Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MATA..
IYAYEN..
GIJI

DAGA ALƘALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
(MRS BUKHARI)

(GAWURTATTU UKU)

( WANNAN LITTAFIN BA ƘIRƘIRARREN LABARI BANE. LABARINE DAYA FARU A ZAHIRI. LABARINE MAI CIKE DA ƊUMBIN DARASI. DUK WATA MACE DA TACI KARO DA LABARINNAN, TAYI ƘOƘARI TA BIBIYESHI HAR ƘARSHE. ZATA AMFANA DA ABUBBUWA DA DAMA.)



LAMBA TA ƊAYA

SAMFOTI

SADAUKARWA:
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN KACOKAM ZUWA GA JAM'IYYAR MATAN AREWA. ALLAH YA ƘARA ƊAUKAKA WANNAN ƘUNGIYA.


GAISUWA: Gaisuwar ban girma a gareki, shugaba uwa jagorar mata. ( Hajiya Rabi Saulawa. President ta jam'iyyar matan Arewa) Ina miƙa saƙon gaisuwata a gareki da ahalin gidanki baki ɗaya.

JINJINA:
ina miƙa jinjinata ga dukkan wata uwa ta faɗin duniya baki ɗaya. Mata iyayen giji.

ƘAWAYENA:
Maman Khairat. ( Ke alkhairi ce a rayuwata)
Maman Yaseer ( ƙawar arziki)
Ummu maheer miss Green ( Mai farar zuchiya)
Ummu Affan Fatima Sunusu Rabi'u. ( Ke ta musamman ce)
Hajjon Bakori ( Ƙawar amana)
Anty Laila Ali Othman ( matsayinki da banne)
Ummu Affan

Da sauran ƙawayena da ban kira sunanku ba. Kuna da yawa ne.


GAISUWA ZUWA GAREKI UWAR ƊAKINA:
ANTY HADIZA BARA'U GIDAN IKO. SARAUNIYAR MARUBUTA, INA JINJINA BAIWARKI, KUMA INA AMFANA DA RUBUTUNKI"



KATSINA
ƘARAMAR HUKUMAR BAKORI:

LAILA:

Wasu shekaru da suka shuɗe a baya can_can:

So! So!! So!!! Itace igiyar da take zarge da ko wanne ruhi. Wannan igiyar ita ta jefani a cikin gadar da taima rayuwata mugun bugun da saida ta haddasa ma rayuwata karayar da babu maɗorin da zai iya kawo mun ɗauki. Ashe na shiga ban ɗauka ba baya fidda ɓarawo, tunda so ba goriba bane balle kace zarenta iyakar haƙori zai zarge ma, in ka gaji kayi fatali da'ita. Dama ace ina da ƙafafun da zan iya shure so, ko kuma sandar da zanbi so da mugun gudun da saina halakashi kowa ya ma ya huta. Akace so Zuma ne, ni dana sha sai ya zame mun farar guba mai ruguza gangar jiki, so ya maisheni nakashashshiyar ƙarfi da yaji. Kallon mai lalura akeyi mini, har wasu na danganta hakan da shafar junnu, ba su son so bane yabi dare ya durƙusar dani ba. Na tattare kaya na daga majalisar so, ni da wannan majalisar haihata_haihata.






Ƙunshin kayana dana ƙunso a ɗankwali mai ɗawusu na yar a filin tsakar ɗakin mahaifiyata. Idanuna caɓe_caɓe da hawayen daya haɗu ya dame da farin kwallin dake idanuna. Hakan ya saka fuskata ta ƙara yin baƙi. Mahaifiyata ta dubeni tace.
"Karfa kice mun yaji kikayo da yamma sakaliya haka Laila, baki da hankaline, ko so kike ki zubar mana da mutunci a gari, ince dai surukanki, da facalolinki basu san yaji kika yo ba ko?" Cikin in_da_in_da nace."
Ba yaji nayo ba Inna, Auren Shehu ne na dena. So yake ya kashe ni Wallahi".
Bub, ta bige mun bakina da bayan hannunta, take bakina ya fashe ya soma zubar jini. Ga tsohon ciki a jikina haihuwa ko yanzu ko anjima.
"Kul kika ce zaki toni asirin mijinki, babu kyau yin hakan sam, labule ai asirin ɗakine. Ki ɗauki ƙunshin kayanki, tunda duhu ya soma rufawa, ki yi komawarki ɗakinki tun kafin mahaifinki yazo ya tadda ki, wallahi bazaki ji da daɗi ba. Ba tsohon ciki gareki ba, wallahi ko haihuwa zaki yi yanzu, saiya saɓa miki. Kuma kinsan baki da wajan zama a gidannan ai. Shashashar kawai, yara basu san darajar aure da miji ba, sai shirme, da bankaura kaɗai suka iya a gidan mutane." Ni dai ina tsaye, sai shirɓine hawaye nake yi da bayan hannuna. Muryar mahaifina muka jiyo yana kwaɗama Innata kira.
"Ke Ta Asibi, Ta Asibi ke" Mahaifiyata sabida kaɗuwa kasa amsa kiran tayi. Labulen ɗakin ya yaye, ya doge a baƙin ƙofar, yana kallona.
"Dan ubanki ashe da gaske ne ke aka gani ɗin kenan?" Ƙunshin kaya na dake ƙasa ya duba, ya ɗago ya zuba ma mahaifiyata idanu. Dani da'ita duk kawunanmu a sauke suke.
"Ta Asibi, yaji Lailan tayo shine kika bata wajan tsaiwa, kin tsaya sauraronta kenan ko, sabida zaki bata mafita?".
"A'a Malam Haram giya a gidan liman. Ban tsaya naji komai ba, kuma yanzu zata koma dama. Laila ɗauki ƙunshin kayanki ki koma ɗakin mijinki, aljannarki tana ƙarƙashin tafin ƙafarshi, kiyi mishi biyayya. Duk macen duniya da kika ga tayi lib a gidan mijinta, haƙuri take yi, kuma tana duba makomar rayuwar yaranta. Aure wata tara, baki taɓa zuwa ganin gida ba sai yaji? Wallahi in kika sake yin wannan kuskuren ni da ke ne, tunda ko saɓani baki taɓa ganin mun samu da mahaifinki ba, ballantana harta kaini ga yin yaji." Cewar mahaifiyata kenan. Da jin muryarta cike take da tsantsar tausayina.
"Au jawabi ma kike yi mata? Bari kiga."
Shigowa mahaifina yayi, banyi auneba ya rufeni da duka takota ina. Ko tausayin abunda ke ƙunshe a cikina baya ji. Wai me yasa maza suka ɗauki mace tamkar baiwar da su ka siyo a kasuwa da silalla danta bauta musu ne?" A guje na fita da ƙunshin kayana, nama mance cikine a jikina, tsabaragen kaɗuwar da nayi. Da Kishiyar mahaifiyata naci karo a tsakar gida. Ina wuce ta nayi da mugun gudu. Mahaifina ya biyoni da mugun gudu shima har waje. Gudu nake yi sosai yana bina, ina kukan fitar rai, sai da mu kai nisa, sai naga mahaifina ya dakata., Yana nuna ni da karar dake hannunshi"
Tsaiwa nayi nima na dinga sauke numfashi, ga wani irin haki da yake ta taso mun, irinna masu tsohon ciki. Haka naita dawowa baya cikin jan ƙafa, har zuwa tashar (Bodi) Keken shanu.
Malam zaka ƙarasa Ƙauyan unguwar Alƙali?"



Kauyen Unguwar alkali dake qarqashin karamar hukumar Bakori ta jahar katsina. ya kasance kauyene daba makarantar boko, babu ta addini, ba su da wutan lantarki, ba asibiti, ƙauyene dai irin ƙayau ɗinnan zamu iya cewa. tunda ko ilimin addini bai wadacesuba, sannan basuda wadataccen ruwa haka suke rayuwarsu.
A qauyen sau daya ake aurar wa shine lokacin kaka wato hatsi yadawo gida, suna noma sosai da sosai. In aka tashi biki, Abokan ango suke girka abincin daza aci aranar daurin aure wannan al adarsu tun iyaye da kakanni in aka kai amarya da yamma, to adaren ranar akwai wasan da suke yi tsakanin abokan amarya, da abokan ango, Wanda abokan ango zasu zuba kudi, na amarya ma zasu zuba. Wanda nashi yafi yawa to shi ya ciri tuta, za kuma a yi mishi kyauta ta kayan noma, ko buhun masara, ko dawa, ko gero. Wannan kenan.
Dubana matuƙin bodinnan yayi, yace.
"Gaskiya bazan ƙarasaba, iyakacina Rimi nan dandali, anan zan tsaya." Bance mishi komai ba na shiga cikin Bodinnan na zauna. Mata ne su biyu a cikin Bodin, ko wacce da goyo a bayanta. Gaggaisawa mu ka yi da matannan. Sannan mu ka ci gaba da zaman jira, saida muka cika mu goma cib matuƙin Bodin ya ja linzamin bakin shanun suka soma tafiya." Tafiyace mara sauri sam, dan hanyace mai cike da ciyayi, da gonakai, da kauci. Baka jin ƙaran komai a hanya, sai haushin karnuka, da kukan kwaɗi, da kukan gyare. Da duk wata dabba da dare ne yake zama rana a wajanta. Tsoro ne fal raina, dan muna fama da mayu sosai. Munyi tafiya mai ɗan karen nisa kafin muka iso Rimi dandali. Sai lokacin na sauke ajjiyar zuchiya, dan ina jiyo hayaniyar samari da ƴan mata, ga hasken wutar kara ina hangowa. A hankali na sauka, dan jikina yayi mugun laushi, ga ƙafata bata da wani ishashshen lafiya guda ɗaya, ta ɓarayin hannun dama. A bakin dandalin na tsaya, wajan masu sai da ƙwalam da maƙulashe. Dangin Algaragis, carbin malam, hana kwalla, alawar ɗinya, ɗan ta matsitsi, kwaskwaro, kantun riɗi, tsami gaye, ƙurmus, hallaka kwabo. Ga ɓangaren kuma masu, ɗan gauda, bagalaji, tako, rama, dinkim, ɗan malele, wara, da sauransu.
Ke bani Tako na sile biyar."
Hannu nasa a cikin lalitata na kwaso tsaabar dake ciki, na ƙirga tsabobinta sile biyar na bata, ta zuba mun tako a leda, harda ƙara mun mai da albasa mai lawashi." Tako wani abin maƙulashe ne na katsinawa, anayin tako ne da kofaton dabba, saniya, rago, akuya. Katsinawa suna mugun son tako. Duk da gidan da ake sarrafa tako baya ko iya shiguwa ta daɗi tsabar wari. Ina tafe ina cin tako na, na ɗaura ƙunshin kayana a kaina. Wani ruwane, naji yana bin ƙafata dalalala, kuma kamar ruwan yana da ɗan yauki. A haka dai naci gaba da jan ƙafata a hankali. Wata ƙatuwar mage ce tazo ta wuceni. Gabana ya yanke ya faɗi, yaron dake cikin cikina shi kanshi saida ya zabura.
"Laila Uwar maza" wannan magen naji ta faɗa, da wata dattijuwar murya. Nan na ya da ƙunshin kayan nawa na ari na kare. Gudu nayi sosai, ta tsakiyar maza masu kwana a ƙofar gidajensu na ratsa na shige gidan aurena a guje." Tsattsallake mata, da yara, dake kwance a tsakar gida nayi. Dan tsakiyar lokacin zafi muke yanzu, ɗaki baya shiguwa, garin Katsina ƙasace mai zafi, kasancewar tana maƙwabtaka da ƙasar dake da sahara." Garam na tura ƙyauran ɗakina na shiga."
Shehu na gani a kwance a maulidi na, +gado mai rumfa) Babu ko wando a jikinshi, ya shirɓine jikinshi da man shafawa mai gurguwa, sai wasa da jikinshi yake yi, a ƙoƙarinshi na son gamsar da kanshi." Kuka na rushe dashi kawai, ga wani irin kaɗuwa da hantar cikina take yi, marata ma sai tsungulina take yi.
Da sauri Shehu ya diro a gadonnan, ya riƙoni yana ɗan jijjigani.
"Manene Laila, ko Babane ya biyo ki da gudu har nan?
Bai bani zarafin yin magana ba, ya shiga laluben hakkinshi. Tsabar takaici, ban iya cewa dashi komai ba, a halin da nake ciki ya shiga biyan buƙatarshi, wanda hakan ya ɗebemu mintici da dama, marata ce ta shiga ciwo ganga_ganga, bayana da ƙafata mai lalura sai amsawa suke yi. Nayi yunƙurin ture Shehu amman na kasa. Ƙara na saki mai amon da sai da kowa ya jiyo. Da sauri Shehu ya sake ni, ya rarumi wandonshi da ƴar shararshi ya saka.
Wayyo zan mutu, Shehu ka kirawo mun Matar malam, haihuwa zanyi, Shehu zan mutu." A gaggauce Shehu ya fita tsakar gidan, ya barni a kwance a leda ina juyin azaba."


Mrs Bukhari ce


Ku kasance tare dani, dan karanta wannan littafin mai ɗauke da salo irin na rayuwar iyayenmu ta shekarun baya. Labarine mai ɗumbun darasi. Duk macen data karanta littafinnan na tabbatar zata ilmantu da ilimi mai tarin yawa.


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_

*Mrs Bukhari ce 👉🏾👉🏻*
MATA...
IYAYEN..
GIJI


BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)




LAMBA TA BIYU
SAMFOTI


*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*




MATAR MALAM:
Fitowarta kenan daga sakaki ( Bayan gida) ta jiyo ihun Laila. Sai kuma taga Shehu a ruɗe ya fito.
"Shehu lafiya, Laila ta dawo ne, ni naji ihu ko?"
"E matar Malam, naƙuda inaga ta soma, sai juyi take yi aƙasa." Butar hannunta ta ajjiye tace.
"Ka tashi Mai riga, da Iyami maza. Bari ni in soma zuwa." Tana kaiwa nan ta shige ɗakin Laila, shi kuma ya wuce Shiyyar su Baba Mai riga mahaifiyarshi.
"Baba Mai riga, Baba"
"Kaik waye wannan haka nenene?"
"Shehunki ne Baba mai riga " Da sauri ta miƙe zaune, tana mutstutstsuke idanu.
"Yaya dai Shehu, ko duk a kan tafiyar Lailan ne? Infa iyayenta na gidi ne, to wallahi cikin darennan zasu dawo da'ita ko ka gansu asubar fari, abun kunya kuma ta riga data jama kanta, harfa yaran data haifa za'a iya goranta musu in sun girma. Kama kwantar da hankalinka kaji ko?" Shehu ya sosa kai yace.
"Tama dawo, naƙudace ta tasan mata Baba. Yanzu haka matar Malam na kanta." Ba shiri ta miƙe daga ita sai ɗaurin gaba, mayafi ta jawo a igiya, ta wuce ta Bar Shehu tsaye a wajan. Iyami, da Laure surukanta, facalolin Laila ta taso, suka shiga ɗakin Lailan a tare."


Laila;
Ina zaune dirshen a kusa da kwallayen dake jere hawan hawa a ɗakina, sai yarfe hannaye nake yi, idanuwana sunyi ƙwala_ƙwala, jikina kuwa a jiƙe sharkab yake da ruwan jiɓi."
"Ki durƙusa Laila, ba zaki zauna dirshen haka ba, saiki kashe abunda ke cikin naki." Da jin haka ba shiri na durƙusa, hannayena duka biyun a dafe a ƙasa. Kafin kace me, ɗakinnan ya cika da mata, duk sun tsaya akaina. Ga wasu a barandar ƙofar ɗakin, duk sun tare mun iska.
"Iyami maza ki samu Shehu, yaje ƙwar gida ya taso Malam yai mata rubutu tasha, sai kiga yanzu ta samu kai. Sannan yaje gidan Unguwar zoma ya tado ta itama. Da hanzari Iyami ta fita, ta faɗama Shehu saƙon da aka bata ta bashi. Da sauri ya fice zuwa waje, ita kuma ta dawo ciki. Kamar minti talatin haka, ina tsaka da cin kwakwa. Shehu ya kawo rubutunnan, Unguwar zoma itama isowarta kenan. aka ɗirka mun, amma shiru kake ji. Awa ɗaya awa biyu. Na gama galabaita na fice a duk wani hayyacina. Sai sannu suke yi mun. Ni kuma haushi suke bani ma.
"Mai riga a samo barkono, sai anyi mata hayaƙi ina ganin." Cewar unguwar zoma kenan." Baba mai riga tace.
"Laure a duba kaskon nan baya rabo da gaushi, a ɗebo, saiki kawo barkono guda bakwai."
Azaba kan azaba kenan. Dan mugunta haka anguwar zomannan ta rufeni da zane, ta zuba barkono a ciki ƙaramin kasko, ta ajjiyeshi gabana. Nan take yajin barkono ya turniƙeni. Kowa ya dare a ɗakin, daga ni sai ita. Tari nake yi ina zubar da hawaye da majina, sai atishawa nake yi, kamar wacce ta hau na kada. Ƙashin kwankwasonane naji ya buɗa, wani irin nishi ne naji yana tunƙudo ƙanshi da kanshi. Wani abune naji ya tokareni. Wannan anguwar zoman na haskawa, sai naji ket, tasa aska ta ƙarani. Hannu tasa ta jawo jaririn.
"Ayririri yiriririhhhh ta samu kai"
Ɗakin nan ya kuma ɗinkewa. Mabiya kuma akayi akayi ta fito abu yaci tura. Muciya unguwar zomannan muguwa tasa aka ɗakko mata. Ai kuwa haka taita turbuɗamun a baki, ina kakarin amai.
Mabiyar ce ta faɗo, take aka yanke cibi.
"Subuhanallahi mai riga me zan gani, kinga aljanin da surukarki ta haifa kuwa." Ras naji gabana ya tsinke ya zube. Aljani kuma? Na nanata a zuchiyata. Ina durƙushe jaririna sai canyara kuka yake yi. In wannan ta leƙo saita matsa, sai waccan ta leƙo itama saita matsa. Ni dai tsabar kunya kaina yana ƙasa, amma zuchiyata sai daka take faman yi.
Baba mai riga ce ta tsugunna, tasa hannu tana duba jaririn. Ɗaga kai tayi ta dubi Matar Malam tayi shiru, tama rasa ta cewa. Jaririna kuwa sai canyara kuka yake yi. Ƙauna da tausayinshi sai buga mun tambari yake yi. Ina ji ina gani aka rasa wanda zai ɗaukeshi, ko ya bani umarnin rungume kayana, inna ɗago kuma ace nayi rashin kunya a gaban surukai, da matan Yayun miji."


Shehu:
Yana zaune a kututturen itacen dake ƙofar gida. Shi da abokanshi biyu. Haruna, da Hamza. Kukan jariri suka soma jiyowa, yanata canyara kuka.
"Inya_inya_inya_inya"
"Anya kukannan da baƙon duniya yake yi na lafiyane kuwa? Naji kukan yai yawa. Inji abokin Shehu.
"Nima haka nake ji dai. Amma bana shiga ciki ba, su Laure su sani a waƙa in suna dakan dawo a tsakar gida.
Malam ne ya tawo shida Baba Kabiru mahaifin Shehu, wanda akafi kira da Baban Yara. Malam yace.
" Kai Shehu ka leƙa masu haihuwarna kukan kamar bana lafiya ba. Kafin Malam ya rufe baki, zuruf Shehu ya shige cikin gidan.

Laila:
Hawaye nake ta fitarwa na tausayin jaririna. Muryar Shehu muka jiyo yana tambayar Iyami matar wanshi ko lafiya?" Iyami tace.
"Wani babban al'amarine mai cike da almara jaririn yake tattare dashi Shehu, danni tunda uwata ta haifeni ban taɓa cin karo da jariri irin na Laila ba. Amma duk yanda akayi ɗan ruwa ne, ko kuma mayu sun shafeshi, ko kuma aljanu sunyi mata canje.Tana kaiwa nan tasa hannu ta ɗauki jaririn tasa akan tsumman zani. Shehu kuwa dajin haka ya fita guiwa ba ƙarfi. Ajjiyar zuchiya na sauke. Baba mai riga tace.
"Allah ya baki lafiyar shayarwa Laila. Tana kaiwa nan ta juya tayi hanyar fita. Surukan gidan suka mara mata baya. Ɗakin ya rage dani ni sai matar Malam, Sai Iyami.
"Tashi zauna Laila, bari insa a hura wuta a ɗaura ruwan wanka. Iyami a nemi tsumma a naɗe mahaifarnan da safe sai aba Shehu ya birne. Iyami tace.
"To matar Malam, amma ruwan wanka kam inaga bojuwar ta juya yanzu, sai dai a kwashe a kwatanniya kawai. Tun sanda take kan guiwa nasa Laure ta hura wutar.
Ina miƙewa jini kamar jira yake yi saiya ɓalle, take na nemi ganina na rasa, yarab na faɗi idanuna na shirin kakkafewa. A guje Iyami ta kirawo Baba mai riga da Shehu. A lokacin aka kwanɗa kiran assatu.
Dishi_dishi nake ganin Shehu da jaririna wanda ko fuskarshi ban kalla ba. Da sauri Laure ta shigo hannunta riƙe da kofi.
"Ga mandan Baba na jiƙa"
Manda aka ɗagani aka ɗuramun. Kamar ɗaukewar ruwan sama jini ya tsaya cak. Daga nan ban sake sanin ina nake
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment