Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallama masa ina sauraron maganganun da yake furta min, ba yau na saba jin haka daga gare shi ba sai dai kalaman yau sun sha bambam da waɗanda yake sanar min. Ina yunƙurin yi masa magana cikin tsawa na ji ya furta, "Ki tashi na ce ki aiwatar da ƙudurunki cikin jarumta domin ke ba ki kasance gajiyayyiya ba." Tamkar wacce aka ƙarawa ƙaimi haka na ji wani masifaffan ƙarfi ya mamaye ilahirin jikina, a zabure na waiga wurin Barde da ya yi yunƙurin kawo min duka sai dai ɓarin makauniyar da na yi masa a fuska ne ya azabtar da ruhinsa. Ƙaraji yake tamkar wanda ake zare wa rai saboda azaba, kamar yadda na ƙudura a zuciyata haka na sake jadaddawa. Daga jikin ƙuguna na zaro wata ƙanƙanuwar wuƙa na ƙarasa gaban Barde kafin ya yi wani yunƙuri na kauda kai gefe haɗe da tsige al'aurarsa daga gangar jikinsa. Maƙarrabansa su baƙi-baƙi na ganin haka kowannensu ya cika wandonsa da iska saboda sun lura a yunwace nake da su ina iya tsalle na dira a gabansu na yi musu makamancin abin da na yi wa Barde, saboda duk tafiyarsu ɗaya hallayarsu ɗaya duka tare suke aikata kowanne irin ɓarna sai dai Barde ya fi su yin ƙaurin suna wurin aikata badaƙala.

Ina yunƙurin juya wa wurun tawagar da ke farmakar rayuwa na neme su na rasa tamkar ɗaukewar ruwan sama, jinin da ke ci gaba da zuba daga jikina ne ya haddasa min raunin garkuwar jikina, na fara takawa ina layi ga idanuna da suke yi mini dishi-dishi har ta kai ba na iya bambamce takamaimar hanyar da zan bi na koma ga muhallina. Kwatsam! Ban yi aune ba na ji na faɗa jikin makamanciyar halitata ta bil'adam wanda hakan ya haddasa min sakin ragowar jikina a jikinsa. Muryarsa ba baƙuwa ba ce a gare ni hasali ma takan faranta zuciyata domin shi ɗin wani ɓangare ne daga tsakin zuciyata, ya kasance jini da tsokata ta yadda a kowanne hali nake ciki ina iya tabbatar da siffarsa mai cikar haiba da kamala. Idanuwana ne suka fara lumshewa, na riski ya huro min iskar bakinsa akan fuskata yana faɗin, "Abar bauta ta dafa miki a duk lamuranki ya ke sarauniyar maharba amanar Goje, ba kyau ba daɗi murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya. Wane Mutum wawan mutum rana mai haske duniya kowa ya ƙarasa a bar shi ya kawo ƴar tsatson maharba. Cau cau cau cau sai ke Damisa amanar Duna, da wuya a dajin Gurɓu da wuya a dajin Dagumba wata wuyar sai mun tsallaka dajin Bagege. A lafiya shawarar Goga a lafiya amanar Goga, a lafiya wakiliyar Goga ko yau ko gobe kwarankwatsa dubu ko bakya nan ina yi miki yaƙi." Kirarinsa ne ya sake ƙarfafa zuciyata na ɗago a wahalce na jingina kerena (Ɗaya daga cikin makamin maharba ne.) A jikin Barandaminsa cikin amsa gaisuwa irin tamu ta Maharba na furta, "Sa'a dai mai dawa amanar Shamuwa amana sai ɗan amana, amana ta kai maka har dajin Gaduru." Ina rufe baki ya cicciɓe ni ya ɗora a kafaɗa sannan ya wuce gida da ni. Tun a cikin dajin na ji yana yagar ganyayen magunguna da zan yi amfani da su, muna ƙarasawa gida aka kwantar da ni akan fatar kura wacce ta zame mana mashinfiɗin da muke hutawa. Hayaniya ce ta fara tashi a wurin matasa maza da mata suka cika damƙam, ganin halin da nake ciki ya sa Mahaifina ya sallami sauran mutanen da ke tsaitsaye a kaina, cike da takaici ya tsugunna a daidai kaina ya yin da ya yi tozali da irin jini da yake fita daga jikina sakamakon mummunan saran da Barde ya yi, yanayin fuskarsa ne ya bayyana min ɓacin ran da ya ziyarci zuciyarsa. Runtse ido ya yi ya furzar da iska mai zafi sannan ya furta, "Abar bauta ta ci gaba da dafa wa lamuranki ya ke sarauniya. Haƙiƙa ina baƙinciki raunin da yake ziyartar ruhinki, wanda dalilin haka yake sa a yi yunƙurin yin galaba a kan ki." Hannunsa na kama da hannuwana biyu, ina jin hawayen baƙinciki na neman ɗiga daga idanuna. Sarewa da karaya ba hali ko ɗabi'ata ba ce amma a wannan karon ina jin ƙwarin gwiwata ta yi rauni fiye da kullin, Mahaifina na lura da halin da nake ciki don haka ya shafa kaina tare da furta, "Namiji ba ya sarewa da ƙarfin magauta. A zahiri ke macece amma ni nasan nagartaccen jarumin namiji na haifa. Kada ki taɓa bari wani ya lura da rauninki, ko da wasa kar na sake ganin ruwan hawaye a ƙwayar idonki domin zai ba wa magautanki ƙwarin gwiwa a kan ki har su yi nasara su kai ruhinki kushewa." Daga wurin da nake kwance na dube shi sannan na furta, "Wuya bata raunata zuciyar 'yan maza koda kuwa a tsakiyar rundunar mayaƙan maƙiya ne, raunina ya dogara a kan ɓoyayyan lamarin da yake faruwa da ni ta yadda ba na iya mallakar gangar jiki da ruhina. Na yi rantsuwa da abar bautar da ke raya dare zuwa rana ta samar da yalwatacciyar ni'ima da kyautata noma, ba zan sake bayyana raunin da zai bawa magauta dama akaina ba koda kuwa rikicitaccen al'amarina zai ci gaba da farmakar rayuwata." Mahaifiyata ce ta miƙo masa ƙaron marke da ganyen zaƙami, ya saka su akan fatar zomo ya ƙwanƙwasa su da dutse sannan ya fara shafa min a wurin da yake zubar da jini. Ba a ɗauki lokaci ba jinin ya tsaya na riski muryar mahaifiyata tana faɗin, "Baushe me za a yi wa yarinyar nan a kan karyewar asirin jikinta, tun da abar bauta ta wanzar da ruhina ban taɓa bada maganin ƙarfe ya karye ba. Amma yarinyar nan babu abin da ba a bata ba duk lokacin da wannan al'amarin zai same ta sai ta rasa duk wani tsarin jikinta." Da kansa ya ɗauke ni ya kaina cikin bukkar mahaifiyata sannan ya tsaya a bakin ƙofar bukkar yana faɗin. "Kyauta ita kaɗai gare ni a faɗin duniya, don haka ba zan yi ƙasa a gwiwa ba don sake roƙar mata abar bauta akan ta shiga lamurunta idan akwai zunubin da ta aikata ta shafe mata shi. Ban san zunubin da ta aikata ba da farauta take yi mata gudun mutuwa, ban san ya aka yi tsatson maharba yake son bijirewa zuri'arsa ba. A duk binciken da na yi babu tasirin tsafi ko asiri a jikin Kyauta, rauhanai sun sanar mini akwai wani ɓoyayyan al'amari game da ita sai dai sun garara sanar da ni komai daga cikin al'amuranta. Zan ziyarci abar bauta da mataimakanta ta taimaka min domin ita ce madogararmu mai taimaka mana da kawo mana mafita, ba zan rasa ki ba Kyauta domin lokacin mutuwarki bai zo ba har sai mun shiga Dajin Mugazu ta karɓo kambun sarauta da hannunta." A hankali na yunƙura na tashi zaune azabar da nake ji ta sa na cije bakina sannan na furta, "A taimaka a sada ni da Abar bauta akwai maganar da nake son tattaunawa da ita." Da mamaki ɗauke a fuskokinsu na ga sun kalle ni, Mahaifiya ta ƙaraso wurina ta ɗago ni tana cewa. "Abar bauta za ta saka miki albarka ziyararki babbar nasara ce albarkacin tsafi da farauta." Mahaifina ne ya kama ni muka wuce tsaunin Abar bauta ya yin da Mahaifiyata ta ci gaba da ba wa Kandala kulawar da ta da ce tana gasa ta da ruwan zafi don warkewar raunin da ke ƙasanta.

Daular Sarki Damina.

Duk yadda Mai babbar turaka ta kai ga ƙin amince wa da buƙatar Sarki fir ya ƙi sauraronta, da ƙarfin tsiya ya fisge ta ganin tana son kunto masa matsala ya cicciɓe ta ya ɗora a kafaɗa. Ciccila ƙafa ta rinƙa yi tana dukan kafaɗarsa bai saurari roƙonta ba ya fice da ita, a tsakar gidan keɓaɓɓan gida ya dire ta sannan ya kalli waɗansu ƙosassun dakaru masu siffar adawa ya ƙwala musu kira, tun bai rufe baki ba suka ƙaraso wurinsa sannan ya ce, "A gaggauta sada ta da Yarima almuru ya ƙarato zan kai gaisuwar ibada da roƙon ruwa." Kuka Mai babbar turaka take rusawa kamar ranta zai fita, yana shirin tafiya ta rarrafa tana jan ciki haɗe da ruƙo ƙafarsa tana faɗin, "Damina ni ce fa mahaifiyarka wacce ta ɗauki cikinka tsawon lokaci yanzu da kanka za ka sada ni da Yarima ya haike min ina ji ina gani?" Taɓe baki Sarki Damina ya yi ya tsugunna sannan ya ruƙo haɓarta ya furta, "Ban fiya son ja'inja da ke ba don ina matuƙar ganin mutumcinki." Ya ɗago yana kallon dogaran tare da furta, "A yi gaggawar wuce wa da ita." Daga haka ya fisge ƙafarsa mai babbar turaka ta faɗi gefe haɗe da kifa kanta a ƙasa tana ci gaba ta rusa kuka mai cin zuciya. Da ƙarfin gaske suka fisge ta duk irin magiyar da take yi musu bai sa sun saurara mata, saboda sanin kansu ne matuƙar suka saɓa wa umarnin Sarkin Damina tabbas za su tsinci talatarsu a laraba domin na su hukuncin sai ya ninka nata sau dubu.

Suna gab da shiga ɗakin, Mai babbar turaka ta dubi Nalami dogari cikin karayar zuci ta furta, "Ka taimaka ka bar ni ko na taƙi kaɗan ne zan bar musu wasiyyar da ba na son ku buɗe ta har sai bayan babu rayuwata. Jikinsu ne ya yi sanyi duk da kasancewar ba sa daga cikin masu tausayi, ganin tausayi na neman tasiri a zuciyarsu ya sa suka fisge ta da ƙarfin tsiya. Kamar mayunwacin zaki haka Yarima ya kurma wata uwar ƙara haɗe da janyo Mai babbar turaka da ƙarfin tsiya, ganyan da ke maƙale a ƙugunta da ƙirjinta ne ya faɗi gefe Yarima ya haɗe ta da jikinta tare da sauke buƙatarsa a haukaca akanta. Cikin fitar hayyaci ta riƙa ambatar sunan Damina tana tsine masa da aibanta shi da miyagun kalamai marasa daɗin saurare, sai da Yarima ya dawo cikin hayyacinsa ya fahimci Mai babbar turaka ta galabaita. A wahalce ta dubi Yarima yana faɗin, "Yarima mahaifinka ya yi min abin da ba zai taɓa albarka ba, akwai laƙanin da nake son taimakon wannan daular da shi amma yana cikin turakata..." Da sauri Yarima ya tallafo kanta yana faɗin, "Laƙanin me ye kar ki tafi ba ki gaya min ba." Cikin kakari ta furta, "Ka tabbatar da ka yi tozali da sabuwar sarauniyarmu kuma ita ce za ta ɗauko..." Daga haka harshenta ya sarƙe idanunta suka ƙafe ta faɗi matacciya.

Zuwanmu tsibirin keda wuya muka samu dubbannin jama'ar yankinmu sun yi dafifi akan tsiribirin, da yake duk ranar talata da daddare muna taruwa akan tsibirin domin miƙa buƙatunmu ga abar bauta. Mun yi amanna akan duk wanda ya faɗi buƙatarsa a kan tsibirin tabbas buƙatarsa za ta biya. Kasancewar sun lura da halin da nake ciki ya sa suka buɗe min hanya muka wuce don isa ga abar bauta saboda akwai ƙudurin da nake son sanar da ita duba da rikitattun al'amuran da suke baƙuntar rayuwata. Muna gab da ƙarasawa muka riski sautin wakiliyar Abar bauta, ba mu sake tsinkewa daga lamarin ba sai da muka yi tozali da ita ta fito matsayar da ko a tarihin rayuwa ban taɓa jin ta fito harabar wurin ba. Kamar ɗaukewar ruwa sama haka wurin ya yi tsit kowanne ya baje majiyar sauti da maganansa, ko a mafariki ban taɓa tozali da siffar wakiliyar Abar bauta ba sai dai labarin da magaba suke ba mu akan samuwarta da tasirinta ga rayuwarmu.Tun bayan kafuwar yakinmu a tarihin da muka taɓa fuskanta, abar bautar wancen yankin bata taɓa fito wa ba sai a ranar da wani mummunan al'amari ya faru da su wanda sanadin haka ya sa aka kafa tarihi har muka mayar da ranar Talata a matsayin ranar karɓar addu'a kuma ranar biyan buƙata, domin a cikinta ne al'ummar Maharba suka samu ƙarfin iko da nasara akan Baƙar Daular da ke gaba da yankinmu. Sannan mahaifina ya tabbatar min a bisa al'ada duk lokacin da Abar bauta ta bayyana akwai wani mummunan al'amari da zai faru wanda zai hargitsa al'ummarmu. Ban gama dawo wa daga duniyar tunani ba na riski sautinta tana faɗin, "Ya waɗannan al'aumma yau na bayyana kaina ne domin na shaida muku mummunan al'amarin da yake tunkaro mu kwatankwacin mummunar ƙaddarar da ta faru a baya. Kogon bincike ya ƙone ƙurmus! Hasken wutar abar bauta ta ɗauke. Buzun zakin abar bauta ya miƙe yanzu haka yana cen yana fidda aman wuta.

A yau na tsaya a gabanku domin na tabbatar muku da bala'in da yake tunkaro rayuwarku, ga taron rundunar baƙar inuwa tana tunkaro mu don haka ya zama wajibi mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu sake tserartar da yakinmu domin gujewa abin da ya faru ɗaruruwan shekarun da suka gabata, a zahiri dukkan alamun da suka bayyana a baya sune suke sake bayyana a wannan lokacin domin yanzu haka tazarar da ke tsakaninmu da wannan baƙin yaƙin bai fi taƙi kaɗan ba. Ina jin tsoron kada farmakin Baƙar Daula ya wanzu a gare mu duk da muna da tsarin da ko tsuntsu ba za su iya gani da idanunsu ba matuƙar ya kasance ɗaya daga cikin ahalinmu na Maharba." Ras! Na ji gabana ya faɗi musamman da na tuna Kandala bata daga cikin zuri'ar Maharba, hasalima tsarinmu ya katange da ita." Ina tsoron kar wani mummunan al'amari ya faru da ita. Hankali a tashe na furta, "Ba zan bari ba Kandala! Ba zan taɓa bari a cutar da ke ba tun da kaina na ɗauki alƙawarin kulawa da rayuwarki. Zalincin baƙar Daula ba zai taɓa ɗarsuwa a kanki ba koda zan rasa rayuwata tun da ni ce sillar salwantar iyayen da suka haifo ki don haka zan bada jini da ruhina akan ki.

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

4


*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

Gudun kada Abar bauta ta fahimci abin da nake faɗa ya sa Mahaifina ya damƙi hannuna mara ciwon sannan ya yi min raɗa a kunne da cewar, "Ɗaure bakinki ya fi miki alheri akan mummunan fushin da abar bauta za ta yi da ke." Idanuwana na ɗago ina kallonsa, har ƙwayar idona ta ciko da ƙwallah sai na haɗiye abina don na tuna gargaɗin da mahaifina ya yi min akan zubar ƙwallata. Muryata na rawa na furta, "Ina gudun abin da zai faru da Kandala don ka san tsarinmu ba zai taɓa tasiri a tattare da ita ba. Ta kasance bata daga jinin Maharba da mafarauta, idan baka manta ba da bakinka ka gaya min Abar bauta ta tsarkake iya zuri'ar wannan yankin namu ne kawai, ka na ganin idan wani abu ya faru da Kandala zunubi da munanan abubuwa ba za su ƙaru a kaina ba duba da abubuwan da suke faruwa da ni? Na yi sanadiyar mutuwar iyayenta, kuma tun da dokar dajin na lashi aniyar kare haƙƙinta kamar yadda iyayenta za su kula da ita. Don Allah kada ka dakatar da ni saboda ina tausayin rayuwarta, ta rasa iyayenta a yankinmu, ta rasa zuri'arta a yankinmu, ta rasa budurcinta a yankinmu shin wannan kaɗai bai isa ya sa a tausayawa rayuwarta ba?" Jikin mahaifina ne ya yi sanyi tamkar wanda aka zare wa laka, ya dube ni haɗe da sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, "Shi kenan Kyauta! Abar bauta ta kawar da muguwar rana a kan ki, za ta shiga lamuranki ba za ta da mu kunya ba albarkacin tsafi da farauta." Jin daɗin kalamansa ya sa na sakar masa murmushi a daidai lokacin na ji Abar bauta ta sake cewa, "A daren yau zuwa gobe za a katange yankin nan daga baƙar guguwar da ta taso mana. Ya zama wajibi a zubar da jini ga rauhanai don su sake dafa mana akan sha'anin rayuwarmu, wannan shi ne abin da zan iya sanar da ku don na taimaka muku. Idan kuka bijirewa umarnina zan iya sauya sheƙa daga wannan yankin zuwa wani na kafa daulata, munanan abubuwa za su yi ta faruwa a kan ku haɗe da farmakai daga sauran ƙasashe musamman Baƙar Daular da kullin burinta ta shafe tarihin Maharba a faɗin duniya." Cikin aminta da kalaman abar bauta da ba ta yarda ya sa muka amsa mata da faɗin, "Uwar gijiya abar bauta ta dafa mana ta shafe matsalolinmu, mun dogara da ke don haka ke ce mai yaye mana damuwa da ba mu waraka a kowanne lokaci. Mun ji mun amince za mu yi abin da kika ce domin mu ma su bin umarninki ne, mun dogara da tsafi da sihiri sune madogarar abar bauta ita kuma ita ce madogararmu a koyaushe."

Fuskar abar bauta ce ta fasalta irin farincikin da ta yi da mu, don haka ta ɗaga hannunta sama ta wara ƴan yatsunta nan take wani mulmulallan haske ya dira a kai. Ta dube mu ta sake kallon haske sannan ta furta, "Albarkacin tsafi da sihiri, albarka da tabbata a gare ku ya ku wannan zuri'a ta mafarauta masu albarka. Shin akwai mai son a bincika gobensa don sanin abin da zai faru da shi? Akwai mai ciwo mu warkar da shi? Ko akwai mai son mu ninka nasara da tsaririn tsafinsa don ya gagari kowanne rauhani a dajin farauta?" Tun bata rufe baki ba mahaifina ya ɗaga hannu sama, kasancewar mahaifina sarkin Maharbin yankinmu ya sa mutanen garinmu suke matuƙar ba shi girma domin mutum ne mai adalci da son talakawansa. Ganin mahaifina ya yi magana ya sa alummar da ke wurin suka fara kai masa gaisuwa cikin girmamawa, "Sarki ya zo mutuwa ta zo, mutuwa mai kai ƴan maza ƙasa ko da son rai ko babu. Abar bauta ta riga da ta buɗa maka kwarankwatsa dubu sai ka gama lafiya amanar ƙauran garin Dume, amana ta kai mana amana ta kai maka mun baka amana ka ba mu gaskiya ko sun ƙi ko sun so sai mun bar wuya a dajin Gagarar maza. Sa'a dai maza sa'a dai uban dawa wuya mai sa ƙarar kwana ga ƙananun maharba uban dawa sai ya kai labari ko da daɗi ko babu." Sunkuyar da kai Mahaifina ya yi alamar gaisuwar tana kai masa sannan ya ɗago ya amsa musu da cewar, "Dawa dai mazaje! Ba kyau ba daɗi, idan wuya ta yi wuya yaro ke guduwa ya bar babansa. Kwarankwatsa dubu ranar Talata mai zuwa sai na kai hallitun dawa dubu biyar da ɗoriya ɗan butar uwa, Abar bauta ta buɗe mana dai." A hankali muka riƙa takawa har kan tudun tsira sannan mahaifina ya tura ni daga gabansa kaɗan ya fara yi mata magana."Abar bauta ta yafe min kada ta yi fushi da ni a yau ma na sake dawowa da 'yata Kyauta domin ta shiga lamuranta. Ɓoyayyun al'amura na sake bayyana a tattare da ita, don haka na sake dawowa da ita don na ji ko akwai wani taimako da Abar bauta za ta yi domin Kyauta ta rinƙa rayuwa kamar kowa." Daga can duhu-duhun wurin da mutane ke tsaitsaye na hango wani matashin saurayi yana ƙara kutso kai sakamakon jin bayanin da Mahaifina ya yi, muna haɗa ido ya sakar mini murmushin da ban san dalilinsa ba, sai dai abin da ya ɗaure min kai ba kasafai na cika tozali da matashin ba sai a ranaku makamantan waɗannan da muke kai wa Abar bauta kukanmu.Hasali ko kaɗan ba ya daga cikin zuri'armu domin gabaɗaya mun san kanmu waɗanda suke rayuwa a yankin. Ina cikin wannan tunanin na riski muryarta tana faɗin, "Akwai ɓoyayyun lammura game da Kyauta don haka nake gagara bincika abin da yake damunta, a duk lokacin da na bincika gobenta ba na samun biyan buƙatata. A duk faɗin yankin nan babu wanda zan bincika rayuwarsa ta gaba na samu tangarda sai Kyauta, ina mai yi maka albishir da cewa ita ɗin ta musamman ce don haka waɗansu abubuwa suke baƙuntar rayuwarta. Babban abin da za mu saka a gaba shi ne, mu mayar da hankali wurin zagaye garin nan domin idan muka zagaye gari na yi ammana da tsafi da sihiri babu abin da za same mu." Wurin ne ya yi tsit muna sauraron ci gaban bayanin da abar bauta take. Sai da ta sake hawa can ƙololuwar samman tsauninta sannan ta ci gaba da cewa, "Albarkacin ranar talata da nasarorin da ke cikinta muna miƙa wuya ga alƙaluman tsafi akan zan sanar da talakawa su nemi waɗannan kayan tsarin su aiwatar da shi domin neman warakar su. Da farko za ku saro kan wani ƙasurgumin kumurcin maciji da ke Dajin Bawaya, sai ku kawo min na jiƙa shi da ruwan sihiri haɗe da tumfafiya, idan ya kwana ɗaya a jiƙe sai a dake kan macijin ku samo mana ruwan kogin haladu a wanke idon matasan makafi a haɗa da ƙasar kabarin Jarumi Baushe uban Yaɗiya, idan kuka yi haka ku kawo min na haɗa sauran mahaɗin da kaina. Zan baku shi ku je ku zagaye garin nan da shi kuma duk abin da za ku gani kada baki ya furta ko zuciya ta tsorata, duka waɗannan abubuwan za a same su ne a cikin ƙasa da kwana biyu." Duk da zuciyoyinmu sun fara karaya bai hana mun amsawa abar bauta ba, tana gama jawabin ta dafa raunin da ke jikina haɗe da ɗaura min wata baƙar fata wacce da alama ta baƙar wahainiya ce. Nan take raunin jikina ya warke wani ƙarfi ya ratsa ni tamkar wani abu bai taɓa faruwa da ni ba, daga haka ta sallame mu sannan kowa ya watse gidansa.

Sannu a hankali na rinƙa waige-waige don ganin na lalaubo matashin da nake ɗora zargi a kansa, amma sai haƙana ya gagara cim ma ruwa. Na neme shi sama da ƙasa na rasa! Dama na san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya. A duk lokacin da na yi tozali da shi haka

Please Login or Register in order to submit comment