Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka ɗaiɗaice." Kamar sabon munafiki haka Sarki Damina ya fice sum sum sum rai a ɓace, cike da hargowa ya rufe Dogarawansa da faɗan babu laifin tsaye balle na zaune.

Lokacin da Sarki Damina ya sa aka kai su Mahaifin Kyauta ɗakin duhu gabaɗaya sun gama galabaita saboda tsananin zafin rana da yunwar da take sasaƙar cikinsu, a can tsakiyar gidan masarautar ɗakunan suke. A ƙarƙashin ƙasa aka samar da wurin saboda waɗanda suka aikata mummunan zunubi ko kuma waɗanda Sarki Damina ya yi mummunan fushi da su, baƙiƙƙirin wurin yake saboda babu ɗigon haske da yake ratsawa da ciki. Duk yadda ka kai ga son ganin tafin hannunka ba za ka iya ganin ba balle waɗanda aka saka ku tare da su, sai dai ku riƙa lalubar juna kuma yin magana a haka. Cikin ɗakunan cike yake da kunamu suna harkokinsu kamar yadda kiyasai suke kai kawo a doron ƙasa. Ana saka su ita ce ta fara yi musu marhabun lale ta rinƙa sakar musu cizo ta ko'ina ban da ihun yara da na iyayen su kansu babu abin da kake ji. Da suka lura ihu ba zai kai musu ba haka suka riƙa lalube da hannuwansu da sun ji ƙatuwar kunawa su saka hannu ko ƙafa su murtsuke ta. Duk da haka ko kaɗan ba su tsira ba haka suka haukace saboda azabar harbin da take yi musu, a yammaci zuwa wayewar gari ƙananan yara huɗu ne suka rasu da manya biyu sanadiyyar mummunan harbin da kunamar take yi musu. Washegari suna nan zaune jigun-jigun cikin baƙar azaba suka ji an buɗe ɗakin da suke ciki, sai a lokacin da hasken rana ya hasko suka fahimci a zaune suka kwana har gari ya waye, cike da ƙarajin ban tausayi suka fashe da kuka suna faɗin, "Ku taimaka ku cece mu duk abin da kuka saka mu na aikin wahala mun amince za mu yi bakin ƙoƙarinmu." Badakaren da fuskarsa babu alamun wasa ya furta, "Ba don Sarki Damina ya so ku da rahama ba da a nan za ku dauwamma har sai kunamun ciki sun hallakar da ruhinku. Ya ba ni umarnin a fito da ku zuwa sararin haraba zai rarraba ku gida-gida domin kowa ya san irin aikin da zai rinƙa yi." Saboda murna har kwanciya suka yi suna gode masa suna cikin godiya suka ji ya buga musu tsawa yana cewa, "Yau kwananku nawa rabonku da abinci?" Bakinsu har rawa yake suka furta, "Yau kwana huɗu." Girgiza kai ya yi sannan ya furta, "Idan kun je za ku ci a cen." Daɗi ne ya mamaye zuciyarsu sannan ya buɗe musu suka riƙa fitowa ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda ya san su a baya matuƙar ya gan su a wannan lokacin ba zai taɓa gane su ba, saboda wani irin burɗun-burɗun da jikkunansu ya yi. Da wata irin rama ta ban mamaki da suka yi sun yi wani irin baƙi tamkar waɗanda suka shekara suna matsananciyar jinya.

Sarki Damina na sauka daga tsaunin boka mai zamani kai tsaye gida ya wuce, yana shiga turakarsa ya samu Usaina zaune ta haɗa kai da gwiwa. Duk duniya babu abin da Sarki Damina ya ƙi jini ya ƙi tsana sama da ya ga ran Usaina a ɓace, don haka a rikice ya dube ta yana tambayarta. "Yake faruncikina uwar gida a wurin Damina uwar Yarima bada kanki a sare. Ya ke Hasana shin waye ya taɓa min ke yanzu na sa a sauke min kansa ƙasa ko shi ɗan gidan uban waye, idan kuma bautarwa kike so ki gaya min wanda kike so duk matsayinsa a yankin nan na sa a bautar da shi." Sai da ta goge ƙwallar munafurci sannan ta ce, "A lokacin da Maharban suka shigo Daular nan haka kawai na ji jikina ya ba ni zuwan su babu alheri a ciki, na ji an ce har da wacce ta zo da jariri a ciki ko?" Usaina ta yi tambayar tana ƙura wa Sarki Damina idanu don ta karanci yanayinsa, tun ranar da tawagar farko ta shiga cikin Daular Bawanta mai yi mata leƙen asiri ya ke kai mata ɓoyayyun bayanai, har ta kai ga ya sanar da ita zuwan tawaga ta biyu da jaririn matar nan kafin Yarima ya hallaka shi. Sarki Damina na gama jin bayaninta tsaf ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya sannan ya furta, "Tuni shalelenki ya gama da shi indai wannan jaririn ne." Cikin kissa ta sake tambayarsa nan take ya zayyana mata duk irin kisan rashin imanin da Yarima ya yi masa. Ajiyar zuciya ta sauƙe a fili saboda ko ba komai ta san ta gama da jaririn da Boka mai zamani ya sanar mata ya wanzu a nahiyar maharba, babban aikin da ke gabanta bai wuce ta gano wane ne tauraro na biyu da na uku da ke cikin masarautarsu ba domin tana gudun kada gaba allura ta tono garma. Ta san ɗayan tauraron cikin maharban shi kansa ba zai yi mata wuyar gani ba domin sannu a hankali za ta saka Sarki Damina ya riƙa salwantar da ruhinsu ɗaya bayan ɗaya. Ganin yadda Usaina ta bashi fuska ya sa shi jin daɗi domin idan bata ga dama ba hatta ɗakin akwai wurin da take yi masa iyakarsa. Don haka a daren ranar Usaina ta bashi haƙƙinsa musamman da ta tabbatar da ta bashi haɗin da Boka mai zamani ya bata ta tashi kuma ko kaɗan bai tambayeta ba balle ya musa mata, tamkar ajiya ya bata haka ya amsa hannu bibbiyu ya kafa kai ya shanye. Washegari sai da yamma ta yi sosai sannan ya saka Dakarunsa su fito da iyayen Kyauta, haka aka sake fito da su jama'a sai kallonsu suke yi. Suna ƙarasawa tsakiyar filin aka saki kiɗe-kiɗe da bushe-bushe, masu giya suka fito da ita suka riƙa sha suna tamɓele a wurin. Abin da ya ɗaure wa su Iyayen Kyauta kai bai wuce yadda suka ga duka al'ummar wurin sun yi ado da zanen fari da baƙi ba. Hatta Sarki Damina da Dogaransa duk sun fante jikinsu da baƙi da fari, sai da suka ƙura ido suka lura da cewa zanen jikin mutanen ba komai ba ne face zanen idanu. Kowannensu babu wanda ba ya zance zuci a cikin zuciyarsa, suna tsaye a tsakiyar rana aka kawo musu dafaffiyar jar dawa babu komai a cikinta. A yunwace suka ɗauka suna na ci kafin wani lokaci tuni sun cinye sakamakon dama ba wata ta kirki aka kawo musu ba, wani irin jan ruwa aka kawo musu kamar turɓaya. Shi ma ba su ɓata lokaci ba suka daka masa wawa, nan take suk shanye shi. Sarki Damina ne ya ɗaga hannu lokaci ɗaya mutunen wurin suka yi tsit, Waziri ya miƙe da wata sanda a hannunsa mai kan zaki ya fara kallon mutane ɗaya bayan ɗaya sannan ya ce, "Musha giya mu ji daɗi don yau ranar ido ce a gare mu babu wanda ya isa ya zura mana ido." A hankali Mahaifin Kyauta ya sake maimaita maganar ta shi don ko kaɗan bai fahimci komai a maganar ba, yana cikin nazari ya riski Wazirin ya ci gaba da cewa. "A yau ba za mu duba tsofaffin Bayi ba za mu ɗauki sadaukarwar idon babban dodo a wurin waɗannan la'anannun bayin maharban,
." Ya ƙarasa magana yana nuna wurin da su mahaifin Kyauta suke tsaye. Ilahirin jikinsu ban da rawa babu abin da yake yi, Waziri na rufe bakinsa ya ƙarasa wurin ya jango Mahaifin Gogo saurayin Kyauta. Sai da aka kai tsakiyar filin aka zaunar da shi a kan kujerar ƙasa aka ɗora kansa a kan hannun kujerar, wasu garadan Dogarai ne suka ƙarasa suka ɗaure hannuwansa ta baya sannan ya ɗauko kaifaffiyar wuƙa ban da sheƙi babu abin da take yi, saita ramin idonsa ya danna wuƙar da ƙarfi ya ƙwaƙwalo ƙwayar idonsa. Wani irin gurnani yake yi saboda azaba jikinsa na wani irin karkarwa kamar ransa zai fita, a cikin wani ƙoƙon kai ya saka ƙwayar idon sannan ya sake saka wuƙar ya ƙwaƙulo ɗayan idon sai kuma ya ɗebo wani ruwa mai koriyar kala ya zuba masa a ƙwayar idon. Daga haka Dakarun suka ɗauke shi aka wuce da shi ɓangaren makafin cikin gidan, wannan lamarin da suka gani ya sake ɗugunzuma hankulansu. Don haka wasu daga ciki suka riƙa zubda ƙwallah wasu kuma suna roƙon mutuwarsu kafin a ɗanɗana musu wannan ukuɓar. A karo na biyu Waziru ya zaƙulo Mahaifiyar Kyauta, ganin haka ya sa ta fashe da kuka mai tsanani tana ɗaga wa mijinta hannu, ko me Waziri ya tuna sai kuma ya hankaɗata ta koma, ya miƙa hannu ya janyo wata matashiyar yarinya da ba za wuce shekara goma sha uku ba. Tana kuka mahaifiyarta na riƙe ta haka Waziri ya fisgeta ita ma ba a ɗauki lokaci ba aka cire nata idanuwan aka wuce da ita. Bayan ita Wata mai tsohon ciki suka ɗauko ita ma sai da suka ƙwaƙwale nata sannan ya burma wuƙa a cikinta ya zaro jaririn da ke kwance a cikin cikinta. A daidai wannan lokacin ayarinsu Kyauta suka ƙarasa cikin filin manyansu da ƙanana, ƙura ce ta gauraye wurin saboda yawansu sakamakon tawagar dakaru biyu ce suka shigo. Yawan mutane da tashin hankalin da suka yi tozali da shi ya sa kowannensu ya sha jinin jikinsu, mummunan kamannin da danginta suka sauya ya sa ta gagara bambamce ainihin surarsu, sai dai a lokacin da ta gan su ta fahimci irin suturar yankinta ce. Lokaci ɗaya tunanin iyayenta ya faɗo mata hawaye ya ciko idanunta take tunanin halin da suke ciki, don a tunaninta ƙila tuni an gama da su.

Dum! Na ji kaina ya yi min tamkar an ɗora min dutse, haka kawai na ji hajijiya na neman ɗaukana har sai da na jingina kaina jikin sauran mutanen da ke tare da ni. A hankali na samu damar buɗe idanuna, ban yi aune ba na hango wata ƙasaitacciyar kujerar zinari daga can nesa da ni, Jarumin mazajen da ya saba faɗo wa rayuwata na hango yana kirana da hannunsa. Farin dokin ne ya fara takowa har ya zo gabana yana ci gaba da goga kansa a jikina, karon farko na kalli Kyauta sannan na ce, "Kyauta kina ganin farin doki a kusa sa ni?" A wahalce ta girgiza min kai ta ce, "Sai dai idan gizo idanunki suke yi miki amma yanzu haka muna wani wuri mai iya tsinka zuciya, na shiga tashin hankula kala-kala amma ban taɓa cin karo da makamancin wannan ba." Ina yunƙurin bata amsa na riski sanarwar mutumin da nake tsammanin shi ne mai mulkar wannan yankin bakiɗaya, sai da ya miƙe tsaye sannan na ji fara sanarwar da cewar. "A ware mini al'ummar Maharba ɓangare guda ba na buƙatar a haɗe su da waɗannan bayin da suka shigo wannan Daula tamu mai albarka yanzu." Tun bai rufe baki ba Dogarawan suka zabura da sauri suka fara yi mana iyaka da al'ummar da aka kira da Maharba. Tun da na ji ya ambaci haka na riƙa leƙawa koda zan samu na yi tozali fa mahaifana, duk da na aminta da zuciyata ba ƙaramar yaudarata take yi ba. Kwatsam! Kamar a mafarki na yi kwalli da su, kamaninsu duk sauyin yanayin da suka samu ba zan mance su ba. Iyayena da nake ƙishirwar gani, da su na yi tozali a lokacin da ganinsu ba zai yi mini amfani ba. Hawayene ke bin idanuna bibbiyu ya yin da na sake tabbatar da wanzuwar halitata tana da sanadi da ƙaddara wacce bawa baya taɓa tsallake mata. Ina cikin wannan yanayin na ji ya sake faɗin, "A kunkunce wannan tagawar sannan a zaɓo mini kyawawan ƴanmata daga cikinsu, a wannan ranar ba zan kira Yarima ba domin ya fi ƙarfin gabaɗaya waɗannan ƙasƙantattun don haka a zaɓi nagartattu sha biyar a tura masa su." Babu musu suka aiwatar da abin da ya umarce su, suka shiga kwance mu nan take daɗi ya mamaye zuciyata ko babu komai za mu samu hutun ɗan taƙaitaccen lokaci. Hannun Kyauta na riƙe muka riƙa kutsawa tsakiya don kada su ɗauki ɗaya daga cikinmu domin tun da na ji an ce za a kai ƴanmata wurin Yariman Daular na san ba abin kirki zai aikata mana ba, ina daga lungu ina hango yadda ake fitar da ƴanmata mafi yawa daga cikinsu iyayensu na jansu suna ihun rabuwa da su. Ban yi aune ba na ga wani Gabjejen Badakare ya fisgi hannin Kandala, a hargitse na yi kukan kura na cafko hannunta ya fara fisgarmu tare. Yana ganin ina jan hannunta ya ƙaraso a fusace ya ɗauke ni da wani irin gigitaccen mari wanda zafinsa ya sa na kife a katsa tare da jaririn hannuna, cike da azaba ya tsanyare da matsanancin kuka. Inna wuro ce ta ƙaraso wurina ta karɓe shi ina yunƙurin tashi ban yi zato ba na ji ya dawo ya fisge ni, ya hankaɗa ni da ƙarfin gaske. Kandala na ganina ta rugume ni tana kuka ni ma ban da zaɓi da ya wuce na zubda na wa hawayen, muna cikin wannan yanayin na ji Badakaren nan ya kwarara ihun da ya sa idanunmu suka koma kansa. Zaro idanuwa na yi cike da fargaba abin da na gani, gefen fuskarsa ce ta hau daddarawa haka kawai kamar ana yaga tsuman zani. Wani abin mamaki ɗaya ɓarin wurin babu abin da ya same shi. Ganin yana neman hautsina wurin ya sa Sarki Damina ya tura wasu daga cikin Dogarawansa suka kai shi turu (Gidan mahaukata.) Da kansa ya ƙaraso wurinmu ya fara zaɓar ƴanmatan da za a kaiwa yarima, ba zato na ga ya sa da ni a ciki wanda za a kaiwa Yarin, hakan ya sake sabbaba mini kaɗawar hanta. Mu goma sha biyar ya wara daga cikin waɗanda aka zaɓa sai ƴanmata biyar da na ga ya lissafa daga ciki har da Kandala. A gaban dubbanin jama'a babu kunya maganaina suka hango min yadda ya fara kai hannuwa jikin su Kandala yana taɓa al'aurarsu. Duka babu wacce bai kai hannu jikinta ba sannan ya bada umarni da akai masa su can gidan shaƙatawarsa da ke bayan gari. Mu kuma ya sa aka tarkata mu aka wuce keɓaɓɓan gidan Yarima da mu, tun daga tsakar gidan Dakarun suka yi ta tsige mana suturar da ke jikinmu. Tamkar dabbobi haka suka tura mu cikin ɗakin da na hangi wani matashin saurayi na zaune ya kifa kansa da gwiwa, jin motsinmu ya shi ɗagowa yana zaro idanu haɗe da kallonmu ɗaya bayan ɗaya. Ban yi mamakin ganinsa ba domin fuskarsa ba baƙuwa ba ce a wurina, sai dai na yi mamaki a tsawon shekarun da ya shafe yana ziyartar duniyata da bai sanar da ni yana da alaƙa da wannan Baƙar Daular ba. Dama shi ƴan biyu ne bai sanar da ni yana da wani ɗan'uwan ba? Idan haka ne kenan yana da alaƙa da zuwanmu wannan azzalumar Daular, ya aka yi na bar shi a filin can na sake riskarsa a wannan ɗakin har na ji ana ambatonsa da sunan Yarima? Ban gama jerawa zuciyata tambayoyi ba balle na bawa kaina amsa na ji ya yi kukan kura ya fisgi ɗaya daga cikinmu ya fara biyan buƙatarsa da ita, kuka nake mai tsuma zuciyar mai sauraro tausayin kaina ya mamaye zuciyata. Yana gama amfani da ita ya rufe ta da duka kamar ya samu jaka har sai da ta daina motsi. Haka ya bi mu ɗaya bayan ɗaya yana amfani da mu, wanda ni ce mace ta ƙarshe da ya keta wa haddi ya raba ni da martabata ta ƴa mace. Tun yana jikina na ji ya fara wani irin munshari mai ban tsoro wanda haka ne ya tabbatar min da bacci ya ɗauke shi, da ƙarfi na ture shi na koma gefe ina ci gaba da hawaye. Dakarun da suka kai mu ba su suka zo suka kwashe mu ba sai da dare ya tsala sannan aka ɗauke mu aka kai mu wani ɓangare wanda na ji suna kira da, ƴantattun bayi. Wani abu da ya tsaye mini a rai bai wuce yadda komai na Yarima yake min kamanceceniya da Jarumin da ke ziyartata ba, sai dai lokaci ɗaya tsanarsa ta mamaye zuciyata na ji danasanin shigowarsa rayuwata. Gari na waye da shi na yi tozali a tsakiyar kaina ina yunƙurin magana na ji ya furta min, "Kada laifin wani ya shafi wani domin kin san kama da wane bata wane." Bai jira cewata ba ya ɓace min da gani, a hankali na miƙe ina zagaya lungu da saƙon wurin tafiyata keda wuya na ji Dogaran Sarki sun zo da shelar kiran gaggawa da Sarki Damina yake yi ga waɗanda aka kai ɗakin yarima.

Wannan shine shafi na biyun ƙarshe na free pages. Hajiyata kada ki bari a yi wannan tafiyar domin wasan yanzu ya fara ɗaukan zafi💃🏼 Wai ko dai Yarima ya warware ne🥵🤣😂

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

Last free page 10

🥳 in ka ji busa tabbata Sarauniya ce ta ƙaraso, ina kuke matan ƙwarai, mata ba muna mata ba, shin kin jaraba kayan *HONEY-DROPS* me kike jira har yanzu?, Manyan mata, mata masu aji na ta dafifi wajen kwasar kayan gyara, me ya sa za ki kashe kanki da ƙuruciyarki, ko tsohuwar ma na zuwa karɓar nata, kina fama da matsalar bushewar gaba, ɗaukewar sha'awa da ni'ima, ƙaiƙayi ko ƙurajen gaba, jin zafi yayin tarawa da maigida, sanyi ya taɓa miki mahaifarki?, Kina ta allura da shan magunguna ba su miki aiki ba, wane kalar infection kike fama da shi?, Staphylococcus, Gonorrhea, Syphilis, UTI, STDs ne?, Share hawayenki kukanki ya ƙare je ki nemi *HONEY-DROPS INFECTION FLUSHER* ke da sanyi sai dai ki ba da labari, kin gama cacar kuɗi, cikin kwana uku zaki fitsarar da duk wani sanyi da dattin da ke tattare a mararki, ki gyara zamanki gidan aurenki don sanyi kashe mace yake har buzunta, duk wani magani da za ki sha muddin da sanyi a jikinki iyakar shi cikinki, ba zai sauka ba. Magani ne ingantacce made of herbs, In kin gama da wannan akwai na gyaran other room, akwai Exclusive Gumba ta manyan mata ke nan, ko matar Gwamna ita take sha, ga Gumbar babbar mace mai tada tsohuwar soyayya, akwai fa tsuumi na matan gaske, akwai *HONEY FLOOD TSUUMI* kan ƙiftawar ido ni'ima ta yi ta kwararo miki, akwai BUJENTA JAGAB, da Tsuumin Ɗafau, daga jin sunan kun san akwai zance na bar muku ku ƙarasa, akwai sauran kaya masu zafi🔥

Muna da bridal package

Diamond - 100k
Gold - 50k
Silver - 30k

Ga kuma na postpartum (wanda suka haihu don dawo da martabarsu)

Diamond - 50k
Gold - 30k
Silver - 15k

Kuna iya samun mu ta 08167888934, ko 08067770852



Ba ƙaramin ruɗu da tsananin mamaki ya shiga da faruwar lamarin, a saninsa duk rana kamar wannan matuƙar ya miƙa kuka da buƙatarsa ga Sarauniya Shakundum tana share masa hawaye ta hanyar amsar buƙatunsa. Koda ta daina yin magana amma akwai alamun da yake ji na amsar addu'a da roƙon nashi. Miƙe wa ya yi tsam daga wurin da yake ya fara kai kawo a cikon kogon dutsen cikin mamaki, bakin wani baƙin kasko ya tsugunna ya ɗebo garin sihirtacciyar bishiyar kukar da ya taɓa aika wani ɗan autan aljanu ya ɗebo masa a dajin Buzurul-shusu. Barbaɗawa ya yi da zummar ya ga ainihin abin da yake faruwa da Gunkin Sarauniya Shakundum, kasancewar a ƙa'ida idan har Almuru ya yi babu shi babu ziyartar muhallin Gunkinta. A maimakon komai nata ya bayyanar masa sai gani ya yi wutar ta ɗauke, ya gwada haka ya fi a irga daga haka jikinsa ya ba shi tabbas akwai wani sabon al'amari da yake faruwa. Don haka a gaggauce Boka mai zamani ya ɗauko madubih sihirinsa yana karkatar da shi kusurwar kudu ya fara karanta waɗansu irin ɗalasuman tsafi tun bai ƙarasa ba ya ga jini ya ratsa ta jikin mudubin yana ɗiga. Da sauri a jiye saboda sababbun al'amuran da yake gani masu rikita lissafi, ko tunanin me ya yi sai ya sake ɗauko mudubin yana bincike game sauran al'amuran da ke faruwa a cikin Daular. Tamkar an saka masa hoto a majigi haka ya riƙa ganin duk abin da yake faruwa, yana sake karkata mudubin zuwan binciken Sarauniya Shakundum kamar wancen karon haka ya sake ganin jini na ratsowa ta cikin madubi. Yana nan zaune yana ganin abin da yake faruwa sai ganin wata ƙanƙanuwar wuta ya yi harshenta na ratsowa ta tsakiyar madubin, ruwan tsafinsa da ke ƙoƙon baƙin ƙarfe mai ɗauke da waɗansu irin zanen baƙaƙen aljanu ya ɗauko ya watsa. Amma abin da ya sake tsinka hanjin cikinsa yadda ya ga wutar ta taso masa gadan-gadan har sai da ta fara lasar naman jikinsa. A firgice ya riƙa ɗaukan abubuwa yana jefawa don ya samu wutar ta mutu amma kamar ƙara mata makamashi yake yi, babu shiri ya ƙarasa bakin wani gajeren kabari ya ɗebi ƙasar saman kabarin a tafin hannunsa. Nan take ya fara kiran sunayen aljanu, sai da kira sama da goma sannan ya rufe idonsa yana kiran Aljanu Gagare, ya jima yana abu ɗaya sannan Aljani Gagare ya bayyana tare da faɗin, "Me yake tafe da kai a tsohon daren nan ya kai wannan tsoho mai surkulle kala-kala?" Bakin Boka mai zamani na rawa ya furta, "Ka taimaka min Ubangidana Kogon tsafina ya kama da wuta sha'anin Sarauniya yau ya zo da wani irin salo." Yana rufe baki Aljanin ya bushe da dariya mara daɗin saurare sannan ya ce, "Wannan wajibi ne a gare ta domin matuƙar kiɗa ya canja dole rawa ma ta canza. Sarauniyar da ka sani a baya ta bambamta da ta wannan, don haka ka yi takatsantsan wurin tsaurara bincike a kanta idan ba haka ba watarana za ka nemi rayuwarka ka rasata gabaɗaya." Ganin wutar na sake ruruwa ya sa Boka ya ce, "Na

Please Login or Register in order to submit comment