Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jagoran zamannu, yarda da kumna amincewa juna, kin gane? Ni kam bankalina a kwance kwarai yake har abada na san da izinin Allah na san ba zaki ta ba bayar da kanki ga wani ba, ni ra so k Yarda cewar ni mutum nc wanda ban yiwa Allah alkawari in saba, Da ce na tauba bazan sake aikata zina ba, zan fi kowa farin cikin ace na tafi dake to amma yaya zan yiin tafi dake da jarnrai guda uku? Ya zuiba min ido yana kallona na kwanatr da kaina a kiriinshi dukkanmu shiru muka yi na wani lokaci kafin ya sake cewa ina ganio hakuri kawai zamu yi kamar yanzu ne zaki ga najc na dawo, na ce Allah ya dawo dakai laliya, ya ce amin, na tashr na dauki rigar barcina ina sanyawa ya kalleni ina zaki kuma? Na cc zan baiwa yara nono ya ce jirani in rakaki sai da ya shiga ya yi wanka ya iito sannan muka je, ni kam har kulium ina mamakin dabi' un Muktar babu yanda Za a yi komai sauri ka ga ya yarda ya li1ta dakinshi da datti. Bai damu ba a cikin dare ya yi wanka sau biyu ko ma fiye da bakan amma in dai zai ita, to zai yi wanka in ya so in ya dawo ua sake yin abinda zai sake sanyashi wankan sati uku da aka baiwa su Muktar na kanmmala shirye shirycnsucikin wadannan kwanakin babu abinda ban yi ba don ganin na faranta mishi rai ana saura kwana uku su tafi na yi mishi rakiya zuwa Zaria, falon baba babba muka fara sauka don shi akdaine a ciki har gabanshi Muktar ya je ya ajiye mishi Ummu ya yi sauri ya karbeta yana dariya wai wannan kiba da yaran ke yi inda mnulum daya ne yake shan nonon zai ganu kuwa? A Soba ma da muka jc abin gwanin dadi inna sai murmushi lake yi tana cewa Allah gwanin Badi'atu na ta zam maman 'yan uku, Muktar ya yi murmushi ye ce inna ba ia ta son a rinka kiranta da wanan sunam Ipna t nkehakinuna alarnar mamaka ta ce to akan me? Mata nawa kika gani da yan uku? Daga Soban bar Zaria kwana daya muka vi muka wuce Sakkwaio wur in da Gali yakc a yanzu muna shiga gidanni kam ban san sanda na kyaIkyale da danya ba wai Galine a kicin yana daure da (Apron) rngar da masu girke ke ratayawa a wuyansu don kare kayan jikinsu daga lalacewa ya dage sai kokarin tuka tuwo yake yi, ita kuwa gimbiyar na hangeta cikin falo kwance shame-shame kan doguwar kujera gabanta kuwa kayan ciye-ciyene iri-iri in ta mika hannu sai ta dauka ta sanya a baki tana daga kwance.
Muktar ya iso yana rungume da su Abba a kirjinshi ya kulli Gali rike da muciya ya ce yallabai barka da aiki, Gali ya juya suka hada ido Muktar ya Ryalkyale da dariya, to meye abin dariyar in ji Gali, bani yaran ka shiga ka dauko mun tukunyar miyar, Muktar ya mika mishi su ya wuce zuwa falo yana cewa Allah ya sawwake ai ni rabona da ina taba tukunya na manta ba kuma zan taba ba yau don na zo gidanka a falo da kyar Nuwaira ta iya mikewa ta karbi Ummu tana cewa mamana Gali ya zauna yana rungume da yaran yana magana tun jIya Nuwaira take son cin tuwon masara miyar kuka Kande ta y mata jiya bai gamsar da ita ba, shi ne na ce bari ni in yi mata ko zai mata. Muktar ya ce ai sai ka kawo mata tun bai yi sanyi ba, Gali ya ajiye yaran kusa da Nuwaira ya nufi kicin ya kawo abinci a tire, ya ajiyewa Nuwara nata yazo gabanmu yana ajiyewa, Mukta ya girgiza kar nuna alamar a'a ya ce mu kam mun gode a yanzu a koshe muke a kira Kande kawaio ta yi mana girki. Gali ya galla mishi harara ba dai zaka ce bai yi dadi ba, malmala ne kawai bai yi kyau ba ni dai ina hira da Nuwaira ina kurna kokarin hana kaina dariyar fadan Gali da Muktar akan tuwonshi Nuwaira ta gama cin tuwon Gali ta yamutsa fuska tuwon ya yi dadi amma zuciyata tana tashi, cikin saun ya zo yana shaf amata kijinta wai zai kwantar mata da hankali ta wankeshi da amai, Muktar ya ce wai lalle ana renon ciki a gidan nan da kaina na tashi na tsaftace wurin shi kuwa Gali da Nuwaira suka nufi daki don tsaftace kansu kwana muka yi muna hira bayan mun kammala cin abincin dare wanda ni na yi mana washe gari kuwa muka taho gida kwana daya muka yi ne sake yiwa Muktar rakiya zuwa Legos inda zai kwana daya washe gari su tashi a gidan su Mami Hajiya Mariya muka yi hira kafin muka isa hotel dinmu da safe kuwa a kan idona jirginsu Muktar ya tashi zuwa kasar Korea ta Arewa na dawo gida zuciyata cike da begen Muktar sai dai ban yarda begen nashi ya hanani aiwatar da abinda ya zama wajibi a kaina ba a yanzu gidana a cike yake da jama'a gaya' yana uku rus ga masu tayani hidimarsu ga karatuna da yaek gab da karewa, wata biyu da tafiyar Muktar muka yi bikin Nati'u da 'yar wani commissioner na yan sanda daga Katsina State safiyah sanin da na yi idan Muktar yanabnan shi zai dauki nauyin shirya kayan auren ya sa na tsaya na shirya akwatuna guda hudu da kit na aike dasu zaria tun kafin ni in je a bikin muka hadu dasu Nuwaira cikinta har ya fara dan fitowa Uzairu ma ya kammala hidimar kasa har ya kama aiki a Benuc Cement Company ni da yaran dukanmu lafiya karatuna yana gab da karewa, ina shirye-shiryen zana jarrabawata ta karshe a jami'a don samun takardar shaidar digiri kan ilimin na'ura mai kwakwalwa wato 'computer ina zaune da Nafi'u a falona wanda tun tafiyar Muktar ya dauki matakin zuwa duba yara duk sati biyu hira muke yi yaran kuwa suna ta kokawarsu don su dukansu a yanzu tafiya suke yi Umar ya turmushe Ummu a kasa da sauri Nalfru ya tashi ya je ya dagashi yana cewa haba Malam ba a fa san babba da cin zali ba, na kamo Ummu zan bata nono don in rabata dasu kememe ta ki yarda Nafi'u ya yi murmushi ya ce da kin ajiyeta ta je cikin yan uwanta, na ce wahala suke bata duk wanda ya tashi cin zalinshi 1ta yake dannewa, amma ita bata son rabuwa dasu. Nafi'u ya yi dariya ya ce ai niAnti da akiban yaran nan da kin burgeni, wallahi na harareshi na ce wato ni ce ma zan baka su'? Ya yi murmushi ya ce a'a ai ni kece matsalata ayya Muktar ai ba zai hanani ya yanshi ba na ce haka kake gani? Ya ce kwarai sati biyu kafin in fara jarrabawata ta karshe a jami'a aka aiko min da labarin haihuwar Nuwaira a Sakkwato inda ta samu'ya mace, haka na tsallake dimbin karatun dakc gabana na nufi Sakkwato daga ni har ya'yana su Joda da hari muka tafi suna tuna ana saura kwana biyu suna, ina rungume da jarunyar wacce komai nata irin na uwarta ne, na kall Nuwaira na ce ke kam kin ji dadi kin samu mai kama da ke, amam ni dubu na haili ya' ya amma aka rasa wanda zai min kara ya biyoni duk sai suka bi Muklar, ta kyalkyale da dariya te ce to ai gara haka Muktar din bai fi ki kyau ba? Nace Ia ila ha illallahu, ban taba jin wanda ya yi min wannan zagin ba sai ke yau ta sake kyalkyale da dariya Gali ya shigo muka gaisa na kalleshi na ce rashin lafiya ka yi ne ko? Ya ce uh uh fargaba ne kawai ai mun ji jiki da cikin nan mun dai gode Allah an rabu lafiya, na yi darıya na ce to Allah ya kara rufa asiri, ya ce amin, gagarumar hidima Gali ya yi a sunan nan Kiris ya rage a sanyawa jaririyar sunan baba Sabuwa, sai ga aikenta kan wai a radawa yarinyar Fatima sunan mahaifiyar Nuwaira, hakan aka yi Suna da kwana biyu na shaidawa Gali gobe zamu koma ya ce to tunda ga jarrabawa a gabana in bar musu yaran su yi musu bakunta na ce ai ban yayesu ba, ya ce a yayesu anan goggo Uwale da Halima su zauna tare dasu ni da Joda da Hari mu koma gida in zai taho Zaria zai zo min dasu lokacin na kammala jarrabawata, na ce mishi to ina zaune a dakina kan dardumar dana idar da sallolin nafilar godiya ga Ubangii bisa kammaluwar jarrabawata tunanin mijina ya tsaya mun wata tara yau da tafiyarshi bayan an ce mun wata takwas zai yi na dai sarnu wayarshi gab da zai cika wata takwas din hakuri ya banu kan wai an yi musu karin kwanaki arba'in akan wata takwas din saboda wasu dalilai da ba zai yiwu ya gaya min a waya ba to gashi lokacin ya yi kome zai ce min yanzu kuma obo? Ranar Litinin da safe ina ta kaiwa da kawowaa gida kewace ta fi komai damuna ya'yana watansu biyu a Sakkwato ga Muktar shitu ga karatuna ya kare bani da abin yi in banda zama na koma aikin girkin gidan na hutar da Barratu amma hakan bai debe min kewar da nake eiki ba, na yiwa Uzainu waya ya je Sakkwato ya debo min yara ya ce in yi hakuri amma shi ba zai aya zuwa ya cewa yaya Gali wai ya bada yara ba, shma Nafi'u dana mishi maganar ya je ya debo min yaran murmushi ya yi ya co wai kyan wannan in je da kaina ni kaina na rasa yanda zan yi in je gidan gali don in debo ya' yan Muktar, ina kwance kan gadona ni kadai na lulluba da bargo barci ya ki daukata duk da matsanancin ruwan saman da ake zabgaa kamar da bakin kwarya ga walkiya da cida, na ji wayar dake dakin ta yi kara na mika bannu na dauka na ce wanene? Muryar Muktar na ji don Allah ki yi hakuri Badi'atu mutanen nan sun sake kara mana sati biyar da karfi na kurma mishi ihu wayyo Allah na ni badi atu na ga ta kaina, na saka mishi kuka ina cewa ni na gaji wataani takwas sun zo sun wuce da kyar an kara sati shida, surma na daurs sun cika har sun fara wucewa yanzu zaka sake kira uin sali biyar to ba zan iya ba in kai baka damu ba ni wahaia ta ishepi, dakata-dakata mana ki ji da kyar na iya yin shin haba maman'yan uku ke kina kuka yaran kuma ta? Na ce oho suma sun san kewar upansu ta dameni, to ke dai bude min kofa, cikin saurn na ce eye, ya ce btude min aana Badiatu ru wa la yana dukana, na tabbatar da gasken don in zolayala yakc bai yiwuwa ya san ana ruwa anan da gudu ni fita na bude kofar falonshi yana tsaye sai digar ruwa yake yi tsalle na yi na makaios1sbima ya kankameni ya sureni da gudu sai dakinshi dama kuwa kullum a cikin tsaftaceshi nake sai kamshi yake yi ba tare da mun cewa juna komai ba Muktar ya shiga tu6eni nima ina
tubesti saboda tsananin matsuwa da juna da muka yi sai na ji tamkar
ba mu taba mu'amala mai dadin na ran nan ba ina kwance a jikin Muktar yana maida numfashi a hankali ya ce ya'yana fa Badi'atu ina son ganinsu na kara kwanciya mishi sosai na bashi labarin haihuwar Nuwaira zuwanmu suna da yanda Gali ya ce abar mishi yaran har gayawa su Uzairu su dauko min yaran na yi sai dana gaya mishi ya yi murmushi ya ce da kin yi abin kunya Badi'atu kuma a tsiyar Gali dana sani ba zai bada su ba in ya ga dama kuma ya ki dawo dasu ni kuma kin san ba zani in ce aka wo su ba tsawon lokaci muna hira ina bashi labarin abidna ya faru bayanshi shima ya gaya min yanda ya yi koos dinshi da irin kewata da yara da ya yi gab da ruwa zai dauke muka Iito bayan mun yi wanka, ni na shiga kicin shi kuwa ya shiga amsa gaisuwar masu zuwa mishi sannu da zuwa kunun gyada na fara dama mishi na kai mishi ka lin in gana mishi abunci na koma kicin na shiryawa muklar kuskus da miyar taushe mai wadataccen naman saniya da tantakwashi sai kuma na shirya mishi york shire pudding da roast beel, ga abubuwan da na yi amlani dasu:- flour, kara, madarar ruwa, man gyada sai gishiri dan kadan shi kuwa roast beef din namnan cinyar saniya na yanka mai nauyin kilo daya na hudashi ta kusurwa biyu ya bullo ta kusurwa biyu na daureshi da irin jijiyar nan da aka samu a kings way ta yin gashin nama na dauko bluc band din dana riga na cakuda da garin maggi da kori da barkono da gishiri dan kadan na yi ta murzawa naman nan ina cusashi ta wacec käla na samu kusan minti goma aikin da nake yi kenan sai da naman nan ya nade blue band din nan tas na sanyashi cikin oben na daidaita mishi wuta na koma kan lour da na riga na kwaba na shiga suyan yorkshire pudding da mangyada yana fitowa bisa tsarin yankan dana mishi tamkar kwabo-kwabo sai da na kammala soyashi na je dakına na yi wanka na zauna na lailaye jikina na yiwa Muktar kwalliyar sannu da zuwa, sannan na dauki abincin dana shirya mishi na je na kai mishi yawancin mutane da Suka shigo sun tafi sai Major Amadu suna hira muka gaisa ya tayani murnar dawowar Muktar na ajiye abincin na koma kusa da Muktar na zuba mishi abincinshi a plate yana cin kuskus din ina aikin yankan naman nan ina nadewa cikin failan yorkshire pudding ya ture platdin kuskus ya shiga soke shi da cokali mal yaisu yana ci shima Major Amadu yana yin yanda ya ga ina yi yäna CA SAuna kuma hurarsu yawanci akan abinda ya shafi aikinsu na soja, ni kam ina jinsu ban kuma tsoma musu baki suna gab da gama cin abincin na ji Major Amadu ya cewa muktar anya yallabai mace gwanar girki zata yiwa mijinta laifi kuwa? Muktar yana taunar yorkshire a bakinshi ya yi murmushi ya ce kasan yau da gobe Major Amadu ya ce ammna za a yi saurin yafe mata don kuwa kauma tana faranta maka, a yanda kake da yaWan bakin nan in banda kana da wannan rulin asirin al da Tanka ya baci ya sake mumushi yace yallabai ai Wa tal lokaci na kap yi tunanin in banda a bariki kake da gidanka ya zama matattarar jama'a Muktar ya yi murmushi ya ce aine la dan fan a wurin iyayena maza guda uku kannena kadai Sun fi arba' in na zubawa Muktar ruwan matsattsen lemo na mika mishi ya karba ya mikawa Major Amadu na sake zuba wani na ajiye mishi na kwashi kwanukan na tafi na barsu suna ira, daren ran nan ko rintsawa ni da shi bamu yi ba washe gari da safe na kammala shirya mishi abin karyawa misalin tara da rabi na safe na je na yi wanka n ayı kwalliya cikin wata riga da Muktar ya riko nmin ita a yar karamar jakar da ya zo da ita a hannunshi rigar ta karbeni ba karamin kyau na yi ba, ga kamshi mai dadin ji dake tashi a jikina, ina cikin shirya kayan a falon Muktar kafin in je dakinshi in taso shi Daniel ya zo ya shaida min isowar baba babba da babanlungu na je na bude musu kofar falonshi suka shigo na zauna cikin ladabi na gaishesu baba ya min murnar Muktar ya dawo ban yi magana ba murmushi kawai na yi ya fita ne? Baba ya tambayeni na ce a'a yana dakinshi na shiga na tasoshi ya fito sanye da rigar barcin a kasa ya zauna yagaishesu, cikin ladabi baba ya ce sia kuma ka-kayi ya Muktar ya ce e, wallabi baba mun samu Fatimab, to yaushe 2aka ganinsu? Ya dan yi shuru kadan sai ya ce in banda su Abba suna can ai da gobe na je ganinta, Baba ya ce su Umar ai suna tare da babansu a London Gali ya tafi dasu da Uwale. Halima kuwa tana tare da maijego a Sakkwato ita da Hajiya Sabuwa bayan haka Murja ma ta haihu an samu da namiji ni da Muktar muka yi murna muka ce Allah ya raya baba ya cc amin Muktar ya ce to gobe in Allah ya yarda zan fito zan je Kaduna in ga iyalin Nafi'u daga nan in iso Zaria ganin sabon yaro sai in wuce Sakkwato wuria Nana Fatimah in ganta na koma wajna na barsu suna karyawa har sar da na kammala abincin rana na kai musu na samesu hira ta y musu dadi bayan sallar La'asar suka tafi. Washe gari misalin bakwai da rabi na safe na kammala mana shirye-shirye bar abincin da zamu ci a wunin ran nan na shirya mapa a manyan foodflast kwalliya sosai na yi na yafc jikina da lafaya irin ta bare-bari sai kuwa Muktar manyan kayane a jikinshi D Class Combatable one door Ita ce motar Muktar da zamu yi tafiyar a ciki kusan ma wannan ita ce tafiyar da za a yi da ita na farko don bai dade da saenta ba, ya tafi kasar North Korea da wuri kwarai muka isa Kaduna gidan Nafi'u tarbar da Nafi'u ya yi mana ba Karama ba' ce, a yau ne na kara gane kaunar dake tsakann Nafiu da Mukatar don kuwa saukar gimamawar da ya yi mishi tana da yawa, matar ce dai ban ga kamar ta iya karba baki ba, ko kuma don yau ne zuwana na farko tun bayan bikinta oho, ruwan tea kawai Muktar ya sha na kuma san don Nafi'u ya sha ni kuwa tunda na ga matar bata iya fara'a ba na ce a koshe nake. Awa biyu cif Muktar da Nafi'u suka yi suna ganawa ni kuwa muna falon amarya Safiyah muna zaman jugum-Jugum jilfa jifa dai na kan dan nermata da magana cikin zuciyata kuwa ina cewa uh uh uhum gida har gida maigidama haka sai dai matar gidan ne cikas, da zamu tafi kyautar sarkar diamond sigen wacce Muktar ya bani daren jtya ita ma ye bata akan hanyarmu la zuwa zaria muna hira na sako zancen yanayin gidan Nafiu dana gani tun kafin in gama gaya mishi ya shamur ya dan hararcni zaki koma gidansu da zamane? Na ce a'a ya ce to babu ruwanki da halin matarshi, kin girmeta a shckaru kin girmcta ta wajen ke matar wanshi ce doa haka ki kama girmanki, na coe to a Zaria kuwa sashin babanlungu muka tara sauka ganin majego da danta dukansu gwanin sha'awa dasu lafiyar kalau tubarkallah muna Zana har sai da muka yi sallar La'asar uku da rabi muka mika hanyar luntuwa kan hanyarta zuwa Gusau daga nan mu wuce Sakkwato a farkon taliyar kaset din 'Celine Dion cikin wakar A new day has come ne ya debe mana kewar zaman shiru saboda taliyar ta yi karfi da yawa, daga Rersbe kuwa na sanya mana Power of love shima dai Celine Dion Muktar ya kalleni cikin murmushi ya ce kc dai kina son matar nan na tayashi mummushin na ce a1 ni a wajena ita ce uwar mawaRa, ya sake mumushi ai ni ma kin koyan sonta a tafiyar nan da na yi duk lokacin da kewarki ta dameni man shalawarki nake daukowa dove 1n tsiyaya a haununa in ji karmshinshi sar in ji kamarjikinki nake sunsuna in kuma na saaya kaset din Celine 1Dion din sai ini kamar muna tare tunda ba kya rabo da jin wakokinta dadi ya kamani cikn uciyata na ce ashe dai Muktar ya yi ba duk da tsayuwa da muka yi a hanya har sau biyu a gidan galli muka yi sallar isha'i falon ya sha ado hotunansu Abba kowa nashi shi kadai sai kuma aka sake yi musu su ukun tarc Muktar yana rungume da yarinyar addu'o'iyake ta karantowa yana tola mata tsawon lokaci kafin ya dago ya kallemu ya ce Aah ya yi mata albarka na ce amin suka shiga gaisawa da Nuwaira suka shiga hira jimawa can na ce baka fa je ka gaida Baba Sabuwa ba, ya ce Nuwaira gaya mata zaan shigo mun gaisa shi a Nuwaira suka shiga ni kuwa Halima ta zo wajena.muna kara gaisawa da tambayarta labarin bayan saduwa sai da ta fita sannan na bi bayansu na samu Muktar yana cevwa ato Umma ai laifin mamun nasun ne da ta haifo na ce guda daya da biyu ne kinga da bata hadasu rigima, na ce to ai sai ta karo daya kafin badi su zama 'yan mata biyu Nuwaira ta galla mun harara akwati na uku shake da kayan jarirai ya kuwa yiwa Nuwaira na kyautar mota Honda Prelude sabuwa dal mai Rofa daya a Sakkwaton ma ya sayeta kwananmu biyu muka dawo Abuja, watanni biyu da dawowar Muktar ina dakinshi ina shirya mishi jakar da zai yi tafiya da ita shi kuwa yana kokarin karasa kwalliyar shi takalmi black mocasin ne a kafarshi farin wando chınnose poduct din D.K.N.Y ya sanya rigar T. shirt baka nike ya dora shirt akanta short sleave beach wear milk clour agogon hannunshi kuwa rolex sai daukar ido yake yi ya kammala ta je gashin kanshi ya ce ya ya dai Madam na cinye? na kalleshi na yi murmushi kafin in yi magana ne jero atishawa har sau biyar ya kalleni cikin tausayawa 'yar hamakillah, na amsa mishi. Ta hanyar rama mishi addu'ar da ya yi mun yace an ya Badi'atu wannan. murar taki banine sanadinta ba kuwa? Na kalleshi.
kamar yaya? ya yi murmushi ya ce to naga taku karewa duk magungunan da kika sha ko a jikinta na yi kamar ban gane abinda yake nufi ba na ci gaba da kokarin rufe mishi jakar, kwanan Muktar hudu a Lagos kan wani aiki da aka turashi inda zai yi sati guda ni kadaice a falo sanda aka yi sanarwar shugaban kasa mai ci wanda yake soja ne mai mukamin General wanda kuma yake da matukar larin jini wurin talakawa don shirye-shiryen da ya gabatarwa na kawowa talaka sassauci zai gabatar da jawabi na mika hannu na dauki remot na kara maganar daidai an soma kada taken Nigeria ya soma jawabinne da gaisuwa ga yan Nigerna sai ya Ci gaba yana gaya mana halin da kasamu ke ciki matsayin tattalin arzikinta a jiyarta a bankin duniya abinda ake binta bashi da abinda ta biya tun hawanshi kan karagar mulki nasarori da kurakurai daya samu tun hawanshi ya kuma rokijama'ar Rasa da su kara hakuri da juriya don gwammanti ta samu ta ida manufofinta don samun cimma bukata cikin gaggawa majalisar koli ta soja tayi taro inda ta zartar da yin wasu canje-canja a jihohi an canzawawasu gwamnoni wuraren aiki yayin da aka nada wasu sabbi ya soma fadin wadanda aka yiwa canji yana kammalawa sai ya shiga fadin
sabbin gwamnonin da aka nada "Col Muktar Zubair is the new military administrator of Adamawa State" Abidna na ji shugaban kasa ya fadi kenan kan in yı komai da gudu Joda ta fito daga dakinta inda take nata kallon Badi' atu na ji kamar shugaban kasa ya kra suna maigidannan me ya y1? Na ce an nada Muktar Joda ya zama gwamnan Adamawa, Joda ta kidime cikin farin ciki gida ya kaure da sowar murna da gudu Hari ta shigo ta rungumeni tana murna ta ko ina makobta sai shigowa suke yi na ce Hári ki lura dasu a raba musu lemo su sha akwai fivealive a sito, ta ce to ni kuma na amsa wayar dake ta kara, muryar Gali na juyo daga

1 Comments On NAGA TA KAINA 2 and 3
avatar
aisha-5-5-1

2 years ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment