Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki daya Alhaji Gali Abdulwahab yana mika takardunshi na ajiye ailki wai zai fsunduma cikin harkokin siyasa na ce naga ta kaina ni Badi'atu.me ya kar Gali kuma Siyasa? A kidime na yiwa Nuwaia waya ina tambayarta ina dalilin wannan aikin bayan Gali yana gab da kure mukaminsu zai ce ya ajiye aiki? Sai kawai na ji ta yi dariya wai alamar ita bata cikin damuwar da nake ciki ta ce ba zaki gane ba don ke yanzu kakin sojane kawai ba kya sanyawa amma tunaninki da halinki inin na Su ne, na ce to Allah ya rufa asiri ina babangida? Ta ce ya yi barci na ajiye wayar, nan da nan jama'ar kasa suka amsa kiran da shugaban kasa ya yi musu na su fito su kafa jam'iyyun siyasa, guguwar siyasa ta motsata ko ina sabbin kungiyoyi kakc ji wadanda ake fatan ayi musu rijistar su zama jam'iyyu watani uku bayan nan ayi rijiyar jam'iyyu guda hudu cikinsu akwai jam'iyyar talakawan kasa wacce Gali ya ke ciki yan kwanaki kadan da yin rijiyar jam'iyyu aka nuno Gali a Sakkwato wajen da suke yi convention dinsu wai ya lashe zaben zama shugaban jam'iyyar tasu a lokacin kuma Muktar yana wurin taron gwamnoni na buga waya Kaduna inda ayanzu Gali da iyalinshi suke da zama don in tayasu murna cikin hargowar jama'a take 'yan taya murnar Gali ya zama shugaban jam'iyyar talakawa na kasa baki daya sun ciki gida na sake yiwa Muktar waya na shaida mishi nasarar da Gali ya yi a Zaben zama shugaban jam'iyya yayi dariya ya ce yanzu na gama tayashi murna ya dawo gida da kwana biyu muka nufi Zaria tafiyarta gaggawace don amsa kiran baba babba ya yi muna zaunc a kasa a gabanbaba wanda ya zama tamkar a tabashi da tsinke jini ya tsirto saboda kyan jiki ya mulmule ya yi gwanin sha'awa furfurarshi sai sheki take yi Anti ta shigo tana rike da kwano ta ajiyc gabanshi ta budc mishi shake yake da farfesun kaji cikin zuciyata na ce watakila wurin baba
Muktar ya koyi cin kaji sannu Shema'u Allah ya yi miki albarka, Anti ta yi murmushi ta ce mishi amin La fita baba ya soma magana Muklar kuwa ya Rkara sunkuyar da kanshi Rasa nuna ladabi da sauraro na kiraka ne Muktar don in damka maka kanncnka a hannunka ko da yake dama nauyin komai akanka yake na hidimar mu dukanmu amma umamin yi ko hanawa ko zariar da hukunci ni ke wannan to na mika maka daga yau ya koma kanka cikin ladabi Muktar ya lambayeshi baba wani abu yana mak ciwo ne? Baba babba ya yi murmushi ya cc lafiyata kalau Muktar to amma duk yadda na kai da lafiya da karli ai na san yamma la yi mun ranata ta doshi faduwa tunda Manzo S.A.W. ya gaya mana cewar shckarun al'ummarshi sittin ne ko saba'in kadan ne kwarai suke zarce hakan ta ni ina cikin 'yan kadan din da suka zarce don a yau ina da shekaru saba'in da biyar ne a duniya kai kuwa shekaran jiya ka yi arba'in da biyu, Muktar ya ce e, baba ni ma har na manta ban tuna ba sai dana dawo gida cikin darc na samu Badi'atu a zaune tana jirana na tambayeta abinda yahanata kwanciya, ta ce min jirana take yi ta tuna min na cika shekaru arba'in da biyu a duniya baba ya yi murmushi ya ce to ko sanda aka haifcka shckaru talatin da biyar nc dani shekaru goma sha udu kcnan da yin aurcna don ni ba Zubairu ne kanina mai bina ba akwai wasu su uku basu rayu bance tsawon lokaci baba yana bamu labari daya gama sai ya cc Badi'atu al'amarin kannenku zai kara komawa hannunku gaba daya sai ku kara hakuri akan wanda dama kuke dashi, Muktar ya ce baba ina ganim Anti tayi maka rakiya zuwa Jidda a duba lafiyarka daga nan sai ka yi ummara, baba ya yi murmushi ya ce to Muktar amma abinda nake so ka sani shi ne yanda duk ka kai da kula alafiyata hakan ba zai hana ajali zuwa ba, shckara daya na mulkin Muktar a Bayclsa ranar na wuni ina saduwa da kungiyoyin mata daga kabilu daban aban na jihar da suke zuwa tayani murnar nasarar mijina a shekara daya da ya yi akan mulkin jiharsu na fito daga dakin dana gama saduwa dasu na dawo falon Muktar don in ga bakon da aka sanar dani zuwanshi Uzairu na samu a zaune ya zama wani kato pashi ya ajiye kasumba kai in ka ganshi sai ka ce shi ne gaba da su Muktar din na ce haka ka zama Uzairu? Ai ka tsufa, ya yi dariya ya ce haba Anti zaki sa gabana ya ladi, na zauna muka gaisa na ce ka samu ganin maigirma gwamna kuwa? Ya cc mun gaisa sai dai ina ganin kamar yana fushi dani don bai wani amsa da kyau ba balle in yi mishi wata magana, na ce ato tsawon lokaci muna hira da Uzairu kafin Muktar ya shigo zai wuce dakinshi ne alamar zai kwanta Uzairu ya ce your excellency da ina son magana ne Muktar ya sha mur ya ce amma yanzu nina kiraka maganar da ta sani kiranka kawai zan gaya maka in ka samu lokaci ka dawo sai ka gaya min maganar aka zan sanya bikin su Zainab karshen watan nan in na je Zaria daga wurinmu uwa wunn babanlungu 'yan mata biyar za a aurar samarı uku zasu auro na ura yayen wadancan su sanya tasu ranar don mu daidaita namu lokacin duk masu yin auren nan ka girmesu shi ne nake so in ji abinda kake ciki, Uzairu ya dan sunkuyar da kai a hankali ya ce ina dan dubawa ne a hankali ban samu ba tukuna, Muktar ya cc to ka je ka samu Hindatu ku daidaita, wacce Hindatu? Uzairu ya tambaya na ce Hindatun baba Sabuwa ko? Ina kallon Muktar, Muktar ya kara daure fuskaya ce shima ya san ita nake nufi yana sha'awar yin wasa dani ne, Uzairu ya kara nutsuwa jin maganar Muktar cikin ladabi ya ce ba haka bane our excelleney ka yi hakuri ya dan saki rai ya ce in ka ganta kun daidaita sai ka je Kaduna ka samu Gali ku gayamishi ba kuma na ce ka je ka ganta bane don ka dawo ka ce min baku daidaita ba, ya wuce dakinshi na sallami Uzairu ya iso masaukinshi ni kuwa na dawo na shige gun mijina washegari da sale misalin goma muna karyawa da Uzairu ya ce min ina son ganin maigimma gwamna kafin ya je office na ce Muktar yanzu yana Abuja tun takwas da rabi ya bargarin nan akwai mitin din gwamnoni da shugaban kasa bisa shirye-shiryen ba yar da mulki da ake yi ya ce to amma Anti yarinyar nan bata mn Kankanta bakuwa?
Tsananinta fa sha bakwai ko sha takwas, na harareshi na ce to a daura maka da Joda mana ko goggo Uwale ya yi murmushi ya ce zan tafi da Umminmu la yi mun hutu na ce Allah ya kiyaye dayake kaga ni da ake zuwa wa gwauro hutu na mike tsaye na suri gyalena dake ajiye kusa da jakata ian gyara lullubina ina gaya mishi in ka tafi ka gaida gida, mutune suna jirana zani ziyartar yara a asibitoci da gidajen marayu kasan yau ranar yara ce ta duninya, ashinn da bakwai ga watan biyar ya mike tsaye zai mun rakiya zuwa inda 1awagata take yana cewa Anti ba a taba bani kujerar Makka ba la, sa1 dai in ji ana ta rabo, na ce ba irinka yake baiwa ba Uzairu kai kana da hali baka ga damar zuwa banc, gaba daya yaran Muktar ya sanya ranar bikinsu 21/7/ wanda ya 2o daidai da ranar A sabar ni da Nuwaira mun kasance cikin shin mai yawa ni dai ta bangarcna banda kasancewar Muktar zai yi bikin kannenshi guda tara mata biyar maza hudu uku cikin yaran nan ya yan Antina ne da ta haifanwa baba babba wannan kuma shi ne lokaci na farko da Anti da baba zasu yi bikin 'ya'yansu na cikinsu duk hidimar bikin da suke yi a baya ya'yan 'yan uwanc sai yanzu ne zasu ga bikin Abdulwahab baban Anti da Zainab da Saliha wadanda suka zama kansu daya lamkar yan tagwayc don haka aka hada su shi baban Anti ina dai Innala ce ta hada na shi auren da yar kaninta na Yola kawu Yero bayan ya kammala karatunshi a makarantar koyon tukin jiragen sama dake Zaria, ila kuwa Zainab wani abokin Gali Dr. Manniru zata aura a gidan Galin ma ya ganta a Kaduna don haka zata Gali nc a matsayin mace ta biyu sai Saliha ita kam auren soyayyanc ita ta kawo mijinta don haka ina cikin matsanancin shiri ita kuwa Nuwaira 1ana zumudin innar zata aurar da yar autarta Hindatu, ni kam tun sati biyu kafin bikin zaman Bayelsa ya gagareni na koma zaryar Zaria, Soba, Yola da Kaduna a ranar daurin auren kuwa a gabansu baba babba Muktar ya daur auren 'yan mats shida don itama Dintadu babansu Gali Muktar ya baiwa waliccin aurenta don haka shi ya daura auren baba babba ya karbarwa Uzairu yana gama bayar da nashi kannen ya nufi Yola don karbarwa baban Anti auren Bintu yar kawuna Yero ya kuma wakilta Gali da Nafi'u suka je karbarwa sauran yaran maza guda biyu na dawo daga Kaduna inda aka yi budar kai Zainaba a gidan Dr. Mannir ina yiwa Antina bayanin abinda ya wakana Wasila ta leko tana cewa ina kirjin biki, na yi kamar ban ji a ba, sauran mutancn dake lalon Anti suka yi dariya Wasila ta shigo ana gaya min yaya Muktar ya yiwa Inna waya dazu ya ce ta gaya miki ki bar komai ki isa Bayelsa gobe don ki samu halariar bikin da matan kabilar wawan ke yi sbekara shekara wai sun roki ki zama musu babbar bakuwa a wurin, na ce irkashi to rakanı gidan su Luba in zaga su kafin in tafi goben.
Ina Bayelsa na haifi mai sunan Antina Shema'u, duk da a Zana aka yi suna liyala sosai matan garin suka shirya don tayamu murnar karuwar da muak samu, siyasa ta kankama sosai har an fara gudanar da za6a66uka yau ma ranar zabece da wurio Muktar ya tasani a gaba muka je muka jefa kuri'ar mu a mazaba ta 4 dakc garın ycnagua, indá aka yi mana rijista mun dawo gida ni da shi muna zaune a falonshi na yi waya Kaduna don taya su Abba murnar cika shekaru bakwai bakwai a duniya Ummuce ta fara magan da alama tana cikin farin ciki salamu alaikum baba abinda ta fara fada kcnan, amin wa alaikum salam Muktar ya amsa barka Ummu da cikarku shckaru bakwai ta ce yawwa baba mun gode, amma bakwai da yawa kuwa baba? Cikin sauri Muktar ya ce da yawa kai Ummu daga daya fa aka faro har kun zo bakwai ai Kun kama hanyar girma, ta cc to kai shckarunka nawa? Yace ni yanzu ina da arba'in da uku watanni kadan ne babu ibu ta saka mishi arba'in da auku fa ka ce baba muka yi tayi kara alamar an fige wayar daga hannunta, ni ne. soja baba na saramaka baka ganni banc Muktar ya yi maza ya sara cikin murmushi ya ce nima na sara maka baba don na yi yanda ka bugi kasa da kafarka sai dai mc yasa ka kwace waya a hannun 'yar uwarka? ya cc ta cika surutu baba zata bata mun lokaci Muktar ya ce to kun cika shckara bakwai yau ko? Ya ce e, amma ni zance babanmu ya kara mun nawa tunda Nafisu karfi dukansu na iya kayar dasu na kuma fisu iya gudu da tsalle, ni kam dariya nake yi Muktar kuwa ko a jikinshi sai ya ce yi hakuri ku tafi tare kawai baba hakan bawai yana nufinka fisu shckaru banc sai dai alamune na kai din sojane rikici ya kaure tsakaninshi da Umar akan karbar wayar Muktar ya ce kai soja baiwa dan uwanka wayar nan shima mu yi magana, Umar yana karba ya ce baba shi karfi da tsalle ya fini ni kuma na fishi kokari a aji na wuceshi a karatun Alkur'ani ni na yi haddar izufi goma sha bakwai shi ya yi sha biyar wel done babana to ai dama kaine babbain ji Muktar kuma yau da sassafe da babanmu ya kaimu gidan baban Sakkwato mu gaya mishi shekarunmu bakwai ni ya baiwa kyautar mu da ya bamu na rike to ai kaine babban Muktar ya sake fadi yanzu an jima zamu ziyarci gidan marayu babanmu zai kaimu da yamma zamu yi gasar karatun Alkur'ani kuma ni zan cinye gobe kuma za mu je Zana da Soba shi kenan jibi zamu koma makaranta Muktar ya ce na gode muku dukanku Allah ya yi muku albarka suka amsa amin, ya katse layin ni kam a yanzu nafi kowa murnar zamansu Abbawurin Nafiu gaba daya lokacin shi na yaran ne ga cikakkiyar tarbiyar da yake basu, sakamakon zabe ya fito jan'iyyarsu Gali batayi nasara ba sai dai sun samu gwamnoni goma sha biyu daga cikin talatin da shida jam'iyyar da ta yi nasarar tana a gwamnoni sha biyar nc sauran jam'iyyu biyun suka sauran gwamnonin a tsakaninsu talakawa Sun zabi wani raba, shugabane da ya yi alkawarin larlado da taltalin arzikin kasa, darajar naira la bunkasa ya wadata asibitoci da magunguna, kyauta ya magance matsalar dauke wutar lantarki ya bayar da ruwan sha mai tsafta kai alkawura dai masu dadin to Allah ya yi mun nikawa farar hula mulki mun dawo barikin soja da zama Muktar ya zama Bnigodicr Gencral ko wata shida bamu yi ba a Rukuba Barrack dake Jos aka turashi Bakassi cikin sojojin da aka dora musu nauyin lura da yanda za a mika wurin ga Cameroun, yana can bai dawo ba wani umarnin ya sakc fitowa cewar ya nuli kasar Indiya don yin kos na watanni shida kan aikinshi dai na soja, yana dawowa ya zama shugaban rundunar ta 4 ta askarawan Nigeria dake Bauchi mun sbekara a Bauchi aka cc ya nufi jaji ya zama shugaban makarantar borar da hafsoshin soja dake can muna jaji shekararmu daya da wata biyu a lokacin ina goton Muhd Gali, Muktar ya zama Major Gencral a duk lokacin a mukc cikin wadannan ayyuka da canjc-canjc Gali yana can yana fafatawa cikin harkokin siyasa, kasa tana ncma ta rikice al'amura sun cabe komai ya ta barbare Gali kullum yana cikin babatu a gidajcn jaridu da talabijin kullum cikin kushe yanda gwamnati take tafiyar da al'amuran kasa yake, tun jama'a suna ganin adawa ce tasa Gali iin wadannan maganganun har dai aka gano gaskiya yake fadi, gwamnati sai almubazzaranci da dukiyar kasa take yi cin hanci da rashawa ya yi katutu an kasa biyan ma'aikata hakkinsu, masu fansho kuwa tuni suka shiga halin ha'ula'i farashin man fetur sai tangal-tangal yake yi wai an bar yan kasuwa su yi yanda suka ga dama, gwamnati ta cire tallafin da take yiwa man, tuni talakawan kasa suka soma fadin sun ga ta kansu.
Ran nan Muktar ya dawo daga kasar Germany tafiyar shi ce ta kashin kanshi ya yi ind aya tafi da Ummi Nafisatu da Nana Fatima suka yi mishi rakiya ya dawo da sati biyu ina gida na amsa wayarshi daga office shirya maza Badi'atu gani nan zuwa zaki rakani Zaria yanzu sa ce lafiya ya ce lafiya mun isa Zaria kusan sallar La'asar ne yana cikin falonshi can muka sameshi ni dia Muktar mun nutsu sosai don oima maganar da Muktar din ke yi ta kashe min jiki kwarai baba babba ya gyara rikon da ya yiwa baban yara ko Gali ya ce amma a matsayinka na yanzu ka bar aikin soja Muktar? Ai na dauka zaka bari ka kai matsayin General tunda kana gab da kaiwa Muktar ya kara sunkuyar da kai ya ce burina kenan amma abinda nakc hange ya sanyani bakura da hakan in dai ba kainc ka ce baka amince da barin aikin nawa ba, don na shiga wani hali na canka-cakare, ko da Muktar bai furta ba daga ni har baba mun fabimci akwai wani abind aya hango nan da nan baba ya amince da barin sojan Muktar ya shiga yi mishi fatan alheri wata hudu kaca idan wannan maganar sai ganmu a sabon gidanmu na Kaduna Muktar ya zama ritaya Major General yan uwa da abokan arziki sai zuwa mana murna ake yi Muktar ya fita aikin soja lafiya, nan da nan ya shiga shirye-shiryen abinda zai yi cikin kankanin lokaci ya bude kamfanin sufurin jiragen sama mai suna ZU U MA AIRLINE, ina tare da Muktar a ranar da aka kaddamar da jiragen muna barin wajen Zaria muka nufa don shaidawa baba babba jirgin ZU'UMAN ya tashi na shiga dakin
Antina ina mata sallama zamu tafi, anti ta kalleni ta ce ke dai kullurm daga ciki sai goyo wahalar nakuda bata damunka nayi murmushi na ce Ant.i kowa da irin zuwanshi da kuma arzikinshi ni kuma kin ga wannan din London Muktar ya ce zani awonshi ta ce ai sai ku yi ta yi na yi dariya kawai na tafi muna kwance cikin dare ni da Muktar wasanninmu muke yi na farantawa juna rai rabon damu mallakawa juna kanmu irin na yanzu tun kafin Muktar ya zama gwamnan Adamawaa a yanzu ni dashi mun zama tamkar amare ko ina zashi ni ce 'yar rakiyarshi in kuwa kwanciya zai yi zai ce bar abinda kike yi ki zo ki mun tausa, in ce to, karar waya ce ta damemu Muktar ya mika hannu ya dauka, hello na ga alamar fuskarshi ta canza, na ji yana cewa yanzu? Wanc asibitin zaku kaishi? Ganinan 2uwa yanzu, da sauri Muktar ya dira daga gadon ya shiga bandaki wanka mai sauri ya yi ya fito yana sanya kayanshi yana bani amsar tambayar dana yi mishi babana bashi da iafiya Badi'atu, abinda babanlungu ya gaya min kenan wai yana ciwon habo, na ce irinshi ya taba yi Muktar sanda baka nan kana dajin nan biyo Muktar na yi ina mishi wannan bayanin don tuni har ya shige motarshi yana kokarin fita daga gidan ba zan iya jiranki ba da safe kawai ki zo na ce to Allah sawwake na dawo dakinshi na kwanta barcin da na yin ba mai dadi bane daga idar da salla ta na shirya cikin motata na nufi Zaria daga ni sai Gali karami mu biyu ina isa kofar gidanmu na ga motoci sai isowa suke yi na kauce don in yi parking gefe daya sai kawai naga Muktar kanshi babu hula kafarfshi babu takalmi shi da wasu mutane suna kokarin fito da makara daga ciki Tukuna
A ranar kaddamar da littafin a jihar bayelsa Wanda yayi daidai da ranar da mukhtar ke cika shekaru hamsin cif a duniya zan iya cewa gaba d'aya Nigeria ta taru a bayelsa, shugaban kasa da mataimakinsa suna can ministoci gwamnoni da sarakuna da duk wani mai fad'a aji ya zo uzairu na zab'a chief launcher don shi ke shagabancin zuuma airline, Alhaji Gali Abdulwahab uban taro, mai masaukin bak'i gwamnan bayelsa, Ina zaune cikin hijabi da bak'in madubi kusa da mijina masu jawabi suna ta yi, yabona suke yi suna fadin namijin kokarin da nayi wajen kammala tarihin da nayi da aka gama jawabai sai aka shiga lunching, Ni kam da naji abinda uzairu ya bayar rike baki nayi, jama'a suka yi ta fadin abinda suka bayar, jihar adamawa ce take fadin yawan littafin da ta saya akan miliyoyin nairori a lokacin da mukhtar ya juyo yana tambaya ta ranki ya dade wadanannan miliyoyin da ake Tara Miki me zaki yi dasu? Ko zaki ajiyesu ne ki yi ta shirya min gara Ina Sha , in yi ta cin Bean And meat casserole? Nayi murmushi nace your Excellency zaka Sha gara ne inka in ka warware bakin aljihunka, wadanannan makudan kudaden da kake magana a kansu zasu tafi ne wajen aiwatar da shirina na taimakon yara qanana masu fama da ciwon zuciya, samar musu magani kyauta da Kuma daukar nauyinsu zuwa kasashen waje in har hakan zai Zama shine hanyar warkewarsu. Mukhtar ya kama hannuna ya rike da karfi ya ce Badi'atu, a lokacin da Babana ya bani ke biyayya da gudun bacin Rai ne yasa na karbeki a yau Ina alfahari da kasancewata d'a mai biyayya ga iyaye don Kuma hakan ya sani na samu abunda nayi ta roko tun Ina d'an k'arami shi ne ubangiji ya azurtani samun mace ta kirki.
Shekaru hudun mulkin mukhtar sun kusa cika jama'ar k'asa sai Kira suke yi mukhtar ya sake fitowa su zabeshi ya ci gaba da mulkinsa saboda a zamaninsa kasa ta yalwata zaman lfy ya tabbata jama'ar k'asa sun samu kwanciyar hankali an raba su day talauci da wahala an rabasu da ambaton kalmar *NAGA TA KAINA!*
sai anjima
Taku
Hafsat sodangi
Sai mun sake haduwa a wani littafin.






















An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On NAGA TA KAINA 2 and 3
avatar
aisha-5-5-1

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment