwa tayi da kyaw tana kallonta mimi ma jin masifaffen anshin da ya ke tayar mata da zuciya ta fara qoqarin miqewa tayi nisa da anshin bu'de idanunta tayi a hankali suka kuwa fa'da kan Najwa da itama na ta ke kan mimi cikin rashin walwala


Irjin mimi ne ya buga taji take jirin ya tafi ta zabura tana qoqarin tashi cikin mugun tashin hankali har ta fara ruwan hawaye.. Zenat duk itama ta gigice tanason gane mai ke faruwa ta kalli Najwa tace "kin san ta ne" Najwa ta kalli mimi da gaba 'daya Hankalinta ya gama tashi sai ruwan hawaye ta keyi tace "Matar Hayat ce" zaro idanu Zenat tayi ta kalli Mimi sannan ta juya tana kallon baba da ke qarasowa inda suke ta furta "NAJWA ko dai mai kama da ita ne"? Najwa da idanunta ke kan mimi da ta fara ja da baya cikin mugun tashin hankali tana girgiza kai tana hawaye ba qaqqautawa na sabon tashin hankalin da ya tunkarota baba ya tsaya gurin yana kallon su ya furta me ke faruwa.? Zenat tayi shiru tana kallon Najwa yayinda Najwa ta miqe ta juya tana kallon baba ta furta "Hayat bazai qara cigaba da auren 'yerka ba domin kuwa yanzu da na gano manufarku ku da Yasmin wlh za muyi komai ni da 'yen uwana domin raba auren "Farida da Hayat" irjin baba ne ya buga nan ya juya yana kallon yadda mimi ke ta girgiza kai kamar nahaukaciya kafin ya dawo da kallonsa kan Najwa ya furta "Ban fahimci mai kike nufi ba.? Cikin tsagwaren tsana da qasqanci Najwa ta 'dan qara matsawa gaban baba ta furta "ina magana ne shirin da kukeyi kai da Yasmin domin raba mu da yaron mu har ka bashi 'yerka ba tare da neman danginsa vae wanda kowa yasan dangin uba ke aurar da 'da mace ko namiji amma indai dangin na raye amma sabida sharrin da muguwar manufar da kuke da shi a kan "AQIDARMU" yasa kuka yi auren (Farida da Hayat) baku sanar da mu ba yawu baba ya ha'diya na baqin ciki ya kalli Zenat da itace ya sani ya furta "Zenatu wannan wacece"? Zenat tace baba qawata ce 'yer Iran ce nan ta bashi labarin dangin Zenat da alaqarta da Hayat wani irin jiri baba yaji yana fusgarsa ya kalli mimi da tazama qaramar mahakaciya can nesa da su domin har lokacin girgiza kanta kawai take tana hawaye baba ya fara takawa zuwa inda take tana qara ja da baya har ta kai bango kallonta baba keyi yana wani irin hucin baqin ciki ya keyi yasa hannunsa ya shaqo mimi ya shar'ba mata lafiyayyen mari da numfashinta ya 'dauke ya qara shar'ba mata na biyu numfashinta ya tsaya na second ya wullata qasa ta saki qarar da wasu cikin gidan su kaji mummy ma fitowarta kenan da gudu ita da dada suka nufi falon baba da suka jiyo daga nan qarar ke fitowa irjin mummy ne ya buga ganin Najwa taja ta tsaya itama taji kanta ya wani irin sarawa tana tanbayar kanta "tayaya"? Baba ya juya dada za tayi magana ya dakatar da ita yana kallon mummy cikin mugun 'bacin rai ya furta "'danki 'dan wace AQIDA ne"? Jikin mummy ya fara ya fara ka'duwa baba ya daka mata data irin tsawa ta saki hawaye bakinta na rawa tanason yin magana ta kasa sai rawar tashin hankali jikinta ke yi Najwa ta kalli baba cikin gadara tace "mu 'yen asalin Iran ne iyayanemu da kakanni kuma (AQIDARMU) tun iyaye da kakkani har gobe shine (SHI'A) kasan kanada matsala da 'yen "AQIDARMU" ta yaya ka aurawa 'danmu 'yer ka"? Baba da Dada suka ha'diyi yawun bakin ciki taci gaba au ko kuma dama kwa'dayin tarin dukiyar da mahaifinsa ya bar masa ne bayan wanda kakkaninsa suka bar masa kasan ku 'yen sunna kwaiku da shegen kwa'day..... Baba ya tsinketa da lafiyayyen mari da sai da walkiya ya fito sannan ya kalli Zenat cikin mugun 'bacin rai yace maza ku fitarmin a gida Zenat za tayi magana ya daka mata tsawa itama jikinta na rawa ta jawo hannun Najwa zasu fita Najwa ta fusge ta tsaya ta kalli inda Mimi ke kusan sume ta kalli baba ta kalli Yasmin ta furta "za muyi komai domin ganin bayan wanda duk ya nemi shiga sabgarmu musamman ta zuri'armu har kuma ya nemi cire wani daga cikin Iyalanmu daga "AQIDARMU" tana ganache fa'd'i ta fisge hannunta cikin na Zenat ta fita gidan har da qafa ma take tafiya sai da Zenat ta bita a mota tukuna ta shiga suka bar kinkinau


Dada mummy baba duk suna tsaye tun bayan fitar su Najwa baba ya kalli Mummy ya furta "na baki 30mnts ki barmin gidana sannan kisani ko 'danki ya saki mimi ko bai saketa ba indai ni ne uban mimi a yanzu a wannan duniyar to babu ita babu 'danki har abad... Bai qarasa ba suka ga mimi riqe da qafarsa ta rungume tana kuka duk fuskarta a kumbure kallonta duk suke baba yana motsa qafarsa tana qara rungumewa tana kuma "tausayinta ne ya cika mummy da Dada ta furta "baba don girman Allah kayi hakuri kayimin komai amma karka rabani da shi wlh shine rayuwata" qoqari baba ya qarayi ya janye qafarsa ta ringume gam tana kuka mummy da Dada ma kukan su keyi a hankali ta fara magana "baba nasan nayi laifi nabi tsarin Ya Salman da goggo ba tare da izninku ba kai da Mama, amma don girman Allah baba inason hayat bazan iya rayuwa da kowani namiji ba sai sh... Wani wawan fincika baba tayi mata ya jefa ta gefe ya kalleta yace wlh Farida wannan jika kuma 'dan AQIDAR shi'a ko shine qarshen namiji a zan gwammace na ki mutu babu aure da ki....su kaga ta salale a gurin da sauri zasu qarasa ya daka musu tsawa yace su fita Dada za tayi magana ya furta wlh 'kina furta ko wace irin mamma ce a bakin aurenki.. juyawa tayi ta fita mummy ma za tayi magana "ya furta nace na baki 30mnts ki barmin gidana in ba haka ba hukuma ce zata fitar da ke daga gidan nan" jimm tayi cikin tashin hankali ta fita falon yana inda yake Karin shima fitowar yayi ya kulle qofar falon da key duk 'yen uwansa qanninsa na qofar falon sunji duk abinda ya faru goggo can nesa da su sai hawaye ta keyi ya kalleta yace "anjuma ka'dan kiyi shiri ki bar gidan nan kada na qara ganinki" ya wuce abinsa zauren waje inda duk a ka juya a na kallon goggo asma wasu na jifanta da mugayen alkaba'I wai ta zama annoba a danginsu kanta na qasa tanata hawaye


Mummy ma tayi kuka har ta gaji kafin ta fara tattara kayanta ta gama tas ta fito ta shiga gun dada ta mata godiya sannan ta bata wata recorded tace ta bawa mimi hawaye dada keyi mummy ta fito duk a nata binta da kallo har ta bar gidan napep ta 'dauka zuwa airport zata koma Iran dukda wani masifaffen tsoro da ya shigeta a kan batasan suma yaya zata qare da su ba acan domin zuwa najwa Nigeria na nufin sun fara zarginta sunan Allah ta fara kira a kan ya kawo mata 'dauki har ta iso airport ta bi jirgin abuja a can abuja ma cikin sa'a ta samu flyt 'din Tehran ta shiga zuciyarta cike da saqe2


Salman yayi shiru mai ke faruwa tun jiya da ya sayi sim yanata neman layin mama off na goggo off ga mimi ba waya tunani yayi baiso a san yayi nisa ba sai ya 'dan kwana biyu but yanason sanin halin da gida ke ciki musamman in ya tuna halin da ya bar mimi no ba Safwan ya fara kira saidai wayar na ta ringing Safwan na Office ganin no waje yayi tsammanin ko wani daga cikin abokansa ne ya 'daga Salman yayi sallama safwan ya ansa ya 'dago wayar yana kallon no wannan no na (Malaysia) ne cike da mamaki da tsana da 'bacin rai Saddam ya furta 'dole ka bar qasar tunda burinka ya cika bu qatarka ta biya ka yiwa qanwarka auren samun ku'di to albishirinka mugun kwa'dayinka kai da goggonka yayi ajalin mamanka' irjin Salman ne ya buga yace Safwan maganar me kake yi ne.? Tsaki Safwan yayi ya tsinke call 'din yana hucin baqin ciki labarin da Layla ta bashi 'dazu wai mimi na ta ihu tana roqar baba ya barta ta koma gun mijinta tana mutuwar sonsa , jifa Safwan yayi da wayarsa qirar Samsung s8 ta tarwatse yana fidda huci mai zafi yana tuna tunda ya ke neman mimi har ya aureta har suka rabu ko (kana burgeni bata ta'ba furta masa ba bare ina sonka wai yau baban da kowa ke shakkarsa mimi take roko tana kukan ya barta da wani sabida tsabar son da take masa; huci ya furzar mai zafi tabbas zasu saka qafar wando shi da Mimi domin kuwa bazai ta'ba bari ta ku'buce masa ba


Cikin tashin hankali Salman ke nanata abinda Safwan ya fa'da masa da sauri ya lalubi wayar Dada sanin tafi kowa Sanyin hankali cikin iyaye mata na danginsu tana 'daki zaune har lokacin tausayin mimi ya hanata sake fitowa waje taji wayarta na ringing ta 'daga ko kallon no batayi ba Salman ya mata sallama ta ansa a qagauce kamar dama tana jiran kiran nasa hakan da ya fahimta ne yasa jikinsa ya qara sanyi ya furta "Dada mai ke faruwa"? cikin jimami ta fara bashi labarin komai har izuwa abinda ya faru yau kuka ya keyi tabbas shima yayi danasanin wannan badakala da ya kawo sakamako mara kyaw lallashinsa ta fara yace dada zanyi bucking yau IA zuwa taso hanashi sabida gudun wani sabon tashin hankalin da baba saidai ta tuna mahaifiyarsa ce ta rasu dole ko mai zai faru ya zo sannan ko ba komai qanwarsa zata 'danji sanyi in ta ganshi ganin har goggonta baba ya kora ga danginsu yanzu kowa ya fara tsanarta jin tana Hayat ta ke so ba Safwan ba saidai dada bata fa'dawa Salman wannan 'bangaren ba ganin hankalinsa ya gama tashi da rashin mahaifiyarsa ko bayan sun gama waya da dada sosai yayi kuka ya bu'de system 'dinsa yayi bucking ya shirya kaya ka'dan just 9dys zasu lecture kuma baima gama sauran hidimominsa ba amma yace mama tafi komai domin dama sabida ita na keson yin komai


Koda suka isa U/rimi Najwa taqi magana da Zenat saida Zenat tayi ta lallashi kafin tace 'kenan kinyimin qarya kuma 'yen Aqidar Izala ne.? Zenat tace wlh qawata AQIDARMU 'daya kawai a akwai abinda mu ke son ganowa ne a AQIDARSU kasancewarsa babban malamin AQIDAR anan kaduna shiasa mu ka yanke hukuncin yin binciken gurinsa domin dayawa basusan mu 'yen shi'a bane muna 'boyewa sabida yadda a ke tsanarmu sa AQIDARMU, na tabbata shima surukarku inda yasan ainihin AQIDARMU wlh ko karen gidanmu bazai kula ba, tsaki Najwa tayi tace zancen banza talaka ma kawai AQIDARMU ai itace Aqida kuma ko Hayat zai mutu da son 'yer sa wlh zamu rabasu domin babu wanda zai kawo mana arshen AQIDARMU a zuciyar wani daga cikin iyalanmu domin kuwa in bamu raba Hayat da Farida ba to tabbas ita zata rabamu da shi sabida tunda ya aureta ma ya zama sakarai nan komai ya saki na family ya dena zuwa gurinmu ko yaushe yana gida in ba aiki sannan tana juyashi son ranta ko gaban 'yen uwansa in sunje gidansu sannan kinsan a tsarin danginmu indai 'da namiji ya auro mace a na bawa matar 5%100 daga kason kamfani dayawan yaran matan da ke auren yaranmu ko sabida wannan kwa'dayin suna mana biyayya amma mu kayi mamakin ita Farida tunda a ka aurota ko kamfanin bata ta'ba saka qafarta sannan in contract yazo sauran surukanmu duk da kansu suke zuwa har kamfanin suyi signing amma ita ko mun tura mata documents gida tayi signing sai ta qi ashe tabbas ba shi ya kawo ta ba aiki ne tazo yiwa Yasmin na su raba mu da Hayat ko kuma cikin firgici fa kalli Zenat da tunda Najwa ta fara magana bata ce qala ba cikin mugun tashin hankali da 'bacin rai Najwa ta kalli Zenat tana girgiza kai ta furta na yanzu ma na gano ainihin manufar Yasmin na aurawa Hayat Farida kallonta Zenat keyi domin sarai tasan halin Najwa 'yer bala'i ce " ta furta manufar auren itace cire Hayat daga AQIDARMU ta iyaye da kakanni a zabure ta shiga 'dakin da a ka sauketa ta fito da lapton 'dinta ta shiga video call da 'yen uwanta cikin sa'a duk suna tare dama su haka suke indai ba waninsu bane yayj tafiya zuwa wata qasar to a Iran ko da yaushe suna tare dare kawai ke rabasu kowa ya tafi gun iyalansa nan najwa ta basu labarin komai da ya faru da kuma abinda take zargi a kan mummy inda suka shirya yadda zasu fara 'daukan mataki a kanta


Wani wawan kullewa taji mararta tayi wanda ba komai bane illa yunwa domin bata tuna yaushe ne rabonta da abinci hakan ya sanyata farfa'dowa daga dogon suman da tayi ta fara qoqarin bu'de idanunta da kamar an 'dora mata gum samansu haka taji da kyar ta riqa qoqarin bu'dewa har Allah ya bata nasarar bu'dewa saidai mararta ya riqe kamar wani gingimemen dutse a ka ajiye mata a mararta jan 'duwawu take kamar gurguwa har ta kai main falon baba hango kula da su drinks tayi taci gaba da jan jiki har gurin sam batajin cin komai don haka ko kallon kular ba tayi ba ta jawo gorar ruwa ta fara sha saida ta shanye tas ta ajiye gorar tana mayar da numfashi a kamar irjinta zai 'balle


Salman na jirgi ya nufo Nigeria saidaj duk duniya ta gama fita a ransa yanata tunano iyayensa yau su duka na rasa su ya furta yana sharar qwalla


Mummy ta sauka Tehran direct "Thariq Ahnan memorial Hospital" ta nufa saidai ga mamakinta tun daga Bakin gate securities ne maqil irin kuma securities 'din nan na manyan sojoji da manyan attajirai da manyan 'yen securities 'din sunkai 'dari suka tare ta za tayi magana suka nuna mata jikin bangon shiga main hospital 'din inda ta fara karantawa kamar haka "Daga yanzu babu mai shiga an tsayar da 'daukan marasa lafiya har sai bayan babban jikan na "Thariq Ahann" ya farfa'do kuma babu mai shiga sai yaran Thariq Ahnan guda biyar " yawu mummy ta ha'diya har ta fara hawaye tab 'din wani security ya fara ringing ya 'daga video call 'din ya fara magana kafin ya juyawa Mummy wayar tana kallo gaba 'dayansu kawunan Hayat ne Abu'Ahlam ya kalleta yace Yasmin damar ki ta kasancewa cikin rayuwar Hayat ta qare mun baki dama dayawa kika ha'incemu don haka zuwa yanzu mun yanke duk wata alaqa tsakaninki da Hayat kuma in maganar matarsa ne mun raba auren shima kuma zamuje mu ga babanta munji tanada ciki kuma lingo kowa sanin yadda mu ke kaunarmu jininmu a duk inda Allah ya qaddari fitowarsa kuma wlh kika je kuka fitar da cikin domin gudun kada ya tashi cikin cikin AQIDARMU da itace gadonsa wlh tallahi daga ke har uban nata sai mun tabbatar kunyi dana sanin zuwanku duniya mummy ta ha'diyi yawu call 'din ya tsinke tana sakin hawaye cikin mugun tashin hankali.....
💖AQIDARMU💖

Na

Boyayyiyar marubuciya



🅿️21/22



Durqusawa mummy tayi ta fara roqar security 'din wai ya kira Abu'ahalm za tayi masa magana saidai kamar baya gurin inda a qarshe ya ce mata in bata bar gurin ba zai saka yaransa su wulaqantata cikin tashin hankali da kuka ta tashi tana tafiya ta kuka tana juyawa har ta Fito taxi ta 'dauka direct "medical institute Iran" tana shiga direct office 'din Banat ta wuce yana ciki ta shiga tana sakin kuka tare da furta (banat ka taimakeni hayat 'dana ne yaya ta bani shi tun tanada rai" banat ya taso daga kujerarsa yana riqeta ya furta mummy pls ki zauna ya zaunar da ita ya 'diba mata ruwa da kansa ya bata ka'dan ta sha ta ture tana kallonsa ta fara magana " Banat kana sane tun kuna yara iyayen Hayat na raye amma gurina yafi zama girgiza kai banat yayi za taci gaba da magana ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru tana hawaye sakamakon tunawa da tayi kwai kyakykyawar zumunci tsakanin zuri'arsu Banat da ta su Hayat wanda hakan yasa 'yen gidansu Banat biyu na auren cousins 'din Hayat yayinda maman Ahlam itama goggo ce a gurin Banat duk kuma duk AQIDARSU 'daya tun kakanni don shiasa duk amincin Hayat da Banat bata ta'ba bari Banat ya gane tana son Hayat ya bar Iran ba domin tasan hatsarin yin hakan jin tayi shiru shima ya sauya maganarsa zuwa cewa "mummy ciwo da sauqi duk yana gurin Allah Hayat zai iya warkewa a kowani lokaci pls ki kwantar da hankalinki , ajiyar zuciya tace bari naje gida na huta zan bi jirgin safe gobe ta miqe tana share hawayenta ta kalli Banat da shima ita ya ke kallo ta fara magana cikin yanayin da dole mutum yaji sai ya tausaya mata tace 'Pls Banat inaso domin Allah da amincin da ke tsakaninka da Hayat kayimin alfarmar turamin video 'din situation 'dinsa a kullum da safe da kuma yammA zan iya amincewa da kai.? Cikin mugun tausayawa yace Mummy IA na miki alkawari (Tnx) tace tana share hawaye ta fita ta hau taxi ta nufi gida zuciyarta kamar zata fito sabida damuwa tana shiga falon ta fara tariyo ranar da ta kawo mimi Hayat ya qura mata idanu har sai da ta dungure masa kai yayi dariya yana ra'da mata (Mummy a ina kika samo wannan cute babyn.)? Kallon mimi tayi ta kalleshi tace (ba ruwanka da ita tana ja masa kunne yace to mummy yayi dariya yana kwantar da kansa kafa'darta zama tayi kujerar tana hawaye sosai tabbas burinta na shekara da shekaru ya rushe burinta mafi tsada da daraja cikin duka burukanta na duniya ya rushe garin yaya.? Sosai mummy ke hawaye tare da qara jadaddawa kanta bazata karaya ba zata koma Nigeria ta qara tunani da neman mafita sannan dole na ta rigasu kar'be abinda duk mimi ta haifa ko mai ze faru bazata bari su kwace jaririn ko jaririyar ba da haka taje tayi wanka ta mayar da sallolinta ta 'dan nemi abinci taci ta Sara shirya kayanta..


Babu irin roqon da Mami ba tayiwa baba ba ya bu'de mimi yaqi tace ko don abinda ke cikinta wanda bashida laifin komai baba yace wannan ma shine babbar matsakarta a yanzu zata haifi jinin shi'a.. goggo hanne ta ansa ai kuwa wlh yaya gara ma shegen cikin ya fita ko zamu tsira da mutuncinmu wannan jagwalgwalo yayi yawa in maganar nan ta fita waje mai zamu cewa duniya ana kallonmu a matsayin babban gida wanda a ke koyi da tarbjyar yaranmu yau a ce 'yermu ta auri 'dan shi'a har tana suma sabida jarabar sonsa wlh in mimi zata mutu bazamu barta ta koma hannun 'yen wannan aqidar ba baba kam tashi ma yayi ya tafi abinsa 'bangarensa har lokacin yabajin kamar yaje ya shaqe mimi ta mutu su huta


Dab asuba ne zazza'bi mai masifar qarfi ya dirar mata tun tana kukan 'dauki har hawayenta ya qafe hakoranta duk sun cije kanta na wani irin sarawa ta idanunta suka fara haurawa sama numfashinta yayi qasa har shiru...


Dada dai bacci rabi da rabi tayi duk hankalinta na kan mimi...


5:23am jirginsu Salman ya sauka abuja bai ko 'bata lokaci ba ya 'dauki shatar mota har kinkinau


Yana sauka qofar gidan baba na shiga baba bai ganshi ba ya tsaya yana sallamar mai mota baba kuma dab zai shiga gida Fauza ta tsuguna gabansa tana kuka ta furta don Allah baba ka taimaka ka fito da Mimi ko wanka tayi yayi kamar zai wuce ta sake furta baba ko zaka qara maidata don Allah ka bari ta fito tayi ko da wanka ajiyar zuciya yayi ya furta minti goma ta gama komai ta dawo fauza tace eh baba ya fara bu'de qofar ya bu'de suka yana tsaye ta shiga saidai yaji ta saki mugun qara da duk gidan a ka fito shima baba ya 'dan razana da yanayin da tayi qarar a daidai lokacin Salman ya shigo shima ganin iyayensu na rububin shiga falon baba kuma ga baba a tsaye sai shima ya kutsa kai,,, numfashinsa ne shima ya tsaya ganin mimi a sandare babu alamar rai a tare da ita kuka fauza ke yi Sosai tana jijjigata tana furta mimi ki tashi don Allah... a hankali cikin mugun tashin hankali har jikinsa na rawa Salman ya qarasa yana sunkuyawa gaban kanta ya 'dora hannunsa irjin ta yaji tsit ya saki zafafan hawaye yana sunkuyar da kansa goggo jummai cikin rawar murya tace wai mai kuke jira ku 'dagata muje asibiti mana dada ta kalleta tace bana tunanin hakan na da anfani a yanzu.. goggon cikin gigicewa tace kamar yaya...? Fauza ta qara sakin kuka tace goggo mimi ta mut.. maman Safwan ta fara salati tana furta wai wannan wace irin jarabawa ce baba ma dai a yanzu hankalinsa ya tashi duk yana jinsu

1 Comments On AQIDARMU
avatar
maryam-shaleele

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment