Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shigo cikin ladabi ya gaisheta ya kuma yi mata sallama sai ta ce-mishi ka bar Badi'atu anan in ta haihu ta yi wanka sai a kawota ya ce to ya fita har na dan ji dadi don kuwa ni kadai na san abinda nake ji sai ga Naff'u da sauri shima shirin tafiya yake yi ya zo ya zauna cikin ladabı ya ce Inna wal Badi'atu ta fito su tafi in ji Baba babba, ta ce to tashi ku je, na tashi na yi mata sallama ko wurin Antina ban shiga ba, a kofar gida bab babba yana tsaye ya sha manyan kaya tamkar wani mai mulki saboda kwarjini shi kuwa Muktar yana jikin motarshi ku je gida Badt'atu Allah ya kaiku lafiya, na cc amin na je na shiga mota na zauna na ji Muktar yana cewa buba Babba idan abokina ya kawo matarshi yimu uku sallama a hadosu da goggo Uwale su zo, ya ce to In Allah ya yarda zasu zo, wata inin tafiya mai matukar wahala na yi sai dai cikin yardar Ubangiji mun isa lafiya mun isa kuwa kayan haihuwa kawai Muktar ya dauka ya nufi asibiti dani mun yi sa'a Dr Lami tana nan ita ta karbeni, ta gama dubani ta cewa Muktar in yana da abin da zai lya tafiya don kuwa ko zan haihu zan kai wajen magariba, na kalli agogon dake dakin naga lokaci a zuciyata na ce wato kusan awa takwas kenan daga yanzu lallai kuwa za a taba jifa-jifa Muktar kan dawo ya dubani na rinka ganin awa takwas din nan da likita ta diba tamkar ba za su taba zuwa ba saboda wahalar da nake ciki sannu a hankali sai gashi sun cika ban halhuwa ba suka fara wucewa azaba ta gallabeni na shiga wani hali na gajiyar da azabar da nake ciki na rasa inda zan tsoma rayuwata in ji dadi, tun bayan sallar isha'i nake tare da Muktar a dakin haihuwa har wajen hudun asuba na kalieshi lokacın da yake ta aikin goge min gumi na ce Muktar a kira min Antina kawai ina ganin mutuwa zan yi cikin sauri ya ce stop it Badi' atu ya kankameni yana min magana a kunne yana kara karfala min gwiwa kar ki ji tsoro kar ki karaya haka iyayenmu suka wahala kafin suka haifemu shi yasa ya zama tilas mu yi musu biyayya muryata tana rawa na cc Muktar zan mutu ya kara kankamcni daina Badi'atu daina fadin haka ba zaki mutu ki barni ba na riko Ubangiji in har zan rayu to ya rayani tare da ke ne ki yi hakuri ki yi hakuri kin ji? Yi nishi Badi'atu umarnin da likita ta bani kenan Muktar yana rike dani don kara min karfi yana min magana daure ki yi nishi Badi'atu ko ma samu Allah ya taimakemu ki huta da wannan wahalar da iya karfina na kc nishin na ji tahowar wani abu na ji tamkar kokarin rabani biyu yake yi jikina sai bari yake y na kidine saboda azabar da nake ciki na saki komai na koma kiran Ubangji ina cewa "Hasbuneliahu wa ni'imal wakil a haka na haihuwa, Muktar yana gopge mii gimı da gcien rigarshi yana fadin Alhamdu lillahi kin haifi daya saura daya, duba mana ka gani Muktar ko Shine mai hannu ukun abinda na fara gaya mishi kenan da sauri ya nufi gun likita wacce ka gwade nauyin jaririn ya karbeshi ya zo dashi wurina hannu biyunc dashi' Badiatu kin ganshi? Dogone Sambalcle kyakkyawa kaleshi ki gaya min dawa kika ga ya yi Kama? Duk da ban gama wartsakewa ba sai da na yi murmushi ya Bama tofeshi da addu'o'i ya mikawa nurse din da tazo karbarshi, su Hari da Goggo Uwale suka aiko min da gaisuwa na ee ina amsawa a gajiye kwarai na haifi daya yaron don kuwa shima na wabala kafin in haifeshi cikin matsananciyar murna Muktar ya shaida min shima hannu biyu ne dashi Badi' atu kin ganshi komai nashi irin na dan uwanshi ne har nauyinsu, sa mnusu shaida don mu ganc na farko da na biyu ya umarci nurse din likita ta ciro min mahaifa ta kuma shi latsa cikina a kokarın da taek yi na gano hannun da suka ce sun gani, mawa kadan sai ta cewWa Muktar akwai sauran da acikin an na in numfashi flasbunallahu wani imal wakil, in ji Muktar ni kam kidimewa na yi na shiga halin targaba saboda tsoron wahalar da zan sake shiga shi kuwa yana ta gaya min kalmomin karfafa gwiwa ciwo ya taso na ji tamkar ya zarce duk wanda na yi a baya tunda yanzu kam jina ya yi tsami duk idna aka taba min sai in ji tamkar famani akayi na rasa inda zan sa kaina Hafsa ma'aunin likita kin yarda na yi a dora min shi a cikin rarrashina Muktar yake yi yana bani hakuri yi nishi Badi'atu in ji Likita ta fadi hakan ya fi sau ashirin shima Muktar ya yi iyakar taimakonshi na kasa, Badi'atu zaki kashe yaron fa gashi ya sauko ki yi nishi ta fito mana Dr. Lami take gaya min a firgice, hankalın Muktar ya kai matuka wajen tashi ya yi duk abinda zai yi na kasa nishı ji yake. yi tamkar shi ya yi min nishin babu hałi, yana rike dani sai bari jikinshi yake yi yi kokari Badi'atu a hankali na dago idona na kalleshi da kyar na iya buda bakina na cc mishi ka yi hakuri Muktar karfina ya kare ji nake tamkar numlashina zai tsaya ka yale min laifutfukan da na yi maka na sake lumshe idona saboda jinn dake dibana da gwiwoyinshi biyu ya durkusa a kasa ya kifa fuskarshi akan tawa yana sissika tamkar mai yin kuka yana fadin ya Allah abinda na saui kawai shi ne na ji lokacin da Dr. 1Lami ta ke kokarin tura min injun din da zai taimaka musu Ciro yaron da aka cc ya saura a cikina na dawo cikin nayyacina, na ganni cikin wani dakin na daban Muktar yana zaunce Kan kujera yana rike da hannuna da ake min karın ruwa ta jikinsn Antina kuwa tana tsayC sai faman lyacc majina take yi Innalila Wa inna ilaihir raji'un abinda na fara fada kenan Muktar da An Kamar rigc-rigcn kiran sunana suke yi sannu Badi'atu na kallcshiu a hankali shima ya yi muzai-muzai kamar tare muka yi nakudar na ce Sun Cire yaron ko har yanzu tana cikina? Cikin sauri ya ce sun cire Badi'atu mace muka samu sai dai itama kamar ke ta wahala da yawa dukansu suna dakın renon jarirai wasu hawaye da ban san dalilınsu ba suka gangaro min Antina ta matso kusa dani kar ki yi kuka Badi'atu ki yiwa Allah godiya ya yi miki kyautar da bai yiwa dubban mata ba, 'ya'ya uku kika haifa lokaci daya na zuba mata ido ina kallonta ta sake kusantoni yau ke da Muktar 'ya'yanku uku kuyi farin ciki ku yiwa Allah godiya na ce to Anti kafin yamma asibitin ya cika kwarai da jama'a masu taya mu murnar samun yan uku. Dr Lami ta shigo tana auna jinina bata da wata matsala sai na karfin jiki ina ganin tunda kuna son ta koma gida sai ku tafin kawai, nurse din da kace in samo maka akwai kanwata ta gama karatunta na nursing bata samu aiki ba sai ta zo ta kula maka dasu Muktar ya ce na gode, Dr Allah ya saka da alheri ta yi murmushi ta kalleni to Badi'atu sai na zo gida ganinki da yaran ko? Na ce to Dr mun gode, mun iso gida Antina tana rikc dani saboda rashin karfin jiki su I lari suna rungume da yawan muna isa hanyar da ta raba sashina dana kicin ma hango Nuwaira a ciki tana ta aikin girkin abincin dare tamkar ita ce matar gidan. Anti tana gyara min kwanciya Nuwaira ta shigo tana murmushi na ce amarya ce da aiki haka kace-kace? Ta ce to amarya ta samu 'ya'ya uku ras ina ta ga ta zama, gaba daya aka yi dariya, na cc ke da wa kika zo? Ta yi wani irin lallausan murmushi da nake zaton in a gaban Cali ta yi kila sai ya kusa shidewa, don dadi ta ce ni da ango saukeni ya yi ya shiga kasuwa, wai zai yiwa babin da ya buya musu nata sayayyar me zan kawo miki1? Na ce Nuwaira da masu aiki a gidan nan kar ki wahalar da kanki ta kalleni la ce ni fa mijina ya cc in na zo gidan Muktar in maida gidan tamkar nashi na yi dariya na ce gaskiya ya gaya miki Nuwaira to kafin in ci komai ina so in yi wanka, cikin sauri ta je ta juyc min ruwa, gaba daya hidimar Muktar da abokanshi Nuwaira ta dauke gata itama gwanace kwarai wajen iya girkI gata gwanar karbar baki duk yawansu ta san yanda zata yi dasu ni kam sai binta nakc yi da kallio ina tunanin sakarcinta da Gali yake bani labari da yamma Dr. Lami ta kawo mana nurse yarinya nulsattsiya kyakkyawa da ita ga kunya da girmama mutane nan da nan ta kama aikinta tana maganar yaran suna bukatar hutu a daina yawan daukosu don baki sun zo a rinka akai bakin dakinsu suna ganinsu, da daddare Anti da sauran bakin da zasu'kwana suna dakin baki ni da Nuwaira ne mu biyu tana kallona tana kara gaya min mamakinta kan haihuwar ya'ya uku da na yi, na ji karar waya nasa hannu na dauka na ce hello Gali ne yake magana cikın wata irin murya da ban taba sanin yana da itaba a marairaice ya ce haba Nuwaira ni da ke ta ba yara bane kanana, na yi saurn katseshi da gaya mishi ba Nuwaira ba ce ya cc at mai jego ce? Toya ya karfin ikin naki? Na ce da sauki na mikawa Nuwaira ban san me yake gaya mata ba na dan ji tana cewa aa ba zai yiwu ba, ta sake sauraronshi tsawon lokaci sai kuma ta ce ka gayawa Anti fa ka ce? Ban san abinda ya cc ba sai ta ce to gaya mata mana ai itama ta san dole aka maka ka karbcni balle ko acc in hakura da takurawarka saboda kana sona ta aiyc wayar na kallcta a hankali na ce ina zata zaki br umarnin da ya y miki takalleni ta yi wani lallausan murmushi ta ce na gode maka Alah da ka nuna min karshen tsiyar Gali na bita da kallo na cc Nuwaira in tambayeki mana? 1a sake wani murmushin ta ce tambayeni ni kuma in gaya miki gaskiya, na ce amma ke dai ba tulastaki auren Gali aka yi ba ko? Ta yi wani murmushin tare, da cewa ban gane ba? Na ce ina nufin dama kina sonsh1, ta ce uyh to haka ne ba haka bane na ce ban gane wannan amsar ba, ta ce gaskiya a larkona ban taba kallonshi da wani nufi ba face na yan uUwantakar dake tsakanina dashi, to amma alokacin da na lara girma na tara samarı mutane suka yi ta fitowa suna nuna kaunarsu a gareni na shiga turasu wajen Inna ta gansu su gaisheta sai na lura hakan yana bata mata rai, wata rana na je Zaria gaisheta sai ta ce min ni kuwa Nuwara da zaki yarda ki mun wani alberi da zan ji dadi kwarai na ce na mcnenc Inna? Ta ce bana son ganinki da samari don ni na sha' awar aurenki da wannan yaron tun kina yar jaririya na yi burin hakan wannan shi nc dalilin da ya sma na reneki ba tare da.na shayar dake nonona ba, nan take na ce mata daga yau ba zan sakc yn samari ba, Inna ta ce Allah ba yi miki albarka, tun daga nan ban sake sauraron wani saurayi ba, ba kuma sai na gaya ba kcma kin san tilas zan y1 masoya sai dai kawai in ki bayar da hadin kai, na ce haka ne ta ce to zuciyata ta kamu da son Gali saboda dalila1 da yawa na farko Inna ta ce ta haifeshi a rayuwata kuwa ina ganin babu wani wanda ya fita sona, na rayuwa gabanta ba tare da na san ni din marainiyacc ba, a lokacin da mahaifina ya karbeni daga hannunta na dauka riko aka bayar dani don na sha gudowa in dawo wurinta ya biyoni ya tafi danı ni da ita mu yi ta kuka, sai daga baya na ganc Hunkuri din na da nake zaton riko aka kaini nan ne gidan mu, mahaifiyata kuwa babana ne ya shaida min cewar tun ranar data haifen ta bar duniya na kuma gane yana matukar sonta don kullum zai ambaci sunanta Fatimah, yayi mata addu'a shima yana sona ni ce'yarshi ta fari saboda haka duk da bana jin dadin zama da maatrshi sai na hakura na zauna sai dai akai-akai ina zuwa gun Innata dana samu labarin abinda Gali ya fada a kaina kuwa wai bai sona saboda ni a ruga nake a cewarshi duk da an sanyani a makaranta ba zan yi wayewar da yakc son matarshi ta yi ba bayan haka kuma wai ni shagwababbiya ce shi kuwa bashi da lokacın tarairayar mace yana ririlata, ban yi shiru ba na yiwa Inna magana, na ce to ki zan ci gaba da yin samarınanc? La ce kar in sake kula zancenshi da sannu wata rana zai shiga hannuna in juyashi yanda naga dama sai dail in na tuna dan uwanane in yi mishi sassauci na ce to sai dai duk zaman da muka yi dashi ban yarda ya gane yana da wani mnatsayi a zuciyata ba don ko kallon inda yake bana yi a ranar dana zowa Innata sallama kuwa na koma gidanmu aka sanyani a lalle ita ce ta min hudubar inna je gidanshi kar in yarda tsiyarshi ta yi yawa in yi kokarın kawo karshenta, na ce to don haka ni na yi mishi shigo-shigo ba zurit na kuma yi mishi saki kecece ta yanda ya kasa fita daga dakin, bar san lokacin da na kyalkyale da dariya ba, Jin maganar Nuwaira, ta sake wan murmushi ta ce ai indar za a so hutawa a tare dake na ganin karshen kiyayya kuma uz0 ta sake lumshc ido ta ce ina son Gali Badi'atu dan uwanane jarumine mutum ne me yawan alhere bayan haka kuma yakkyawar halitiar da aka yi mishi wayar Gali ta sake shigowa la amsa ba atre da ta dauki kan wayar ba don haka ina Jinsu Allah Nuwaira ina sonki ni in banda tsiyarkima dana gaya miki wani shirme dana rayu ina yi ban sani ba, ta ce gaya min ai bani da wata tsiya da zan yi ma ba ahannunka nake ba? Ya ce a'a ni ne dai a hannunki da gaske Nuwaira na zamo mai sha'awar zana surorin kyawawan mata don haka a duk lokacin da nake cikin hishadi na kan yi irin wannan zanen sai dai baki sanı ba, a duk lokacin dana takarkare na yi irin wannan zanen ban iya zan akowa sai ke ta ce ga alama dai kai kadai ne a dakin ya ce e, kin san Muktar Jiya ya taya matarshi nakuda ya shige dakinshi ya kwanta ganin haka yasa kowa ya kama gabanshi sai mi kadai, ta ce to gani nan zuwa ta tashi ta shiga wanka tsawon lokaci bata fito ba ya sake waya Nuwaira kina kallon agogo kuwa? Na cc wanka take yi ta fita tana shafa ina kallonta a raina na ce lallai Gali ya mori mace sai da ta gama ta fita sannan Antina ta shigo tana murmushi ta ce ai na gode Allah da ya hada Gali da maganinshi na yi barci sosai kafin Anti ta tashen ta ce llalima tana maganar ki je ki baiwa yaran nan nono na ce to muka fito tare dakin yaran ya yi matukar tsaruwa komai a cikinshi uku-uku ne ga rubutacciyar Ayatul Kursiyua dukkan kusurwowin dakin na kana wata takarda dake reto a tsakiya dakin ga abinda na gani a rubuce:
To Mr. & Mrs Col Muktar Zubair
The joy of this day is like a dream we do very litle to get it but the memories will last a life time, may Allah in his never falling way be ever present you more conmfortable, guide you help you through-out the life of the children may He bless the family more joy more happiness. Congratulations and say welcome to the triplet babies. Brigedier General Kabir Isiyaku & Family Na zauna Halima tana miko min su daya bayan daya ina shayar dasu nono har sai da sukä koshi muna shirin fita sai ga Muktar ya shigo, ganin Antu ya sa ya ja zai koma ta ce a'a shigo abinka ni dama yanzu zan fita, sai da ta ita ya shigo ya kalleni yana munnushi ya ce maman'yan uku na ce kai kumma la Ya ce ni sunana mjin maman yan uku. kina yawan cewa Alhamdulillahi kuwa? Na ce kwarai kuwa.
Washe gari da safe Gali ya nuti SSakkwato ya bar Nuwaira wai ta taya mu aikin jego sal ana gobc suna zai dawo, da daddarc muna kwaace ni da Nuwaira akan gadona ni kam har na lara barci sai na ji waya, Nuwaira ta yi maza ta dauka wata kila ta san mijinta ne na ji tana cewa a kwance nake ina shiria yin barci, sha daya ne fa, yanzu, ta dan yi sauraro kafin na ga ta yi nurmushi sannan ta ce haba yaya Gali auren yan kwanaki kadan shi ne kewata zata dameka? Ta sake yin shiru sannan na ji tana cewa to a yi hakuri na daina cewa yayan, amma wannan sunan da kakeso in kiraka sai a gida don kar aj1 mu ace mun cika zumudi, kwanan yara uku ran nan da sassafe sai ga su baba babba Nafi'u ne ya kawo su shi ne ma ya shigo ya fita musu da yaran Suka gansu daga nan suka yi musu huduba shi Nafi'un ne kuma ya zabi sunayen da za a sanya musu Muktar da abokanshi sun yi hidima ta ban mamaki a Zaria aka rada sunan yaran Umar, Usman da Ummulkusum shima Muktar din ya halarci radin sunan da yamma kuma suka iso Abuja suka halarci hyafar cin abincin dare nima anan gida kawayena irinsu Asma'u Adam, Barira Inuwa dasu Hari da Nuwaira sun kayatar da mata da liya la a ranar sunan da yamma ina zaune a dakina da daddarce ranar sunan sai walkiya nake yi Joda ce lake tambayata ni sunan suwa aka sanyawa yaran nan? Na ce Umar sunan baba babbane
Usman sunan baba Soba, Ummu Kulsum kuwa sunan Baba Sabuwa, mahailiyar Gali, Joda ta rike baki at ce kai amma Nafiu ya yi bikıma wajen zabar musu sunayen. Washe garin suna da yamma duk jama'ar da suka balarci suna sun koma gidajensu daga ni sai yaran sai goggo Uwale da Joda da Muktar ya roki ta zauna ta taimaka mana kula dayara sai Halima nurse dinsu sai su Barratu dama su yan gidane muna tare, Nuwaira kuwa da ta tsaya kints amin gida tana falon Muktar don Gali yana nan a gidan, na fito daga wanka na yi shafa na shirya tsaf, na dauko Suwaita na sanya saboda sanyin da ake yi na shiga kicin na duba aikin da ake yi na dibi dambun nama a plate na je falo wai in kai musu Gali da Nuwaira suna gefe daya ta shirya mishi salad yana ci, Muktar yana can gefe shi kadai ya zubawa talabijin ido yana kallon tashar Aljazira, nima kallonsu kawai na yi na wuce naje wunn Muktar na bi Idonshi da kallo don in ga abinda ya ja mishi hankali haka sojojina Amcrica ne a cikin tsaunukan kasar Aganistan wai suna farautar Usama Bin Ladin na firgita kwarai da ganin inn neman da suke mishi na ce anya ba zasu ganshi ba kuwa Muktar? Ya kallcni a hankali ya ce al'amarin ba na allah banc? Na yi hanzarin amsawa kwarai kuwa, na matsa kusa dashi na ajiye mishi dambun na,man ya soma ci yana kall kallona ai yanzu nake tunaninki a zuciyala na ce to ita mai jego bana ga in an yi suna tana firtowa ba' Amma shru ko kuwa don an samu yara sai Kuma a mance da wanda ya yi sanadin zuwansu? Na yi murmushi na ce kai babansu Abba kar su Gali su ji abinda kake fada ko da yake hankalinsu baya nan, Muktar ya ja tsaki ya ce ai ni Gali kunya yake bani ya karbi mata da kyar gashi ccikin sati biyu kawai ta kidimashi Gali ya juyo ya kallemu ya ya na ji kamar ana ambaton sunanmu? Muktar ya sha mur ya ce a'a me kuka yi da za a ambaci sunanku? Ya ci gaba da cin dambun namanshi Nuwaira je ki kicin ki debo miun dambun nama kin ji? Ta kalleshe tana murmushinta na hila yi hakuri yayana sai an jima ka ci sakwara da rana yanzu ka ci salad ina ganin a bar dambun naman sai an jima, ya ce to shi kenan ni da Muktar muka kalli juna muka yi dariya cikin sati shida yaran dukkansu tubarkallah, kowaya gansu sai ya ce kainononki yana da kyau Badi'atu, dubi yanda suka yi kiba, gashi kuma kin ce nonon kadai kike shayar dasu, in ce e, wata na biyu da haihuwa aka yiwa Brigedier General Kabir Isiyaku transfer daga nan Abacha Barrack zuwa barikin Dodon a Legos, abinda ya yi matukar tayar min da hankali saboda yanda muka shaku dashi ban wartsake daga kewarsu ba sai kuma umarni ya fito cewar Muktar Zubair yana cikin sojojin da zasu lafi kos na watanni takwas a kasar North Korea don koyon sabbin dabarun aikin soja, na kammala shirina da daddare bayan na je na baiwa yara nono na kuma shaidawa Halima kar ta nemeni cikin dare zan zo da kaina ta ce to na kammala feshe jikina da. turare na ja kofata na nufi wajen Mukta ina tunanin kwankwasa kofa zan yi ko me zan y1? Tunda yau ne ranar farko da zani dakinshi tunda na haihu ina murda kofar na jita a budeahankali na shiga na laluba gadonshi na hau don fitilar dakin a kashe take ya mika hannu ya jawoni jikinshi yana cewa uh na ji kamshun dana dade ban ji ba na yi kewarki Badi'atu, gadon nan ma da yana da baki daya ce ya yi kewarki ya kara cusa hancinshr cikn gashin kaina yana shakar kamshin ya.ce uhbh na godewa babaua da ya bani ke Baui aiu, gashi baki gaya min kina zuwa yau ba balle in shirya miki sauka arama bani in miki wacce ta samu ya sanya bakinshi a nawa muka shiga tsotson juna tsawon lokaci tsawon dare ran nan ni da Muktar a makale da juna muka don kuwa mu dukaninu niun ji kewar juna wajen karfe ukun dare ina kwance a jikinshi wadansu irin kalamai masu dadin ji da sauraro yake gaya min da ya yi sbiru sai na ce mishi Muktar ya kalleni a hankali ya sake jawo bakina ya tsota kalin ya ce min babansu Abba sunana Badi'atu na yi murmushi na ce to babansu Abba ya ce uhun ina jinki menene? Na ce so nake ka tafi dani Korea, ya yi shiru nuna alamar a tunani kafin ya ce ko meye dalili? Na dan yi ajiyar zuciya ce watannin sun yi yawa kuma ni ina jin isoro ya kara kankameni ya juyani daya geten gaya rnin gaskiya meye damuwar ki ban in ga idonki don in kara gasgata abinda zaki gaya min ya sa hannu ya kunna fitia haske ya bayyana na kare idona da dantsen hannuna saboda kallon da yake min ina suararonki na boye fuskata a jikinsbi kafin na iya cewa gaskiya ni Muklar na kishu, watanni takwas sun yi yawa na yanda zaka iya yi kai kadai ya yi murmushi ya ce Badi'atu kenan akwai abinda nake so mu sanya ya zamo shi ne

1 Comments On NAGA TA KAINA 2 and 3
avatar
aisha-5-5-1

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment